Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 4
Cheaters club book 2 complete novel Chapter 4: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 4. Tsabar ran khalid ya baci duhu duhu kawai yake gani agabansa…
3,349 words
Tsabar ran khalid ya baci duhu duhu kawai yake gani agabansa ayyin dayake saukowa kasa cikin sauri baima lura da su meenal dake zaune sunyi jungum junmgum a corridor din wajen ba.
mita yake arnsa yana cewa "i must knw who wrote dis review againts me, haaaa..wann ai bata suna ne...wai harnine za'a cire ni akan case din halisa mansa da lefin rashn bin dokar aiki? Who even show them my files,waye ya nuna ma board cewa banmi tsarin aikina akanta ba? This is pure hypocrisy..haaaaaa, my enermies ooo....my enemies oo, nasan babu wanda zaimin wann abun inba khaleel ba, dat boy is daring me...and i wll deal with him..nima zan nuna masa cewa ina da ubanin gida asama. I wll make him regret this day...da wayann raye rayen aransa ya wuce office dinsa tunda ya zauna kiraye kiraye awaya kawai yakeyi koda zaiji damshin gaskya bisa zarginsa akn khaleel dayakeyi da masa cune a sama sai kuma yaji wani zancen daban daya kulle masa kansa sosai.
Domin kuwa yawancin mutanen daya tuntuba dan sugaya masa waye yatoni asirinsa ce masa sukeyi wai wani nakusa dashine ya kawo cunen sa..Ranar gabaki daya ya kare masa ne akan bincike da tunanin wayene daya tsanesa harda zai zauna ya tattara information dinsa kaf akan halisa yakai gaba har a ciresa akan case din jinyar haliisan gabaki daya.
Daya daga cikin abokansa dasuke kud da kud duk sun gayamai cewa zaiyi wuya ace khaleel ne, dan hatta binciken sirri dayay akan halisa duk zancen ya kaiga shiga kunnen board ...dayan abokin ne ya bashi shawara akan yay komi ahankli ynxu kar hakan ya jawo masa kora mai gabaki daya.
Hanklin khalid sosai ya tashi, yakasa zama baki daya adan dolensa ya bar asibitin ya wuce gida da tunani mai yawa aransa baisan da cewa Zach ne ya dirka masa wann aika aikan ba yafi bada zarginsa akan khaleel. Tunani kawai yake ta wani hanya ne ya dace ya billo masa dan bazai taba kyalesa ya hanashi kusantar halisa da dukiyarta ba.
Ata fannin su meenal kuwa kusan zaman kurmaye sukayi awajen da suka zauna suna jiran wani kwakwarn labari akan lamarin jikin halisa,
tsakaninta da jasmine sai kallon tsana da na harara, hjy nadiya taja tsaki awajen yafi sau tamanin dan badon yarta tana wajen ba da babu abunda zai saka tazo nan bare ta damu.
Basu wani jima sosai ba saiga nan shemau ta faso, a hujajan tazo wajen danata tashin hanklin, Tana gaishe da hjy nadia ta jawo su meenal gefe suka tsunduma hirar lamarin kowacce tana kawo nazarinta akan dalilin da zai saka halisa ta yanke hukuncin kisa a wann yanayi.
Kamar yadda vicky bata wani amince da hakan aranta ba hakama shema'u ta dinga fada tana cewa lallai lkci yay da zasu tashi tsaye su bincike zach hala shine yakeson yay amfani da wani salo domin ya kashe musu halisa.
As usual meenal ce kawai bata amince da wann shirin ba, nan ma ta kuma tubure musu tace musu samm ita tana da tbbacin cewa bafa zach bane dalilin dayasaka halisa fadawa cikin wann halin saidai in kawunta..babu kalar musun da basuyi atsakaninsu ba,amma duk wajen saida tafisu zakewa badon komi take son tajuya musu akalar maganan ba saidan batason asake tono magana aje asirinta ya tonu.
Wann karon shemau da vicky suka tsaya akan ra'ayoyinsu dan aganin su abunda aka ma halisa awajen aurenta yafi cin rai akan wanda aka mata awajen party shin mezai sa batayi tunanin kashe kanta awcn lokcin ba sai a wann lkcin tabbas sai inda akwai wani abu da basu sani ba.
Jasmine dake jinsu daga ca agefe sosai ta dada fahimtar abunda yasaka meenal take famar bobboye zancen zach abun sosai yakeci mata rai zucyarta nata zugata akanda ta tona mata asiri agaban sauran kawayen sedei tunanin yadda halisa zataji inta wargaza musu clique dinsu yasa bata yanke wann hukuncin ba.
Wuni khaleel yay yana aiki akan gwaje gwajen da yay ma halisa sosai yasha mamaki dayagane abubuwa dayawa aciki harda cewa babu wani dandanin percentage na giya ko drugs ajininta ko over dose na wani magani.
dake bata farka da wuri ba. Hudu na yamma nayi ya saka aka koresu meenal da ayarinta suka bar wajen suka koma gida yace ace musu su dawo gobe da safe.
Uxtaz ne kawai aka barsa yana tare da securities dake tsaron inda suke shikansa baiya cikin hayyacinsa dan haryanzu lamarin na caza masa kansa sosai dan gani yake kamar yafi kowa sanin yadda halisa take da tsananin juriya tare da dauriya dan wann abun bazai taɓa sakata tace zata kashe kanta ba.
Ata fanninsu meenal din ma yau kusan a gidan shema'u suka baje koli Tun barinsu asibitin har izuwa karfe sha biyu na dare hayaniya kawai sukeyi atsakaninsu.
Musammn ma da hadiza tazo da nata zancen akan bata ƴarda da zach ba. A daren kusan haukacewa ne kawai meenal batayi ba ganin kawayenta kaf suna son su taru sutono mata inda batason budewa.
Kusan dukansu bakinsu daya itace kawai nata da daban..ganin sun fi karfinta yasaka tasaka musu kuka, duk basu gano ta ba,sai cewa take kawai abar maaganan sai halisa ta farka idan aka tambayeta akaji ta bakinta sai a dau kwakwaran mataki.
Tay musu hakan ne da tunanin gobe halisa tana farkawa itace zata soma zuwa kanta ,snn zatayi kkrin juya ra'ayin halisar akan zancen bincikar zach batare da sanninsu ba sai kawai abar zancen cikin ruwan sanyi.
Vickyne kawai ta wuce gida itakam awajen shemaun ta kwana haka tasaka shemau agaba da kareraye har suka raba dare suna tattaunawa kafin can sukayi bacci.
Daga asibitin kuwa tun wajajen karfe 10:30 na dare kafafun jama'a ya soma daukewa wajen ya dadayin shiru sosai...
Khaleel ne zaune akan kujerar office dinsa da wata mini ipad agabansa Dake lokci izuwa lkci yana dan zuwa dakin shidakansa yana mata allurori yana dubata kafin ace karfe takwas vitals dinta sun soma dedetuwa wanda ya dada bashi tabbacin cewa zata iya farkawa bada jimawa ba.
Hakan yasaka bacci kauracewa a idanunsa tunda ya zauna ya bude tab dinsa binciken akan rayuwarta kawai yakeyi dan Duk wani tag da activities daya shafe rayuwar halisan yake jo yana dubawa yanamai duba ire iren abubuwan da mutane suka cewa akanta dame kyau din da marasa kyau din musmn game da alakarta da zach da kuma abunda ya faru yau da ita.
Wani abun harya dan sosa masa ransa amma hakanan dai ya daure ya cigaba da dubawa harya dan soma fahimtar wasu abubuwa masu matukar muhimmanci game da ita.
Abubuwa dayawa daya gani sunsaka Yakasa samun sukuni a zcyarsa Shide haryanzu baisan meyakeji aransa game da itaba sai yabari kawai akan he is just doing his job as her therapist. And it doesnt matter ko dan ya tsane halin yarinyar da ita kanta, sede kodan sabida haushin zach din nan da yakejin aransa yakejin zai iya temakawa.
Ya jima sosai yana shige shigen files da shafuka yana dubawa harsai Wajajen karfe daya na dare kafin nan ya samu sararin hutawa.
Uku na dare nayi sharp Kaman an tsikare Halisa tabude idanunta ahankali tanabin inda takeda kallo tabbas tasan nanba lahira bane, ahankali tajuyarda kanta karin ruwa datagani dakuma oxygen da akai hanging datagani yasa ta lumshe ido dan tagane she's alive but inane nan?
Yunkurawa tayida kyar kusan a rude ta tashi tazauna tanadanjin jiri kadan sann tasake bin dakin asibitin da kallo taga ICU room ita kadaine aciki..
Tsakiyar dare ne Waje yay wani irin shiru sai kuma taji tsoro mai tsanani na shigewa bargon jikinta da kwakwarlta.
Ahankli ta kalli ruwan da aka saka mata tabi ta kure ledar ruwan da ido na tsawon lkci yadda yake sauka in drops yasaka brain dinta ya cirke gabaki daya atake atake sai ya soma dawo mata memoryn dukkan abunda ya faru dazu.
Bari jikinta ya soma yi shikadansa, tabi ta Lumshe idanuwanta tana tuna Abunda zach yace ma media akanta,har lkcin da su meenal din sukazo suka dauketa suka kaita gida,duk wani abunda ya faru daga lkcin har izuwa lkcin da meenal take gayawa mumnynta komi da komi har fitarta agidan da zuwanta bakin gadan da hada ido da khaleel da sukayi da fixge hannunta anashi tayi da faduwarta cikin ruwan da binta cikin ruwan dayay da lkcin da yake kkrin hura mata iska abaki, iyanan memerynta ya tsaya mata cak bata iya sake tuna komi ba.
Kuka takeso tay amma dake khaleel yay mata allurai da dama yasaka tension din bai tsananta mata ba. Hawaye kawai ta dinga saukewa daga zaaune tabi ta kure bangon asibitin da ido.
Daganan ta nitsar da zuciyarta matukar nitsarwa snn ta soma lissafi da ayyana wasu tunane tunane masu tsananin zurfi akan rayuwarta iriin wanda bata taɓayinshi ba...
Dukkan wani dan adam dayake cikin rayuwarta saida tay kyakkwan nazari akansa sann ta soma dora kowa abisa sabuwar matsayin da ta bashi azucyrta a yanxu.
Tamkar wata Daban haka takejin kanta acikin daren, ji tay kamar mutuwan gaske tayi snn Allah ya sake tada waata halisar daban, ba halisar da kowa ya sani ba. dan ita kanta tanaji ajikinta cewa ta samu sauyi sosai bisaga tsarin tunaninta da rayuwarta saidai batasan yadda mutanen dake zagaye da ita zasu dauke wann sabon sauyin datakeji ajikinta ba.
Yadda kasan mutum mutuminta akayi haka ta kafe waje guda da idanunta tay nisa sosai acikin tunani.
Washe gari da safe Wuraren biyar da rabi bacci mai balain nauyi ya wuce da khaleel bai farka ba har uztaz har yay alwala baigansa ya fito ba saiyazo ya tadashi kafin nan shima ya wuce masallaci.
Bayan sun idar da sallahn andan ragu khaleel na zaune ata baya yanata lura da yadda uztaz ya daga hannuwansa sama yanamai rokon Allah akan da yabada halisa lafya da kwanciyar hankli me dorewa har idanuwan sa suna tara ruwa. Shidai khaleel mamakin sa yaketa sha..ya rasa wani kwakwaran halin kirki halisa take dashi da har ma'aikacin nan nata ya damu da ita.
Beside jya dayay bincikensa kusan rabin abunda mutane ke cewa akan halisan sam bai masa dadi ba dan dayawan maza da mata masu tsananin jin kishinta da hassadar daukaka da arzikin da Allah ya bata gani suke kawai na karuwanci ne musammn ma da akasan cewa bata da kowa.
Shikansa kiris ya rage ya amince da cewa dan kudi kawai halisa take soyayya da zach dan iya abunda yaga anfi cewa akansu kenan snn ya kasa fahimtar meyasa mutane dayawa suke tuhumarta da zargi iri daya..aransa sai ya soma tunanin ko halama gaskiyane karuwancin kawai takeyi.
Saidai ganin uztaz a wann yanayi yasaka ya soma tunanin kozai hakra ya sassauto da nashi harsashen ya tuntubesa domin ya masa tambayoyi game da ita dan jikinshi na basa hala zai iyajin wani labari nadaban daga bakinsa tunda alamu ya nuna cewa shine mafi kusanci da ita.
Da kyar ya yanke hukuncin ayyana hakan aransa dan haka kawai baison yay wani abun da zai jawo masa raini a idon kowa.
Ahaka Har ya tashi ya bar cikin massallacin uxtz bai kammala mata adduar ya fito ba.
Deciding yay akan bari yaje ya dubata yaga yaya jikin nata yake tunda yasan dolene ta farka ayau din bisaga yadda yaga komi nata ya soma dawowa jiya daddare.
Yana shigowa ward din tun bai kaiga bude kofar ba ya hangota ta glass din windown tana zaune akan gadonta ta kafe bango da idanu batako motsi.
Da sauri yabi yakai idanuwansa kan monitor sai yaga komi nata ya dawo normal sede bai fahimce yanayin daya ganta aciki ba. Wanda yay masa kama da na cewa tunani me nisa takeyi wanda shikansa he cant begin to imagine menene haka take tunawa sann nazarin me takeyi haka da harta tara dukkan nitsuwaarta da lafyar iwakwalta awaje guda tayi shiru cikin nitsuwa.
Tsayawa yay daga windown yanata kallonta jim kadan saiga uztaz yataho wajen ya jonasa.
Kallonta sukeyi kowa da abunda yake rayawa aransa...uztaz ya kama hanya zai shiga dakin ya sameta kenan yaji ancapko hannunsa yana daga ido suka hade ido da khaleel ahankli ya girgiza mai kai da alaman karya je bare ya katse mata tunaninta.
Jiki a sanyaye uztaz ya tsaya yanata kallon yanayinta saiji yay khaleel din nace masa yallabai muje office dina mana kasha shayi,i think she need to be alone after some time saika dawo.
Uztaz bai musanta masa ba hakan ba duk dama baida niyyar binsa office din sedei yanayin yadda khaleel din ya katsesa da idanuna yasakashi kawai ya bishi abaya sukaje..... #SURAYYAHMS 08060712446 IS NOT A FREE BOOK
1️⃣0️⃣▶️1️⃣1️⃣ #SURAYYAHMS NOT A FREE BOOK 500 VIA 08060712446 CHATS ONLY....
jitayi gabaki daya ranta ya hargitse ya ɓaci kanta na juyawa da sauri sauri.
aranta kkri takeyi dan ta dawo cikin hayyacinta amma inaa tsananin zafin zazzabin tare da ganin meenal tare da mahaifyarta a asibitin yasaka taji zucyarta nay mata mummunan zafi.
Bata san lokcin isowar khaleel daf bayanta ba kawai jin inuwarsa tayi a daf da ita tazarar dake tsakanin su baifi taku daya ba,tunda ta san shine akanta sai taji wani gulluton abu na tsananin haushi ya tsaya mata a makwaronta ta kasa iya hadiyeshi'...
Yana zuwa batare da ya kalleta ba ya zuba fararen idanuwansa akan screen din monitor din snn ya dawo ya dora hannunsa asaman goshinta yanamai feeling zazzafar tempureture nata daga nan, kirjintane ya buga damm zuciyanta na wani irin racing kamar zai ballo ya fito waje dan hargitsi jin daɗddar qamshin turarensa yanamai dada bata haushi.
a hnkli ta juyo cikin sauri da kuma fargaba tana kuwa juyowar ta tsinci kwayar idanun ta acikin nashi itama kallon san kawai take dan kusan atake idanunsu yay mummunan sarkafewa acikin najuna, nan da nan tafara tunowa da komi daya faru ayayin da ta fadi acikin ruwan yabita ciki..
Lkci guda mind dinta ya doka mata tambayoyi daban daban sunkai kala goma as to why wud he even risk his own dear life for her sake???? Bayan tasan hala bazata taba iya budan baki ta gode masa akan hakan ba dan har yanxu gani take kamar khaaleel din tsinannen dan rainin hankline wanda bai iya komi ba sai girman kai arayuwarsa.
Fuskrta kamr na wanda zata fashe da kuka dan har iynzu ji take kamar ta tsaneshi, ta tsane duk wani abunda ya shafe rayuwar meenal da koma miye dake tsakaninsu gabaki daya. Irin feeling din nn na i want to be alone shine kawai takeji aranta da zciiyarta ynxun kawai ji take kamar batason ganin kowa akusa da ita.
Cikin wani irin yanayin datazo masa bazata ya sauƙe ajiyar zuciyar acikin wani siga mai cike da jikakken kasaita wnda yanayinshi yake Tamkar wanda yake tunanin wani abu dayake kallontan dashi..
duk tsananin duhun rudanin da suke ciki bai hana shi hango kwayar idanunta yanajin wannan nakasashen yanayin ba
tabbas sai yau yasan tay jarumtaccen kkri da har ta iya calming kanta a irin wann situation na repeated traumas dake faruwa acikin rayuwarta.
Ganin yadda yake kallon ta yasaka Da sauri ta dauke kanta ta mayar gefe ayayinda shima ya sassauto da nashi kallon ƙasa yabi ya harde ransa tamau kamr wanda yake gaban mutuwa fuskokin su duka babu sauki dan tamkar yadda suka saba a duk sanda suka ga juna haka yau ma abun ta kasance.
Kukan datakeyin take kkri ta hadiyeshi gabaki daya, da kyar ma ta iya aikata hakan, snn ta bar hawayenta na zilalowa kasa kamar ankunnasa.
a hnkli ya dago ya kalleta akaro na biyu, hannun ta yay niyyar kamawa dan ya juyo da ita, sai yaga ta firgita tamatsa can nesa dashi ta dada tamke fuskrta cikin disashen muryanta mai tsananin kaushi kmr ba acikin hayyacinta ba tace"
"What do u think u are doing?Batare da ya kalleta ba kasar wuyarsa yace.."okay, girl..u need to relax. Wani harɗe fuskanta tayi cikin gallazamai harara. Snn tace "i want to go home now..a masife ta furta Yay kamar baiji ta ba
...Ruwan Allura yake kkrin hadawa domin ya mata yasamu ya saukar mata da zazzabinta dayake ganin kmr shine yake kkrin hanata nitsuwa.
Tay shiru Tanagani dede yay ready knn zai danna bakin Alluran a vein dinta Da uban karfin da saida tasashi ya dakata tace
"Uz...uztaz?
Da sauri uztaz ya turo kofar ya shigo ciki..
Yes ma'am
Lunshe ido tay kafin nan ta bude hawayenta na zubowa ta mikamai hannunta dake rawa rawa tanamai cewa please take me home. Ka kaini gida ynzu. I cant stay here....tafara kkrin tashi jin ta kasa motsi sai Ta dan saci kallon khaleeel din sama da kasa da wani irin taurin kai ayanayinta ahankli tace im really suffocating,all this bunch of...i dont even knw..just take me out of here.
muryanta cike da tension mai tafe da takurarren sheshekar baqin ciki daya tokarate a kirji ta fadi tana hawaye at same time fuskrta a murde.
Sai kallonta khaleel yake aransa banda tsaki babu abunda yakeja dan yasani sarai zai sha fama da ita dama.
He sees her as a crazy stubborn freak ita kuma kallon marar hankli mai girman kai take masa.
Kkri take zata cire canulan ta sauko yanata kallonta bai hanata ba dan yasan dama bazata taɓa amincewa ta zauna a inda yake ba.
Kamr wanda yake karantar zciyartan dan ko a cikin rantana masifa takeyi dan bataga dalilin da zata farka da fuskokin mutanen da ta tsana da wanda take jin haushinsu aynxu azagaye da ita..
Tana kammala cire canular tay yunkuri zata sauko kasa wani irin jiri me karfine ya tashi zai kadata kasa tay luuuu zata rikito saidai kafin nan uztaz ya karaso,har khaleel ya tarota jikinshi Ya riketa sosai.
...suna hade ido wani irin sarkafewa sukayi cikin kallon idanun juna, a Cikin firgici tafara kkrin kwace kanta ya riketa dam dam wanda shikasan baisan meyasa yay mata irin wann rikon ba.
A mugun fusace tace malam ka sakeni mana wai wayace maka bazan iya tsayawa dakaina ba.
Sautin Masifar dataa hantaresa dashi yasa yaji kamar ya saketan ta fado kasan kawai amma ya daure har saida ya daukota ya dangwalata akan gado yabi ya hade ransa snn ya karkakde tafin hannun sa.
Duk abunda sukeyi su meenal sunajikin windon sunata kallonsu hjya nadiya kamar zata fashe dan haushi.
Tambayar meenal take Kode ciwon haukane ya kama halisar?
Lkcin bam jinta Meenal takeyi ba, shiru tay sosai tanata kallon kalar rikici tareda fushin dake wanzuwa acikin yanayin halisa wanda tunda can da suke tare bata taba ganin irinsa atattare da ita ba. Its seem halisa is frustrated and angry abt sumting har abun yana nunawa akan fuskarta.
Itade Tasan Yawanci a nitse halisan take farkawa, bata fushi bata hantarar kowa yau kuma sai taga kmr abun ya sauya gabaki daya Koda khaleel ne???
Gani tay Banda masifa babu abunda take saukewa khaleel din duk da dukansu sunsan ba acikin hayyacinta sosai take ba amma dukkan wani zafin fushinta akansa kawai taketa saukewa .
Tana hawaye cikin mita tanacewa "Dont save me anymore..."Banaso, ni bance maka inason wani temakonka ba..let me die mana ina ruwan ka dani.
Dik yabi Ya rasa metake nufi da borin nata.
Dont save me din nan dan ya tarotane ko dan ya risking din rayuwarsa ya cireta daga cikin ruwa??? Idanunsa duka na akanta aransa yace ....This girl is purely insane amma zanyi maganinta,..Ya raya hakan aransa yabi ya harde ransa sosai.
Kusan A dame uztaz ya karaso kusa da ita ya dan tsaya yanamai cewa Kiyi hakuri ...ure not strong boss...Dr khaleel is going to inject u and i promise zan kaiki gida bayan nan,. Ya dada sassauto da muryansa kasa kasa sigr lallashi
Hawaye mai sanyi ya kufce mata ahankli tace nooo nooo nooo. Nan din ne kawai banaso i wanna leave. Am already fine. Banajin ciwo a ko ina..
Karamin Tsakin da Khaleel yaja ne ya katseta ta juyo ta kallesa ganin fuskrsa babu wani alaman rahama ..yace mata Ure not the one to decide that just relax..tun bata amsa ba ya dauke kansa tareda kamo hannunta da karfi izuwa nashi snn ya rikeshi gently tay tay ta kwace hannun amma ina karfinsu ba daya ba, jin bata iyayin ko motsi yasaka ta saki hawaye.