Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 67
Cheaters club book 2 complete novel Chapter 67: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 67. Tana cikin wann tashin hanklin daga can lagos kuwa harsaida…
3,311 words
Tana cikin wann tashin hanklin daga can lagos kuwa harsaida halisa ta isa kafin nan aka sanar da ita cewa an samo utz bata yarda bama saida aka kaita icu ta shiga Dakin tagansa da idonta his vitals are soo lowww amma yana numfashi
Ranar sai da taji kamar wani bangaren rayuwan ta daya rushe ne ya sake dawowa har wani karamin zazzabin murna saida tayi.
Washe gari da sassafe ranar sharia aka kwaso familyn uztaz din aka zo dasu tare da Duk wani eviidence aka zo dasu.
dake shariar da yamma za'ayi kusan duka kawayen halisa sun hallara cikinsu vicky ne kawai bata samu zuwa ba amma hadiza da jasmine duk sunzo ganin karshen Amina talba.
Dagaata daya bangaren kuwa lawyrnsu meenal tunda safe ya kira hjya nadiya, acikin ciwon yagayamata Labarin abunda ake ciki, yace mata yanxu fa komi babu kanta..
Hanklinta ya tashi matuka ahaka acikin ciwon ta daddafa ta yi amfani da canjin kudin dake wajentta taje police station na maiduguri ta tsaya ma meenal duk uban kyamatarta datay amma ji tay bazata iya barinta ita daya a wann ranan ba.
Meenal duk ta rikice ta zauce hanklimta ya fice ajikinta tunma batasan me zai faru da ita fully ba.
Tana ganin hjya nadiya tazo wajen tafara jin dama dama, saidai bata taba ganin ta tana kiraye kirayen yan uwan ubanta tana kuka duk ta rikice tana rokonsu akan suzo su tsaya ma meenal ba sai yau..
Duk kiraye kirayenta haka kowa ya juya musu baya hatta kawu tjay da suke morar junansu wann karon dayaji bayanin halin da suke ciki tunda ya kashe wayarsa bai sake kunnawa ba.
Daga ita har yarta sun bala'in rudewa, ranar sharian sassafe aka sakasu a mota aka kaisu airpot frm der aka sauke su awani police station dats two hours away frm lagos anan aka kammala wasu abubuwan daga nan ne aka sasu a motar convoy na polisawa har izuwa lagos gabaki daya sun galabaita barin ma hjya ndiya datake fama da mummunn zafin ciwo dan tun tasowarsu daga maiduguri ta dinga gaya ma meenal maganganu masu tsuma tana ce mata nasu ne ya kare kuma tasan ta cuceta da bata dorata akan hanyar gaskiya ba tun tana karama, ta yafe mata akan irin rayuwr karya dana gurbatccyar gata data dorata akai, duk wani gaskiya da dacan bata gaya mata akan rayuwa sai yau ta bude zucyarta take gaya matasu bata boye mata komi ba game da asirin datay ta raba mahaifinta da yan uwansa harya mutu yan uwansa basuzo kan gawarsa ba..
Babu kalar tone tone da nasihe nasihe da batama meenal ba, meenal tay kuka tay borin tay zage zage harta gaji daga bisani tsorone me girma ya rufeta musammn ma dataga ankawosu babban kotun lagos Kotu ya cika da jama'a makil.
koda aka shigo da ita kusan Rudewa tay Ganin ga kawayenta da mijinta da matarsa ga yan uwa kowani bangare, haka aka dinga tono asirin lefukanta one after the other ana fedesu agaban kotu dan lawyern fadila ma kadai bakaramin tonon silili ya musu awajen ba, dukkan lefikanta da aka tono su wanda kashi 90% ta aikatasu ne akan son zuciya, hassada, da danyen rashin tarbiya da kuma girman kai da mugunta....
Kusan awa uku akayi ana case dake ko wani irin sheda yana hannu nan da anan aka zayyano lefukan meenal datayi dat are purnishable by law banda ma da Allah ya saka uztx din bai mutu ba da hukincin rai da rai amma dake yana raye yasa aka bata 8yrs imprisoment a duka duka abunda aka lissafo harda wanda bazata iya biyan fine akansu ba. Dan lefin ta tsakaninta da hukuma kadai anci tararta na 500million, banda fine na damages da murder attempts datayi su ga lefin kazafi ma miji ga lefin satar mahaifa komi akamata jam'insu a shekara takwas a gidan yari aka bi aka basu takardan sakinta saki uku me gabaki daya.
Tunda aka haife meenal bata taba shiga hanklinta tagane cewa tay wani abu me muni da girma a rayuwnta ba saiyau dan banda firgici da ihunta babu abunda yake tashi a kutun tana daka tsalle tana rike mumynta ana janta tana riketa tana cewa mummy mummy mummy karki barsu su tafi dani mutuwa zanyi mummy mummy ihun tadingayi Har aka wuce da ita...
Mummyn nata kuma aka bata 1yr 8months for being a culprits of crime and for obstruction of justice.
Cikin daren labarinta ne ya baza koina a media sabida abubuwan data aikata itada uwarta ya zame ma wasu abun al'ajabi wasu kuma suna ganin lamarin kamar abune wanda ya zama ruwan dare yanxu.
sati guda kenan da Shemau ta haihu da kyar cikin rai da mutuwa ta samu ɗa namiji a asibtin datake zuwa kai yaron jinya taga labarin meenal a tv sabida tunda ta haife yarontan baiyi lafyar numfashi ba, ahakama wani mutum ne nebonta shima dan arewa ne dayazo aiki awajen dayaga wahalar datake sha ya taimaka mata ta ta samu kanta hartake dan fafatawa tana fitowa
dan tunda tafara nakudar taso Allah ya dau ranta Bayan da ta haihun kuma babu abunda takeji face matsanancin nadama da damuwa bata bacci sam ga jaririn ba lafiya dan dan duk sanda ta dau jaririn tagansa xak zak kaman alhaj shafiu ta amayo saita tuna yadda tay rayuwa ta walaknta rayuwarta akan abun duniya da niimar aure wanda duka biyun saida mijinta mahmud ya batasu isasshu bata taba godewa ba, dama can hausawa saida sukace wanda bai gode ma niimar Allah ba zai godewa azabarsa, gashi batay sharar masallaci ba tazo tanayin na kasuwa, bacin zuciya dai shine tabbatacen halakar gangan jikin mutum.
shema Tana cikin damuwar nata rayuwar amma dataga na Meenal batasan sanda ta rushe awajen da kuka ba babu abunda take furtawa sai Allahumma aajirni fiii musibati innnalillih wa inna ilaihi rjin meenal harda tsafi, harda zancen kashe mutum? Lamarin meenal din sosai ya razanata, bibiyar labarin ta dingayi she came to understand that Babban matsalar meenal yafara ne daga mahaifyarta
ranan cikin dare shema tay kuka tay kuka har muryanta saida ya dena fita ba akan komi tay kukan na sai akan nata iyayen.
Ganin Itafa Allah yay mata gata ya bata iyayene na gari da suka tarbiyantar da ita suka nutsar da ita suka nuna mata dede da ba dede ba. Lamarin meenal yasaka shema ta Dada shiga mayucin hali na matsancin kukan nadama da tuba da rokon Allah yafiya da rahama akan abunda tama iyayrnta na cin amana da toxarta.
Ata bangaren su halisa kuwa bayan da aka gama sharia a Washe gari aka shirya uztaz aka kaisa india for advance treatment dake haryanzu bai farfado ba amma yana raye his chances are increasing day by day... Hadiza jasmine kowa dayaga abunda ya faru a kotu duk jikinsa yay sanyi kowa na adduar Allah ya kawo masa sauki anashi rayuwar sabida tun daga kan lamarin shema har izuwa na meenal darasi ne babba ga kowa dan abubuwan da suka fara sun taba rayuwar kusan kowa.
After 6 months ********
Rayuwa ya fara dawowa kowa normal cikin waynn watannin su halisa sunyi tafiye tafiye sunje india dake acan Uztaz ya samu lafiya sukabi suka gaida dr Aseem da famlynsa shima. Snn khaleel ya kaita gidansu a somali tay hutun sati biyu kafin yazo ya tafi da ita saudi arabia suka cigaba da rywan auren su acan dake tana da ciki Yanzu fadila da Anita ke kulawa business dinta na nigeria after 4 months of complted rest kafin uztaz ya jonasu yanxu sun dawo kmr yan uwan jini da fadila har kafin nan ta wuce spain bakin nata aiki tare da shuaib itama
acikin watanni shidan Kusan watanni hudu masu kyau su halisa sukayi a saudi arabia yana aikinsa acan yana kula da matarsa batare da sun dawo nigeria ba
Ata bangaren su mahmud kuwa kusan bayan haihuwar shema da sati biyu zuwa uku hafsa ta haifa masa da namijin shima aka samai suna muhammad Ameer Shagali harda mahaifyar Shema saida tat tattaki daga bauchi tazo taay musu kwana uku akayi komi na suna da ita
Zuwanta ne da suka samu tattaunawa me tsayi da iyayen mahmud suke jin cewa tana neman yarta shemaun amma matsalar kawai shine mahaifin shema Da haryau bai sauka ba Saidai tana da yaqinin cewa inta samu shema komi zaiyi sauki.
Haka suka saka ana ta musu adduan Allah ya bayyana musu ita dan duk bincikenta tace musu bata same labari akanta ba.
ata fannin shema Cikin watanni shida da suka shuden banda wahala da kuncin rayuwa babu abunda take cin karo da shi dan tsabar jinyar jaririnta dtakeyi abunda zata saka abakinta ma saida ya gagareta yaron na ciki wata biyar da sati Allah ya amshe abunsa.
Ranar da Abun ya faru da kafafunta ta tako tundaga asibiti da gawan yaronta a kirji ta iso gida ta samu an kulle gidan da kwado..
Hannu ta dora aka hawaye na zuba mata tana furta Allah na tuba Allah na tuba kukan datakeyi yahaeo hanklin nebonta yafoto ya bata takardan cewa me gidan ne yace mata ta tafi ga kayanta ma ya aje mata su.
Haka ta amshi takardan babu yadda zatay ta goyo gawan yaron ta fita neman wanda zasu tayata a binneshi.
Tana tafiya da goyo akan titi tana hawaye kana ganinta kaga wacce take cikin damuwa batama sanin inda take dosa kawai neman masallaci take inda zta kai damuwarta koda ma arabata da gawan yaron nan tukun tasan inda dare ya mata.
Ahaka harta fara tunanin komawa gaban iyayrnta inma mutuwa zatay gara ta nemo gafararsu koda bazasu yafe mata tasan dai ta nemi gafararsu..
Tana tsaka da wann tunanin taji karar babban mota abayanta ana mata horn garin firgitowa baya ta fadi kasa cikin tubaya sai motar ta tsaya bata ma ga wacce ta fito ba saida taji qamshin turarenta snn taji duniyar ya tsaya mata cakkkk ganin hadixa ce.
Tunda suka hade idanunsu waje guda basu iya saukewa ba har saida hadizan ta dagata sama suka tsaye atsaye suna kallon junansu da mamaki kowa idanunta na zubda hawaye
yau kwanan hadiza uku kenan agarin sunzo harkan siyasa da mijinta dama kuma can tana rike da lamarin shema aranta ita hadiza sam ba bakuwar zafi bace, bata dauki rayuwar nan wani abu ba, her heart and life is soo simple, shiyasa daga tay kuskure inhar ta gane tay abu marar kyau zakaga ta amshe gyaranta akan lkci.
Tun a lkcin bikin halisa dataga sakon shema tausayinta ya tsaya mata aranta saidai tsoro ne ya hanata yin komi akai face saida lamarin meenal yazo ya sake daga mata hankli taji gara ta nemi shema wata rana taga halinda shema take ciki koba komu su musulmai ne, kuma sun more junansu, rauni da kuskure kusan halittan dan adam ne. Inde taga akwai chance na yafewa da taimakawa shema gani take ba wani abu bane awajenta dan tay hakan. Shiyasa suna zuwa wann garin da mijinta tay amfani da information din da yar uwanta haneefa ta bata akan shema tazo yankin datake tanata nemanta ahakan ma da kyar ta sameta ayau din.
Idonsu cikin na juna zuciyar hadiza yaa mugun karyewa data yadda wahalaa da kunci yadaka shemau ta dawo, sunanta ma dakyar hadizan ta furta dake shemaun ce ta fara durkushewa kasa cikin rauni tana kuka ta dauka gizon hadiza take gani
Tunda ta durkushe kuka take tana cewa na cuceki hadiza, na hainceki, naci amanan yardan dakika min..hasada da kwadayi ya hallaka ni, ya rabani da rayuwata da kawance na hadiza kiyi wa Allah kimin aikin gafara.
Haka mutane suka fara taruwa suna kallonsu sabida irin kukan da shema take tana rokon hadiza gafara, a raunane hadizan ta tsuguna ta rungumeta batare da tace mata komi sukay ta kuka. Daga bisani ta saketa ta jawota suka bar wajen izuwa wani hotel nan ne shema ta gayama hadiza duk wani abunda take ciki tun tana da auren mahmud bata boye mata komi ba.
Hadixa tay kuka hartana sheshheka dan sosai labari da nadamar shema ya girgizata bama kadan ba.. abu na farko da suka fara aka binne gawar...sann aka bataa masauki, bayan kwana biyu da suka samu nitswa suka zauna suka tattauna me tsayi.
Shema tagama karaayaa da rayuwa amma haka hadiza ta bata karfin gwiwa tace mata bawa baya cire ransa akan niimar ubangijnsa as long as tana raye akwai wann chance din nafara gina rayuwanta daga farko. Snn hadixa tace mata tay kokari da bata zubda cikin ko ta kashe danta ba, hakan yana nuna cewa tana da imani dan haka ta cire rauni ta farfafo da imaninta ta nemi gafarar iyayenta ta fara rayuwanta akarkashinsu a fresh.
Atakaice dai da kyar shema ta qamsu da hakan badon komi ba saidan tsoro, kunya da nauyin da zuciyarta yake ciki akan abunda ta aikata
Dan haduwarsu da hadizan yasaka tadan wanke daudar jikinta ta dawo kamar mutum aka bata abinci tana ci akai akai bayan sun yi sati hadixa ta rakota suka dawo lagos daga nan suka fara neman iyayenta, har suka same su anan bauchi.
Hadixan ce ta rakota har gidan iyayenta kusan kwanansu uku shema tay tana aikin neman gafarar su da kyar da wuya kafin nan suka barta ta shigo ciki kafin suka amsheta Ahakama baban nata bawai ya gama sake jiki da ita bane. Mahaifyrta ne kawai ta sauya mata gabaki daya, tafara jan ta ajiki yanxu sosai kusan kowani rana saita mata nasiha akan rayuwa duk wani alheri da mahmud ya musu tasha mamaki sosai.
Cikin halisa na shiga wata takwas suka dawo nigeria domin ta haihu anan tay wankan gida
Wajen sunan vicky suka hadu dukansu su ukunsu ita da vickyn da hadiza After a long while bayan abubuwan nan duka sun faru, Baby girl kyakkawa vicky ta haifa an saka mata suna Isabella wajen suna aka sha shagali har dare suna tare inda hadixa ta kawo musu bayanin abunda ya faru afanninta da shema
Dukansu saida jikinsu yay sanyi sosai. Halisa ta yabi halayyar hadiza na tausayi, imani da yafiya, sosai vicky tay hawaye dan itace tafara cewa zata taimaka ma shema da financial assistance dan ta tada rayuwanta tunda duk sunsan dawowar kawancensu kamar dacan da su shemau abu me wuyane sabida kowa yanxu yana da rayuwarsa kuma sun dauki darusa masu yawa masu nauyi dan har akan meenal saida suka tattauna Halisa ce ta gaya musu cewa hjya nadiyan has been seriously sick ana batun za'a kawota asibiti once her case its aproved.
Kowa ma jajantawa dan ayanxu babu sauran wani fushi ko haushi Cikinsu babu wanda yake iya jin wani abun aransa game da yan uwansun face tausayi da adduar samun saukin rayuwa
Labarin meenal dake zuwa shine babu wanda ya taba zuwa dubata tunda aka kaita wajen babu wanda ya lekata haryau har kwanan gobe daga ira sai halinta sai tunaninta tun tana raya masu muni harta fara tuna kalar kuskuren da ta aikata.
Bayan sunan Vicky da wata guda harda sati Halisa ta haihu agidan surakunanta a lagos da tsakar dare dake tun dawowarsu jikinta yay nauyi agidansun kawai take zama.
Khaleel ne ya amshe haihuwar shikadansa tana kuka yana hawaye yana tarairayer har ya zaro yaransa guda biyu daya mace daya namiji
Shi ya mata komi a dakin ya gyarata tsafff tsaff ita da babies din ya mata asalin wankan ruwan zafi ya tabbata tasa ruwan shayi acikinta me kauri ta samu bacci tare da babies dinsu, macen zak zak kamannin khaleel, namijin kuma sosai yake kama da mamansa.
Khaleel almost cudnt take his eyes off her and the kids dan bazai iya misalta farincikin da ke yawo aransa a wann daren ba dan Saida yay nafila yay godiya yay addua ma future din yaran da zuriarsa gabaki daya. Ko baci baijin a idanunsa Haka ya wanke kayan jinin ya kimtsa komi har asubahi tazo ta sameshi. Fitarsa salla duk yana jin kunya sai yake gayawa Aliyu, Aliu ya gaya ma babansa da mamansa...
Da hijabin datay sallah suka dunguma ita da aliyu suka je dakin murna har baki, Kowa na shan mamaki ganin khaleel ya gama komi. mhfyrs ta dau yaran tana hawaye ta rungemesu ajikinta snn ta fito waje ma mahaifinsa dasu dake shi bai shiga room din ba abakin kofa ya tsaya yanata hamdullhi hannun sa harna bari bari ya amshe yaran yanata kallonsu with immense grandfather love and proudess yanata musu addua rana ce garesu da bazasu iya mancewa ba dan krfe shida na safe nayi aka kirasu daga meduguri cewa maryam ma ta haife mace da namiji.
Satin gabaki daya shagalin shirin suna aka dingayi, baki daga ko ina suka zozzo anty jamila kanwar mahaifyar halisa itace ta zo da wuri tun awashe garin haihuwa..
Irin gatan da halisa ta gani a satin bazai misaltu ba Sumtimes ma sai tay dagaske take iya daukar babies dinta sabida kowa yanason ya dauka ya rike.
As usual wann karon hidimar nasu uztax ne dan shine ya dauki jigila akan komi dashi akaje meduguri akayi bidirIn suna bayan suna da kwana biyar duka suka dawo lagos kowa ya kama abunda ke gabansa masu komawa somalia ma suka tafi
Babban acikin causin dinsu halisa na somalia wato nana ai da anty salma sune suka zauna sukay sati biyu har aka gama halisa wankan jego. Anty salma ta sake hadeta tay mata shiri sosai na tarban miji dake ma asalin jegon dacan aka mata ba irinna zamani ba. They make sure she must eat, kuma abinci na musmmn suke mata,dagwalan ppersoup na kajin gida, kunun daka me yaji da hade haden gyaran ruwan nono, tare da ganda daya dahu yaji romo me masifar dadi da sinadari. Banda kana kanan dabaru da ake mata na tari sanyi daga shigewa jikinta da kuma ingantaccen wankan ruwan dumi.
Komi game da kula da yaran ana dora bisa hanya bare ma mahaifyr khaleel bata wani kyaleta tasha wahala da yaran sosai.. bayan wucewar su anty salma, mahaifin khaleel yace musu suma su tattara su koma asalin gidansa dake nan lagos din..LITTAFIN NA NA KUDI NE 08060712446 TO PAY
COMPLETE NOVEL WAIT LIST GROP IS OPEN
*_"MUFTARIQ"_* BY SURAYYAHMS. ®Edited seriies.
_labarin wata tsaftacciyar Soyayya hade da rayuwar wasu yan mata kyawawa guda biyu da suka kasance yan uwan juna ɗaya ta kasance tamkar "hagu" daya ta kasance 'dama" wajen raayi da yanayin rayuwa, sun ci karo a acikin Duniyar_ _kokonto tare da banbance kiyayyar talauci da soyayyar gaskiya akan namiji guda ko ya abun zai kasance oho??_
*the book is ready* amma Will be out only...on *30th August* Wanda suka booking dawuri will get discount on the document...
*Buy now sai asaka a wait list group..yana sauka a tura maka documents naka kasha karatu🤧*
Labari ne me cike da darusan rayuwa...
Dont miss it❤️❤️
#SURAYYAHMS #2024 #CHEATERS CLUB #08060712446 #PAID BOOK #ENDPAGE
yau ne zasu tare a gidansu dake lagos dan haka mahaifyar khaleel ta shirya jariran tsaf a dakinta takimtsa su tun da kafin yamma ya rufa aka killace tsaf da kya da kuma adduoi, sai can Wajajen bayan isha'i Halisa ta kammala shiryawa wani sssnyr kwalliya nude make up tay akan fuskanta ta fito sanye da wata arniyar tsadaddiyar ceibo lace olive colour me touches din gold ajiki dinkin yay mata cass sophiscated peplum blouse and strait skirt na manyan mata ta bi ta yafa babban golden colour mayafinta jakarta da takalminta na amina muadi to march koinanta na fidda qamshi kanta akasa ta karasa babban falon mahaifin nasu bata iya hade ido da kowa ba dan bakaramin kyau tay ba. Da sanyin murya tai sallama aka amsa,lkcin kusan kowa ya hallara, iyayen khaleel nazaune akan doguwar kujera tare da jikokinsu a hannu, A kusa daf da inda khaleel yake halisa ta dan zauna akasa ganin inda yake satar kallonta shidinma yay kyau dan kuwa farar yadi marar nauyi medan sharara ya saka ajikinshi goggiya kan nan nashi ya sha hula wanda ta masa kyau sosai.