
Post
FUSATACCE PAGE 7-8
..... no one made this decision from him except the sheikh" he did it because he knew that the sudais were not following his orders" everyone was afraid of him because of the anger of the sudais "But he withdrew everything or Ammah didn't know" around 12:00 pm Abbu and Alh Mukhtar went home "Ammah was in the kitchen with Jummi Me Aiki they were preparing lunch" she wanted to come at 1 o'clock they sent Abdu He is having lunch at 2 o'clock" and her daughter-in-law is sure that he will come home around 4 pm" that's why she cooks for me" from the hall of the house to the main parlor of the house, the smell of me comes from cooking. and Alawa, "Abbu is fixing his hair, he opened the door to the parlor and said, "No one knows about me except you." But how do you think you won't be able to give me sudais....look mukhtar! You say Alkhairi or keep quiet, "I am repentant." Then they entered the parlor and greeted me. On the phone" Just when Ammah came out of the kitchen holding a tray.....
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🔥 FUSATACCE 🔥👮♂️
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written By Mommyn fareesa
*Dedicate* to
Hjy maimuna Umar sadeeq (mommy) Ina Alfahari dake 😍❤️
*Dominki* Hjy Salma Abbah nijar❤️ d'aya tamkar da dubu Allah yashiga lamarinki tawan 👏
Special gift for all members of my groups🥰💔 Ina yinku over guys
Tukwici ne gareki *hajara Ibrahim dallatu*😘🥰 bazan tab'a mance Alkhairin kiba "Alkhairin Allah yakai miki har bisa gadon baccin ki
Free page 7&8
.......Tun bayan gama d'aurin Auren mutane da yawa ke mamaki sbd sunsan dai sunan Angon Abdul Raheem gashi kuma An d'aura da wani daban"Abbu da sheikh suna tare cikin farin ciki mutane natayi musu Allah yasa Alkhairi"Alh mukhtar(k'anin Abbu)da shine waliyin Ango yana gefe yana tunanin meke damun yayansa da zai yiwa tilon d'ansa daya mallaka A duniya *Auren dole?*....Abbu besan yanayi ba da zuciya guda ya had'a wannan Aure sbd sheikh ya bashi tausayi matuk'a"baya so yaji kunya musammun tunda ya raba Iv"sannan ita kanta yarinyar yana tausayinta"beyi shawarah da kowa ba ya yanke wannan hukuncin daga shi sai sheikh"yayi kuma hakane sbd yasan sudais be k'e tare Umarnin sa"dukda yana fargaba Aransa sbd fusatar sudais "Amma ya janye Komai ko Ammah bata sani ba"wajen k'arfe 12:00pm Abbu da Alh mukhtar suka nufo gida"Ammah na kitchen tare da jummai me Aiki suna girka lunch"tana so zuwa k'arfe 1 sun idar sbd Abbu k'arfe 2 yake yin lunch"sannan d'an lelanta tanada tabbacin wajen 4 pm zai dawo gida"hakan yasa take girki na musammun"tun daga haraban gidan har zuwa babban parlourn gidan k'amshi na musammun ke tashi na girki....Ahhhhh! Lallai yaya da Alama hjy sa'adatu tasan da wannan Aure tunda gashi Anata girki ko Ina na k'amshi "cewar Alh mukhtar dake d'auke da ledojin goro da Alawa "Abbu na gyara malun malun nasa ya turo k'ofar shiga cikin parlourn yana fad'in" babu wanda ya sani daga ni sai kai"Amma yaya kana ganin sudais bazai baka....look mukhtar! ka fad'i Alkhairi ko kayi shiru"shikenan tuba nake"daga haka suka shigo da sallamah "babu kowa cikin parlourn ,ga TV na Aiki "Alh mukhtar ya Ajiye ledar hannunsa saman center table suka zauna gefen kujerah "Abbu na latse latse A waya"Adaidai lokacin Ammah ta fito daga kitchen rik'e da wani tray data kifo wani Abu bisa..... da mamaki tace" Alh ! yaushe kuka shigo?"ta tambaya tana kallonsu da kallon ledar dake Ajiye "saida yamata d'an murmushi kafin yace"shigowar mu kenan kinbar parlourn babu kowa"Muna jin motsin kowa Ai"sannun ku da zuwa da fatan An d'aura Aure lafiya?"lafiya qlau"hajjaju Ina wuni?"lfy qlau Alh ya mutanan gidan?"Alh mukhtar ya Amsa da lafiya lau "kafin Ammah ta wuce dining area ta Ajiye tray d'in hannunta"harta gifta su zata wuce Abbu yace"dawo ki zauna muyi mgn "bata ce Komai ba ta wuto ta zauna gefensa"idanunsa Akanta yace "*sa'adatu!*....gabanta ya fad'i "bata Amsaba sai idanuwa data tsurama fuskarsa"ki duba waccar ledar"goron d'aurin Auren yaronki ne *Mahmood mashi*! dashi Aka d'aura bada wancan yaron ba"sbd sun nuna basuda mutunci da girmama talaka"hakan yasa sheikh ya sanar mun bazai basu y'arsa ba"ni kuma naga imaan da sudais ta dace....Allah yasa hakan shiyafi zama Alkhairi "ubangiji ya basu zaman lafiya"daga haka Ammah tayi shiru zuciyarta na girgiza"Alh mukhtar ya mik'e tsaye yana fad'in yaya zan wuce babban gida da waccar ledar sai Abama kowa hakk'insa"zan kuma yi musu bayanin da kace"okay hakan yayi"daga haka ya wuce ya fita"Ammah itama ta yun k'ura da nufin itama ta tashi tabar wajen"Abbu yayi saurin ruk'o hannunta guda yana murmushi yace"haba sa'ar mata! miye na fushi?"kamata yayi ki tayani yak'i da babanki ya Amince da imaan A matsayin matarsa"maybe ta haka koya rage wannan zafin ran nasa"wannan Auren shine rufin Asirin Amininah"ya shiga damuwa da tashin hankali sbd Abinda iyayen yaron sukayi"shiyasa yace bazai bayar da y'ar saba"tun tana waje yayi haka inaga taje gidansa??......Ammah na kallonsa ta katsesa da cewa"Alh kasan me kayi kuwa?"kafi kowa sanin halin sudais da fusata shine zaka Masa Auren had'i kuma da k'aramar yarinya fisabilillahi?wlh harna fara jin tausayin yarinyar nan....kinga bana son wannan tunanin "koma miye da zuciya d'aya nayi kuma Alkhairi nake nufi ba sharri ba"sudais ya isa Aure harma yafara zama tuzuru"yak'i yayi budurwa balle Azo batun Aure"bayan sa banida d'a ko y'a"inaso in sha Allah naga yaran sudais Amma kike fad'in hakan?"idan mutum yanada wani hali da ba'a so ko Ake shakkarsa sbd halin"baso Ake ya dauwama ba da halin"so Akeyi ya canza"in sha Allah zakiyi mamakin sudais da imaan"so idan yadawo yau da safe zan sanar masa Komai Agaban ki"kece zakiyi yak'in nuna Masa yaso matarsa su zauna lafiya"nasan imaan Sarai tun tana yarinya in sha Allah zaiji dad'in zama da ita"Abu na gaba sai next week za'a kawota"sbd za'a Kai lefe kuma zai k'ara gyara gidansa sbd zuwan Amarya"babu wani bidi'a da za'a yi....gaskiya Alh zanyi taro "bikin baban nawa sunkutukum? shikenan bah damuwa"Amma Alh imaan zatayi shekara nawa ?"inaga 20yrs ne"okay miye sanadin fasa Auren?"kaf Abbu ya shiga sanar mata sanadi"Ammah na salati tace"basu kyautaba gaskiya"nasan dama family d'in *Alh idris marafa*! da nuna su wasu ne"Allah yasa su gane gaskiya"imaan kuma zaman su nan kusa damu shiya fi"sbd muga yana yin zaman nasu"kasan halin fusatar yaron nan Sarai Alh "Abu kad'an zai maidashi babba"gashi bason yin mgn yake ba saidai ya dinga nunal"Abbu na murmushi yace" ja'iri wata ran zai koyi surutun wajen imaan"sbd na santa tana yarinya Akwai surutu"saidai maybe yanzun ta dena tun.... ringing d'in wayarsa yasaka yayi shiru ya zaro wayar yana dubawa"oh kinga d'an halak d'in ne "halan sudais ne me kiran?"shine fa da kansa"Allah yasa be kira niba"sbd wayar na saman bed na bari,nafi Awa guda rabona da dak'in "ta k'are maganar Adaidai lokacin da Abbu ya d'aga wayar da sallamah"sudais ya Amsa cikin rashin walwala "Abbu na b'oye murmushinsa yace"babyn Abbu lafiya?"murmushi ya sub'uce ma sudais mashee"kafin cikin husky voice yace"Abbu bah kaida Ammah bane"laifin me mukayi?"nayi tafiya harna sauka zamu shiga meeting shine baku kirani ba?"kuma na kira Ammah sau biyu batayi picking call d'ina ba....I'm really very sorry "bata kusa ne"ni Kuma Ina wajen hidimar d'aurin Auren imaan"yamutsa fuska yayi yana jin wani irin haushin yarinyar"wato sbd ita mahaifinsa ya mance da shi??"shifa haka kawai yaji tana bashi haushi tunda ya ganta babu d'an kwali da hijab tana tallar gashinta.....kana jina?"Abbu ya katse Masa tunani"uhmm"ga Ammah d'in taka....no Abbu! zamu shiga meeting ne"idan mun fito zan kira ku vedio call back"okay"daga haka sudais ya yanke wayar "Ammah na murmushi tace"yaron kirki kenan da baya girma wajen iyayensa"wai yau babana ne keda mata....kedai bari" nasan idan ya dawo yaji Ammasa wannan Auren zaisha fushin sa ya gama"Amma kasan Alh duk Abinda sudais yasan dole ne Koda be masaba hak'ura yakeyi be nuna Komai"tunda yasan idan ya nuna fushi ba mafitah zai samu ba??wannan gaskiya ne "Allah yadawo mana dashi lafiya"inaso ko goben ne yaje ya duba imaan"nasan maybe itama tanata fushi "sbd zataji Abun daga sama"hakane sai hak'uri"bara naje wajen jummai na barta kitchen "kasan sudais besan girkin daba nawa ba"shiyasa idan yarinyar nan tazo nake ganin zatayi wata batayi girki ba "Akan me?"sai sun huta idan Akwai grikin da bata iyaba cikin wad'anda yakeso saina koya mata....gaskiya kina shagwab'a yaron nan da yawa"tana dariya ta wuce ba tace komai ba"Abbu ya girgiza kansa Afili Yana fad'in *Allah yaji k'anki khadijah*.......!!
Wanene sudais mashee?? Alh kabeer Abubakar mashee! Mahaifinsa d'an Asalin garin mashi ne dake jihar katsina"kasuwanci ya kawosa garin yolah"har Allah yasa yayi Aure Acan "yana sana'ar kiwo da noma"cikin ikon Allah ubangiji yayi Masa Albarka dukiya ta bunk'asa"har ya k'ara Auren mata biyu bayan uwar gidansa hjy binta"daga ita sai hjy Aminah da hjy Rashida"hjy binta nada yara 5"hajarah,kabeer , mukhtar,Almustapha sai Auta saudat"sai hjy Aminah nada yara ukku" haruna,kabeer sai sa'idah"itama hjy Rashida nata yaran ukku ne Amma duk mata ne"sun taso cikin had'in kai inda Mazan duk sunyi karatu me zurfi"kuma kabeer shine babbah namiji"yana kasuwanci da kuma karatu har Allah yasa ya kammala ya zama babban Alk'ali"be jima da fara Aiki ba Allah yayima mahaifin su rasuwa"duka iyayen da yaran da basuyi Aure ba suka cigaba da rayuwa A gidan da suka sakama suna *babban gida*!.....Alh kabeer kyakykyawan gaske ne hakan yasa Allah yamasa farin jinin y'an mata "hakan yasa da yawa mata ke shige Masa"sai kuma Allah yasa be cika son yawon shigema matan ba"ya fara soyayya da khadijah ,gefe guda kuma Akwai y'ar Abokin mahaifinsa dake masifar sonsa"sunanta sa'adatu"be damu da itaba khadijah ce gabansa har Allah ya kaisu ga Auren juna"sunso juna sun zuba soyayya me tsabta"kowa yasan yadda Alh kabeer keson matarsa"suna tare bayan shekara guda ta samu ciki"hakan yasa kulawar da yake bata tafi tada"gefe guda kuma sa'adatu ta shiga damuwa harda ciwo sbd soyayyar maso wani data Azama kanta"daga k'arshe data kwanta Asibiti ta kamu da ciwon hawan jini"hjy binta ta had'a kabeer da matarsa ta rok'esu dasu hak'ura kabeer ya Auri sa'adatu kodan sbd son datake Masa"shidai bece komaiba "khadijah cikin b'oye kishinta tace"babu Komai hjy ya Aureta Allah yabamu zaman lafiya "sosai hjy tayi Murna ta tashi ta tafi gida"A ranar Alh kabeer fushi ya kwana yanayi da khadijah sbd yana ganin bata kishinsa"sai washe gari ta dinga lallab'ashi da bashi baki da nuna Masa"tana sonsa tana kishinsa"kada sanadin k'in Amincewarsa yasa danginsa suga laifinta"kuma yarinyar ta shiga wani hali"Amma tana son yabari sai bayan ta haihu ya Aureta "kowa kuma yayi na'am da zancen"Aka zo Aka saka rana"tun bayan saka ranar sa'adatu ke zuwa gidan khadijah"daga matar gidan har me gidan suyi watsin tsiya da ita Amma bata fushi"wasu na cewa Kodai Asiri ne Aka yima sa'adatu?"sbd na cinta yayi yawa....tun khadijah bata sake mata fuska har take sake mata"idan kuma tazo gidan itace ke mata duk wasu Aikace Aikace"musammun dataga tayi nauyi sosai "Aiko mutane Akayita kace nace wai sa'adatu ta cika naci kuma batada kunya "tun kafin ta shiga gidan Auren ta take musu zarya" khadijah ta maida ita baiwarta y'ar Aikinta "itadai saidai ta toshe kunnu wanta"befi saura bikin sa'adatu da Alh kabeer wata biyu ba khadijah ta haifi "santalelen d'anta kyakykyawan gaske"bayan tayi wanka harma ta shayar da yaron washe gari da safe Allah yayi mata rasuwa "fad'in tashin hankalin da Alh kabeer ya shiga b'ata baki ne"ga yaro jariri Abin saiya Masa yawa"Abin mamaki kuma sa'adatu tace" zata shayar da yaron dukda tana budurwa"iyayenta sun Amince "bayan Sunje Asibiti Ammata Abinda yadace ta fara shayar dashi"saidai Alh kabeer be yarda yaronsa ya koma gidan su sa'adatu ba"hakan yasa bayan sati biyu da rasuwar khadijah Aka d'aura Auren sa da sa'adatu "ta tare taci gaba da shayar da baby da yaci suna *Mahmood*! Itace da kanta take kiransa da sudais sbd sunan mahaifinta da yaci.....yadda sa'a datu ta rik'e sudais ta kula dashi da bashi gata shine sanadin da ya jawo soyayyarta Acikin zuciyar Alh kabeer "sai Abu na k'arshe da shine ya saka yaji babu wata mace dazai so bayan sa'adatu sbd sadaukar war data Masa"shine bayan ta yaye sudais dangin miji Aka fara k'orafin bata haihuwa "hakan yasa sukaje Asibiti sbd Abincike su"ita lafiya qlau take Amma Alh kabeer shine keda matsalar"beda k'wan haihuwa"k'wan haihuwarsa guda ne gashi nan yazo duniya"yayi zaton tun A Asibitin sa'adatu zata nuna su rabu"Amma sai bata nuna ba"Asalima daya mata zancen cewa wane hukunci ta yanke game da matsalar?"Kai tsaye ta sanar masa za taci gaba da zama dashi da yaronsa dukda bazai haihu ba"A ranar har kuka Alh kabeer yayi na tausayi da soyayya"ya yarda sa'adatu na masa son gaskiya shida yaronsa"hakan yasa yayi gargad'i da babbar murya Akan" baya son kowa ya sanar wa sudais hjy sa'adatu ba ita bace mahaifiyarsa."kowa yayi na'am da zancen sbd halaccin data yima Alh kabeer.....tun daga lokacin sa'adatu ta k'ara samun soyayya wajen mijinta itada yaron su"wanda sudais befi 8 yrs ba Aduniya ya fara bama mutane mamaki"sbd ko'a skul daya shiga cikin sa'anninsa sukayi dambe yake musu mugun duka"gashi d'an zafin zuciya besan yawon mgn saidai yayi nunal"sannan duk yanda malami zai dokesa baya kuka saidai idanunsa suyi jajir"Abin be bama iyayen sa mamaki ba saida sudais yayi fad'a da d'an primary 5 shi yana primary 3 kuma yasaka yaron kuka"sannan malamin su yabashi rashin gaskiya "Koda yadawo gidah yana sanarwa Amman sa sai cewa yayi"Ammah idan na girma police zan zama"zan yi hukunci Akan ko waye in har bashida gaskiya"hjy sa'adatu ta k'ara Masa k'arfin gwiwa"har sudais yayi saukar A'lk'ur'ani me girma yaje secondary skul burunsa na nan"saidai jarumtarsa naba iyayensa tsoro"ga fad'a da Allah yayi shi dashi da fusata"Abu kad'an zai fusatu....tun suna secondary skul suke tare da Jamil kuma burunsu d'aya ne"Abbu ne ya tsaya musu Suka cigaba karatu har Allah yasa burunsu ya cika"bayan sbd sudais na gudun fushin iyayensa shiyasa yake kauda kansa Akan wasu Abubuwan "Amma bayan yafara Aikin police ba'a cikakken sati d'aya ba'a kawo k'arar sa wajen Abbu bah"ga bak'in miskilanci da yake dashi"Koda ya tambayesa meya had'ashi da mutane?sai yayi shiru"daga k'arshe yabama Abbu ko Ammah hak'uri....tun daga yarinta har zuwa girmansa besan cewa Ammah ba ita bace mahaifiyarsa ba"kawai dai dangin mamansa Ana nuna Masa suma dangin su Abbu ne......sudais na matuk'ar son iyayensa shiyasa yake musu biyayya,ga kuma ingattaciyar tarbiya ya samu"sbd besan yayi nisa dasu shiyasa daga baya da Abbu ya nace saiya gina masa gida yace kusa dasu yake so"hakan yasa da yake filin na Abbu ne saiya gina Masa"hakan yasa ya dena kwana gidan su sai nan....sudais mashee! kyakykyawan gaske ne sai kuma ka nutsu zaka gane baiwar kyawun hallitar da Allah yabashi"ga jarumta sbd Allah yamasa k'arfaffen jiki ,ga kwarjini da Kamala"hakan yasa da yawan mutane ko A office basu iya musu dashi"zamansa kaifi d'aya yasaka shi kansa CP kejin shakkarsa"sudais mutum ne me ibaba da kyautar bazata"idan be gadama ba beyin kyauta"yanada tausayi Amma be cika son mutane ba" kasancewar sa marar son hayaniya"hakan yasa da yawa cikin friends nasu na skul ke cewa yanada girman Kai "matan dake cewa suna sonsa be iya k'irgasu"saidai ya sharesu kawai"friend d'insa guda mace itama kiristan ce kuma tanada Aure "sunanta engozi....yawanci duk bayan sati d'aya ko biyu ya kanje babban gida shida Abbu ya sada zumunci ranar Friday....A rayuwa yana da son Abu me zak'i da kuma me sanyi"hakan yasa Koda yaushe d'akinsa Akwai chacoolates ko biscuits"Abinda kuma baya so shine k'arya da kuma mutum me saurin kuka"be kuma son raini"Alh mlm sheikh sulaiman babban Aboki,kuma Aminine ga Abbu"A shekarun baya wajen sa sudais yayi Karatun litattafai na Addini"time d'in ba'a haifi imaan ba.....tun bayan ya kammala karatunsa Abbu ya bud'e Masa company na siyar da karafuna"suna siyan k'arfuna su fitar k'asar waje A sarrafasu ta wani fanni"yawanci week end sudais d'in yake zuwa campany..... wa'annan sune Abubuwan da suka shafi me gayya me Aiki Anan gaba zakuji wani Abun....!!
Cigaban labarin✍️
wannan book din na kudi ne babu regular Vip 700 post sau biyu Arana special grp 1500
Mutanan PC Vip pc vip 1k Special PC 2k
zaku biya kud'inku ta wannan acc number 8100084251 Nabila Aliyu monie point shaidar biya ta nan👇 08100084251 ga wanda acc nasa be nuna monie point saiya saka tanan 2230373842 Nabila Aliyu uba bank
ku sani ba'a turo card saita acc number za'a biya
Bana son kira dan Allah❌❌ ta what's kawai za'a mun mgn ✔️
y'an nijar ku tuntubi wannan number +227 88 01 90 50
Vip grp 500f Special grp 1000f