Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 39

Batuol mamman complete novel - Chapter 39

Batuol mamman complete novel Chapter 39: Batuol mamman complete novel Chapter 39. "Kayan masoyi ai naki ne...ke da kuke sharing spoon meye don ya saya miki…

3,373 words

"Kayan masoyi ai naki ne...ke da kuke sharing spoon meye don ya saya miki maltina?"

Bata sake iya magana ba taji kunya ta koma ta zauna shiru har suka isa. Ita bata taba zuwa gidan ba. Su kuma rabon su da zuwa tun bikin Ghazalatu farkon tafiyar Awwab Ukraine. Su ne a gaba ita a karshe suka bi bayan mazan zuwa cikin gidan.

Zahra ke ta sallama shiru ba'a amsa ba. Mai aiki ce ta leko daga baya lokacin Awwab ya fara jin haushin zuwan nasu tace su shigo Mummy tana sama za ta yi mata magana.

"Kice mata su Zayyana ne" Zahra tace su duka suka sami wuri suka zauna a falon da mai aikin ta kaisu.

Muryar mace tana kuka suka ji wata tana daga murya "Mummy ba fa zan koma ya kasheni ba"

Kafin Mummy Gambo tace wani abu mai aikin ta fada mata suna da baki.

"Su waye?"

"Wai su Zayyana"

A dan tsorace tace "ba dai falon kasan nan kika kawo min su ba ko"

"Mummy ke kika ce nan zan rinka kawo bakinki"

Ranta a bace kamar ta kai mata duka ta fasa tana huci. Karshenta sun ji hargagin Ghazalatu. Tsaki tayi tace ta kai musu abin sha tana saukowa. Bayan fitarta ta koma kallon Ghazalatu da ta rame tayi baki kamar ta dade tana cuta. Ga fuska a kumbure. Ido daya yayi ja jini ya kwanta.

"Sami wuri ki kwanta zan kira Hussaina idan sun tafi ba aura masa ke akayi don ya kasheki ba"

Cikin takun kasaita ta sauko ta ga falon nata a cike. Duk yadda taso daure fuska kasawa tayi tana ganin Jawad da Femi suna ta kai kawo babu mai shekara biyu cikinsu amma duka akwai girman jiki da lafiya. Iyayensu sun gaisheta harda Radhiya da bata gane ba ta dan saki fuska tana yiwa su Jawad wasa.

"Yaya Mamin taku kowa lafiya ko?"

Zayyana ce ta amsa da "lafiya kalau"

"Madallah, ku masu gida ina cefane ko haka kuka zo min hannu na dukan aljihu?"

Dariya ce su Fauziyya ke yi ta yake kowa ta ciki na ciki yadda ta yiwa Maminsu rashin mutumci musamman da bikin Ghazalatu.

"Awwab yaushe a gari? Yaya aiki?"

"Shekaranjiya muka zo da Zahra. Ga mijinta Raji"

A ladabce Raji ya sake gaisheta don Yarbawa akwai ladabi sosai. Kyakyawan mutum a haka harda dan gemunsa na ustazai amma ita ce mai yadawa a dangi cewa Zahra ta rasa miji an buge da auren bayerabe. Sai gashi a gidanta ido ba mudu ba yasan kima tasan cewa babu tsiya a tare dashi. Kyakkyawar yarinyar da take ta wasa da Femi ta kalla "wannan fa, bakuwa kuka yi?"

"Radhiyan Hamma Awwab ce" Fauziyya tace kai tsaye lokacin da Ghazalatu take saukowa. Ita da Mummyn suka zuba mata idanu sai ta basar duk da ta sake takura ta koma gaishe da Mummyn.

Ghazalatu kamar ta juya ta koma don bakinciki. Radhiya dai da ta sani 'yar kauye mai askakken kai ce a haka kamar wata balarabiya. Murmushin da Radhiyan tayi tana kallon Awwab shi ya gaskakata mata ita saboda wannan dimple din nata. Mayar mata da martani yayi har yaso ya manta a ina suke.

Kishi fal a cikin Ghazalatu ta kalli Awwab yadda ya sake zama babba ga cika ido. Sai zaman ya koma na kurame tunda akace Daddy Haroun baya nan. Mummy tana hango wautarsu Ghazalatu tana jin takaicin rabasu da Mummyn tayi. Nura dukanta yake kamar jaka idan Mummy tayi magana sai Hussaina tace Ghazalatun ce bata da tarbiya. Kudi ne suka so tatsa Mummy taki saki shiyasa suka dorawa 'yarta karan tsana. Drinks aka kawo harda maltina amma Radhiya ta kasa sha musamma da Ghazalatu ta rinka jan Awwab da hirar aiki da course da taji yaje Ukraine.

"Muna jiran tsarabarmu"

Tausayi take bashi yana son tambayar me ya sami idonta yana tunanin kada ya bata kunya sai yace "zan kawo miki kafin ki koma KT. Bari mu wuce muna sauri ne"

"Da wuri haka Awwab ina zaku je, zaku dawo ku gaisa da Daddy ko"

Fauziyya ce ta sake cafewa "gidan abokin baban Radhiya"

Ghazalatu tace "a nan din? Nufina a Abujan nan? Cikin Nyanya hala"

Cin fuska Awwab ya hade rai Zayyana ma da abin ya bata haushi tace "gidan gwamnan Plateau a Asokoro"

Mummy sai ta hangame baki tsabar mamaki. Kai gidan gwamna ai da mutane kila dai maigadi ko irin gardiner dinnan.

"Hamma kafin ya fara kira yace ya jimu shiru. Kasan halinsa da yaji Radhiya tazo Nigeria ya rinka damuwa kenan"

Sakato Ghazalatu tayi tana kallon su "ba a Nigeria take ba?" Tace da mamaki Radhiya kunya ta kamata yadda su Zahra suke jindadin abinda suke yi musu.

"Kakanta ya kaita France ai can take karatunta"

Awwab kasa jurewa dramar matan yayi yace su fito haka. Harabar gidan Mummy ta rakosu tana takaicin me ya rabata da yayarta mai sonta da zuciya daya da yaranta. Ta dawo daga rakiyar Hussaina amma kunya harda ta Ummansu ta kasa fadawa kowa halin da ake ciki.

Suna mota Fauziyya tace "dalla muna ta wasa ki maimakon ki turance su ko kiyi french ke da Yousuf tunda ba kowa ke jinsa ba ki tada hankalin 'yan bakinciki"

"Naga alama kin fini rigima yanzu Adda"

"Hmmm ai dole bakina ya bude in fada miki 'yan mata sun saka min miji a gaba da waya. Shi kuma ya fiye shiru shirun wai wulakanci babu kyau. Tuni na mike kafin ya dauko min qaya"

"Su Fauziyya an iya kishi"

"Allah Yasa my in law ya kyallo wata idan kunje garinsu"

"Ba amin ba"

Radhiya da Zayyana suka rinka dariya yadda yayyen nasu ke fadan sakuwa da sakuwa.

An san da zuwansu gidan Excellency suna isa aka bude musu gate. Cikin girmamawa aka kaisu falon matar gidan. Bata da ji da kai kamar mijinta ta rinka jansu da hira tana fada musu me yiwuwa fa sai sun dawo cikin sati saboda jibi Excellency zai taho.

"Munyi waya nake ce masa zaku zo yace gobe yana son ganinka da wuri Awwab wai akwai important issue da zakuyi discussing"

"Ko maganar Arifah ce" da yake ta nuna sha'awar zuwa Ukraine masters yace sai ya tambayi Awwab yanayin kasar.

Radhiya sai ta zaci ko maganar hadin aure ce kishinta ya motsa. Suna haka Radhiyan ta shigo tabi matan nan kowacce ta rungume tana murnar ganinsu.

"Ashe duka kunzo babu gayyata. Mom kinga ni nake son zumunci dasu basa nemana. Captain ne nawa shi kam bama kwana uku bamu gaisa ba"

Ta sake kunna Radhiya bata sani ba. Wancan karon Ghazalatu yanzu kuma Arifa. Itama haka zai zo yace ta hakura ya fara aurenta? Zaman sai taji ya isheta so take su tafi kawai. Tana kallo suka tashi suka bi wata kofa Mom dinta na cewa dama an dade ba a hadu ba yau tasan zasu sha hira ne.

Haushin kowa ta rinka ji harda su Fauziyya. Basu dade ba suka dawo ta fada masa ne Excellency ya karbi nambar wayarsa a wurinta yace zai kira shi kada yaji waya bazata ya dauka wani abu ne. Suna dawowa yace zasu tafi Mom ta hada kowa da gift tana ta godiya.

A jikin motar da matan suke Arifah tace musu gobe idan suna da lokaci me zai hana su je park. So take su saba da juna sosai. Zahra ta amince ko don mijinta mai zuwa camping a filling station.

********** [5/22, 11:03 PM] Sis Ruky: Mamaki sosai yayi da aka sanar dashi bakon nasa yace da sakatariyarsa tayi sauri ta shigo dashi duk da cewa ya gama shiri zai tafi gida ne lokacin tashi yayi. A bakin kofa ya tsaya ya tarbe shi yana murmushi suka kama hannuwan juna suna gaisawa. Kowannensu sanye yake da manyan kaya da babbar riga. Kana ganin bakon kasan naira ta zauna da kyau. Daga hularsa har zuwa takalmi babu wani abu da kudinsa yake kasa da dubu ashirin.

"Alh Salisu wai kaine nake gani ko dai mafarki nake yi?"

"Tuba nake Alh Musa ni din mai laifine a wurin mutane da yawa. Nine da kaina ba sako ba na yakice ayyukan gabana nace sai nazo"

Alh Musa ya nuna masa wuri ya zauna sannan ya tashi ya kira sakatariyarsa ya soma fada mata me zata hadow bakon ya dakatar dashi.

"Kada ka damu kanka a koshe nake."

Zama ya sake yi suka kuma gaisawa da tambayar juna bayan rabuwa.

"Yara suna dakunansu ko?"

"Wallahi kuwa"

"Naso zuwa daurin auren nan amma wallahi Musa zama a wuri daya na sati gagarata yake yi"

"Ya fa kamata ka sassautawa kanka Alh Salisu. Mutum yana fafutukar neman kudin nan fa kawai sai mutuwa ta riskeshi. Sai ya laluba ya ga babu wani abin arziki da ya tara sai wahala. Shiyasa ka ga na makale wuri daya yanzu"

"Mtsww ni zan fada maka yawon nan baiyi ba ko kadan. Amaryata fa mai aiki ta kama da dreban da na daukar mata a cikin gidana don bala'i"

"Subhanallahi garin yaya haka ta faru?"

"Kaima ka sani ai, cewa tayi bana zama bani da lokacinta. Inda na gode Allah bamu haihu ba da ta saka ni wasiwasi"

"Ka chanja tsari Alh Salisu. Girma sai dada kamamu yake yi da kunya irin wannan na fitowa daga gidajen aurenmu. Ai kamata yayi ace macen kwarai ko bata sonka ta san kiyaye addini da darajar kanta"

Daya daga cikin wayoyin Alh Salisu ce tayi kara ya kasheta sannan yace "ka tuna Halifa ai babban dana. To mahaifiyarsa wallahi ita ta cire min son mata gabadaya shiyasa bana damuwa da zama dasu tunda nasan kudin ne ya kawosu sai na basu kawai. Da bamu rabu ba ina mai tabbatar maka ko zanyi yawo ba kamar yadda nake yanzu ba. Sannan mafi yawa tare zamuyi gani gata"

"Kace kun zuba soyayya" Alh Musa ya fada da dariya.

"Wace soyayya? Matar da ta aureni alhali tana son mijin kanwarta. Kaji fa kanwa da suka hada uba kuma bata iya boye min. Kishi take da kanwar abin babu kyaun gani. Shiyasa da na saketa bayan abin ya fito da mijin kanwar ya rasu ko shi Halifan bana bari yaje wurinta sosai"

"Amma kuwa kayi kuskure Alh Salisu wa yake raba da da uwa banda abinka? Nima nayi irin auren nan amma wallahi Zainab 'yar halak ce. Ka tuna kazo daurin aurenmu. Ita dole aka raba auren mijin ya sami paralysis ga rashin magana amma ta kafe sai ta zauna dashi. Kasan Allah ko zanyi rantsuwa bani da kaffara tunda na aureta Zainab bata sake zuwa Kano ba sannan ko a bayan idona idan tayi waya da danta bata taba cewa ina mahaifinsa. In karkare maka zance na saketa kuma mijin ya sami lafiya. Aisha ma ta kirani wai ta haihu...kai kaji kudura ta Ubangiji"

Sosai Alh Salisu yaji dadin shawarwarin Alh Musa don gaskiya yasan bai kyauta ba. Kasuwancinsa ya bunkasa sosai amma zumunci dai bashi da lokacinsa. Yana China babansa ya rasu haka yana India babarsa ta rasu da kyar ya roki yayyensa aka jinkirta jana'izarta. Kudi dai danginsa sun warke amma ganinsa yayi wuya.

"Nagode Alh Musa, zan gyara don ina komawa zansa a kai Halifa Sumaila wurin babarsa da kakaninsa. Bai saba da kowa ba sai ni. Cikin gidan ma kannensa ba shirginsu yake shiga ba ni kuma ban damu ba ganin duka mata ne"

"Matan idan babu kai ba shine gatansu ba?"

"Hakane, sai ka tuna min da abokaina na kuruciya da duka na watsar da kace mijin matarka na da yana da paralysis. Akwai aminina soja ne a yaki ya kamu da wannan lalura. Sau biyu naje duba shi shikenan kamar wani sallamamme na dena waiwayarsa. Daga baya kunya da nauyin jinkirin yasa na kasa zuwa kuma"

"Tunda kana da rai ai babu wani jinkiri. Itama Zainab din mijinta fa a yaki ne tasa lalurar sunansa Hadir"

Alh Salisu sai ya gyara zama da kyau "Hadir Murtala mutumin Kano?"

Da mamaki sosai a fuskarsa yace kwarai kuwa "shine aminin naka?"

"Shine Alh Musa wallahi shine. Ina zuwa Kano gidansa zani...ni kam kudi naga sharrinsa tunda ya nesanta ni da makusanta na"

Alh Musa yayi matukar mamaki. Da Alh Salisu ya rike zumunci da Hadir bai kwashi wadannan shekarun a kwance ba. Kudi ne dashi fa na ban mamaki don shi a haka bai kama kafarsa ba. Duniya komai sai Allah Ya nufa amma sakacinmu ke janyo mana. Adireshin gidansu na Abuja ya nema wurin 'yarsa ya bashi.

"Daga nan ni sai birnin tarayya inji mutanenmu."

Godiya mai tarin yawa ya yiwa Alh Musa sannan ya koma katon gidansa dake garin Port Harcourt din. Halifa ya kira yace masa ya shirya gobe ya taho Abuja. Bautar kasa zai fara dayake a turai yayi karatu ya gama da wuri. Sake tunani yayi na tuna cewa yaron da kannensa ma babu shakuwa yace masa dashi da kannen nasa mata ne su hudu su taho tare. Sai kuma ya kira matarsa uwar uku cikin yaran Farida, Husna da Meena. Dayar mai bin Halifa a jerin haihuwa Hibbah tata maman ta dade da fita itama ya fada mata tace yaran su shirya. Baiwar Allah har ranta taji dadi yau da kansa yana wani garin yace a tura masa 'ya'yansa kuma wai kuma su da Halifa. Bata taba kin yaron ba duk miskilancinsa da shiru shiru. Irin 'ya'yan baba dinnan ne sangartattu amma ba wai ya lalace da dabi'un banza bane sai son jiki.

Halifa yaro ne sa'an su Ibrahim sai dai ya fisu duka girman jiki. Ga tsaho kuma da 'yar kibarsa daidai misali ta hutu da jindadi. Bashi da matsalar komai a rayuwa sai mahaifiyarsa Salame. Duk kudin babansa yafi ganewa ya saya masa abubuwan bukata ya bashi kadan kawai don kada ya kai mata. Ita kuma da zarar ta ganshi tamkar ta ga nama ta rinka bani bani kenan. Ga matsalar muguwar kazantar gidanta ko yawu baya iya hadiya idan yaje. Kannensa na gidan idan suka yanyame shi ya rinka yamutsa fuska kenan. Daya kanwar tasa wadda Salame ta auri babanta farkon mutuwar aurenta bai fi sau biyu ya taba ganinta ba. Itama nata baban sai a hankali babu kudi amma dai bata da roko, sunanta Rahima. A haka itama bata huta da bani banin Salame ba idan taje gidanta idan tace babu ta hadasu ita da mahaifin nata da danginsa ta zagesu su tas. Yarinyar da iyakarta secondary don ma tana sana'ar kunshi da abin sai ya fi haka mun.

Washegari Alh Salisu da 'ya'yansa suka sauka a gidansa na Abuja yace su huta ana magariba zasu je gidan abokinsa.

**********

A can Jos Excellency bai huta ba Chibuzor bai huta ba. Bincike da tambayoyi yasa ake ta yi masa sai yau ya gama samun duk wata shaida da zata tabbatar masa cewa Chibuzor ba dan aiken 'yan hamayya bane sannan ba wata damfara bace ta kawo shi. Hankalinsa in yayi miliyan to a tashe yake da yasa shi a gaba yana bashi labarin rayuwarsu a kurkuku. Abu dai sai da ya kai Gwamna da zubar hawaye. Duk wani aiki da yake gabansa yasa an dakatar dashi domin ya samu yayi aikin Zayyan kawai. A ka'ida Major Mustapha da Hadir ya kamata ya nema amma sai ya tuna cewa yadda suka yi zaton Zayyan ya rasu haka shima yayi wannan tunanin. Abinda yaga yafi dacewa shine yaje ya kawo Zayyan Nigeria ya dangana shi da iyalinsa. Shawarar tayi masa, shi kadai bayan sunyi waya da matarsa akan zuwan su Awwab gidan ya sake shawarar gara ya tafi dashi ayi komai a gabansa har zuwa dauko shi.

Da wannan shirin suka kwana gobe zasu tafi Abuja shi da Chibuzor hedikwatar sojoji dake unguwar Garki. Mukaminsa na Gwamna kuma tsohon soja yasa tun a daren da yayi waya ya nemi ganawa da Chief of Army Staff Lieutenant General Enejo Adaji mutumin Kogi aka saka masa appointment din karfe biyu da rabi na rana.

Dukkan wata kulawa da ta dace da bako mai mahimmanci ita ake yiwa Chibuzor. Emma tayi murna sosai da ya fada mata yadda komai ya kasance. Da safe suna tashi da wuri aka dangana su da filin jirgi. Convoy din Excellency dama a Abuja suka kwana. Arifah da Mamanta sai ganinsa suka yi da bako kuma ko minti talatin basuyi a gidan ba suka wuce Nigerian Army Headquarters.

Bayan 'yan gaishe gaishe irin na manyan mutane Rtd Col. Nasiruddeen ya gabatarwa da Lt.Gen Enejo da Chibuzor da bayanin da yazo dashi.

Hankali a tashe Chief din na army staff ya soma buge bugen waya aka hau bincike a bangaren aiki da na'ura mai kwakwalwa akan waye Chibuzor Kalu, asalinsa da sana'arsa domin a tabbatar da ingancin zancensa. Yaga tasku ranar duk da babu duka amma fa an kaishi dakin bincike ace wannan ace wancan duk don su ji ko zai chanja magana idan bashi da gaskiya. A bangare guda kuma an binciko files din sojojin da aka tura Liberia daga Giginya Army Barrack na Sokoto a shekarar 1993. Zancen gabadaya an saka shi a jerin CLASSIFIED INFORMATION ba kowa ya sani ba sai mutane kalilan. Sunci karfin bincikensu washegari zasu nemi sa hannun shugaban kasa domin ya bada izinin ganawa da gwamnatin kasar Liberia. Excellency dai yayi ta rokon a gaggauta komai don a matse yake da yaga an fiddo Zayyan Tureta daga kasar nan.

*********

Alh Musa ne ya kira Ibrahim ya fada masa bakin da zasu yi yace ya sanar da mahaifinsa. Gobe zasu taho shi da Emzee. Ya gama jarabawa da kwana biyu kenan ya tsaya jiran Emzee su taho. Bayan ya fada masa shine ya kira Mama ya fada mata. Mamaki kwarai kuwa ya kamata ta sanar da Baba Hadir. Shi din ma mamakin yake. Yaushe rabonsa da Salisu, har ya manta. Rubutawa Mama yayi cewa ta fadawa Ummi tunda a iya saninsa akwai haihuwa tsakanin yayarta Salame da Salisu.

Itama tayi mamaki sosai nan fa suka hau shirin tarbar baki tunda ance shi da yaransa ne. Mama da Ummi suka yi ta mamakin wai yau Salisun da ko ita Ummi da ya taba auren yayarta rabonta dashi tun gaisuwar Zayyan. Halifa kuwa zata iya kirga sau nawa yaje gidan Malamijo tun tana makauniyarta.

Sun shirya komai a gidan Mama suka tafi yin sallah. Awwab, Yousuf da Raji basu wuni a gida ba ya kaisu ganin gari suma sai magaribar suka dawo.

Motocin biyu su Alh Salisu suka yi shi da 'ya'yansa. Daddy yaje gidan Daddy Haroun sada zumunci da magana akan halin da Ghazalatu take ciki a gidan Nura da ya fada masa. Shawara yake nema akan yadda zasu fadawa Alh Baba kada rigimar ta wuce yadda take yanzu don Gambo da Hussaina harda zage zage tsakaninsu. Rufa rufa suke yi kowacce bata son fitar da maganar kada aji ayi musu dariya.

A kofar gida Baba Hadir ya taresu suka karasa ciki shi da yaran. Zayyana ta tafi bangaren Mami da Hibbah wata uwar surutu da karadi irinta. Yanzu take SS3 saboda haka hirar ta 'yan mata ce masu tashen girma. Kanenta su Husna suna can suna fadan daukar Femi da Jawad suna ta musu wasa. Dukkansu son yara garesu kamar su daukesu suke ji. A falon gidan Mama su Zahra sun gaishe da Alh Salisu suka koma bangaren Ummi a falo suka dasa tasu hirar.

Baby Zayyan Ummi ta mikawa Alh Salisu yace "Mairama ko ina da bakin wanke kaina a wurinki da Hadir? Duk wani rikicin gadonku bani mantawa anyi dani haka lalurar Hadir amma neman kudi ya hanani yin abinda ya kamata. Tabbas ba karamar kunyarku nake ji ba ko ban taba auren Salame ba a matsayinki na matar Zayyan baici ace na yanke zumunta daku ba"

"Komai ya riga ya wuce sai dai mu fuskanci gaba. Kurakuranmu sai muyi kokarin mun gyara saboda kada yara su tashi basu san juna ba"

Halifa ya kalla da yake zaune ya karbi babyn yana masa wasa "Halifa wadannan duka iyayenka ne saboda haka a rike zumunci"

"In sha Allahu"

"Ina Ibrahim ne da Zayyan?" Alh Salisu ya tambaya.

Mama ce ta masa bayanin suna makaranta amma zasu taho gobe. Sai Radhiya da ya gani cikin matan da suka shigo dazu.

Awwab dasu Yousuf da suka dawo sun shiga bayan sun gaisa dashi Mama tace ya nunawa Halifa bangaren Ummi ya gaishe da Nasara tunda can zasu koma cin abinci.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull