Kenza eBookz

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 49

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 49

Cheaters club book 2 complete novel Chapter 49: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 49. shema tay dariya tace kai kawata kode kin siyar kin biya…

3,347 words

shema tay dariya tace kai kawata kode kin siyar kin biya bashin kamfani? wallh ko jiya naji ana maganan cewa zaki saida kamfaninki sabida tsinannen bashi Meenal wai me kike da kudi ne, u dint change house, u didnt change cars.. toh ina kudin bashin sukaje?

Cikin rolling ido tare da jin zafin maganan tace Shema pls, enuf of this sau nawa zan gaya maki cewa batamin suna kawai ake sonyi have u seen my acct balance? Beside my husband is on top of one big arab contract kwanan zaki sha mamaki...

Shema tay yake batace komi ba, dan ambatar contrct da meenal tay kadai saida atake ya tuna mata gajen hakuri da tayi akan mahmud.

"Ina su hadiza?..

Shema tace suna ciki Da halsy tana tayata saka kaya.

meenal Ta kyabe baki hmm kuce dai nikadai ce nayi latti anyways thank god i am here. Tana gama rufe bakinta saiga su hadizan sun fito halisa na mata video hadizan tasaka Golden Lace irin soltis swiss din nan me shegen tsada da ake bugashi originally a kasar switzerland, yau kusan komi da hadiza tasaka is golden in colour dayake nuna yadda dukiya da hutu ya gama rtsa mata fatar jiki gashi tay wani kwalliya me daukar hankli..

Daga ita har halisan baka isa ka iya dauke ido akansu ba. Halisa ta saka tsiririn wittels bach diamonds necklace me tattare da hadadden agogonsa saida zoben su da khaleel to touch up the look. Kalar kayan data saka sky blue ne kuma atamfa sai tay kamr wata amarya.

hadiza kuwa wata mahaukaciyar sarkan Gold ne da warwaronsu suke wani walwali a wuyanta kamar wata sarauniya..

Kusan suman tsaye shema tay tare da jin kanta na juyawa, idonta atake ya ciko da ruwan bakin ciki da kuma zafin hassada me tsanani tanaji a zciyarta cewa itace tay asalin dacewa da tay irin wann luxurios life din, ba simple and kind woman wacce bata damu da abun duniya kmr hadiza ba.

vicky ta mike tsaye tace ohhhhhh my god hadiza u killed it...

Meenal take ta dauke cak wajen kallonsu duka dan duk sai taji ta mugun raina kanta.

Murmushin dole take yi Tuna manya manyan gwalagwalnta data siyar sai atake taji wani abu ya cakketa a kirji haka tay saurin shanyewa tace woooowww..dizo, dizo.. dizo.. tafara hailing din hadiza badan taso ba.

Ko juyawa halisa batay ba bare ta kalle meenal da ta kafeta da idanu kamar ma bata gane ta ba.

She is actualy thinking of how and when halisa ta dinka wnn kayan daya mata mugun kyau dan tasani sarai halisa bata taɓa saka atamfa ba bare harta san ya ake dinkasu. Hmm, Ba wann bane ma babban abun da yafu ci mata tuwo a kwarya face damuwar ta na ganin kamr bata da wani matsayi ko saurqn muhimmci wajen halisa itade tanata tsammanin ko ciwon nan ne ya sauya ta.

Abunka da me fuska biyu halisan bata kulata ba amma haka nan taje ta rungumeta suka hi hi cikin kyabe baki tace " su halsy manya ashe kin iso shine ko ki kirani awaya muzo tare ainima da na tsaya kin shiryani.

Halisa tay murmushi tace u look good Amina Ke ai babbace basai an shiryaki ba. Daga nan ta wuceta ta nemi waje ta zauna daf da vicky kusan kowa da abunda yakeji aransa tasan meenal bata ga zoben bane har yanzu. kafin Kace wani abu har an shanye na ciki an tsunduma hidima kayan ciye ciye da shaye shaye kowa na hiran shirmensa zaka rantse babu komi aransu.

Hadiza ta fara magana Me dan tsayi game da abubuwan da suka faffaru snn vicky tay musu godiya ta kuma cakka magana direct ma meenal akan masu fuska biyu, sai Shema tay akan abun duniya,sann akazo kan meenal yar fafa da cika baki tanami nanata musu cewa ita she is fine Snn Sudena daukar rumors akanta intana da wata matsala sune zasu fara sani. Abun dai ya daure ma hadiza kai sosai sabida bata taba samun kuskure wajen samun labari amma tunda meenal ta dage sai aka basar. Halisa tace she have nothing to say.

Aka kawo photographers ya musu hotona masu kyau na tarihi, sann aka kawo wani katon golden and milk colour cake mai hawa biyar kowacce zata yanka step daya ta saka a plate nata taci.

Shema da vicky suka fara yanka aka tafa musu sai hadiza ta yanka sai meenal ta yanka dede ta kai baki kenan Halisa takai hannu kan cake din zata yanka, wani gufff meenal taji cake din ya shakureta a wuya badon komi ba sai ganin twin ring na diamond data gani a yatsar halisa.

Wani irin fetto cake din tay waje tare da sakin tari me mahaukacin karfi da ya riketa, atake hadiza ta rike ta cikin sauri sauri shema'u ta dauki goran ruwa takai mata baki

Vicky dake lura da komi ta jawo halisa suka tsaya agefe anata sannu sannu ma meenal ko ajikin vicky sai ma kyabe baki datakeyi cikin ko in kula Tanakai cake bakinta cikin salo. Halisa bata motsa ba ta zubawa meenal din ido.

tari me yawa Meenal take yi tana bubbga kirjinta nan tabi ta dawo musu kamr wata me aljanu kafin kace wani abu hawaye masu yawa sun wanke mata fuskanta.

cike da tsokana Shema tace kai Amina garin hadama zaki kashe kanki nan ta ficcikota sukayi bathrum dake kusa ta kwara mata ruwa a fuska tana dan bubbuga mata kriji da kyar meenal ta dawo dede.

Shema ta kalleta gaanun tana bari bari tace ke lafya kuwa?? Kode wani abu kika tuno..

Meenal tabita da zazzfar harara ke bana son iskanci..uban wayace miki ki watsa min ruwa mtschwnn..da bacin rai ta fita ta bar shema a tsaye..

tana fitowa Taji zuciyarta ya kasa hakuri kai tsaye taje gaban halisa ta dan kama hannun ta tana kallon ring din..

a mamaknce Hadiza tace whats going on meenal? Nan sai ga shema ta fito tana kyabe baki, meenal sai kallon ring din take tanajin kamr zuciyatta zai amon wuta, vicky kuwa ji take kamr ta shakureta dan takaici Halisa tace Amina lafya kika rike min hannu?

muryanta na dan rawa rawa tace lafiya can i talk to in private?

Caraf Vicky ta amshi maganan tace excuse me? Hey, der is no private here dukkan mu kamr yan uwan juna ne so tell us what is going on.

'It is btwn me and haliisa okay..

Shema tace ohh abun haka ya dawo?

Hadiza ta dan dafa kafadun meenal tace Haba Amina hush down meye ne..whats up.

Rau rau da ido tay cikin rasa ma me zatace saai tace kawai dama tambaya ce

a nitse Halisa tace tambaya akan me?

Nan ta juyo ta kalle idon halisan snn tace this ring, really looked like my husbands twin ring.

Hadiza da shema suka kalle juna snn suka kwashe mata da wata iriyar mahaukacyar dariya..

shema tace Bura uban can..amma meenal ke asalin yar iska ce Yo akan wann abun kika shaƙe Har kike wani abu kamr me aljanu..hmm sannu me miji.

Hadiza na dariya tace "looked like? Yo ma shi kawai akayi design din hala.

Vicky Ta mugun hade rai taja tsaki me tsayi snn tace inma mashi ne sai akayi yaya baida damar yay kyauta ma duk wacce yaga dama ne, and wat sort of childish insecurity is dis mtswss.

Halisa tay karamin murmushi snn ta dafa kafadun meenal din

ahnkli meenal Din ta bude lumsashun idanun ta da suka ciko da ruwa dan bakaramin takaicin dariyar da su shema suka mata taji ba.

suna hade ido da halisa taga tana murmushi me sanyi ahankli tace mata idan kyautar yay miki zafi then talk to ur husband abt it okay..he gave me sumtimes back, nina dauka ma ya gaya maki ne.

take Meenal taji kamr ruwan zafi na tafasa akan zuciyarta da kwakwarlta saidai yadda halisa take maganan with calmness ta rasa gane kan komi.

Da kyar ta shanye abun muryanta na rawa rawa tace No, nifa bance wani abu ba, kawai de nasha mamaki ne naga ai baku shiri and he gave u such a lucrative gift?? Kuma shine ko ki gayamin.

cikin katseta Vicky tace enuf,..meenal wann magana ce da zakiyi da mijinki bada halsy ba ke ko kunya ma bakiji yadda kike tsitsiyeta agaban mutane da tambaya akan mijinki..ure just too insecure. And mind u mijin nan banaki bane ke kadai..i dont get why ure attacking halisa .

Shema tace gane min hanya vickay, shebi i told u kai halsy gidan meenal jinya is a bad idea tun a asibiti take nuna mana kamar ita kadaice me kyakkwan miji..koda shike munfa san ya akayi kika samoshi da kyar but still trwing ur insecurites on halsy is not fair.

Hadiza tace anji basa shiri amma ai ya mata jinya kusan rabin shekara so i see nothing wrong in gifts.

Vicky tace meenal u shud be ashame irin wahalar datay akan mijinki da baki nan harma kinada bakin magana, u left them for 2 fucking months she cook and cleans kuma tana jinya..

Kusan ihu meenal ta saka a tsakiyarsu is enuf guys naji naji naji nayi kuskure halsy i am sorry okay?? I am hapy he gave the ring. Shikenan magaña ya kare.

vicky tace weda ure hapy or not mijinki zai yi aure kuma u must have to deal with dat.

Shema tace tabbas, halsy datake da saurayi ma yanxu me mezatay da naki mijin..

Ni bance zatay wani abu da miji na shema bana son iskanci da munafruci

Vicky tace toh inma mijinki ne saurayin nata yaya zakiyi?

Shema ta tuntsire da dariya tace sai mutuwa

cikin sanyin murya Hadiza tace toh ya isa Guys is enuf..halsy dan Allah kiyi hakuri

Halisa tay murmushi batace komi ba. Sai kuma abun ya dame meenal aranta bana wasa ba taji dama bata daga maganar ba

Waje ta nema ta zauna kamar an mata mutuwa Tafara basu hakuri wanda daga ji kasan ba daga har zuci yake fita ba

Hadiza da shema suka karbe ring din suna kalla Shema sai kara azazzala ma zuciyar meenal wuta takeyi cikin raha tana cewa wayyo Allah dis must be a very special gifts wallh. Hadiza ta dauko abun gwada diamonds dinta suka gwada suka kalle juna

Hadiza tace wow 'Rare designs..toh gaskiya mijin meenal ya iya bada kyauta..halsy ure lucky.

Shema tace inama ace dukanku ya aura musha kallo. Wani irin dariya vicky tayi snn tace In halsy ta shiga gidan ai bata da kishiya..Halsy is a queen in every man's heart..maqi gani ya rufe idonsa.

Shema suka dinga dariya ita da vickyn, ganin mood din meenal ya sauya yasaka hadiza ta kunna music, Abataso haka suka jawota cikinsu suna rawa har maganan yadan yi sanyi suka denashi meenal ne kadai takeji kamr ta kama hannun halisa ta cire zoben ta gudu da shi.

ana cikin shagalin yamma yay liss wani baqi qirin din haddari ya hadu, nan sai shema ta dan fita tabarsu taje dayan falon domin amsa wayar yar uwarta Amal dan sunyi akan cewa zata aro motar haya tazo ta dauketa dashi kuma dama gashi ta gama hada plan dinta akan hadiza sosai.

Bayan ta gama wayar kenan hadiza ta musu kyautar Sabbin motoci kirar benz E-class na zamani kowacce cikinsu taji dadin kyautan, amma haka girman kai da jiji dakai yasa meenal taki karban motan tace musu ai mijinta zai siya mata sabbin cars nagani na fada kwananan.

Hakama halisa ta basu kyautar sourverniers na expensive gold jweries and watches datay odernsu a website din mum din khaleel kowa ya amshi nashi amma haka kishi yahana meenal..

Vicky ta kawo musu card na invites a exclusive spa session a hotel din datake zama da cewar ita zata biya musu komi Wann ne ma meenal ta amsa..shema kuma bata amsa ba sabida yanayin laulayi datake boye ma kowa.

Shema looks fine amma Aranta taji babu dadi da bata bada wani gifts ba amma dake meenal ma bata bayar ba sai abun be wani dameta can can ba.

Suna zaune suna dan hira sama sama aka kira magrib halisa na gefe akan kujera tana famar chatting da khaleel tana murmushi me snyi jin ya nace mata saidai yazo ya tafi da ita gida. Sunata musu akan meenal yace mata sam saidai shi yazo ya dauketa kawai yauko uztaz bai yadda ya kalle mishi iya dayawa ba..

ana cikin hakan Hadiza da shema suka dan shiga ciki meenal na zaune tana kiran khaleel Awaya bai daga ba, vicky sai satar kallonta take tana dariya kasa kasa sanin cewa he is busy chating halsy aranta tace maganin munafuki dama ramin mugunta mugun ne ke fadawa aciki.

Ita kuma meenal so take in khaleel yazo sai ta tambayesa zancen ring din agaban kawayenta Hala ko zai bafa wani excuse da zai wanke ta kunya she is totally pained and embrssd da abunda ya faru musmn ma mgaganun vcky dama shemau sun mata zafi bana kadan ba.

She called him like 8 times kafin ya katse chat dinsa da halsy ya dauki wayar..dede lkcin hadiza da shema sun fito kenan

Dagangan ta danna wayar a handsfree khaleel yay sallama ta wani hade rai bata amsa na nan tafara masa magana da wani irin raini da gadara..toh mun gama..kazo ka daukeni I am too tired i dont think i can drive come fast kar ayi ruwa..da wani irin comanding voice ta fada kamar da driventa take magana duk dan ta burge kawaye.

Tana rufe baki kai tsaye khaleel yace "toh sannu uwata, see,..i can't. Tot u have sumting important to say a wann uwar miscals din, Ni dan Allah ki kyaleni kinji ko..bafa na son hauka inkinga dama ki kwana wajen

A zafafe ta bude baki zata masa ihu sai kyat ya katse wayar. Da wani irin baci rai tace khaleel??? Sai taji shiru. Hadiza da halisa suka kalle juna

Shema da vicky suka wani irin tuntsire da wata arniyar dariya har suna tafawa.

wani fuuuu meenal ta dau jakarta ta wuce wash room da sauri yanayinta cike da borin kunya hadiza tabita da girgiza kai...

Kasa fitowa daga washroom din meenal tay tsabr borin kunya daya lullumeta after few minutes sai ga uztaz nan ya iso gidan sabida haddari ne me mugun yawa agari, nan halisa ta musu sallama ta fita vicky ta rakata har waje. Suna kaiwa gate din sai ga nan Khaleel cikin wata hadaden dark blue jumfa data masa shegen kyau ya iso wajen da wata hadaddiyar farar motarsa kirar DBX jeep data sha tinted tana baza kyalli.

Vicky ta kalle uztaz tace sai kayi hakuri tunda oga ya zo ko, .. Uztaz yana murmushi ya gyada kai ya koma ciki ya dau motar sun ya kama hanyar gida.

nan Vicky ta raka halsy har gaban motar khaleel suna tsayawa sai gashi ya fito ko alaman dar dar babu aransa yana sakin murmushi me sanyi yazo ya bude ma halisa gaban motar ta shiga ta zauna aciki snn suka gaisa da vicky sosai. He offer su rage mata hanya tace masa tazo da nata motar itama yanxun nan zata wuce. Tana tsaye har ya kunna car din, sun wuce kenan sai ga meenal ta fito, tare da shema da hadiza..

meenal Ta dinga kallon bayan motar khaleel gabanta ma faduwa da sauri sauri snn ta kalli vicky tace vick ina halsy tayi?? Vicky ta kalle tsakar idonta tace ohj oga dakansa yazo ya dauketa sun tafi.

budar bakin Hadiza tace Dat uztaz is very loyal kugafa yana ganin hadari haryazo daukar halsy.

Fadin hakan da hadiza tay yasaka hawan jinin meenal yadan sauka.

imani ya taba ran Vicky sai kawai tay shiru.

Suna tsaye awajen Amal tazo ta gaggaishe su, sai nuna hadiza ma Amal shemau takeyi tana cewa ga hajiarmu nan fa.

Amal kuwa banda kallon ruwan gwalwalan gwal dake wuyan hadiza babu abunda takeyi har abun yaso yakara bada meenal haushi. Ba ajima shema tabi amal suka wuce banda hirar daular da hadiza tale ciki babu abunda sukeyi har suka isa hotel dinsu basu fasa ba. So take ta cusa ma Amal kwadayin kudin hadiza badon komi ba saidan tay amfani da ita wajen gida kanta dashi

Vicky ce ta dan tsaya ma hadiza for quiet some time suka tattauna akan batun soyayyarta da kayden hadiza tanata bata kwarin gwiwa harda tsarabar maganin mata.

Shema na tafiya gida meenal ta wuce nata gidan da gaggawa da zimman zataje ta sauke ruwan buhun barkwanon masifa ma khaleel akan dizgata dayay and most importantly akan zobe daya bada halisa aranta ji take kamr yau zata iya ma khaleel abunda bai taba tsammanin zata iya masa ba...NA KUDINE 08060712446 CHAT ONLY SURAYYAHMS

meenal tana kallon fadila dishidishi kmar a mafarki wani irin jiri me karfi ne ya rufe tay kamr zata fadi kasa a gigice,fadila dake tsaye a wajen tay sauri ta rirriketa tana wani irin murmushi, bakin meenal na bari bari tana vibrating kamar an kunna engine markade tafara cewaaaa F..ffadila..fadila fad..iilah Fadila,Faffafffafffa..dila?

sanda Fadila ta mikar da ita tsaye snn tace mata "yes, fadila ce., fuskanta dauke da murmushi tace "hellow Amina talba, so why are sounding so shocked ko baki gane ni bane? it is me fadila!

Wani gigitaccen ihun sunan fadila meenal tay tareda fincike jikinta da mugun karfi nan ta fara wargaza takardun dake kan table izuwa kasa duk sanda mutanen dake wajen duka suka rikice, kamar wata sabuwr kamu ahauka tafara cewa no noo no no no no oh my god nooo..noooo noo fadila noo not my company nooooooo

Wani suuu tay a jirigice zata kai kan gwiwarta jin notinan kanta na kan kuncewa Kafin takai kasa kan gwiwartan nan fadila ta kalle sauran mutanen dake tsaye awajen kowa na kallon haukar da meenal takeyi .

fadila tay kwafa tana dan murmushi tana kallon meenal ahanki snn tace musu thank u evryone and pls excuse us..

nan da nan kowa ya fita yana girgiza kai akan yanayin meenal na borin hauka.

a mugun xuciye kuma ahaukace meenal ta taso tsaye idonta kamr zasu amayo wuta, azafafe "tace karyane wallah karya nee, karya ne, i cant believe this, lallai fadila kin cika babban Munafuka, makira, muguwa,mayya witcht aaaaaaaahhhhhhhhhhhhthis can neva be, karya ne, you slyyy..ki gaggauta maida min kamfanina, hw did u ave the gutss?.

a tsawace fadila tace ke da Allah ki rufa min baki..

Data fadi hakan saida meenal ta yanke kukan cak ta tsaya tsorace kamr wanda aka harbeta da mashi a kirji.

Kallon fadilan takeyi tanajin kanta kamar a mummunan mafarki.

Kanta fadila tazo ta tsaya tare da dasa mata mugayen idanunta acikin nata, cike da izza tace Amina talba u btter mind your language, yau ya zama maki rana na karshe da zaki min magana a yanayin hauka, "i am not ur mate so u can't speak to me like dat kingane ko.

Budan baki meenal tay zata magana a zafafe Cikin datsar numfashinta fadila tace Nace miki ya isa haka be quiet...Rembr i just bot ur company iya kan abunda kike takama dashi kenan dama kuma nasaya ahakane badan bani da kudin kwacewa da karfi ba, Sai dai dan in nuna maki cewa dake da duk abunda kika mallaka ku duka kaskantantttu ne awajena. Wani irin numfashi me zafi meenal taja kamar iskan bakinta zai hura wuta...

Neman waje fadila tay ta zauna a hakimce snn tace I heard ure looking for me toh gani nazo..u have 2 mins to speak dan bani da lkcin batawa akan empty skull irin naki.

Wani irin runtse ido meenal tay tafara kuka me tsananin kuna fa zafi ahnkli bakinta ya furta na shiga ukuuu na lalace and How can dis be..how how wnn wani irin abu ne Allah yake min, fadila faaa amma an cuce rayuwata this isnt my destiny..

fadila tamata wani irin kallo snn tace "ke jahila, wa uban waye kike gayawa haka dan Allah de ba abun wasanki bane..nasan baki sanshi bane shiyasa kiketa mamaki da ikonsa but anywys u have to deal with yr reality.. It is me fadila, the girl u used, destroy my life and threw me unto the street to die.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull