Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 47
Cheaters club book 2 complete novel Chapter 47: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 47. saida ta bar amal tagama zagayenta snn Rana daya ta zaunar…
3,363 words
saida ta bar amal tagama zagayenta snn Rana daya ta zaunar da ita ta wanketa tass sann tace mata ta nitsu dan kuwa ita karamar kwaro ce wayann mutanen yan siyasa ne datake kkrin shige musu kuma zasu iya sakawa a shafeta a duniyan nan ita da zuriarta sann su zauna kalau, Haka shema tay amfani da weaknesses tare da sirrikan Amal ta zazageta dasu har Amal tay kuka Sann daga baya tace mata wann mission din yana da hatsaro sosai Saboda irie irensu alhaj kyari gaggan yan siyasa suna tsare kansu wasun su mayu ne ko suna cikin cult me karfi ba lallai ne Taci nasara akansa da garaje ba.
Dan haka ta tsara musu cewa zasuyi abun ne kamar deal, ita zata musu hanyar shiga gidan hadizan amma riban game din zasu rabane 50-50 shema tace Amal auren alhaj kyaro zatay ta tattaro musu kudi kafin asiri ya karye saita bar gidan.
It seem like a perfect plan Amal was all excited abt it suna gama hada plan din basu bata lkci ba suka shirya suka saida abubuwan su da suka rage suka wuce niger awajen wata buzuwa me amfani da baqaqen aljanu wajen yin sihiri kwanansu shida awajen kafin suka samo abunda suke so suka dawo ko dakin kwana da kyar suka samu kudi suka kana makansu na kwana biyu. Wahalar da suke sha yasaka shema tace saidai kawai su fara aiwatar da aikin.
Kwana biyu takan kira hadiza tana janta da labari tanajin information akan yaushe ne alhaj kyarin zai shigo gari.
Tafiyar meenal baifi da sati biyu ba khaleel ya dawo nigeria Koda ya kikkirata saidai tay ta masa ihu akan ciwon mamanta bata ma tsaya ta saurare shi ba shikuwa tunda ya lura da hakan sai kawai ya kyaleta ya cigaba da abunda ke gabansa suna yawan haduwa da fadila akai akai suna harkan marketing proposal wani bin har yamma.
Ta fannin Halisa kuwa she is still trying to figure it out, musmmn da mahaifin khaleel din ya kirata ya mata nasiha da karin ilimi akan auren tun ranar duk ta kwanta bacci sai tay tunanin zantukansa. da can dik Sun dauka ko tanajin tsoron ko zasu karbeta ne ko bazasu karbeta ba sabida addini, ko tana tsoron lamarin aurensa da meenal amma duk dai ya warware mata su acikin nasihar da ya mata, snn yace mata ba laifi bane inshi ya zamar mata tamkar uba.
Ayanayin datake ciki wnn satin ta gama lissafi snn ta tura uztaz ta saka yaje shi garinsu domin duba mata kawunta koma yaye ne dai tanason takai maganan gida koda basu amsheta ba amma kuma gani take kamar right din su sucan cewa zatay aure, tun mutuwar grace ya zamo bata da wani hanyar samun wayarsa gashi bata san meyake faruwa acan ba.
Banda uztaz babu wanda yasan abunda take shirya wa, yau monday bayan sunje office ta rakashi ya wuce garin Benue din da zimman zaiyi kwana uku acan ya duba mata kawu inyaso ko zuwa zatay wajen ta sameshi taji me zasuce bfr she rules her own decision.
Ustaz yaje benue da kyar ya samu location din gidan kawu badon komi ba saidan rushe gidan da akayi aka gina wani katoton shagon saida giya da gasashen naman alade awajen, a labarin da uztaz yajiyo shine mama g ta karbe gidan ita da saurayinta tace gadon yarta ce sun fitar da kawu ya shiga duniya a halin da ake ciki basu san inda kawun yaje ba.
Hanklin halisa yay mummunan tashi da wnan labarin, and she cudnt tell anyone not even khaleel sabida abune daya shafi familynta, ustaz ne ya dinga kwantar mata da hankali tare da ce mata zai zauna agarin har sai ya samu kawu snn ya dawo this whole situation remain a secrt btween them.
Ana cikin wann yanayi lamarin Amal da shema ya fara fitowa fili kusan koyaushe zasuje gidan hadiza shema ta dinga rudar hadiza ta karya cewa taji labarin cewa mijinta yana neman wata budurwa, ta riga tasan weak point din hadiza shine tsananin kishi, shema tana zugata a gefe kuma amal tana harhada chats din karya suna tura ma hadizan tana gani, hankaliin hadiza ya tashi sosai musmmn ma da alhaj kyari yadawo baiya samun time sabida harkan siyasa,. Acikin text din sun nuna na hadiza cewa ai auren da zaiyin ma a asrince zaiyi.
Kwana goma bokanyar ta basu suna zuba wata magani acikin ruwan shansa hakan kuwa akayi duk sanda shema tazo ma hadiza da maganan kishiya sai ta sanda yadda zatay ya zuba magani acikin ruwan shan alhaj dake dakin acikin private distillernsa. Kwana goman na cikawa haka tazo ta kama gyara ma hadiza daki na karya ta tsiyaye sauran ruwan ta saka sabo danma kar maganinsu ya lalace.
As usual cewa tayi zata taya hadiza zuwa wajen malamai dan haka kusan kullum tana gidan ita da Amal haka zasu jira har sai alhaj kyari yadawo tun baiya kula shishhigin Amal har maganinsu ya soma ci akansa ya soma bata fuska sosai.
Duk wata plan dinsu sun hadashi na yadda zasuyi abunsu smoothly batare da wata hayaniya ba, dake ma shemau nuna ma hadiza take kamar tana taimakon rayuwar aurenta ne yasaka suke abubuwansu a asirrince kamar yadda suka saba hadiza bata gayama kowa ba gashi ta aminta da shema dari bisa dari.
Tunda Amal ta samu shiga wajen alhaji ta fara tura masa nudes dinta a wasap kusan kowani dare saiya kwana yana chating da ita sabida maganinsun dayasha a ruwa yasaka ya zamo kamr baima san meyake ba, Dama kuma shi sihiri yakanzo ya tarda halin mutum ne, da kuma zuciyar da bawai ta nitsu akan ibada bace, bugu daya Amal ta gane cewa maganinsu yaci akansa sosai. Hankli kwance take trowing masa kanta abubwa nan suka fara damun hadiza sosai
Duk da tazo tana kuka haka shemau zata ce mata ai alfahnta yanakan hada musu magani karta damu. Gashi bakaramin amincewa da shema tay ba.
Yau ake cika sati uku da tafiyar meenal Abuja jinyar mummynta wanda ranar ne Amal da shemau suka zo gidan hadiza da wasu tarkace acikin ghana must go
Ranar juma ace da yamma liss hadiza tana zaune ko sallahn magriba ba akira ba suka jata dakinta suka dinga bunka mata hayaki suna dura mata magnguna akan cewa yaune zasu raba alhaj kyari da budurwansa. Tun suna mata hayakin tana gane kanta harta zo ta suma daga nan bata sake gane kanta ba sai bayan washe gari.
Tana farkawa taganta akwance akasa tana bacci, a firgit ta miƙe jin ta kasa tuna komi, haka ta fito rike da kanta dake mata wani irin ciwo da nauyi bataga shemau bare Amal duk sun kwashe kayan tsafin su, waje yay shiru duk sai ta rasa meya faru da ita jin gabobin jikinta gabaki daya babu karfi.
da sassafe ne dan haka Tafiya take ahnkli har takaita sashen mijinta dan ta dubashi zuciyarta na wani irin bugawa da tsananin karfi.
Isarta keda wuya taji sautukan muryan mace da wani irin sauti na kaman ana dambe aciki
A hujajan ta jawo kafafunta tayo wajen saida ta matso kusa snn ta shako ihun amal, tana ashhhh washhh wasshh a rikice ta dafe jikin kofar zuciyarta na bugawa da tunanin ko alhaj ya kamasu ne jiya da suke mata hayaki sam bata kawo cewa gurnanin sex bane ke tashi ataciki.... NA KUDINE 08060712446 SURAYYAHMS
PAID NOVEL
zuciyarta na matsanancin bugawa Ta turo kofar kusan a tsorace ta shigo ciki tana daga idanunta sama kirjinta ya kara bugawa kamar zai faso waje jin ta kasa motsawa ganin pink nite gown dinta akasar floor ga Amal haihuwar uwarta akan gadon mijinta tay masa goho suna wani irin dirty sex, tafi minti goma a tsaye batare da tasan inda hanklinta yake ba.
Koda suka ganta su tsaya mana, amma ina wani abun ma da gayya Amal takeyi, Zuciya yadebeta ta taho zata finciko Amal din sai luiii wani hayaki ya turnuketa ta fadi kasa ta suma..
Allah kadai yasan irin maganin da jiyan suka ba alhaj kyari yasha duk da hadixa ta suma basu dena abunda suke ba har saida suka gama ya dawo hayyacinshi suka dau hadiza aka kaita room dinta aka kira mata likita ya dubata hadizan ta dau lkci sosai kafin ta farfado taga shema zaune a kusa da ita.
Hadiza ta shiga wani yanayi na rudani daga farko dake shema ta nuna mata cewa ai Amal ta mata wayo ne ta aiyawartaan da hakan
But bayan kwana biyu sai taga abun ya fara wuce tunaninta gashi bata iya tashi tsaye sabida ciwon da zucyarta ya fara mata Kullum likitoci nakanta shema kuma ta hana ta kiran kowa. Intace a kira mata mijinta haka zataji shiru saidai shema ta mata wala wala.
Kan kace kobo sun tare da zama agidan hadiza.
Amal ta bude wata sabuwar shafi na sexual relship tsakaninta da alhaj kyari dake ita dama harkanta kenan duk ranan da ya kwana da ita saita caski kudi ita da shema nan da nan suka fara cashing out da kudade manya manya shikuma baiya ma cikin hayyacinsa bai ma tunawa da hadiza agidan bare yajega tunata.
Ayayin da rayuwa ya kasance haka, Amal ta zama tamkar karuwar cikin gida wa hadixa, a satin farko shema ta siya gidan miliyan goma ta koma ciki tana zama, sunata jiran next cash out su sayi mota, ita kuma Amal tara kudin takeyi, duk sanda ta wage ma alhaj gindi ya ci takan samu 2-3, to 5 million at most, itakuwa tun da taga kudaden na zuwa mata kamar banza a wajen alhaj kyari tafara tunanin kawai saita aure shi koda shema tana so ko bata so.
Hadiza tana cikin matsatsin ciwon dayake neman ya taba mata zuciya tun a sati na farkon ta soma gane manufar shema amma ta kasa yadda da hakan face saida ta hada baki da likitanta yana mata recording komi dake faruwa ata waje kusan sau uku likitan tana musu labe tana kwaso ma hadiza information awaya. Tun da hadiza tazo taji recoding din kusan ince hadiye ranta ta mutu ne kawai batay ba dataji maganganun da shema da Amal sukeyi akanta.. the betrayl hits her soo deep dat she cant explain, sai yau take fahimtar cewa ashe shema da Amal are behind all this ibtilai datake fama dashi sai yanzu ta gane asalin dalilin daya saka shema ta hanata amfani da wayarta.
Zuciya ya kasa barinta tay hakuri shema tana shigowa dakin tana daga kwancen ta kama ta da dambe, amal din ce ta shigo ta rabasu, shema has no oda choice face ta gayawa Hadiza tarin abubuwan dake ranta akanta tun farko, da irin hasssadar data keji akanta, da irin abunda ta rasa ita anata rayuwar, ranar hadiza ta girgiza snn ta tay kuka bana kadan ba, Amal kuma tace yanxu ta fara zama agidan tare da alhaj kyari. Snn suka fara tsirata ta Amal tace ta saka aranta sai sun kashe likitan data kawo mata gulma. In kuma batason a kasheta to marmaza tace mata tabar garin snn karta sake zuwa jinya agidan
Hakanan suka kira ma hadiza likitan agabansu suka sakata yin magana hadixa tana kuka tace ma likitan ta bar garin kawai and neva to tell anyone abt this.
Bayan nan suka amshe wayar hadizan suka tafi dashi, shema babu dandanin tausayi, sabida hassada da son kai ko sau daya batayi tunanin ko hadiza zata iya mutuwa ko zata rayu da wann baqin cikin da suka cusa mata aranta ba..
Itadei kawai damuwarta shine tay kudin ta dawo kamar da can tunda ayanzu ta rasa komi da kowa kuma babu hanyar da zatay ta samesu inba ta hakan ba.
Bayan sati biyu masu kyau da faruwar haka hadiza na fama da ciwon zciya a daki bata iya motsi akan gadonta kullum kuka ga saida azo abata ruwa da abinci na dole su kawo likitansu wanda shima saurayin Amal ne.
Duk randa Alhaj kyari bayanan likitan ne zai kwana da Amal agidan dake harija ce kowani irin jarabar namiji zata iya dauka inde zai bata kudi koya biya mata bukata
hanklin Halisa da uztaz gabaki daya nakan lamarin neman kawu a benue ayayinda ayukkan office yadawo rabi a hannun fadila yanxu
Jikin mumyn meenal ya farayin muni Alfah ya kira meenal yana gaya nata cewa maganin ciwon mumynta bana asibiti bane amma haka taki jinshi sam. Tace masa maye me shegen son kudin tsiya sai bai sake kiransu ba. kaf kaf kudinsu dake abuja saida suka karar wajen yawon neman asibiti da magani Abubuwan duniya suka dameta kawunta ta harna mata gori akan aurenta khaleel.
Yakance mata ina amfanin aurenta da khaleel din tunda yanada uban kudin nan amma ace uwarta tana kwance zata mutu tana Nan tana kame kamen kudi.
Abun yabi ya ishe meenal ta kirashi duk da bata gaya mai a yanayi me dadi ba amma ba shi ya hana ya tura mata kudin jinyar ba, he sends five million naira na magani and she send it back tace masa ya kasa, ita bazata karba sai dai yabata rubinsa sau hudu. Akan haka rikici ya sake barkewa tsakaninsu, gashi yawanci ta kira zaka samu yana tare da Fadila, duk sai tabi tasa aranta cewa ai budurwan san ce ke juyashi akanta tun awayan take zage zage ga baqar kishi.
Ganin ya sakata a blck list sai ta dau kudin daya rage musu cancak tay hiring private investigator akan abibiye khaleel a lagos samu mata labari da hoton yarinyar dayake yawo tare da ita abun ya isheta yanxu.
ana cikin wann yanayin ata fannin su kayden kuwa ranar da ya cika shekaru ashirin da hudu sukayi masa hadadden lavish birthday party ita da few friends dinsa guda biyu, da halisa da shema dake ma sun kikkira meenal, da hadiza basu samu ko daya acikinsu ba, shema kuma bata nuna musu tasan komi akan hadiza ba.
Awajen birthday kayden yay engaging din vicky da wani expensive diamond ring, and she accepted him babu tantama they shared a very long kiss agaban kowa, kusan kowa yanata tayasu murna har aka gama komi lafiya aka watse batare da wani matsala ya taso ba...
Iyakar abunda ke damun shemau yanxu baifi dataga yadda Amal tayi babakere agidan hadiza tana shige da fice da kayan sawan hadiza tana kuma baza mulki iya son ranta ita da saurayinta likita agidan, while alhaj kyari yaje kasar waje daga cewa zaiyi kwana uku yau kusan kwana bakwai kenan bai dawo ba.
awayann lokutan Hadiza ta ga jarabawar rayuwar da harta mutu bazata iya misalta zafi da ciwon daya jefata aciki ba dan tsabar kukan datakeyi har saida hawaye yazo ya kafe a idanunta kotana kuka hawayen basu fitowa ba saidai kaji tana kara ita kadai.
Tamkar wacce take prison haka suka katse suka tsare agidan and shema was busy taking care of all the security personal bawanda yay Zaton komi na faruwa Ataciki sabida yanayin shakuwarsu, masu aikin gidan ma gani suke kamar hadizance ta bawa shemau dukkan wani dama duk dama Amal na jawowa ana suspecting dinsu da irin yadda take baza mulki agidan sosai gata da son saka kayan hadiza tana burga dasu.
Ahalin da ake ciki jira suke alhaji kyari ya dawo su amshi kudaden da zasuy motoci da wanda zata aje a acct dinta while Amal tana rage zafi da likitan da suka dauko yana duba hadiza.
Bayan kwana biyu da engagement din Vicky iyayenta suka bukaci tazo da kayden din garinsu domin amasu prayer session bayan nan kuma zasu wuce kasar wajene wajen iyayen kayden din for formal introduction na aure as They want to get married as soon as posible batare da sun yi jinkiri ba sabida izuwa yanzu soyayya da shakuwarsu ta wuce yadda sukansu sukayi zato.
Wannn dalilin yasaka Vicky ta fara tunanin neman hadiza sabida shirun hadizan ya fara damunta aranta sosai.
Faninn meenal kuwa yau take tsammanin jiran result na aikin binciken data saka ayi mata akan khaleel wanda yaci karo da sati na karshe da khaleel din zaiyi aiki da fadila so kusan koyaushe fadila tana yawan zuwa wajenshi ko shi yaje wajenta sabida ta kware sosai shikansa baison yay missing wani session datake dora shi akai.
Washe gari Sassafe tun sakon datake jiran be iso ba Alfah ya turo matada sakon cewa inhar tana son mumynta ta warke saita samu ruwan da halisa tay wanka dashi ta bawa mummynta tasha inba haka ba her mother wll spend 70yrs in dis condition with no cure excpt death..
aranta Tanason taki zancen alfah amma sai kuma kawunta Tjay ya zaunar da ita ya warware mata komi ya gaya mata cewa ai asiri hajya nadiya taje tay akan halisa kuma yana ganin cewa asirine fa ya dawo kanta dan haka idan tay taurin kai uwarta ne zata cigaba da shan wuya kamr yadda kudadensu yake kan karewa akan jinya bayan ko sau daya basu ci karo da sauki ba
Babu yadda meenal ta iya Ahujajan ta shirya dawowa lagos aranar babu wanni jira, first time in her life kenan daya zamo she cant afford first class plane ticket haka ta shiga economic din ta dawo duk ranta a dagule. Wani sabuwar tashin hanakli taji na ya za'ayi tafara samun ruwan da halisa tay wanka dashi. She off her phone for a while dan kar matsalar khaleel yay distracting inta.
Lamarin shirun hadiza ya dame vicky yau da safe she wakes up da tunanin hakan sai ga kirar halisa ya shigo, halisa tace mata tay mafarkin cewa hadiza is very sick, kuma ta tsorota da mafarkin, kawai su kira shema suje gidanta su dubata kawai da yamma tun kafin vicky ta shirya goben su tafi.
Babu kalar kiran da basuma shema amma bata dauka ba karshe ma sukaji wayarta switch off. Kawai sai suka hakura suka yanke aransu cewa su biyun kawai zasuje gidan hadizan da yamma.
ata fannin shema kuwa tun dawowarsu daga hidiman engagemt din vicky ta fara ciwon ciki me tsanani me gigitarwa tana zuwa asibiti aka bata gado tare da sanar da ita cewa cikin dake jikinta yana kkrin shiga wata uku da wasu kwanaki kenan , kusan hauka ne shema batama likitan a asibitin ba sedei babu wanda ya kulata, tunda aka confrmiing mata cewa tana da ciki ta san da cewa tabbas cikin alhaj shafiu ne wani irin sabuwr baqin ciki da tashin hankalin data binnesu abaya haka suka tattaso mata suka dawo fresh a memory inta wanda shiyasa ta kashe wayar gabaki daya.
Kwana biyu datay a asibtin batazo gidan ba ya jawo wata mai aiki ta dan leko dakin hadizan sai hadiza tace mata ta riketa takaita bayi tay wanka sabida tsamin datakeyi danko brush basu mata bare su mata alwala. Sosai nadama da ciwo da radadi yasata ta gane cewa, duk wani abunda kayi ba'a akan hanyar Allah ba will come back to u and haunt you twice the amount dat u dish out, kawai gani take kamar wnn abun izina ne ya sameta, da kuma kira dan ta nitsu ta gane cewa babban kuskurenta shine biyewa shema datay tana sako harkan bokaye akan mijinta wanda gashi itama yau ya rufta da ita aciki.
Me aikin ce ta taimaka mata tay wanka dake sai an dagaata an kwantar Dakyar ta tsaftace kanta tazo ta sauya kaya ko hitawa batayi ba tace me aikin ta bata wayarta marmaza zatay wani kira, kafin ta gama rubuta lambar wayar sai kuma likitan ya zo ya kamasu amal tazo ta kore mei aikin a agida suka mata rashin mutunci, Suka saka hadiza agaba suna gaggasa mata magana masu zafi she was busy recording it da wayar me aikin data boye akasar pilownta, yadda Amal take cewa zata aure mijinta zasu kasheta ko su haukatata kamar yadda suka haukata amaryan alhaj wacan ministern. She had to pretend she is heart struck dan su kyaleta.
Haka tay suman karya suka barta a dakin da wayar, ta dinga kuka babu lambr da bata kira ba amma duk bata samu nasara akan kowa ba sabida shema ta riga ta san me tay akan hakan.
Ita kwawrriyar lawyace tasan duk hanyar datake bi ta toshe hadiza daga neman taimako, Hadiza ta rasa meke mata dadi, that recording was all she had.