Kenza eBookz

Damuwata complete novel - Chapter 12

Damuwata complete novel - Chapter 12

Damuwata complete novel Chapter 12: Damuwata complete novel Chapter 12. "Ki tafi gida idan kin dawo zaki ganta."

3,311 words

"Ki tafi gida idan kin dawo zaki ganta."

"Dan soyayyarka da Ma'aikin Allah ka barni inga halin da Mamana ke ciki kafin in tafi."

Sakina ya yi wani hannu mai mugun d'umi sama dana Uncle ya kamani haka nasoma binsa tamkar jela a k'ofar wani d'aki ya tsaya ya juyamin baya dama banga fuskansa ba, ban kuma damu da sai nagani ba.

"Ki shiga tana ciki amma idan kika d'aga mata hankali da wannan kukan naki tabbas da kaina zan fito da ke."

Motsa kai na yi tare da tura k'ofar d'akin na fad'a ciki da sauri dan gani na ke tamkar Uncle zai hanani duk da baibiyo bayanmu ba.

Mama ce zaune saman gado, nurse na bata tea a baki. Da sar-sarfa na isa bakin gadon sai kuma na tsaya tsak ina sauke numfashi hawaye na bin kumatuna.

"Uwata taho kusa naji d'uminki."

Da sauri na k'arisa na zauna tare da mannuwa a jikinta.

"Mamana in na rasaki nima binki zanyi."

"Ki godewa Allah shi ne abin buk'ata kafin furta komi Uwata."

"Alhamdulillah ala kulli halin."

"Masha Allah."

"Mamana ta ya...

"Kiyi hak'uri da duk kan tambayoyinki yanzu tana cikin hutu ne ba'asonta da yawar magana."

Motsawa nurse din kai na yi ta murmusa tare da mik'amin kofin tea d'in.

"K'arasa bata ina son gabatar da sallah."

"To."

Na amsa tare da komowa inda ta tashi na zauna. Da ido muke magana da Mama muna saukewa juna murmushi. Bayan ta gama shan tea d'in ta kwanta ina rik'e da hannunta barci ya d'auketa wanda nagano anyi mata allurar barci ne kafin in shigo.

"Taho ku tafi suna jiranki."

Idanu na zuba masa yana kama da Uncle sosai tamkar 'yan biyu sai dai wannan yafi Uncle jiki da tsawo domin shi irin mutanen nan masu girman jiki yayin da Uncle ya ke cikin matsakaita. Duk a d'an kallon dana k'are masa na gano ba wani mai shekaru ba ne girman jikin ne kawai.

"Idan kin gama kallon munin nawa sai ki sanarmin da abinda ya fi burgeki ko baki tsoro a halittana."

Ware idanu na yi baki bud'e.

"Dalla wuce ki bani wuri mummuna kawai, wallahi Yaya na cikin wahala da yake sonki domin ba abinda zakiyi masa sai shirme da uban kallo kamar yar daji, wata k'ilama gara sakaryan matarsa na gida da ke."

Juyawa na yi jiki a sanyaye na sumbaci goshin Mama bayan na tofa mata addu'a, nazo na wuce ta gefensa kaina sunkuye.

"Haramun ne saka turare mai janyo hankali dan haka ki kiyaye saboda cika sharud'an addininki."

Ban kula zancensa ba na yi gaba ina maijin haushinsa haka nan naji baimin ba.

Naso tambayar su Fanta d'an fiti nan mai kama da Uncle amma gudun kada su juyamin zancen da tsokana sai na tsuke bakina sai dai kalamansa na k'arshe sai amsa kuwwa sukeyumin a kunnuwa domin ban saka turare ba sam amma dan neman magana ya ke yimin wa'azi, siririn tsaki na ja wanda nikad'ai najiyo kayana. Har muka isa gida bandaina zantukan zucci.

Cikin sakin fusaka na yo wanka tare da cin abinci wanda muka siyo a hanya. Sai tsokanata Fanta keyi da nuna irin kukan da na yi Bintu na karemin.

"Ki kyaleta Bintu ai itama ta yi kukan."

"Aikam kowa ya yi kuka hatta da aunty Nafisa ta shiga damuwa sadda ta sami labari."

"Anya Sister Safina hakan ne kuwa?"

"Gara dai ki tambayeta kam domin mun san ta shiga damuwa ne saboda mijinta na tare da ke."

"Kai Sister Beebah wai me yasa kike yin haka ne?"

"Safina k'arya ko da wasa haramun ne, kinsan da haka to me zaisa ki fad'a abinda ba haka ba ne? Ko Deejah ta aminci Aunty Nafisa ta shiga damuwa saboda ciwon Mama na tabbata a fatar baki ne amma a cikin zuciyarta ba aminta ta yi ba domin zan iya cewa tafimu sanin halin yar uwarmu saboda nuna mata halayarta da ta gamayi."

"Haka ne sister Beebah nima ban san me ya janyo na kama sunarta Aunty Nafisa ba."

"Is ok Sister Safina an kulle babin yanzu kuzo muyi addu'ar dorewar samun lafiya ga Mama."

Firdausi ta ambata.

Zama mukayi a carpet Beebah ta jero addu'a tana gamawa na soma ina gamawa Safina ta d'auka haka mukayi har zuwa kan Fanta, Firdausi da Bintu sannan muka shafa, bayan munyi tawasaali da addu'o'in akan Allah ya bawa Mama lafiya mai d'orewa.

"Gobe zaku wuce gida ko?"

Na tambayesu cike da jimami.

"Sai munji daga Uncle."

Bintu ta amsamin.

"Uhm nikam zaku barni da kewa."

"Fanta na tare da ke dan Uncle ya soke tafiyarta tare da mu saboda ya ce kewar zaiyi miki yawa."

"Allah sarki Uncle, mutumin kirki."

"Kina son shi ko?"

Kallon Fanta na yi kawai batare da na ce komi ba."

"Fanta shiru alamun amincewa ne."

Bintu ta amta cikin kannemin ido.

Murmushi na yi kawai domin har yanzu damuwar laluran Mama bai sakeni ba.

"Muna sonki tsakani da Allah Deejah shi yasa bamu taya yar uwarmu kishi ba saboda mun san kyawun halinki bazaki tab'a cutar mana da jini ba, muna bayan aurenki da Uncle d'ari-bisa d'ari."

Safina ta furta hakan cikin sanyin murya mai cike da natsuwa abin da ya janyo shigar zantukan cikin kowani kofa na jikina kenan.

"Kuma muna fatan itama bazata cutar da ke ba saboda abin da ta tsana a rayuwarta shi ne bin bokaye da mugayen malamai sannan masifarta zamu tayaki da addu'a Allah ya sanya sanyi a lamarin ku zamo abin alfaharin mijinku, inuwa mai kore masa dukkan damuwa."

Kallon Beebah na yi sadda ta rufe baki, kwalla ne suka cikomin saboda kalamansu ita da Safina sun jefani cikin wani hali wanda na ke hango bijirewa auren Uncle tamkar watsa musu k'asa a idanu ne tare da yi masa butulci.

'Mama da ku kun sakani a tsakiya amma bakomi na amince hakan kaddarata ce, Allah ya baki ikon faranta muku tamkat yarda ku ke kan farantamin.'

"K'awata insha Allah zakiyi alfahari da wannan auren, ina ji ajikina jinkirinki alkhairi ne tunda gashi tashi d'aya Allah ya baki miji d'aya tamkar da dubu, irin Uncle. "

"Allah ya amince hakan Fanta"

Na ambata a hankali.

"Amin."

Suka amsa a tare cike da wal-wala.

"Hak'ik'a bazan manta da samuwarku cikin rayuwata ba, kun ciremin kokwanton dana ke ciki na ganin ko bak'in jini na ke da shi da k'awaye basa hurda da ni."

Dariya suka kyal-kyale da shi jin kalamaina cikin k'ok'arin fitar da murya.

Sallaman Uncle yasa suka natsu ya daga labulen ya ce "Ki taho muje ku kuma ku kwana a gidan sabida kada abarshi ba kowa."

Suka amsa da to cike da ladabi, na yi musu sallama muka fice.

"Baba ya sani kuwa?"

Na cillowa Uncle tambayar sadda muka hau titi.

"Eh, yanzu haka a can na baroshi tare da matansa."

"Uncle ance tana buk'atar hutu kada su dameta da hayaniya."

"Sa'ad zai kula da lamarin."

"Likita ne shi?"

"A'a."

Shiru na yi ina hasko surar mai kama da shi wanda nabawa suna da d'an fitina. Runtse ido na yi da sauri hasko matar da zai aura wacce zatayi aiki da masifarsa tamkar yarda Mama ke kan hak'uri da sababin Baba.

"Aikam ta gamu da aiki babba."

"Wa ne?"

Kama baki na yi jin a she zancen zuccin ya fito fili ban sani ba.

Gyaran murya ya yi ganin banda niyyar amsa masa.

"Mama jinnu suka bata tsoro amma masu karatu sun saita lamarin dan malamin ya sanarmin wai turensu akayi mata sai akayi dacen ta rik'e azkar domin anso ta haukace ne Allah ya bata kariya sai abin ya tsaya a rud'ewa na d'an lokaci."

"Allah ya k'ara karemu."

"Amin."

Zuwa can na kuma jin muryan Uncle.

"Su kuma Likitoci sunce ta kamu da hawan jiki shima sunyi nasarar saita komi sai ki dage da yi mata addu'ar samun kariya har da ke kanki, gobe Malamin zaizo dubata a Asibiti zaiyi magana da ke dan na ce ya taimaka ya baki addu'o'i tare da wasu nafil-fili saboda na fahimci Baba na da sakaci akan bawa iyalansa kariya daga miyagun lamura duk kuwa da matsayinsa na nasanin ilmin addini."

"Uncle nagode sosai Allah ya biyaka da khairan."

"Amin."

"Banso sanar miki ba amma ya kamata ki ji ne sannan banso Mama ta ji, lamarin ya tsaya tsanina da ke da kuma Baba da ya furta kalamin."

"Me Baba ya ambata maka Uncle?"

"Idan Mama ta dawo gida zan sanar miki."

Shiru na yi amma a zahiri naso jin abinda Baba ya ambata masa.

"Kina son saurayinki Aliyu ko?"

Da sauri na kalle shi ya gyad'an kai sai na girgiza masa nawa murmushi ya yi mai sauti na juya fuskata gefe ina jin fad'uwar gaba saboda zuciyata Aliyu ta ke so domin shi ne first love d'ina, shi ne mutumin da bazan tab'a mantawa da shi ba wanda ya kawo iyakar DAMUWATA na rashin masoyi.

'Ba zan iya furtawa Uncle ina son Aliyu ba.'

"Ina kuma rok'on a bani gurbi ko da d'an mitsi-tsine wanda idan na kira waya a amsa min ko da ba'a bani damar soma zuwa zance ba."

Nok'e kai na yi ya ja jelar kitsona da ya fito waje sai na tura kai tsakanin cinyoyina. Sai da na ji ya kashe motar sannan na d'ago na tsirawa harabar Asibitin ido.

"Sarkin kunya muje ko?"

Wani kunuyar ne ya sa ke kamani, ficewa ya yi yana 'yar dariya, nima dariyar na sanya amma a tak"aice wanda ban bari Uncle ya jiyo ba, saida ya k'wan-k'wasamin galass sannan na fito ina nok'e kai.

"Nana Khadijatu sarkin kunya, Allah ya yi miki ludifin da ya tanadar masu kunya wato ya k'ara wadata k'irjinki da Imani mara iyaka."

"Amin ya rabbi "

*Masoya kunsan tafiyata a hankali ne, duk wanda ya ke bin books d'ina zai tabbatar da hakan, bana rushing haka bana yanke labari ko aya yake so dan Allah ku cigaba da bina a yarda na tsara labarin domin bazan yanke ba haka ba zan tafi da gudu ba dan tafiyar mai dogon zango ne gami da fad'i, nasan kun fahimci hakan tun a shafin farko na labarin, masu k'osawa da jin asalin Deejah kada su damu lokaci dai fad'in Mama Hurera. A dukkan komi a kwai sanadi to sanadin asan Deejah bai zo ba, aci gaba da gashi fans. Allah ya k'ara mana kwarin idanu, amin.*

*TALLA.*

*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*

Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/26, 10:33 PM] 💘: DAMUWATA BY MRSJMOON

E.W.F.

Page 14.

A tare muka jera zuwa cikin asibitin duk kuwa da yarda naso ya yi gaba na biyo bayarsa ya k'i. D'akin ba kowa sai wata nurse domin na yi zaton zan sami su Baba a ciki. Nurse d'in na ganin mun shigo ta mik'e ta fice, na matsa ina lek'en fuskan Mama wacce har lokacin barci ta ke yi, a kwana da yini har ta rame sosai sai dogon hancinta tare da fuakanta suka k'ara tsayi, haske kam wannan ba'a magana domin sai ta koma tamkar balarabiya wanda da ganinsa kasan bana lafiya ba ne. Sumba na sauke mata a goshi ina maida kwallan da ke neman zubomin.

"Ya rabbi ba dan halina ba ka bawa baiwarka lafiya alfarman Annabin karfo da k'arshe."

"Amin ya rabbi, insha Allah zata sami sauk'i burina ki cire damuwa domin ita kanta bazata so ta farka ta ganki cikin yanayi mara kyau ba."

"To Uncle zanyi k'ok'arin cirewa."

"Hakan ya kamata."

Shiru ya ratsa na minti biyu zuwa uku.

"Da alama wannan d'an ka iyan bai bar kowa ya shigo ba sai Malam."

Uncle ya ambata yana waige-waige kamar mai neman wani abu.

"Har shi ban bari ba."

Muryan d'an fitinan ya ratso, na juyo da sauri na tsira masa ido ya sanja sutura zuwa manyan kaya akan d'azun da ya ke sanye da k'anana.

"Kai wallahi Brother over acting d'in ka ne wata rana ke sanya mu b'ata da kai, yanzu har mijin nata ka hana shigowa ya ganta? To me kenan kayi fisabilillahi?"

"Eh fa har shi d'in banbari ba saboda kiyaye dokan Likita kuma a gabansu ya zo ya kuma tabbatar musu da kada wanda ya shiga ko waye nata."

"Wannan plan d'inka ne Brother domin nafi kowa sanin waye kai, inaga makaranta zaka koma ka zamo Likita akan Engineer tunda ka shiga rigarsu ta zartar da hukuncin da ko su basa yinsa wato hana murarrami ganin halalinsa."

Dariya ya fashe da shi yana rawa da kai na kuma zuba masa ido ina kallon dimful nasa da suka lotsa duka biyun.

"Yaya wallahi na yarda kafi kowa sanin halina shi yasa Abba ke had'ani da kai dan gano gaskiyan abinda na b'oye a ruhina."

"Ba dai ka kyauta ba Brother, a ce har mijinta ka hana shigowa ganin iyalinsa, haba dan Allah me yasa wata rana lamuranka baka sanya tunani cikinsa?"

"Kaima zaka fita idan ka cigaba da mita."

"Au har da ni?"

"Eh har dama Matarka mai kallon tsiya kamar goyon k'auyawa."

Uncle ya kalleni na juya baya ina mai maijin kunya.

"Kaga Brother zanci gidanku in ka ce zaka sanyawa iyalina ido."

"To ka sanar mata ban son kallo in ba haka ba zan tsire mata idanu sai ka zamo d'an jagora."

"Amsa naka na ce Sa'ad."

Jin Uncle ya ambaci sunarsa yasa na juyo da sauri na kuma tsira masa ido kamar mai son gano tawayarsa.

'Dama shi ne Sa'ad d'in?'

"Khadijatu meet my blood brother Sa'ad."

Maganar Uncle ya katsemin zancen zucci, kauda kai gefe na yi tamkar banji me ya ce ba saida ya sa ke mai-maitawa.

"Ok, ina yini?"

Na furta ina kuma kallon cikin idanunsa.

"Fine mai kallo k'urillah."

Murmushi na yi dan nafahimci yana da son raha kuma shima ya tsani kallo kamar yarda na tsana amma sai gashi yau ina yi har ana sanarmin da ba'aso lamarin da ya zamo karan farko cikin rayuwata.

"Kaga Brother zan sanya Abba ya yi maka aure da yar daji mai tallan Nono in har baka daina takurawa iyalina ba."

"Wallahi na bari Yaya domin ban shirya kashe 'yar mutane ba, good night, iyalin big brother Allah tashemu lafiya.."

Ya fice da sauri, kallon Uncle na yi ya girgiza kai tare da janyo kujera ya nunamin da yatsa na zauna ya dawo bayana ya dafa kujerar na kalleshi ya jinjinamin kai tare da cewa.

"Kinga na kori mai takura miki cikin ruwan sanyi."

Shiru na yi tare da kallon hawa da saukan numfashin Mama.

"Alamun ta samu lafiya kenan insha Allah wani abin cutarwa ya bar k'ara shigowa gidanku balle ya nemi tab'a ku."

"Allah ya amince hakan Uncle."

"Amin iyalina."

Murmushi mai sauti na yi saboda tun d'azun sunar ke bani dariya.

"Insha Allah ke iyalina ne Khadijatu."

"Uncle ka tafi gida kaga dare ya soma yi."

Na sauya akalar maganar saboda yarda ke bani kunya.

"Tare zamu kwana."

Idanu waje na ke kallonsa.

"Ko tun yanzu kina son nunamin Maman ke kad'ai ke da ita?"

"A'a fa kawai hakan bai kamata ba ne dubi da kana da iyali kuma na tabbata suna can suna dakon dawowar ka musanman ganin baka saba kaiwa dare a waje ba."

"Sun san inda na ke to ba damuwa."

"Uncle dan Allah ka tafi kada fa ka zamo mara adalci tun ba'ayi nisan zango ba."

"Oh da haka Kuma fa, nagode da tunatarwa, na tafi ki kula da kanki tare da Mama dan Allah."

Kai na motsa ina kallon fuskansa ya yi da ya ke tafiya da baya da baya saida ya kai bakin k'ofa ya d'agamin hannu cikin cewa "Good night Iyalina."

Da kallo na raka bayarsa ina hasko wal-walar da ke kwance saman fuskansa abinda ya sanyani murmusawa tare da jin sanyi na shiga cikin ma'adanar halittar zuciyana.

"Uhm Uncle manya, sam baya duba girmansa sai ya yi tayimin abinda matasan samari ke yiwa 'yan mata."

'Shi ne So wanda ake kira mai maida tsoho yaro.'

"Aikam in haka ne to So babban kalubale ne a cikin rayuwar bil'adam, tunda yana maida mai natsuwa zuwa kishiyarta."

'Ke dai Deejah ki taka a sannu ka da reshe ya juye da mujiya.'

Idanu na zaro ina jinjina amsan da zuciyata ta bani. Gyara zama na yi cikin k'ok'arin kauda tunanin tun ban soma zamowa mahaukaciya ba. Sai dai abin mamaki fuskan Uncle da na d'an fitina su ne ke tamin gizo a idanu duka na kaiwa goshina ta ke na saki yar k'ara ina liliya wurin saboda zafin da na ji.

Cool music na jiyo nesa da ni mai taken soyayya, inda wayar ke haske na tsirawa ido saboda tun daren jiya rabona da ita.

"Uncle yazomin da ita kenan ko wa?"

Ringing wayar ta kuma na tafi da sauri na d'auka duk kuwa da bak'uwar number ce. Sallama na yi maimakon a amsa sai saukar ajiyar zuciya akayi tare da datse kiran baki d'aya.

"Wa ye?"

Ganin zan sanyawa kaina ciwo akan son gano ko waye sai na watsar da lamarin na koma gaban Mama na zauna na tsirawa hawa da saukan numfashinta idanu tamkar mai irgawa. Addu'a na yi ta karantowa Ina tofa mata zuwa wani lokaci barci ya soma kamani na tashi na kulle k'ofar tare da tofe ko wani sak'o na d'akin da Ayatul kursiyu na haye gado na kwantar da fuskata a kirjin Mama ba jimawa barci ya d'auke ni.

*** Uncle Muhseen ko da ya isa gida bai shiga gidansa ba a k'ofar gidan su Deejah ya tsaya ya kira wayar Beebah bata daga ba ya nemi na Bintu a kashe , sai da ya kira duka wayoyinsu duk ba wanda ya yi dacen an d'aga, fitowa ya yi ya tura k'ofar gidan ta bud'e ya yi jim saboda tunaninsa a kulle zai sami k'ofar. Hasko shi akayi da filita mai mugun haske ya kare fuskansa hucin duka ya jiyo ya sunkuya da sauri hakan ya yabawa mutumin damar ficewa gidan a guje bayansa Uncle ya biyo amma ya nemesa k'asa ko sama ya rasa, kirjinsa na dukan uku-uku ya nufi cikin gidan, d'akin Deejah ya shiga ya samesu suna ta barci ajiyar zuciya ya sauke ganin babu alamun an tab'a su, ya fito waje yana haskawa da fitilar wayarsa buhunan waken suya ya ciki karo da buhunan waken suya an fito da su an jera.

"Ikon Allah wato barawo ne ya shigo sata, to wa ya bud'e masa gidan? Domin na tabbatar su Bintu sun kulle gidan tunda suka kwanta barci."

Komawa d'akin ya yi dai-dai lokacin Fanta ta tashi zatayi fitsari ganinsa saida ta tsorata dan batayi zaton ganin mutum ba, kiranta ya yi da hannu suka fito waje saida suka kai zaure ya ce "Kulle gidan ki tofa addu'a na shigo duba ku ne."

"To Uncle amma ta ya ka shigo alhalin mun kulle k'ofa?"

"Nima abude na gansa shi yasa na shigo duba ku."

"A bud'e kuma?"

"Kinga kulle ki tafi ki kwanta securities zasu zo gadinku insha Allah bakomi sai khairan."

"To Uncle saida safe."

"Ok mu kwana lafiya."

Yana tsaye ta kulle gidan shi kuma ya kira waya kimanin mintoci goma shabiyar 'yan sanda uku suka zo a mashin sun jima suna magana kafin ya barsu ya shiga motarsa zuwa gidansa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull