Kenza eBookz

Damuwata complete novel - Chapter 9

Damuwata complete novel - Chapter 9

Damuwata complete novel Chapter 9: Damuwata complete novel Chapter 9. Bugun numfashi ya k'aru, innalillahi wa Inna ilaihin raji'un kawai na ke ja dan ban…

3,374 words

Bugun numfashi ya k'aru, innalillahi wa Inna ilaihin raji'un kawai na ke ja dan ban zaci Uncle zai iya ambatamin wad'annan kalaman ba ido na ganin ido.

"Ina neman alfama da kiyimin girki dan na yi kewar abincinki, shin Zan samu?"

Motsa kai na yi kawai saboda yarda bakina ya yimin nauyi.

"Nagode."

Ya ambata cikin fitar murmushi mai sauti.

Horn ya yi a gate d'in gidansa na dubesa da sauri.

"Dan Alalh ka bari in sauka a nan."

"Ba'a nan na d'aukeki ba."

Ya bani amsa a d'an fusace.

Yana gyara Parking Aunty Nafisa na isowa wurin.

"Kagani ko Uncle da ka saukeni a bakin gate na tafi amma yanzu gashi nan matarka zata kuma il...

"Kiyimin shiru Deejah ko ranki ya b'aci."

Tsuke bakina na yi tare da zamewa na kwanta cikin seat, ina ambaton sunar Allah.

"Malama ki fito kije kiyimin abinda na ce."

Fitowa na yi jikina na rawa aikam Aunty Nafisa takawomin cafka na kwalla ihu tare da komawa cikin motar na kulle.

"Nafisa wallahi zan sab'a miki gaban ma'aikatanki.."

"Wallahi baku isa ba ku ci amanata ace bazanyi magana ba sabida mulkin mallaka, na rantse yau sai na lahira ya fita jin dad'i."

"Kika sake magana billahil azim saina baki mamaki, in kuma kince wasa ki sake furta kalma kigani."

A fusace Aunty Nafisa ta bar wurin.

"Fito muje ciki."

"Uncle dan soyayyarka da Manzon Allah ka barni inyima girkin a gidanmu."

Shiru ya yi na sakonnni sannan ya ce "Ok fito ki tafi can d'in."

Motsa kai na yi tare ficewa rik'e ledar da ya siyomin turaruka da wasu kayan da banfahimci meye su ba.

"Bakiji ba."

Cak na tsaya.

"Ki had'omin da zob'o drink d'in nan mai d'and'ano kinji?."

"Insha Allah."

Ina amsawa na yi gaba dama ban juyo ba koda na tsaya, ina ji ajikina kallona ya keyi shi yasa har na fice ban waigo ba.

"Tana da kyawun sura dana zuciya da yardan Allah ke d'in uwar 'ya'ya na ce."

Ya ambata cikin murmushi, ya juya ya nufi ciki, kafin ya shiga falon ya sauya yanayinsa zuwa fuskan shanu saboda tuno 'yar darun matarsa.

Nafisa na tsaye goye da hannayenta cike da masifa tana jiransa, yana shigowa kuwa ta nufesa cikin da baka'i ya yi hanzarin d'aga mata hannu cak ta tsaya tana kallon fuskansa sai jikinta ya yi sanyi bai kalleta ba haka bai furta mata kalma ba ya haye sama cikin sar-sarfa.

"Thank you Beebah da kika kawomin shawara mai kyau, insha Allah Azumin bana dake zamu tafi Umrah dan kin can-canci tukuici."

"Wato da jinina ka had'a baki ake son ganin bayana ko Abban Hafiz?"

"Zato zunubi koda ya zamo gaskiya dan haka ki kyautatawa 'yar uwanki zato."

"Bazan kyautata ba, wallahi sai naci ubanta shi yasa ta maida gidan tamkar gidan Ubanta a she tasan munafuncin da ta ke k'ullawa kenan? Shi yasa d'azun ta yi ta bani hak'uri to yanzu bata isa hanani zuwa na tijara Uwar Deejah ba, munafukan banza da wofi masu shiffan 'yan wuta kawai."

Ta kai k'arshen maganar cikin sauke nunfarfashi tamkar wacce ta yi gudu.

"Nafisa wallahi tallahi kinji na rantse idan kika kuskura kika fita gidan nan bada izinina ba sai kin tafi Maiguduri komin dare a yau d'in nna."

A razane ta ja baya tana kallon idanunsa ya kuma zare matasu cike da b'acin rai, kafin ta furta kalma ya shige bathroom tare da bugo k'ofar.

"Me suka bawa mijina ya daina lallab'ani? Me na ke shirin ji da gani idanuna biyu ba mafarki ba? Kalman saki fa ke shirin samuna dik akan wannan shegiyar yarinyar wacce bata isa komi ba. K'alu innalillahi wa Inna ilaihin raji'un! Kishiya ni Nafisa zan zauna da ita? Kai wallahi sam ba zai yiwu ba, dik abinda zanyi sai na yi dan ganin ban zauna kishi da ko wacce d'iya mace ba."

A fusace ta fito d'akin ta shiga nata ta kulle ta d'auki waya rubutu ta yi na sakonnni ta tura tana ganin ya tafi ta cillar da wayar gefe ta mik'e tsaye ta soma kai da kawo tamkar mai nak'uda.

"Kai Nafisa matsala ce na yarda da zancenki Beebha ita d'in zuma ce shanta saida wuta, daga yanzu na sanja miki Nafisa, dik kika b'atamin zan rama dai-dai da abinda kikayimin na daina yi miki uzuri wanda sam bai amfanamin komi, ina kuma gode miki Beebah dan kin haskamin hanyar dawo da 'yar uwanki tunaninta."

Yana maganar ne cikin fesa turare a kan yallabiyarsa, yana gamawa ya sakko falon k'asa ya kunna TV ya kamo world sport, kwallaon da suke haskawa ya d'auke masa hankali, ya gyara zama cike da jin natsuwa domin ya sami bakin kashe rigimar Nafisa cikin ruwan sanyi.

*** Ina shiga gida kiran Aliyu ya shigo wayana da kallo nabi number har ya tsinke ban d'aga ba, wani ya sake shigowa sai na maida wayar silent, na iso gaban Mama na russuna wacce ke yanka alaiyahu.

"Sannu da dawowa Uwata."

"Yawwa Mama sannu da aiki."

"Yawwa."

"Ina Beebah?"

"Daf da zaki shigo ta fita."

"Ok, bari in hanzarta na samawa Uncle abinci dan ya rok'eni da in dafa masa wani abu."

"Me zaki dafa masa?"

"Ban sani ba Mama sai na shiga kitchen d'in tukunna zan duba."

"In zaici Tuwon Shinkafa da miyar Agushi da sai ki d'iba masa wanda na ke yi."

"Zaici bari in watsa ruwa nazo, zuwa lokacin miyar ta yi ai."

"Insha Allah ta kallama kam."

Daga haka na shige d'akina.

"Uwata manya, komi naki a tsare yake, rayuwarki abar koyi ne ga dibban Mata, Allah ya zab'a miki miji na gari wanda zai baki kulawa fiye da wanda na ke yi miki fatan samu."

Mama ta ambata cikin murmushi.

Saida na gabatar da sallar azuhur sannan na zauna shafa mai, na yi kyalliya kamar ko yaushe mai sauk'i na sanya gown na yi rolling da k'aramin gyale na fito na samu Mama ta kammala har ta killace na Uncle a kula mai kyau, jug na d'auka na zuba masa zob'o wanda Mama ta dafa ta saka a fridge kafin ta zuba a robobi. Kayan da zai k'ara masa d'and'ano na zuba na jerasu a kwando.

"Mama bari in mik'a masa."

"Tam ki dawo lafiya."

Baba maigadi na bawa ya tafi kai masa, ina tsaye ya dawo na yi masa godiya na juyo idanuna ya sauka kan Aliyu zaune a saman lipan d'insa sabuwa dal, nuno shi na yi da yatsa ina murmushi ya ko zabgomin harara dafe bakina na yi ina dariya k'asa-k'asa.

"Nagode Khadija."

Da sauri na kalle shi jin voice d'insa irin na mai fushi.

"Na kiraki baki d'auka ba, na zo gidanku kin sanyani gaba kina dariya saboda ni talaka ne banda mota da kyau, balle uwa uba kud'i to nago...

"A'a Aliyu kada kayimin wannan fahimtar tun bamuyi nisa ba."

Na katse shi cikin tsare gira.

"To wacce kike so inyi miki Khadija?"

"Ta karamci mai cike da yarda, ban son sake jin ka ambatamin kalamai masu nuni da bambanci tsakanin talaka da mai kud'i saboda ka san dukkanninsu bayin Allah ne, ba wanda yafi wani a gurinsa sai wanda yafi jin tsoronsa. Sannan kiranka na gani ban d'auka ba ne sabida ina son kammala aikin dake gabana yanzu kuma ina yiwa fushin da kayi dariya ne sabida baiyi maka kyau ba amma duka Ina neman affuwa insha Allah zan kiyaye gaba."

Murmushi Aliyu ya saki cike da samun natsuwar ruhi.

"Ya wuce dama ruhin Aliyu batayi fushi da abincinta ba."

"Ka ganka da iya tsokana."

"Ba tsona ba ce Matar Ali ke abaincin ruhina ce."

"Uhm ka dai bani kunya please."

"Kunya adon Mata, right?"

Harara na cilla masa batare dana amsaba.

"Affuwan na daina baki kunya kinji matar Ali?"

"Aliyu bakajin magana ko?"

"Bari in wuce zuwa yamma zan dawo dama yanzu na biyo zuciyata ce kuma na gamsu da abinda nagani, bye."

Da kallo na raka shi har ya b'acewa ganina.

"Uhm Aliyu kenan, shima salonsa kusan d'aya ne da Uncle, oh ni Nana Khadijatu ta haka soyayyar ta zomin? Allah ka zab'amin mafi khairan cikinsu."

"Amin Aminiyata."

Na tsinkayi muryan Fanta daf da kunnina, juyowa na yi ta saukemin duka a shoulder cikin cewa "Baki da kirki Deejah."

"Me na yi kuma?"

"Wato maimakon ki kawoma Uncle abinci da kanki sai kika aiko masa Baba maigadi."

"Fanta tsoron had'uwa da Aunty Nafisa na ke yi."

"To ai ko yanzu baki tsira ba dan shi ya aikoni da kizo da kanki."

Idanu na zare ta kwashe da dariya.

"Dalla matsoraciya, Allah ya ceceki ni Baba ya gani na amsa na kai masa falonsa saida na zuba masa ya soma ci sannan na fito."

"Nagode Aminiyata."

"Bakomi, muje na ci nawa dan ina zubawa Uncle ina had'iyar miyau."

Murmusawa na yi muka jera, muna shiga da Beebah mukayi arba zaune saman tabarma tana cin tuwo.

"Dama ba gida kikaje ba?"

Na jefo Mata tambayar.

"Eh naje layin baya ne na siyo mana fruit, ai ina kallonki kina soyayya na yi hanzarin shigewa gida dan bansan ya ganni."

"Saboda me?"

Cigaba da cin tuwonta ta yi kamar batajini ba. Wanke hannu Fanta ta yi da zauna sai nima na wanko, Fanta ta zubo mana muka soma ci, ina hankalce da Beebah yarda ta ke kallona ta gefen ido tana sakin murmushi.

"Da alama sister Beebah na son in daina kulata."

Na ambata cikin doka mata harara.

Dariya ta kyalkyale da shi wanda ya janyo hankalin Mama tafito a hanzarce.

"Me ya faru Habiba?"

"Mama bakomi kawai nishad'i na ke ji."

"To Allah k'aro nishad'i mai sanya nutsuwan ruhi."

"Amin Mama."

Fanta da Beebah suka amsa yayin da ni kuwa na yi tamkar bana wurin.

"Uwata ya dai?"

"Lafiyalau Mama."

"Anya? Nasan kina tare da damuwa."

"Mamana ina sonki matuk'a."

"Uwata kenan mai wayon sha-shantar da abinda na ke son ji."

Tashi na yi na kama hannunta muka shige d'akinta, cikin bedroom muka nufa na zaunar da ita a bakin gado ni kuma na janyo stool na zauna a gabanta, na marairaice fuska sannan na soma magana "Mamana bisa alamu hasashenki akan Uncle zai tabbata, ina jin tsoron abinda zai biyo baya gashi ruhina ta kamu da son Aliyu kuma bana son in bijirewa buk'atan Uncle ko dan tarin alkhairorinsa garemu sannan ina matuk'ar tsoron zaman kishi da matarsa. Mama dan Allah ki taimakeni ki sanar da Uncle ya yi hak'uri, nasan idan kika fad'a masa zai fahimta sama da ni."

Tsawon mintoci uku Mama ba ta yi magana ba.

"Mama nasan tunaninki Uncle zaifi Aliyu rik'eni tunda ya fisa sanin waceceni sai dai ina son kiyi nazarin rayuwar da zanyi a gidansa na rashin 'yanci da tarin fargaba."

"Uwata ko shi Alhaji Muhseen baisan komi akanki ba, abinda na ke so da ke shi ne ki barwa Allah zab'i wata k'ilama ba mijinki cikinsu.

"To Mama."

"Uwata ki kulasu duka, ki basu soyayyarki dai-dai misali, kada ki zafafa son wani cikinsu wanda rabuwarku zai zame miki k'alubale. Aliyu da kike ambata kina sonsa ban amince ba."

"Mama ban fahimta ba."

"Nufina ban yarda kiyi masa wannan k'aunar da na gani a idanuwanki ba tun bai soma takowa k'ofar gidanku zance ba sannan bama shi ba kowaye ya furta miki kalman k'auna ban amince ki zurfafa son sa ba, kiyi masa dai-dai misali da fatan kin fahimce ni?"

"Eh Mama."

"Da kyau tashi kije wurin su Fanta kada abarsu su kad'ai."

Fitowa na yi na samu sun gyara wurin sun shige d'akina, ina shiga Fanta ta rangad'a gud'a na ja baya idanu waje suka tafa ita da Beebah, tsaki na ja cikin raina na janyo stool na zauna na zuba musu ido, iska Beebah ta huramin na kullesu da sauri.

"Wani sak'o Uncle ya sanarmiki ki fad'amin?"

"Yana muradin da ki zama matarsa ta sunnah uwar d'iyoyinsa, kin amince?"

Numfashi na sauke ahankali.

"Zanyi tunani."

"Ai baki isa ba, eh kawai na ke son ji yanzun nan ba sai anjima ba."

"Kina farin ciki da ayiwa yayarki kishiya kenan?"

"Eh."

Ta amsamin kai tsaye.

Murmushi na yi dan sam banji mamaki ba.

"To ni ina tsaron kishi da ita, ki sanarwa Uncle da haka."

"Ma'ana dai kin amince zaki auresa Aunty Nafisa ce matsalarki?"

Dan Allah Beebah ki fahimceni mana, ke fa Aliyu ya aiko amma yanzu kinayi tamkar baki san komi ba."

"Ke d'in allurar cikin ruwa ce mai rabo ka d'auka dan haka Deejah sanin mijin sai Allah, wata k'ila daga Aliyu har Uncle ba mijinki cikinsu sai dai abinda na ke son ki sani shi ne mace bata tsaida mutum d'aya ta ce shi zata aura, tana iya yin samari sama da biyar kuma sai kiga wani daban ya fito ya aureta, yanzu dai ki nemi zab'in Allah cikinsu dama wanda zasuzo nan gaba."

"Tabbas maganar Sister Beebah gaskiya ne insha Allah Deejah sai kin had'a goslow a k'ofar gidan nan masu gulman kin rasa masoyi suji kunya."

"Uhm Fanta kenan, kidai tayani addu'ar samun miji nagari kawai, masu gulma kuwa banda lokacinsu, su aiki ya sama."

"To Allah ya bamu baki d'aya."

Beebah ta ambata a hankali.

"Amin."

Muka amsa atare da Fanta.

"Deejah wallahi inajin murna ainun ganin yarda kika soma tara masoya damuwarki akan rashinsu ya zamo tarihi."

"Nagode Beebah, ni kaina ina cike da mamakin lamarin."

"Komi fa lokaci ne K'awata."

"Haka ne kam Aminiyata."

"Aha ansoma nuna wariyar ba."

Beebah ta ambata cikin zabgo musu harara.

Dariya muka sanya har ita.

"Yau su Bintu na hanya ya kamata in dafa musu abincin tarba."

"Yes Deejah tafi mu san abiyi musu dan yau Aunty Nafisa bata cikin kuzarin dafa komi shi yasama inaga Uncle ya ce kiyi masa girki."

"Sabida ta ganni tare da shi ko?"

"Oho mata dai."

Fanta ta amsamin cikin zunkud'a shoulder. Kafin in sa ke magana ta fice. Beebah na kalla ta saukemin murmushi ta ce "D'azun Aunty taga fitarku ta yi nufin zuwa ciwa Mama mutunci kafin ta iso Fanta ta kirani sai na tareta a waje na maidata gida amma dan Allah kada hakan ya baki tsoro domin hausawa sunce auren da aka soma samun rikici yafi k'wari."

"Uhm wannan kawai zance ne ba tabbas a cikinsa."

"Ni dai na rok'eki domin Allah da Manzonsa kada ki bijirewa muradin Uncle."

"Beebah na rasa gano abinda yasa kuna 'yan uwa na jini ga Aunty Nafisa amma kuke goyon bayan mijinta da yayi mata kishiya."

"Tashi muje idan su Bintu sun iso sai muyi maganar a gabansu kiji kalamin bakin kowa akai, ina ganin zakifi gamsuwa."

Tashi na yi muka fito daidai lokacin Baba na shigowa, dank'e hannuna Beebah ta yi jikinta na rawa, kallonta na yi na kuma sauke idanu kan Baba wanda ya shigo a fusace

"Innalillahi wa Inna ilaihin."

Na ambata a hankali.

"Ubanki kika tsaya kallo mai siffan aljannu?."

Na tsinkayi muryan Baba saman kaina, ja baya na yi cikin girgiza kai.

"Hurera!"

Ya kwallawa Mama kira. Bata amsa ba ya kuma kiranta, sai da Baba ya kirata sau hud'u sannan ta fito tana murza ido bisa alamu barci ta soma, kallon da Mama ta saukemin yasa na ja hannun Beebah muka shige kitchen wurin Fanta.

*TALLA.*

*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*

Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/23, 2:05 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Safiyya (Mrsjmoon)

E.W.F.

Page 11.

"Kiyi hak'uri Deejah amma mahaifinki ya cika fad'a, wallahi tsoro ya bani ganin yarda ya shigo a fusace sannan d'azun da safe na sunkuya ina gaisheshi amma ko kallo ban isheshi ba, na yarda wannan halayyan nashi ya sanya baku jituwa."

"Sister Beebah halayyan Baba halitta ce dan koni ada tsoronsa na ke ji amma tunda na fahimci haka Allah yayoshi sai na saba kamar yarda Aminiyata ya bi jikinta."

"Uhm ku mumaida hankali a kan aikinmu kunsan kowa abin da tafi so za'a dafa mata."

Na datse zancen saboda yarda na ke jin b'acin rai kuma ban son su gano hakan.

"Hakan ba zai yiwuba kawai muyi musu girki d'aya wanda zasuci baki d'ayansu."

"Nima hakan naga yafi Sister."

"Ki tafi ku huta insha Allah kafin su iso na kammala komi."

Na kuma ambata cikin tsare gira.

"Baza'ayi haka ba Fanta tafi ki d'ebo komi a gida kizo ayi amfani da shi."

"Idan ta d'ebo kada tazo dashi gidan nan, insha Allah bazamu rasa abin yin amfani ba duk da muna talakawa."

"Ya Salam, please Deejah ki fahimce ni mana."

"Beebah dan Allah kiyi shiru muyi abinda ya kamata dan banjin ina da natsuwar fahintarki ba."

"Tam na yi shiru Aunty."

"Ko ba Aunty ba."

Dariya suka kyalkyale da shi ganin yarda na tsuke fuska.

"Fushin baiyi miki kyau ba Aminiyata."

Murmusawa na yi.

"Yawwa ko ke fa sai annuri na kuma cika kyak-kyawar fuskanki."

"Ban da zagi fa Aminiyata."

"Allah ba zancen zagi domin ke kanki kinsan mai kyauce tamkar tauraruwa cikin dubbab taurari."

"Kinyi na kud'in ki wallahi."

"Ai gaskiya Fanta ke fad'a ke d'in tubarkallah masha Allah, tamkar 'yar buzaye ko Shuwa Arab."

"Eh wallahi Sister Beebah."

"Dan Allah ku barmin kunnuwa su huta."

"Ank'i sai kin sanar da mu nasabanki daga wani yare kika fito."

"Yaren Baba mana Hausa Fulani."

"Amma kinsan Allah ko a farce baki kama da Baba haka 'yan uwanki duk kinfisu kyau duk da suma da farare cikinsu amma naki hasken na dabanne."

"To ni bakuga yarda Mama ke da haske ba, ita na d'auko."

"Eh gaskiya hasken Mama kikayo aminiyata amma duk da haka kinfita fari."

"Eh nafita kam amma ai munyi kama."

Karkacewa Fanta ta yi tana k'aremin kallo na kai mata duka ta ja baya cikin cewa "Kuna kama a halittan idanunku da kyawun diri amma in banda nan ban hango ta inda kukayi kama ba."

"Kai Fanta ki duba dai da kyau hatta madai-daicin bak'insu iri d'aya ne."

"Kai Beebah a she haka kika k'arewa Mama kallo?"

"No a photonku na tantance."

Banza na yi da su ganin in na biye musu ba zamuyi abinda ke gabanmu ba.

Bintu Alale, Firdausi jelop d'in macaroni jelop sai Safina shinkafa da miya. Komi dai-dai mukayi yarda bazai zamo anyi albazaranci ba. Mun jere abincin a d'akina muka zauna muna hira Fanta ta kalli Beebah ta langab'e kai.

"Me ye malama?"

"Dan Allah Sister idan ya iso ki kulashi kinga domin ke zaizo"

"Wai Yaya Abdallah zai kawo su?"

"Eh."

Dogon tsaki Beebah ta ja tare da mik'ewa zata fice.

"Kada ki yi haka sabida ance bak'onka Annabinka."

"Fanta wallahi inda na san munafuncin da kuka k'ulla kenan tabbas da bazan jirasu ba zan wuce amma ko yanzu ba zaku sami abinda kuke so ba na rantse."

"Eh mun yarda amma dan Allah ki kulashi cikin walwala in ya wuce sai kiyi mana duk masifar da kika so."

Shiru ta yi, Fanta ta janyo hannunta ta zaunar gefen katifa tana yi mata magana a kunni, tagumi ta zabga na yi gyaran murya ta kalleni na girgiza mata kai, murmushi ta saukemin wanda a fili na dole ne saboda hakan ya bayya a saman fuskanta.

"Me ke faruwa, kuke 'yan b'oye-b'oye?"

Na cillowa Fanta tambayar duk da shiga lamarin rayuwar mutane ba halina ba ne.

"Gata nan kiyi mata nasiha ta daina wulak'anta mana Yaya, saboda shi tak'i bin su Bintu sada zumunta shi ne ya biyosu domin ya ganta dan ta yanke alak'a dashi tsawon wasu watanni, ta daina d'aukan wayarsa tayi blocking nasa a k'arshema ta saka shi a black list, in kuma ya kirata da wayar Mamansa ko k'anninsa tana jin muryansa zata kashe wayarta baki d'aya."

"Innalillahi, me ya yi zafi haka?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull