Kenza eBookz

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 15

Complete book: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy)Chapter 15 of 21FantasyBy Mamy Kabir (aunty Maamy)

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 15

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 15: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 15. Shiru yaji zuciyarsa ta daiab bugawar ta koma…

3,361 words

Shiru yaji zuciyarsa ta daiab bugawar ta koma normal yadda take ada, Lumshe idonsa yayi tare da shiga cikin motar, ya fifa kansa akan sitiyarin motar yana ji kamar ya kwalla ihu,

Yau kimanin watanni biyar da kwanaki rabon daya sanya khadeeja a idonsa,yazaiyi da rayuwarsa? Ya zaiyi da dunbin sonta daje barazanar tarwatsa zuciyarsa? "Ya Allah help me"

Ya fada idonsa na tsiyayar da kwallah, Gaskiya so bala'ine ! So masifane ga wanda Allah ya jarabta , Kuduba izza ,isa ,takama irin na kameel ,amma yau gashi yana kuka da idonsa akanso,

Fadar manzon Allah ne (s a.w) karka tsananta kiyayya domin wataran tana iya komawa so.

Sanna karkatsananta so wataran yana iya komawa kiyaya. Yanzu dai kuduba kameel ,dan hakin daya raina bama tsoke masa ido yayi ba ,so yake ya tsiyayar da ruwan idon . Allah ka barmu da masoyanmu na hakika ameen.

Haka kameel ya karaci tsayuwarsa agurin kafin ya nufi gida dan yau bazai iyazuwa sahad din bama ,yadda yakejin zafi azuciyarsa da gangar jikinsa

Zazzabine sosai ajikinsa Allah ne kawai ya kaishi gida lafiya, yana zuwa ya shige dakinsa ya kwanta yana karkarwar sanyi.

Bayan sati biyu da faruwar wannan abun, Sosai kameel yasha jinya dan har saida ya kwanta agadon asibiti ,da gyar yayi kwana uku asibitin yace gida zai koma ,

Tayaya zai zauna ana kuma khadeeja taje sahad baya nan ?bazai yiwuba doke yau ya bar asibitin nan.

Da gyar Abba ya lallabashi suka koma hida yayi wanka ya danci abinci da magani sanan ya fice shi kadai ko guard dinsa yanzu baya yaeo dasu.

Haka kawai yau khadeeja taji tana son fita yawo ,dan haka mommy ya fadawa zasu sahad su dan siyo kayan makulashe,

Allah ya kiyaye mommy tayi musu tare da basu kudi.

suka tafi , Khadeeja sanye take da doguwar riga sai katon hijabi har kasa,dan tunda take ita bata taba sanya mayafi ba tafison hijabi bare yanzu da take da aure.

sai islam datake sanye da doguwar riga tayi rolling da mayafin.

Suna tafe suna hira ,gaban khadeeja sai faduwa yake ,amma tayi shiru tana addu'a azuciyarta Har suka isa sahad store.

Kameel yana zaune akan kujerar sayake zama yana kallon masu shiga da fice acikin store din ,

Kullum baya dauke idonsa akan computer din nan ,amma yau kam idonaa alumshe yake sakamakon wani irin yanayi dayake jinsa aciki mai kama da fargaba, farin ciki ko tsoro .

Dan haka baiga shigowar su khadeeja ba .

Sukuwa shiga sukayi suna ta siyayyarsu,saida gaba daya khadeeja bata jin dadin jikinta , Wani iri takeji Sun siyi abinda zasu siya suka dan zauna dan khadeeja tace ta gaji kuma gabanta zai faduwa yake,

Sister ko ruwa zan samo miki? Islam ta tambaya ,

"Aa sister idan na dan huta ma an ware jikina ne ba dadi ji nake kamar wani abu zai faru dani," Khadeeja ta fada cikin cikowar hawaye a idonta.

Ba komai sister in sha Allah alkairine zai faru dake kidaina damuwa kinji? Cewar islam tana kokarin kwantarwa da khadeejan hankali.

Gyada kai khadeejan tayi tana murushin karfin hali.

Allah yasa haka yar uwa ,amma jikina na bani wani gagarumin abu na shirin faruwa dani.

Khadeeja ta fada idonta nakan islam .

Karki damu sister Allah na tare damu kinji ?haba Mrs kameel , Wllh sister mijinki ya hadu sosai ,ko wace mace zataso ace shine mijinta ,nidai fatana Allah ya bani koda wanda yayi rabinsa ne ,ga kyau ga kudi ga salo ,wow sister gaskiya kinyi dace fa. Islam ta fada tana kallon khadeeja da murmushi.

Khadeeja kuwa wani kishine ya turnuke zuciyarta, Danme islam zata rinka yabon mijinta haka ? Harda cewa dama ta sami irinsa?

Dan hade rai khadeeja tayi batare da tasan tayi hakan ba ,

Dan harga Allah batajin dadin yadda islam ke wani koda mata miji.

"hmmm sister kodai kina son kameel din nan ne?

khadeeja ta tambaya cikin dan hade rai ,

Kana gani kasan kishine ke dan tabata.

Dariya islam tayi cikin tsokana tace" Kai sister kuma kishin hardani za'a nunawa?

Ki kwantar da hankalinki,yallabai kameel na deejen mommy ne kadai .

Kuma har abada bazan taba son koda wanda kikayi soyayya dashi bane bare mijinki, Ta fada tana dafa kafadar khadeejan .

Kunyace ta kama khadeeja ,

Tadanyi murmushi tace nima fa wasa nake miki sister,

Dariya islam tayi tana cewa ohh!! Su khadeeja irin wannan kishi haka ?

Gaskiya kameel sai yayi da gaske idan ya tashi karo amarya .ta fada cikin tsokana tana dariya.

"Allah ya kiyaye wllh bana son kiahiya nikam ki daina yimin wannan fatan" ta fada taba turo baki.

Sorry siaterna wasa nake miki ,kinji bana miki fata ,ke kadaice gurij kameel hajiyata.

Dariyar farin ciki khadeeja tayi tana hararar islama cikin wasa.

Tashi tayi suka nufi gurin biyan kudi ,suna tafe ahankali ,kawai gaban khadeeja yayi wani irin bugawar da saida ya haddasa mata wani irin sarawar da kanta yayi ,da sauri ta dafe kanta tace "washhhhhh???

Sai kuma jiri ya kwasheta ta tafi luuuuuuu zata fadi ,

Kara ta kwalla sakamakon ganin zata fadi idonta arufe rubbb !! Tana jiran tajita akasa.

Saidai maimakon ta jita akasan, sai ji tayi ta fada wani jiki mai mugun kamshin da takeji kamar ta taba sanin irinsa,

Bude ido tayi ahankali ta sauke akan wanda ta fada hannun nashi...

Toh fa !!! Masu karatu hannunwa khadeeja ta fada?

Wanene wannan mai kashin d Khadeeja takeji kamar ta sani? Amsar ku na ga anty mammynku🙏

mrs babi💘💘

Share and comment please.

More comment mo typing. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

GIDAN AIKINA 🍒🍒

Na mammy kabeer (anty mammy)

ELEGANT ONLINE WRITER'S

Page 55/56

Bude ido khadeeja tayi ahankali,ta saukesu akan wanda ta fada hannunsa.

Gaba dayansu zaro ido sukayi saka makon sarkewa da idonsu yayi cikin na juna,

Kameel ne rike da khadeejansa ahannunsa, Ya zaune agurin daya saba zama haka kawai yaji ya zabura ya tashi, Sakamakon bugawar da zuciyarsa tayi ,hakan ya tabbatar masa khadeeja na gurin nan.

Haka yayi ta bin sautin bugun da zuciyarsa keyi har gurin dasu khadeeja ke tafiya.

Daga nesa ya hangosu ,tabbas wannan khadeejansa ce ,domin ko mutuwa yayi ya dawo zai gabe khadeeja.

Tahowa yayi gareta cikin sassarfa ,kawai yaga ta yibaya zatafadi,

Wata irin suba yayi ya karaso gareta shine ta fado ahannunsa. Ido suka kurawa juna na tsawon lokaci ,kowannensu ya kasa koda kwakwkwaran motsine ,

Yana rike da west dinta daya hannun na rike da kafadarta , Ita kuma ta rike gaban rigarsa kamm.

Cikin wani irin rawar murya da tsantsar farin ciki kameel ke motsa bakinsa yana son yin magana ,saidai tarin farin cikin dake tare dashi ya hana muryarsa fitowa ,

Itama khadeeja kallonsa take cikin bugawar zuciya da wani irin farin ciki mai tattare da fargaba ,yau kam ta kasa dauke idonta akan kameel ,kamar yadda shima ya kasa cire nashi idon daga cikin nata.

Kowa na karbar sakon dake cikin zuciyar dan uwansa ta cikin idanu.

Hawayen kameel ne ya zubo akan fuskar khadeeja ,dan motsawa tayi alamun zata tashi ,

Sai lokacin kameel ya sami karfin gwuiwar kiran sunanta.

KHADEEJA!!! Yaja harafin cikin wani irin shaukin so da kauna,mikar da ita yayi tsaye ,baibata wata dama ba kawai ya rungumeta ,

Tsamtsam ya rungumeta ajikinsa yana wani irin ajiyar zuciya ,zuciyarsa na wani irin racing na ban mamaki.

Hawaye ne kawai ke sauka akan idonsa yama kasa magana, Kara rungumeta kawai yake ajikinsa yana wata irin ajiyar zuciya,

Itama khadeeja bata san sanda ta rungumeshi ba ,tana kuka saidai bata bawa kukan nata damar fitowa ba .

Dagata kameel yayi yana juyi da ita ,kamar afilm ,mutane sai kallonsu suke ,amma ko kadan kameel bai damu ba.

Ahankali ya dago da fuskarta ya zuba mata ido kuri yana kallonta ,

"ina kika shiga kika barni cikin azaba da radadin zuciya? Meyasa kika ki dawowa gareni ? Khadeeja na kusa mutuwa da rashinki, Kinsan yadda nakeji azuciyata kuwa ? Why khadeejana ? Why ? Ya fada idonsa na zubar da kwalla sosai, Ya kara rungumeta ajikinsa ,

Allah na gode maka ,kafitar dani daga cikin halin da nake ciki ,ka misanya da muwata da farin ciki,ka dawomin da rayuwata Allah na gode maka" ya fada yana kara rugungumeta ajikinsa,

Khadeeja kam tayi shiru tana sauraron sururun da kameel kayi, Kenan ya shiga damuwar rashina shima? Ya damu dani ne sosai haka? Wayyo Allahan kasa ya damu dani yana sona kamar yadda nake sonshi,kasa yana jin irin abinda nakeji game dashi.

ilslam fa ta koma gefe ta zama yar kallo ,sosai abin ya bata tausayi ya kuma burgeta ,wannan wane irin sone haka? Allah ka bar wadannan masoyan su rayu da junansu.

Kallon khadeeja kameel Yayi "i missed you so badly my wife ,please kizo mu tafi gida kinji ,ya fada yana kamo hannunta.

Zame hannunta tayi tare da dan kawar da kanta gefe ,tana turo baki.

Kallonta kameel yayi gaba daya ta sauya ,ta zama wata zazzafa ,tayi kyau ainun ,ga alamar hutu da jin dadi atare da ita ,ji yake kamar amafarki ,wai khadeejansace wannan .

Cikin dan daga murya yace "Allah na gode maka rayuwata zataci gaba da tafiya kamar da koma tafi dadin ,farin cikina ya dawo gareni Alhamdulillah ya fada yana sanya gabansa gabas yayi sujudid shukur.

Islam ce ta matso kusa da khadeeja ta dan dafata tana murmushi ,karki bada kanki yar uwa ta akwai bukatar mu gano asalin abinda ke cikin zuciyarsa.

Girgiza kai khadeeja tayi alamar tana sane da hakan , Kafin ta kama hannun islam din suka fara tafiya,

Saidai taku daya biyu taji anriko hannunta .

Tsayawa tayi cak tare da runtse idonta da karfi gabanta na matsanancin bugawa.

"ina kike tsammanin sake tafiya ki barni khadeeja? Kina tunanin zan kara barinki kiyi nisa danine? Har abada bazan kara wannan gangancinba , Mutuwa ce kadai zata kara nesantani dake ,karki gujeni akaro na biyu wllh mutuwa zanyi.

Da sauri khadeeja ta juyo tana kallonsa ,gabanta na fafuwa kamar zai fito waje ,mutuwa kuma idan ka mutu nima mutuwa zanyi ,ta fada aranta,

Kallon juna suke bako kyaftawa ,kana kallonsu kasan so na wahalar da zukatansu.

sannan farin cikinsu sam yaki boyuwa akan fuskokinsu,saidai khadeeja na kokarin boye natan ,amma abin yaki yiyuwa,

Zame hannuta tayi ta juya taci gaba da tafiya ,bin bayanta kameel yayi,yana tunani aransa , To me hakan ke nufine ? Batayi farin ciki da ganinsa bane kome? Yasan cewa abinda aka mata dole ranta ya baci, amma shikam ai tasan baida laifi ?

koda sukaje gurin biyan kudin bata tsaya ba fita tayi ,zuwa wajen motarsu,

Kameel kuwa mukullin tsadajjiyar motarsa ya mikawa Managern gurin as a gift ,ya fice da saurinsa,

Dan haka ko kudin kayansu islam ba'a karbaba dan suna ganin abinda ya faru agurin ,

Yana zuwa shima ya shige cikin motar ya zauna inda khadeeja ke zaune yana kallonta kamar yau ya taba ganinta.

khadeeja kuwa cikin daure fuska tace" malam lafiya kuwa ?zaka shigo mana cikin mota kai tsaye?

"Haba khadeeja wai baki Ganeni bane ? Nine fa kameel mijinki ,dan Allah khadeeja ki manta da komai kiyi hakuri ki zo mu koma gida please,ya fada yana rike hannayenta.

shiru tayi dan gabanta sai bugawa yake ,wani irin so da kaunarsa ne ke baibaye dukkan wani sassa na jikinta ,ji take kamar ta rungumeshi ajikinta tayi ta kuka,ko hakan zi rage mata radadin da zuciyarta keyi.

Shigowa cikin motar islan tayi taga kameel azaune ,zama tayi agurin driver taba kokarin tada motar ,

cikin fada khadeeja tace "islam kice ya fice ko kuma ni nafi "ta fada cikin muryar mai son yin kuka.

"Plaese khadeejana dan Allah karki gujeni ,nasha wahala wajen nemanki kiyi hakuri da duk abinda ya faru abaya ,dan Allah karki kara gujemin akaro na biyu,ya fada yaba janyota jikinsa ya kankameta tsam gabasa na wani irin bugawa da mugun karfi,

Kwanciya khadeeja tayi ajikinsa lamo,tana saurarin yadda zuciyarsa ke bugawa da karfin gaske

Shiru sukayi dukansu kowa yana jin irin bugun da zuciyar dan uwansa keyi, Islam kuwa wani irin tausayinsu ne ya cika mata zuciya ,gaskiya su mommy sun dau alhakin bayin Allahn nan dubi wanna kayan tausayin dan Allah!

Zamu iya tafiya? Islam ta fada ahankali.

"Muje yar uwa kameel ya fada yana rungume da khadeejansa.

Kunna motar islam tayi suka nufi gida.

Shiru bakajin motsin komai sai sanyin a,c dake tashi acikin motar.karatun alkur ani mai girma islam ta kunna, cikin Kira'ar sudais ,inda yake karanta suratul mulk ,

Ajiyar zuciya suka rinka saukewa ahankali nutsuwa da imani na kara shiga zukatansu,suna tuna iko da kudirar ubangiji.

Sosai kameel ke jin wata nutsuwa da farin ciki azuciyarsa ,lallai ,duk wanda yace wayyo toh hakika ya manta da ubangijinsa , Yanzu dubi irin yawon nema da wahalar dayasha akan khadeeja ,sai gashi Allah ya nuna masa ita alokacin d bai taba tsammataba ,Allah shine abin godiya. ya fada aransa yana ,yana kara rungume khadeejan .

Ita kuwa tayi shiru tana jin wani irin dadin da bata taba jin irinsaba arayuwarta ta duniya ,lallai Allah yayi ikonsa akansu domin da alama shima kameel yana cikin matsananciyar soyayya shigen wacce take ciki koma tafi wacce take cikin.

haka suka karasa kofar gidansu islam din ,bata tsaya ba ta shige cikin gidan ta sanar da mommy abinda ke faruwa.

Sukuwa suna cikin mota khadeeja na son fitowa amma kameel ya riketa gam yace shi bazai iya barinta ta fita ba kawai ta tsya yayi waya azo adaukesu su koma gida.

Kallonsa khadeeja tayi tare da murguda masa baki tace" "Ni kaga malam ka gyaleni in tafi gida ,haka kawai zaka zo ka takurawa rayuwata "ta fada tana turo baki ,

Kamota yayi sosai zuwa jikinsa ya rike fuskarta ya hade goshinsu ,yana kallon cikin idonta,

Dan Allah deejena ki zo mukoma gida nayi missing. Dinki kamar hauka , Allah kin kusa rasani fa ya fada yana matso da bakinsa zuwa nata ,

Kokarin dauke kanta take amma yayi carab ya cafki bakinta ya fara tsotsa kamar ya samu alawa,

Shiru khadeeja tayi itama tana dan kokarin kwace bakin nata,amma zuciyarta na hanata ,dan ba karya tayi kewar soyayyar mijin nata ,

Shikuwa kameel sosai yake son ya huce akan bakin nata ,kissing dinta yake tun karfi ,jikinsa har ya fara rawa .

Da sauri ta cire bakinta daga nashi ganin yana kokarin cinye mata baki ,kuma sakonsa ya fara ratsa jiki da kwakwalwarta .

Dan shagwabe fuska yayi kamar wani yaro cikin shgawba yane ,

"ni dai ni dai ki bani abuna wllh bai isheni ba kika kwacemin ,ya fada yana kallon dan bakin nata ,

Turo baki tayi ,toh haka kawai zaka cinyemin lips ,kabar masoyana da kuka.ta karasa tana murguda baki.

Waye masoyan naki inbani ba, kuma konacinye ai nawaneko,ya fada cikin shagwaba .

Sosai kameel ke jin kansa kamar wani dan yaro ,ji yake yana bala'in so yayi ta mata shagwaba dan tahakene kawai yake ganin zai fanshe kwarta da yayi.

"khadeejana !! Ya kira sunanta da shakakkiyar murya,cikin wani salo na daukar hankali,

Shiru khadeeja tayi dan har cikin ranta taji kiran dayayi matan ,

Kamo hannuta yayi ya rike gam cikin nashi yana kallon fuskarta .

Yace"khadeeja ina sonki ! Ina matukar kaunarki azuciyata, kece haske arayuwata ,khadeeja ki yarda dani ,khadeeja bazan iya rayuwa babu keba .

Ya fada yana sumbatar hannunta ,

Wani yummmm khadeeja taji tundaga kanta har tafin kafarta ,"Allah yasa har cikin ranshi yake fadar wanann maganar ,wayyo Allah na ni khadeeja danafi kowa farin ciki ta fada tana sunkuyar da kanta.

Dago kanta yayi da hannunsa yana kallonta yau kam fadin irin farin cikin dake cikin zuciyar kameel sai Allah , Shikam zai iya cewa bayan first nit dinsu ,bai tana cintar kanshi cikin farin ciki irin na yau ba.

" ina sonki deejena,wllh kece rayuwata ,ina son kasancewa dake har karahen rayuwata, Dan Allah kizo mu koma gida ,ina son ganinki da ciki ,ki haifamin yara masu kyau kamarke,ya fada yana kissing din goshinta,

"Hmmmm ciki kuma ? Bayan wanda kayi min dake jikina . Yana nufin kenan bai kula da cikin dake jikina ba? Hmmmm.

Bude baki kameel yayi zaiyi magana sukaji an kwankwasa kofar motar .

Da sauri khadeeja ta kwace hannunta ta bude murfin motar ta fito .

Da sauri shima ya fito ya tsaya akusa da ita yana rike da gefen hijabinta.

Dariya islam tayi ganin abinda kameel keye,

Shima murmushi yayi yana kallon fuskar khadeeja ,datake wani marairaicewa kamar zatayi kuka tana kallon yadda ya wani rike mata gefen hijabi kamar wacce zata gudu.

Kashigo inji mommy ,islam ta fada tana yin gaba .

Khadeejama binta tayi da dan sauri,amma tuni kameel ya riko hannunta ,yana tabe fuska kamar zaiyi kuka "ni karki tafi ki barni zanyi kuka Allah ,ya fada yana turo baki.

Ita wllh khadeeja har kunya ma yake bata shi ko kunya bayaji yayi ta mata wasu abubuwa kamar yaro , Harara ta galla masa ta yi gaba yana biye da ita har ciiin gidan.

Zama yayi kusa da khadeeja har kafadarshi na gogar tata ,kallonshi khadeeja tayi cikin kasa da murya tace" Dan Allah ka matsa bakaga mommy bane agurin?

Kallon mommyn yayi cikin ko ajikina yace"mommy wai kinji saina tashi daga nan gurin ya fada yana turo baki .

Dariya mommy tayi kasancewarta wayayyiyar mace tace "khadeeja ki barshi ya zauna mana.

Baki bude khadeeja ke kallon kameel ,lallai kameel ya cika marar kunya wllh Allah ya kyauta .

Kallon mommy kameel yayi cikin girmamawa yace"mommy ba abinda zance miki sai godiya Allah ya saka miki da Alkairi ,kin kulamin da khadeeja kin bata duk wata kulawa data dace,kullum adduata Allah yasa khadeeja ta fada hannu na gari,alhadullh Allah ya karbi addu ata naga khadeeja cikin yanayin da ban taba cammata ba,mommy na gode kin kulamin da rayuwata .

Sanna ina son ki bani khadeeja nayi alkawarin zan kula da ita zan bata kulawar da bazan bawa kaina bama , Mommy nasan khadeeja ta sanar dake duk abinda ya faru ,amma ki yarda dani balaifina bane ko kadan .

Ya karasa maganar cikin damuwa.

Bakomai kameel Allah ya kare gaba khadeeja matarkace ba wanda ya isa yayimaka iko akanta ,saidai kasani bazan baka yata ba har saita yarda zata bika dan haka gaka gata nan ku shirya kanku saika dauki matarka Allah ya rufa asiri.

murmushi kameel yayi ,yace "nagkde mommy Allah ya kara girma,

Ameen tace tana tashita bar falon . Islam ma barin falon tayi daga khadeja sai kameel ,dayake ta wani nanike mata.

hannuta ya kamo ya rike sosai cikin nashi ,

khadeeja ina son ki bani damar kulawa da rayuwarki dan Allah kibini mu koma gida kinji ?ya fada yana marairaicewa.

Tashi khadeeja tayi tare da nufar dakinsu ,bata ce komai ba tana shiga ta cire hijabin jikinta ,tana kokarin cire rigar jikinta kameel ya shigo.

Kallonsa khadeeja tayi tare da murguda masa baki ,ya haka zaka wani biyoni har cikin daki ,kuma da kashigo ina cire kayana fa ?ta karasa tana turo baki ,

Kallonta kameel yayi ya bude baki zaiyi magana idonsa yasauka akan katon cikin dakejikinta,

Zaro ido yayi kamar zasu zazzago kasa,

Cikin sassarfa ya karaso kusa da khadeeja yana kallon cikinta ,hannunsa na karkarwa ya ke nuna cikin jikinta cikin rudewa .

khadeeja wann......

Kash masu karatu shin kameel zaiyi farin ciki da cikin jikin khadeeja ?

Sai mun hadu yan uwa taku anty mammy kabeer🙏

mrs babi 💘💘

Share and comment please .

More comment more typing. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

GIDAN AIKINA🍒🍒

Na mammy kabeer (anty mammy)

ELEGANT ONLINE WRITER'S

Page 57/58

"Khadeeja wannan me nake gani ajikinki" Ya fada yana nuna cikinta ,hannunsa na karkarwa.

Kawar da kai khadeeja tayi tare da daukar hijabinta tana kokarin sanyawa.

Da sauri kameel ya kwace hijabin ya jefa akan gado ,sannna ya kamo rigarta ya daga cikin abinda baifi second goma ba.

Kallon cikin khadeeja yake baki bude,yama kasa cewa komai .

Dago kai yayi y zuba mata kyawawan idonsa yana kallonta ,kawai sai hawaye sharrr,

Janyota yayi ya rungumeta ajikinsa ya kama kuka ,tsakaninsa da Allah yake kukansa , Toh shidai baisan me zaiyi ya nuna farin cikinsa ba idan ba kukanka.

Readers Also Read