Kenza eBookz

Damuwata complete novel - Chapter 18

Damuwata complete novel - Chapter 18

Damuwata complete novel Chapter 18: Damuwata complete novel Chapter 18. Cikin daren Dr. Jalal ya dubani sosai bayan ya matsamin saida na sha tea, ina…

3,356 words

Cikin daren Dr. Jalal ya dubani sosai bayan ya matsamin saida na sha tea, ina gamawa ya kama hannuna na kalle shi ya motsa kai cikin cewa "Khadija rayuwarki tamkar rayuwar mutane masu yaww like Mama, Yaya Muhseen, su Hajiya Inna da ma k'awayenki su Fanta tare da al'uman Annabi irinmu masu tausayin halin da kika sami kanki ciki na rashin lafiyar jiki d'an haka na ke baki shawara da ki jajirce wurin kauda damuwa a zuciyarki, ke malama ce kin san kalolin addu'o'i na tafiyar da duk kan damuwar jiki da ruhi, to ki sanya su zamo aminan zuciyarki wurin tuno da su ta hanyar ambatarsu, kada ki sake bari damuwa ya kwantar da ke akaro na uku domin banjin zaki tashi da lafiyar tunani ba ko na jiki. Dan Allah da Manzon Allah ki bamu hadin kai aikinmu ya sami nasara, lafiya ya wadaci jiki da ruhunki baki d'aya."

"Insha Allah Doctor zanyi bakin iyawata na ganin damuwa bai yiwa rayuwata illa ba."

"Masha Allah, ina rok'on sauk'i a gareki dama duk kan masu fama da rashin lafiya."

"Amin. Nagode."

"Ki kwanta ki huta kinji?"

"Insha Allah."

Bayan fitarsa Hajiya Inna ta zo ta zauna saman kujera ta dubi Mama dake manne da ni ta ce "Hurera ku kwanta ku huta dan kema ba lafiyar ce ta isheki ba."

Ba musu Mama ta kwanta gefena sai na kwanto rabin jikina a saman nata na lumshe ido ina mik'a godiya ga Allah da ya bani mahaifiya irin Mama mai damuwa da dukkan DAMUWATA.

Karatun Qur'ani Hajiya Inna ta soma cikin harshen karatun zaure saboda shi ta iya, na yi tsam ina saurarenta domin naji dadinsa har ina burin iyashi, natsuwar huri ya wadacemu baki d'aya barci ya daukemu batare da mun sani ba. Hak'ik'a samun ilimim addani musanman na Alqur'ani babban falala ce, gashi haske ne ga dukkanin duhu.

*** Baba gidan ya koma cike da fushin yarda Mama tak'i yi masa magana tunda ta kulashi sau d'aya bata sake nuna tana wurin ba wannan abu da ta yi ya k'ona masa rai. Wanka ya yi da ruwan sanyi saboda ranar da ya kwaso tare da tiri-rin da zuciyarsa keyi masa. A baranda ya zauna yana bincikensa, sai tsaki ya ke ta dokawa saboda ya kasa gane komi, zuwa can ya ture mazubin k'asar gefe ya zabga tagumi.

K'arar da wayarsa ta yi ne ya katse masa tunani ya d'auka da hanzari ganin sunar Babban yaronsa Auwalu ya bayyana. Sallamarsa ya amsa bai tsaya amsa gaisuwarsa ba ya rufeshi da fad'a akan kiransa da ya yi.

"Kayi hak'uri Baba matsala ce babban yasa dole sai na kiraka."

"Me ye shi?"

"Innar su Kamalu da Innar su Anas na wurin 'yan sanda."

Tsaye Baba ya mik'e yana cewa "Me! suka janyowa kansu ni Hadi?"

"Wallahi Baba ban san ainihin abinda ya faru ba amma dai Baba Usman ya sanarmin wai Innar su Kamalu ce ta jefa 'yar sanda a rijiya daga tazo da K'asimu cikin ankwa."

"Innalillahi! Yau na shiga uku da wad'an nan matan jaraba, to yanzu anciro 'yar sandan ko kuwa?"

"Eh ancirota amma da wuya ta rayu saboda ance bata motsi yanzu dai an wuce da ita Asibiti dan a tabbatar da rayuwarta."

"Kai kana ina ne yanzu?"

"Ina bawa d'alibai karatu."

"To ka sallamesu ka tafi ofishin 'yan sanda idan an tamabayeka inda na ke ka ce na yi tafiya yau da subahi ban san komi akai ba saboda ba a gidan na kwana ba."

Jim Auwalu ya yi amma tsawar da Baba ya daka masa sai ya amsa jikinsa na rawa. Ka she kiran ya yi yana share gumi.

"Amma anyi shegun nata masu janyomin bala'i ina zaman lafiyana, wallahi ba mai kaini belinsu, su da suka janyo masifar ya k'are akansu, yanzu bari in nemi Alhaji Muhseen muje wurin 'yan banzan yaran can a zabgawa iyayensu tara na samu na sakawa a aljihu domin walalhi cewa zanyi sun kwashe rabin waken sun siyar sun dawo kwashe sauran ne Allah ya toni asirinsu aka kamasu kuma sai anbiya ninkin kud'in, duk buhu d'aya a sittin da biyu zai tashi na ce buhu ashirin da biyar suka sace, iyayensu sayi maganin shed'ancinsu domin sunji a jikinsu."

Murmushi ya yi jiyo k'amshin zuwar kud'ad'e a bulus.

Cikin gaggawa ya shirya ya fito yana sab'a babban riga ya doshi gidan Uncle dan ya tabbatar zuwa yanzu ya baro Asibitin. Mai gadi ya aika ba jimawa sai Uncle ya fito cikin shigar kamala sai k'amshi ya ke bugawa. gaisar da shi Uncle ya yi amkar wani abu mara dad'i bai faru ba. Suna tafiya cikin mota Baba na sanar da shi yarda yatsara za'a amsa wurin iyayen yaran shi dai Uncle baice uffanba saboda ya san darace zataci gida domin tuni ya sami labarin 'ya'yan Baba ne b'arayin. Suna isa 'yan sanda suka kewaye Baba zasuyi masa tijara, Uncle ne ya yi musu magana tare da tunasar da su girman rawanin da ke kansa. Baba kam sai zare ido ya ke yi jin abin da 'yan sandan ke fad'a.

' Yanzu b'arayin nan ashe su Kamalu ne? Iyayensu suka turo su? Kenan na shigo hannu duk boren danayi bazanyi asarar kud'i ba a she sai na yi dai, kai anyi sokayen mata marasa sanin ciwon kai, inbanda b'atan basira ta ya zasu shigo sata gidan Hurera, gidan da akayi saukan Alqur'ani mai girma cikinsa, to wallahi zanyi belin ku amma zan baku mamaki matuk'ar mamaki, zaku san kun zubdamin da martaba.'

"Baba muje ciki."

Ya tsinkayi muryan Uncle daf da shi wanda ya taimaka wurin katse masa zantukan zuccin da ya ke yi. Wani kallo ya saukewa Uncle tare da girgiza kai.

'Kome ya faru kai ne sanadi da baka kira masu babbak'un kaya ba da banga zubewar mutunci ba, wallahi ni kad'ai nasan tsiyar da zan shuka maka.'

"Baba ka natsu ba wanda ya isa ya kulleka tunda ina wurin kuma belin matarka zanyi shi insha Allah tunda anyi sa'a 'yar sanda da ta jefa rijiya bata mutu ba haka bataji babban ciwo ba balle buguwa mai wuyar magani firgicin ne ya sanyata dogon suma amma yaran sai sunje gidan yari domin gaba suji tsoron aikata sata."

"Nagode Alhaji."

Abinda Baba ya iya ambata kenan shima jin ba shi ne zai kashe kud'in belinsu Asabe ba amma ba dan ya daina jin haushin Uncle ba

Duk wani kace na ce Uncle ne ya shige gaba har aka basu belin su Hinde wanda suka sha dukan tsiya fuskansu dik ya bumbure sakamakon sanadin jefa 'yar sanda rijiya da Asabe ta yi shi yasa ana kawosu 'yan uwan aikinta mata suka rufesu da dukan kawo wuk'a. Hinde kam ta tsinewa Asabe ba iyaka ya yin da Asaben ke saurarenta ta kasa ramawa saboda tafi buguwa.

Kallonsu Baba ke yi a tsiyace ba d'igon tausayin halin da suke ciki ya yin da su kam sun kasa had'a ido da shi, ko wacce cike ta ke da farban makoman aurenta domin sunfi kowa sanin masifar Baba barinma da duka zubar masa da mutunci aka kawosu gidan masu babbak'un kaya, gidan da keyiwa tofin Allah tsine ba gaira ba dalili.

*** Sadda na farko gari ya yi haske, Mama na hango rik'e da Alqur'ani tana bita a sirrance, ban nuna mata na tashi ba sai na lafe tare da lumshe ido ina kallonta ta k'asar gashin idanu cike da k'auna mara misaltuwa.

Hajiya Inna ce ta matso kusa da Mama ta yi k'asa da murya bayan ta saukemin kallo na seconni. Samun kaina na yi da bud'e kunnuwa da kyau domin jiyo zancen da zatayi wanda na raya a kaina ne sai dai sab'anin zargina sai na ji ta soma cewa "Hurera su Babanki zasu dawo gobe insha Allah sannan ya ce in sanar miki da ki zauna cikin shiri na tafiya duba Alhaji Abdul ganiyu domin tafiyar gaggawan da ya yi sanar masa akayi ya rasu shi ne ya tafi domin ya sami jana'iza sai ya samu dogon suma ya yi."

"Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, Insha Allah da Uwata ta sami sauk'i zamu tafi Inna, dama ina shirin tafiyar ne lalura ta samemu."

"Hakan ya kamata, sannan Alhaji ya sanarmin shi Alhaji Abdul ganiyu na son magana da ke baki da baki."

"Ayya Baba ai da ya sanarwa da Baba Umaru sai ya sanarmin."

"Ba zai rasa sanar da shi ba amma dai yafi buk'atar ya yi maganar da ke ido da ido."

"To ina nan tafe da yardan Allah."

"Madallah, sannan ina baki shawara idan kun baro kwara to ku sauka a Sokoto sada zumunta, ki watsar da duk abinda ya faru abaya inda hali ki yafe musu domin kema Allah ya yafe miki."

"Inna ban jin zan iya yafewa dangin mahaifina, sannan bazan tab'a waiwayansu ba, yarda suka bawa Duniya ni to zan tabbatar musu ni d'in ta Duniya ce domin na gamu da ku masu karamci fiye da su marasa adalci."

"A'a Hurera ki zamo mai yafiya sannan idan kika aikata haka mahaifinki ba zaiji dad'i ba domin duk tunk'ahon d'a ko 'ya da asalinsu suke tutiya ko da kuwa a ya suke su ne dai ababen adonta duniya da hahira"

"Allah sarki Babana mai sona tare da damuwa da duk abinda ya shafeni, da shi na saba saboda mahaifiyata banyi wayon saninta ba amma yarda ya ke bani labarinta sai na ke ji tamkar na rayu da ita sannan indai sune zanyi tink'ahon da su wallahi gara na dauwama ba dangi tunda ina da sanyin idaniyata Nana Khadijatu."

"Allah ya gafarta musu da Rahma, amma Hurera ya kamata ki rage zafin nan da kika d'auka ki tuna bawa bai tsallake zanen k'addararsa domin lamari ne da Allah ya samar da shi tun kafin tsiron halittar bayi."

"To Hajiya Inna zan duba."

"Hakan na ke son ji domin rik'o bai da kyau."

"Nagode Inna."

"Bakomi, sannan abu na gaba dole ki sanar da Khadija...

"Dan girman Allah Inna mu bar wannan maganar."

"Saboda me kike b'oye gaskiyan alhalin lokacin abayyana ya yi?"

"Bana son damuwarta saboda DAMUWATA ce."

"Wannan ba hujja ba ce Hurera."

"Hajiya Inna dan girman Allah na ce ki bar magana zamuyita gaba."

"To ai shi kenan tunda kinga hakan yafi miki."

"Dan Allah kiyi hak'uri Inna."

"Bakiyimin komi ba Hurera dama shawara ce na kawo tunda kince sai nan gaba ina yi miki fatar kaiwa lokacin cikin rayuwa."

"Allah ya amince."

"Amin."

Daga haka suka sanja labari zuwa zancen mugun halin Baba wanda banso hakan ba.

"Bisa alamu Mama na da babban damuwar da ta ke b'oyemin."

Na furta hakan wanda fitar sautinsu suka tsaya a iyaka saman lab'b'ana.

*Munata gangara izuwa k'arshen free pages dai.*😍 Pay 300 to 0468069082 Haruna Safiyya GTbank. Send the evidence to WhatsApp number 08132166848.

*TALLA.*

*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*

Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [11/3, 11:29 PM] 💘: DAMUWATA ( Sanin abin adona) By Mrsjmoon

E.W.F.

https://youtu.be/v9iNYDvS8JM

Pls 'yan uwa ku dannamin subcribe a YouTube d'ina, nagode.

Page 20.

Tsam na yi ina nazarin zantukansu tare da son gano abinda Mama ke b'oyemin amma iya hangena na kasa gano abin, lamarin da ya sanya sanjawan bugun numfashina ya soma fita da sauri batare da na san dalilin faruwarsa ba, na yi hanzarin kulle bakina gudun kada sautinsa ya bayyana su gano na farko har na jiyo hirarsu tunda na gano basa so inji.

Hakan danayi ya sanya na sark'e cikin fitar da tari mai k'arfi. A tare suka iso gareni, Mama ta soma shafamin baya cikin jeramin sannu Hajiya Inna kuwa ta kafamin kofin ruwa a baki, bayan tarin ya tsaya sai na tsirawa Mama ido ta ware nata na lumshe nawa tare da motsa leb'b'ana.

"Me kike son sanarmin Uwata?"

"Godiya na ke son yi muku."

Na furta duk da ba shi ne a raina ba.

"Da akayi me?"

"Kula da ni batare da gajiyawa ba."

"Wannan hakkin mu ne Uwata dan haka babu godiya a tsakaninmu, kinji ko?"

Motsa kai na yi ina saukewa Hajiya Inna murmushi wacce ke binmu da kallo cikin sigan tausayi.

'Da magana a bakinki Hajiya Inna kuma zan jiyo shi da yardan Allah.'

Na ambaci hakan a raina tare da zamewa dan in kwanta saidai Mama ta hanani hakan inda ta umurceni da in sauka in d'auro alwalla inyi Sallar Subahi. Na sakko ina cije baki saboda jirin da baigama sakina ba. Ita ta taimakamin na shiga toilet, tana tsaye na yi tsarki tare da d'auro alwalla muka fito saboda ta san halina da son wanka ina iya k'ara sanyawa jikina ruwan sanyi da zarar ta bani wuri.

A Zaune na gabatar da sallah a cikin sujata na k'arshe na rok'i Allah da ya bayyanamin abinda Mama ke b'oyemin ko da jinsa ko ganinsa zai zamo ajalina ne.

Na yi wannan addu'ar ne saboda yarda na ke son sanin lamarin.

Haka nan kawai naji b'acin rai ya kanai-naye ruhina cikin sekonni bayan na d'ago daga sujjadar, koda na sallame sallar sai na koma saman gado na kwantar tare da juyawa su baya.

"Uwata jikin ne?"

"A'a."

Na amsa a tak'aici abinda ban tab'a yi mata ba kenan bata amsa cikin rashin girmamawa.

"To tashi kisha tea kafin Likita ya shigo."

"Barci na ke ji Mama."

Wannan karan cikin rawar murya na amsa mata.

Hannunta na ji cikin sumata sai na sake lafewa batare da na juyo ba.

"Uwata na san kina tare da damuwa b'oyenmin kike yi."

Tashi zaune na yi cikin son dai-daita fuskata zuwa wal-wala.

"Kada ki wahalar da kanki Uwata wurin layancewa domin na jiyo dirin damuwarki a k'irjina, oya maza sanarmin da shi tun ban sab'a miki ba."

Dariyar dole na sanya duk dan in nuna mata ban tare da damuwar komi na d'aga yatsa na nuna Hajiya Inna wacce ta bud'e baki tare da zaro idanu jin abinda Mama ta ambata ina cewa "Kalli Hajiyarki k'uda na shirin fad'awa bakinta."

Harara ta zabgamin na kamo hannayenta na rungume a k'irjina ina doka murmushi.

"Harbawan me zuciyarki ta ke yi haka da sauri?"

"Wai tana neman ki aminta da kalaman d'iyarki ce na bata tare da damuwan komi."

"Na amince Uwata bata cikin damuwa tunda muna tare da ita a ko da yaushe kuma zamu cigaba da kasancewa da ita har zuwa sadda k'asa zai rufe idanunmu tare da burin had'uwa da juna a gidan Aljanna."

"Allahumma Amin Mamana."

"Wannan k'auna taku Hurera na bani tsoro anya lamarin nan kuwa mai b'ullewa ce?"

"Inna bakomi sai khairan, wannan shi ne ni'imar da Allah ya dasa a cikin shayar da 'ya'ya nono ko da ba...

Sai kuma ta yi shiru tare da mik'ewa ta nufi hanyar toilet.

"To Allah ya tabbatar da khairan mara iyaka Hurera."

"Amin tsohuwar su Mama."

Na amsa cikin tsokana.

"Fad'i ki k'ara da ihu tsohuwar su ce ko wani ya ce taki ce?"

"Eh kince dole sai na kiraki da Inna kinga kenan kin saka dole kin zama tsohuwata."

"Takwara ciwon nan naki yazo miki da son surutu."

Lumshe ido na yi bance komi ba itama daga haka bata sake magana ba.

Ganin Mama ta ji bata fito ba sai Hajiya Inna ta hadamin tea mai kauari ta tsareni saida na shanye. Lokacin dMama ta fito kanta k'asa dan tak'i kallona saina nuna tamkar ban lura da b'oyemin fuskanta da ta ke yi ba na d'auko apple na soma gutsira cikin zantukan zucci masu yawa a game da bak'on lamarin da na kasa gano kansa balle tushensa.

"Kunga tafiyata na koma gida na huta tunda duk kun warke."

Hajiya Inna ta ambata cikin kallon Mama wacce da alama ta yi nisa cikin tunani bata jiyo maganar ba.

"Ayya Hajiya Inna ki jira mu tafi tare tunda zamu sami sallama yau insha Allah."

"Takwarata su Malam na kan hanya dawowa to ina son zan sama musu wani abu kafin su iso."

"To tafi na baki izini tafi."

"Ja'ira kin samu lafiya fa bakin ya bud'e da tsokana kala-kala."

"Eh dai tafi sai nazo kwance jikka."

"To amma dai ki tabbatar kin maida jikinki saboda Malam bai sakewa ramamman mace fuska dan na tabbata wannan manya idanun naki da suka sake fitowa zasu firgitamin miji tsaf."

Kafin in bata amsa ta fice da sauri tana dariya Mama na tayata domin ta maido da hankalinta kanmu.

"Hajiya Inna kenan ta san kan iya tsokana."

"Uwata ke ce Inna ke sakewa irin haka duk cikin jikokinta saboda bata yarda da wasan jika da Kaka ba gudun rashin kunya irin na wasu jikokin sannan wasan kansa wasu Malaman sunce baya cikin musulinci."

"To Mama me yasa ni kad'ai takeyiwa?"

"Ita zata amsa miki wannan tambayar kam."

"Mama wai me...

Dawowar Hajiya Inna yasa ban furta abin da na yi niyya ba, muka zuba mata ido ta iso ta ja hannun Mama suka fice zuwa can ta dawo ita d'aya tare da d'aukarwa Mama hijab shima bata jima ba ta dawo ta zauna saman kujerar roba a gabana muka zubawa juna ido, numfashi ta ja ta soma magana "Nana Khadijatu Allah ya jarabceku da rayuwa k'ark'ashin baudd'en mutum sam Malam Hadi bai aiki da saninshi a matsayinsa na babban Malamin da ake ji da shi."

"Me ya faru kuma?"

"Ina fita na had'u da Alhaji Muhseen yazo tafiya da Mamanki wai ya tsayar da matarsa a waje sai sun nemi gafarar Hurera kafin kafafunsu ya shiga masa zauren gida sannan ya tara mutanen unguwa nata fesa musu lamarin da bai kamata ba domin ance duk wanda ya rufawa wani asiri to Allah zai rufa masa."

"Duk me ya janyo hakan Inna?"

Tsit na yi jin bak'in labarin abin kunyar da matar Baba tare da 'ya'yansa suka tafka.

"Dan rashin kyautawa kam sunyisa Takwarata amma ai fad'ar cikin gida ne bai kamata ya bari na waje su ji ba ko dan mumbarin da ya ke hawa bada sallah."

"Abin kunyar ce kam hakan Inna kuma ina tabbatar miki da wata manufa nasa yasa shi kiran Mama."

"Abinda itama ta ke sanarmin kenan dan ta nuna bazata je ba na bata kwarin guiwa."

"Ko me ye dai Allah na tare da masu neman taimakonsa."

"Wannan haka ya ke Khadijatu, masu neman taimakon Allah cikin lamarinsu basa tab'a ganin bak'in cikin ratuwa."

"La shakka babu Inna."

Munyi shiru zuwa can Hajiya Inna ta soma yimin hira inda yawancinsa akan yarda rayuwa ta ke juyawa al'umma ce musanman wad'anda suka d'auki duniya da fad'i. Knocking a kayi Inna ta amsa da a shigo matar Kawu Habibu ne tare da Aliyu Muktar, ware ido na yi shi kuwa ya tsaya a k'ofa yana jefomin murmushin k'auna, sunkuyar da kai na yi jin Zainab na tsokanarsa, bai kulata ba ya iso gaban Hajiya Inna ya sunkuyar har k'asa ya gaisar da ita ta amsa cikin tambayar sa mahaifiyarsa.

"Hajiya ya mai jikin?"

"Gatanan ta warke tunda bakiyi tunanin zuwa cikin lokaci ba sai da kikaji mijinki zai dawo gudun kada ya saukemiki halin nasa yasa kika zo to angode amma ki sani shi kyautatawa abune mai kyau kuma lalura na kan kowa dan Khadijatu bata zo miki barka ba bai zama hujjar da zaki riketa ba domin kinfi kowa sanin halinta na rashin son jama'a."

"To Hajiya ai duk rashin son jama'arta sai ayi mata fad'ar rik'o da zumunci tunda duk abu d'aya muka aikata har gara ni da ita."

Shiru Hajiya Inna ta yi cike da takaicin domin abinda ta tsana kenan ta nunawa mutun kurensa ya k'i amsa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull