Kenza eBookz

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 65

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 65

Cheaters club book 2 complete novel Chapter 65: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 65. Harta gama serving dinsa suka zauna taga har lokaci ya tafi…

3,334 words

Harta gama serving dinsa suka zauna taga har lokaci ya tafi yau meenal bata fito ba abun yadan bata mamaki aranta Duba da yadda jiya ta cika mata bakin cewa zata karbi matsayinta na uwargida.

Haka har suka kammala cin abincin khaleel ya shirya ya dan fita yace mata yanxun nan zaiy dawo.

Bangaren meenal din kuwa duk tagama zagaye dakinta cikin tunanin abunda ya hana khaleel zuwa jiya da dare, sai kuma tafara jin haushi da tunanin koma halisa ta canza haline bata masa maganan ba.

Da wann haushin aranta ta yanke hukuncin zata zo ta sake samun halisan nan ta shiga bathrum ta kimtsa kanta ta saka wani matsatsen fitted gown bata daura dnkwali ba ta saka takalmi ta fito...

Lokcin halisa na tatattare kayan da sukayi break din kenan zatakai kitchen tana mugun jin qwiuwar wankewa sabida kasalan datakeji ajikinta tana daukar tray din sai taga taga tex dinshi akan cewa tafito waje ta karba mashi aika ynzun nan.

A gurguje ta Aje tray din dai dai meenal na fitowa kenan ta ganta har ta dauka ko wajen ta zata zo sai kuma taga ta shari kwana zata fice waje..

Sadaf sadaf ta shiga binta abaya halisa tanay taba bude kofar kafin tay hankara ba taci karo da smilling face dinshi wanda kamar an cillo shi ne agabanta.

Tsaban bugun da xuciyar ta yy yasa ta dafe kai janyo ta yay jikin shi ytin kafin ta fara korafi ya manna mata tsumamen kiss agefen wuyar ta kafinnan ya ciro red blind fold daga aljihun shi ya daure shi idanun ta..

cikin kunnenta yace "Can u walk with me bby girl? Tan murmushi Tace yeah amma Ina zakay kaini haka? Hannunsa daya na cikin nata daya kuma ya dora akan cikinta. Dede tasaka mai muryan shagwaba har tana bubbuga kafa akasa kenan saiganan meenal itama ta fito

wani mugun harde rai tayi daga bakin kofar falon gabanta na bugawa da tsananin karfi ta zuba musu idonta dya jaaa kamar zai kama da wuta.

Binsu da ido tay har suka kai gaban wata katowar abu da atake ya tuno mata da memoryn first gift dinta da mahaifinta alhaj aliyu talba ya bata lkcin ma baida lafya he gifted her her first car in a box tun tana yar karama sosai dake bakaramin soyayya iyayenta suka raineta aciki ba.

Lumshe ido tay tanajin ina ma ace da babanta yana raye da duk bazata ga walakancin nan ba

tana bude lumsashen idanunta ta dorasa akan khaleel daya makale cute fuskanshi a gefen wuyan halisa ya kankameta ajikinshi..daga nan tana jiyo muryansa "yace ready?...halisa tace yes.

hannun ta ya makale jikin wani jannnn igiya ta dan rike suka janye tare snnn ya kunshe blindfolds din ahankli tana bude idanun ta suka sauka akan wata latest lamboghini urus sport car ce fara kalll sabuwa dan tsaban tasan na musnman ne sunanta aka rubuta agaban deck din motar personalised nata ne ita kadai Ajiyan ya iso cikin dare aka kawo mai yau da safe.

Da sassarfa meenal ta karasa fitowa jin jinin jikinta ma tafarfasa Ta tsaya cak abayansu tana kallon komi..

Wani uban tsalle halisa ta daka ta yi kan motar ta shafa snn ta rungumesa sosai tana cewa ohh my god my first personalized sport car...soundin so excited ta makalkaleshi tana masa godiya tana masa addua masu shegen dadi.

Wani murmshhi yake yi yana cewa she dersev more for keeping his child and hersefl safe alwys And for making him happy..

Tagode masa hade da kuma masa adduar samun budi.

Kan meenal na juya altho tasan halisa can afford dat car amma kuma the fact dat khaleel has personalised it for her da kudinshi stasan bakaramin kudi ya narka awajen kerarsa ba come to think of it urus is one the most xpensive lambo collection taya ma zaayi ya bada shi kyauta ma halisa akan me???

..fuskan ta Take yayi jaaaa da alaman bakin ciki da tashin hankli...

Keys din ya bata cikin murna da rawar jiki ta karba tanace mai ya shiga ta danashi yana dariya tana kaiwa hannu zata bude cikinta yayy wani irin juyi take ta sake key din cars ya fadi kasa ta tsuguna awajen aragwabe ta fara kwaza amai mai yawa mai kuma kara kafin kace wani abu khaleel yay kanta yadan dagata kadan harta gama aman duk jikinta yay laushi tace masa bazata iya tashi ba tana nishi dakyar tafara cemai zata sha ruwa..

Me gadi ya kira ya kawo mai ruwa a gora ya bata tasha kadan tafara kwaza aman kumay

Nan ne meenal ta karaso kansu tanata kallon meke faruwa ko sannu batace ma halisan ba bare shi dataga ya daga hanklinsa kamar zai yi ma mace kuka..

Babban damuwarta ba halisan bane key din motar daya fadi kasa take so ta dauke tana mika hannu jikinta harna rawa rawa zata dauka sai caraf mai gadinsu ya rigata dagawa ta dalla mai harara ko ajikinshi ya mikawa khaleel..

Khaleel bai karba ba yace ka rikemin kabiyoni dashi ciki yanxun nan.

yana fadin hakan ya ciccibe halisa a hannun sa suka wuce ciki meenal tafara binsu abaya tanason sanin meya same halisan inma zata samun hanyar kasheta dashi da sauki.

Dede kofar dakin ta fauce key a hannun mai gadin tace masa Da Allah ka koma waje ka kwashe aman da akamin a tsakiyar gida ni zan bashi key din.

Me gadin da taurin kai bai wuce ba saida ya leka dakin yace oga key din sabuwar motar hjya na hanun wann matar

khaleel ya sallameshi Meenal taja tsaki ta shigo dakinsun dashi

Wani yatsine take tana kallon dakin up and down ranta a mugun dagule shide baice mata komi ba ya fara duba jikin halisa ya duba BP dinta Kafin nan ya saka mata ruwa ya dauko file dinta dake cikin wata jakarsa ya rubuta abubuwa ya barsa anan akan table.

Ya zauna yana latsa wayarsa lkcin jikin halisa yay lugwi kamar ba itace awaje take tsalle yanxu ba.

Gyaran murya meenal tay Muryanta ciki ciki tace ga "key din ka..Batare da ya kalleta ba yace drop it on the table. Da kamar bazataje ba dataga file din abude sai taje da sauri ta zuba ido akan file din dan tasan khaleel yana da very clear hand writing aikuwa tana lekawa taga sunan halisa And her pregncy test result attachd to it cikin har ya wuce wata guda yana neman shiga da sati biyu. atke Tay lissafi a mind dinta taga auren nasu ma kwata kwata wata biyun ma yanxu ne yake cikawa wani doguwar hmmmmm ta saki aranta tanajin matsanncin zafin kishi na cinta aciki wato sati biyu kenan da shigarta gidan tay ciki.

tana juyowa Dukansu tabisu da harara mai zafi aranta tace jarababbu akasa ta buga key din da zafin kishi ta fita waje bata masan ko khaleel ya daga ido ya kalleta ko be daga ba...

Batama ganin gabanta tsabar duhu tana isowa dakinta ta rushe da wani matsanancin kuka me uban kara...

Duk sai ta rasa me ke mata dadi ta dauki wayarta ta kira mumynta ta dinga surutan da ta saba tana cewa anci amananta khaleel yaje yay ma halisa ciki bata yafe ba menenenta..

Tun hjya nadiya najin tausyinta harta dawo mata masifa ta kara mata da nata borin haukar tanace mata ai na jima da baki shawarar kiyi cikinsa ki haihu dashi koma meye ne da zaina ragar maki akan abunda zaki haifa masa amma haka kika maidani mutuniyar banza yanxu wa gari ya waya..

agabanki kawarki tazo tay cikin, kuma tana da kamfani wanda ma yafi naki daraja tana kuma kula da mijinta amma duk be hanata yin cikinshi ba...Amina kinga dik abinda nake gaya maki kenan kina runtse ido akai to ni me zanje miki yanxu..

Wayann maganganun bakaramin tsaya ma meenal arai yay ba

Tanata kuka tana nadaman kin bin wann shawarar..wayasan ma hala itama daya saya mata abubuwa koma ya fara sonta inta haihu masa she jst realise dat she fucked up one big time again..Yauma bakaramin cizon yatsarta tay cikin kukan nadama ba, ga dumbn mamakin sanin cewa khaleel is capble of pampering his woman this way dat she neva expect to see.

Aranta cewa take datasan haka maza ke tarairayar matan su da duk dai batay masa wasu abubuwan girman kai da hauka datay adacan ba

yauma Saida likitanta ta bata maganin depression kafin nan ta samu nitsuwa.

Zuwa can da yamma datagama tunaninta taga ne me zatay snn ta fito Waje ta zo ta samu gidan ya cika da baki yan uwan khaleel...maryam da mijinta sunzo duba jikin halisan ga aliyu yazo all the way frm lagos zai xauna a maidugurin dasu for a while sabida yana hutu sai wasu causin dinsu mata su uku kyawawa dasu sosai.

Tun data kare musu kallo daga nesa taga kaf cikinsu babu wanda zatamai kallon banza sai taja tsaki kawai ta koma dakinta ta zauna tanakan jira su gama surutunsu su fita.

Time to time takan leko wani bin hartaji cousin din suna magananta calling her all sort of names kowa nacewa ta boye kanta a daki ne sabida ciwon Haukar karya.

This moments hurt her soo much, dama ta tsane taga yan uwansa .sai taji ranta na kuna musmmn ma da aynxu bata da wasu kayan da zata sako na barazana bare ta fito ta musu rashin mutunci susan ba tsoron uban kowa takeji ba.

She was boiling inside har saida yamma yay suka fito zasu tafi kafin nan saigata nan ta fito tana yatsine tanabin su da kallon banza.

Maryam da ciki ya saka tay freshh ko kallonta batayi ba hargara ma su aliyun da suka ce mata sannu tay banza da su Sai basu kara kulata ba Ruwa kawai ta dauka a fridge ta zauna a dinning tanasha dan ta kalle komi dan bakaramin saka ido da baqin cikin taji dataga uwar hidimar abincin da aka ci da kalar tarban mutuncin da halisa ta musu ba, upon duk da cewa bata wani jin dadi amma da jikin ya wartsake bashi ya hanata ta jonasu a falon sukasha hira ba.

This is sumtin she can Neva tolerate Allah ya kiyaye mata zama da dangin miji kaf a mtsyin munafakai mayu maroka take kallonsu..

sai can Wajajen sallahn magbr snn suka watse Aliyu ya bi yayansa sukaje masallaci ita kuma halisa a kofar gida kawai taraka sauran bakin ta dawo dakinta tay alwala ta shimfida sallahya ta gabatar da sallahn magrib..

bata tashi awajen ba Ta dau qur'ani ta na duba abinda khaleel yake koya mata every morning har aka kira isha'i ta mike tsaye ta gabatar dashi a nitse shima..

Ta yi sallama kenan taji an turo kofar ahankli tana daga kai taga meenal da wani irin mamaki meenal din take kallonta kafin nan ta sake kofar da sauri jikinta harna rawa ta karaso...halisa lallai kin cika babban makira munafuka..hmmm na sara maki...wai dama dagaske kike kin musulunta??? Yanxu tsabar son ki makalkale min mijina ki rabani dashi shine har canza addininki saida kikayi ke wata irin mayaudariyace haka.

A kasale halisa tay murmushi tace thats is a very good way to express ur shock Amina. Koma me zakice ki fada i dont owe u any explanations.

Tana maganan meenal na kallonta da dumbin mamaki harta cire hijabinta ta linke ta nade sallayar ta aje ta daga qur'ninta ta ajeshi kan gadonta ta nufa meenal nakan binta da kallo me cike da baqar kishi dan wata shegiyar abayace me tsada ajikinta purple colour tana zama abakin gadon ta kalle meenal din snn tace Waime ya kawoki dakina ne ko kinxo neman mijinkin ne?

Nannauyar ajiyar zucya ya kwace ma meenal dan har yanxu mamakin ganin halisa tay sallan bai saketa ba...muryanta wani iri iri tace "kinsan ni ba muguwa bace kamr ki nazo ne inga ko kin samu sauki dazu naga kinata suma haqqi na yafara binki muguwa ...

Dariya halisa tay tace thanks jikina da sauki..

...waje ta nema ta xauna abakin gadon halisan snn tace "wai ciki kike dashi???

Halisa tay shiru sai kuma tay murmushi tace Eh.. haka champ ya gaya min..we are going to be parents soon.

take fuskar Meenal yay jaaa da mugun kulli aranta tace hmmmm Okay.. kin masa magana na ko dama makirci da karyankine??

kai tsaye Halisa tace ive talked to him, amma yace zaiyi tunani akai

Tsaki meenal taja snn ta mike tsaye tana cewa dama abunda ya kawoni kenan inkin ga dama karki warke kimutu ahaka Znga kuma dan uban da zaki haifa agidan nan wallh baki isa ba..

Dariya kawai Halisay batace mata komi ba harta fice tanajin haushin dariyan halisan aranta bana wasa ba...

Koda taje room dinta kasa zama tay tayi nan tay nan tanata tunanin yadda zatayi itama

washe gari sassafe ta fito ta jira har saida halisa ta fito snn ta tsareta da magana,duk dama ba me dadi take gaya ma halisa ba amma sosai halisan ta bata shawarar akan ta sauya takunta intanason kan mijinta sabida apart frm mugayen abubuwan da meenal tamata wann soyayyar datake ma khaleel din shikadai ne yakesata taji tausayinta aranta duk dama bata fiye nuna mata a fili ba.

Bayan nan Meenal tafara tunanin bin salon halisan koda itama zaa kulata saidai itafa tafison abunda zai mata aiki ne cikin agaggawa, yau kwananta biyu kacal da sanin cewa halisa na da cikin amma tabi ta dora abun aranta cewa itama lallai sai tay wnan cikin sabida khaleel ya juyo da kulawarsa da hanklinsa kanta babban burinta shine ta kore halisa agidan ta mamaye dukiyar mijinta itama taji irin dadin da halisa take ciki yanxu..

Tanason taga sun gwabza akan miji da halisa amma Gashi babu sauran lokci, sati biyu ya tafi already acikin wata gudan da kotu ta basu dan haka she have to take all risk to see her dreams comes tru.

a kwana na ukun Sassaafe ta saka likitarta tamata gwaje gwaje ta bata maganin da zai dakatar da drug din datasha dan ya katse mata yin period da kuma haihuwa tun da jimawa

ranar da likitan ta bata maganin tasha ko aiki baiyi ba saida aka sake mata allurai snn jini ya barke mata tayta fama da azaban ciwon ciki, kafa, baya, ranar tasha azaban bana wasa ba.

Ana washe garin ranan da khaleel zaiyi deciding yafara zuwa dubata din kamar yadda halisa ta bukaceshi meenal tafara shirin daukar cikinshi saidai Haryanxu jinin da suka ballo yaki tsayawa

Shikuwa koda yazo ya samu halinda take ciki dama baizo da noyyar tabata ba Haka yace lallai saidai a dangana akaita babban asibiti aka fara duba lamarinta..

Ranan bakaramin baqin ciki da haushin hakan taji kawai ta lura dashi neman duk wata hanya yake da bazai hada gado da ita ba..

Atakaice saida tay kwana hudu masu kyau a asibiti akwance tana xubda jini Ganin abu yaki ci yaki karewa ga lkci ma tafiya tafara ta fara daagawa hajya nadiya hankli akan lallai itadai sai taimaka mata an tsayar da jini dan ta dau cikin khaleel din itama.

Da wuya da wahala Da Taimakon Alfah jinin ya tsaya a akwana na biyar ranar ranar tace ma likita sam akaita gida wajen mijinta ai yau kwanta ne bana halisa ba..

Now dat she have just 12 days with them tanajin kamar bazata iya lalata koda awa guda na rayuwanta wajen sanya akan khaleel ba..

Tunda har halisa tay cikinsa a sati biyu itama tanason within this days taga cikinnan ya shigeta Kota halin kaka ne

And her medical reports is showing red ga chronic depression ga mugayen ciwukan infection na mahaifa ko binta kan bayanan likitan batay ba tunda alfah ya dakatar da jinin taji karfin gwiwa...

yau tunda suka dawo gidan da likitarta babu wanda yaji sarari miji nata ne a abatajin dadin wai itama sai tay masa girki irinna halisa kiris ya rage gobara ya kama gidan khaleel Allah yaso megadi yana nan shine Ya taimaka ya kashe mata gas akan lokci.

Duk ranta a dagule bata iya komi ba gashi Aliyu ya dauke halisa sunje cikin family house ziyara dan harga Allah bata iya boye kishinta itama wata rana.

Meenal ce kawai take zagaye ita kadai dan abunda ta caccagabar sunyi baki kiri sun kone murus haka ta zuba su a kondon shara.

duk wann be dameta tundaga lagos tasaka mummynta aiko mata sexy nity Tana Allah Allah dare yay khaleel ya shigo

Bai kuwa tashi shigowar ba sai can wajajen sha daya na dare fuskansa ma ba asake ba yazo ya samu tajirasa tagaji har bacci ya fara daukarta

Abakim gadon ya zauna yagama chat da halisa kenan zai kwanta taji motsinsa daga cikin baccin ta farka a firgit.

Firigtan datay yasa taji mararta ya wani murdata ihun bazata tay saida ya juyo yaganta harta zabura ta mike tsaye a take sai kuma taji dumi me mugun yawa na sauko mata kasarta kafin kace wani abu jini guda guda sun tuttulu sunabin kafarta yarrrrrrr sunbi sun wanke kafafunta ixuwa kasa suna sauka dan ko pants bata saka yau ba ta shanya gindi tana jiran miji yaxo..

kusan rudewa tay dataga jinin na sauka dan a take jikinta yahau karkarwa tafara cewa na shiga uku Wayyo Allah na karkamin haka mana...na shiga uku na..

Da mugun sauro khaleel ya dira akan gadon bakinsa yanamai furta innalillahi wa inna ilaihi rajiun...

Rushewa tay da kuka ta tsuguna akasa tafara zage zage tana cewa ta shiga uku.

Bai tabata ya kama hanya yafita after a while sai gasu nan sun dawo tare da halisa suka dau wayar meenal din suna kkrin kira mata likitar gwamntin da aka hadosu da ita.

Meenal kuwa tana ganin halisan tafara ihu tana cewa muguwa azzluma algunguma burinki ya cika kin min asiri dan kar mijina ya kwana dani Allah saiya tsine maki halisa ta dinga ihu tana tsine mata..

halisa tay tay da Khaleel ya taimaka yaki sam karshe ma ya barsu a dakin yaje cikin motarsa yashiga ya kwanta abunsa yay banza da su.

Halisa ne tsaye akanta dik uwan ruwan boma boman zagi da sharrin duniyan saida ta mata amma bata damu ba tana tsaye tare da ita har aliyu ya taho da likitan acikin dare aka hau dubata.

She is having a severe uterine infetion side effect na maganin tsaida menstural flow dinta datay tun tana yar shekara sha takwas da zimman cewa ita bazata sha wahala ba, she is boss lady, equal to men, Shiyasa bazata juri yin al'ada yana katse mata harkokin gabanta ba.

Yau taji babu dadi sosai aranta komi ma ya fara bata haushi tana jin kamar ta musu hauka, dantagama saka rai tay lissafin cikin kwana goma zata dau cikin khaleel ko ana so ko ba aso.

Tunda tafara lamarin zubar jinin nan gidan ya zama ba azaman lafya dan akoyaushe tana cikin tada rikicin cewa halisa ce ta mata asiri dan kar miijnta ya kusanceta.

Khaleel harya yafarajin kamar hakurinsa zai kare akwanakin musammn data fara tarar halisa da mortal combat da dambe, dan tausaya mata da halisan takeyi duk saida tazo ta kwabar dashi sabida she was soo desparate itadai saita sami cikinshi kota halin kaka ne ..

Ana saura sati guda akoma kotu gidan ya dawo kamar wanda ake zamn doya da manja.

Meenal ta sakasu agaba da da fitina da sharri at same time tace ma mummynta lallai kawai ta Amince ta kwana da alfah on her behalf domin ama khaleel wata muguwar asirin mallaka ita tagaji da hakuri kawai gara ta masa asiri me kankat ta mallakeshhi

ganin meenal ta daga hanklinta sosai yasaka hjya nadiya ta aikata hakan snn Alfah ya bata asirin wani abune kamar ruwa akwalba aka bata akan tazo dashi, ya musu list da wasu abubuwa harda buran kare, da jinin al'ada, da danyen placenta aciki yace musu sun tabbata sun nemo wayann abubuwan suyi stew dashi kuma meenal din ce zatay girki tazuba ma khaleel tare da ruwan kwalban abincinsa yaci abincin akalla sau uku sai shikenan bazai sake tuna wata halisa ba sai meenal har mutuwarsa kuwa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull