Kenza eBookz

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 13

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 13

Cheaters club book 2 complete novel Chapter 13: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 13. Muryanta kasa kasa Tace Come in..

3,366 words

Muryanta kasa kasa Tace Come in..

Uztaz ya shigo looking stressed out daga ganin sa kasan ya gaji kallon shi ta dingayi tanajin matsanancin tausayinsa aranta har ya karaso bakin gadon nata ya zauna cikin nitsuwa.

"Are u alright.. Ta masa tambaya da sanyin muryan da yaso yabashi mamaki ganin yadda ta kureshi da kallo

Ya juyo ahankli ya dubeta damuwar dayake cinsa akan lfyarta ya cikke kwayar idanunsa cikin sauke ajiyr zucya yace i am fine Boss ya jikinki

Tace Da sauki, amma u look stressed..aikin office din yay yawa ne?..ko kana bukatar anemo maka masu taimakawa..asin ur personal assistants.

Yace no no aikin baifi karfina ba...Im just worried about u all day.

Hannunsa ta riko cikin jimantawa tace kalleni nan...

Ya juyo suka hade ido cike da son ta kwantar mai da hankli tace uztaz i am fine Kadena damuwa akaina.. inma waidan zamana anan ne danace banaso toh na hakura zan zauna ayi jinyar okay? Nasan abunda kake son ji kenan.

Nannauyr ajiyar zucya yay tare da gyada mata kai ahankli.

Cike da lallami Tace tou Kawai kayi concentrating akan aikin dake gabanka ..I really feel bad da bana tare dakai but i promise u zan warke na dawo kan aikina..idan na dawo ma ya kamata mu dauki hutu muyi tafiya muje wani waje me nisa a duniyan nan mu huta ko??.

Murmushi mai fadi yay dan ya jima baiji ta fadi magana da sakakken zuciya kamar nayau ba.

Ya gyada kansa ahankli yace shikenan boss.. naji!

ahnkli ta sake hannunshi tare da sakar masa murmushi me sanyi snn tace "what do we got?..

Yace alot, dan ina da dukkan wansu bayanai akan aiyukan mu zan saka miki su a computer ki zaki iya dubawa duk sanda kikaga dama..

Sann akwai foreing investors da suke son shigowa harkan saida kaya da doller a wasu kamfanonin mu, da akwai mace datake son kuyi business din saida sarkan gold atare she is frm congo hamshakiyace sosai amma ban amsa kowa ba sai na kammala binciken sirri akansu sabida banason muyi sana'a da masu dukiyar haramun zai iya lalata mana albarkan dake cikin cinikin mu.

Halisa data nitsu tana jinshi cike da gamsuwa tace very good. Harka da sabbin fuskoki yana bukatar kulawa sosai sai Ka kiyaye business da boyayyun drug dealers, child/sex traffickers da kuma money lounderers ..bana son kamfanoni na su hada harka ko hanya da masu gurbatattun sana'oi. But Let every company knw dat Halisa is open to new growth. I only want to do business. kawai inka gama binciken ka akansu ka gamsu sai ka dauki dikkan wani matakin daya dace karka damu da sai na saka hannu.

Cike da ladabi yace thank u for trusting me, in sha Allah duk abunda ake ciki zakiji Allah ya baki lafiya.

Tana murmushi tace Ameen...are you not hungry Comn we shud eat together yau. Kayi mana oder din Abinci inason naga kaci abincin agabana.

Yay murmushi yace yes boss.

Toh tayani tashi zanje nayi wanka inka gama sallan ishai saika kawo mana Abincin muci tun kafin wann wawan likitan naka ya xo yace zai bata min mood dina.

Baice komi ba ya gyada mata kai yana murmushi Ahankli ya amshi hannun ta ya cire mata canula din ya kulle sann ya tayata ta mike tsaye.

Yana ficewa ta shiga bathrum ta cire kayanta tafara wanka acikin cold shower tanajin jikinta da dan karfi karfi bakamar da can ba.

Bayan ta kammala wankan ta yi brush ta daure suman kanta data jikashi da ruwa acikin towel snn ta fito dakin ta samu uztaz harya fita siyo musu Abinci, acikin dan kankanin lokaci tay sauri ta shirya kanta dama bawani kwalliya takeyi ba nan ta nemi waje ta zauna akan cushion tana latsa wayarta acikin nitsuwa.

Dagata dayan bangaren khaleel ya dawo daga masjid kenan jikinshi sanye da brown jallabiya data sha guga kai tsaye ya shiga dakin binciken sa ya tsaya agaban suirvellnce computersa dan ya duba ko halisa ta farka daga baccin ko bata farka ba, cos too much sleep is also part of signs and symptoms na depression shide yana ta iyakar baqin kkrinsa wajen gane dukkan wani halin datake shiga ciki domin yasan menene ya dace yayi.

Ganinta a zaune akan couch tana latsa waya cikin kwancyar hankli ya bashi mamaki, she look very innocent and calm yanata kallonta yadda ta zauna ta nitsu har yarasa mesa yake kallontan Can yay tsaki ya dauke kansa ahankli cikin sauke ajiyar zuciya.

Cikin dakinsa ya koma tare da daukar agogon sa na phatek dake aje a saman drawer gefen gadonsa ya kalli time its almost 7.30pm baiji duriyar meenal ba kuma bata kirashi awaya ba duk dama bai wani damu ba dan yasan Aldartace ficewa a duk sanda ta ga dama takan dawo kuma a duk lkcin datake so inyay korafi sai tace mai bazai taɓa fahimta ba dan kulawa da babban business da kamfani ba abune me sauki kamr aikin likitanci ba.

Meenal bata taɓa rasa wani hanyar da zata gayamai baƙar magana kota masa gori ba musammn ma akan abun duniyar data tara shiyasa wani lkci ya gwammaci ya dauke kansa akan wasu abubuwan datake aikatawa daya tsaya tana gayamai maganan banza.

Cikin sauke ajiyar zuciya ya aje agogon yanamai rayawa aransa cewa yakamata halisa taci abincin dare dan ya bata maganinta da wuri sabida yana da ayyukan da zaiyi acikin daren nan.

Wadrob dinsa ya bude kai tsaye ya ciro wata casual dress ɓakin jean da fitted short sleeve shirt sea green ya saka ajikinshi bakaramin kyau ta masa ba dan kuwa tamkar saurayi dan shekara ashirin hakann dressing ta maidashi.

Yaci akalla minti sha biyar yanakan shirya kansa dan kusan komin sa anitse sosai yakeyin shi sumtimes kamar ba namiji ba.

Bayan ya kimtsa suman kansa mayukan qamshi da brush yabi ya fetsa turarensa masu sanyin qamshi snn ya dauki key din mota ya juya zai dauki wallet dinsa sai bangansa anan ba.

Tunawa yay ya ajeshi acikin room din aikinsa agaban computersa kai tsaye ya koma dakin tun kafin ya miƙa hannu ya dauka idonsa ya sauka akan halisa da uztaz suna zaune a tsakiyar dakinsun suna cin Abinci kamar yan uwan jini suna yi suna dan hira.

Ta sake ranta sosai acting like she is fine dan Babban burinta shine ta cire wa uztaz damuwa a zucyarsa dan sosai takejin tausayinshi.

Hasalima itake take motivating dinsa Yana cin abincin sosai.

Gashi bata wani karya dokar ba, iya Abincin daya gindaya akan tana cinsu da dare din shine agabanta tana ci duk dama tin a fuskarta zakasan na dole ne take durawa.

Shikansa khaleel dake tsaye awajen ya riga ya gane sabida uztaz take cin abinci.

Mamaki ya daskarar dashi awajen cos At times sai yaji aransa kamr halisa tana da personality disoder yau ita mutuniyar kirki ce gobe kuma babu wani marabarta da cikakken mahaukaciya.

Haryanxu jiyake kamr He just cant belive dat she is dis down to earth and easy going person da ma' aikatan ta har haka.

Ahankli Ya kyabe baki cikin rashin son barin zucyarsa ya yaudauresa akanta dan bazai taɓa mance irin tantarin rashin kunyar data masa abaya ba musamn ranar dataje har wajen aikin sa ta wanka masa mari agaban kowa akan meenal.

Cusa wallet dinsa yay acikin aljihunsa snn ya fice a dakin tunda yaga halisa tana cin Abinci sai baije dakin ba ba ya sauka kasa yafita ya dau motarsa ya jeshi regular wajen cin Abincinsa ya saya Abincin yaci awajen bai wani jima sosai ba ya kama hanyar dawowa gida.

Lokacin Su halisa har sun kammala cin Abinci uztaz ya kunna mata computerta ya saka mata dukkanin files datake bukata yanamai dada mata bayani ita kuma tanamai dada wayar masa kai akan abubuwan daya dace yayi dan Allah ya bata basirar kasuwanci bana wasa ba.

Tun da suka zauna anan babu abunda takeyi face dorashi akan hanyar da zai kaisu ga nasara a kamfanoninsu.

Khaleel na kammala parking ya wuce sama tattaro maganin halisa na dare anan ya xauna ya shiga harhadawa dan yagane kmr tana yawan tsorata inyana hada su agabanta tana gani.

Yana aikinsa a zaune agaban computer yana kallon su ita da uztaz dake yana respecting privacy nata sai bai saka volume ba, yakan iya kallon dikkanin motsinta ammma bayajin me suke cewa, ganin su kawai yay azaune suna tattaba computer halisa tana ma uztaz bayani shikansa khaleel din ya rasa meyene suke tattaunawa da suka nitsu akai sosai.

Shigarsa gidan bada wani jimawa ba meenal ta dawo gidan a mugun gajiye da riki rikin take aways na Abinci data kawo ma halisa.

Iya Jakarta kawai ta aje a dakinta ko wanka batayi tsayayi ba ta dan rage kayan jikinta ta sako wani marar nauyi ta nufo dakin Halisa da bags din chops din.

As usual bata wani knocking kawai ta turo kofar ahankli kusan dukan su saida suka kalleta a lokci guda.

Kafin kace wani Abu har halisa ta yi closing tab ta kashe computer dake gabanta cikin son ta biye komi nata cos she cant risk it anymore with fake friends.

Meenal na murmushin yake tace "Hey babe. Wow U seem okay, Wayyo Allah na naji dadin ganinki ahaka are u working?

Babu yabo babu fallasa halisa tace nop.

Da rawan jiki ta karaso Tanamai cewa I brout u food..nan ta fara babbaje su tana budewa daya bayan dayan gabaki daya qamshin abincin ya cike dakin.

Kallo daya me kyau halisa bata kara mata ba bare Abinci ahnkli ta kalli uxtaz ta masa alaman yaje gida ya basu waje.

Babu tantama ya miƙe tsaye zai fice.

Meenal tay saurin dakatar dashi a walaknce "Hey hey you mr worker Ina zakaje baka serving inta abincin ba ko nine kake tsammanin zan maka aikinka.

Kafin uztaz ya amsa halisa ta kalleta tace let him be Amina, ni nama koshi yanzu nan muka ci abinci thanks.

Baki galala meenal take kallon Halisan batace komi ba har sukayi sallama da uztaz ya fice abunsa.

Acikin abubuwa masu yawa da suke damunta game da halisa ayanzu "AMINAn' da halisa ta dawo tana ce mata shine yake so ya fara daga mata hankali tarasa mesa Halisa ta sauya mata gabaki daya.

Hawayen makircin data saba ta kwkwalo zata fara kwarorowa halisa zantukan ban tausayi

"Na hana kaina cin komi tun safe a tunanina zanzo muci abincin tare dake aminiyata, Halisa meye na miki pls, Abincin nawa ne bazaki ci ba Cos how cud u just say kin koshi? Is very disgusting kina cin abincin da mai aiki haba.

Halisa tana budan baki sai sukaji sallama ata bayansu khaleel ne ya shigo dauke da medical pan tray a hannunsa ya bisu da kallo daya ya dauke kansa.

Daga ita har Halisan babu wanda ya amsa sallamarsa wanda hakan yasakashi ya dada harde ransa sosai..

Meenal na ganinsa tafara karya wuya dan makirci please halisa kici Abinci...

Halisa tay kamar ba da ita takeyi ba

Ta juyo ta kalle khaleel cikin langwabe wuya babe kace mata taci Abincin mana dan Allah tay maganan tanamai kallon khaleel a shagwabe.

Baice mata uffan ba ya cigaba da abunda yakeyi

Ran meenal sosai ya sosu da sharetan dayay

Ahnkli Halisan tace mata na riga na ci Abinci,u see he cant force me to eat again . Kici Abincinki inkuma kin koshi kibawa wani yaci.

Meenal tay rolling idanunta cikin jin haushi tace dont bother i think ive just lost my appetite

"Okay goodnite" Acikn rashin kulawa Halisa tace mata hakan

tay saurin dagowa ta kalleta da matsanancin mamaki ganin irin ko in kula da rashin nuna damuwa da ita da batay ba.

Aranta tasan Halisar data sani da tausayi da saukin hali koda bazataci abincin ba da zata iya tursasa kanta taci na dole kodanta kwantar mata da hankli..halisan data sani ba wann bace.

Rai a bace ta miƙe tsaye batace musu uffan ba ta fita acikin sauri ta koma sashenta da tunane tunane.

Ko kallon inda tabi halisa batay ba. Hakama tun da khaleel ya shigo dakin basu cewa junansu uffan ba.

Bayan ya zuba mata ruwan magani acikin normal dosage dinta na induction sai kafin nan ya taho ya tsaya a kusa da inda take yanamai kureta da kasaitaccen idanunsa mai cike da kwarjini.

Tunda ya zuba mata ido banda Bugawa babu abunda kirjinta yake amma babu alaman hakan data nuna a fuskarta.

Cikin wata sauti mai bala'in sanyi da dadi yace "How are u feeling?

Kanta na kasa kamar bazata amsa ba tace "Good".

Tanaji Yay karamin scoff, snn yace "I see. Sann ya tsuguna daf da ita zuciyarsa yaji ta rike shi gamm ganin yarda ta yi saurin dauke kanta ta maidashi can gefe dan ma karta kalleshi.

Banda Qamshin turaren sa danata da suka gamutso suna fidda wani irin daddar qamshi babu abunda suke shaka daidai.

Lumshe ido tay sosai jin kamar zata nitse cikin kasa jin Ya kama hannun ta a hankli izuwa nashi ya rike tsananin taushi da laushin hannun nasa Atake ya saukar mata da ruwan kasala agabobin jikinta gabaki daya.

Ata fanninsa kuwa kkrin danne numfashinsa dake kufcewa da karfi yake dan baison tagane cewa kirjinsa yana bugawa da karfi idan ya matso daf da ita sosai. Dan tazarar dake tsakaninsu baifi tsanguli daya ba.

Kusan acikin numfashin sa dake fitowa da kyar yace mata "Can u relax?

Lumsashun idanunta ta bude sann ta kalleshi sama sama tace ummm

Ya rike hannun ya daure snn ya saka Allura akan jijiyarta yay mata acikin dan kankanin lokci yasha mamaki dayaga batay motsi ko ta zageshi ba duk dauriyarta yana zare alluran taji azaban zafi awajen bai hankara ba yaji dumin hawayenta tsilli guda ya zubomai a hannu. Hawayen ya dinga kalla batare da ya goge shi ba har ya kammala dressing wajen ya saketa ya mike tsaye

Aransa so yake yace mata sorry amma kuma sai yaji ya kasa.

Yana daga tsaye harta miƙe ta haura kan gadonta ta kwanta yazo ya jona mata induction dinta na dare.

Bai jima da barin dakin ba alluran ya dan warware bayan ta huta kadan nan ta kunce ruwan ta sauka kasa ahankli ta tattara abincin da meenal ta kawo taje har waje ta bawa me gadi yanata gode mata.

Dawowarta dakin kawai khaleel yagani duk ya dauka ko bayan gida taje sai kawai ya kashe computern ya fita direct ya wuce dakin meenal daga nan ba akarajin motsinsa ba sai washe gari da safe.

Washe gari sassafe Halisan nadaga kwance ta farka kenan tay addua makanta zata koma baccin safe Kusan Kirar Fadila ne ya katseta.

Halisa taji dadi sosai da yadda fadilan ta damu da ita. Koba komi tasan tana son xuwa ta dubata amma kuma batason ta taka kafarta ixuwa gidan meenal shiyasa kawai haryanzu bata iya samun daman zuwa dubata ido da ido ba.

Bayan sun kammala wayar ne tafara nazari akan wani abu sai can kuma tay murmushi ta rubuta ma uztaz sako akan idan zaizo ya kawo mata littafinta da Dr khalid ya bata Daga nan wani Baccin safe mai dadi ne ya debeta. DO NOT SHARE د.NA KUDI NE TO SUBCRIBE CHAT SURAYYAHMS 08060712446...... 27

#SURAYYAHMS #PAID BOOK

** the same morning sassafe wajajen bakwai saura prince Femi ya iso bakin babban gate din gidansa yanamai danna horn cikin sanyin jiki dan izuwa lokcin kwakwalrsa ta riga ta kammala hadamai duk wani manipulation tricks da zai yi aiki akan matarsa victoria dan ya wanke kansa daga lefin da ya aikata mata.

Ya riga da yasan da cewa victoria babbar macece me ilimi tanakuma da wayewa sosai inhar yace zai saukar dakansa ya lallabeta zai jawo ta zamo soo emotional ahakane kuma zata samu hanyar gaggaya mai laifukansa wanda ya san bai shrya jinsu ba bare yasaka ranar gyarasu.

So what he need to go for a reverse phsycology, maaña maida lefi kan wanda baida lefi, mafi saukin abun shine yay normalizing situation din ya kuma nuna mata kamar baisan ya aikata wani abu me tsanani ba kawai itace take da matsalar fahimta.

Wann shawarar sosai ta zauna masa a zucyarsa aganinsa itace kawai masa mafita guda daya.

Mai gadi na bude masa kofa ya shigo ciki yay parking snn ya fito yanamai takawa ahankli har yakai cikin main mansion dinsa.

Gashinan dai ko ina a kimtse amma Wani irin shiru na ban mamaki yaji gidan ya dauka dashi.

Duk anje hutun aiki sai Baiga wasu ma'aikata ba bare ya tambayesu wasu abubuwa game da vickyn Da zai bashi wani heads up.

Ya duba agogonsa yaga 10 minutes past 7 am aransa yace haka farkawa ne basuyi ba dan haka kai tsaye ya haura sama ixuwa dakin vickyn yana tafiya kirjinsa na bugawa sosai.

Bai tashi jin fargaba me yawa ba face saida ya bubbuga kofar dakin baiji tazo ta bude mishi ba.

She was strucked with hangover giyar data sha ajiyan me tattare da maganin baccin da kayden ya zuba mata shiyasaka ta samu isashhen bacci harta makara bata farka ba.

Hanklinsa inyayi dubu ya tashi jikinshi na rawa rawa ya harba dakinsa yaje ya bude drwersa ya bincika ya ciro spare keys agaggauce ya dawo

Tsabar fargaba kusan a gigice ya fado cikin dakin wanda shiya razanata ta bude idonta daga baccin atake batare da ta gama watsekewa ba.

Cak ya tsaya a mugun daskare yanamai bin dakin da wani irin kallo ganin inda ta kawata shi in the best romantic way possible koina yay kyau gwanin ban sha'awa atake yaji jikinshi yay sanyi sosai.

acikin dan kalilin lokci ya kalle kan gadonsu yagan shi tsaf tsaf alaman bata kwanta akai ba, snn ya juyo ya kalle kasa yaga inda tay uwar watsi da kayan dake kan mirror wanda ba sai angayamai ba yasan ta shiga wani hali na bacin rai sosai.

Jikinshi na ɓari ɓari ya taho kanta tare da zube giwarsa akasa gwaraf agabanta muryansa har na rawa rawa ya dora hannunsa agadon bayanta bisa kan temporary tatto din dayaga sunanshi akai muryansa harna kakkaryewa yanamai cewa "victoria.. Vicky.. Ya langwame murya kalar tausayi "Wify Are u okay........?

Shaky and trembling voice nashi dataji yasaka Ta kwace baccin a idanunta da uban karfi danta miƙe daga kwancen datake akasa ta zauna tagan koshidin ne dagaske ba mafarki takeyi ba.

Dan ko da ta kwanta awajen ji tay kamar an tsane mata shi acikin ranta. Batama son ta hade ido dashi bare tay doguwar magana da shi.

Kallonta ya dingayi ganin ta rike kanta da alaman yana mata ciwo da nauyi sosai.

Kwalban giyan idanunsa Ya sauka akai ya mike tsaye a gaggauce yaje ya kawo mata neutrilizer me sanyi sa lemon tsami aciki yahau bata abaki tasha ahankli.

Tunda datasha tasoma dawowa hayyacinta sai taji kamr ta shiga wani hali musmmn ma data gane cewa femi ne agabanta yana durkushe.

She kept asking her self acikin ranta what does he want frm me? How can i react..what shud i do? Shud i listen to him or not. Shud i leave or stay...wani mataki zan dauka akansa? Dan Ta riga ta ci alwashi aranta cewa bazata kara yin wani juriya ko hakuri akan femi ba saidai komi da zai faru ya faru.

Tana cikin ayyana hakan aranta shikuwa yay zugum agabanta kamar zombie yana kallonta dan sosai ya riga da ya shagala wajen kallon irin masifaffen kyau da jann kayan data saka ajikintan yay mata.

Tana kammala zantawa da kwakwalrta ta kalleshi a takaice Batace mai komi ba.

Duk ya rude yakasa karantar yanayinta cos This is actually not wat he expected yazo ya tarar

Ya dauka zaizo yaga tatattara kayanta ajaka ko ta cika faammmm tana jiran shi da buhun masifa.

Da baiga ko daya ba A dan sakankace Yay murmushi ya riko hannunta bata kwace ba batace mai uffan ba yace

...u wanna freshen up?

Da giranta kacal ta amsashi snn ta kwace hannunta coldly saida yaji wani abu na fargaba ya cakke shi aransa, snn ta mike tsaye tana tfiya ahnkli sabida jiri haka ya dinga binta da kallo harta shige bathrum abunta bata sake juyowa ta kallesa ba....

Shigartan ne ya bashi daman tsayawa ya kare ma dakin kallo, he felt really really guitly and bad dayagagga kkrin datayi sai yanxu ya Gane cewa bai kyauta mata ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull