Kenza eBookz

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 5

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 5

Cheaters club book 2 complete novel Chapter 5: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 5. Dada harde ransa yy bai saketa ba har saida ya kammala dukan…

3,363 words

Dada harde ransa yy bai saketa ba har saida ya kammala dukan alluran da zai zuba awajen snn yabi yay mata dukkan abunda yaga ya dace yayi kafin ma ya gama harta fara sanyi tasoma dawowa cikin hayyacinta dan already ya zuba mata antidepressant masu karfi aciki.

Wann anti depressant din ne ya sakata ta nitsu tay shiru kamar ba itace take mitan nan ba, ta nitsu da hawaye abisa fuskrta tanata kallon uxtaz daya zauna agefenta batare da sunce ma junansu komi ba..

Suna hade ido da khaleel yace masa malam pls inganka a office dina mana..

Tun uztaz bai amsa ba Halisa tace no babu inda zaije gida kawai zamu tafi.

Karar Wayarsa ne ya dan dauke kansa akanta yaga security ne ke kiransa saiya dan ja daga gefe Dan Tun bai tankata ba saiga nan su meenal din sun shigo ciki kawai sai ya dauke wayar ya kara a kunnensa yana magana da security.

Daga can Security ya sanar dashi cewa sunyi baki da suke son ganin marar lafiyar

Khaleel Yace One person at a time...sabida bama bukatar hayaniya.

As usual da wani irin sauri mai tattare da kukan makirci Meenal ta taho cikin rauni zata rungume halisa domin ta gabatar da qudirinta

Lkcin kirjin halisan na bugawa da tsananin karfi tun meenal batakai ga taɓa jkinta ba tay firgit tamaida kanta can baya saman gado ta dauke kanta adan fixge batare da ta sake musu fuskarta ba.

Kusan a rikice meenal din kecewa halisa its me meenal what happen? Meyafaru kiketa fushi baki gane mu bane nida mummy ne fa..we r here for u as a family.

Ahankli halisan tabita da wani irin bakuwar kallon rashin sani dan dukkan maganganun nata sai dawowa mata akanta suke yuuuu tanajin kamr ta wanka mata mari ahalin yanxu...

Bama abunda tay matan ne yake mugun bata haushi ba, iya wann fuska biyun datake sakawa agabanta tanamai nuna cewa tafi kowa kaunarta a duniya yafi komi cimata ranta ayanxu bana wasa ba.

Ganin halisar tay banza da ita yasaka Ta wani fashe da kuka hartana ragwabewa hajy nadiya tabi ta rirriketa...

Mummy banajin Halisa is okay..kamar fa...

Batare da ta karasa ba ta dawo daf jikin gadon snn tace ..halisa are u okay??Sam sam halisa taki tace mata komi kuma tabi ta hanata taɓa mata jikinta

A ragwabe Tace Halisa ..i am here for you...

ahankli halisan tace okay..Kaina na ciwo i cant talk now.

Cike da sigar masifa hajya nadiya tace halisa kinban mamaki Akan me zaka yanke ma kanki wann hukunci akan ɗa namiji???? mtssss Ko shine autar mazane da bazaki iya kyalesa kiyi rayuwarki ba. Kiga irin halin dakika saka kanki aciki ganan yar uwarki amina ma kwana tay tana kuka akanki duk ta galabaita ko abinci bata saka acikinta tun jiya ba kidai dingayi wakanki fada wann soyayya dakika cusa aranki ta banza da wofi kina mutuwa dik ya zama tarihi awajen kowa bama wanda kike shhirin kashe kanki akansa ba.

Masifar takeyi kodama halisa zata hatsala ta gaya musu abunda yake cikin cikinta amma sai ta kalle hjy nadiyan kawai tayi batace musu komi ba.

Cikin kifta mata ido Meenal tace haba mummy calm down nasan kin damu da rayuwar halisa amma meyasa zakice mata hakan bayan ninasan ba akan zach bane ko halisa ??? Cikin lallami ta zauna kusa da halisan tanamai mata magiya

Halisa Pls tell me is not bcos of him.

Hawaye taf idanun halisa danko sunan meebal din kasa furtawa tay ahakli tace pls i need to be alone for now.

Meenal tace I cant leave you alone bayan kinsan ko duk duniya basu bukatarki ni bazan taba iya rayuwa batare dake ba. Pls ki gayamin menene matsalar halisa nayi maki alkwari koma miyene shi zan tsaya maki akansa sai munga bayansa.

Nan da nan tafara wasu iriyar maganganu masu saka tausayi tanamai kawo wasu ire iren nata salon makircin ackiin furucinta.

Harta kammala zancenta halisa bata yarda ta taɓata ba kuma batace mata komi ba.

Khaleel yana tsaye yanata shan mamakin abunda meenal din take ta faɗa gameda alakarta da zach. Shikansa saida makircin meenal din ya soma tabamasa zucya yaji kwakwarlsa ya rude yafara tunanin ko is all about zach din dagaske if not meyasa halisa taki amsawa.

Shikansa so yake yaji ta amsa wann tambayar

Dan haka kawai aransa yakeji kamr yana bukatar jin hakan sedei baida tabbacin kunnuwansa suna son jin cewa akan zach ne halisan ta shiga wann halin datake ciki

Sosai draman meenal din yadan cusamai son shima yaji wann amsar daga bakin halisa aransa

Sedei irin kallon da halisan take mata ne duk yasaka duk ta kasa samun cikakken nitsuwa

Ganin halisa taki kukata yasata Ta juyo kan khaleel din tace masa yanaga tana rejecting din kowa khaleeel???pls do sumting bana son ciwon nan yay tsananin da zai saka a jerata acikin masu bukatar ganin likitar mahaukata.

Shide Baice mata komi ba, Daga cikin ran hjy nadiya ma so take hakan ya faru koda wani abun zai sauya dan harga Allah ita bawai ta damu da rayuwar halisan bane barema ya dameta...

Kin musu magana da halisan tay ya dada saka su acikin tashin hankli.

Khaleel na ficewa awajen uztaz yabishi sukaje office dinsa suka soma magana akan further treatements dinta inda ya yanke hukunci cewa harsai ta samu sauki kafinnan su iyacewa komi.

Dan haka dukkan wasu harkokinta dolene ta dan sauka akai harsai ta samu cikkaken lafiyar kwakwala

Daga can dakin halisan kuwa kusan suke kidansu suna rawansu agabanta, meenal tay iya bakin kkrinta wajen kawo mata zancen qudirinsu hadiza tanamai kushe plans dinsu, halisa dai batace musu uffan ba saidai ta zuba musu idanunwanta dukansu basusan abunda take rayawa aranta game dasu.

Jim kadan saiga nan shemau da vicky sun shigo ciki suma, nan kusan kowaccen su tazo ta dan rungumeta suka mata jaje halisa bata dai tarbe kowa acikinsu da sakin jiki sosa ba

Sudinma haka suka yi iyayinsu suna masu tambayarta ko zach ne matsalar dansu dau mataki amma halisa batace musu komi ba wanda hakan ya matukar daurewa meenal kai bana wasa ba.

Hajya nadiya tace inhar bazatay magana ba kawai ku kyaleta nide na gaya maki halisa wann salon da kika daukar wakanki bamai billewa bane dan bake kadai wann abun zai shafa ba harda mu. Haka ta gama bambaminta tay waje halisan batace mata uffan ba.

Yau haka sukayi zaman diris a asbitin tare da ita amma Gabaki dayansu basu gane kanta ba..

Gashi meenal tay babakere a asibitin duk ta hana kowacce acikin kawayen kebewa da ita duk dama halisan taki ta kulata itama..... #SURAYYAHMS Is not a free book. 1️⃣2️⃣ #SURAYYAHMS _PAID BOOK 500# VIA 0152983148 MOHD SURAYA SULE GTB._

Kusan Dukkansu sun rasa meyake faruwa da halisa data daukewa kowa wuta taki cewa komi game da halin da take ciki. Harma gara gara jasmine idan tazo tana iya kyaleta ta dan rungumeta suyi kukan su atare.

Bakaramin tausayinta jasmine takeji ba shiyasa a duk sanda suka zauna atare sai tay mata hawaye , Duk sanda suka dan kebe daga hayaniyar meenal sai ta tambayeta halisa kin tabbata zaki iya daurewa acikinsu kowa????

Inhar kinason afasa kwai kisane ina tare dake..cos i cant wait to expose that evil woman..zanso inga me zatacewa sauran kawayenku akan abunda tayi maki da rayuwarki.

Halisa saidai tace mata kibar maganan kawai jasmine tonowa meenal asiri tamkar tonowa kaina asirine aynxu.. Banajin dadin rayuwata bazan iya jure wani tashin hankli yanzu ba Komi da kika gani yar hakurice da sannu ahnkli zanbi lamarin..kiyi hakuri jasmine Banason na sake memeta tuninin abunda nayi...its wrong i shudnt have tried to kill myself.

Kusan jasmine dinne kawai tasan halin da halisan take ciki sede tun zuwanta da halisan tay mata alaman cewa bata son kowa yasan da akwai wani abunda ya faru a tsakaninta da meenal talba wanda shiyay musabbin jefata acikin wann hali yasaka jasmine din bata nuna musu alaman komi ba.

Duk da shirun da halisa tay bai hana sauran kawayen cigaba da kkri wajen ganin sun bincike zach ba, meenal tay nan tay can, tarasa meke mata dadi, halisa taki sake mata taga kmr ma jasmine ne kawai take sakewa tay magana me tsayi da ita, daga ita sai kuma uztaz .. ganan ma su shemau sunki sam su bata hadinkai ita da vicky bare abar maganan zach ya wuce mata.

Itakanta shemaun ba adede take ba dan kuwa tun jiya wayarta yake akashe sabida bata son ta amsa kirar mahaifyrta data umrceta da akan taje Abuja ta kula da lafyar mijinta mahmud yau kwana biyu kenan amma batavisa Abujan ba.

Itama so take halisa ta tabbatar musu cewa zach ne musabbabi dan koda zata wuce Abujan ta tafi da shirinta akansa sedei shirun halisan ne ya dakatar musu da komi.

Wani binma jasmine ne kawai take iya sakata budan baki tay magana da kowa bayan nan shiru takeyi ko tace thanks ko okay sai uhm mmmm.

A brain dinta kusan kowani dakikanin lokaci lissafi take na yadda zata soma sabuwar zama da su meenal dan gani take dolene ta hakura ta fahimce asalin wacece meenal talba kafin nan ta fara tunanin yanke mata wani hukuncin daya dace inma rabuwa da ita zatayi batason tay mata hukincin acikin fushi ko garaje.

Ayayinda case yay zafi kowa ya zuba ido yana sauraran abunda zatace.

Washe gari sassafe khaleel ya dawo daga masallaci kenan sao ganan wasu mutane sanye da bakaken kaya suna hade ido suka hau bibiyarsa abaya abaya.

Tafiya yake gabansa yana faduwa har saida ya cimma kofar gate din asibitin kafin nan suka ciimmasa dayan gayen ya sha gabansa dayan ya taresa ta baya.

Gabansa na faduwa yace malamai lafya?

Dayan murdadden gayen yace ..."Dr khaleel?

Yace yes .

Ogan mu ne ya aikomu wajenka...

Khaleel yace oganku? Waye kuma oganku..

Batare da sun amsashi ba dayan ya fidda wata envelope daga aljihunsa ya mikama khaleel snn yace kaduba ciki kagani ko kasan wann yarinyar?

Tun kafin khaleel ya bude gayen ya fidda wata arniyar bindiga daga aljihunsa yanamai nuna masa cikin wata dakakkiyar murya ...hurry we got a message for ur patient doc ..

Khaleel yana bude envelope din yaga hoton halisa tare da zach sunyi matukar kyau they both look so happy and in love dan sabbin hotunan da suka dauka kenan kafin ranan aurensu da meenal ta tarwatsashi.

Kansa yaji yana sarawa daya gansu ahaka dan Bai wani bata lkcin sa wajen kallon halisan ba zach din kawai yaketa kalla dake bai wani sanshi sosai hakannan ba sai a social media da ake ta nuna speech dinsa akan halisa.

Har cikin ransa yaji tsananin kishin ganin hoton duk dama baisan kishi yake ji ba...he just tot he hated this guy.

Ya hade rai I'm sorry i cant take u to her, kuje kucewa ogan naku inhar sako yake son ya isar mata he shud find a way to knw how to do that amma bata hannuna ba...what nonsense ya fada cikin masifa.

Dukansu suka fidda bindigoginsu na gaban yace Doc i am warning you.. i don't have alot of patience.

Dayan gayen yace kana wasa da rayuwarka ko Sai mu kasheka anan mu kashe banza...

Khaleel yace is my job to protect my patient u can do what ever u wish kodan kun fito da makamaai kuke ganin zanji tsoronku.

Dariya dayan gayen yay Doctor munsan baka tsoron mutuwa... Infact, our boss is impressed with u..u save her life ...bazai taɓa sakamu mu kashe wanda ya ceto rayuwar macen dayake matukar kauna ba..shiyasa ma ya aiko mu wajenka..baka sani ba, hala ma tanada bukatar ganin wann sakon..5 mins, and we r out.. hadin kanka kawai muke bukata ..

Khaleel yay tsaki dan shikadai yasan abunda yakeji aransa yace musu is not possible to let u in. Ina saqon kubani...i will decide intana bukatar gani. Babu yadda basu so su tsorashi ba amma yaki sam.

Sai cam dayan Gayen ya ciro wayarsa daga aljihunsa ya danna wata lamba,.snn ya ja gefe yay magana ya dawo yace "Okay fine...zamu baka sakon. Amma dolene mutim daya acikinmu yabika domin mutabbata ka miƙa mata.

Khaleel baice musu komi ba sukaje suka dauko wani envelope da wasu manya manyan bonquites na flowers shikansa khaleel baisan tarkacen flowers bane saida sukahaura sama Lkcin halisan tana bacci

Suna shiga cikin room din gayen ya nemi waje agefen gadonta ya aje bonquets din sann ya yaye abunda suka rufe flower dashi, wasu red rosesss ne masu tsananin kyau tare da strands din white roses daddaya ajikinsu bakaramin kyau flowern yay ba kana ganinsa kaga mei tsada sosai.

Kallo daya khaleel yay ma flower ya dauke kansa har gayen ya mika masa wata envelope snn ya fita ya jima awajen yana kallonta aransa harji yake kamar ya bude sakon yaga meyene aciki ya kasa motsi cikin ransa sam babu notsuwa yabi ya kure envolpe din da idanunsa yana lissafin yadda za'ayi ya budeshi

Motsawar da halisan tay acikin bacci yasakashi dawowa cikin hayyacin shi. Da sauri yay gaban flowers din ganin Igiyar canular dinta ya sarkefe jikin flower din yana kkrin rabawa kenan ta dan fixge hannunta cikin bacci dawani irin karfi suka rikota kasa glass din daya rike kasar flower Ya fashe tasssss saida ta farka kusan a gigice.

Da wani irin kallon bazata suka kalle direction din atare zucyarta na zillo da mamakin ganin khaleel agaban flowers tana kkrin miƙewa zaune da kyar ayayinda hannunta yaci tuntube da envelope din dake gefenta.

Wani irin girman kan ta tambayesa na waye takeji wanda hakan yasaka ta dauka sann ta budeshi kai tsaye.

Akaro na fako dataci karo daa handwriting din zach saida ta lumshe ido kafin nan ta bude nan take tafarajin kamr ma kawai ta rufe sakon ta ƙona ko ta yaga basai ta karanta shi ba, dan bataga dalilin da zai saka ta karanta ba, dacan harta yanke hukuncin aikata hakan aranta sai kuma taga irin kallon da khaleel yake mata wanda sam ta kasa ganeshi, his expression was blank and unreadble...

Irin was he expectiing her not to read it sabida da sakon daga wajen zach ne?....

Duk dama a zahirin gaskiya abunda yake ransn kenan ko kadan baisan halisa ta bude sakon nn barema ta karantashi amma kuma baisan meyasa yakejin hakan aransa ba

Dan kamar yadda yaga su shema'u da vicky tare da hadiza sunata kkrin su rabata da zach din nan kwata kwata shima aransa kusan hakan yafi amincewa dashi...

Dan bisa da kalaman mutane gani yake kamar zach ne babban matsalar dayake cikin rayuwar halisa ayanzu ..

alho meenal is the only one denying it, saidai shi kansa yafi gamssuwa da harsashen dumbin mutane akanta fiyeda na zantukan meenal datake kkrin cusamasa aransa najin cewa kmr child hood trauma ne kawai yke damun halisa babu batun zach din aciki

Yabi ya zuba mata idanu koda zataji nauyinsa aranta taja tsaki ta bude kawai ta ƙure rubutun da idanuwanta yana kallon ta harta kammala karantawa tanamai sauke wata nannauyar ajiyar zuciyar dayasaka yaji nashi zcyar ta buga.

Ahankli ta lumshe idanuwanta da suka ciko da ruwan hawaye masu tsananin zafi da karsashi.

Dan da alama zaach ya girgiza matukar girgiza dayaji labarin cewa har tay ynkurin kashe kanta. A tunaninsa lefinsa ne dan saida ya dawo hayycinsa snn yake gane cewa abunda yay matan sam sam ba girmansa bane saidai sharrin shaidan daya zugashi dan ya toxartata da tsananin soyayya tare da kishinta dayakeji aransa dayakasa control nasa.

Dukkan wani abunda ya wakana tsakanin sa da meenal bai boye mata yau ba ya gaya mata iyakar abunda bata sani ba. Wanda already yanxu hakanma ji take kamar tafishi sanin hakan tunda da kunnuwanta taji meenal din ta furta harda dalilinta na aikata mata shi.

For her peace of mind he his willing to leave the country for good, snn ya nemi gafararta, yace mata rayuwarta yana da muhimmaci agaresa fiye da komi dayakeji na ciwon rasata dayayi a duniyarsa gabaki daya.

Hawayenta masu zafi haka suka dinga zuba ayayinda take tunowa da nitsatsuwar kalamansa masu cikke da nadama da neman yafiya aciki.

Saiyau ta fahince zach sosai, ta kumaa gane cewa meenal is really poisonous and she can do much more maybe tunda harta iya dasa masa abubuwa marasa goguwa acikin kokon ransa game da ita.

All the dirtiest part of her life dat he is not willing to accept duk da irin son dayake ikirarin yana mata aransa har yanxu

Altho he was soo late, yau datake aranar daya tona asirin meenal din already ta rigashi jiyowa ata wani sigar da batay tsammanin zataji shi ba.

Yadda ta rungume letter bisa kirjinta yasaka khaleel kangarewa awajen yanamai kallon ta bakinsa kusan abude..

Kusan Babu abunda kwakwalrsa take ayyana masa alkcn face ko hala zach zai dawo gareta ne wanda yasaka ta shiga irin wann tsumamamen yanayi kuma agabansa batare da taji ko dar dar ba.

So where was he when she was tryng to kill herself??? Lallai wasu matan sai ahankli,.. yaja wata arniyar tsaki mai tafe da tsinannen haushinta aransa

So is true dukkan wann lamarin data tsoma kanta aciki sabida zaach ne bama dan sabida abunda yake damunta na rayuwarta na baya ba.

God damn it a tunaninsa halisa ta gama wuce ajin da zatayi wa namiji wann makahuwar soyayyar..

Shidai tun baisan menene acikin takardan ba yagama sawa aransa cewa soyayyar zach ce kawai yake haukata kwakwalr halisa yake kuma ratsata wanda ahalin yanxu yakeji aransa cewa babu tantama sai ya kawo ajalin wann soyayyar...

Batare da ta sani ba ya zame bar wajen ya koma office dinsa anan ma ji yay ya kasa zama zai jela ka dawo yake yanamai tuno da dukkan munanan kalaman da zach yay ranar akanta amma sai yasha mamakin ganin wai halisa ta rungume sakonsa tana zubda masa hawaye sosai wann abin ya taɓa masa zuciyarsa bana wasa ba

A office dinsa ya zauna har wajajen goma na dare bai zago ya dubata ba..wa jasmine kawai ta nunawa letter datazo mata sallama zata koma london tanada fashion show, tabi ta haɗa ta da letter danma kar ya fadi wani yaje ya karanta san tace mata taje ta kona matashi acan intaje

Now she have all the evidence na cewa meenal ne ta aikata mata komi daya faru aa ita sede kalar hukuncin da zata yanke akanta ne haryanzu bata sani ba dan ita ire iren mutanen nan ne da sukeda wani irin nagartaccen zuciya.

Wacce komin sharrin mutum kafin nan suyi tunanin sharrinsa daya sai sun tono da alherinsa goma wanda hakan yasaka takejin kamr bazai taba yuwa ta iya yanke ma meenal talba wani hukunci ayanzu ba.

Tun bayan tafiyar jasmine sai ya kasance su meenal din ne kawai awajenta kusan kowani lkci suna muhawwara akan lamarinta dataki tace musu komi akai.

Yau kusan kwananta uku kenan a asibitin Izuwa yanxu har sun gaji da tambayarta matsalartan sun zuba mata idanu.

Meenal tay zuciya sosai dan gani take kamar itace akabarta da damuwar tsoron kar asirinta ta tonu, Allah Allah take taji raayin halisa kodama zata samu nitsuwa acikin ranta.

Bata rai ta dingayi wai koda ma halisan zata sauko da nata daure fuskan ta kulata amma kuma sai taga halisan tay kamar batasan tanayi bama.

Haka kawai jiiknta yake ta bata cewa kamr halisa ba lafya take ba.

Abun na matukar bata haushi Musamman ma da halisan ta lallaba su vicky akan da sukoma bakin rayuwarsu kawai she will be fine kuma basai an dauki wani fansa akan zach ba.

Wann furucin nata yay ma meenal dadi har ranta bana wasa ba، Duk dama sauran kawayen sunta daga mata jijiyar wuya akan ko kareshi kawai takeyi saboda haryanxu tana boye sonshi aranta.

Itade batace musu komi ba kowa ya gama masifarsa yay shiru kusan dukkan abunda yake faruwa khaleel yana lura sosai.

Shikansa jiyake kamr its becoming too obvious for him cewa halisa is still in love with zach.

Tun ranar Kullum in ya fita sallahn asbh sai ya tsaya ya leka koda zai ga mutanen zach din sun sake dawowa ,tunanin hakan zai iya sake faruwa yasaka a daren ranan ya rubuta sallama duk dama bata gama warkewa sosai sedei ba gidantan yace wuce da ita ba

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull