Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 14
Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 14: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 14. Karba islam tayi tana yiwamaryam din godiya…
3,371 words
Karba islam tayi tana yiwamaryam din godiya ,wacce idonta ke kan Khadeeja ,sosai jikinta ke bata cewa wannan Khadeeja ce.
Tafiya suka farayi cikin sauri duk da cikin dake jikin Khadeejan, hakan bai hanata sauri ba kamar zata kifa. Allah Allah take subar gurin kafin maryam ta ganota.
Sunzo fita kenan Khadeeja ta waigo ta kalli maryam ,
Aikuwa suka hada ido dan itama maryam din kallonta take,
"khadeeja ki daina wannantafiyar mana haka da sauri ,saikinje kin fadi? Doctor ta fada tana biyo bayansu .
Dammmmmm!! Gaban maryam yafadi.
Wllh itace ! Khadeeja ce! Tabbas dama dama jikina ya bani itace ,wayyo Allahna ! Ta fada tana dafe kirjinta cikin farin ciki ,yau ya yaya zaiji idan nakai masa wanna labarin?
Dago kai tayi dan yi musu magana ,amma inaaa sun bar gurin tuni.
Da sauri ta boyo bayansu saidai tana fitowa suna jan motar . Binsu tayi tana daga musu hannu,wait wait , Amma basujita ba .
Saidai Juyowa khadeeja tayi tana kallonta itama tana kallonta har sukayiwa juna nisa.
Ajiyar zuciya Khadeeja tayi tana jin wani iri aranta , Hakika tana son ganin mijinta ,tana ji kamar zatayi hauka saboda soyayyarsa aranta ,amma bata son kara komawa gidan nan kodan tsira d rayuwarta data abinda ke cikinta.
Hawayene suka zubo mata sharrr sai kawai ta fashe da kuka,ta fada jikin islam.
Subhanallah Khadeeja menene ? Me ya faru ? Bakida lpy ne ?
Doctor ta fada tana neman waje ta faka motar, dan basa cikin cunkoson ababen hawa.
Mommy wllh tunda muka hadu dawata a store din Can, naga hankalinta ya tashi, da alama dai sunsan juna saidai ita dayar bata gane Khadeeja ba.islam ta bawa mahaifiyar tata amsa.
Shiru doctor tayi tana nazari,kafin tace "amma khadeeja meyasa baki nunamin ita ba ? Sannan ma wacece wadda kuka hadun ?
Cikin son hana kukanta ci gaba da zubowa Khadeeja ta share hawayen idonta tace"mommy yar gidan danayi aikice"
Kina nufin kanwar mijinki ce ko aishan dake son aurensa?
"Kanwarsa ce mommy" Ta bawa mommyn amsa.
shikenan ki kwantar da hankalinki in sha Allah komai zaizo karshe kinji?.
Cewar mommy cikin kwantar da hankali.
Gyada kai kawai Khadeeja tayi ,ta jingina da kujera,
Zuciyarta na hasko mata kameel ,sosai take jin wani irin so da kaunarsa azuciyarta.
Duk sanda gubar sonshi ta soketa ,haka zata zauna tana kuka tana shafa cikinta ,tana fadin"ina sonka mijina ,ina kewarka ,sannan danka ko yarka suna son kasancewa dakai ,saidai bazan sake ganinka ba ina son na rayu na haifi abinda cikiina ,nayi masa tarbiyya irin wacce babansa ya rasa ,sannan ko badade ko bajima zaizo gareka."
"Allah ka tsaremin mijina ako ina yake ,ka shiryar dashi bisa hanya madaidaiciya."
Tafada ahankali yadda ba wanda zaiji.
maryam kuwa kota kan abinda tazo siya bata biba, kawai mota ta shiga ta nufi hanyar dasu Khadeeja sukabi,
Ammako kadan bata riskesuba.
Haka tanufi gida,cikin zullumi ,dakuma farin ciki .
tana shiga ko rufe motar batayiba ,ta nufi dakin kameel.
Duhu sosai adakin dan komai akashe yake .sai qamshi dake tashi akowace kusurwa ta dakin.
Kunna haske maryam tayi tana neman yayan nata , Yana kan sallaya ya kudundune kanshi akan cinyarsa . Ga carbi ahannunsa ,ya tara uban gashi agemunsa da fuskarsa .
Kai bakace kameel dan gaye bane,yayi wata muguwar rama sai hanci kamar ya karye.
Dago kai yayi ganin ankunna hasken dakin .
Kallon maryam yayi tare da maida kanshi inda ya cire,
zuwa maryam tayi kusa dashi cikin doki ta zauna ,tare da kamo hannunsa ,
Yaya! in sha Allah damuwarka ta kusa kaiwa karshe .
yaya yau nagano maka abinda zaisaka farin ciki da annashuwa. Ta fada tana murmushi harda kwalla a idonta.
Kallonta yake cikin raunananniyar fuska ,kafin yayai murmushi mai ciwo yace"maryam kina ganin ahalin danake ciki yanzu akwai abinda zai sani wani farin ciki? Babushi maryam ,mommy tayi sanadin rabani da duk wani farin ciki nawa ,mommy bata sona maryam" ya fada idonsa na kawo ruwa .
Hannu maryam ta sanya ta share masa hawayen da ya zubo akan fuskarshi,kafin tace"yaya koda labarin ya danganci Khadeejank a?
Zunbur ya mike tsaye yana kallon maryam cikin rawar jiki.
"maryam me kike son fada minne please?" Ya fada yana tsakumota da sauri kamar zai balla mata kafada .
yaya ka nutsu please kaji? Ta fada tana dan zame kafadarta dan taji zafin yadda ya tsakumota.
"Dalla ki fadamin abinda zaki fadamin maryam wane nutsuwa zanyi kinga alamun nutsuwa atare dani?"
Ya fada cikin tsawa.saida maryam ta tsorata ,
Yaya yau naga Khadeeja da idona ! Dararararammmm!! Gaban kameel ya bada wani irin sautin bugu .
saida nima nadan koma baya😜
Maryam tana ina? A ina kika ganta ? Ita dawa ? Kun taho tare? Tana ina maryam ? Ki fada min mana ? Ya jero mata wadan nan tambayoyin cikin rawar murya da rawar jiki, Yana jijjiga maryam din.
Yaya naganta a store ,saidai kafin nayi wani abu tuni ta bar gurin ,na tabbata kuma ta ganeni yaya ,saida ta waigo ta kalleni dazata bargurin ,kuma naji ankira sunanta .maryam ta fada tana kallon yayannata.
Why maryam ? Why? Metasa kika barta ta tafi bayan kinsan ina nemanta ? Me yasa baki kirani nazo ba ? Maryam kina so namutu kema ? Kin daina tausayin yayanki ne maryam .
Ya fada yana jijjigata ,duk da yaji mugun dadin cewa Khadeejansa na cikin garin kano ,amma yaji takaicin da maryam ta barta ta tafi bata riketa ba.
yaya kayi hakuri ,da farko bamganeta nima ,saida ta bar gurin .
Kuma yaya Khadeeja tayi sauyawar da zaiyi wahala mutum ya ganeta lokaci daya.
Zama yayi abakin gado ya dafe kansa . Kafin ya mike zunbur "maryam a ina kikaga Matata?
Sahad store,ta bashi amsa.
Nufar kofa yayi da sauri ya fice ,
maryam tana kwalla masa kira amma ina ko juyowa baiyiba .
So take ta bashi labarin cikin data gani ajikin Khadeeja amma yamaki tsayawa.
Kai tsaye sahad store kameel ya wuce yana ta kallon hanya har ya karasa .
asukwane ya shiga ya fara duba mutane ,yayi nan yayi nan ,haka yayi ta gararanba a store din yana duba Khadeeja ,amma ko mai kama da ita bai ganiba.
Ya gaji sosai ,ga yunwa ga gajiya duk ya fice daga hayyacinsa .
Zama yayi akan wata kujera ya dafe kansa dake matukar sara masa kamar zai rabe gida biyu.
Ya Allah ka bayyanamin matata ! Ka nuna min ita aduk inda take ,karna mutu vangantaba ya fada hawaye na zubowa daga idonsa.
sai bayan magrib sannan ya hakura ya koma gida .
lokacin daya koma su mommy na babban falo suna zaune tanayiwa maryam fadan danme zata fada masa zancen karya wai taga wata khadeeja ?
wacce kilama tana can tana karuwancinta .
Mommy dan Allah ki daina wannan abinda kikeyi wllh bai daceba ,koba komai fa khadeeja yar uwarmuce ta jini abinda mukayi mata abayama cikin rashin sanine ,amma yanzu duk sanda muka hadu zamu nemi yafiyarta. Ummi ta fada tana kallon mommy.
Nikam ummi yaushe kema kika zama sallamammiya ne? Yanzu akan wannan shegiyar kuka tasani agaba kuna tamin wani zancen banza?
Tih bazan daina abinda nakeyinba dan ubanku ,ku dauki mataki.ta karasa cikin fada da bacin rai. Tabe baki yaran sukayi maryam tace"
Allah dai yana kallonki duk mugun abunda zakiyi. Ta fada cikin rashin shayin uwar, dan ba wani girmanta suke ganiba, tunda ta batasu tun suna yara.
Cikin takaicin rashin damuwa da damuwarta da yayan nata suke nunawa take kallonsu ,tana harararsu ,
Shegun yara masu halin dangin ubansu na bakin hali.ta fada tana tagumi dan abin ya fara isarta ,kwata kwata kameel ya daina mata magana ko tazo inda yake tashi yake daga gurin sam ko kallo bata isheshiba.
Sanna ga yan matan suma sam basajin maganarta ,ko suji tausayin halin damuwar da take ciki. Ga mahaifiyar aisha kullum cikin barazanar tona mata asiri agurin mijinta take .
Shikansa alhajin yanzu baya daukar raininta ,sam baya raga mata sosai yake rufe ido yayi mata tass,alamar asirin jikinsa ya karye.
Abin duniya ya isheta yayi mata yawa ,shiyasa kullum takekara tsanar Khadeeja aranta .
Kameel kuwa koda ya shigo kai tsaye dakinsa ya nufa bai ko kalli inda suke zaune ba.
Yana shiga yayi alwala yayi salla ya zauna ya dauko alkur'ani mai girma ya fara rairo karatu .
Sosai zakuyi mamakin yadda kameel ke karatun alkur 'ani cikin murya mai dadin amo da bawa kowane harafi hakkinsa.
Tuni ya koma makaranta duk dare yana daukar karatu amasallacin kofar gidansu .
Kuma dama ba jahili bane duniyace ta shagaltar dashi.
Amma yanzu sanadin Khadeeja ya koma ga Allah ,baida aiki sai karatun alkur 'ani ko zikiri da istigfari,sadaka kuwa kullum cikin yinta yake .
Tun daga wannan ranar kullum kameel sai yaje sahad store ,yayi ta neman Khadeejansa ,domin yana kyautata zaton wata rana zai ganta agurin .
khadeeja kuwa ta maida hankali sosai tana karatunta ,kasancewar makarantar private ce akwai karatu sosai .
Gaskiya idan mutum bawai yayiwa khadeeja kyakykyawan sani bane, toh zaiyi matukar wahala agareshi ya ganeta lokaci daya.
Tayi wani irin kyau na ban mamaki ,tayi kiba tayi mulmul da ita .
Ga cikinta yayi girma sosai kamr bana wata biyar ba ,yayi mata das ajikinta .
Yanzu khadeeja ta zama classic baby inka ganta zakayi tunanin yar wani hamshakin mai kudince.
Suna zaune ita da islam afalo ,domin mommy tana asibiti.
Ni kuwa sister in tambayeki mana? Cewar islam tana cin apple.
"ina jinki sister tambayeni ko menene zan baki amsa ,"
Cewar khadeeja cikin wani salon magana da jan aji ,sosai fa khadeeja ta sauya ,hadda salon maganarta abin burgewane ga mai sauraro.
nikam khadeeja dan Allah kima son mijinki kuwa? Cewar islam.
Dammm!! gaban khadeeja ya buga ,dan tambayar tazo matane abazata,
Ajiye apple din hannunta tayi ,cikin mutuwar jiki.
me zatacewa islam ,tariga dai tasan cewar, idan tace bata son kameel tayi karya .
Dan haka kallon aisha tayi cikinn murmushin yake tace "ke kuwa sister me ya kawo wannan tambayar ana zaune kalau?"
Hmmmm khadeeja kenan! Nifa yar uwarkice ,ya kamata ki fada min abinda ke cikin zuciyarki game da kameel.
Shiru khadeeja tayi ,gani take idan tace tana son kameel za aga wautar tane ,domin kameel ba ajinta bane ,yafita gata ,ya fita kudi,sannan kuma ga kyau ga nera. Ta yaya tana yar aiki zata zurma kanta cikin abinda yafi karfinta .
Duk da kameel ya furta mata kalmar so , tasan ya fadi hakanne danya karbe mata budurci ,amma bawai dan yana son nata da gaskeba.
Sister ki fadamin gaskiyar abinda ke zuciyarki,domin mu sami mafita kafin lokaci ya kure mana. Islam ta fada tana kallon khadeeja.
Kallonta khadeeja tayi kafin,ahankli ta bude bakin cikin ajiyar zuciya tace" islam bazan boyemiki sirrin dake cikin zuciyata ba, Domin koba komai nasan zaki bani shawar ta gari,kuma hakan zai ragemin radadin danakeji cikin zuciyata.
Tayi shiru tare da ajiyar zuciya,sannan taci gaba cewa"
"islam !! Na jima da soyayyar kameel acikin zuciyata, tunda nake ban taba jin son wani abu aduniya sama da yadda nake son kameel ba ,hakan nema yasa duk abinda yake min ban taba jin na tsaneshiba ,
Kullum burina shine Allah ya shiryar dashi ,na sha tashi cikin dare nayi masa addu'ar shiriya .
islam ina son kameel sonda ni kaina bansan irin saba ,kuma bansan ina sonshiba sai yanzu .
Duk irin cin mutuncin da zaiyimin ,nakansamu nutsuwa da kwanciyar hankali idan yana kusa dani,
Islam ina son mijina ,amma dole na cire hakan araina dan nasan yafi karfina." Ta fada hawaye na zubowa daga idonta.
Rike hannunta islam tayi cikin tausayawa sosai tace" Khadeeja na jima da sanin kina son mijinki, Domin nasha jinki kina mafarkinsa ,
Shin khadeeja kameel ya taba nuna miki alamun soyayya ko kuma ya fada miki yama sonki? Islam ta karasa maganar da sigar tambaya.
Girgiza kai khadeeja tayi ,kafin tace ,
"bai taba nunamin alamun soyayyaba ,saidai lokacin daya karbi budurcina ,kuma nasan wannan dan ya san ya rabani da abinda shine kadai gatana.
saidai nasan yana nunamin kulawa daidai gwargwado ,daga baya ya daina takuramin sanan yana fada harda mahaifiyarsa akaina idan tayi min ba daidaiba."
Hmmm khadeeja tabbas kameel yana matukar kaunarki shima ,kuma bakomaine yasa yake cin mutuncinki ba,saidan yana ganinbkamar ya wuce ajinki ,kuma ta yaya zai kamu da sonki? Wannan shine dalilin daya sa yake cin mutuncinki.
Inba hakaba yana da damar dazai hukuntaki ba tare da ya aureki ba,
Soyayyarkice ta sanyashi auroki ,ba wai daukar mataki ko fansa ba.
Amma hakika kameel yana kaunarki fiye da yadda kike tunani ,tunda har zai iya fada da mahaifiyarshi akanki, wllh ko kaffara bazanyi ba kan cewar kameel yana mugun sonki da kaunarki. Islam ta karasa tana kallon khadeeja cikin murmushi ,
Amma ya zama dole koda kin koma gareshi ki kama kanki ,karki nuna masa soyayarki da sauri har saikin gano wane irin karfi soyayarki tayi agareshi ,ta fada tana jinjina hannun khadeeja da take rike dashi.
Wani irin farin cikine yake lullube khadeeja har cikin bargonta ,
"da gaske kike islam ? Kameel yana sona ? Kin tabbata yallabai yana kaunata? ta fada hawaye na zubomata na farin ciki.
Yana sonki na tabbata khadeeja ,yallabai dinki na kaunarki sosai.
Rungume islam Khadeejatayi cikin tsantsar farin ciki ,tana kukan dadin Kafin ta bude baki tace.......
Masu karatu me zakuce game da khadeeja ,ashe dama ta jima da fadawa cakwalkwalin soyyaya bamu saniba 🤔
sainaji daga gareku ,taku anty mammy🙏🙏
Mrs babi 💘💘
Share and comment plesae. More comment more typing. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
GIDAN AIKINA🍒🍒
Na mammy kabeer (anty mammy)
ELEGANT ONLINE WRITER'S
Page 53 /54
Rungume islam KhAdeeja tayi ,ciki tsantsar farin ciki tana kukan dadi . Kafin ta bude baki tace.
"Na gode islam kin sani cikin farin ciki yau,kin karfafamin gwuiwa ina godiya mai tarin yawa agareku,
Kun taimakeni adaidai lokacin da nake bukatar taimako ,kunyimin komai arayuwa Allah ya biyaku da mafificin alkairi. Ta karasa tana kuka tare da kara rungume islam sosai ajikinta.
Hakika ba abinda zata cewa wadannan bayin Allahn ,sunyi mata karamcin da yan uwan na jini ma basu mata ba, Bazata taba mantawa da wadannan bayin Allahn ba.
Kinga nikam karki fara min wannan kukan naki na shagwaba ,salon mommy ta dawo tace na taba mata yar lelenta ko.? Islam ta fada tana sharewa Khadeeja hawaye.
Dariyar kuka khadeeja tayi kafin ta dan harari islam tace,
" Ato mutum ya bari mommy ta ganni ina kuka yasha bulala" ta fada tana murmushi.
Rufamin asiri ranki ya dade ,da girman kujerarki mrs kameel kiyi shiru kafin mommy taci kaniyata .islam ta fada itama cikin murmushi tana mikawa Khadeeja apple .
Karba tayi tafara ci suna hira ,Allah ya taimaki Khadeeja cikin nata bamai laulayi bane sam ,kuma komai ta samu ci take , Dan ita batasan ma tana da cikin ba saida yayi wata uku , Shima mommy ce ta fada mata.
Ranar tayi murna kamar zatayi ihu dan dadi ,
Kameel kuwa ya dage da zuwa sahad ,kullum yana can ,har sunyi sabo da yan gurin. yanzu baya yawon nemanta saidai su bashi ya kalla ta cctv cemera.
Kuma suna tausaya mashi sosai ,dan ya fada musu natarshi ce ta bata kuma ance an taba ganinta anan gurin shine yake zuwa dubata.
Rayuwa fa tayiwa baba umaru zafi ,dan gaba daya kudin nan dasuka karba agurin kameel ya kare tass, Komai ya cunkushe musu.
Gashi yanzu zainab ta dauko musu abin kunya, dan tana nan da katon cikinta na shege,tayi kokarin zubarwa likita ya ce idan aka zubar da cikin zata iya rasa rayuwarta ,dan wannan shine na kusan biyar da take zubarwa.
Haka ba yadda suka iya suka hakura suka zauna da cikin.gashi babban danshi na mijin ya zama rikakken baro ,sata kala kala ba wacce bai iya ba . Gashi indai ka aiki yarka mace a anguwa saiya sata alungu ya lalibeta,
Abin duniya ya taru yayi masa yawa,bashi da cin yau bare na gobe ,dama zainab ce ke kawo musu .
toh itama yanzu tana fama da kanta . Tayi baki ta rame kamar ba itaba.
Toh sai muce dama abinda ka shuka wataran shi zaka girba.
Bangaren mommy kuwa, abin ba'acewa komai ,dan yanzu damuwa tayi mata yawa sosai , Saidai kaganta ta zauna tayi tagumi tana tunani .
Miji ya juya mata baya ,yaya sun rainata baruwansu da damuwarta, Sannan dan lele shima ya kauracewa gidan ma gabadaya .
Idan ya fita tun safe sai gomn dare yake dawowa yana can neman khadeejansa.
ahaka akayi bikin ummi da mijinta mahmud dan gidan wata kawar mommy ce ,babansa minista ne yana da mugun kudi sosai .
Bayan anyi biki anwatse lpy ,wannan karon harda yan uwan abba akasha bikin ,bakin ciki kamar ya kashe mommy .
wai yan uwan Abba sunzo sun cika mata gida suna neman gindinn zama ,habaici kala kala sunsha shi ,amma bayin Allah ko takanta basu biba.
Wata rana khadeeja sun taso daga makaranta,yau sai yamma suka gama lecture gaba daya agajiye take suna dan takawa da islam dan ba wani nisane tsakaninsu da makarantar ba .
Dan haka akafa suke tafiya saboda khadeeja ta dan warware jininta.
Sunyi nisa dan sun kusan zuwa gida ma, kawai gaban khadeeja ya yanke ya fadi ,har saida ta dafe kirjinta tare da runtse idonta da karfi tana salati.
da sauri islam ta riketa ,khadeeja lpy kuwa? menene?
Shiru khadeeja tayi tana waige waige ,aikuwa idon tane ya sauka akan kameel , Wanda shima yana cikin tafiya amotarsa kawai yana zuwa saitin dasu khadeejan suke gabansa yayi wani mugun faduwa, cikin sauri ya tsayar da motar yana dafe kirjinsa .
"Tabbas khadeeja na saitin gurin nan "ya fada yana bude motar da mugun sauri yana waige waige shima.
Da sauri kjadeeja ta ja hannun islam suka buya abayan wata gatuwar bishiya,
Tana dafe da kirjinta ,"meke damun yallabai kameel haka? Ya naga ya rame sosai ? Gashi ya tara gemu kamar bashiba?"
Sister wai menene ke faruwane naga kin janyo mu nan gurin?kodai wani abu kika gani? Islam ta tambaya ganin yadda Khadeejan ta wani rude sai haki take ,
Mika hannu tayi tana nunawa islam jakarta dake hannun islam din.
Fahimtar me take nufi yasa da sauri islam ta bude jakar ta dauko mata inhelarta ta mika mata.
Karba tayi tare da shaka tana sauke ajiyar zuciya.
dan lekawa tayi ,har yanzu kameel na gurin sai waoge waoge yake ,da alama kana ganinsa kasan wani abu yake nema .
Kamo hannu islam tayi ta nuna mata inda kameel yake da hannunta.
Kallon gurin islam tayi ,ta kurawa kameel ido ,tabbas ko ba'a fada mata ba wannan shine kameel din Khadeeja.
Masha Allah shine abinda islam ta fada tana kallon kameel ,wannan mutum ne kuwa ko aljani? Dan ita gaskiya bata taba ganin muyum bai kyau da tsari irin wannan mutumin ba ,mutum saikace balarabe?
Kallonta Khadeeja tayi ganin yadda ta shagala da kallon kameel din,sai taji wani iri aranta ,haushine ya kama khadeejan ta dan harari islam din,kafin ta janyota da dan karfi.
Da sauri islam ta dawo hayyacinta, tana kallon khadeeja ,cikin dan jin kunya tace"sister wannan shine yallabai kameel?
Gyada kai kawai khadeeja tayi batace komai ba.
Gaskiyane banga laifinki ba ,dan kin kamu da son wannan mutumin . Dan ba wacce zata ganshi bata gyasaba,koni nan wllh ya burgeni matuka. Islam ta fada azuciyarta ,amma afili cewa tayi "amma sister anya ba ganinki yayi ba kuwa? Dan naga da alama wani abu yake dubawa mai muhimmanci agareshi .
Kamo hannunta kawai khadeeja tayi ,tare da cewa"mu tafi islam"
Saida islam ta kara juyawa ta kalli kameel kafin suka bar gurin da sauri. Zuciyar khadeeja na wani irin azalzalarta akan ta kara juyawa ta kalleshi ,amma taki bata hadin kai.
Kameel kuwa waige yake tun karfinsa ,ya waiga can ya waiga ,can kamar wani zararre.
Tabbas yasan khadeejan sa na kusa da wajen nan. Amma ta ina take? Wane wajen take anan? Ya fada azuciyarsa yana dafe saitin zuciyar.
Ahankali kuma yaji bugun zuciyarsa yana raguwa ,alamar khadeejansa nayin nesa dashi,
"Nooo!! Khadeeja karki tafi please ki tsaya kusa dani dan Allah " Ya fada idonsa alumshe,baidamu da yan tsirarun mutanen dake kallonsa ba, dan abinda yake kamar wanda ya zautu.