Kenza eBookz

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 13

Complete book: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy)Chapter 13 of 21FantasyBy Mamy Kabir (aunty Maamy)

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 13

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 13: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 13. Ya qarasa cikin hawaye sosai ,

3,363 words

Ya qarasa cikin hawaye sosai ,

"kayi shiru Abba nayi maka alkawarin duk inda Khadeeja take afadin duniyar nan zan nemota".

Ya fada cikin karfafa gwuiwa.

"Shikenan Kameel kaje ka kwanta ,zuwa safiya zamu tafi malam madori domin ganin ko tana can ,sannan zan tafi daku duka dan kuga danginku na wajena."ya karasa cikin wani irin farin ciki da ya tsinci kansa aciki .

"Shikenan nan Abba kasamu kayi barci karkasa damuwa aranka". Kameel ya fada yana riqe da hannun Abban.

"Toh Kameel Allah yayi maka albarka,ya qara shiryamin ku gabadaya."

Ameen ya Allah.ya fada yana ficewa daga dakin .

Koba komai yanajin wani sanyi aransa ,"ashe dama Khadeejansa qanwarsa ce? Wayyo can't wait to see Khadeeja as he's sister,kuma mata , Farin ciki sosai ne aranshi duk da yana farga bar kar yaje kuma ace batazo malam madirin ba? In sha Allahu ta can ma.

Abba sam kasa barci yayi awannan daren ,tunani ne kala kala aransa ,yana da yan uwa sannan shidin mai haline ,yayin da suka kasance,masu karamin karfi,amma ya watsar dasu ya daina shiga sabgarsu gaba daya, Dole ya gyara kuskurensa.

Ta bangaren Kameel ma dai haka abin ya kasance dan sam kasa rintsawa yayi ,dan haka kwana yayi yana salla da addu'oin Allah ya sa Khadeeja tana can garinsu , Har asuba bai kwanta ba ,yanayin salla kuwa ,wanka yayi ya shirya cikin wani yadi mai matukar tsada da kuma kyau,ya feshe jIkinsa da turare mai dadin kamshi.

Fitowa yayi zuwa falo ,inda ya tarar da Abba yana zaune shima cikin shiri,

Sukamsu su ,ummi sun shirya . Fitowa sukayi gaba daya suka shiga mota .

Kameel shida maryam amota daya sai guard dake tuka motar .

Abba muma shida ummi suna cikin daya ,inda suma guard daya na yukasu.

Mommy kuwa ana can asibiti dan acan ta kwana da Aisha,tasami karaya ahannunta ga uban ciwuka ajikinta .

Karfe 10:00am suna kofar gidan su Abba ,

Wani irin farin ciki yakeji marar misaltuwa atare dashi ,wai yau shine amahaifarsa ?bayan kusan shekaru goma sha rabonsa da zuwa garin ,

Haka suka fito suka shiga gidan ,amma Kameel sam qin shiga yayi saiya fara zuwa ya duba Khadeejan sa.

Sosai yan uwa sukayi murnar ganin abba kaseem ya dawo ,da iyalinsa ,gidan cika yayi anata koke koke.

Kameel kuwa cikin zumudin son ganin Khadeeja ya tsaya abakin kofar bai manata gidan ba . Yau kam da kanshi ya je har bakin kofar gidan . Yaro ya samu yace yaje yace ana sallama da mai gidan .

baba umaru ne ya fito jin cewa bakin da mota sukazo. Aikuwa idonsa na sauka akan Kameel ,yawani washe baki yana kokarin tsugunnawa, Ranka ya dade barka da zuwa sannu sannu ,shigo daga ciki mana,aida ka shigo kai tsaye basai ka nemi akiraniba kaima ai gidankune ko,ya fada yana rawar jiki.

Kallonsa Kameel yayi cikin tabe baki,har yanzu halinsa nanan kamar da na zalama da kuma son abin duniya.

"No kakiramin Khadeeja zamu wucene,"ya fada cikin kyautata zaton smunta gidan.

Ikon Allah ita khadeejan tace maka ta tahonan ne ,?yallabai aini nayi tunanin ma tare kuke da ita ,dan rabona da ita yau kusan wata hudu kenan tunda kuka bar gidan nan tare.

Baba umaru ya fada cikin mutuwar jiki,

"innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!!! Kenan Khadeeja ba ta taho gida ba ? Wayyo Allah na ina zan ganki matata ? Kameel ya fada cikin mugun rashin hankali ,dafe kanshi yayi dayake masa wata irin bugawa kamar ana sara masa guduma ,

Lumshe ido yake dan dan ji yayi gaba daya nunfashinsa na neman kwace masa.

Da sauri ya bar kofar gidan cikin rashin sanin madafa ,nunfashi yake sama sama ,gaba daya ji yayi duniyar tayi masa zafi,ina zaiga Khadeeja ?ina zai samota?

Aisha ta cuceshi ta rabashi da farin cikin rayuwarsa ,wllh saiya ci ubanta idan ya kara ganinta ko a inane shegiya karuwa.

Tafiya kawai Kameel yake batare da yasan inda zaije ba.

Guard dinsane ya zo da sauri ya tareshi , Oga ga mota canfa kuma ba hanyar da muka biyo kake biba,

Ko kallonshi Kameel baiyi ba yaci gaba da tafiya ,binshi kawai guard din yayishima dan baisan ina ogan nashi zai tafiba ,

motar su Abba ce ta karyo kwana ,ya hango Kameel na tafiya cikin tashin hankali.

Da sauri ya ce maza driver ya bisu.

Fitowa Abba yayi ya riko hannun Kameel .

"Ina zaka Kameel "? Abba ya fada yana rike da hannusa.

Kallon Abba Kameel yayi cikin rauni yana juya kanshi,

"Abba bata nan " Ya fada hawaye na zubowa harrrr!daga idonsa.

Janyo hannunsa Abba yayi "zo muje Kameel "ya fada yana jan hannunsa ,

Gidansu Abba suka koma ya zaunar da Kameel yana masa nasiha.

"Kameel kayi haquri ,in sha Allag zamu samo khadeeja duk inda take,karka damu , Na tabbata bata bar garin kano ba tana can "

Ai kafin ya gama rufe bakinsa ,Kameel ya miqe tsaye ,"Abba mukoma kano dan Allah yanzu Khadeeja na can tana jirana na sani,Abba bata san kowa ba ,bata da lpy" ,ya fada kamar wani zararre,yana nufar kofar fita daga gidan .

Ba yadda su abba suka iya haka suka taso suka biyo Kameel ,wanda ko tsyawa baiyi yan uwa suka ganshi da kyau ba.

Kudi sosai Abba ya basu akan suyi hakuri saiya dawo anutse.

Abangaren khadeeja kuwa sai wajen la'asar ta farka daga barcin da take , kallon daki tayi sosai ta gane a asibiti take , Shiru tayi tana tuna abinda ya faru da ita daga daren jiya zuwa yau ,kuka ta sanya sosai tana tunanin rayuwa ,

Gaskiya su mommy basu da imani ,basa da tausayi ko kadan ,In sha Allah ta bar gidan nan daga yau ,gara ta zauna a ko inane kodabara zatayi gara tayi akan ta koma wannan bakin gidan .

Tana cikjn kukanta saiga likitar nan data tsinceta ta shigo dakin .

Da sauri ta karaso cikin dakin ,

Haba petient dina yada kuka haka ?

Is ok kiyi shiru kinji ko wani gurin yana miki ciwone?

Girgiza kai khadeeja tayi ,alamar ba inda ke mata ciwo,duk ta tana jin jikinta ba dadi ,

Ya sunanki ?

Mayar ta tambaya,

Khadeeja !! Inane gidanku? shiru khadeeja tayi batace komai ba sai hawaye .

kinga kiyi shiru kwanta ki huta zamuyi magana anjima ,bari na kawo mikj abinci.

Bayan khadeeja ta gama cin abincinne ,ta bata magani tasha .

Sannan tace ki fadamin dalilin dayasa na ganki awannan gurin ,

Shiru Kadeeja tayi tana tunani kodai ta bata labarin rayuwar tane ? Ko Allah zaisa ta taimaka mata ,dan ta ga matar tana da kirki.

"Ki fadamin damuwarki in sha Allah zan taimakamiki." Matar ta fada cikin kokarin kwantar mata da hankali dan ta yarda da ita ,tanaji aranta tana son taimakawa. Yarinyar.

Ahankali Khadeeja ta bawa matar nan labarin rayuwarta tundaga farko har karshe ,har zuwa lokacin data tsinceta awanan halin.

Sosai matar ta tausayawa Khadeeja harda hawaye .

Sannan ta ce karta damu in sha Allah zata taimaka mata iyakar iyawarta.

Dan haka koda ta tashi daga aiki gidanta ta wuce da Khadeeja ,

Ta nuna mata dakin dazata zauna ,sannan tace ta huta zata dawi suyi magana ,kafin nan yarinyar ta tadawo daga islamiyya.

Kwanciya Khadeeja tayi cikin zullumi dakuma fatan Allah yasa alkhairine ya hadata da wannan matar mai kirki.

Saikuma tunanin Kameel ya dawo mata Allah sarki ko yana ina yanzu? Ko ya zaiji idan ya farka bata nan? Anya ma kuwa zai wani damu idan yaga bata nan? Share hawayen idonta tayi tana gyara kwanciyarta ,

Allah yasa da gaske yake dayace yana sona ,ta fada aranta.

Tare da lumshe idonta tana hasko kyakyawar fuskarshi , Bude ido tayi da sauri ,meyasa nake ta tunaninsa ne? Yanada kirki shiyasa !ta bawa kanta amsa,

Gashi kyakykyawa ina sonshi ,ta fada batare data shirya fadin hakan ba ,

Zaro ido tayi tare da rufe baki toh fa masu karatu da gaske Khadeeja ma tana sin Kameel?..........

Sai mun hade next page,taku anty mammyπŸ™

Mrs babiπŸ’˜πŸ’˜ [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

GIDAN AIKINAπŸ’πŸ’

Na mammy kabeer (anty mammy)

ELEGANT ONLINE WRITER'S.

Page. 49./ 50

Zaro ido Khadeeja tayi ,tare da rufe baki. "me nake cewa ne? Nashiga uku ,aa ba sonshi nake ba gaskiya ,kawai yana da kirkine .

Tana kwance ,kokarinta kawai ta manta da Kameel da tunaninsa a zuciyarta ,amma abin ya faskara ,sosai take ganin fuskarshi idan ta rufe ido.

Likitar matar nan ce ta shigo dakin,bayan tayi wanka ,macece yar gayu fara kyakykyawa da ita.

Zama tayi akusa da Khadeeja tace "ki kwantar da hankalimki Khadeeja ,ki daukeni kamar mahaifiyarki,zan kula da al'amarinki zan baki kulawa ta yadda zaki zama abin alfahari arayuwar wadanda suka maisheki marar amfani Kinji?. Matar ta fada tana dafa ka fadar Khadeeja.

Murmushi Khadeeja tayi tana jin son matar aranta , "nagide hajiya" Ta fada ahankali .

Ba komai, sunana doctor zainab ,yata tana kirana da mommy, Ita kadai na haifa ,mijina ya rasu da jimawa,fatan zaki daukeni amatsayi uwa ,duk wata damuwarki ki sanar dani kinji.

In sha Allahu mommy zan daukeki tamkar uwar da ta haifeni. "Nagode sosai da taimakonki gareni ."

Ba komai khadeeja Allah yashige mana gaba,ameen

Koda islam yar gidan doctor zainab ta dawo ,sosai taji dadin ganin khadeeja ,nan da nan ,suka saba da juna kasancewar islam akwai surutu .

Koda su Kameel suka dawo ,gida gaba daya baya cikin sukuni ,ko cikin gidan bai shiga ba ,yace shikam zai wuce neman khadeejan sa ,

Bayadda Abba baiyiba,akan ya hakura ya dan huta ma ,amma firyaki Zama ,haka ya wuce police station ,ko akwai wani bayani.

Amma sukace ba wani bayani da suka samu akanta ,kuma suna kan nemanta,

Allah sarki ,haka kameel yayi ta yawo cikin garin kano yana neman Khadeeja,amma ko mai kama da ita baigani ba , Gefe ya samu ya faka motarshi cikin matukar damuwa ya kifa kansa akan sitiyarin motar, Hawayene ke zuba sharrr akan kyakykyawar fuskarsa,

"ina kike matata ? Ina kika shiga ? A ina zanganki?

Khadeeja kina ina?"

Ya fada kamar zai kwalla ihu haka yakejin zuciyarsa na masa daci kamar zai yi hauka haka yakeji,

Dama haka so yaj Ke? Haka dacin rabuwa da masoyi yake? "Allah ka bayyanamin matata aduk inda take.

Bashi ya koma gida ba sai bayan sallar ishsha, wajen qarfe10:00pm na dare .kai tsaye dakinsu ya wuce batare da yayiwa kowa magana ba duk da suna zaune afalon har mommy.

Ummi tana bata labarin sunje garinsu Abbansu. "

Na shiga uku ni yar nan ! Yanzu kina nufin kunje can malam madorin har Abbanku yaga yan uwansa ? Shikenan tawa ta sameni ta fada tana dafe kirji,

Kallon juna ummi da maryam sukayi ,kafin suka tabe baki ,dan ita kam ummi yanzu ta yarda duk wani makaman yakinta akan khadeeja tunda ta gane yar uwartace, Kuma tana fatan Allah ya bayyanata tanemi yafiyarta akan abinda tayi mata abaya.

Maryamce tace"mommy kinsan wani abu kuwa ? Ta fada ciki doki da zumudi.

"Saikin fada maryam, Allah yasa dai ba cemin zakiyi ya sami wannan shegiyar kanwar tashi dana sha fama kafin na cireta aranshi ba. Mommy ta fada cikin damuwa,.

Mommy ya tabbata dai Lhadeeja ya ce agurin Abbanmu!! Yar gidan umma maryam ce kanwar Abbanmu.ta karasa tana mai murmushi cikin jin dadi.

nashiga uku !!! mommy ta fada tana dafe kirjinta da yake bigawa kamar zai fashe,

Wace khadeejan kike nufi maryam ? Karki cemin wannan shegiyar yarinyar dana batar da ita ,ta fada cikin tashin hankali.

Kallon juna su ummi sukayi,

Mommy da gaske dama da hadinbbakinki kuka batar da Khadeeja ? Ummi ta fada cikin yanayi na tuhuma .

Cikin son kawar da musu dazancen mommy tace "ina tambayarku kuna tambayata,ko so kuke ku titsiyeni? ta fada cikin fadan da basu san ta iyashiba,

dariya ummi tayi cikin raini tace " Mommy kenan yanzu dai kinga mugun abunki yana nema ya koma kanki ,tunda ga danki can ya susuce akan yar da kika tsana, kike kallonta matsayin makaskanciya , Ta fada cikin rashin kunya da tarbiyya.

Klalonta mommy tayi tace "Ummi dan ubanki ni kike fadawa wannan maganar ? Ta fada tana huci tsabar bacin rai ,

Dariyar rainin hankali ummi tayi kafin tace ,"yo mommy inba'a fada miki gaskiya ba me za'ayi ,ke haka kike bakyason gaskiya ,saikiyi tayi ai nikam kinga tafiyata ,dan tsuntsun daya jaaa ruwa shi ruwa kan duka ta fada tana shigewa dakinta.

Maryam ma dai tashi tayi ta bar falon ta shige dakinta,

Zama mommy tayi cikin tashin hankali da damuwa,abubuwa sunyi mata yawa,ga damuwar danta daya zurma cikin soyayya da yar da ta tsana fiye da komai.

ga rashin kunyar da yayanta ke tsula mata agaban idonta ko shayinta basayi,

Yanzu mai yakamata nayi ta fada tana sintiri cikin rashin sanin madafa , wayarta ta dauka tana kiran wata number ta shige dakinta.

Kameel kuwa yana shiga dakin nasu kwanciya yayi akan gado, tare da takurewa guri daya.

Gaba daya jinsa yake tamkar wani maraya,kewa da kuma bukatar ganin matarsa suke damunsa , Allah sarki gashi bata da lpy ,

"mommy kincuceni ,kin gama da rayuwata ,kin daukemin farin cikina ,kin rabani da abinda nake matukar so da kauna . Why ?why? mommy meyasa kikamin haka? meyasa ? Ya fada da karfi yana cillar da fillows din dake jere akan gadon .

Tashi yayi kamar wani dan maye ,so yake ya sha wani abun da zai mantar dashi komai ,dan haka bude fridge yayi inda kwalaben giyarsa ke jere.

Dauko daya yayi ya bude cikin zakuwa da son sha ya nufi bakinsa da ita .

saidai kafin ya kaita bakin nashi ya tsay tsak, hannunsa yana karkarwa,tunowa da nasihar da Khadeeja ke yawan masa akan kayan maye dayake sha.

Cilli yayi da kwalbar da karfi ta tarwatse, gaba dayan kwalaben ya rinka cillarwa yana kuka sosai ,duk ya farfasasu gaba daya ,ya koma kan tsadaddun kwalaben turarensa yayita cilli dasu yana ji kamar zuciyarsa zata tarwatse ,

" I hate you momm!!!

Ya fada da karfi yana cilli da wata kwalbar turare da kudinsa yakai 30k.

Karar fashe fashen da Kameel keyi shine ya janyo hankalin iyayen nashi ,suka nufo dakin da gudu ,

Yana zaune kamar wani mahaukaci duk ya hargitsa dakin hannunsa sai zubar da jini yake dan duk ya yanke .

Son menene hakan ?kana so kayiwa kanka illane akan wata banza? Haba sob bafa nice na bata ba.mommy ta fada tana kallon yadda ya ke zubar da jini ahannunsa.

Wani irin kallo da Kameel ya watsawa mommy saida gabanta ya fadi tayi saurin ja baya,

Abba ne ya samu ya shigo cikin dakin ,ya zauna kusa da Kameel ,ya riko hannayensa duka biyun har wanda ke zubar da jinin.

Kameel !! Ka nutsu kasanyawa zuciyarka salama ,kamaida al'amuranka ga Allah . Shine maganin komai arayuwa ,kayi ta addu'a in sha Allahu matarka zata fito aduk inda take".Abba ya fada yana shafa kan Kameel ,

Dora kanshi Kameel yayi akan kafadar Abba, Abba ina sonta ina kaunarta ,bana son tayi nesa dani Abba ji nake kamar zan bar duniyar ,ba abinda nake sonji da gani sai Khadeeja ,Abba ka taimakamin please . Ya fada yana zubda hawaye gwanin tausayi.

In Sha Allah kameel zata bayyana aduk inda take ,zanyi iya kokarina akan ganin ta bayyana kaji? Ya fada yana dan buga kafadar dan nashi.

Mommy kuwa sosai tausayin dan nata ke damun zuciyarta ,amma har yanzu tana nan akan bakanta na kin Khadeeja.

"Son kayi hakuri ka manta da batun yarinyar nan tunda ta riga ta bar gidan, shikenan tayiwa kan.....

Momm !!! Leave me alone ,i hate you !!!!

Ya fada cikin tsawa,jikinsa har rawa yake.

Abba kace ta tafi bana son ganinta ,itace ta batarmin da mata ,ya fada yana rungume Abban cikin kuka.

wani kallo da Abba ya aikawa mommy, saida hantar cikinta ta kada, Sum sum sum,ta fice daga dakin ,dan ta fahimci alhaji kasseem fa ya dawo asalin kaseem dinshi.

Sosai Abba ya kwantarwa da Kameel hankali ,yayi masa dressing din hannu, ya lallabashi ya sha tea tare da alwala yayi salla ,sannan ya kwanta .

Abba ya lullbeshi da bargo sannan ya fice daga dakin.

*********

Yau kusan kimanin wata biyar kenan da batan khadeeja ,

Tana zaune gidan hajiya zainab tayi matukar chanzawa ,tayi fari sosia tayi kiba ,idan ka ganta ahalin yanzu ,to ba lallaine ka ganeta ba dan tayi wani irin canzawa na ban mamaki.

Islam ce ta shigo dakin da khadeejan kezaune da handout ahannunta ,tana dubawa dan tuni doctor ta sanyata awata private school tana karantar bussiness add.

"Khadeeja bakya gajiya da karatu ko tausayin kanki bakyayi ga ciki ajikinki " . Ta fada tana zama akusa da khadeejan .

Murmushi Khadeeja tayi , Tace"toh menene abin wahala akaratu ?kinsan ina matukar son karatu arayuwata ,dole na dage da karatu dan cikar burina da kuma na mommy." Khadeeja ta karasa tana shafa cikinta ,dan aduniya ba abinda take kauna ahalin yanzu irin wanna cikin dake jikinta ,kullum idan ta kalli cikin jikinta tana kara son wanda yayi silar samuwar dan tariga ta gane cewar ta kamu da matsanancin Kameel.

Islam ce tayi dariya tace hakane sister Allah ya cika mana burinmu baki daya .

Ameen !khadeeja tace.

Sukaci gaba da dan taba hirarsu.

Ta bangaren Kameel kuwa idan ka ganshi ahalin yanzu bazaka taba tunani cewa shine Kameel din nan mai keta da cin mutunci .

Gaba daya ya sauya, ya zama shiru shiru kullum yana masallaci yana salla ko karatun kur'ani ko kuma yayi zamansa yana salati..

Sadaka kuwa kullum cikin yinta yake ba dare ba rana ,yanzu kowa nashine, Sam baya kula mommy baya zama a inda take bare har yaci abincin gidan maryam ce kullum ke masa girki tana dan kwantar masa da hankali , Cigiya kuwa kullum cikin yinta ake da sanya kyauta mai tsoka ga duk wanda ya ganta.

Aisha kuwa tun daga lokacin nan data gama zamanta asibiti kusan watan ta biyu a asibiti ,tana warkewa ta koma gidansu ,dan tace bazata zauna Kameel ya kasheta ba ,

Kuma mommy tace ta kwantar da hankalinta, bata da miji sai kameel .

Ankawo kudin auren ,ummi zata auri wani dan kawar mommy data hadasu dashi dan sam taki yarda da samarin da ummi ke kawowa ,wai basu daabin hannu . Gaskiya halin mommy sai ita.

Wata rana khadeeja da doctor dakuma islam sunje super market donyin siyayyar kayan jarirai ,cikin khadeeja wata biyar amma idan ka ganta zakayi tunanin ya kai wata takwas ,dan yayi wani irin girma sosai ,tayi kiba tayi kyau sosai.

Suna zabar kaya ita da islam suna dan hira doctor kuma tana can wajen irin gadajen nan na yara ,

wata riga khadeeja ta dauka zata sanya cikin kwandon kawai sai rigar ta fadi kasa , Durkusawa khadeeja tayi zata dauka amma ta kasa tace "washhh"

da sauri wata matashiyar yarinya ta tsugunna ta dauko rigar tare da mikawa khadeeja tana cewa,

Kiyi ahankali sister kidaina garajen durgusawa haka, Ta fada tana mikowa ,Khadeeja rigar,

Yawwa na gode yar uw....... Cak maganar ta tsayawa khadeeja sakamakon hada ido da sukayi da maryam , Kallon kallo sukewa juna ,saidai ga dukkan alamu maryam bata gane khadeeja ba ,amma yanayin kallon da take mata nason tuno inda kasan mutum ne.

da sauri Khadeeja ta karbi rigar tare da kamo hannun islam cikin gaggawa tace dan Allah islam mu bar gurinnan akwai matsala.

Sun fara tafiya kenan ,maryam tace ku dan tsaya ,ta fada da sauri....

Toh fa masu karatu shin maryama zata gane khadeeja kuwa? Ya kuke ganin kameel zaiyi idan ya sami labarin anga khaddejansa.

Muhadu a next page in sha Allah .

Taku anty mammy

mrs babiπŸ’˜πŸ’˜

Share and comment please,

More comment More typing. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

GIDAN AIKINA πŸ’πŸ’

Na mammy kabeer (anty mammy)

ELEGANT ONLINE WRITER'S

Page 51 /52

"kudan tsaya"maryam tafada da sauri ,

Tsayawa sukayi cak ! Amma Khadeeja taki waigowa,idonta arufe dan bata fatan maryam ta ganeta.

Islam ce ta waiga tana kallon maryam ,dan jikinta ya bata akwai sanayya tsakaninta da Khadeeja ,saidai Khadeejan bata son maryam ta ganeta.

Miko musu poss din Khadeeja maryam tayi ,wacce ta fadi lokacin da tayi arba da maryam din.

Readers Also Read