Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 52
Cheaters club book 2 complete novel Chapter 52: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 52. *Buy now sai asaka a wait list group..yana sauka a tura…
3,372 words
*Buy now sai asaka a wait list group..yana sauka a tura maka documents naka kasha karatu🤧*
Labari ne me cike da darusan rayuwa...
Dont miss it❤️❤️ Jikinshi yaji Yana amsawa da wni irin internal joy duk sai yaji ya rasa abunda xaice gabaki daya, daf da shi ta dawo ta zauna yana juyowa taga dan karamin hawaye aka fuskansa.
Cikin snyin murya tace Champ im srry for not telling u first, i have my reasons..
murmushi yy me yawa sn ya share sassanyar hawayen nasa daya sauko kasa da sanyin murya yace" Haleesa, nayi miki sha'awar musulunci da jimawa amma kinsan abunda yasaka ban taba takura maki akai ba..?
Tana kallonsa cikin tsumayi tace aa
Yana murmushi "Yace sabida banason kiyishi ne sabo da wani abu..not me..not love..Not marriage..i wanted it to be strickly ur own choice and alhamdullh. I dont care in ina wajen ko bana wajen, weda u tell me first or not its doesnt matter as long as ra'ayinki ne, ...This is the best evening of my entire life..and i am going to make sure i cherish and love u forever and more. Yana maganan yana murmushi amma sabbin hawaye ne ke diga akan fuskansa sosai. Yadda xakasan abun ya mugun masa dadi he barely resist frm smilling duk dama idonsa is flowing with silent tears.
Ahankli ta dan jingina ajikinshi cikin lunshe ido da budewa tace "thank you.. in sha Allah nothing can ever seperate us ure mine forever..
Daga nan hira suka danyi kadan tana mai gaya masa duk wani abunda take ciki..
So, they want the wedding to be done nan da sati biyu if possble saida yanason ya koma saudi arabia anytime soon sabida aikinsa, just a simple weding marar hayaniya amma babban burinta shine yakasance wani jininta na asali yana wajen koda ba adadin rai ba she wants sumone to be der as her famly shiyasa ta damu sai ta samu kawunta.
sunkai kusan sha biyu na dare suna tattaunawa Baxaka san khaleel na da xumudi sosai ba saida suka fara tsara rayuwar aurensu, he cant stop making promisss of providing security and love and intimacy.
wajajen sha biyu da rabi saura ta rakasa ya tafi gida, washe gari sassafe a massallacin kofar gida suka gamu da mahaifin sa tun anan Suka samu tattaunawa sosai har ya gaya masa cewa halisan ta amince xata auresa
bayan sun dawo gidan ne suka xauna su ukun tareda a mum dinsa a falo suka kara masa nasiha me shiga jiki tareda nuna masa cewa so xasu riketa ne tamkar amana tamkar kuma ya.
Tare da maryam da baban ne kawai xasu je benuen ayau ,sai yace ma khaleel ya taho da mum dinsa su same su acan daga baya..
Sassafe Halisa ta hau shirya kanta cikin wata black abaya na ellie saab bata dauki komi ba face jkrta da wasu kananan abun bukata da kuma kudi.
Tana kn shiryawan kenan saiga mryam ta shigo....
bakaramin dadi taji da tasann da Maryam xasuje ba mryam kuma she was all excited and emotional sabida dadin jin karbn musulncin da halisa tayi and Its her biggest dream ayi aurenta tare dana dan uwanta khaleel kuma gani take kamar hakan ne xai faru.
Wajajen 9;30 pm suka wuce aiport mahaifin khaleel ya riga ya biya musu komi suka wuce garin benue akan lkci sun isa wajen 11 sede daga aiport xuwa inda gidan nasu yake sai da yakai su Almost 4 hrs a wani masallaci suka tsaya duk suka gabatar da sallahn xuhr snn suka je su wani restaurant sukaci abinci.
Gashi garin anyi ruwa wani irin sanyi ne ya sauko bayan sunci abincin sukaje suka kama masauki, mahaifin khaleel yay waya da wani mutumun daya sani awajen shine yaxo ya daukesa akan xasuje wajen wani police dake kulawa da case din dan yakara musu cikakken bayani.
Halisa da maryam aka bari a hotel din jim kadan suna kallon tv halisa tace ma maryam taga an wuce da wani gawa daxu suje wajen hala uncle dinta xai bi xugarsu ya shiga tunda dama ance masu kai gawa yake bi kowani lkci.
Sede Basu bar hotel Din ba saida suka kira mahaifin khaleel awaya yace musu badamuwa suje wajen kawai xaixo shima ya samesu awajen yanxu dan duk wani bayani dalla dalla akan kawu halisa ya samesa awajen police din sosai jikinshi yabi yy sanyi bana kadan ba.
Su halisa sun iso makabartan lokcun masu kai gawan har sun shige ciki suna tonon rami duk sun saka bakaken kaya anata al'ada dake christian cemetry ne.
dake bakaken abaya ne ajikinsu ita da maaryam yasaka securityn wajen basu tsaresu ba, Kai tsaye suka wuce can can ciki maryam nabin halisa abaya..
Tafiya halisan take kirjinta na matsancin bugawa gabaki daya sai tanajin memery din mutuwar iyayenta na dawowa mata fresh a brain dinta baxata taba manta yadda ya kasance ita kadaice ta saka kasa akansu aduka ranar mutuwarsu ba atake taji hawaye masu xafi sun cika mata ido cikin dauriya ta shnyesu har suka kai tacan karshe
A very painful and bad childhood memry exprience can neva be erase from a child's mind dan kuwa halisa na iya tuna duk wani ciwon rashi dana kunci da taji aranta ayayin data binne iyayenta duka biu anan wajen ayayinda take fama da karancin shekaru shiyasa duk yawan qabarin dake wajen bata mance inda na iyayentan yake ba.
Kai tsaye ta kai kan na babanta ta tsuguna kasa agaban kabarin batace komi ba hawayenta ne kawai suka hau xubowa kasa sosai kamar baxasu dena xuba ba.
gabaki daya Maryam ta kasa motsi ko taba ta tsabar tausayinta dataji ya rufeta sosai..
Saida ta kusa minti talatin awajen kafin nan ta tashi tsaye ta dan leka ta bayan kabarin taga tabbas da akwai alaman wani yana kwana awajen But what really happen to kawuntan da yake zwa kabarin dan uwansa yake kwana? Tasan dai tun mutuwarsa xaginsa sukeyi shida mama g basu taba fadin wani alhairi akansa ba.
Kanta akasa ta mike Ta koma ta can gefe inda kabarin mamanta yake dake basu da wani nisa.
Isarta wajen kenan taga wani dankwali akasa baki sai bata kula ba ta tsuguna ganin duk da ant tsaftce kabarin sosai amma tsirrai ne suke fitowa agefe agefensa very fresh harmless leaves springing from it.
nan ma batace komi ba sai hawayen ta me sanyi dayake xuba can ta kalle dankwalin sai ta dauka ta rike a hannunta tare da jakarta da niyyar mikawa masu gadi idan xasu fita.
..She spend at least 10 mints sai taji maryam na kiranta kafin ta dau wayar sai taji mutum yace Halisa? tana daga kai wani mutum tagani agefen maryam din da bata san shi ba sai tamike tayi sauri ta fara tafya ta wajensu.
cikin sauri ta wuce wasu mutane da suka kai uku na tsakiyar babban mace ce sosai sai kallonta take a tsandare bata kalleta dakyau ba harta wuceta da sauri dake ta saba da irin masu mata irin wann kallon kurillan dan bayau aka saba mata kallon kykwar mace ba.
Tana xuwa ta samesu a tsaye nan mutumin yy introducing kansa a matsayin me kula da wajen suka gaisa yake ce mata me takeyi agaban wancan kabari me fidda lafiyayyun tsirarrai din dake dokansu ne suna bada tsaro sosai sabida they dont allow oda ppl to pick sand or leaves from oda ppls grave Kar Suje suyi wani tsafi ko wani ritual dashi. Is stricky againts the cemetry law aynxu.
Dake yaga tana da kyau alamar dukiya da hutu ya gama ratsa mata fatar jiki sai yasaka ya mata bayanin hakan politely bai mata wani ixgili ko tsawa ba, tambayoyi ya fara mata, tare da ce mata ai yasan masu kabarin ne kuma sun bada ajiyarsa sama da shekara goma kenan ko yaushe shekara ta raba tsakiya suna yawan xuwa dubawa shiyasa ma yake tambayarta kota sansu ne..
da mamaki ayanyinta Tace masa wasu mutane kuma? abun sai ya daure mata kai dake tasan Ai kabarin mahaifyrta ce dan haka babu wani me qabari inba ita ba.. ..Mutumin was shocked to hear this. Suna cikin maganan duk sun kasa fahimtar juna sai can ta hango matar data wuceta daxu ita kdai tana ta dube dube da alaman wani abu taje nema
Nan ta kalle mutumin snn tace masa "Excuse me. Ina xuwa.
Kafin ya amsata ta wuce wajen da sauri mutumin shida maryam suka hau biyota abaya yanacewa maam maam..pls wait
Maryam tace halisa wait mubi abi ahkli kamar masu claimin grave din ne sukaxo fa
Bata sauraresu ba tana kaiwa wajen matar ta dago kai suka hade ido sunfi minti biyar suna kallon idanun junansu cikin jin matsanancin bugun xuciya...
can halisa ta ciro veil din tace Ahmm are u looking for this??
karamin Hawaye tagani ya ciko a idanun matar sai kuma tayi murmushi me sanyi tace yes. Thank u. Where did u find it.
Halisa tace here. On the ground..
dan shiru matar tayi kafin nan Tace ohhh goodness and ur name is Halisa did i ques right?
Naksshyr murmshi Halisa taci tace yes. my name is haleesah
hawaye suka sauka a idon Matar xirrr ta kuma cewa did u even knw this person?? Ta nuna kabarin....
Kan Halisa adan kulle da yanayin matar tace ohh yes..she is my mother.
a mugun raxane sosai matar tace "Ur mother? "ur mother?? Cikin barkewan kuka matar ta memeta...
hankli adan tashe Halisa tace yes did u knw her Da xakuwa a muryanta tace "Are u her friend..pls tell me bantaba sanin wanda yasan mama na ba.
Matar batace komi ba bakinta na bari bari acikin kuka mai tsuma tace Halisa, ure halisa doter of maryam..
A mugun rude halisa tace yes my mothers name is maryam, and dis is her grave , how did u knw, who are you, i am confuse..maamm
girgiza kai matar tafara yi da wani irin birkitaccen yanayi ta bangajesu cikin kuka tana cewa oh my god, da wani irin ihu tace..baba baba baba baba...baba..baba...halisa is alive da mugun gudu ta fita awajen tayi hanyar waje...
Halisa xata bita a guje kuma a rude mutumin yay wuff ya rikota lkcin xucyata kamar xai fita ajikinta tsabar bugawa dan gabaki daya hnklnta da xcyarta mugun rude yake ta kallesa tace let me go..
Yace wait wait madam Wann matar fa sune masu kabarin nan Sune nake gaya maki sun bada ajiya kinsan su ne
acikin matsancin rudani tace no no pls Just let me go and see her first. She knws my mother Tunda aka haifeni bantaba ganin wanda yasan mama na ba sai ynxu... Bakinta na rawa rawa tace i hear my mums tone in Her voice, her eyes, she knows my name and my mothers name..tana kkrin fincekewa kenan sai taga xugan mutane sunkai su hudu abayan matar suna binta aggagauce tana tahowa wajenta da gudu dayan na bayantan tsoho ne futuk anrikesa suna tahowa dashi agaggauce
Tana isowa ta finciko halisan tariko ta tace musu i found her, she is our halisa, ta maimata hakan yafi sau biyar ajere. Jikinta na rawa rawa.
Kusan a tsandare halisa take kallonsu jin kamar ana sassaka mata gangan jikinta da xcryta alkci guda Dan tsohon da aka rikon bakaramin kama da mamanta yake ba like a spitting image of her mum kominsu iri dayane daga gani babu tanbaya.
tunda suka hade ido da tsohon ya fara bari kar kar kar snn ya fashe da kuka me radadi yanamai nuna ta da hannu..
Dayan dake gefen ta namiji ne ya rike shi yana cewa Alhamdullh Allahu akbr Allah me iko dama baka taba amincewa da batun mutuwar halisa ba kuma Kasha cewa anan xaka sameta wata rana and this happen to be ur last visit gashi nan Allah ya bayyana maka ita...
dayar matar dake gefensu banda kuka babu abunda take dan har kasa kan gwairta takai tana kuka sosai Kamar ranta xai fita.
haliisa tana daga ido data kalleta sai taga kamr ma maman nata tke kallo Jikinta taji ya fara rawa rawa jin tsohon yana kiran sunanta dana mamanta yana kuma ce mata grand doter.
wanda ta fara ganin halisan kuwa ita kanta sai kallon halisa take tana kuka tanajin kamr ma mafarki sukeyi ba reality ba
Halisa bata iya motsi ba dan kanta taji yana wani irin juyawa sosai tanajin kamar xata yanke jiki ta fadi akasa.
Maryam ce tayi dauriya snn ta shiga tsakaninsu muryanta na rawa rawa tace pls musu we dont understand,who arr u ppl??
Namijin ne ya share hawayensa snn Yace Sunana leut. Abubakr Hakeem,This is my sister captain jamila hakeem, and our eldest sister hajiya Maimuna hakeem yanuna tsohon snn yace and this is our father ..The 100th general comander general of somalian army 1953.
and the woman lying under this grave is his youngest doter our sister maryam hakeem a decorated undercover of somalian army..we lost her 35yrs ago,kafin nan mukaji mutuwarta anan kasar. And We learn dat she have a child name halisa....and.
dede nan Halisa tayi kamar xata ynki jiki ta fadi Kasa dan ji tayi gabaki daya kanta ya kasa daukar komi.
dayan matar ta riketa da karfi ta fincike kamr me borin aljanu wani irin ihu ta saka masu saida karankaf makabarta ya dauka da kararta datayi shi a cikin tsananin rudani da tashin hankli
ranta kamar xai fice tafara kuka me tattare da tashin hankli da raunata da kuma rudewa aciki tace oh my god, i cant belive dat my mum had a family..numfashinta yahau yin sama sama ayayinda brain dinta yafara tunawa da irin wahalar da maman nata tasha, cikin kuka me tattare da xuciya me rauni tace "why, why, why did u do this to her...u left her to suffer, and die..
Da sauri leut. abubkar din yaxo xai riketa ta bangaje shi cikin kuka me karfi axuciye cikin rudani tace stop stop stop dont touch me...ure lyieng, u are lying..to me. My mum neva knws anyone, we were all alone and i tot ure all dead and she had to suffer alone, ..with sickness...and she died...she left me..duk kuna ina, u left her...ure suppose to look for her not wen she is dead..
dayan matar data durkushe akasa a raunace ta mike tsaye tana kuka mai rauni, tana kkrin rike halisa a mugun raunace halisan ta bangajeta ta kara fashewa da kuka me tsuma "Pls let me go, i am out of here, I dont want to see u dama ni basaninku nayi ba...leave my mother alone nd dont eva come back..bata taba ihun da jijiya ya bayyana akanta sai wann lkcin..
Gabaki daya saita basu mugun tausayi sabida kowa yasan bakaramin rudewa tayi ba.
tana gama furta hakan ta juya aguje xata bar waje dede lkcin mahaifiin khaleel tare da khaleel din da police da kuma kawun halisan suka iso wajen suma.
Ganin halisa sukay tana kuka Me kara tana kuma falfalowa da uban gudu duk ta yasar da takalmta abaya mutanen suna binta suma agggauce kawunta da yy kusan kamota yana riketa ta wani irin jan xciya kafin kace wani abu ta xube ajikinshi sumammiya.
Khaleeel ya fara isowa dan Kusan atare duk suka rufu akanta kawun nata leut. abk Ya dagota sama cancak suka fita waje da ita aggagauce nan gabaki daya aka dunguma aka bisu abaya har waje agaban wasu mahaukatan convoy da wasu sojjoji suka tsaya Suna isowa aka bude musu cars din gabaki dayansu haka suka dunguma suka nufi babban private hospital dake garin.
Maryam databi motarsun itace taketa ganin ikon Allah dan atake captain jamilan tayi wani kira kafin sukai asibiti wasu kwararun likitoci na daban ma aka turo musu Suka wuce da halisan ciki suka fara dubata.
Lokacin kusan kowa a rude yake khaleel da mahaiifyarsa da maryam suna tsaye awaje guda Maryam din tanata kuka bata iya gaya musu komi ba.
Mahaifin khaleel kuwa atsaye yake da police da kuma kawun halisa da ya jejjeme yayy baki kirin ya xama kamar mahaukci
tunda yaga familyn maryam ya xama He was terribly shaking in terror and fear dan yariga yasan abunda yayi.
All the family of hakeems suna xagaye da special likitocinsu making sure dat halisa wll be stable as soon as posble.
Baifi minti biyar da hakan ba sai ga leut abk ya fito Idanunsa sunyi wani irin ja kafin su hankara sukaji yy wuf ya kwamusho kawun halisan wani irin damka ya masa wuya wanda da xan iya cewa numfashi na karshen ma ba lallaine ya iya fitarwa ba.
Take take idanunsa yyi fari fall yafara kakarin mutuwa, rudani me yawa ya sake cike wajen dan Gabaki daya maxajen dake wajen haka suka xo dan karbnshi amma da kyar suka iya kwaceshi...
Ire iren su kawun halisan na da yawa acikin al'ummar mu na ynxu wanda son xuciya da son abun duniya yasaka su suke rike yayan wasu, snn suyi karyan sun mutu, suna masu rabasu da gatar su dan su more gadon iyayensu ko dan kwadayin qaddara ko wata dukiya.
Ana gama kwaceshi a hannun leut., kenan baiko dawo hayyacinsa ba, captain jamila tamasa wani irin naushi acikinsa saida ya gigice ya suma a tsandare, ana kkrin riketa data kwace ta masa wani irin duka akai saida atake ya farka da ga suman cikin rikicewa da gigita jini ya fara fita daga hanci da bakinsa.
the energy and the furiosity yasaka gabaki daya awajen cikinsu ya duri ruwa, Mahaifin khaleel nema yy karfin giwar tambayarsu meke faruwa.
Leut abbkar dake bari bari ransa a mugun bace yafara gaya musu irin tsinannen karyn da kawu ya hada musu for many many years yasaka suka aminta da cewa Halisa ta mutu tun tana yar karama. Har ya nuna musu wani hoton konannen mota sukace musu ai konewa kurmus halisan tayi a car accident ahanyar dawowarta daga schl ita da wasu mutane.
Shida mama g Sun jima suna boye halisa sabida su samu suci gadon ubanta da kyau snn duk xuwansu nigeria suna haduwa dasu amma bakaramin karya suke shinfida musu akan mutuwar halisan ba.. #SURAYYAHMS... PAID BOOK This was a very cruel and painful story to hear dan banda layi da jini dake fitowa a bakin kawu ko magana bai iyayi ba kuka yake jikinshi na bari yana cikin wani irin matsancin gurnanin axaba, ga tukukin kunci da nadaman da yakeji kamar itakadai ma axaba ce agareshi babba...
Ataikaice dai da kyar police da kuma mahaifin khaleel suka lallafar da maganan, har lkcin da Halisa ta farka..suka dunguma suka dawo wani katon gidan da bakinsu suke sauke.
Babban police din ne yakaisu can dake shidin musulmi kuma yasan mahaifin khaleel sosai yake darajashi.
Haka halisa taki fir ta kulasu, da kyar da lallami da nasiha da wayo sann ta hakura ta xauna acikinsu snn aka fara warware maganan.
Kawu aka taso a tsakiya yy kneeling kamar dan tsana yana confessing abubuwan daya aikaita.
Acewarsa asalin sunansa micheil mansa sunan babban yayansa robert mansa, sun taso su biyu ne kacal awajen mahaifinsu mansa wanda yakasance dan siyasa ne, mamansu ta rasu tun suna yan kananan yara shikuma sai Allah baiyishi me ilimi kamar robert mansa ba. Ya taso da kishin dan uwansa sabida duk wani abu me kyau a duniya Allah ya bashi..
Ga nitsuwa ga ilimi ga farin jini ga jarumta shikuma Allah bai bashi ko daya acikin wann ba..
Ya girma ne da tsanar babban yayan nasa dake Robert mansa airforce ne A nigerian airforce commison dake can yankin niger delta state. Jajirtacce ne dan haka mahaifinsu mansa ya dauki son duniya ya dora masa. wata rana sai robert ya dawo gida da wata mata ana ce mata maryam snn yace ma babansu cewa acikin ruwan taku ya sameta sunyi wata biyu acan jejin dayake aiki yana mata jinya snn ya daukota dan tace masa xata biyosa gida.
yace mahaifinsu baiyi wani doguwar bincike da tunani ba ya amshe maryam sabida yarda da dansa roberts dayayi sosai.
Shikuma sai yaji ya tsaneta sabida sallah takei, snn ta samu matsalar mantuwa ta mance daga inda ta fito.
As time goes on shakuwa ta shiga tsakanin robert mansa da maryam, roberts yace lallai xai yi musulunci ya aure maryam, shikuma dayaga hakan sai kishi me tsanani ya kamasa sosai sabida maryam din kyakwar mace ce kuma ya tsani musulunci a rayrsa sosai.