Kenza eBookz

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 12

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 12

Cheaters club book 2 complete novel Chapter 12: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 12. Me gadi na bude mata gate ta shigo sede bata kai ga wajen…

3,374 words

Me gadi na bude mata gate ta shigo sede bata kai ga wajen parking motoci ba ta aje motar Zata dauki make up purse dinta sai taga sabuwar heneikan bootle akan seat tasan inta shanye zai mantar da ita komi so she just picked it subcontiously batare da ta damu ba.

Main entrance na mansion din nasu ta nufa looking soo hurt to the point dat she just want to pass her self out.

Tana bude kofa bata tsaya a koina ba ta haura can sama cikin babban Dakinta inda ta gama musu decorating hawaye cike a idonta taturo kofar kamar me aljanu at same time ta doshi gaban madubinta da sauri ta aje kwalban giyan akan table ahankli tanamai sauke zazzafar numfashi.

Hannayenta duka biyu ta dora akan table din tabi ta sunkuyar dakanta kasa hawayenta masu sanyi suna zubowa yarr kamar an kunnasu.

Alkcin sai taji wayarta yay kara har sau biyar cikin dauriya tabude lumsashen idontan ahankli snn ta mika hannunta ta dau wayar ta bude taga notifications daga shafikan fans din din Femi.

A karo na farko ta dauka shirmen post ne da aka saba sai wani abu yace mata ta duba dai tana budewa kuwa kirjinta ya bada sautin bindiga darammm ayayin da idanunwanta caraf suka sauka akan hadaddun hotonan da akayi ma femi a spa lkcin da ake shiryashi zaije wajen chief yay masifar kyau hotonan sunkai takwas each caption with #love wins, #Alpha# Prince #Best Day #happy birthday to us❤️ sai video guda daya da femin ya turo ma fans dinsa a lkcn yana gidan chief tare da chief din kafin su yanka cake, femi ya rike camera akaan fuskarsa yanata zuba yana zuga chief, shikuma chief din dariyarsa kawai ake ji acikin videon ba agan fuskrsa ba sabida bai saka kaya ba.

hannunta na rawa Ta bude coment section taga mutane da so many tags sunata tambaya a inane zasuyi shagalin birthdayn?...

Abun ya bata mamki da takaici makura, bata san lokcin da ta aje wayar akasa ba ta dawo jikin madubi ta kalle kanta tafara tuna irin lokcinta data bata, da uban kudin data kashe, da Abincin data zauna ta dafa dakanta sabida dashi, da dukkanin hopes dinta na kawo karshe wa matsalokin rayuwar aurensu ayau din, she sees her dreams being crushed bcos of one stupid birthday. Extreme anger yafara running tru her veins a haukace ta yi watsi da kayan gaban mirror suka zube kasa ta fashe da wani irin kuka me karfi.

Wani zaiyi tunanin cewa Abun bai kaina har haka ba, Sede ita awajenta ya kai harya wuce hakan, sabida ta riga ta saka dukkanin kwayayen ta a kwando daya, tana kuma tsammanin yaune zai kasance mata wata rana na musammn a babi auren ta, kuma rana na daban datake tunanin zai kawo mata kakkarfan maslaha game da sexual life dinta gabaki daya.

Har kasa ta durkushe bisa kan gwiwanta tana rero kuka mai kara mai kuma ciwo da radadin takaicin femi.

She just cant belive she failed to mend her marriage again.

Depression da tsananin Haushi yasakata ta zauna awajen tumus acikin decoratons din ta dinga kuka tana tuna irin yawan hakurin datay da halin femi, da irin kame kanta datakeyi duk dama bai taba bata wani gamsuwar aure ba. To stay Few month witou sexual satisfaction in marriage is not even a bearable bare ita datayi shekaru yaukam ita kanta tasan ta riga da ta kure gejin haqrinta..

She cant take it anymore. Dis pain and suffering has to stop!

Aranta ta jima da sanin cewa Alakar femi da chief okoro yana daya daga cikin babban matsalar dake damun aurensu, its emotionally draining her musammn inta yi lissafin yadda femi yake bada muhimmnci da fifiko akan chief harma fiye da ita datake matarsa na aure abun har yanzu bata fahimce sa da kyau ba

In har she is dis irrelevant to him to ya zamo dolene kenan ta dena kokartawa akansa gabaki daya tunda yau ya nuna mata da alaman yana samun kwancyar hanklin da bata bashi ba awajen chief okoro.

Gani tay Wann auren nasu ne su biyu ba nata bane ita kadai. Babu wani dalili da za' ace ita kadaice keneman gyara shikuma hanklinsa yana ta wani wajen akan aboki bama dan uwansa ba unless if he is tired of her and the marriage.

Tun zamanta anan babu abunda batay nazari akai ba..sosai jikinta ya dauki zafi dan takai karfe biyun dare tana sobbing tana kuka, jin kamar kanta na bugawa yasaka tabi ta jawo kwalban ta bude ta fara shansa akai akai har ya kashe mata jiki karshe awajen tabi ta kwanta bacci me nauyi ya saceta.

Ayayinda vicky tay kwana cikin tsananin baqin ciki da kuncin yanayin rayuwarta, mijinta femi da masoyinsa chief okoro kuwa kwana sukayi a gidan suna morar junan su har saida asubahi tay kafin suka kama bacci.

******* Washe gari Sassafe wajajen karfe shida Henry ya damesa da kira, acikin gigin bacci ya farka ya dauki wayar babu bata lkci henry ya gaya masa cewa vickyn tazo nemansan jiya snn gaskiya shi yanata tsammnin cewa ta gane cewa dashi sukayi waya dan haka yaanaa baashi shawara yaje gida kar vicky taji haushi tace zata rabu dashi maganan ya jawo masa babban scandal da zai saka mutane sufara bibiyar alaqarsa da chief okoro.

Acewar henry muddin jama'a sukaji cewa aka Chief ne matarsa ta rabu dashi toh tabbas da akwai wayanda duk tsiya sai sun bankado gaskiya.

Da can maganan bai wani shige jikin Femi ba face saida ya sauƙa akan gadon da kyar ya wuce bathrum ya gasa kansa a ruwan zafi ya sha pain killers yaji dama dama kafin nan maganganun suka soma making masa senses sosai.

Just then he realized He cant afford to loose vicky sabida itadin kamar garkuwa ce babba wa rufin asirinsa da chief okoro.

Atake atake yahau shirya kansa zai tafi gidan yaje yaga meke faruwa da ita.

Yana cikin saka kayansa chief ya farka yanayin gigin bacci ya hade ransa yanace masa ina zaije bayan basuyi soyayyar safiya ba.

Femi bai wani kulasa ba har saida ya kammla saka kayanshi tsaf snn ya taho gefen gadon ya zauna snn yahau masa bayanin abunda henry yace masa akan vicky

Da mamakinsa sai yaga chief baiji haushi ko ya hanashi tafiya ba dan kuwa burinsa ya riga da ya cika wajen nunawa vicky cewa tabbas shine da zucyar femi ba ita ba.

Alkwarin dayay mata na cewa zai jefata acikin baqin ciki ranar anniversyn su ya cika..

Duk da baccin dake idonsa amma yau Har gaban mota ya rako femi yaname cemasa inhar vickyn tana bukatar wani abun duniya koma miyene kawai ya gaya masa shizai siya mata sabida tay hakri.

Agaban femin sai yay fuskar tausayi kamr irin shima baiji dadi da suka mata hakan ba alhali aransa murna yakyi sosai.

Tunda femi ya watseka ya dawo hayayyacinsa yakejin fargaban tunkarar vickyn na shigarshi..

What if she really want to file a divorce yakenan zaiyi? Shide baison ma su rabu bare yace zaiyi tunanin auro wata dan baisan ya zasuzo su kare da asirinsa ba.

Karfe shida darabi yay masa a hanyar gida sai sharar gudu yake akan titi yana goge kansa da hanky time to time duk ac dake busoshi bai hanashi jin zafi taciki ba.

***************** Ata daya bangaren kuwa tunda Halisa ta koma bacci bata tashi farkawa sai can da wayarta ya dameta da kara sosai.

Tun bata kammala bude idanuwanta ba ta damke saman kanta dake mata wani irin nauyi sabida maganin bacci da khaleel ya zuba a ruwan ya balain bugar da ita sosai

Batare da ta bude idanunta ba ta luluma kam gadon har saida ta capke wayar tata kai tsaye ta jefashi a kunnenta batare da taga wayeke kiranta.

Muryanta kasa kasa sigar bacci tace Helooo

Ajiyar zuciya Jasmine ta sauke tanamai cewa oh thank god u picked up har kinsan naji tsoro.

Halisa Tanajin muryan jasmine din murmushi ya kufce mata ahankli tace " tsoron me, why, Did u think im dead???

Jasmine tace "You dare not die! Ki cire zancen mutuwan nan abakinki mana halisa? Da muryan lallami tace "cmon tell me Are u okay???

Ahnkli halisanta bude lumsashun idanunta da sukayi jaaa tsabar tsumayin bacci tace Kowa zai mutu Jasmine Death is inevitable komun so ko bamuso ba

Jasmine tace naji..ki amsa min dayan tambayar.

Nannauyar ajiyar zuciya halisa ta sauke tace wani tambayane jass?

Jasmine ta dafe kai "Ohh Bazaki gayamin yadda kike din ba kenan kinfiso na cigaba da zama acikin fargaba.

Jasmine kidena fargaban komi i swear to u bazan taɓa kara tunanin kashe kaina ba, wai saunawa zance miki ive regreted it ne, wallh nayi nadaman yin hakan.

Cikin katseta Jasmine tace good nide babban fargabana da damuwa shine zamanki agidan wann baqar macijiyar cos i am sure she is stalking u.

Ahankli tace "Yes she is, but am not allowing it anymore jasmine. Kawai zama agidan nan ne is more than living in Hell

Jasmine tace meyasa?

Mikewa zaune Halisan tay da kyar snn tace "Duk lokcin danaga fuskar meenal kona naga na mijinta a kusa dani ji nake kamar na mutu dan haushi suke cusamin. Gashi na buga na buga amma da alaman babu wanda zai amince dani msmmn innace bazan sake aikata suicide ba. Dr Asim baima dauka na me cikakken hankali ynxu. Kowa gani yake kamar am mentally unstable, inna koma gidana zan je ne in kashe kaina. But seriously takaici ma kadai zai kashe ni anan gidan.

Cikin yanayin tausaya jasmine tace Hakane Halisa amma kiyi hakuri mana ki daure u need to obey the doctors dan su gane cewa kin warke suyi suyi su sake miki freedom dinki da wuri

Cikin kyabe baki halisa Tace hmmm me ? Obey which doctors..pls take off that plural(s) nide likitana daya ne kuma shine kawai nake ganin girmansa.

Jasmine tace Kai halisa karkice min har yanzu kina bada gayen nan ciwon kai?....

Nake bashi ko shi yake bani jasmine ke kinsan iskancin da gayen nan yakemin kuwa? So yake yamaida abun wasan yara, dama neman dama yake da zai walakantani sai kuma gashi ya samu.

Jasmine tace dont see it like that halisa ..ki karbi abun kawai da zucya daya nide nasan da yanada niyyar walkantaki da bazai fa risking rayuwarsa yabiki cikin wann babbaan tekun ba.

Shikenan kuma dan ya ceto rayuwana akace saina fara bauta masa? Nan Tafara mita tanamai zayyana ma jasmine din duk yadda sukayi da shi tun datazo gidan .

Banda dariya babu abunda jasmine din takeyi cikin daruyar tace "are u serious ya doraki akan diet time table? Dama kin rame wallh Oh Allah ashe akwai wanda zai saki cin abincin dole Hahahah my god this is getting intresting..

Halisa ta hade rai Pls How is this intresting jasmine kema fa babban munafukace bayansa kike bi ko bayana?

Jasmine na dariya tace I'm with u my friend amma da kika tsaya kina masa kukan ne naga wautarki. Ya riga yasan bakaunar zama a inda yake zakiyi ba, kekuma taurin kai toh ai zai ta amfani da taurin kan nakine yana sakaki a matsala awajen Dr aseem karshe sai kiga kinyi shekara kina jinya a hannunsa.

Halisa tace God forbid Ai satin nan ma banaso ya kare ina gidan nan wallh na rasa yadda zanyi ne in gunduresa ya kare jinyan nan akan lokci ya sakeni in tafi.

Jasmine tace hmmmmm They are many ways baby girl.. kibari kawai zan rubutu miki tactics din a tex anjima..ki gwada zaki ga shida kansa zai dena shiga harkanki inbaiyi wasa bama sai kiga yana Allah Allah ya gama ya turaki gidanki kawai within kwana uku.

Cikin tsananin farinciki halisa tace Jesus i just cant wait to see that text.

Dariyar shaqiyanci sukayi atare halisa tace So hows ur show in london? Sorry ban ma tambayeki ba.

Jasmine tace komi ya tafi dede. Sede anan ma mutane da yawa sunji labarin case dinki na suicide..tsoffin boses dinki na fashion house sunata tambyana wai ko kin fara shan drugs ne.

Dariya Halisan tay cikin kyabe baki tace "wato idan kika samu mutanen movie indusry dana fashion industry to kin gama zuwa bus stop din gulma kenan. Suyi ta harsashen su nide bana cewa kowa komi. Naga Rayuwata ce!

Jasmine tace yeah rayuwarki ce halisa Dan yanzu haka sai kiga anyi show akanki inkika basu attention sai afake ace kedin ai tsohuwar star dinsuce amma mu mun sani duk dan neman kudine, damuwar su shine suyi amfani da damuwarka su samu attention din media da yan wasu kudade kinsan wann karamin aikinsu ne.

Halisa tace hmmm Su sukaji wajen ni de yanzu inba naga na fita anan gidan ba hanklina bazai wani kwanta ba.

Tace nima bana son zamanki agidan ko dan waccan mayyar, amma kingane ko, Duk wani abu da kikaga ya faru dake akwai tsarin Allah aciki, Sumtimes what we think is worst for us is actually going to be the best for us, nide shawarar da zan baki shine ki daure ki tsaya akan jinyarki ki warke din sabida zai iya kawo miki koma baya akan business dinki anan gaba. Think about inbaki samu kin fita agidan ba ya zakiyi kenan halisa? Zaki ta fushi kina bata ranki akansu kenan har Abada?

Cikin lumshe ido da budewa tace naji jasmine dama ai zan zauna mana for this one week amma pls u have to send me dat tips. Allah inason nayi maganin gayen nan Banason sunamin kallon me taurin kan seriously he is using it againts me bakiji wai har barazana yakemin akan zai kai karana wajen doc aseem Dan akaramin weeks agidansa ba.

Jasmine tace dats the point amma inhar zaki bi tips din da zan turo miki a sakona trust me one week din nan ya ishe sa haka..inason kiyi jinya amma u cant be around dat monster meenal alwys kinma yi kkri inda ace nine da tuni na zuba mata poison tasha ta mutu.

Halisa tay murmushi Tace Da Allah dena cika baki kamar zaki iya kashe mutum..

Dariya jasmine din tay tace " inba zan iya ba amma banajin ko shedan yakaini tsanar yarinyar nan she is a devil herself really.

Halis atace hmmm Okay abar hirar tan kawai dan ban fiye son jin sunanta ba. It reminds of alots.

Jasmine tace fine lets talk about business then

Nan suka bige da hirararki da dama duk dama jikin jasmine yay sanyi data lura kamr halisa is no longer free and open kamar da can gabaki daya har yanayin magananta ya sauya sosai.,

Tabbas cin Amina da cutarwa tare da tsanani yafi komi saurin sauya halayayyr mutum komin saukin halinsa.

Da can zakayi hira da Halisa me tsayi akan abubuwan data saka agaba cikin raha da wasa da dariya.. sede tunda abun nan ya faru da Meenal tay betraying din trust dinta shikenan ta zamo bata iya sharing plans dinta deeply saidai sama sama.

Sosai jasmine ta lura da sauyawa Halisa but deeply in her heart tay mata uzuri sabida tasani bakowa zai iya daukar Abubuwan da zucyarta ya dauka ba.

Hakan yasaka bata nuna damuwarta akan kwane kwanen da halisan ta dinga mata acikin hirar tasu ba, saima karfin giwar datake dada kara mata, da nuna mata cewa she doesnt need anyone to feel validated.

Kusan awa guda sukayi suna wayan wanda shine ya warware mata mood dinta sosai sai can kuma da tafara jin tsinannen yunwa na damunta dan hryanxu bata san da cewa khaleel yana saka mata maganin cin abinci ba a induction nata ba kawai ta dauka ciwon ne yazo mata da sabuwar salon jin son cin Abinci

Suna kammala wayar taji ta kasa iya dauriya nan ta sauka kasa taje waje ta same me gadi na zaune...yana ganinta ta fito da drip a hannu ya miƙe jikinshi na bari ya iso wajenta yanamao gaisheta da dar dar a tunanin sa itama muguwace kamar meenal dake yana dan ganinsu atare yadauka halinsu zai zamo daya.

Fuskarta babu yabo babu fallasa ta amsa shi snn ta bashi kudi akan ya taimaka ya siyo mata abincin da zataci.

Babu musu ya amsa ya fita waje jikinshi na rawa yanata sauri sauri yaje ya siyo dan bakaramin izgili da walaknci yakesha a hannun meenal ba

Waje halisan ta nema a harabar gidan ta zauna looking at how compound din poorly kept, dirt nan dirts can, bishiyoyin duk sun sauke musu datti ga ciyawai sun fara girma acikin boundries, dama can me gadin ne kawai yake dan multi tasking yay shara ya kimtsa gidan sede ba lallaine mishi yay kullum ba sabida aikinsa na tsaron gidan yfi muhimmci.

Tay tsaki aranta tana ta wondering akan meyasa baza su debi enuf workers da zasuna kula da gidan ba tunda sudin basu da lokci.

Can kuma ta kyabe baki tace Su sukaji wajen.

Daga nan Tay shiru tana shaƙar fresh iskan da bishiyoyin ke busowa.

Tana daga zaune awajen after like 20 min me gadin ya dawo mata da Abinci ta karba ta cire roba daya aciki ta bashi kyauta snn ta masa godiya. Mamakin saukin kanta yasaka shi mata godiya muryansa kusan a rude, kallonta ya dinga yi Harta koma cikin gidan bai motsa ba sabida tun da yake gidan inba Khaleel ne yaci Abu ya rago sauran daga office yazo ya bashi ba toh ba ataba bashi kyautar abinci haka agidan ba.

Fried rice ne ga katoton chicken wings akai bai taba tsammanin mashi ta saka odern ba.

Halisa tana shiga dakinta ta shimfida akasa taci Abinta tay nak saida taji cikinta ya cika tammm ta mugun koshi takai makura.

Sauran appetizers din da ice creams ta aje su akan table na gefen gado ta. a nemi waje ta zauna tana shan chokolate ice cream tana scrillong wayarta caraf sai ga nan sakon jasmine ya shigo

Aje ice cream cup din tay caraf ta bude tahau karantawa tanakaiwa karshen sakon babu shiri ta fashe da wata iriyar dariyar da ta jima batayi irinsa ba. DO NOT SHARE PLEASE NA KUDINE TO SUBRCIBE CHAT 08060712446 26.

Dan Dauke kanta tay akan saƙon tana dariya snn ta danna wa jasmine din kira bayan kamar ringin biyu aka dauka kamar wanda suke jiran su shaqi numfashin juna suka hau kwaashewa da dariya.

Jasmine i cant believe u wrote dos devilish things.

Jasmine Tace ke tsaya nan wasa shiba namiji bane? Just do what i said inhar da gaske yana da kamun kai zakiga yay Allah Allah ya sallameki

Halisa ta lumshe ido snn tace Very good..i love this plan. Infact yanxu zanyi odering kayan aiki

Cikin katseta jasmine tace No no Wann ai akaina yake tunda nice na kawo wanm shawarar just chill zuwa gobe da sassafe zakiga aika daga wajena.

Annuri da nishadi ke wanzuwa akan fuskar Halisan tace awwn I love u babe, thank you so much tacha.

Jasmine tay murmushi "Shushhh Will u keep that a litle quiet, dont thank me babu wani godiya a tsakaninmu.

Tace toh naji Acikin shoping list din naki karki manta da marlboro me kyau Kinsan Uztaz shima ya dawo wawa yana biye ma khaleel ne kowa sunan shi oho innace ya siya min cigarete zaije ya gaya mashi sai suhada kai suhanani sha.

Jasmine na murmushi tace Dont worry zan aiko miki dashi acikin shoping din gobe.

Halisa tace okay toh bari na barki kihuta.

Ahankli Jasmine tace okay, take care of uself kinji?

tace i wll sann ta katse wayar tare da sauke ajiyan zuciya After a while bayan ta huta a zaune can data gaji sai ta koma kan gadon ta kwanta akai ta dan jingina kanta da pillow tayi shiru ganin kamar tunani zai mamayeta yasaka ta bude wayarta sharp sharp ta shiga watsap Taci sa'a kuwa hadiza maitama na online haka suka ta chating mai cike da nuna kulawa junansu har saida bacci ya sake dauketa.

Ita kanta batasan awa nawa tay tana baccin ba kusan ana kiran magrib ta farka a rude ganin har angyara mata kwanciya an maida mata drip din data cire a hannunta an saka mata sabuwar ruwan magani.

Cikin lumshe ido da budewa wani Karamin tsaki ya kufce abakinta Yunkurin mikewa tayi danta zauna sai ga sallama daga bakin kofa Wanda koba a fada ba tasan wayene.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull