Kenza eBookz

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 8

Cheaters club book 2 complete novel - Chapter 8

Cheaters club book 2 complete novel Chapter 8: Cheaters club book 2 complete novel Chapter 8. Murmushi ta cigaba da yi tanamai shafa kan kayan ahnkli da…

3,359 words

Murmushi ta cigaba da yi tanamai shafa kan kayan ahnkli da dogayen yatsun hannunta dayaji tattalin manicure da zara zaran farcunta na zamani.

As usual Tsabar yawan takalmanta nata takan rasa wannene zata dauka hannu ta zura ta fito da wedges na gucci ta dudduba bai mata ba ta jefar kasa, ta dauki designer heels kala kala yakai biyar duk basu mata ta watsar,ta sake komawa kan flat duk ta jefar kasa. Haka tabar wajen abude ta koma cikin closet dinta, dan madaidaicin dakine shima da reserves na kayayykin sawarta ya ke jere aciki, tana shigowa ciki bata wani bata lokci ba ta jawo wata karamar side bag na fendi me hade da shoes dinsa ta zura akafarta sann ta dawo dakin kallo daya tay ma takalman data watsar akasa ta dauke kanta ta feffetsa turare agugurje snn ta fito.

Tafiya take kamar bazatay ba domin itakanta qamshin turaren data fetsa ajikin nata tsabar yawansu da karfin qamshinsu ji take kmr suna bugar da ita.

Daya bayan daya take dora kafafuwanta akan step dede lokcin ranta yake ayyana mata taje ta ta duba halisa hala ta sauko sai kuma wani zucyar ya kaucar mata da tunanin hakan acikin sauri. Gara kawai taje wajen mummy koda ma zata bata wani haske.

Dede ta sauka akan stairs din kenan aka bude kofar main falo, a rigime sosai kamr wata sarauniya ta daga kanta sama domin taga waye yake shigowa.

Aranta Jira take in jasmine ne ta shigo ta sauke mata buhun haushin datakeji akan sabbin halayyar halisa sai kuma akayi rashin sa'a ganin kmar mutane biyune suke tunkarowa.

Take ta dauke wuta ta hade ranta sosai ganin uztaz ne agaba nata sauri sauri dauke da karamin beige trolley box a hannunsa da kuma ledar Abinci daya riko daga fav restaurant din halisa yana sauri. Ganin irin kallon debar albarkn datake masa yasaka ya dan ja yabawa khaleel din hanya ya shige gaba.

Hura hanci take har suka karasota uztaz yana gaisheta ta sharesa dan batace musu uffan ba.

wata sihirtacciyar numfashi khaleel yaja ya kalleta sama da kasa ahnkli snn yace " Madam Where to? Cikin idonsa ta kalla kafin nan Ta dauke kanta batace mai komi dan tasan tafi karfin tagaya masa inda zataje shine kawai baya gajiya da tambayarta kowani lokci.

Agogon hannunta ta kalla sann ta kallesa atakaice, batare da wani kulawa ayaninta ba tace.."Ya bakaje wajen aiki ba?.. Bayabo ba fallasa yace most of my work is here at home now ko kin manta ne??

Wani Abu taji ya tsaya mata a kirji ta juyo ta kalleshi dan sai yanzu ne ma tadada tunawa da cewa shine zai cigaba da kulawa da lfyar kawarta halisa mansa.

Cikin kasar ranta bawani ganin khaleel yana bada cikakken attention dinsa akan wata ƴa macen takeyi ba sede tunawa da cewa shemau tace mata ta kwantar da hanklinta tunda halisa da khaleel din basa shiri wanda hakan ne kawai yasaka takanji dama dama.

Motsi bakinta yahauyi da alaman tana son ta furta masa wasu abubuwan sai ta kuma fasa Sanin cewa Dazun da yazo dubata halisa bata wani kula daga ita har shi din ba.

Son jin mezaiyi ynxun yasaka ta kallesa sigar makirci tace did u need my help?? kasan halsy batason Allura zan iya binka ciki na tayaka convncing dinta, khaleel ya girgiza kai yace thanks, Am just gonna make sure taci wani abu sai Abata magani dats all babu wani abu dan Wann satin gabaki daya na hutu ne agareta And i am here to make sure of it.. Muryanshi a nitse take fidda maganan with no string or attachemnt, meenal najin dirar nitsutsayr sautin nashi har cikin kwakwarta. gashi de very simple amma haduwar tasa yasaka damuwa da kishi yake cakkarta bana wasa ba. Tafiso koda ma ace khaleel dinta ne zai kula da lfyar kwakwalr halisa yazamto cewa cikakkiyar Amincewarta shine ya basa izinin yin hakan, ba doka daga wajen ogansa ba.

Hakan ne yasaka sam Abun bai wani kwanta mata aranta sosai ba but she can't show it sabida kowa yasan tafi kowa zakewa akan lamuran halisa mansa.

Har ranta Tanason zama tare da halisar amma ba awann yanayin datake ganin kamr tana fushi da ita ba dan gani take hala bazata iya controling din tunaninta ahakan ba.

Cikin dakikanin lkci ta kalle hanyar kofar dakin halisan snn ta kalle khaleel atakaice, aranta tanamai jin tsoron what if halisa ta gane cewa khaleel mutunin kirkine sanadiyar kusancin da zasu samu ta jinyar nan kenan duk abunda take zayyanawa akansa karyane.??

Gaskiya dolen ta nemi wani hanya da zata sakasu su cigaba da gaba da junansu agidan sosai dan bazai taɓa yuwa tabar khaleel ya wanke kansa agaban halisa atacikin sauki ba gani take kamr hakan zai lalata kusan kashi tamanin acikin yardan dake tsakaninta da halisa tuna cewa tajima tana mata karya akansa tin ma bai aureta ba .

Wani irin kallon mai cike da mutsamutsan kishin ne ya chakketa ko iya daga idonta bata karayi akansa ba..

Daga tsayen Tagama ayyana abubuwan da zatay aranta Muryanta kasa kasa tace okay. Bye. Snn tafara tafiya kamr bakomi aranta alhali Allah Allah take taga ta isa wajen mummynta dansu tattauna.

Daga ta dayan bangaren Uxtaz ya samu halisa akwance gabaki daya idanuwanta sunyi luhu luhu sun nuna alaman galabaicewa. Yunwar datakeji alkcin ya kazanta dan har amai amai takeji zuciyarta na kuma tashi.

Uztaz ya zauna abakin gadonta ahankli ta miƙe zaune dakyar tanata kallonsa nishi na kufce mata ahankli.

Cikin sanyin murya yace mata sannu da sigar tausayawa sosai Sanda ta kare ma ledojin Abincin daya shigo dasun har guda biyu kallo snn Ta gyada masa kai muryanta a sanyaye tace "Am farmished ka siya min regular burger dina?Kar kace baka siya min ba kasan shikadai nake sha'awar ci ayanzu ko.

Uxtaz yy murmushi yace how can i forget. sai yay shiru baice komi dan baisan ya za'ayi ya mata bayanin cewa khaleel ne ya zaba mata kuma yasiya mata Abincin ba.

Hannu ta miƙa masa alaman zata miƙe tsaye a firgit ya rikota ahnkli cikin kulawa harta sauka kasa ta tsaya batare da ta motsa jikinta ba sabida jiri.

Acikin sauri uztaz ya dauko wata bedroom sleepers mai laushi ya aje mata akasa sanda tadan dafa kafadunshi kafin ta iya daga kafarta ta zurasu aciki jikinta babu karfi sam tana takawa ahnkli hartakai kanta cikin bathrum.

Bibbiyu take gani amma haka ta daddafa ta rike kan sink din ta kunna ruwa yahau tsiyaya akan hannunta atake kuma sai tafara tuna fadawarta acikin tekun, ajiyan zuciya me matukar karfi ne ya kwace mata tabi ta fixge kanta da karfi daga cikin wnn tunanin snn ta deba ruwan ta watsa bisa fuskrta sanyin ruwan na ratsata har ta cikin gangan jiki, snn ta hau wanke bakinta dashi tana fetsarwa.

Sam sam taki ta dago kanta bare ta kalle kanta a madubi, dan wnn karon sosai tay makanta alkwarin daurewa, ahaka harta kammala ta jawo karamin towel ta goge fuskarta after like 3 min ta bude kofr ahankli fito.

Ganin khaleel a tsakiyar dakin yasaka ta tsaya Turus ta zuba musu ido daga inda taken tanata kallonsa ayayinda shi kuma ya juyamata baya.. #SURAYYAHMS. ****Bayani kawai yake shararowa uztaz akan abubuwan dayakamata tanaci da muryansa mai cike da slangs wanda ko harshen hausa yakeyi dolene zakaji accent din kwarewarsa a turanci aciki"...Her diet is very important sabida tana bukatar isasshen lafia ajikinta, inbamu bada hakan muhimmnci ba kwakwaltata bazai samu cikakken lafya ba.

Cikin lumshe ido da budewa taja tsaki aranta tanamai cewa kajishi sai kace shidin kwakwalrsa cikakken lafya yake dashi.

Da yanayin damuwa Uztaz yace na fahimta Doctor. Amma ina bukatar lkcin da zan dan fahimtar da ita akan sauyin da aka samu. Ta riga ta saba da cin Abunda take so kuma yanxu haka ma shidin takeso taci bazan iya ce mata kartaci ba...

Khaleel na shirin amsawa kenan suka hade idanunsu waje guda da halisan Wani irin harara tabi ta watsa masa tabi ta dauke kanta.

Sunfi minti biyu ahaka snn ya sauƙe wata sassanyar ajiyar zciya gamida wata kyakkwar murmushin data wakana akan kyakkywan fasalin fuskarshi mai tsananin sanyi da ɗarsa wani muhimmyar yanayi najin karfin qwiwa atattare dashi.

kirjintane ya buga damm zuciyanta na daka tsalle kamar zai ballo ya fito waje batare da tasan cikakken dalili ba.

a hnkli ta juyo cikin sauri sauri tana kuwa juyowar kuwa ta tsinci kwayar idanun ta acikin nashi.

atake idanun su yay mummunan sarkafewa acikin na juna..

Cikin wani irin maraitaccen yanayin datayi masa bazata ya sauƙe ajiyar zuciyarsa acikin wani siga boyayya

Da sauri ta dauke kanta ta mayar gefe ayayinda shima ya sassauto da nashi kallon ƙasa .

a hnkli ya dago ya kalleta magana yake shirin mata sai yaga ta firgita ta matsa can nesa dashi cikin wata sassanyar muryanta mai tsananin taushi da sanyi tace".

"Uztaz where is my food pls.

Adame Uztaz ya daga kai ya kalle khaleel da yanayin dar dar aransa ganin khaleel ya gyada masa kai yasakashi ya sauke ajiyar zcy snn ya mike tsaye cikin sauri ya tattara Kayan Abincin ya wuce kitchen ya zubasu akan plate yadda ya saba snn ya taho mata dashi.

Shiru dakin ya dauka dashi dan tun fitarsa cikinsu babu wanda yacewa dan uwansa cikanka hasalima shine kawai yake kallonta da ynyin jin mamakin jiji dakai irin nata.

Itakuwa harɗe fuskanta tayi ta bashi baya kamar batasan da wani halitta acikin dakin ba.

Sallamar uztaz yasaka khaleel yadan dauke kanta akansa ya kallesa Riki riki da tray din Abincin a hannu.

Kada kansa yay kawai ganin uztaz ya saka mata cheese burger dinta agefe duk dama yace masa karyana bata irin wayannan junks din da safe kawai gani yake kamr tsoronta uztaz yakeji shikuwa uztaz baison kokadan yaga ya bata mata ranta ne dan kamr jininshi hakanan yakejinta aransa.

Uztaz Yana aje abincin agabanta khaleel ya karaso ya gyara mata zaman canula pin din a hannunta snn Ya tsaya agefe Yana kallon yadda ta kure abincin da wasu irin kallon kallo alaman bata gane kan Abincin ba.

Mita take aranta tana cewa "Kowa yace ma uztaz ya siyo mata wayyann omalete da ganyeykin oho.

Ahnkli Ta kyabe baki Batare da ta damu ba Ta miƙa hannu zata dauki burger dinta dake sakale agefe danta faraci tanamika hannu kusan atare suka kai hannayensu kan burger din tare dana khaleel jin balain taushin hannunsa ya gogi nata tay saurin sake mashi burgen ya dauke cak tanata kallonshi har yakai bakinsa ya gutsira batare da yacire kwayar idanunsa anata ba ahnkli ya lumshe ido ya bude tare da bada sautin mmmmmmmmmm.

Lokacin ji take kamar ta shakureshi tsabar ruwan takaici..

kamar zatay kuka ta kalle sa snn ta kalle uztaz a yanayinta hatsale kmr na yarinyar da aka kwace mata Abincinta.

Shagwababben muryanta mai cike da takaici ya ratsa dodon kunnensa har wani yarr yakeji ajikin sa.

Ta nunashi ma uztaz da yatsa.. "why did he take my food?

Uztaz ya rasa me zaice ya fara kame kame.

Cikin katsesa khaleel din ya nuna mata omalate da greek salad dake gabanta snn yace mata "Dat is ur food. Kiyi kkri ki cinye sabida na baki maganinki. ya fada mata hakan ko ajikinshi hanklinsa kwance majestically ya fita da favrite burger din nata a hannun sa Abunda ya dada bata haushin ma cin dayakeyi yana kada kai da alaman burgern tay masa dadi.

Takaicinshi taji ya gumeta har wuyarta,

Yanaficewa adakin tasauke hawaye mai zafi, snn ta dawo kan uztaz da wata balaieyar masifa. "Kana kallo yana dauka min Abincina bazaka kwace min ba. duk dama yasan masifar da frustration aciki amma ganin tana hawaye sai yaji hanklinsa ya tashi sosai, bakin shi harna rawa ya fara lallabata yanamai mata bayanin yadda sukayi da khaleel akan sauyawar diet routine dinta.

Kowani safiya 30 min bayan ta farka daga barci zatana cin Abincin safe kuma bazai wuce 7-8am na safe ba. Hakama lunch 12:30-2pm, bazata kuma ci abinci karfe 4 na yamma ba sann da dare zata ci abinci atleast awa uku kafin nan tay bacci.

Yace Ure going to avoid hot, acidic, spicy, fried, cold and sugary foods.

Tun kafun ya kammala bayanin halisa ta dada fashewa da kuka mai sanyi aranta Tana mugun regreting Abunda ya sakata ta Amince wa Dr Aseem zatay jinyan nan.

Duk bayanin nan da uztaz yake mata wayarta na hannunta tana kirar layinsa amma baya shiga sam.

Ta rike wayar ta cigaba da hawaye sosai danko ta kirashin itakanta batasan me zata gayamai takamamme dan ya yarda ba, koda ce masa tay tatsane khaleel tasan sedei yace mata ta daure tay hakuri.

This One week is going to feel like the worst week of her entire life.

Ta kalle uztaz tace ka tafi da abincin kawai bazan ci ba tunda Har abunda zanci ma sai ya gaya maka I will not let anyone decide what and how i will eat.

Hanklin uztaz ya tashi ya nata bata hakuri amma taki sam ta kulashi.

Irin rikicin nan me tattare da baqar yunwa take yi shikansa yagane yunwa ya nakasata sosai.

Haka ya dau Abinci ya rike ya kasa fita waje dashi yanata kallonta intayi kuka ta gaji sai tay masa masifa kuma tace mai bazataci Abincin ba.

Da shagwaba da zafin ciwo sai Ɓari da jikinta ya somayi, zazzabi mai tsananin zafi ya rufeta ta aje kanta akan pillow tana hawaye tamkar marainiya.

Bayan kamar minti Arba'in Uztaz yana daga kai akanta sai ga kiran khaleel din ya shigo wayarsa ya dauka baice komi ba.

Atakaice khaleel yace masa "Whats going on?..

Sai ya dan ja gefe kadan yace uhhmm Dr she's not cooperating and she's weak dole ne zata ci abinci fa.

agogon sa ya duba cikin sauke ajiyar zucya yace its to 10 kana nufin har yanzu bata ci komai ba

Yace yess yess sir.. .

yayi tsaki can kasan makoshi yace bari kawai gani nan shigowa ya katse wayar a hanzarce ya bar inda yake ya dawo gidan cikin gaggawa, awaje ma yabar car dinsa, quickly majestic ya shigo cikn gidan, face nashi a daure yana tafiya nan ya iso sashen nata kai tsaye.

Knck dayay yay kafin nn Ya bude kofar suka hade ido da ita da sauri ta kau da kanta wasu tsabbin tears din ne suka ciko mata tabi ta hadiyeshi cikin sauri.

Hannu ya mika ya karbe plate din a hannun uztaz yabi ya kama hannunta yagyara mata zaman canula data cukuiyashi

..shikuwa uztaz sai ya ja gefe ya na kallon su..

Yanayin yadda ya rike hannun ta yana gyarawa ba ko tausayi ya sa ta juyo da fuskan ta fusace tana kallonsa ita sam duk abunda yayi mata zafinshi take ji fiye da na kowa sabida haushi da tsanarsa datakeji aranta

Shikuwa Haushi taurin kan nata yake bashi... har idanunsa sun fara sauyawa izuwa jaaa yana sake hannunta yace zaki ci abinci yanzun nan ya hade rai sosai with a comanding tune ya gaya mata haka...

kafin nan ta bude baki ya dago abincin dake ajiye agefe ya mika mata..

"Eat"...ya fada tare da watsa mata daring looks.

Uztaz yana shiru shikam yana ganin ikon Allah ,ta dau 3 mints bata kalleshi ba snn ita batace komai ba kuma bata sa hannu ta amsa abincin ba..

lumshe idon sa yayi in anoyyance yace will u just take it?.kusan tsawa yay mata. "I said eat ur food my friend...ko bakiji..ure not a child for god sake.

Doctor khaleel please take it easy on her Uztaz yafada hakan da magiya da kuma alaman damuwa a yanayinsa.

Khaleel ya hade rai ya daga masa hannu irin enough dan yasan ba'a jinyar me taurin kai da lallami.

Koda taga yay nasara fahmtar da uztaz hakan Haka kawai taji kuka na shirin dawowa mata, shirin jan cannulan takeyi again zata hade kanta da gwiwa amma yadda ya daure da dan zafi yasa ta kasa iya aikatawa ..

A nitse ya taho ya dangwala mata Abincin agaban ta suna hade ido cikin sauke murya kasa kasa yace mata idan baki dauki abincin nan kin fara ci ba zaki ga abunda zan miki, i assure u,..u and i are going to be spending forever in this house...very silly ...muryan slangs dinsa har ringing yake a kunnen ta tanaji kamr ta shakure shi..

Da kyar ta daure Muryan ta a dishe cikin masifa Tace "fine..you and i till eternity ni bazan ci abincinka ba ana dole ne.

Yayi tsaki wayarsa ya shiga zarewa daga wandon aljihunsu yace zaki san dole ne kuwa.

Tay banza dashi duk ta dauka baxai samu Dr Aseem awaya ba tunda itama ta nemeshi bata samesa ba. Sede Tana jin Wayar ya fara ringing tafirgita jikin ta yafara tsananta rawa ta ciki tyi kifi kifi da ido tana satar kallonsa dan batason ya jawo mata karin sati irin na dazu.

Harararta yay yace kin dauka kina ci ko sai na kirashi na gaya masa? U knw He is going to Add days to ur treatment ryt?

Wani irin taurin kai ne ke damunta amma tsoron yadda taga baida kirki ya ya sa ta jawo abinci ta rike a hannunta..

Shidai uztaz yana tsaye baison ma su hade ido

Halisa ta daga spoon tana juyawa tana jan shesshaka ahankli..

Khaleel Ya sauke wayar a kunnensa yace "eat"ta dago da sauri tana ganin yadda ya daure fuska ta sake hawaye mai sanyi wanda yay mummunan kashemai jiki.

Cikin basar da hakan kasar wuyarsa yace i just hate nonsense duba yadda kike bata min lokaci, batace mai komi ba ta soma dura ma bakin ta abincin batare da sani ba..

Wani Shiru ne ya ratsa wajen tana hawaye tana ci sunata kallon ta...

Aransa yace Indai dani zakiyi taurin kai zaki sha wahala cikin ransa ya furta...

Sai da tayi kusan loma 5 masu kyau sannan ya juyo ya karaso kusa da ita ko ajikin sa ya shiga hade ruwan allurarsa..

Idon ta ta dage tana duban shakurarren fuskansa har ya gama hade ruwan Alluran.

tsoro ya hanata sake kai abincin bakin ta...ai kuwa yana kammalawa ya juyo da wata stern devilish look...Suna hade ido Yace pls ki cigaba dacin Abincin ki...

kamar zata ja abincin a tsakar kanta tafitar da shesheka...slowly ta sake kai spoon wanda ya taho da hawaye sosai...

Yaji tausayinta aransa da yasan batajin dadi ko kadan amma ya fuske yace take more of it.. ya fada ayayin da ta cigaba da jan lokaci kowanne sai tayi masa hawaye....

Tana gamawa ya karbe plate din ya mika wa uztaz tun kafin ya juyo ta saka masa hatsalallen ihu ni kar kamin wani Allura ya isheka haka tafada shaking in anger and hatred...

Yayi mata shiru sai da ya zare kan syringe din snn yace.. if u dont relax is going to pain u....

"I hate you....ta furta masa so weak kuma hatsale...

Yaja tsaki ya zauna ta gaban ta ya matso ta jikinsa ya danna mata ruwan allurar..

shikansa sai da yaji nauyin fitinannen kuka mai dauke da disasshen murya din data sauke masa har ransa ya ji tausayin ta sosai..

A fuska yay kamr bai damu ba musamman daya ga ta birkice tana ce masa maye, mugu..ta tsane shi Allah zai saka mata Her just wonder wann wata irin sakaltacciyar mace ce at this age tana masa kukan allura haushi ma tabashi as usual ko sannu baice mata ba ya mike.

Uztaz ne ya matso kusa da ita yanata bata baki sai kuka takeyi sosai..

Khaleel bai tsaya ba ya kwashi wasu pack din vitamins na saka cin Abinci ya bude ya juye mata rabi acikin hanyar ruwa daga nan yana kade hannunsa ya fice ya fita baiko kalle ta ba..

Dai dai bakin kofa wayarta ya fara ringing bata iya daukawa sabida kukan datakeyi da uztaz kawai doc Aseem din ya gana shiya gayamai komi daya faru.

Tun khaleel baikai ga motarsa ba dr Aseem din ya kirashi yanamai tambayarsa jikin halisan yace its okay Sir aita ci abincin yanzu..

Yy murmushi yace "meyasame ta toh take kuka?

Kansa ya sosa kadan snn yace sir mata fa na tsoron Allura, she is probably crying bcos of that. bacci zatayi insha Allah.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull