Kenza eBookz

Damuwata complete novel - Chapter 16

Damuwata complete novel - Chapter 16

Damuwata complete novel Chapter 16: Damuwata complete novel Chapter 16. Murmushin yaudara da cilka masa ya maka mata harara ta kuma murmusawa cikin cewa…

3,331 words

Murmushin yaudara da cilka masa ya maka mata harara ta kuma murmusawa cikin cewa "Manufata Nuhu almajiri da ka duka har ya zamo sanadin barinsa gidan duniya shi ne muke maida zancen har na ke cewa itama tana da alhakin kisan kai tunda ita ya yiwa laifi ta sanar maka kai kuma ba bincike hau dukan...

"Dalla can rufemin baki, sokayen Mata kawai da iya janyo masifa ana zaune lafiya, maza ku kama aikin gabanku ban son munafunci da maido zancen da ya wuce sabo."

"Had'a idanu sukayi suka murmusa batare da Baba ya gansu ba.

Sab'a babban rigansa ya sake yi ya shige d'akinsa yana cewa "Gidan Hurerama zan kwana saboda b'arayi sun soma kaiwa dukiyarta hari, makwafcin kirki ta samu ya sanya makatan tsaro amma yau na koresu ni zanyi gadin dukiyar iyalina."

"Aikam ka kyauta."

Suka ambata a tare.

"Ko ban kyauta ba matsalarku ba ce, mahassada kawai, ai duk kallon munafuncinku na ke yi dan nasan komi amma duk ranar da kuka kaini bango wallahi sai kunga tijara ganin idanunku."

"Malam me mukayi mata kuma?"

"Farin ciki da ciwonta Mana."

"In wannan ne ai ba wanda ya kaika murna."

"Me kike nufi da zantukanki Asabe!?"

Ya furta cikin fad'a tare da fitowa waje.

Ja baya sukayi ya watsa musu mugun kallo ya koma d'akin yana ta sababi wanda basa fahimtar me ke cewa.

Jan hannun Asabe, Hinde ta yi suka shige k'uryan d'akinta gudun kada ya jiyo abinda zasu tattauna.

"Yaya wallahi ki daina kaini bango kada wata rana na tona asirin dake birne."

"Hinde wai har sai yaushe zaki daina yimin barazana kina doramin alhalin mutuwar Jaririn da tuncan a matacce ya iso duniya?"

"Yaya wallahi ke kika kashewa Hurera d'a dan najiyo kukansa amma kafin in shigo kin aikata mugun nufinki."

"Ikon Allah, a she har yanzu sharrinki bai ragu ba Hinde saima k'aruwa?"

"Sharrinmu dai zaki ce."

"To naji nina kashe Jaririn Hurera amma aikema kinyi mata asirin da bazata sake haihuwa ba tare da sanyawa Uwani bak'in jinin rashin mijin aure."

"Au haka bokanki ya sanar miki da ni ce na aikata wad'an nan aiyukan?"

"Ko me zaki ce na tabbata ke ce kikayi su."

"Bilahil azim ban shiga lamarin Uwani ba na sandai na kashewa Hurere kwayoyin halittar haihuwa."

"Oh a she kema kin aikata kisan kan kenan?"

"Ni kam Yaya ba wannan zancen ya sa na janyoki muyi ba dan Allah mu rufe babinsa tunda duk munsan gaskiyan muna yiwa Hurera zagon k'asa tsawon shekaru kuma har yau bamuyi nasarar ganin bayanta ba."

"Naji, ina sauraren dalilin janyoni k'uryan d'akinki ya ke jikan iblis."

Dariya Hinde ta yi sai kace wacce aka ambatawa sunar arziki ta ce "Yaya matso ki ji abinda na shirya a game da zancen zuwar Malam gadin dukiyan Hurera."

Da sauri Asabe ta kai kunninta daf da bakin Hinde, zuwa can suka shek'e da dariya tare da tafawa.

"Hinde a gaskiya ke d'in shu'uma ce ta k'arshe."

"Kiyi shiru kawai mu jira baiyanar sakamako wanda zamu kwashi rawar d'aga buje, muci kaji mu more a cikin dukiyar bulus, bamu tara ba amma munfi mai ita cin moriyarta."

Wani shewan suka kuma sakawa har da daka tsalla tamkar yara.

*** Iya gigicewa Aliyu ya yi ganin halin da Masoyiyarsa ke ciki tsakanin rayuwa da mutuwa. Sai kallon na'urar da ke nuna tana da rai ya keyi tamkar ya tafi ya latsashi ta dawo hayyacinta.

Mama sai kallonsa ta keyi tana tantance natsuwarsa.

'Shi da Alhaji ko wa ye mijin uwata cikinsu oho?'

Ta ambata cikin ranta.

Kasa jurewa ya yi ya fice daga d'akin, ya zauna gefe ya dafe kansa, Salma tazo ta tsaya gefensa saboda itama lamarin ya tab'a ranta.

Beebah ce ta matsa daf da shi wacce ta biyo bayansa ta ce "Duk halin da muke ciki kenan Aliyu, kayi hak'uri insha Allah zata dawo hayyacinta."

"Allah ya amince hakan."

"Amin."

"Na yi ta kiran wayarta bai shiga naki kuma baki d'auka."

"Wayarta ba asan inda ta ke ba nawa kuma na dakinta an kulle."

"Ayya nima na sami k'aramin hatsari ne jiya da Rana."

"Sannu Allah ya baka lafiya."

"Amin."

"Zan wuce."

"Ok Agaida Hajiya"

"Zataji."

"Sister sai anjima."

"To Allah ya kara musu lafiya."

"Amin, mungode."

Beebah ta dawo d'akin jikinta a sake saboda hango k'aunar Deejah mai tsanani a idanun Aliyu da ta yi.

'Allah ya baki lafiya Deejah.'

Ta furta cikin ranta.

Aunty Nafisa kam jikinta ne ya yi mugun sanyi dan ita sam bata kawo haka jikin ya yi tsanani ba, mugun nufinta kauda shi gefe ta yi ta ja kujera gefe da zauna tana nazarin rayuwa.

Su Bintu ba su bar Asibitin ba sai bayan sallar magriba lokacin da Hajiya Inna ta zo. A hanya ba wanda ya yi magana hatta Aunty Nafisa ta kame bakinta. Sai da suka shigo layin gida sannan Beebah ta ce "Ita dai rayuwa wata aba ce mai ban mamaki yanzu ka ke mutum anjima ka zamo gawa dan haka mu aikata khairan domin bamusan aya mutuwa zata riskemu ba."

"Zantukanki abar yin nazari ne sister, Allah ka sanya-ya mana zuciya."

"Amin Fanta."

Suka amsa Banda Aunty Nafisa da ta yi nisa cikin tunanin yarda zata raba mijinta da Deejah cikin ruwan sanyi.

Uncle suka samu zaune a falo tare da yara wanda sukayi barci a saman jikinsa. Duk a falon suka zauna tare da gaisar da shi ya amsa cikin tambayarsu jikin Deejah.

"Da sauk'i amma na musulinci."

Fanta ta ambata cikin rawar murya.

"Insha Allah zata tashi cikin lafiya."

"Allah ya so hakan."

Suka amsa masa.

Siririn tsaki Nafisa ta ja suka kalleta sai kuma suka mik'e a tare suka bar falon.

"D'auki yaran nan ki kaisu d'akinsu."

Banza ta yi da shi ta mike ta haye sama. Girgiza kai ya yi yana jan Mata shiriya cikin ransa, yaran ya d'auka ya kai d'akinsu.

Har ya kwanta ganin Aunty Nafisa ta shigo sai ya sauka ya fice d'akin da sauri ta biyosa amma kafin ta cinmasa ya fice falon baki daya.

"Me hakan ke nufi? Abban Hafiz na nufin na zamemasa dodo kenan?"

'Ga alamu nan kin gani.'

"Wallahi bai isa ba."

Ta bawa zuciyarta amsa cikin fushi.

Da takaicin ya isheta sai ta zube saman kujerar falo ta fashe da kuka mai sauti wanda har su Fanta na jiyota amma ba wanda ya yi yunk'urin fitowa.

Uncle kuwa ficewa daga gidan ya yi baki d'aya saboda baya muradin sauraren zantukan Nafisa wanda ke saka masa ciwon kai. Daga inda ya ke tsaye yana hango duk abin da ke faruwa a k'ofar gidan su Deejah.

"Wallahi ina tausayin halin da kike ciki Khadijatu, Allah ya tashi kafadarki lafiya alfarman Manzon Allah S A.W."

Ya furta a hankali. Wayar Dr. Jalal ya kira sun jima suna tattauna yarda jikin nata ya ke. Ya kashe wayar ya juya zai shiga gida yajiyo tsayawar mota waigowa ya yi samari biyu ya hango sun fito a cikin motar na d'aukan kaya wato mai budadden baya wacce ake kira da akori kura. Gidan su Deejah suka shiga ya ware ido yana mamakin daga inda suka zo. Kimanin mintoci biyar da shigarsu suka fito kowa d'auke da buhun waken suya a bayansa da alamu a kwai wanda ya d'ora musu aciki. Gyara tsayuwarsa ya yi cikin sake shiga mamaki, yana nan har suka gama zuba buhunan waken wanda suka cika motar taf. Ganin zasu tafi ya isa wurij da hanzari duk suka sakko suna kallonsa cikin alamun rashin gaskiya.

Sallama ya yi musu suka amsa cikin muryan mashaya.

"Wa ya turoko d'aukan kayan?"

"Mamallakinsu."

Suka amsa a tare cikin cijewa na 'yan daba.

"Wa kenan?"

"Mai gidan."

"Baba ko Mama?"

Nan fa sukayi shiru zuwa can dayansu ya amsa "Mama."

"Ok kud'an bani mintoci biyu."

"Muna sauri ne Malam bazamu iya jiranka ba."

"Ok to zaku iya tafiya amma ba da kayan ba."

"Yallab'ai me kake nufi?"

Cigaba da danna wayarsa ya ke ta yi wanda tun soma yi musu magana ya fara.

Kallon juna sukeyi sai suka koma saman motar tare da bawa driver umurnin tafiya. Yana kunna motar wata mota ta gyara parking a gabansa, kafin samarin su san abinyi 'yan sanda sun kamasu sun tura cikin motarsu har da drivern.

Hannu Uncle Muhseen ya d'agawa 'yan sanda dan su tafi saboda ya sami wayar Dr. Jalal.

"Kaiwa Mama please."

"Ok ganima tare da ita nazo bata magani."

"Had'ani da ita."

"To gata."

Gaisheta ya yi cikin girmamawa ta amsa itama cikin girma.

"Mama kinyi magana ne azo a kwashe waken suyar da kika ajiye?"

"A'a."

"Ok to ya jikin naki?"

"Alhamdulillah."

"Na Khadijatu fa?"

"To angode Allah dai."

"Insha Allah muna tare da nasara."

"To Alhaji, nagode sosai da kulawa."

"Bakomi Mama masu iya magana sunce yiwa wani yiwa kai."

"Haka ne, Allah ya rubuce."

"Ami, sai da safe."

"Allah ya tashemu lafiya."

"Amin."

Wayar Mama ta tsirawa ido.

"Tabbas da abinda ke faruwa amma tunda ya nuna bai son fad'amin na barwa Allah lamarin, Allah yasa khairan ne."

"Amin."

Dr. Jalal ya amsa.

"Likita wai me ye ma'anar wannan k'aran da wancan na'urar keyi wanda kika sanyawa Uwata?"

"Shi ke nuna tana da rai."

"Ikon Allah sai kallo."

"Kuma idan kin lura da kyau zakiga tana sauke numfashi sai dai in ta yi d'aya tana d'aukan sekonni kafin ta k'ara amma duk ba matsala ba ne insha Allah zata tashi cikin k'oshin lafiya."

"Allah ya nunamin wannan lokaci."

"Amin."

Shigowar Hajiya Inna ya bawa Dr. Jalal daman barin d'akin. K'aramin Qur'ani Hajiya Inna ta mik'awa Mama ta amsa tare da yi mata godiya.

"Ya zamo shi ne abin yin bitarki Safe, Rana Dare domin duk kan waraka yana cikinsa, duk in kin idar da karatun kiyi tawassali da sunayen Allah d'ari ba d'aya ki rok'a mata sauki, insha Allah zakiga rahma na samuwa gareta tare da ke kanki."

"Nagode Inna, wallahi kunyimin duk kan komi, bazan tab'a mantawa da ku ba cikin farihin rayuwata, Allah ya saka muku da gidan Aljanna."

"Amin, kada ki samu ke d'iyarmu ce tamkar Habibu haka muka daukeki."

Kuka Mama ta fashe da shi Hajiya Inna ta matsa ta dafa kanta ta soma tofa mata addu'a, rungumeta Mama ta yi ta cigaba da kukan wanda damuwar halin da Deejah ke cike ne jigon yinsa.

Uncle Muhseen kam suna gama wayar ya kira wasu matasa suka maida waken ciki ya sallamesu ya koma gidansa ya d'auka kwad'o ya kulle gidan inda anan yaga wanda suka yanke da zarto. Tuno yarda sukayi da Baba yasa shi kiran number da ya amsa wurin Mama sai dai ya kira wayar nasa har sau biyar ba'a d'aga ba kallon agogon wayarsa ya yi yaga k'arfe Sha d'aya saura.

"Dare ya yi dana tafi gidanka na sanarma da abin da ke faruwa amma insha Allah gobe da subahi zan isa masallacin da kake limanci muyi maganar dan bana son muna samun sab'ani a matsayinka na mahaifin wacce na ke burin ta zama uwar 'ya'yana nan gaba."

Ya ambata cike da damuwa ganin dare na k'arayi sai ya koma gida cike da takaicin rashin aikinyin da ke jefe matasa cikin halin sace-sace gami da shaye-shaye.

*TALLA.*

*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*

Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure.)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/31, 9:28 PM] 💘: DAMUWATA. (Sanin abin adona) By Mrsjmoon.

E.W..F.

Page 18.

K'arar na'urar da ke nuna Deejah na da rai shi ne ya tashi su Mama barci a dai-dai lokacin kuma anata kiraye-kirayen sallar subahi. Dr. Jalal tare da Nurses ne suka shigo a hanzarce sakamakon jiyo k'aran na'urar. Fita su Mama sukayi suka tsaya bakin k'ofar cikin jan addu'o'i nasara.

Bayan wucewar wani lokaci Doctor ya fito da sauri Mama ta sha gabansa murmushi ya sauke mata ya nuna mata d'akin da hannu.

"Tafi ta ganki dan itama ke ta ke ta ambata."

"Da gaske Likita?"

"Eh Mama."

Cikin rawar jiki Mama ta fad'a d'akin ta yi ido biyu da Deejah jingine da gado Nurse na wanke mata baki.

Kulle ido na yi na bud'esu kan Mama wacce ke tsaye hawaye na bin kumatunta.

"Mamana kina raye dama ban saraki ba?"

"Alhamdulillah."

Shi ne abinda Mama ta furta a maimakon bani amsa.

"Gawa ta k'i rami ya jikin naki?"

"Hajiya Inna taho taji d'uminku."

Da sauri suka iso tare da rungumeni. Murna kam naganshi wurin Mama, ni kaina farin cikin da na samu kaina ciki na ganin Mama a raye ba mai misaltuwa ba ne.

"Ina Baba Umaru?"

Ta ambata saboda shi kawai na ke son sanyawa a ido.

"Yana Jigawa."

"Lafiya ko?"

Mamata ta ambata cikin sauri idanunta zube kan Hajiya Inna.

"Sai ya dawo muji saboda bayan na taho Habibu ke sanarmin sun tafi."

"Allah yasa dai lafiya wannan irin tafiya cikin dare."

"Amin."

"Mama muma mutafi dan Allah naga Dattijon kirki wanda bakya gajiya da bani labarin karamcinsa gareki."

"Uwata insha Allah kina warkewa zan shirya mana tafiya."

"Da fatan har Sokoto zakuje?"

"A'a Inna kowanne tafiyarsa daban zan shirya masa da yarda Allah."

"Allah ya amince."

"Amin."

"Mama ki saka mana ranar zuwa dan Allah, ina son ga nina cikin dangi masu yawa, naje can gidan naje can."

"Kin ganki Takwara da salo tamkar abin da kike ambata zaki iya aikatawa, ke da kike kifin rijiya sam ba kya son jama'a."

"Allah Hajiya Inna ina son ganina cikin dangi irin masu yawan nan."

"Uwata bari in had'o miki tea ki Sha."

Mama ta kauda maganar.

"To amma wanda na ke son yi jikina duk ciwo keyimin."

"Ai kam dole ki jiki ba dai-dai ba, kwanaki biyu a kwance ba motsi dole gab'b'ai su amsa."

"Hajiya Inna wai dogon suma na yi ko me?"

"Eh fa, irin wanda ke kama, coma inji turawa."

Shiru na yi ina tuno kalaman da suka shigo kunnuwana lokacin.

"Uwata sannu kinji? Allah kada ya k'ara nuna mana irin wannan lamari."

"Amin Mamana."

"Hajiya Likita ya ce abata abu mai d'umi sai ta sha magani kada abarta ta yi tafiya ita d'aya saboda jikinta ba kwari."

"To nurse zamu kiyaye."

"Nikam wanka na ke sonyi in rama sallolin da ke kaina."

"Ki bari ki warware ai ya shigo babin lalura Takwara."

"Hajiya Inna to a barni inyi wanka na sanja tufafi."

"Anfa samu lafiya kenan agwa-gwa sarkin wanka."

Murmushi na yi tare da komawa na kwanta. Duk yarda su Mama suka so nasha tea na kafe sai na yi wanka.

"To ki jira gari ya gama wayewa sai su Fanta su d'auko miki kayan da zaki sanja."

"To zanyi fitsari."

"Sakko na rik'eki Uwata."

"A'a yi zamanki Hurera, ke da baki da k'oshin lafiya."

"Hajiya Inna ce ta rakani, ina jin fitarta na tub'e kayan jikina na hau watsa ruwan sanyi, ba sabulu na yibta tirje jikina dukbda jirin da na ke gani haka kan na dafa bango ya kammala wankan na d'auro zani na fito sumata na d'igan ruwa, baki suka bud'e ganin wayon da na yi musu.

"Uwata halinki sai ke, narasa inda kika samo wannan tsafta."

"Wurin Kawu Habibu."

"Aikam sai wurin d'an ka iya."

"Zanyi sallah Mama."

"To cire ganin jikinki ga wankakke da Hijab."

Sanjawa na yi na hau sallaya saidai nakasa tsayuwa sakamakon rawar sanyin da na ke yi. Ai kam Hajiya Inna ta balbaleni da fad'a tamkar zata ari baki ya yin da Mama ta ruga kiran Likita. Kafin likita ya iso Hajiya Inna ta cic-cib'eni ta d'ora a gado ta rufeni da bargo tana ta tofamin addu'a sai duk suka bani tausayi na soma nadamar yin wanka da ruwan sanyin.

Ina jin Likita ya shigo ya dubani tare da yimin allura wanda ban jima ba na mance abinda ke faruwa sakamakon barcin da ya d'auke ni.

*** Kamar yarda Uncle ya k'udurta yana idar da sallah ya nufi masallacin da Baba ke bada sallah. Na'ibinsa ya samu bayan sun gaisa ya tambayesa Baba ya sanar masa baizo sallah ba, cike da mamaki ya juya sai ya tsinkayi muryan Na'ibin.

"Amma ga babban d'ansa nan ka sanar masa da sak'on insha Allah zai isar zuwa ga reshi."

Kallon wanda aka kira babban d'an Baba ya yi a ta ke ya aminta saboda kamannin da ya gani.

"Biyoni."

Abinda Uncle ya furta kenan tare da yin gaba.

"Bishi Auwalu kaji da abinda yazo."

"To Baba."

Uncle Bai sanar da Auwalu komi ba har saida suka iso k'ofar gidan su Deejah sannan ya dakata ya kalle shi a natse ya labarta masa abin da ke faruwa.

"Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un."

Auwalu ya ambata cikin sanyin murya wanda ya ja hankalin Uncle har ya zuba masa ido yana mamakin sanyinsa tamkar ba jinin Baba mai zafi ba.

'Tabbas su Kamalu ne da wannan aikin bisa hud'ubar su Inna, da gaske kenan Baba ya sha furan mai maganin barci? In ko haka ne Innar su Anas bata kyautawa Baba ba.'

"Malam Auwalu tunda kaine magajin Baba zuwa anjima kazo muje police station d'in ka gansu tare da bayanin dalilin zuwarsu yin sata."

"Alhaji Baba yana cikin gidan nan, maganin mura ya sha barci mai nauyi na daukesa shi ne suka sami nasarar aikata satan."

Ya ambaci haka saboda kunyar tonawa Matar Babansa asiri.

"Me ye hujarka?"

"Jiya da dare ni na kawosa gida kuma ya sanarmin zaisha maganin mura."

"Ok bari mu dubashi."

Suna shiga da Baba sukayi arba zaune saman buzu ganinsu yasa shi sallame lazimin ya nuna Auwalu da yatsa "Uban wa kabarwa tsaron tsangayar?"

"Antashi lafiya Baba?"

"Ban sani ba, amsamin tambayata kafin gaisuwa ya biyo baya."

"Baba Na'ibi zai kula da su."

"To lafiyalau, me kazo yi?"

"Alhaji zai sanarma, nabarka lafiya, Alhaji sai wani lokacin."

"To Malam Auwalu ga wanna ka hau abin hawa."

"Hannu ya mik'a ya amshi kudin tare da yin godiya, suna had'a ido da Baba ya girgiza masa kai tare da cije leb'en k'asa, murmushi ya yi kawai ya fice yana tir da halin mayintar kud'i irin na Baba.

"Halin Baba sai shi, sam ba'a yiwa mutum kyauta ya kauda idonsa a kai."

Ya furta a hankali.

"Alhaji me ke faruwa?"

Gyarar murya Uncle ya yi sannan ya jero masa duk abinda ya faru.

"Wallahi saina shukawa Hinde rashin mutunci saboda ita ta bani fura mai kayan maye na yi ta shek'a barci wanda ya janyomin asarar sallah cikin Jam'i, ga shi har b'arayi sun shigomin gidan iyali."

"Baba ko dai maganin muran da ka sha ne ya haifar da nauyin barcin?"

"Uban wa ya sanarma na sha maganin mura?"

"Auwalu ne."

"Oh yanzu na gane daga inda iskanci ya fito wato shima ya lalace kenan shi yasa ya siyamin lemu ya zuba kwayoyi shi ne zai ce maka ina mura to billahil azim sai na...

"A'a Baba banda saurin rantsuwa a matsayinka na shugaba kuma jagorar dubannin al'umma."

"Allah ya yi maka albarka Abdul Muhseen dan ka tunasar dani kiyaye harshena."

"Amin Baba."

"Yanzu zamu tafi naga shegun ne ko ya?"

"Sai zuwa hantsi zamuje, insha Allah."

"To amma ka sanar da a sanja musu kamannin ko?"

"Eh, dan yanzu haka ance sun sanar da wanda suka turosu, kafin mu isa za'a kamosu."

"Yawwa hakan ya kamata a had'asu a ci k'aniyarsu yarda gaba ko sunar b'arawo aka kira zasu bar wurin a guje."

Murmushi Uncle ya yi yana k'ara yabawa fitinar Baba.

Bayan tafiyar Uncle Baba ya nufi kitchen yana surutai zuwa can kuna ya soma yabon Mama.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull