Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 7
Cheaters club book 2 complete novel Chapter 7: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 7. Acikin lallami Yace mata calm down na fahimceki my dear. Iya…
3,368 words
Acikin lallami Yace mata calm down na fahimceki my dear. Iya abunda kike so din shi zamuyi... amma kafin nan Abinda zamuyi yanxu shine zan doraki akan wani karamin kwaji,kimin alkwari zaki receiving treatment dinki na wann satin under khaleel supervision zanxo lagos next week zan duba jikin naki dakaina idan naga dagaske zaki iya zama ke kadai toh shikenan we will send u to ur home..is that okay with u????
Ta runtse ido alaman bataso jin hakan ba amma kuma aranta tasan ta hakan ne kawai zatay ta rabu da hidimar khaleel da meenal din cikin sauki dan haka sai kawai ta amince masa cikin ladabi da girmamawa. After all is just a week hala zata iya daurewa, besides what doesnt kill u will even make u stronger.
Sunayin sallama ta taho ta gabansu fuskrta a mugun dore ta mika masa wayar tun kafin ya karba tabita sake masa wayarsa kiris ya rage ya fadi kasa yay saurin taro abunsa yana murmushin ganin plan dinsa yaci a saukake.
Wani tukikin tsaki taja tabi ta kalle uztaz idanunta sun yi ja da bacin rai a muryanta tace "U can go to the office i need to sleep.
Yace okay ma'am Bari na shigo da kayanki toh.
Tace we wll soon leave me zanyi da kayana anan wajen.
A nitse ya matso kusa da ita daf cikin sauke murya kasa kasa yace what about some toiletries?
Batare da ta kallesa ba tace zan tura maka iya abunda nake bukata anja saika kawomin. Ya gyada kansa baice komi ba yay ma khaleel din sallama snn ya kama hanya ya fita. Yana barin wajen itama ta juya zata koma dakin nata,acikin sauke ajiyar zcy khaleel ya fara binta abaya basucewa junansu komi ba suna kaiwa dede bakin kofar taja tayi wani irin baba kere sigar hanashi shigowa ciki....
Suna hade ido yace time for ur morning check up..
Shiru tay Bata ansashi ba dan aranta zantawa take tana cewa wann gayen fa gani yake kamar zai yi amfani da dr Asim ne yasakata tay masa biyayya yay mulki akanta kmr yadda yake baza mulkinsa akan matarsa but she won't just allow that.
Girarta na sama a dage tace "Ohhh..check up?
Yace uhum.
Tace okay I want to sleep, kaje ka dawo anjima in na tashi sai kazo.
Zai magana kenan cikin katseshi da tsawa tace you're not deaf are u???
Karar Tsawar yasaka meenal dirowa akan gadonta cikin sauri ta fito tayota wajensun dan bawani nisa suke dashi ba.
Ganin khaleel din datayi atsaye yasaka ta kara sauri kusan Agaggauce tayo kan halisa tana mai nuna alaman bin biyanta Cikin nuna kulawa tace" what is going on here halisa meke faruwa why are shouting?
Halisa batay niyyar amsata ba amma sai taji kmar bazata iya ba ta dauke kanta a dan fixge
Tace inkin damu kiji damuwata sai ki gayawa mijinki ya fita acikin harkata ana jinyar dole ne????
Juyowa tay zata amsa mata magaanar halisan taja musu tsaki tabi ta banging kofar bammmm a idanunsu tasa key ta ciki snn ta koma kan gadonta ta kwanta tareda lunshe idanunta sosai.
A Sigar makirci meenal ta juyo tare da mayar da kallonta kan khaleel din da sigar tuhuma mai tattare da frustration din attitudes din halisa tanamai cewa.
"Khaleel what did u do to halisa...wai kai wani irin mutum ne, kabita ahankli mana kasan fa bata da lfya, what is wrong with u...
Tafadi hakan ne da sigar raini sabida tasan zei iya mata tsawa halisan taji dan ta dada batashi a idanunta...
Shikuwa kallo daya ya mata sei ya soma tunawa da kalamnta na dazu akansa sai baice mata komi ba ya juya kawai zai bar wajen dan baison suyi abunda ransa zai dada harzuka
Yana saukowa daga side din meenal ta biyoshi fuuu kamar kububuwa dan ta fada masa asalin abunda ke cinta aranta cikin tsaresa tana huci..
Tace dakata min malam Nace meyene ke damun ka? Kasha wani abu ne Answr me khaleel. First of all ka kawota gidana batare da izini na ba, and yanxu tace batason zama damu amma kabi ka nace. Why? Akan me Yarinya tace bataso bataso, so why wont u just let her leave???? Ana dolene ehhh, konima cewa take batason gani na, kaida ma ta tsaneka batason ganinka akanme zaka....
Fincikota dataji yay da wani irin karfi kuma a zuciye yasaka zuciyrta tsinkewa acikin tsananin tsoron yanayinsa na zaki me haɗiya data gani a bayyane.
Cikin kwayar idanunta ya darsa nashi rikutattun idanun meenaal tell me sumting.....
A mugun tsorace da yanayinsa muryanta na rawa rawa tace whaattt khaleel, whaaaaaat and Why are u holding me this way..
Zare mata idanu yay kamar na wanda zai hadiyeta da kyar take iya hadiye yawu izuwa makwaronta dan tsabar tsoronsa da ya lullumeta Muryansa kasa kasa amma zafafe Yace "Have i ever raped u???
Tamkar ba ita ta furta maganan ba tabi ta rikice ta gwalo masa idanunta waje bakinta na ɓari Tace What? Raped? Yaushe.. Akan me kake min irin wann banzan tambayar.
Dada matsota yy saida tay kara mai rauni cikin kunnenta yace..."Don't fucking lie to me.
Ta fashe da kuka ni ka sakeni dan bansan me kake magana akai ba..
Yace "What did u tell ur friend abt me this morning...
Shiru tay kamar bata wajen, ya daka mata tsawa saida ta razana ta fice a hayyacinta yabi ya dawo da ita cikin kara daka mata wani tsawan me kada hanji...
cikin wata makirtacyyar kuka mai karfi tace I dont knw ..ni ban sani ba....Munafuki kawai me shegen gulma...a ina kaji inba karya kakeso ka hadamin ba, maye kawai..
Yace ohh so ure indeed talking abt me then?
A raunane sosai ya saketa yana kallonta da tsananin mamaki aransa muryansa kamar na wanda zai mata kuka yace Amma Meyasa ...Amina mena taba maki..why... why dis harsh and evil describtion of me.. Mena taba miki a duniyan nan ehhhhh?
Kasa amsashi tayi tay tsam tanaa hawaye kamar mutuniyar arziki banda rawa babu abunda jikinta yake tay lissafin duniyan nan amma saida maganan ya tsammace kwakrlwtta da tunaninta dan ko a marfarki batayi tsammanin jin haka abakin khaleel ba.
Cikin waskewa dan karta tambayesa inda yaji yace 'i was coming to the room to check on her sai najiki kina maganan nan and if u dare lie to me zan kawo maki sheda kisan da cewa najiki ... So, Amina is that how......
Cikin katsesa da kukan makirci tace Yes yes i said that naafada khaleel bazan iya maka karya ba.
Kallonta yake tanata wani irin kakalo kuka mai ban tausayi tun kafin yace wani abu yaga harta sulalo kasa timmm bisa kan kafafunsa tabi ta kama masa kafarsa sigar tausyi tare da sunkuyar dakai kasa tana zubdaa hawayenta sosai
..khaleel am sorry.. Pls ka tsaya kaji.. tana fadin hakan ta wani langwameeeee masa wuya kamar almajirar data kwana takwas bataci komi ba.
Khaleel pls Abunda kaji na fada ba gskiya bane nide bada niyyar komi bane yasaka na fadeshi ..they are all lies. U' ve neva raped me, ure good husband to me. Akan me zance mata haka akanka, Wallh Na fada ne kawai domin na jawo halisa cikin hayyacinta..i want her to talk to me. Inasone kawai na sakata magana cos am worried about her mental healtj banason azo ace za kaita gidan mahaukata...
Khaleel dan Allah ka fahimce ni, kana da yan uwa kasan yadda abun yake da ciwo kaga dan uwaka acikin irin wann yanayin...yauko ce mata nayi kana kasheni bai kamata ka daukesa gaskiya ba. i just said it for halisa's sake..pls am sorry my love. Bazan sake ba ..pls forgive me.
Mamakinta yabi ya cikashi yanata kallonta yace da Amina lafyarki kuwa..nace kina da hankli kuwa shin saikin watsar da mutunci nane sann zaki saka kawarki warkewa ko yin magana dake?look, i am very dissapointed in u. This is childishness at it peak. Bansan ma me zance miki ba Amina..amma kiji tsoron Allah.
Matsowa tay zata rike kafarsa yay saurin kwace kafarsa yaja mata tsaki yanamai cewa Let me be. Ai saikije ki zauna da kawartaki kimata jinyar tunda tafi miki aurenki daraja. Yana fadin hakan ya kama hanyarsa yay waje..batako tashi tabi bayansa ba har saida taji karar motarsa snn ta miƙe tsaye ta kar kada jikinta tabi ta share hawayenta taje gaban dispenser ta tsiyayi ruwan sanyi tasha ta sauke wata nannauayr ajiyar zuciya.
Hanyar dayabi tabi da kallo haka kawai dariyar kukan datay ya tason mata tace "such a fool, yanzu fa ya dauke mashi nakewa kuka mtsw..ai me kamani da shaidar wani laifi a duniyan nan sai ya shirya wallhi.
Tsaki taja me sauti ta haura sama dakinta tana isa ta samu wayarta yana ringing video call.
agaggauce ta saka hannu ta dauki wayar ganin mummynta ne yasaka tay sauri ta dauki jan jan baki akan madubi ta hau mulkashi akan fuskarta yay tabbare tabbare dan ace an mareta.
Tana daukar wayar tabi ta sunkuyar da kanta kamr irin an mata dukan tsiya an nakasata din nan, hankli atashe hajiya nadiya da batama lura daa yanayintan ba tace haba Amina wai ina kika shigane inata kirarki baki daukawa kinsan irin hakane yake saka hawan jinina ya tashi. Hjya nakan magana tun bata karkare ba meenal ta dago fuskarta ahankli tanamai sakin kuka
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Amina ? amina meya sameki meya faru.
Rushewa da kukan ta kumayi mummy ba khaleel bane dan nace masa yabi halisa ahankli shine ya mareni
Ya mareki? Kutuman ubancan...ke kuma kika tsaya yin mene.
Mummy na rama mari na mana..kawai de rainin dayakemin din ne yafara yin yawwa mummy haba ace kenan bani da wani iko dashi...mummy we need to talk akan business din nan mummy ince dai dan yana gadara da an dorasa a project din nan ne yafara rainani???.
Cike da bakin ciki Hajya nadiya tace kasssh Amina kaiconki wallh. Seda na gaya maki kizo muje wajen alfa ayi masa me kankata kikace a'a amma inbanda raini har ya isa ya dora hannunsa akanki...bura ubancan yaron nan bai sanni bako? Idanbya sake ya sake marinki to har gidan ubansa zanje na mare uwarsa.
Mummy is okay.. Nide bari na shirya nazo kawai muje ta beach mu tattauna...nan gidana is no longer safe. Khaleel ya sakamin ido yana son yaga bayana.
Habawa yama isa yaga bayanki?..Allah situru bukwui..me ganin bayanki ai saide maqiyinki .marmza ki shirya kizo muje ina jiranki agidana.
A shagwabe tace yes mummy yanxu zanzo
Daga nan ta katse wayar cikin rolling eyes ta mike tsaye tana karkada kafafunta aranta tana cewa inkasan wata ai bakasan wata ba...
**********
Ata dayan fannin kuwa wan satin ya kasance da shauki na musanmaan ga rayuwar vicky dake satine dake dauke da zagowar ranar auren su da mijinta femi.
Duk da yawan matsalolin zamantakewar aure datake fuskanta a rayuwa sam hakan bai hanata binnesu a kasar ranta domin ta shirya musu bikin zagowar wann ranar na aurensu daya kafa tarihi acikin rayuwarsu ba..
Ayayinda take haba haba Da isowar wann ranan ata dayan fannin chief okoro ma shiryawa yake yi sosai domin bikin murnan zagowar ranar haihuwarsa daya fado dede da wann ranan.
Ranar zagowar aurensu kusan lkci ne me muhimmci agaresu wanda hatta femin da bai dauke auransu da daraja aransa ba yafi samun kwanciyar hankli idan yay spending wann lkin tare da ita sede wann karon gani yake kamar zai masa mugu wuya wajen zantar da hukunci bisa ga inda zaije duk dama aransa ya bari cewa he will attend both kawai, Ma'ana inya kammala da vicky sai ya dawo kan chief dinsa su hole junansu, sede ata fannin chief din sam ba hakan bane aransa. So yake ya dandana wa zuciyar vickyn azabar da bazata taba mancewa ba badan komi ba saidan tasan da cewa yanajin mtsanancin Kishin masoyinsa femi....
tun daga yau vicky ta fara decorartng gidanta domin hidimar tunda wann karon indoor celebration kawai ta yanke hukuncin zasuyi sabida sunada bukatar bawa junansu lokci na musamman domin su sake karfafa marital vows da darajar igiyoyin auren dake kansu.
Da zciyarta daya take shirya komi dan aganinta wann karon zata iyayin komi dan su samu karin fahintar juna, su dawo da rayuwarsu ta jin dadi dede tare da mijinta femi cikin nunawa juna so da kulawa.
Daga inda take tsaye akasa ta zuba red roses da wasu irin pure white balloons tako ina suna bouncing akasa har zuwa inda take tsammanin femi zai fara dora kafafunsa.
Daga ido tayi ta kare ma wajen kallo gadon dake dakin ta lailayeshi da farin beddings da kuma farin comfoters masu tsada da armashi sai yanzu ta dada gyara zaman rubutun"I Love you"da red roses flakes din data jerosu akan gadon just beside where she cud reach.
Tun goben baiyi ba dakin ya riga ya dauka da wani irin azababben qamshin lavenders and vanilla notes masu dadin gaske.
Murmushi me nauyi ne ya kufce mata cikin zulumin rashn sanin me zatayi Ta dauke katon single red rose din dake kasa tana kallo ahankli takai hannu ta tura shi kan fuskan ta kamar me shakar daddan qamshin jikin roses din
Wani tsabar sanyi da Farin cikin daya mamaye ta a wannan lokacin jinshi take tamkar babu mahadin shi..
sakin flower tayi akasa da gudu tana dariya ta dauki balloons din dake kasa tana wasa da su.
she looks vry excited harta manta da condition dinta nata na dar dar din zaizo ko bazaizo ba duba da yana fushi da ita, altho she have a strong feeling in her heart najin cewa hala daga goben rayuwarta ne gabaki daya zai sauya mata for good.... #SURAYYAHMS NOT A FREE BOOK MAISON KARANTAWA CHAT ME 08060712446
I WISH U ALL A SUCCESSFUL IBADAT.
IN SHA ALLAH DAGA MUN DAWO POSTING ZAI SAUYA IZUWA BIBBIYU ARANA ADAURE ANA COMENTS DAN DA BAZARKU MUKE TAKA RAWA.
MUCH LOVE...AS WE WAIT FOT THE HOTESST LOVE BANGERS🔥🔥🔥🔥🔥🔥 DAT IS COMING FOR US IN NEXT LINE OF THIS STORY... KU GRGIJE KU SHIRYA MASA DAN AKWAI DRAMA DA ABUN DUNIYAN WATO SOYAYYA🙈🙈🙈
AYI HUTUN RAMADAN LAFIYA⭐ 08060712446 ▶️1️⃣8️⃣.
Bayan kamar awa guda gidan meenal din ya dauka da wani irin shiru tamkar ba ayi wani hayaniya acikinsa da safen ba ayayinda dukansu matayen suke kulle cikin dakunansu kowacce da yanayin data tsinci kanta aciki na hargitsar tunani kala kala kuma mabambamta.
Sam meenal takasa zama waje guda, tsiriyar hannunta mai tsananin laushi dake nan soo fresh yay jazir har ya tara xufa sanadiyar yadda ta damkeshi da karfi tanamai jeka ka dawo atsakiyar fankacecen room dinta da tunanin irin hukuncin da zata dauka akan mijinta khaleel,Da kuma halisa.
Wanda ata dayan fannin Kwance halisan take Dik tinani ya cikata tayi lumi kan gado tana kokarin calming zuciyarta da yau zafi akan zaman dole daya kamata anan gidan da bata kaunar ganin kanta aciki kona scnds wanda duk gani take kamar lefin duka na khaleel ne...
Yanayin yadda ta lumshe idanuwanta ta nitsar da kanta akan gadon zaka rantse babu abunda yake damun zuciyarta saidai ita kadaice tasan me ke mata ciwo arantan sosai. Dan kuwa jitake kmr ma tsanar datake ma khaleel ya karune aranta dan haryau bataga dalilin da zai ajeta agidansa duk da yasan bason hakan takeyi a wann lkcin ba...
Jin kanta takeyi acikin yanayin matsatsin matsi da kuma takura, dan atmospher din gidan baimata dadi sam.
Duk juyin datay akan gadon sai ya taho mata tare da hoton kyakkwar fuskarsa wanda ahalin ynxu haushinsa takeji har cikin kololuwar xuciyarta irin haushin nan da ita kanta batasan iyakarsa ba.
wata hutacciyar tsaki mai cike da yanayin kufula dayake xuwa mata tun daga cikin kokon zucyarta har izuwa kan makwaronta shine yake kufce mata.
Duk sanda ta bude ido ta rufe sai taji zuciyarta ya harba da haushi, atake kuma sai ranta ya dauka da bambami da mita akansa, aranta cewa take "He is so rude, baida aji Komi dei sai ya nuna ikonsa akai Baida tausayi baida tarbiya sam sam, he cant even respect a woman's decison mtswww but she wll make him.
Ta jima cikin zancen zuci kafin nan wata nannauyar ajiyar xuciya mai hade da tsaki mai hautsinannen sauti ya kufce mata,.lumshe idonta tay ta bude can kasar wuyarta ta furta "zanyi maganinshi"".. Sann ta juyo ta hannun hagu tareda rungumar kanta tay shiru batare da ta sake kawo tunanin sa aranta ba, tafi awa guda ahaka Har saida tagaji tadan saka kanta baccin dole na yan mintoci snn ta farka takejn haushin Abun ya dan ragu mata aranta.
Gabobin jikinta duk sun mutu, sam bata jin guzari tabi tay mashak bisa kan gadon, ahankli ta bude idanunta da sukayi jaaa tana bibiyar cikin dakin da kallo. Wani irin takaicin ganinta anan din taji yana shirin shakure mata wuya sede darajar Dr Asim din yasaka ta danneshi tahakura kawai zata dan sassauta ta zauna amma ba dan tanason haka aranta ba.
Ahnkali ta Rungumi pillownta tanamai sauke ajiyan zuciya masu nauyi Cike da ayyana wasu abubuwan aranta.
Bahaushe yay gaskiya dayace fadar dayafi karfinka saika maidashi wasa.
Gefe Ta juya ahnkli ta lalumo wayarta cikin gyara zama ta budeshi ahankli ta fara rubuta sako cikin dakikanin lkci bayan kamr mintina uku ta danna send san ta aje wayar agefe ta yunkura da niyyar miƙewa zaune ahankli jin wani irin jiri mai karfin tsiya na yawo da ita atake ya fixgeta ta dawo baya kan pillow hannunta tabi ta dora bisa kan ta ta rikeshi sosai jin dakin kamar na juyawa da ita tsabar jiri ga wani azaban ciwo dakantan yake mata.
Wanda ko da ba agaya mata ba tasan da akwai na bala'in yunwa datakeji dana tsananin bukatar hutu da sassan jikinta yake bukata a wann lkci. Shafaffen Cikinta taji yana kugi tare da kuka tabi ta damkeshi shima sosai ta lumshe idanunta sosai..
Kowani dakikanin lkcin data dauka ahakan bakaramin azaba takeji ba dan yanayin datakeji na tsananta mata tsabar yunwa har yawunta ya fara daukewa gabaki daya sede kodede na minti daya bata kawo tunanin jin sha'awar cin abincin gidan meenal ba ...
Hannunta na rawa rawa Ta sake jawo wayarta da kyar ta kara rubuta ma uztaz da sakon Abinci snn ta nemi waje ta dan kwanta jin jikinta ya dauka da wani irin zafi sosai.
30 minutes later *********
Meenal ce tsaye agaban fankacecen huge italian oval mirror dinta mai nuna mutum daga sama har kasa dake manne da bangon dakin takurewa kanta idanu ayayin da ta kammala shiryawa cikin sabuwar dressing dinta.
fitted gown ce na tetsur turkish material, green colour mai balain laushi da tsantsi wanda basai an gaya maka matarial din me tsadace sabida kyaunshi dake wanxuwa a sarari.
Juyi take hannunta na bisa kugunta dinkin ya kame dirin jikinta damas shape dinta na yan gayu ya fito zak zak duk dama yau tay kkri ta rufe kanta tay rollng dinshi da multi color veil dan karami.
Babu yabo babu fallasa tay murmushi altho she is not satisfied da dressing din sosai koda shikema mum kawai zata gani dan haka zata iya daurewa.
Da kyar ta bar jikin madubin Bayan ta gama yaba kyaun halittar da Allah ya zuba mata a gaban madubin dan kuwa a kullum ta kalli kanta sai taji ta kara burge kanta dan gani take duk wani wanda ya sameta ya taka karshen sa'a duniya da lahira ya samu rabo. Tana ji da kanta makurar ji dakai. Ta kuma yarda da kanta, tanajin duk duniya ita kadaice macen data san metakyi, me kwakwala da kuma wayewa sosai.
Ahnkli ta tako ta iso ta jikin bango inda wani shirgegen wooden structure me kamar wadrob yake ta danna wani Abu ajikinshi tun daga farkon bangon har karshensa ya budu inda sashi shashi na turarruka da takalman designer da jakuna na zamani suke ajiye kowani bangare da irin tasa desgner din.
Yadda taga kayan nata ajerere rass cikin tsafta da tattali Murmushi me sanyi ne ya kufce mata tuna cewa duk wann aikin bana kowa bane face na halisa tun na ranar datazo mata suka kwana agidan tare ta tsaftace mata ko ina ta gyara matashi.
Duk munin zucyarta tanaji aranta kmr Halisa mansa tana daya daga cikin mutane masu matukar muhimmaci acikin rayuwarta wanda bazata taɓa iya hakura dasu ba.