Kenza eBookz

Damuwata complete novel - Chapter 11

Damuwata complete novel - Chapter 11

Damuwata complete novel Chapter 11: Damuwata complete novel Chapter 11. "Dujengala kice in-law shi ne jarimin?"

3,370 words

"Dujengala kice in-law shi ne jarimin?"

Kauda kai na yi, ya sanya dariya.

"Sai da safenku Yaya."

"Aha mungode Habibu, agaida masu jegon kafin muzo."

"Zasuji."

"Allah kaika gida lafiya Kawulle."

Na furta masa cikin tsokana.

Duka ya kawomin na gofce ina dariya dan nima na sami sunar kiransa.

"Wannan yarinya zata haukatani fa, to na wuce dai."

"Da dai ka zauna neman magana."

Cikin dariya ya fice na kalli Mama ta nunamin d'akina "Tafi ki huta da safe zamuyi magana nasan son sanin inda Habibu ya san Aliyu kike son ji."

Da sauri na fad'a d'akina, ina jiyo dariyarta.

"Sannu da dawowa Aunty Deejah."

Idanu na ware jin sunar da Beebah ta ambatamin.

"Eh ke Auntynmu ce tunda Uncle Muhseen ya fad'a fagen yak'in nemna mallakan ruhinki."

Toilet na fad'a batare da na biye mata ba, dariyar danaji an kwashe da shi yasa na fito da sauri Bintu ce kwance saman katifa sam ban lura da ita ba.

"Ke ma kina bayansu Fanta ko?"

"Eh kuma ki sani har k'anwar Uncle ta Sami labari cikin satin nan zata shigo Kaduna may be time d'in mun wuce dan jibi kamar yanzu kowa na kwance saman gadonsa yana huce gajiya."

"Nikam me yasa kukeyimin haka ne? Yanzu kunsa zata zo idan ta sami labarin ba haka bane me zaku ce da ita?"

"Nufinki wancan yaron kike so wanda bai wuce sa'arki ba?"

"K'anina ne kin manta."

"To wallahi kada ki bashi lokacinki a banza da wofi domin baku dace ba sam."

Banza na yi da ita na koma toilet.

Har na kwanta na jiyo maganar Bintu.

"Deejah kada kiyi Wasa da damarki domin samun miji kamar Uncle Muhseen rabo ne, tun kafin kuyi nisa ki sallami Aliyu dan wallahi indai muna raye baki da miji sai Uncle Muhseen."

"To Baba da Mama."

"Zancen gaskiya ne dan nasan Baba da Mama suna ganin Uncle wanda ya mallaki komi bazasu amince su bawa wanda ke neman na siyan sutura ba."

"Kinga Bintu ki kyaleni inyi barci tam."

"Bazan bar kiba sai kin san waye Uncle."

Banza na yi da ita, Ina jin Beebah na dariya k'asa-kasa bisa alamu ita ta kunna wutan ta koma gefe.

"Ai kin shiga uku tunda Bintu ta ke yin lamarin fiye da kowa."

Tashi zaune na yi na zubawa Beebah idonu ta gyara zama cikin cewa.

"Ni da Bintu da Aunty Nafisa dakinmu d'aya. Fanta d'iyar k'anwar Momy ce. Safina da firdausi su kuma d'iyoyin yayyun Momy ce. Iyayenmu kansu had'e shi yasa muka taso da son juna dan duk gidan da mukaje ba'a nuna bambanci, abu d'aya muke."

"Da kyau."

Na ambata tare da komawa na kwanta.

"Kada ki yi mamakin yarda dukkanmu muke son ki auri Uncle sabida ke ce zaki iya zama da 'yar uwanmu ba cuta ba cutarwa."

"Ni kuma ta cutar da ni ko?"

"A'a fa, Uncle zai baki kariya fiye da tunaninki."

"Shi kenan na amince soyayyarsa amma bance zan auresa ba saboda zab'in Allah na ke kan nema."

"Masha Allah, yanzu kuwa zan sanar masa dan ya soma zuwa zance Kai tsaye kafin Malam Ali ya mallake zuciyarki."

Bance komi ba haka banji fad'uwar gaban da na ke ji ba dyik in anayimin zancen auren Uncle Muhseen.

Wayata ce ta yi k'ara na duba sak'o ya shigo.

"Ina godiya da wannan aminci."

Kallon Beebah na yi ta jinjinamin kai.

"Tukuicina kujerar Umrah a wannan Azimin ya tabbatarmin na can-canci hakan saboda na d'orashi akan hanyar gyarawa matarsa zama tare da yi masa jagorar mallakan tauraruwan taurari Nana Khadijatu."

Ware ido na yi. Ta tashi ta soma rawa cikin ambatar "Khadija haske ce a ko ina." Abinda ta yi ta ambata kenan Bintu na tayata, saida suka gaji sannan suna zube suna maida numfashi.

"Deejah Uncle maraya ne Babansa ya rasu tun yana d'an shekaru biyu. Mamansa ta raine shi na shekaru uku k'anin Babansa ya amshe shi lokacin yana da shekaru biyar kenan, kulawansa ya dawo hannunsa inda ya fuskanci k'alulabe da mafi aka sarin marayu ke fuskanta ko ince wad'anda suka taso ba tare da maifiyarsu ba. K'an warsa Hafsat mamansu ne d'aya, tana tare da k'anwar Mamanta a garin Abuja saka makon rasuwa da mahaifiyarsu ta yi sanadin haihuwar k'anin Hafsa wanda shina kwanarsa biyu a duniya ya bi mamnsa. Su biyu ne rak mamansu ta Bari wato Hajiya Madina.

Muna da dangartaka da Uncle dan sadda yazo neman auren aunty Nafisa aka gano mahaifin Mamansa abokin kakarmu ne, dan 'yar Maiduguri ce ita Babansa ne d'an Kaduna.

Numfashi na sauke cike da jin tausayin Uncle.

"Uncle yana da burin k'anwarsa ta zauna a gidansa amma halin Aunty Nafisa ya hanata zama, duk da bata dukanta bata zaginta amma fad'a da sanya aiki kawai sun isheta ko Fanta dan tana da hak'uri ne wallahi da tuni ta gudu."

Juya baya na yi sabida har ga Allah yanzu bana son ana ambatar sunar Aunty Nafisa a gabana.

"Muna da yak'innin idan kina tare da ita zata soma koyi da halinki na hak'uri da kirki har gidan Uncle ya zamo yarda yakeso wato jama'a su cika shi ana kaida kawo cikin kulawarsa."

"To Allah yaso hakan."

Na ambata a hankali.

"Amin."

"Idan momy ta sami labarin nan zatafi kowa jin dad'i domin tafi kowa sanin kishin Aunty Nafisa wanda idan taga abokiyar zamanta na yin abin alkhairi itama zata aikata fiye da nata musanman intaga Uncle na yabawa aikin 'yar uwan zamanta to zata zabura ta aikata ko dan ya yaba mata, kinga kenan anjefi tsun-tsu biyu da dutse d'aya ."

Numfashi na ja a hankali ina k'ara fahimtar dalilin da ya sanya su Beebah ke goyon bayan aurena da Uncle sabida halaiyan 'yar uwansu ya bak'anta ransu.

'Uhm ni dai gani ga Allah, ban san me ya zab'amin ba.'

Na ambata cikin raina, a fili kuwa na ce "Ya Allah ina fatan samun zab'inka mafi alkhairi a rayuwata."

"Insha Allah Uncle d'inmu zai zab'a miki."

Suka ambata a tare, ido kawai na zuba musu. Ina saurarensu sai ambatar halin karamcin Uncle sukeyi suna k'ara na-natawa.

A makare muka tashi saboda muka idar da sallar subahi barci muka koma. Mama ta kammala duk aikin gidan dan haka wanka mukayi muka karya na wuce Tahfiz a gaggauce dan lokacin shiga ajina ya kusa. Sadda na shigo gate ina kallon Aliyu daga nesa tsaye bakin wani aji amma ban nuna na gansa ba na shige ajin da zan soma da shi.

"Ba ko gaisuwa matar Ali."

Sak'on na karanta na maida wayar silent batare da na bashi amsa ba. Ina tsakiyan k'arin hadda ya shigo da sallama, yaran ne suka amsa masa nikam a zucci na amsa na cigaba da karatuna, tsaye ya yi yana bina da kallo dakatawa na yi na tura masa sak'on dan Allah ya fita, maimakon ya fita kamar yarda na nema sai ya tako zuwa gabana ya tsaya mik'ewa na yi ina kallon yaran na ce "Yau Malam Aliyu yazo tayamu karatu ya kamata kuyi masa wuri."

Dariya suka sanya, shima darawan ya yi ya tafi gefen wani yaro ya zauna.

"Oya ayi mana karatun."

Murmushi na yi na koma na zauna na cigaba da karatu amma duk sai naji na takura saboda yarda idanunsa ke kaina. Aya na sanya ma dubeshi kad'an sannan na ce "Dan Allah Malam ka k'arasa musu ni bari in tafi d'ayan ajin da na ke son yi masu gwaji."

Ban jira amsarshi ba na fice. Daga Ajin da na ke ina yiwo karatunsa cikin d'aga murya, murmushi na yi ta dokawa kawai ina yabawa k'aunata dana hango a idanunsa.

Koda lokacin tafiyana gida ya yi Aliyu na ajinsa dan haka baisan na wuce ba. Ina shiga gida saiga kiransa, d'auka na yi ya rufeni da tulin k'orafi akan tafiyata ban jirasa ya kawoni ba.

"Aliyu mu kame kanmu mu sani makaranta muke ba filin masoya ba, ka daina biyoni gaban d'alibaina kada su rainamu kasan sun soma girma tsaf zasu fahimci inda muka dosa, ka amince mu kasance tamkar bakomi tsakaninmu amma da zarar mun bar kamaranta mu nunawa juna k'au...

Sai kuma na yi shiru ina 'yar dariya.

"Uhm k'arasa mana Matar Ali."

Shiru na yi.

"Na amince da zancenki dear ko dan gudun sa'idanawa masu neman abin fad'a batare da ankasa da su ba."

"Nagode da fahimta."

"Ni ke da godiya, ki jirani bayan la'asar zanzo da sister na."

"Ok sai kunzo."

"Love you always Matana."

"Me too."

Dariyan da ya kyalkyale da shi yasa na datse kiran na kife fuskata a tafukan hannuna.

"Uwata kin dawo lafiya?"

Da sauri na d'ago Mama ce tsaye k'ofar kitchen, kallon da takeyimin ya tabbatarmin da ta ji wayar da na ke yi. Da gudu na kwasa zuwa d'akina. Dariyar Mama na jiyo har da tafa hannaye.

"Ikon Allah, wannan wani irin kunya Allah ya baki Uwata?"

Cukuikuye fuskata na yi da bedsheet, ina sauraren zantukan Mama. Duk yarda taso in tashi nak'i sai kawai ta fice tana dariya mai sauti. Nima dariya na sanya ganin yarda Mama ke farin ciki yafi komi sanyani nishad'i.

"Da alama Aliyu kai alkhairi ne a rayuwata."

Na furta a hankali.

"Uhm."

Beebah ta yi gyaran murya, harara na cilla mata ta kwashe da dariya cikin girgiza sumar kanta dake d'igan ruwa.

"Malama ina Yaya Abdallah?"

"Ya koma garinsu tun d'azun."

"Ayya bana nan bamu had'uba."

"Nima tun isowarsu har ya wuce bamu sake ganin juna ba."

"Saboda me ne?"

"Babu."

"Anya kin kyauta masa kenan? Ko ba dan alak'ar k'auna ba ai kya bashi kula dan zumunta."

"Deejah me kike so inyi masa? Ya zo naje mun gaisa na zauna cikin dangi yana hira da kowa bandani to akan me zan cusa kaina ya zo ya tozartani dan na hango take-takensa kenan."

"To Allah ya kyauta."

"Amin."

"Uncle yana ta kiranki, shin me yasa baki daga ba?"

"Tana silenta ne."

"To ki kirasa kafin ki kwanta dan na sanar masa da zaki kirashi idan kin dawo."

"Nikam kunyarsa na ke ji, please ki sanar masa na yi barci."

"Jibi kamar yanzu ina gadon Momyna, maga wanda zakiyiwa salo."

"Wayyo kewa zai kasheni."

"Ina kika san kewa, ai sai muntafi da aminiyarki."

"Kuna nufi Fanta daku zata wuce?"

"Insha Allah, amma zata dawo."

Kwalla naji sun cikomin na yi saurin juya mata baya.

"Mu muka matsa ta biyomu saboda ku sami fahimtar juna da Uncle batare da Aunty Nafisa ta sanya zargin cewa Fanta ce ke rura lamarin ba."

"Kuna ganin wannan matakin shi ne mafita?"

"Eh domin bazan b'oye miki ba hankalin 'yar uwanmu ya tashi duk yarda muke goyon bayan lamarin tabamu tausayi d'azun da ta ke kuka a gabanmu amma mun nuna mata Uncle mijin mace hud'u ne ta yi addu'a akan lamari shi yafi akan tada hankalinta, da alama ta d'auki nasihohinmu musanman na Safina saboda ita malama ce kamarki sannan Allah ya yi mata baiwar iya lwantarwa da mutum hankali."

"Uhm nidai dan girman Allah ku barni da Fanta."

"Kiyi hak'uri itama tana son kai ziyara taga dangi."

"Shi kenan Allah ya dawo da ita lafiya."

"Amin."

Wanka na shiga na d'auro alwallah na sallaci shafa'i da wutri na yi shirin barci. Kwanciya na yi cike da sake-saken yarda al'amuran rayuwata yasoma sauyawa da salo mai cike a bababen mamaki.

'Wai ni ce wacce ada maza ke k'in kulawa amma yanzu sun soma cajamin kwakwalwa.'

"Inkon Allah kenan."

Na ambata a fili.

"Sai ji da gani ba"

Na tsinkayi muryan Beebah ta amsamin.

Sai da safe na yi mata, itama ta shiga toilet tajima sannan ta fito bisa alamu wanka ta yi.

Tsakiyar dare na farka sakamakon jin motsin ana tab'amin k'ofa, gabana ya fad'i tuno rayuwata na baya wanda na ke gadin kaina a duk tsakiyar dare. Addu'a na soma ja inda ya taimakamin na samu kuzarin mik'ewa na nufi k'ofar.

Ina bud'ewa Mama ta fad'omin a jiki tana nunfarfashi tare da nunamin hanyar k'ofar d'akinta da yatsa dan takasa yin magana.

*TALLA.*

*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*

Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/25, 11:01 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona)

By Safiyya (Mrsjmoon)

E.W.F.

Page 13.

Rungumota na yi ina salati tare da janyota ciki na maida k'ofar na rufe, addu'a na soma tofa mata hankalina a tashe. Saukan fitar numfashinta da sauri da sauri ya tashi Beebah daga barci ta iso gabana tana jeromin tambayoyi ganin ban amsa mata ba sai addu'a na ke aikin tofawa Mama cikin sauri-sauri sai ta zubo ruwa a kofi ta zauna ta rik'e babban yatsar k'afar Mama da kyau ta soma tofa addu'a a ruwan hannunta, tana gama tofawa sai ta guntsa da fesa aikam ta ke Mama ta ja numfashi mai k'arfi, Beebah ta k'ara guntsan ruwan sai dai kafin ta fesa mata akaro da biyu tari ya sark'eta kofin da ruwan addu'ar ke ciki ya kufce a hannunta ya zube a k'asa. Sannu na yi ta jera mata har zuwa sadda tarin ya lafa ta matso muka cigaba da tofawa Mama addu'a. Tsawon rabin awa muna fama da Mama kafin mu samu ta dawo hayyacinta ta soma ambatar Hasbunallahu wal ni'imal wakil, da k'arfi ganin haka muma muka somabinta, zuwa wani lokaci sai ta rufe da salati. Gumi sai b'ulb'ulowa ya keyi daga sassan jikinta, gamin haka sai muka samu madai-daitan towel muka soma goge mata, lumshe idanu ta yi tana mai ambatar albarka a garemu. Bayan munga ta sani natsuwa sai muka kamata zuwa saman katifa, ta dubeni cikin tarin rauni ta ce "Uwata akwai damuwa a gidan nan, hak'ik'a da idanuna naga wani halitta mai kama da maciji na son hayomin gado shi ne ya firgitani wallahi ji na yi kamar zuciyata zata fito sabida tsoron halittar, tabbas da yazo da ajali da yanzu zuciyana ta buga na zamo gawa, kin koma marainiya na hak'ik'a."

"Mama kwanta ki huta gobe da safe sai muyi maganar kuma in Allah yaso kinfi k'arfi dik kan abin sharri daga jinsin mutum da aljan, insha Allah burinki sai ya cika a kaina k'asa bai rufe idanunki ba."

"Allah yaso hakan Uwata."

"Amin."

Muka amsa tare da Beebah.

Maganin ciwon kai ta nemi in bata ta sha, Beebah ta b'allo Boska d'aya Sudrex d'aya ta bata, tana sha bajimawa barci ya d'auketa cikin fitar murmushi mai cike da natsuwa.

Kasa komawa barci na yi sai na d'auro alwallah nasoma jera nafil-fili cikin kaiwa Allah kukana da ya karemu daga dukkan sharrin abin cutarwa na fili da b'oye, Beebah itama maramin baya ta yi, haka muka kwana addu'o'i. Bayan mun idar da sallar Subahi muka shiga d'akin Mama a tsorace bakinmu d'auke da addu'a, bamuga komi ba, Beebah ta ce mu bincika ko ina amma Mama ta hana ta ce mai cire maciji zaizo ya cire shi.

Hak'ik'a abin ya tab'a min zuciya ganin yarda Mama ta koma kamar yarinya domin da taji motsi zata zabura ta k'ank'ameni ko Beebah, sukalewa na yi na shiga bayin waje na kulle kaina na yi ta kuka cikin rashin fitar sauti, bayan na rar-rashi kaina na fito cikin k'ok'arin sanya wal-wala a fusakata gudun sake dagulawa Mama lissafi. Ko abinci ba wanda ya ci dan ko abin karyawa bamu sami damar had'awa ba saboda halin da mukaga Mama ya gama kashe Mana jiki domin da gari ya yi haske ta garas sai ta rik'a sunbatu tamkar wacce brain d'inta ya ke son tab'uwa, da mun had'a ido hawaye ke zubomin amma bana bari ta gani Beebah ce ta fahimta tasoma yimin nasiha a hankali gudun kada Mama taji ta k'ara bircikewa. Haka muka kasance da Mama mun kasa dawo da ita asalin natsuwarta.

Da hantsi mai cire maciji yazo ya gama hayak'insa da bincikensa baiga komi ba ya tafi, Beebah ce ta sanarwa da Uncle halin da ake ciki yana zuwa bai jira komi ba ya kira wani Malami da d'alibansa suka zauna danyin saukan alqur'anin a gidan, mu kuma ya ce mu tafi da Mama asibiti ganin yarda ta ke yin abun tamkar rud'ad'd'iyar tsohuwa, shima lamarin ya firgitashi.

Kwatanta damuwan dana shiga ba mai misaltuwa ba ce, na yi kuka har na ji zuciyata na son samun matsala ta hanyar jin ina fizgar numfashi da kyar tare da jin tanayimin zugi, kan dole na rarrashi kaina da kaina tunda nak'i jin ban bakin su Beebah.

Babban DAMUWATA shi ne na rashin sanin halin da Mamana ke ciki tsawon awanni shida da muka kawaota domin mun kawota da mintoci goma sha biyar Likitoci suka shige da ita wani d'aki sai dai inga sun fito sun shiga ba labarin komi, lamarin ya k'ara d'agamin hankali kenan nakasa sauraren ban bakin kowa hatta kuwa da Uncle domin gani na ke basu san kalan damuwarta da na ke ciki ba ne shi yasa suke cewa na daina kuka dan inda banyi kukan ba tabbas da nima ina kwance a gadon majinyata.

Bayan na gabatar da sallar magriba na dawo bak'in k'ofar da ka saka Mama na kife fuskata a jikin bangon na kuma fashewa da kuka mara sauti saboda tuni muryata ta dushe.

"Dan girman Allah kiyi hak'uri Aminiyata, ki tuna falalar mai yarda da k'addara ta khairan ko kishiyarta, kina da sani akansa shin me yasa bazaki zamo cikin masu mik'a lamuransu ga Ubangijin da baya barci balle gyan-gyad'i ba? Ki yi hak'uri irin wacce Allah ya umurci bayinsa mumunai da su aikata idan jarabawar rayuwa ta riskesu, ki sani Allah da ya jarabci Mama da lalura nan ya fiki sonta sannan faruwan hakan alamun tana cikin bayinsa salihai ne wanda ke dorawa cuta domin gwada imaninsu tare da shafewar zunubai."

Rungume Fanta ya yi tsan-tsan ina kuka mai ciccira.

"Insha Allah Mama zata warke jinkirin bayyanar halin da ta ke ciki alkhairi zai zamo biy jahiy Nabiyyi S.A.W."

"Allah ya so hakan, nagode sosai Aminiyata."

Na ambata batare da tunanin tajiyoni ba saboda yarda muryan ke fita can a mak'oshina.

"Ku tafi da ita gida ta huta."

Na tsinkayi muryan Uncle daf da ni.

Da sauri na juyo na rik'o hannunsa batare da tunanin komi ba saboda natsuwana ya yi balaguro.

"A'a Uncle ba zan iya hutawa ba alhalin Mamana na cikin wannan halin, ka barni har zuwa sadda zan san halin da ta ke ciki."

"Wani hali ta ke ciki?"

Ya cillomin tambayar tamkar bai san komi da ke faruwa ba.

Maimakon amsa masa sai na saki hannunsa na koma jikin Beebah na kwantar da kaina a kafad'arta na fashewa da sabon kuka.

"Beebah ku tafi da ita gida na ce."

"Ba zanje ba!."

Na furta da k'arfi.

"A haka kike son Mama ta yi ido biyu da ke? Kin koma tamkar wacce ta yi amai da zawo, oya ki tafi gida ki huta wannan shi ne umurnina na k'arshe akanki."

Ban sa ke magana ba kuma ban daina kuka ba, hawaye na bin cheek d'ina tamkar an bud'e famfo na motsa masa kai alamun cika umurninsa. Jan hannuna Bintu ta yi na kalleta naga itama kukan ta ke yi.

"Kunga idan kuka zaku koma kunayi banga amfanin had'aku da ita ba."

"Sorry Uncle mun bari."

Fanta ta ambata cikin muryan kuka.

"Ku tabbatar da ta ci abincin kafin in iso."

"To."

Beebah ta amsa a hankali.

"Yaya me yasa bazaka barta ta shiga ta ganta ba? Tana fa cikin yanayi mai kyau itama burinta ta sanya d'iyarta a ido."

Wata murya mai sanyi naji ya ambaci haka, ai banjira amsawan Uncle ba na juyo da gudu caraf Uncle ya kamani ya matse hannuna gam.

Runtse ido na yi saboda da yarda rik'on ya ratsa sassan jikina.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull