Kenza eBookz

Damuwata complete novel - Chapter 15

Damuwata complete novel - Chapter 15

Damuwata complete novel Chapter 15: Damuwata complete novel Chapter 15. "Kinga Hurera ki fita idona in rufe."

3,374 words

"Kinga Hurera ki fita idona in rufe."

"Allah baka hak'uri amma ka sani ba zan tab'a hararan naka mahaifan ba."

Tana ambatar haka ta juya masa baya tana mai ambaton sunar Allah dan samun rinjaye akan zuciyarta domin kallon da ya raka Baba Umaru da shi ya sosa ranta.

"Ke! fice ki bamu wuri munafuka banza kawai, 'yar rahoto."

Da sauri Fanta ta fice tana sharan hawaye dan tana kwance gefen Deejah.

"Hurera kin san Allah na kara ganin Alhaji Muhseen a Asibitin nan sai ranki ya b'aci."

"Malam wai me kake nufi ne? Yanzu Uwata na kwance tamkar gawa amma ka kasa yi mata sannu da jiki balle addu'a amatsayinka na Malamin addini?"

"Uwanki kika ce ko uwata?"

"Tawa ce ba taka ba."

"To sai ki tsukemin bakinki mai kama da Asusu ki saurari kashedina wanda ke makwafin wajibi a bishi in ana son ganin dai-dai."

"Malam dan Allah ka tafi kaina ya somin ciwo."

"Yanzu kika soma ganin ciwon kai in dai bazaki bi abinda na ke so ba."

"Me kake nufi?"

"Abin da tunaninki ya baki."

"Kai ne sanadin ciwo na kenan?"

"Wannan kuma kanki akeji nidai na sanar miki kada Alhaji Muhseen ya sake shigamin lamarin iyali."

"Yanzu kuwa yasoma shiga saboda wata rana surukinka ne shi."

"Au Allah?"

"Insha Allah."

"Zamuga ni."

"Insha Allah khairan gamu gani."

"Shi kenan Hurera ki nunawa duniya ban isa da ke ba kinji?"

"Malam kayi nazari domin wallahi Alhaji Muhseen mutumin kirki ne, kai shaida ne domin kafin zuwar lokacin nan kasha sanarmin da cewa baka tab'a ganin mai kud'i mara girman kai da sanin darajan makwafci irin shi ba."

"Au saboda yana da arziki shi yasa kike son ya auri Uwani?"

Shiru Mama ta yi bata amsa ba.

"Shi ne irin mijin da kikeyi mata addu'ar samu kenan?"

Ya furta cikin cillowa Mama kallon banza.

"Eh."

Ta ambata kai tsaye.

"To ina tayata murna."

Kafin Mama ta san abin cewa ya buga babban rigarsa ya fice.

Dafe goshinta ta yi saboda jiri da ta soma gani. Ba dan Fanta ta shigo ba tabbas da fad'owa k'asa zatayi daga saman kujerar da ta ke zaune. Cikin sa'a Nurse ta shigo ita ta taimwa Fanta suka dorata gefen gadon Deejah, cikin gaggawa aka kawo wani dago d'akin aka maidata kansa, Likitoci biyu suka rufu kanta, cikin mintoci da basu gaza goma ba ta samu barci.

Fad'a Dr. jalal ke yi tamkar zai ari baki a k'arshe ya bada umurnin kada a sake barin Baba shigo masa Asibiti, har masu gadi ya sanarwa wannan kashedi.

*** Kamar yarda Malam Isuhu ya ambata bayan sallar la'asar ya iso gidan Uncle ya fito suka shiga cikin gidan su Deejah suka raba Qur'ani har da Uncle suka soma karatu da ya ke suna da yawa awa d'aya da rabi suka kammala suka soma jero addu'a d'aya bayan d'aya suna daf da kammalawa Baba ya fad'o gidan afujan-jan. Duk yarda yaso yin tijara kasawa ya yi darajar gamin Al-qur'ani sai ya sami kansa da zama aka shafa addu'ar da shi. Kallon da Malam Isuhu keyi masa ne ya yasa jikinsa k'ara yin sanyi.

Uncle ne ya mik'awa Malam hannu sukayi musabaha tare da mik'a godiya, ya dubi Baba ya russuna cikin ban girma ya gaisar da shi ganin karramashin da Uncle ya yi sai ya saki rai ya soma washe bakin dole.

Haka d'aliban suka soma gaisar junarsu ta hanyar musabaha daga k'arshe suka russunawa suka gaida Malaminsu da su Uncle, daga nan suka fice gidan ya rage saura su uku.

"Malam Yusuf ga mai gidan nan ni albarkacin makwaftaka ya sa na jagoranci lamarin."

"Malam Hadi kai ne maigidan Hajiya?"

"Eh, Hurera ba, ai bataje Hajji ba Malam."

"Inda rai da rabo Baba."

Uncle ya mabata cikin murmushi.

Tsaki Baba ya ja ya juya zai fice sai dai maganar Malam Isuhu ya dakatar da shi ya juyo a hanzarce.

"Me ka ce?"

"Cewa na yi na kudiri aniyar maidawa wanda ke son cutar da Hajiya aniyarsa."

"Haba Malam Isuhu kana masanin addini amma kana son saka sharri da sharri, ka da fa kamanta yin hakan d'aukan zunubi ne domin ba lallai ne ya sauka kan wanda ya aikata d'in ba."

"Idan na aikata tabbas sai ya sauka kan wanda ya yi tare da wanda ya yi sanadiin aiki."

"Kuma dai?"

"Eh, saboda rama mugunta ga macuci ba laifi ba ne."

"Kagane Malam Isuhu mubar maganar zanzo gida na sameka sai muyi maganar anatse mai cike da fahimtar juna."

Kallon k'urillah Malam Isuhu ya kafeshi da shi sai kuma ya murmusa tare da motsa kai ya kalli Uncle ya ce "Insha Allah sauka na k'arshe Malam Hadi zai jagoranta shi da d'alibansa."

"Malam da ka cikashe aikinka kawai."

"Alhaji ai tare dani za'a yi har da kai tamkar dai yarda mukayi wannan tare manufata shima Malam Hadi ya kamata ya taimaka da irin nasa baiwar tunda shi ne jigon gidan."

"Haka ne, to Allah ya kaimu lokacin."

"Amin."

Uncle ya amsa Baba kam kai ya wuya gefe zuciyarsa tamkar wuta saboda takaicin ya sa tijarar da ya zo da shi.

Sake yin musabaha da Baba Malam Isuhu ya yi Uncle ya rufa masa baya suka bar Baba tsaye tamkar an dasashi.

"Ya kamata in san inda kaina keyimin ciwo tun kafin gwad'o ya yi min k'afa."

Baba ya ambata cikin zare idanu, ganin Uncle ya dawo sai ya dai-daita natsuwarsa tare dajin wani kalan tak'ama ya ziyarce shi.

"Baba dan Allah kayi hak'uri akan laifin dana aikata maka na shiga lamarin iyalinka kai tsaye batare da na nemi izininka ba, hakan ya faru ne saboda halin dana ganta a ciki wanda tunanin nemanka ya b'acemin sai bayan na kaita Asibiti amma insha Allah hakan ba zai sake faruba, ka ya femin dan Allah."

Shiru ya yi yana kallon Uncle a d'age cikin hura hanci.

"Ni makwafci na gari ne ban aikata hakan don muzguna maka ba sai dan taimako irin ta makwafci na kwarai."

Ya sake ambatar haka a ladafce.

"Shi kenan ya wuce amma ka sani daga yau ban amince na sake ganin kafafunka a cikin gidan iyalina ba tunda ba gidan gala ba ne."

"Insha Allah zan kiyaye."

Tsaki ya ja, Uncle ya kalle shi da sauri domin tsaki nadaga cikin abinda ke fusatashi.

"Tunda kai kayi kid'an to kai zakayi rawar ba ruwan Hadi ciki."

"Ban fahinceka ba Baba?"

"Munufata tunda kai ka kaisu Asibiti ba zanyi asarar ko taro ba, kai da kaja ruwar kai zai duka."

Murmushi Uncle ya yi cikin jinjina halin Baba wanda samuwar lamarin yasa shi ganewa.

"Wannan ba komi ba ne Baba ai yiwa wani aka ce yiwa kai ne."

"To madallah, zaka iya ficemin a gida."

Wani murmushin Uncle ya kuma yi, ya karkace a ya tura hannu a aljihu ya ciro kud'i yan dari biyar biyar masu yawa ya russuna ya mik'awa Baba, wani kallon banza ya saukewa kudin amma a zahiri godiya ya ke gabga masa cikin ransa ya yi hakan ne dan kare marbata.

"Na me ye wannan?"

"Ihisanin dai dana saba yi maka ne na aiwatar amma ba dan wani manufa na daban ba."

"Nagode, Allah ya rubuce "

Ya furta cikin damk'e kud'in.

"Amin Baba."

Sukayi sallama cikin wal-wala lamarin da ya yi ta bawa Uncle dariya.

'Wato kudi masu sayo martaba da k'arfi da yaji.'

Cikin ransa ya ambata yana kuma murmusawa.

"Halayyan Baban Khadijatu nada ban mamaki, gashi dai masanin ilimin addini amma in ya kwab'a wani abin tamkar bai tab'a zuwa makaranta ba balle ace yana koyarwa."

Ya furta cikin ransa. Su Bintu ya gani suna shiga mota wanda ya tabbatar Asibiti zasu, ya k'arasa wurin cikin wal-wala amma ganin yarda fuskansu ya ke cikin rashin wal-wala sai ya tsare gira, duk suka fito suna gaisar da shi bai amsaba sai idanu da ya zubawa Nafisa wacce ke hakimce a gidan baya bata fito ba.

"Ina zaki je?"

Ya jefo mata tambayar.

"Asibiti."

"Kai waye ba lafiya?"

Ya maido da tambayarsa kan su Beebah da ke tsai-tsaye

"Mama da Deejah."

Safina ta amsa masa.

Ya juyo kan Nafisa kafin ya bud'e baki ta rigashi cewa "Makwafci ko me ya yi maka na aibu ya kamata ka saka masa da khairan dan koyi da halin Manzon Allah."

"Sallallahu Alaihi Wasallam."

Ya ambata tare da su Beebah.

"Abban Hafiz ina fatar daga yau fushin ya k'are?"

Ta ambata a hankali wanda da alama shi kad'ai ya jiyo saboda ya matso jikin motar ya bawa su Bintu baya.

"Allah ya kiyaye hanya."

Ya ambata tare da mik'a mata kudi "Ku saya musu kayan marmari."

"Ok."

Ta amsa tana kallon cikin idanunsa, murmushi ya sauke mata ta maida masa da martani. Yana tsaye suka fice inda Beebah ce ke jan motar.

"Allah yasa tuban gaskiya kikayi dan na san waye ke Nafisat idan kin so shirya tsiya."

"Alhaji gashi inji wani mutum ya ce abaka idan ka dawo."

Mai gadi ya ambata cikin miko masa Emblem.

Amsa yi ya ya nufi cikin gida yana kallon agogon da ke d'aure a tsin-tsiyar hannunsa na hagu.

*TALLA.*

*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*

Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/30, 9:42 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Mrsjmoon.

E.W.F.

https://youtu.be/v9iNYDvS8JM

Pls ku dannamin subcribe a YouTube chennel d'ina.🖕

*Alhamdulillah. Masha Allah. Congratulations Sister Aisha (Neesha). A yau Asabar anshiga daga cikin, matakin cikar kamala ya kammalu tsaf, Allah ya sanya khairan tare da dauwaman zaman lafiya, samuwar albarkan zuri'a d'ayyiba tare da so da k'auna mara iyaka, Allahumma Amin🤲.* Shafin na ki ne baki d'ayan shi, Amarya 'yar shagali😍.

Page 17.

*Aliyu.*

"Yaya kayi kyau."

"Wani kyau ga bak'in fata."

"Ai su ne asalin kyawa-wa."

"Fad'arki ba."

"Da gaske Yaya bak'in fata na da kyau kuma ina son bak'in mutum."

"Saboda kinganki fara ba."

"Allah ba haka ne, nidai ina son bak'in abu shi yasa ko a kala ne nafi zab'an bak'i."

"Ke ni rabani da surutu, sanarmin da gaisuwarki zuwa ga My Deejah."

"Au batare zamu tafi ba?"

"Ki rufamin asiri kada Hajiya ta hana fitar baki d'aya."

"Kasan Allah Yaya yau sai naga Khadija ido da ido."

Zama ya yi gefen gado ya tsira mata ido.

"Zan fita yanzu a cewar zani gidan su Alawiyya amso Note book d'ina sai ka fito mu wuce."

Kallonta dai ya ke yi batare da ya yi magana ba, ganin haka sai ta fice tana dariya.

"Salma matsala in ban barta taje ba bazata barni na huta da uban mitaba."

Ya ambata tare da mik'ewa ya k'ara fesa turare, ya fito ya sami Hajiya ya russuna cikin tarbiyya ya yi mata sallama ta rakashi da addu'ar dawowa lafiya.

Tafe suke a Napep sai runtse ido ya keyi saboda yarda keken ke motsi yana jin inda ya bugu na yi masa zafi.

"Sannu Yaya, jikin ko?"

Da kai ya masa yana cije lips.

"Ba dan soyayya ba na tabbata ba mai fito da kai waje ko zuwa gobe ne saboda son jikinka ko mace albarka."

"Kin raina ni ko Salma?"

"Sorry big Brother."

"Idan kinga Mall mu tsaya asiya musu wani abu."

Ya ambata tare da kulle ido.

"To mijin Khadija."

Kunninta ya ja ta k'ank'ame hannunsa cikin yin k'ara.

"Idan mun koma gida ki tanadi abin fad'awa Hajiya domin ba ruwana ban san inda kikaje ba."

"Bakomi zanyi mata bayanin gaida maman surikarta mukaje."

"Da na yanke bakinki kuwa."

"Wai Yaya me yasa bazaka sanar mata da ka samu Mata ba?"

"Zan sanar mata amma ba yanzu ba."

"Uhm wallahi ina guje maka samun matsala tunda gida bai...

"Idan kina son komawa gida da lafiyayyun hak'ora kada ki sake maganar Amira ya had'anu."

"Insha Allah bazan sake ba"

"Hakan ya fi Miki."

"Yaya ka...

"Keep silent Salma, surutunki ya yi yawa."

Cikin hanzari ta kulle bakinta, girgiza kai ya yi tare da lumshe ido surar Deejah na yi masa gizo.

'Ina son Khadija haka ina jin dirin k'aunarta har cikin tsokar zuciyata.'

Ya ambata cikin zuciyarsa fuskansa cike da murmushi. Salma dai idanu ta tsira masa ga magana tana son yi ba halin furtawa sai ta kuma gyara zama tana k'arewa duk kan motsinsa kallo cikin yabawa tare da addu'ar itama Allah ya had'ata da maiyi mata k'auna na hak'ik'a irin wannan.

Ajikinsa ya ji kallonsa ta ke yi ya bud'e ido ta yi hanzari kauda kai rankwashi ya sauke mata ta kyal-kyale da dariya, shina dariya lamarin ya bashi, hatta da mai Napep sai da ya dara duk da bai san abin da sukeyiwa dariya ba.

*** Aunty ga mai fruits in tsaya a siya ne?"

Beebah ta ambata cikin kallonta ta mirror.

"Ki dai tsaya ki d'auki mai saida fruits din duka yafi"

Dariya su Bintu suka kwashe da shi.

"Kun soma haukacewa ne!?"

Nafisa ta daka musu tsawa.

Tsit sukayi, kowacce na tura baki cikin k'un-k'uni.

"Kufuto fili ku zagene da wannan na zuccun da kukeyi."

Ba wanda ya amsa mata ta ja dogon tsaki tare da cewa "Bazan siya musu komi ba wanda ya basu maula ya wadatar."

"Maula kuma?"

"Eh maula, ko kuna zaton ban san komi ba ne?"

"Baki sani ba gaskiya."

Bintuvta amsa kaitsaye.

"Uwar kini-bini to sanar da ni."

Yi ta yi tamkar bata ji ba.

Ya ja kwata cikin watsowa Beebah harara "Saura kuma inji gulman ban siya ba tare da kalman maula wallahi inci uban mutum ba mai hanani."

"Amma Aunty ba girmanki ba ne hakan, tunda Allah ya hore miki ko Uncle bai bada kudi ba ke ya kamata ki siya da naki."

Fiddausi ta ambata cikin tsare gira.

"Na ce bazan siya ba da baki kamar siyad'in!."

"Jikin ya motsa kenan."

"Wallahi Beebah zan ci k'aniyarki domin ba ki wuce in lakad'a miki duka ba kin dai san dai wacece ni, wato ga mmahaukaciya ko?"

"Uhm Aunty Nafisa kenan ni bakiji na kiraki da kalman hauka ba."

"Kina buk'atar dukan kenan?"

"Uhm gaibu."

"Zaki ramane in na bugeki?"

"Ni bance ba amma duka yanzu ai sai su Hafiz."

"Au kinfi k'arfin hukuncina kenan?"

"Ni bance ba fa."

"To me kike nufi da kalamanki?"

"Dan Allah Aunty Nafisa kiyi hak'uri tunda dai kince bazaki siya ba ai shike nan."

Safina ta ambata a hankali.

"Eh bazan siye d'in ba, munafukan banza kawai, ai wallahi da Kaka Alhaji zan had'a ku duk ya cimin k'aniyarki."

"Damu kayi miki me?"

"Kinga Safina idan kika sake yin magana wallahi sai na sumar da ke."

"Abin azimun ne."

Firdausi ta furta tana kauda kai gefe.

"Wai kuna son maidani mahaukaciya ce ko me?"

Shiru ba wanda ya tanka mata, tsaki ta ja Mai sauti, har suka iso Asibitin fad'a ta ke yi. Gyara parking Beebah ta yi ta dubi Bintu ta ce "Idan da kud'i a hannunki ki samo masu fruits a bakin gate bama shiga hannu sake ba domin ba girmanmu ba ne."

"Babu sister."

"Muje da shi a wurina."

Firdausi ta furta tare da bud'e k'ofar motar ta fice

"Wallahi kuka siyo sai na ci ubanku."

"Wai Aunty ina ruwanki ne? Ba fa kud'inki zasu tab'a ba."

"Eh ko ba nawa ba ne ai na isa in bada umurni abi."

"Idan ya kaucewa shari'a, Allah da kansa ya yi hani da bin umurnin na gaba."

"Beebah billahil azim zanci Ubanki a motarnan."

"Allah huci zuciyarki Aunty, uwar gidan Uncle mai kirki."

Tana ambata ta fice da sauri Safina ta rufa mata baya tana dariya ya yin da su Bintu suka wuce bakin gate batare da sun saurari masifar Nafisa ba.

"Wallahi yaran nan duk saina gyara muku zama ba dai ni kuke wulak'antawa kan wata banza ba, uhm ai zaku gamu da Kaka Alhaji ni kad'ai nasan tuggun da zan k'ulla muku, duk ku bar garin nan ba shiri."

Tana nan tsaye jikin mota su Bintu suka dawo. Ba suyi mata magana ba suka wuceta tamkar basu santa ba, bayansu ta bi tana zabga musu harara.

'Idan na b'atawa wanda kuke rawar k'afar nunawa k'auna sama da jininku fuska da ruwan batir ta koma dodanniya abar tsoro ga kowa ai kwa dawo hayyacinku, shegun yara kawai.'

Murmusawa ta yi cike da jin kwarin guiwar aiwatar da k'udirinta wanda shi ne dalilin zuwarta Asibitin.

*** *Baba Umaru.*

"Baba ga wata shawara akan zantukan Malam Hadi."

"Ina saurarenka Habibullah."

"Idan zaka yanke hukunci ka saurari duk bayanen kowa sannan kayi nazarin dukkansu sai ka yanke hukunci bisa tunaninka ba na wani gefe ba."

"Hakan na ke da niyyar aikatawa Habibu."

"Yawwa Baba kuma wallahi na gano rashin gaskiya a lamarin Malam Hadi."

"Habibullah kenan, wani haline na Hadi zaka tusamin da ban sanshi ba? Ai ina kallonsa ne kawai domin na gano Alhaji Muhseen yana taimakon Hurera ne shi ne ya ke bak'in ciki amma na tabbata da zarar ya manna masa kud'i zaiyi tsit kasan indai akan kud'i ne komi zai iya aikatawa."

"Allah ya shirya shi kam."

"Amin. Amma ina cikin nadamar amincewa da auren Hurera ga Hadi, aure rai ne da shi da kuma Allah na fushi da mai guntileshi amma da wallahi Hurera bata kuma zama da Hadi."

"Muyi ta binta da addu'a Baba domin aurenta ya zamo auren k'addara."

"To Allah ya iya mana dace da khairan ba dan halinmu ba."

"Amin Baba."

"Bari inje na gaida Hajiya Inna tare da sanar mata ta shirya cikin lokaci."

"To madallah hakan ya yi, ka sanar mata ta yiwa Hurera abu mai laushi da mara lafiya ke buk'ata."

"To Baban Hurera."

Dariya Baba ya sanya tare da watsowa Habibu dakuwa, shi kuwa ya fice yana dariya.

*** *Hinde da Asabe.*

Yaya nikam da zaki amince munbi Juma inda ta ke amso sa'a har ta mallake kowa na gidan ba wanda ke tsallaka kara duk in ta sanya, kinga da sai mu jefi tsun-tsu biyu da dutse d'aya, mu mallake Hurera da Malam hankali kwance in yaso in munje wurin sai mu raba ni na Mallaki Hurere ke kuma ki mallaki Malam."

"Zancen bur inji tusa. Kinga Hinde ki fita ido ko kin dawo miki Asabena ta zamanin baya."

"To Yaya me na yi kuma daga shawarar arziki sai tijara ya biyo?"

"Son kai dai shawarar arziki ba"

"Ta ina naso kan nawa?"

"Ta mallakan Hurera ni ki mannamin Malam mai mugun tsari a jikinsa, kinga garin neman gira sai in rasa ido a k'arshe na haukace yazamo kinci duniyarki da tsinke, to wallahi aniyarki ta biki, muguwar banza kawai wanda bak'in hali ya gama yiwa sutura."

"To ya isheki haka nan Yaya, kada abin ya koma cin zarafi."

" Bai isa ba, muguwar banza da wofi kawai."

"Duk mugunta na ban kama ko farcenki ba tunda ban tab'a yin kisan kai ba."

"Hinde! wa ya yi kisan kai?"

Muryan Baba ya ratso kunnuwarsu.

Tsit sukayi, ya k'arasa cike da masifa, suka ja baya ya nunosu da yatsa yana tattare babban rigarsa ya ce "Munafukai zaku sanarmin da wanda ya aikata kisan kai ko sai na maidaku b'eraye? Kun k'are a sata cikin kasuwa."

"Tsafi ka koma Malam?"

"Ke Hinde! Shiga hankalinki ko in sab'a miki matuk'ar kika nemi kawomin wargi, kindai san halina ciki da bai."

"Allah huci zuciyarka."

"Amin, maza sanarmin da wanda Asabe ta kashe tun ban mik'aku ga hukuma ba."

"Hukuma kuma?"

Asabe ta ambata idanu waje.

"Eh, in kaiku kuyi bayani a can ko ba dan Allah ba sai dan bak'ar azaba domin sanyawa zanyi suyi muku dukan jakuna masu d'iban yashi da duwatsu."

K'iftawa Asabe ido Hinde ta yi ta karkace ta ce "Malam abinda ya faru kusan shekaru ashirin meye na son ta tado da shi?"

"Ban fahimceki ba uwar salo tamkar d'iyar marok'a."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull