Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 14
Cheaters club book 2 complete novel Chapter 14: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 14. Ficewa yay a dakin domin ya kira Henry su tattauna yasan…
3,361 words
Ficewa yay a dakin domin ya kira Henry su tattauna yasan bazai rasa bashi shawarar akan abunda zai siyo mata ko wani abun da zai mata dan ya shawo kanta tay hakuri ba.
Tunda ya kaiga dakinsa waya kawai sukeyi sede henryn zugashi kawai yakeyi yanamai ce masa victoria ta fiye mita da takuri bata da hakuri kawai nema take ta jawo masa matsala dan haka kawai ya karma ya zaƙe yace saiya lallabata sosai sabida mata mayun kudine inhar zai kiyaye wajen bata attention to bazata wani iya rabuwa dashi ba.
Vicky ta cire kayanta duka acikin bayin snn ta dauko tatto fader gel ta shafa akan doguwar abun gogowa snn ta dinga durzawa a gadon bayanta tana hawaye jin yana mata tsinannen zafi yana mata zugi amma bata bari ba harsaida ta cire sunan femi ajikinta ya rage tabon tatto din ne kawai dankadan dayarage snn ta fada cikin ruwan wankan data shiryashi da essential oils da himalayan salt in other to calm her nerves Dan ta samu cikakken nitsuwa.
Koda take wankan ma babu abunda take tunani face abunda ya dace ta furtawa femi, wanu zucyar na zugata ta haura masa ta gaggaya masa bakaken maganganu wani zucyar kuma yanamai tuna mata cewa the last time datay masa hakan akan nile har iyayenta saida ya saka suka juya mata baya.
She just cant allow him to get to her any longer dan batason ta sake bata lokcinta akansa koda na scnd daya. Shiyasa Taji kamr ta gwammaci tay shiru taga iyakar gudun ruwansa taji me zaice mata kafin nan ta amsa.
After a while ta nitsu har sanda ta gama kammala shirya tunaninta ta dawo bisa seti can snn ta fito daga wankan daure da bathrobe ajikinta kafin kace wani abu harta bushar da sumanta a dryer ta kuma shafawa sulbabben fatar jikinta mayuka tabi ta shafa oil akan tabon da tatto din yay mata abaya.
Daganan ta hau tattara dakinta dukkan wani abu daya danganci shirin anniversryn datay ta tattarasu kaf kaf ta zubasu duka acikin wani katoton jaka ta jashi ta fitar waje ta ajeshi.
Romantic Bedsheets dinma duk ta hada ta tarkata ta bi ta dauki wani blue colour me azaban kyau ta shimfida akan gadon ta sauya ma dakinta qamshi gabaki daya ta dawo dashi tamkar wani sabuwar waje na daban snn ta kara gudun A.c ta zauna agaban madubinta cike da nitsuwa da taurin zuciya ta share dukkan wani abunda ke mata ciwo aranta ta rufesa kirif ta tsantsarawa fuskarta ligh make up me daukar numfashi.
Tana kammala make up dinta ta dauko wani sport wear na hermes all white Guntun skirt da karamin rigarsa iya cibi me hula sann ta kama sumanta duka ta cusashi aciki bakaramin kyau yay mata ba tabi ta saka white sport canvas ta wuce gym din dake gidan abunta dan tasan inbata motsa jikinta ba dolene baqin ciki ya dinga gumeta frm time to time gashi tay alkwarin bazata sake bawa femi alfarman ganin hawayenta arayuwar sa ba.
zucyarta yay raunatuwar da ita kanta bata san yawan shi ba. Haka kawai takejin kamar she dont care anymore, auren ma ya fice mata aranta lkci daya batare da tsammaninin hakan ba.
Its feels natural for her to feel like kamar bata bukatar femi, like she is done trying to fix things with him he can go to hell sabida itama tanada nata rayuwar agabanta dayakamata ta kula dashi.
Tunda ta isa gym din gidan nasu ta hau kan machine din trade mill tana gudu akai babu abunda take ayyanawa aranta face neman mafita, she just want to feel sooo young and successful again.
...wani zucyar yace mata hala dalilin kenan daya saka kamfan elmario ya amshe sakonta duk dama bata wani cancanta ba..
maybe is her wake up call to a new begining dan haka is time ta maida hanklinta akan personal growth dinta ba akan femi ba.
Besides shekara da shekaru bataga wani abu kwakkwara da hakurinta ya sauya akan alaqarta na aure da femi ba...
Is like tana dada rufa masa asiri ne shikuma yane neman ya kureta ya kuma kuntatawa nata rayuwar wanda abune datake ganin sam bazata iya daukarsa ba dan harga Allah gani take kamar tafishi cutuwa.
Tana tsaka da wann tunanin taji an kashe trade mill din tana daga kai suka hade ido da femi da alama shima wanka yay ya sauya kaya kafin nan ya fito.
Suna hade ido Wani irin baqin ciki taji na tason mata musmmn dataga yana kalle mata jiki yana lashe baki acikin sauri tay controling emotions dinta ta kallesa da nitsuwa ayanyinta....
Yace "Hey..ashe nan kika dawo naje room dinki banganki ba.
Atakaice Tace yah, whats up?
Yadda ta amsa shi batare da wani sautin bacin rai ba ya balain darsa masa fargaba aransa bana wasa ba.
Cike da basarwa Yace nothing much just checking up on u.
Bata kulashi ba ta sauka akan trade mill din tanamai juya albarkatun jikinta acikin nitsuwa sai kallonta yake har suka nemi waje suka zauna akan soft cushions din Dake wajen.
Suna zama sai ga suzan me aikinsu ta shigo da tray acikin ladabi ta gaishe su duka suka amsa normally tana kammala serving dinsu shayi tabar wajen taje tafara aiyukanta na safe...
Shiru ne ya ratsa tsakaninsu femi gaba daya ya kasa nitsuwa ganin yadda victoria ta sake ranta tay kyam taki ta nuna wani alamar bacin rai a fuskanta kwata kwata....... DO HOT SHARE PAID PAGES...TO SUBCRIBE CHAT 08060712446. 28
#SURAAYYAHMS
Ganin tay shiru tana shan shayinta da wani irin sanyin aji batace da shi uffan ba yasakashi yin gyaran murya ya dubeta yace "arent u going to ask me?
Saida ta dan ja numfashi snn ta Aje cup din shayin tay relaxing jikinta Ahnkli ta dubesa cikin idonsa "Tace about what?
Yay dan shiru can yace mata everything.
Karamin scoff ya kufce mata, tace "Everything is nothing femi" U just left and now ur back home ...So?.
Muryansa wani iri jin bata bashi vibe din dayake so din ba yabi ya kureta da idanu snn ya kyabe baki..
kai tsaye ya tsunduma cikin maganan dayasan tanaji ransa ne ya furta mata da bakinsa, cikin nuna ko inkula a yanayin sa yace. "you knw i attended my friend's birthday yestade.
Baiyi tsammani ba yaji Tace Oohhh dats nice. Ya birthday..i asummed u enjoyed it.
Kasa iya daurewa yay ya riko hannunta da wani irin sassarfa saida reflex action din nasa ya tursasata ta juyo ta kalleshi da alamar tambaya a kan fuskarta
Yace what are thinking vicky? Meyasa kike amsa ni haka kamar baki damu ba.
Dakakken Murmushin da bata san daga ina ya fito ba ya kufce mata Tace "Damuwa? Akan me zan damu and why did u say that...
Cikin son ya hatsalata yace nothing kawai de U look upset ne. Ko wani abu ya batamiki rai
Atakaice Tace what are u tryng to say huhn?
Girarsa na sama a dage yace "I dont knw ke kikasan me ke damunki..
Yar karamar Dariya me aji tay sann ta dau shayin ta ta cigaba da sha ahankli tay banza da shi takuma shareshi.
A matsayinta na wayayya mace Ta riga da tasan dukkn wani luggan namiji dats manipulative, shine zai maka laifi amma bazai fito fili ya nuna yayi ba sai yadinga alaqanta mace da fushi sabida itadin me raunice matsi zai iya sakawa ta fara reacting ta furtashi waje.
ahankli takai kai shayinta baki tana kurba tana sha tana tunani at same time tana sakin wasu sanyayar murmushi da suka kara wargaza ma femin setin kwakwalrsa gabaki daya dan sosai yaji brain nashi rikice sam ya kasa gane mata.
Batace da shi uffan ba dan Aranta ta riga taci alwashin cewa femi bazai sake samun wani dama awajenta ba bare kuma yafiya akan abunda ya mata jiya musammn ma indan ta wann toxic hanyar yake son yabi toh bazata taɓa bashi dama ba.
Satar kallonta ya dingayi da mamaki da kuma tsananin haushin attitude din datake bashi Numfashinsa na haurawa sama sama har ita datake gefensa tana dan shako motsin da zucyarsa takeyi acikin rudani..
Gabadaya ya rude ya rikice jin bata furta abubuwan dayake so yaji ta furtan ba, tuna da cewa akwai wani hanya nan take ya marairace fuska cike da kame kame ya dan gyara zama yace hey, vick.. I dint really leave this house for anything personal kawai de abubuwane kingane?
Dan Shiru ta yi kafin nan tace its okay i ques the birthday is more important. Ba damuwa!
Baiyi tsammanin jin hakan ba ransa ya jara sosuwa Kai tsaye dan ya dawo da ita hayyacinta Yace mata yes. Kamar kinsani kuwa The birthday was very important to me.
Ya kureta da ido yaga me zatace Dan Shi burinsa shine ta dan yi hayagaga tay bori da kuka sai ya yaji dadin ladabdtr da ita.
Cike da dauriya ranta na tafasa amma Sam Taki ta kalleshi duk dama zucyarta yay baqiqirin da maganan daya furta matan yanzu..
A brain dinta ta furta masa tambayoyi sunfi tamanin amma ta kasa furta masa a fili sabida aganinta inhar zai iya budan baki yace mata birthday abokinsa is more important than their marriage babu amfanin yin wata magana da shi.
Shirun datayi yasaka Dukkansu babu wanda yace ma kowa komi harna dan wani lokaci.
Sai can dayaga kamr bazatace mai uffan ba cikin gyaran murya ya kaucar da maganan hidimar gabaki daya batare da ya nemi su tattauna ko su sansanta kansu akai ko ya bata haquri ba, saima yay kamar abunda yay jiyan ma aiba komi bane normal ne.
Alokcin vicky ita kadai tasan abunda yake mata ciwo, zucyarta na tsananin harbawa, ranta gabaki daya yay baqiqirin amma haka ta daure ta cije tanamai saurarar noise dinsa dayake mata na renin hankli da tsagwaron rashin kunya a idanunsa،,ya nuna ki ajikinsa baisan ma yayi wani abu ba, he talks with full audacity and ego yanamai mata hiran birthday din chief okoro sede bai sani ba with each word he said babu abunda yake kara mata face tsananin nadamar bata lokcinta akansa wajen neman maslaha wa aurensu.
Deep withing her heart she is screaming Regrets on time spent on a man with no emotional intelligence, Femi is a child.. immature! Ta rasa yadda akayi bata gane hakan da wuri ba. Dan in ba brain din yaro ba babu wanda zai aikata wann abu a zamanin yanxu.
Zamansu anan din baifi na minti ar'bain ba they have a non repulsive talk kowa na nunawa kowa bai damu ba. Yana surutun sa a fili ita kuma tanata zantawa da a zuccyarta a sirrance
Ganin be gane kanta kwata kwata ba yasaka yay mata sai anjima ya tashi yana tafiya duk jkin sa yy tsamii yahaura sama dakinsa ya kulle kansa aciki, yana zama ya kira chief ya gaya masa cewa ai vickyn ma bata damu ba, shikuwa chief abun sam bai masa dadi ba dan so yay ace yay sanadiyar rabuwar su ayau. Sai yace masa kawai ya shareta in abun ya cicciyo ta zata neme sa da maganan dan kanta ai mace sam bata yafiya.
Sabuwar Yanayin vickyn sosai ya dame prince femi aransa ta inda basa tsammani kawai dai daurewa yake yana amsar karfin gwiwar da suke bashi na cewa vicky zata dawo masa dede.
Ata fannin vickyn kuwa tunda femin ya barta ta kejin wani irin tsinannen jiri da kyar ta kawo kanta dakinta, ta sulale kasa tana kuka marar sauti atakure...
awajen sa hakan zai iya yuwa trick ne na wasa da hanklinta amma awajen ta iya wann yanayin daya nuna na rashin damuwa akan lefin daya aikata matan yasaka taji ya kara tsane mata aranta gabaki daya.
Yadda ya nuna kamar baima san me akeciki ba sann bema san ya aikata mata komi ba yay mata ciwo fiye da yadda taji zafi aranta jiyan.
Tay kuka a dakin harta gaji tafarajin bazata iya daurewa ta zauna agidan tana kallon fuskarsa ba, deciding tay taje wani waje ta huta dan ta samu cikakken hutu da kuma nitsuwa, yau ko breafsat bataji shaawar ci ba tay baccinta mai nauyi Daga bisani ta farka ta karayin wanka snn ta tattara kayanta a yar jaka tabar masa note cewa zataje business trip a acan Abuja....DO NOT SHARE #SURAYYAHMS. PAID BOOK NE CHAT 08060712446 TO GET URS. 29 #SURAYYAHMS #PAID BOOK #08060712446
******* Yau ake cika kwana daya rak da wuni daya da dawowar Halisa daga asibiti bayan abunda ya faru da ita ayayinda shema'u marafa take famar cin dunuyarta tare da sabon sauranyinta alhaj shafiun tun jiya da safe data iso garin Abuja.
Tun isowarta da sukabar airpot da convoys dinsa suke murza yawukansu na shakatawa atare acikin garin Abuja.
Yakaita nan suje can duk ya gama makantar da ita da dumbin kayan duniyar sa masu yawa da matsanancin shagaltarwa.
Tsabar iya nunawa namiji nananniyar soyayya mai cike kwarewa a fagen makirci da karya bisa ga neman cikar babban burinta na duniya yasaka Alhaj shafiu ya haukace ya kasa iya rabuwa daita aranar da ta iso kowani motsi tay yana manne da ita.
Hakanan ta zaqe wajen shagalatar dashi da wasu sanyayar kalamai manya manya dake rufe da yaudararrun baitukan soyayya kuma nitsatsu masu cike da zakin tsantsar yaudara acikin su.
Babban burinta shine taga ta mallake zucyarsa gabaki daya ya zamo bai ganin kowacce ƴa mace da daraja face ita.
Alhaj shafiu jin kansa yake tamkar wani dan sarki idan shemau tana tarairayarsa tana kuma kalallame shi, dan haryau a budurwa mai ji dakanta yake kallonta daan bata taba nuna mai cewa itadin matar aure bace shima bai taba lura da hakan ba tsabar yadda ta sakar masa zucyarta baki daya tana rikita masa kai da tunani da zafafan kalaman so masu tasiri da kuma dadi.
Duk yadda taso ta isaga gidan su mahmud akan lkci abun saida yaci tura,
kwadayi da buri yasaka ta tabiyewa alhaj shafiun yau sunata yawonsu agari suna ziyartan manyan qaddorinsa na Abuja dan sabida ta dada tabbatar makanta cewa tabbas shidin ma yakai mijin hadiza kudi, anan suka bata lokaci suka kai har wani gaɓa suna hirararraki cikin jin dadin shakawtawa da soyewa.
Karshe ranar awani Babban Mansion quest house dinsa da bata taɓa ganin kyaunsa da irin girmansa ba ya saka aka ajeta to spend the nite tare da hadata da professional masu aiki su kusan goma wanda zasuna serving inta kamar sarauniya.
Dama can ta gaya masa cewa aikine ya kawo ta Abuja dan haka baisan da cewa tazo ta duba jikin mijinta mahmud bane danshi baima san tana da aure ba.
Zama yay agidan ya tayata hira, sai can Wajajen 10 na dare snn sukayi sallama da masoyinta alhaj shafiu Bayan nan She was alone in the house sai masu mata hidima wanda take treating dinsu tamkar bayi.
Hanklinta kwance dan alhajn ya riga dayace mata akan zaije Kasar waje acikin jet dinsa da daren nan, tasan bazasu hadu da safe ba dan haka shemau ta saki ranta acikin daularsa tana baza mulkin fir'auna tamkar ba ita ba.
Gabaki daya ta rikita masu aikin gidan da tsawa da tsiwa, ga cika da nuna isa.
Hatta sleepers din zata saka akafafunta sai ta kira mai aiki tazo tun daga kasa ta saka mata alafarta hakama idan zata cire sai dai ta kira.
Jin kanta a irin wann daula datayi yasa taji ta kara rikicewa da burin son ta kasance acikinsa.
He biggest goal bcom marrying this man, kai sai ma ta aureshi. Dan irin daular data gani yana dashi shine exctly abunda zucyarta yake so din sosai. At this point ji take kamar tarkonta ne ya kama mata babban ɓera. Tanajin inhar bata aure alhaj shafiu ba to hala mutuwa tayi.
A dede wann gabar har ji take koda ace jikinta ya nema bata jin kamar zata iya hanashi dan kawai ta mallake soyayyarsa.
Gidan daya ajetan quest house dinsa ne amma tamkar aljannar duniya haka yake ita kanta shemau saida ta kasa bacci aciki dan guest house din yafi gidan mijinta mahmud sau ashirin a kome da kome.
Aganinta inde wann quest house ne inaga in ankaita asalin main mansion? She cant wait to become the talk of town dan tasan dolene makiya suji haushi inta aure mutumin nan.
Ga masu aikin gidan suna mata wani irin hidima kamar matar sarki, jin kanta ta dingayi acikin wani irin yanayin da bazata iya fassarawa bama dan kuwa wann rayuwarce mafarkinta ba wanda takeyi ynzu agidan mahmud ba.
Akan wani lumtsatsen gadon mai fitinannen laushi tay bacinta har da minshari, Washe gari da safe bata tashi farkawa ba sai wajajen karfe 9:30 na safe, har saida tay wanka snn tay sallah sama sama agurguje, anan ma taga masu aiki sun mamayeta kamar bayi ko tsinke basu barta ta daga ba suka mata komi.
Sanda ta sha wayar soyayyarta me tsayi da alhaj shafiu snn ta mike daga kan couch ta sauko kasa domin karyawa.
Abinci kala kala taga an jera mata akan dinning din kamar ba asonsu.
Bayan ta kammala cin Breakfst dinta tay nak aka sake turowa da wata dunkulliyar jeep mai hade da security escort nan suka kama hanya izuwa gidan su mahmud suna hanya amma duk annurin fuskarta sai daya dauke cak inta tuna cewa auren sa kamar kashin kifi ne awuyanta ayanzu.
Ata dayan bangaren kuwa Washe gari da sassafe mahmud ya farka daga bacci dauke da sallati abakinshi bayan ya kammala karanto adduar sa dayajima yanayi bayan ya farka daga bacci.
.."subhanAllah wal hamdullahi wallahu Akbar kafa goma,yau yayi addua mai dumbin yawa wa iyayensa da matansa da dukkan sauran Ahalinsa, ya saba da musu addua ako wani moment dinsa ta farkawa daga bacci musamman ma irin wnn lkcin data kasance mustajaba baya iya mantawa da kowa.
Daddan Qamshin turaren humra daya tadasa a gajiyayyen baccin dayayi yasaka shi sakin wata kayatacciyar murmushi
saukowa yayi a gadon ya hau lekawa ta windown sanin cewa bazai wuce antynsa bace ta biyosa har nan har acikin ransa kewarta shima yakeyi sosai dan sai agidan su yake iya jin wnn kalar kwanciyar hanklin.
Ahnkli ya sauka yabar kan gadon ya nufi bathrum dinsa ya fada wanka within 40 minutes har ya fito ya shirya kansa tsaf cikin wata lallausar yadi da ake kirar sa mai laushi wanda ko makaho ne ya ratsa ta gaban sa tabbas yasan ansaka abu mai kyau da tsada, sky blue colour ne kalar kayan an masa dinkin jumfa data dedeta da dirin jikinshi sosai yasha adon kece ya dora da hular sa ta tandoran duk sanda yay dressing babu marabarsa da wani angon sai sanyin nitsuwar dake tafiyar dashi, turaren sa ta creed aventus ya shafa kadan qamshinta mai tsananin sanyi ta biye har jikinshi da numfashin sa inya shaka dantana da kama jiki sosai.
Direct sashen maman san ya nufa dan jiya basu wani samu daman ganawa da ita sosai ba sabida suna tare da yar uwarta akusan kowani lokci.
da nitsatsiyar sallamar sa ya kawo har bakin dakin sau uku yana nanatawa baiji an amsa sa ba saiya dan leko kansa taciki, gani da yy babu kowa a falonsu ya sashi karasowa har cikin sashen ya tsaya bai jima ba karar sautin taku yaji ata bayansa wanda yasaka shi saurin juyo da kai izuwa kan matakalar da ake takawa a nitse
Tun basu hade ido ba kirjinshi ta sauya bugu musmmn ma daya hango hafsat acikin wata shiga dauke da tray din Abinci sanyin kunyar dake tafe da takunta yasaka saida yaji wani maqudan sanyi ya ratsa shi ta ciki dan hatta yunwar datake makale acikinshi saida ta hargitso kusa.
kanta ta sauke can kasa tana dan fargaban ganinsa agabanta sede aranta tsabar farincikin ganinsan ne shimfide akan fuskarta shikuwa sai kallonta yake bai dauke kwayar idanun sa aknta ba sabida yadda yaga ta canza acikin peach colour lafayar da hajya binta ta bata tacr ta saka ajikintan gashi bakaramin dauke masa hankli kayan yayi ba dan kalar bakaramar amsar kalar fatar jikinta yayi ba.
Duk dama ya riga yasaba ganinta dukundukun a matsain me aikinsu amma koda yau ta sauya sutura sai yaga kamar watace daban ba hafsat dinba.
Tabbas Bahaushe yay gaskiya dayace sutura shine mutum.