
Post
FUSATACCE PAGE 1-2
"Just like that, when a young man came up, he was wearing a modern rubber mask. It was so beautiful and it caught your attention. But his mask didn't have an Ajiki number." The security officers here were trying to stop him. The machine wearing a bowler hat ran in front of him with a kind of crazy speed" that made all the attention of the people come back to themselves "some of the security officers I like it when I see the guy with a hard eye" they have enough to feel the heat and anger that they will see him..... full of anger and anger he stopped the machine and made a kind of stand up and took off the bowler hat on top of his head" His beautiful face is full of kisses and tears, "but there is no radiance on his face" as if he had been sent a message of death, his face is like this, his eyes are down to his mouth and he is panting, there is no sign of loss or loss.
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🔥 FUSATACCE 🔥👮♂️
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written By Mommyn fareesa
*Dedicate* to Hjy maimuna Umar sadeeq (mommy) Ina Alfahari dake 😍❤️
*Dominki* Hjy Salma Abbah nijar❤️ d'aya tamkar da dubu Allah yashiga lamarinki tawan 👏
*GODIYA*
Alhmdllh Ala kully halin" godiya ta musammun ga Allah S W A daya nunamun na fara wannan littafi lafiya"yah Allah yadda na fara lafiya Allah ka bani Aron rai da lafiya na gama lfy....
*GARGAD'I* wannan littafin k'irk'irarran labarine banyi shi dan wata kodan waniba idan yayi daidai da rayuwar wasu Arashine"Aguji sauyashi ta kowace siga sbd hakkin mallakata ne....
Special gift for all members of my groups🥰💔 Ina yinku over guys
Tukwici ne gareki *hajara Ibrahim dallatu*😘🥰 bazan tab'a mance Alkhairin kiba "Alkhairin Allah yakai miki har bisa gadon baccin ki
Free page 1&2
*YOLAH STATE* Anguwar damare polo....!!"misalin k'arfe 8:12 na daren yau Alhamis "kusan gaba d'aya saman babban titin Anguwar polices ne tsaitsaye suna tsayar da Ababen Abin hawa"suna Aikin su yadda ya kamata"Adaidai lokacin wani matashin saurayi ya taho Aguje saman mashin nasa roba roba irin na zamani me matuk'ar kyau da d'aukar hankalin me kallo"saidai mashin d'in nasa babu number Ajiki"jami'an tsaron dake Anan na k'ok'arin tsayar dashi"yak'i tsayawa saima k'ok'arin bita gaban su daya keyi zai wuce sbd beson ya tsaya"saidai duk yadda yaso ya wuce hakan be samu ba"sbd wani mutum dake saman mashin bike sanye da hular kwano yasha gabansa da wani irin mahaukacin gudu"hakan yasa duk Attention d'in mutane ya dawo kansu"wasu daga cikin jami'an tsaron najin dad'in idan guy d'in naji da tsaurin ido" to sunada isasshen dake ji da zafin Kai da fusatar da zaiyi musu ma ganinsa.....cike da Isa da zafin rai ya kafe mashin d'in yayi wata iriyar shegiyar tsayuwa yana zare hular kwanon dake saman kansa"Atake yalwatacciyar doguwar kyakykyawar fuskarsa dake cike da kasumba da saje ta bayyanah"saidai babu wani Annuri saman fuskar tasa"tamkar An Aiko Masa da sak'on mutuwa haka fuskar tasa take"idanunsa yayi k'asa dasu bakinsa A tsuke yana huci"babu wata Alamar ragi ko ragowa Atare dashi"yana sanye da wondo 3 quarter sky blue da fara k'ar d'in t shirt "wacce ta fito Masa da shape d'in murd'add'an jikinsa"gaba d'aya wajen ya d'auki wani irin sanyayyan k'amshin turarukan jikinsa me kashe jiki da zuciya.....Afusace ya iso gaban guy d'in da Shima ya tsayar da mashin d'in nasa yana binsa da kallo da tunanin waye shi?"da har zai dakatar dashi bayan babu wanda ya isa cikin polices yayi Masa irin haka....*sakko*!ya fad'a cikin fusata da dak'ilewar murya yana d'ago kansa ya bud'e gaba d'aya idanunsa white & brown ya watsasu Akan *mohd Idris marafa*! wanda ke zaune saman mashin nasa.....be sakko ba sai kallo daya bishi dashi "Atake yaji shakkarsa da kwarjinin sa"saidai da yake yana ji da kansa sbd dukiyar da suke da ita"hakan yasa ya tab'e bakinsa yana zaro babbar wayarsa k'irar iPhone 17 pro Max"yana wani basarwa da Jin kansa Asama yace"*yallab'ai ga wannan saka Acc detels naka*!yayi maganar yana mik'a Masa wayar.....gaba d'aya k'ananun polices dake tsaitsaye suka bisu da kallon mamaki "sbd ganin Abinda mohd yayi da kuma yadda *DPO sudais kabeer mashi* ya karb'i wayar"saidai kusan kowa ya d'auke kansa sbd gudun kar suyi laifi wajen sa.....k'arar fad'uwar wayar da tarwatsewarta ya saka duk mutane suka bisu da kallo"DPO bebi takan wayar ba ya matso yana huci ya fisgo kwalar wuyan rigar mohd Idris marafa"cikin fushi ya fara jibgarsa kota Ina kamar Allah ya Aiko sa"Abin mamaki baya mgn"huci kawai yakeyi tamkar kububuwa"yayinda polices d'in dake wajen suka nufesu sbd ganin muddin idan suka barsa "yadda suka sanshi da fusata da zuciya zai iya kisan kai....da k'yar mutum ukku suka janye mohd da baya numfashi jini na zuba ta hancinsa da bakinsa"ko yatsan hannunsa be iya d'agawa"yayinda kusan mutum biyar suka rirrik'e DPO da idanunsa suka rine kamar garwashin wuta sbd ja "basu yadda sun bar guy d'in Anan ba suka bar wajen dashi"shi kuma ya fisge jikinsa yana nufar wajen machine nasa....sergeant dikko! ya fad'a cikin fusatacciyar muryansa me kauri da d'an k'arfi "saidai tanada dad'in Amoh da sauti"*ko Ina zakuje dashi ka tabbatar kun kaishi station"saiya fad'a mun da ubanwa da ubanwa ya tab'a bama cin hanci A cikin mu*!....yana fad'in hakan ya haye saman mashin d'in nasa yana hura hanci da fesar da huci me zafi "ya Aza hular kwanon saman kansa"da wani irin rikitaccen gudu ya fisgi mashin d'in yabar wajen ya nufi *Anguwar sanda*!....baya fitowa da dare "Ayanzun ma yazo ne ya karb'i sak'on Abbunsa daya Aikesa "shine ya biyo ta saman titin "wannan dalilin yasa ya samu hakan ya faru....zuciyarsa na zafi da rad'ad'i ya iso gida da k'yar"sbd yadda yake gudu na fitar hankali"tunma kafin ya iso bakin get me gadin gidan su, dake wajen get d'in ya hangosa"da hanzari ya bud'e Masa get d'in k'ofar gidansa dayake kwana"wanda gidan ke kallon gidan iyayensa"be tsaya ba ya wuce ciki ya jingine machine d'in gefen motarsa ya wuce interest d'in shiga cikin gidan.....Kai tsaye dak'in baccinsa me d'auke da royel bed da kujerah 3 seeter"sai tv stand da kayan kallo"sai k'ofar bath room "dak'in ya gaji da kyau kuma iya dak'in ne kawai Aka shirya cikin gidan"tsabar yadda ya hassala ko kaya be cire ba" be kuma cire takalmin saba yayi wulli da hular kwanon dake saman kansa ya kwanta saman luntsumemen bed d'insa A rub da ciki " time d'in k'arfe goma saura ya rintse idanunsa yana fad'awa duniyar tunani...... Ahankali Abbu dattijon Arzik'i yake sakkowa down stairs d'in "yana sanye da jallabiya milk da eye glass white medical"yana yin shekaru zaiyi kusan 60yrs"matarsa hjy sa'adatu na zaune cikin had'add'en parlour su tana kallon sunnah TV "kayan bacci ne A jikinta "kyakykyawar gaske ce farar bafulatana"yana yin shekaru zata yi 52 yrs"kallo d'aya zaka mata kasan ita d'in y'ar k'walisa ce"Abbu dake d'an murmushi ya k'araso ya zauna gefenta"Alh barka da fitowa "yauwa barkan ki"naji shiru babu ke babu sudais nace bara na fito na dubaku tunda nayi wankan"wlh lallan nan ne ya tsayar dani ban jima da cirewa ba"bara na kamaka coffee "okay sudais be shigo bane?"nifa rabona dashi tun safe daya fita cikin fushi"wlh lamarin yaron nan na bani tsoro Alh"daga kawai khaleesat y'ar wajen hjy zeenat tazo"na tarbe su muna gaisawa shine na Masa laifi nak'i kulashi na kula bak'i "shine fa ya tashi ya fita suna gaidashi ya musu banza"kullum zafin zuciyar yaron nan k'aruwa yakeyi Alh "baya fara'a da kowa sai yabi fuska ya tsuke"K'ato dashi yazo yamun kwance saman cinya"Anya Alh sudais yanada lafiya kuwa?....sa'adatu! yaro nah lafiyan sa qlau "beda wata matsala"Allah yayi shi FUSATACCE ne kawai be kuma da fara'a"bayan haka be damu da kowa ba" ya kanyi zumunci da gaisawa da mutane"so idan yadawo ki rarrashesa"bashida kani bashida k'anwa kinga shagwab'a na damunsa....hmm! Alh bafa ka son laifin yaron nan"ni wlh har tausayin wacce zata Auri sudais nakeyi"kinga mu Ajiye wannan maganar nama Aikesa maybe ki gansa yanzun ko kuma saida safe"daga haka Abbu yayi shiru yana d'aukar wayarsa da Abokinsa mlm Alh sulaiman ke kiransa"yayinda *Ammah*! ta tashi tsaye ta nufi kitchen"ba tafi mintina 5 ba ta fito daga cikin kitchen d'in rik'e da cup d'in coffee me zafi"tabi babban pic d'in sudais da kallo "wanda ke cikin parlourn kamar ka kirashi ya Amsa "dukda yana ga photo ne Amma fuskarsa A d'aure take"Ahankali ta zauna gefen Abbu tana tunanin Anya sudais ya tab'a Koda budurwa ne?"shekarunsa 34 A duniya bata tab'a Jin yace yana son wata y'a mace ba" saidai matan suce suna sonsa shi kuma yana yin biris dasu....wai Alh fara'ar me kakeyi ne?"ta tambaya tana Ajiye Masa cup d'in coffee d'in saman center table"wlh bikin y'ar wajen Alh sulaiman Abokina ya tashi"jibi ne d'aurin Auren.....haka kawai Ammah taji gabanta ya fad'i!"sai tayi d'an murmushi tana fad'in Allah yasa Alkhairi "yana k'ok'arin mgn sukaji muryan me gadi bakin k'ofar yana fad'in"Alh dama Ana sallamah dakai daga waje! yanzun dai k'arfe goma na dare rabe?"Eh Alh "kamarma cikin fushi bak'in suke"Abbu Aransa yace" Allah yasa ba wani babana ya dakaba!..... Ahankali yace Ina zuwa"Ammah tace"Alh dare fa yayi kuma inaga wannan fitinan nan be dawo ba"karka fita gaskiya"karki damu yanzun zan je nadawo"daga haka ya fita daga cikin parlourn....Alh idris marafa na tsaye shida wani mutum da Alama Abokin sa ne"fuskarsu A d'aure sunata hura hanci"sai body guards nasa guda biyu na gefe"Anutse Abbu ya k'araso da sallamah yana bin Alh idris da kallon sani"saidai babu wanda ya Amsa sallamar tasa cikin su"sai bece komaiba yayi tsaye kawai Yana so yaji dame suka zo"Alh idris yace"Ina fatan kaine mahaifin *sudais mashee*?" Eh nine lafiya?"yaron ka beda tarbiya! idan zaiyi takun sak'a kamata yayi ya samu daidai dashi sai yayi" Amma bada yarona ba" sbd ba sa'a sa bane"ya fishi komai"Akan me zai dakesa harya zubar masa da jini sbd yana matsayin wani banzan DPO?"da idan naga dama Ayau d'in nan zan saka A tsigesa daga matsayinsa"kasan kuwa koni waye?.....look bawan Allah! komai sudais zaiyi yanayi ne A bakin Aikinsa ko kuma idan Ammasa laifi"bana goyon bayan yarona "duk Abinda zaiyi zaiyine bisa gaskiya babu zalinci"so zancen kokai waye ne be dameni ba"zaka iya yin duk Abinda kaga dama"inaso idan har kakai wani Ayanzun kayi mgn Atsigesa daga matsayinsa....rabe rabe!! Cewar Abbu fuskarsa A d'aure"me gadi ya k'araso da sauri"karka koma barin irin wa'annan mutanan na zuwa mun gida..... mittsuwww! zan nuna maka Asalin waye ni daga Kai har yaron naka"har Aikin da yake tak'ama dashi zan saka A koreshi"duk wani d'an sanda banza ne me bakin cin hanci da rashawa....iya nan Abbu ya saurara yayi ficewarsa ko Ajikinsa "yasan kowaye shi be isa yayima sudais Abinda Allah be Masa ba"irin haka Anyi yafi sau ukku"sbd haka zai cigaba da bin yaronsa da Addu'a kawai......
******* ******* ******* Imaan ! Imaan!! dattijuwar matar dake zaune gefen kujerah ta fad'a tana kallon k'ofar shigowa "Adaidai lokacin wata matashiyar yarinyar d'anya sharaf ta shigo cikin parlourn da sallamah tana fad'in" mamah gani..... kyakykyawar gaske ce jajir da ita"batada tsayi sosai "ba ramamma bace bame jiki ba"tanada cikar k'irji da kira me kyau"kallo d'aya idan kamata zaka fahimci silent girl ce"parlourn nasu tsab dashi saidai irin na masu rufin Asiri ne....mamah sannu ! yauwa zoki zauna"bah musu ta zauna k'asa kan carpet"mamah ta bita da kallo tana fad'in imaan har yanzun hankalina be nutsu da wannan Auren naki ba"dukda nasan yaron nan Abdul Raheem na sonki" Amma iyayensa Ance basu son talaka"bamu kirashi ba shine yazo yace Yana so"tun jiya da A kaje ganin dak'i dangina dana mahaifin ki jikin su yayi sanyi"bayan haka lefen nan da Aka kawo shima kina ganin irin Abinda suka dingayi?"hakane mamah "Aikin gama ya riga ya gama Addu'a kawai nake buk'ata "munayi imaan ,kuma in sha Allah zamu ci gaba da Addu'a"kema kuma ki dage"jiki A sanyeye imaan ta Amsa dato tana tashi ta koma tsakar gidan su irin na masu rufin Asiri"Kai tsaye cikin kitchen d'in gidan nasu ta wuce sbd ta ci gaba da girkinta....tabbas tana son Abdul Raheem Shima yana sonta"matsalarta dashi nuna shid'in wanine da iyayensa wasu ne"sannan ya nuna mata cewa kayan d'aki beson nasu zai siya mata"ta nuna masa iyayenta zasuyi mata Abinda suke da hali "bayan haka be nuna mata komai ba"yana sonta yana kulawa da ita yana kuma k'ok'arin yi mata hidima"danma bata cika karb'a ba saida Aka saka musu biki take karb'an kud'insa"yanzun haka ya siya mata iPhone itace hannunta"gaba d'aya tunane tunane ne fal Aranta "saidai zata dage da Addu'ar neman zab'in Alkhairi kawai"bayan ta idar da girkin tana zaune dak'in baccin mamanta zata shiga wanka kiran Abdul Raheem ya shigo cikin wayar ta"saida gabanta ya fad'i"ta Ajiye towel d'in ta d'auki wayar ta zauna gefen bed tana masa sallamah cikin siririyar muryanta"ya Amsa yana lumshe ido"Ahankali tace"Ina wuni?"lafiya qlau ya kike?"Alhamdulillah"yau miye kukeyi keda friends naki?"wa'azine"okay gobe Friday in sha Allah Akwai dinner"ki Ajiye wani uztazanci sbd family d'ina nason Ayi dinner d'in Aure nah....kayi hak'uri gaskiya ni bana son bidi'a ,iyayena kuma basu so na sanar maka tuni"ka kuma ce ka Amince....look imaan! ya kamata tun Anan ki fara mun biyayya har zuwa time d'in da zakije gidana" dinner babu fashi za'ayi"zan Aiko miki da gownt goben da kuma wacce zata miki make up "fasa dinner tamkar fasa wannan Auren ne"yana fad'in hakan ya yanke Kiran"tabi wayar da kallo tana sauke numfashi"da tunanin me zata sanarwa iyayenta Akan wannan zancen?"sbd mahaifinta babban melamine kuma limami"taya za'a ce ga Auren y'arsa Anyi wata bidi'a?zata nemi faridah suyi shawarah( babbar k'awar ta)....da wannan tunanin ta shiga wanka...... washe garin safiyar yau ya kama Friday"sudais kamar yadda ya kwanta da kayansa da takalmin sa haka ya tashi da Asubah"sai bayan ya cire yayi wanka ya tafi masallaci "yana dawowa ya zare jallabiyar yayi saura daga shi sai guntun boxer.....hmmm! yanada K'iran jiki murd'add'e duk gashi"beda jiki sosai Amma Akwai manyan damtsa da kwanji"duk kuma hannayensa jijiyoyine"kansa babu suma sosai"saidai fuskarsa cike take da k'asumba me d'auke da gashin bak'i"kai tsaye dak'in motsa jiki ya wuce"be jima da farawaba Abbu ya kirashi Akan yazo ya Aikesa gidan Amininsa Alh sulaiman"bayan ya Ajiye wayar yayi shiru fuskar nan har lokacin babu Alamar rahama ko sassauci cikinta"yadda yake nufi daya shirya yaje ya gaida Ammah ya wuce office"sbd yana so yaje yaga wannan k'aramin d'an iskan"saidai dama can tarbiyan da iyayensa suka bashi baya musu dasu"befi mintina 5 ya k'ara ba Yana motsa jikin"kafin ya baro dak'in da sassarfa ya shiga dak'in baccinsa"sosai yunwa ke damunsa Amma yak'i neman Abinci "ko dinner be yiba A daren jiya....k'arfe 9:11 am DPO sudais ya shigo cikin babban parlourn gidan su sanye da kakinsa yana zuba wani irin fitinan nan k'amshi "yayi matuk'ar kyau Amma har lokacin beda walwala"Abbu da Ammah na zaune A dining area suna break fast "suka bishi da kallo"Ammah na murmushi sbd ganin yadda yaketa cika yana batsewa sbd yana fushi da ita.....Ammah! Ina kwana?"Abbu sannu da hutawa"duk ya furta cikin husky voice d'insa me k'arfi "lafiya qlau autan Ammah sai Ina?"Abbu yace gidan Alh sulaiman zan Aikesa yakai sak'o "okay inaga yama san gidan?duk sudais na duk'e gabansu bece komaiba"Sarai yasan gidan Amma bece komai ba....kaje parlou nah leda na nan Ajiye saman center table ka d'auka kaje Masa da ita"ka tabbatar ya hadaka da sunusi (babban d'ansa) kun gaisa"sbd kwanaki tayita tambayata kana Ina"Amma kasan imaan?.....yayi shiru saidai mik'ewa tsaye da yayi yabar wajen"Ammah tace shi wasu ya sani ba saidai shi A san shiba"bashida wani Abu sai Aiki A rayuwarsa"kinga mu Ajiye wannan zancen kince zaki fita Anjima ?"Eh Alh "okay driver zai kaiki bana son kina driving "ta Amsa dato suka cigaba da break fast d'insu"Akan idonsu sudais mashee ya baro side d'in Abbu rik'e da ledar ga hannunsa ya fita.......✍️
wannan book din na kudi ne babu regular Vip 700 post sau biyu Arana special grp 1500
Mutanan PC Vip pc vip 1k Special PC 2k
zaku biya kud'inku ta wannan acc number 8100084251 Nabila Aliyu monie point shaidar biya ta nan👇 08100084251 ga wanda acc nasa be nuna monie point saiya saka tanan 2230373842 Nabila Aliyu uba bank
ku sani ba'a turo card saita acc number za'a biya
Bana son kira dan Allah❌❌ ta what's kawai za'a mun mgn ✔️
y'an nijar ku tuntubi wannan number +227 88 01 90 50
Vip grp 500f Special grp 1000f
*Idan wannan book d'in ya kammala cmplt pages 1k decument 2k karma ki turamun 700 kice cmplt kike so gara kifara tambaya kafin ki saka kud'in*