
Post
FUSATACCE PAGE 3-4
.....he was breathing heavily from his mouth, he was already accusing CP of bribery, but it is not confirmed now, but there is no problem. His true color was "he was driving and he was confused" and finally he picked up the phone and called another number "double taps" It was taken as saying "*said you monster Arnah*!.....pls Jamil" I want to know which hospital Mohd Idris is waiting for, what room and everything?? I will give you 10 minutes to call me" saying that he hung up the phone and continued driving his face" He was thinking when our country will settle and improve??....check! His thoughts stopped when he arrived at the door of *sheikh mlm Sulaiman's* house.
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🔥 FUSATACCE 🔥👮♂️
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written By Mommyn fareesa
*Dedicate* to
Hjy maimuna Umar sadeeq (mommy) Ina Alfahari dake 😍❤️
*Dominki* Hjy Salma Abbah nijar❤️ d'aya tamkar da dubu Allah yashiga lamarinki tawan 👏
Special gift for all members of my groups🥰💔 Ina yinku over guys
Tukwici ne gareki *hajara Ibrahim dallatu*😘🥰 bazan tab'a mance Alkhairin kiba "Alkhairin Allah yakai miki har bisa gadon baccin ki
Free page 3&4
.......cike da nutsuwa da nuna halin ko in kula da kowa ya fito daga cikin get d'in gidan nasu"bebi takan neman driver ko wani ba ya shiga cikin had'ad'd'iyar motarsa dake fake daga wajen get"sai bayan ya shiga ya manna Blue tooth A kunnansa ya dannama sergeant dikko kira"bugu ukku ya d'auka da ladabi yana fad'in yallab'ai barka!....Ina wannan yaron?"ya furta cikin Arrogant voice...uhmm"dama....dama whattttttttt?ya katsesa A zafafe" Iyayensa sunzo yana Asibiti yanzun hakan"kuma dama CP yace"idan ka iso ka samesa office....d'it! *sudais mashee* ya kashe wayar yana fesar da huci me zafi daga bakinsa"dama tuni yake zargin CP d'an cin hancine be tabbatar ba sai yanzun"Amma babu matsala bazai neme saba"yakuma san waye guy d'in da iyayensa"har zuwan su gidan su wajen Abbie jiya duk yaron sa Umar yamasa bayanin komai"bece komai ba "zai nunama Alh idris marafa cewa ba'a ja da hukuma"CP kuma yana nan zaune wani case me girma zai taso ya d'ora sa Akai Anan zai nuna Masa Ainahin true colour d'insa"yana driving d'in yana sak'a da warwara"daga k'arshe ya koma d'aukar wayar ya kira wata number"bugu biyu Aka d'auka da cewa"*saida kai dodon Arnah*!.....pls Jamil"inason sanin wace Asibiti mohd Idris marafa yake,da room da Komai??na baka 10 minit ka kirani"yana fad'in hakan ya yanke wayar yaci gaba da driving d'insa "fuskarsa A gimtse yana tunanin yaushe k'asar mu zata daidaita ta gyaru??....cak !tunanin sa ya tsaya sakamakon isowarsa daidai bakin k'ofar gidan *sheikh mlm sulaiman*"yanata cin magani yayi parking ya fito rik'e da leda yana tunanin ya shiga gidan kansa tsaye koya turo Amasa sallamah da mlm?? yana wannan tunanin ya lura da wani yaro zai wuce"da hannu ya kirashi yana nufar gefen k'ofar shiga soron gidan"yaron ya tsaya nesa kad'an dashi yana kallon fuskarsa da kayan jikinsa"yana yamutsa fuska cikin wannan arrogant voice d'in nasa me razana marar gaskiya yace"jeka ce Ana sallamah da mlm"bah musu yaron ya wuce ciki"be jima ba yadawo yana kallonsa yana fad'in Ance wanene?"yayi shiru"kaji Ance wanene?"ji yayi kamar ya mari yaron"saidai dukda hakan saida ya hararesa kafin yace"kace sudais ne daga damare polo"da gudu yaron ya koma ciki"shi kuma yaja tsaki yana duba wristwatch d'insa"jifa jifa yana lura da masu wucewa na kallonsa"Ahaka yaron ya fito yana fad'in Ance ka shigo"be kula yaron ba ya nufi cikin gidan da sallamah sau biyu kamar baya so"mamah dake tsakar gidan zaune saman tabarma ta Amsa da kulawa da sakin fuska" tana nuna Masa kujerah y'ar tsugunne dake Ajiye "saida ya fara gaisheta kafin ya zauna yana fad'in Abban na ciki ne?"Eh bara na Masa mgn yasu hajiyar taku?"lafiya qlau suke"to Masha Allah"ta fad'a tana k'ok'arin tashi"hakan yayi daidai da fitowar imaan daga cikin parlourn su"kanta babu d'an kwali doguwar rigar Atamfa ce bubu jikinta...gabanta yayi mummunan fad'uwa data lura da mutum zaune yayi k'asa da kansa"ga wani irin fitinan nan k'amshi daya cika tsakar gidan nasu....lolx"da sauri tayi Azamar komawa cikin parlourn"mamah ta dakatar da ita da cewa"imaan miye haka?"Ina d'an kwalin ki?tayi shiru Adaidai lokacin sudais ya d'ago kansa cikin rashin sa'a ya kalleta suka had'a ido"yayi saurin had'e rai yana kauda kansa gefe "sosai yaji haushin yarinyar sbd ya tsani yaga mace babu d'an kwali....imaan kuwa daburcewa tayi ta kasa cewa komai "ta koma ciki da sauri"sbd ta sako hijab "mamah ta biyota tana fad'in sbd bakida hankali ba zaki gaida bak'o ba?"toni mamah bansan dashi bafa"to yanzun Ai kin ganshi kin san dashi ko?maza ki saka hijab kije ku gaisa yayan kine d'an wajen Alh kabeer mashi Aminin mahaifin ki "k'in mgn tayi ta wuce k'uryan dak'i"mamah kuma ta fita....imaan badan tasoba ta fito daga cikin dak'in sanye da dogon hijab red colour wacce tayi matuk'ar yi mata kyau"haka kawai taji bata son kallonsa"ga k'irjinta nata bugawa "dama tasan d'an gidan Aminin mahaifin nata police ne Amma ta mantashi sbd ba zuwa gidan su yake ba"saiya jima be zoba.....inda mamah ta tashi Anan ta nufa ta zauna tana fad'in sannu da zuwa Ina kwana??yayi shiru"da mamaki ta d'ago kanta tana koma furta Ina kwana cikin d'an bud'e murya "sbd ta zata Kobe jiba"Amamakin ta ta gansa zaune fuskarta babu walwala ko kad'an yana dak'ilar wayar dake hannunsa"Aranta tace" Masha Allah yanada kyau.....mittsuwww! yaja tsaki wanda yasa imaan farga da Abinda tayi"ta kauda kanta tana tunanin meke damun sa wai?sosai ranta ya sosu tana tunanin kawai ta tashi ta kama gabanta saiga Abbanta da mama sun fito daga cikin dak'in Abbun "saita tashi tsaye ba tace komai ba ta koma ciki tana tunanin meke damun wannan mutumin ?"ko kuwa sbd yaga sunada kud'i yanada matsayi shine zai mata tsaki sbd ta gaida shi kawai??saita girgiza kanta tana fad'in Allah ya kyautah ta zare hijab d'in jikinta"Adaidai lokacin mamah ta shigo cikin dak'in fuskarta A sake tace"Ashe Alh kabeer d'in ne ya Aikosa ya kawo gudun muwarsa ta biki"Allah sarki! cewar imaan sbd haka kawai taji bata son zancen"ga wani irin zafin sudais d'in tanaji"tasan mahaifin sa mutumin kirki ne babu irin taimakon da baima mahaifin suba....bayan haka dama tasan beda fuska ga mutane kamar yadda taji Abakin yayanta sunusi"tana kallon mamah na murnanta sbd kud'in da suka samu zasu ishesu su ida siyen Abinda basu siya ba"kuma yau dama za'ayi jere....mamah! ta fad'a fuskarta babu walwala tana zama gefen bed"mamah dake tsaye ta kalleta batace komai ba "dama ya kirani jiya Akan za'a yi dinner....sai kika ce Masa me?"cewar maman tana kallonta da mamaki"bazai yuyu ba nace"hakan shine daidai"zan sanarwa Abban ki"yanzun dai zancen zuwa jere da k'arfe 2 Akeyi "daga haka mamah ta fice daga cikin dak'in.....
***** ***** ***** ***** zaune yake saman bed d'in ya jingina bayansa Ajikin pillow "saman cinyarsa plate d'in Abinci ne"mutum biyu na zagaye dashi"kamar daga sama sudais mashee ya banko k'ofar dak'in ya shigo babu ko sallamah "yana rik'e da wani file A hannunsa da POS"kusan gaba d'aya mutanan dake cikin dak'in suka bishi da kallon mamaki "mohd dake zaune gabansa na fad'uwa yayi saurin janye plate d'in Abincin dake saman cinyarsa yana kallon mutumin naku "da babu wata Alamar dake nuna yasan ragi ko ragowa saman fuskarsa....bawan Allah lafiya dukda kana hukuma ka shigo mana kai tsaye??"cewar lawal yayan mohd"sudais ya Masa banza cike da nuna isa ya matsa gefen bed d'in yana damk'o hannun mohd da k'arfi har saida yasaki k'ara"be saki hannunsa saida ya dangwala sa saman file d'in....wai dama shine ya dakeka?"cewar lawal da mamakin jin kan guy d'in...*nine ko zaka rama Masa ne?* yayi maganar yana zaro idanunsa dake jawur tare da wullah ma mohd POS yana cewa "zaka saka kud'in tara 7k na rashin number da baka dashi ga mashin"bayan haka nanda 2 days kakai kanka ko naje har gidan iyayenka na kamaka"and last dole ka saka number d'in mashin"yana fad'in hakan yaja tsaki yana hura hanci"yayinda lawal tsabar mamaki da takaici ya kasa mgn"wanda suke tare dama yaron su ne bece komaiba"mohd kuwa yajima da tsorata da sudais" hakan yasa ya zaro ATM card nasa yasa musu kud'in be furta ko A ba"dukda ya tsorata dashi baya jin zasu barsa yayi Masa irin haka "kuma har yana gadaran zai kamashi....motsin d'aukar POS dake gefensa da yayi shine yasa yadawo tunanin sa"yana kallonsa ya fice daga cikin dak'in "lawal ya sauke numfashi yana fad'in uban me wannan police d'in keji dashi?"miye gadararsa?hmm! yaya lawal gabansa ya kamata ka fad'i hakan"ban tab'a ganin mutum me fushi da fusata irin saba"tabbas ba zamu barsaba..... mittsuwww! bana son fitinah da kowa Muna Asibiti kuma gashi matsayin hukuma shiyasa na barsa"cewar lawal cikin jin haushin mohd"wanda yayi shiru yana tunanin idan daddyn su yazo zai sanar masa da zancen su d'auki mataki..... Koda sudais ya baro Asibitin Kai tsaye police station d'in yayima tsinke"dukda ya kasance FUSATACCE"Amma yau fusatar tasa tafi ta kullum"hakan yasa kowa yayi biris dashi daya shiga office"yana zaune hakimce saman kujerah tana juyawa dashi ya kama idanunsa ya rufe"t shirt fara jikinsa da wondon yunifoam "ya cire hular da rigar "ga cup nan daya gama shan tea da ledar cake"yaci ne sbd bak'ar yunwar dake damunsa....k'arfe 10:38 am haka Agogon dake cikin office d'in ta nuna"Adaidai lokacin CP ya shigo cikin office d'in da sallamah"Sarai sudais naji Amma yayi kamar be jiba"ko motsi yak'i yi"CP yabi zara zaran eye lashes nasa da kallo"sunyi wara wara kamar An zana su"tun kallon farko daya Masa yasan ba bacci yakeba sbd yasan halinsa in and out "hakan yasa yad'an daki table d'in gabansa yana zama kan kujerah"da k'arfi ya bud'e idanunsa dake jajir ya watsasu saman fuskar CP dake nuna Alamar rashin gaskiya "saiya mike tsaye ya Sara Masa kafin ya zauna yana jawo laptop....inason ka bani Aron hankalinka Anan "yayi shiru be tankaba"nasan kasan waye Alh idris marafa A garin nan?"yasan manyan shugabanni da y'an siyasa"idan kace kayi takun sak'a dashi wlh kaine A ruwa"yaka mata ka yanke Komai game da yaronsa"musammun tunda kaje Asibiti yayi signing ya biya kud'in tara"kaga idan sun so zasu iya k'ararka Akan ka dakesa har hakan ya zama sanadin kwanciyarsa Asibiti.....nawa mahaifinsa ya biya ka?ya furta cikin kwanciyar hankali babu tsoro ko shakka Atare dashi"yana cigaba da danne danne A computer.....what? Kasan me kake fad'a?"harka isa ka fad'amun wannan maganar....na fad'a sir! idan ka tashi ka saka Akoreni kafin na Ajiye takardan barin Aiki "daga k'arshe daga sama idan sun bak'aci jin dalilina"saina Kora musu bayani ko?"ya fad'a yana d'age kafad'a tare da mik'ewa tsaye ya d'auki rigarsa ya saka duk CP yana zaune "bayan fad'uwa babu Abinda gabansa keyi"yasan muddin daga sama Aka gane yana karb'an cin hanci Komai zai iya faruwa....ka gane me nake nufi mana sudais! be tsaya sauraren saba cike da zafin rai da fusata ya d'auki wayoyinsa ya fita daga cikin office d'in "yaci burin saiya kunnowa CP wutar da baya iya kasheta.... zaune imaan suke tare da k'awarta fareedah Acikin parlourn gidan su"tayi shar da ita sbd dilkan da aka mata da lalle"basu jima da dawowa daga wajen gyaran kai ba"mlm kuma ya sanar mata babu wata dinner da zataje"idan family d'in Abdul Raheem zasuyi suna iyayi bazai hanaba Amma ita baza taje ba"ta kuma kirashi ta sanar masa ya Amsa badan yaso ba"fareedah na murmushi ta kalleta tana fad'in Amarya me capacity! Nasan Abdul naki ya k'agara gobe tayi A d'aura ko?hmm! kamar ya hmm? nifa naga ko sakin jikin nan ki masa shagwab'a bakyayi....imaan na k'ok'arin mgn Kiran Abdul ya shigo cikin wayar ta"tana d'an murmushi ta d'auka da sallamah"daga d'ayan b'angaren be Amsa ba yace"kina gida? Eh"okay fito Ina son mgn dake Ina daga waje"daga haka ya kashe wayar"ta kalli fareedah tana fad'in tashi muje *my mine* yana waje"Ah Ah kije dai zan fito daga baya nima da 6 tayi wucewa zanyi gida "harara imaan ta watso mata tana mik'ewa tsaye ta gyara veil d'in saman kanta"ba k'aramin kyau Abayar dake jikinta tayi mata ba"ga k'amshi me dad'i datakeyi wanda ya zauna Ajikinta"A hankali ta fito daga cikin dak'in "mamah da mak'ota da wasu daga cikin dangi nata girke girken tarban bak'in gobe "bayan ta sanarwa mamah zuwansa ta fito k'ofar gidan......yana zaune saman motarsa yana girgiza k'afafuwansa "yana sanye da milk d'in shadda data dace da Aiki me kyau"ya Aza hula k'ube "yana yin shekaru be wuce 32 yrs"d'an boko ne kuma guy ne bazamu kirashi me matuk'ar kyau ba "baza mu kirashi da mummuna ba"tunda ta fito ya bita da kallo tun daga sama har k'asa "ba k'aramin kyau ta mishi ba"cikin siririyar muryarta ta masa sallama tana sunkuyar dakai k'asa "ya diro daga saman motar yana Amsawa tare da cewa"ya hidima da shirin zuwan ki gidana?"tayi d'an murmushi batace komai ba"yayi gyaran murya"ta d'ago kanta ta kallesa"saita kauda kanta k'irjinta na bugawa"I'm sorry to say imaan"nazo muyi mgn Akan kayan jere"last time na sanar miki bana buk'atar komai naku sai ke"kika nuna mun ba haka ba"sai yanzun da Aka gama jere"naje da family nah suka gani" wlh saida naji kunya"so na saka An kwashe komai"yanzun haka suna hanya za'a maido kayan"gobe da safe in sha Allah daga company zasuzo su shirya miki komai Agidan ki"so kiyima su Abbah bayani sbd karsu d'auki hakan da wata manufa"nayi ne sbd banaso kowa yasan cewa kedin ba wata bace"be rufe bakiba motar kayan ta iso gefen su tayi parking.....✍️
Sharhi😎
Bazan ce komai ba Amma wannan book d'in me capacity ne kuma na masu capacity 💃🏻💃🏻
wannan book din na kudi ne babu regular Vip 700 post sau biyu Arana special grp 1500
Mutanan PC Vip pc vip 1k Special PC 2k
zaku biya kud'inku ta wannan acc number 8100084251 Nabila Aliyu monie point shaidar biya ta nan👇 08100084251 ga wanda acc nasa be nuna monie point saiya saka tanan 2230373842 Nabila Aliyu uba bank
ku sani ba'a turo card saita acc number za'a biya
Bana son kira dan Allah❌❌ ta what's kawai za'a mun mgn ✔️
y'an nijar ku tuntubi wannan number +227 88 01 90 50
Vip grp 500f Special grp 1000f