Kenza eBookz

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 16

Complete book: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy)Chapter 16 of 21FantasyBy Mamy Kabir (aunty Maamy)

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 16

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 16: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 16. Khadeeja ta gama masa komai arayuwa ,ta zame masa…

3,374 words

Khadeeja ta gama masa komai arayuwa ,ta zame masa haske ,itace silar shiryuwarsa yakoma ga Allah ,yanzu haka ko warin sigari baya sonji .

"Deejena cikine dake ,Allah na gode maka ,nikam ko yanzu nabar duniya burina ya gama cika ,zankoma ga Allah ina mai godiya da ni'imarsa gareni .

Ina sonki matata "

Ya fada yana dagata sama yana juyi da ita cikin tsantsar farin ciki yake cewa"nima nakusa zama daddy, wayyo ni kameel ashe ni cikkaken jarumine ,akaron farko nayi ajiya."

Sai juyi yake da khadeeja ahannunsa yana dariya ,godiya kawai yake ga Allah.

Khadeeja kuwa sai dan dukan kafadarshi take itama cikin dariya ,dan ba karamin dariya yake bata ba ,yadda yake abu kamar wani dan karamin yaro ,yanzu zakaga hawaye ,yanzu zai fara dariya,

"dan Allah ka saukeni agidan mutane muke fa,ta fada cikin shagwaba .

Direta yayi yana janyota jikinsa , Toh menene ai sunsan munyi kewar juna suma ,kuma gashi ina shirin zama daddy dole nayi murna sahibata.ya fada yana hada hancinsu.

"Toh nidai so nake na cire rigar nan dan Allah ka fita ka jirani awaje.ta fada tana turo baki,

Zama yayi abakin gadon yana dan kishingida,yace "tab meye saina fita zqki canza kaya kuma ? Haka kawai zaki hanani kallon abuna kinsan missing dinki danayi kuwa? Ya fada yana dage gira daya.

Turo baki khadeeja tayi cikin shagwaba harda buga kafa "ni wllh ka tashi ka fita bazan sake kaya agabanka ba.

Kallonta yake ciki wani gagarumin so da kauna ,ba karamin kyau tayi masa ba datake shagwabarnan, ji yayi kamar ya hadiyeta ya huta.

"ina sonki sahibata kece farin cikina " Ya fada yana kwanciya akan gafon tare da lumshe ido.

ganin da gaske ba fitar zaiyi ba yasa Khadeeja bude siff ta dauko riga da zani na atamfa ,ta daura zanin akirjinta kafin ta cire doguwar rigar.

tna kokarin sanya rigar kawai taji mutum yana fama kissing din wuyanta zuwa bayanta.

Jikin khadeeja ne ya fara rawa ,dan tayi kewar mijinnata ,duk yanda taso ta zame masa amma hakan bai yiwuba. Dan ya gama kidimata.

Haka ta biye masa suka zube akan gado ,wani shegen kallo da kameel ya wurgomin ,shiyasani ficewa daga dakin aguje batare dana dauko muku rahoton abinda ya faru ba.

Bayan wucewar wajen awa guda naji dakin shiru ,dan haka na koma tare da buya dan ci gaba da dauko muku rahoto.

Kameel ne rungume da khadeeja tsamtsam ajikinsa ,sai ajiyar zuciya yake saukewa ,fuskarsa cike da hawaye,

Yana shafa kan khadeeja, Wacce tayi shiru itama jiki asanyaye ,amma tana ta turo baki .

"Khadeejana " Kameel ya fada asitin kunnenta,

Lumshe ido tayi saboda yanayin daya kira sunan nata har cikin ranta taji.

"nagode Khadeejana Allah yayi miki albarka ,ya faranta miki kamar yadda kika farantamin ,kinsani nishadin danayi bankwana da sake samunshi ,yayi shiru tare da sumbatar kafadarta sannan yaci gaba ,

Ina sonki ,ina kaunarki kece kadai macen dana fara so arayuwata kuma kece mace ta karshe da zanso .

Dan Allah kisoni koda rabin rabin son danake mikine ,karki gujeni duk wuya duk runtsi ,wllh idan kika gujeni mutuwa zanyi,ya fada muryarsa na rawa sosai,

Juyowa khadeeja tayi suna fuskantar juna ,duk da kunyar dake tattare da ita haka ta daure ta sanya hannu tana share masa hawayen ,kafin ahankali ta rungumeshi ajikinta tana sauke ajiyar zuciya .

Shiru suna kwance rungume da juna na tsawon lokaci ,saida kowa ya gamsu da cewa inba dayansu ,to daya bazai iya rayuwaba. Kafin da sauri khadeeja ta sakeshi ta yunkura ta zauna ,jikinta ciwo yake dan ta gurzu,agurin jarumin nata.

Turo baki tayi tana hararansa,"yanzu dan Allah abinda kayi ka kyauta kenan ? Ta fada tana tabe baki da son yin kukan shagwaba.

Da sauri ya matso ya rungumeta , "me kuma nayi autar mata ya fada yana shinshinar wuyanta ,dan shi baiki akaraba dan wllh bawai ya gaji bane ,kawai ya bartane dan ganin yanayin da take ciki.

"haka kawai kasani abin kunya agidan mutane ,yanzu me zance idan na fita ,salon suce dama son abin nake shiyasa muka shige daki mukayi bulun bugwui aciki.ta karasa tana turo baki.

Allah wannan kameel din baida kunya ,haka kawai agidan mutane yazo yayi dare dare agadonsu ko kunya bayaji,yasani cikin kunya kawai.ta fada tana taturo baki.

Murmushi kameel yayi dan shi wllh baiga wani abin kunya ba matarsa ce fa ? Kuma yaushe rabonsu da juna ?ai sunyi kokarima.

"ayya sorry madam ai ba abin kunya mukayi ba,itama mommy ai likitace tasan na kaa gyaawa ajiya gurine ,kuma nayi ban ruwa ,kinga saidai taji dadima ko? Ya fada yana dan murmushi.

Tashi khadeeja tayi ta shige bandaki,aikuwa ko gama shiga batayi ba kameel ma ya shigo.

Zaro ido khadeeja tayi ,na shiga uku yallabai nanfa gidan mutane ne dan Allah fita ,yau naga ta kaina ni khadeeja .ta fada tana rike haba.

Dariya kameel yayi yana kunna famfom ya kama gada musu ruwan wanka.

"Waike dan Allah meye abin wani zaro ido dan kawai mutum zaiyi wanka da matarsa ? Nifa ko ajikina ban damuba ,indai kina guri to wannan gurin ya zamemin gida kawai ,

Ganin suna kara bata lokaci yasa dole khadeeja ta hakura sukayi wankan ,yana ta neman agana bata kulashiba.

Ita urita kawai tayi ta fice falo dan wllh kunyar hada ido take da mommy.

Bayan sun gama shiryawa ne ,dole tasa kameel ya maida kayan daya cire,atarihin rayuwarsa bai taba yin wanka ya maida kayan daya cire ba koda kuwa yanzu yasakasu ,kuma ya cire yayi wanka? toh sun gama aiki.

Amma yau kam dole ya maida kayansa yana ta dan dagasu daga jikinsa yana tabe fuska.

Falo suka fito ,khadeeja sai wani sunke kai take ba kowaafalon haka yasa ta sauke ajiyar zuciya ta nemi guri ta zauna ,shima kameel zama yayi kusa da ita ya rike hannunta .

Islam ce ta fito daga kitchen ta gansu. Dan sunkuyar da kai tayi dan tun dazu dataji abinda ke wakana sai tayi saurin ficewa daga falom ta koma can farfajiyar gidan .

Mommy kuwa ta shiga makota karbar haihuwa ,inda Allah yasosu kenan.

Abincin ta ajiye musu ta koma ta dauko lemo.

Agabanta kameel ya dage shi zaiyi feeding din khadeeja ,haka ba yadda ta iya ta yarda ya bata abincin . Kadan yaci yace su tafi gida .

Kallonsa khadeeja tayi tace nifa ba inda zan tafi ina nan .

Tuni ya rikice yana rokonta dan Allah ta tashi su tafi ,inba hakaba wllh shima ya dawo nan gidan da zama,

Islamce ta kalleta tare da girgiza mata kai,alamar ta bi mijinta sukoma gida.

Kallon islam Kameel yayi duk ya wani marairaice ,"please sisternmu kice ta bini mu tafi gida wllh bazan iya tafiya ko ina batare da itaba .ya karasa yana wani karyar da wuya.

Tashi islam tayi tace karka damu ,bari na hada mata kayanta tare zaku tafi ,

Cikin murna ya kalli khadeeja "kin amince rayuwata? Zamu tafi tare ko?" Ya fada yana kamo hannunta daga durkushen da yake agabanta.

kawar da kai khadeeja tayi tana turo baki,azahiri tana son bin mijinta saidai tana tsoron abinda zai faru agidan .

Waya kameel ya dauko cikin murna ya kira Abbansa,yana dauka kameel yace"abbana albishirinka ?

Cikin doki dajin muryar kameel cikin farin ciki Abba yace "goro fari kall kameel"

Cikin wani jan nnufashi irin wanda mutum keyi idan yana cikin tsantsar farin ciki kameel yace"Abba i have found her"ya fada cikin wata murya mai bayyana tsantsar farin cikinsa.

Da sauri Abba ya tashi tsaye yace,alhamdulillah Allah shine abin godiya ,kuna ina yanzu ?

"Abba muna gidan da take zaune amma uanzu zamu taho in sha Allah" Ya fada yana kallon khadeeja cikin murmushi irin na masoya.

Shikenan son muna jiranku .

Ba jimawa kuwa doctor ta shigo gidan ,

"Mommy sannu da zuwa kameel ya fada hnnunsa na cikin na khadeeja ,sai kokarin kwacewa take amma ya rike gam.

Yawwa kameel sannunku da gida lallai yau na sake samun wani dan .ta fada tana murmushi.

Dariya kameel yayi yace"mommy indai bazaya bini ba ai anan zanyi zamana ba inda zan tafi ,ya fada yana kallon khadeejan .

Ba komai nidai abinda zance anan shine ,ka kulamin da yarinyata dan Allah kameel kar wani abu ya kara garuwa Allah ya baku zaman lafiya ya sauketa lafiya. Mommy ta fada tana jin ba dadi na tabuwa da khadeejan .

Zuwa khadeeja tayi ta eunhume mommy tana kuka ,"mommy banson rabiwa dake ,ke uwace ta gari bazan taba mantawa da alkhairinki gareni ba na gode Allah ya baki lada."

Khadeeja ta fada cikin kuka.

itama mommy hawayene ya taru a idont ,tana shafa kan khadeejan ,ya isa haka kinsan banason wannan kukan naki ko ? Ai muna tare gari daya muke fa! Duk sanda naso ganin yata zanje ,haka kema zakizo ,zumuncinmu bazai yankeba in sha Allah.

haka suka gama hada kayana khadeeja suka dunguma amotar mommy har mommyn aka tafi gidansu ,kameel din. Kameel da khadeeja abayan mota ,momy kuma da islam agaba.

Har katafaren gidan alhaji saddam.

Yana harabar gidan shida su maryam da ummi, dan itama yayi mata waya ya sanar da ita yar uwarta ta bayyana dan haka mijinta ya kawota .

motar na shigowa sukayo gurinta cikin so da kaunar ganin khadeeja ,

Fitowa sukayi gaba daya gaban khadeeja sai faduwa yake ,dan ma bataga mommy agurin ba .

da gudu maryam tazo ta rungume khadeeja tana kuka , Yar uwa wllh dama nasan ke nagani a sahad store amma kika nuna kinganeni .ta fada tana hawaye,

Da sauri kameel ya janye maryam yana harararta ."bakiga halin datake ciki bane kike wani rugungumeta saikin ji mata ciwo.ya fada yana dawo da khadeejan kusa dashi .

turo baki maryam tayi kai yaya ya zaka hanani jin dumin yar uwata wai?

"jin dumi ko ki karya mata kashi dai "ya fada yana harararta.

Abbane ya karaso ya riko hannun khadeeja yana kallonta cikin tsantsar farin ciki.

Ya dafa kanta , Ashe shiyasa nakejinki araina kamar yarda na haifa? Ashe kedin yar kanwatace jinina? Allah na gide maka alhamdullih!

kallon abba khadeeja take baki bude ,yar uwarsa kuma wacece yar uwar tasa .

Suma dai su mommy cikin mamaki suke .

Kallonsu Abba yayi yana murmushi. Hajiya kuyi hakuri mun barku atsaye matar gidan bata nan ,kuahigo daga ciki ,ya fada yana yin gaba da khadeeja rige ahannnusa.

Ai da sauri kameel ya bi bayan abba shima ya riko hannun khadeeja ta dayam bangaren .

Bayan sun zazzauna an kara gaisawa da juna akayiwa juna jaje ,

Sannan Abba yayi musu godiya sosai akan yadda suka kula da khadeeja.

Khadeeja yatace yar kanwata da muke ciki daya ,nan ya basu labarin komai da komai.

Kuka sosai khadeeja keyi ,ashe dama cikin yan uwana nake zaune? Shiyasa duk irin cin kashin da sukemin ban bar gidan ba .

Allah nagode maka daka nunamin yayan mahaifiyata ,

Ashe yallabai kameel jininane ? Wayyo ni deejen kameel wannan soyayyar danake yiwa mijina ashe jininmu daya.

Sosai khadeeja ke cikin wani irin farin ciki marar misaltuwa.kanta ta dora akafar Abba tana kuka.

Abba meyasa baka nemeni ba ? Nasha wahala arayuwata bayan rasa iyayena danayi abba rayuwata ta shiga garari . Ta fada tana kuka .

Wani irin daci abba keji azuciyarsa yana shafa kan khadeeja ,kiyi hakuri mamana Allah ya riga ya shirya hakan zata faru amma yanzu kina cikin gatanki ba mai kara daga miki koda yatsane.

Kameel ne shima ya dora kansa afayar kafar Abban yana kallon khadeeja ,yace" Abba kace ta daina kuka banaso ,zuciyata tana min zafi da ganin hawayenta ,ya fada shima hawayen na zubowa daga idonsa.

Daga kanshi Abba yayi cikin rarrashi yace " kameel kaje ka rarashi matarka da kanka Domin tana cikin yanayin da dole saitayi kuka zata sami nutsuwar zuciya.

Hannu kameel yasa yana share mata hawayen idonta yana kallonta ,ji yake kamar ya maida komai baya ,yajiyar da ita dadin dabata samu ba abaya ,

"daga yau kin daian zubar da hawaye matata ,zaki kasance cikin farin cikine arayuwarki har karshenta ,ya fada yana sumbatar hannuta.

Haka suka karaci farin cikinsu kafin su mommy sukayi musu sallama suka tafi ,akan zasu kara dawowa akara gaisawa .

Haka suka tafi cike da kewar khadeeja aransu,itama cikin keqarsu take sosai.

Suna zaune afalon suna ta neman yafiyar khadeeja ,akan abubuwan dasuka faru,

Kameel sai cewa yake ta tashi sutafi dakinsu ta huta amma taki ,har saida yace "Abba ya kamata fa abani matata mu tafi daki nima fa ban wani gama ganawa da itaba ,ya fada yana turo baki kamr wani dan yaro.

Murmushin manya Abba yayi dan yagane nufin kameel din sarai dan haka yace Maza kuje ku huta nasan itama agajiye take ga yanayin da take ciki.

Da sauri kameel ya mige ya riko hannuta "tashi muje dakin deejena"ya fada yana mikar da ita tsaye .

Ita duk kunya ta kamata amma shikam ko ajikinsa.

Sunnufi dakinsu kenan,saiga mommy ta shigo falon.

Kallon kameel tayi da yake rike da hannun wata yana kokarin shigewa dakinsa.

Gasu ummi azaune fuskokinsu cike da farin ciki.

haka ma alhaji sai murmushi yake .

Kameel wacece wannan din haka kake kokarin kaita dakinka. Mommy ta fada cikin rudani.

Juyowa sukayi gaba dayansu ,shida khadeejan .

Kallon khadeeja mommy tayi sosai tana zare ido ,kafin idonta ya sauka akan cikin dake jikin khadeejan

What!!!! ..........masu karatu me mommy zata ce game da khadeeja da kuma cikin dake jikinta?

Shin zata saduda ne ko yaya?

Saikunji daga gareni ,taku anty mammy🙏

Mrs babi💘💘

share and comment please. More comment More typing. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

GIDAN AIKINA🍒🍒

Na mammy kabeer (anty mammy)

ELEGANT ONLINE WRITER'S

Page 59 /60

Wannan paging sadau karwane ga member na gidan aikina group ,kuyi yadda kukaso dashi,much kauna.

What !!! Mommy ta fada da karfi tana kallon khadeeja dakuam cikin dake jikin.

Mamaki ,al'ajabi ,fargaba dakuma tsoro sune suka bayyana akan fuskar mommy karara.

Kana kallonta zaka fahimci halin datake ciki.

Me wannan karuwar take mana agida? Waya kawota cikin gidan nan? Mommy tafa cikin rikicewa. Dan bata taba tsammanin ganin khadeeja ahalin yanzu ba .domin yanzu haka daga gurin boka suke ita da maman aisha ,akan akara nesanta khadeeja da garin kanoma gaba daya, Sannan acusawa kameel son aisha ta karfi da yaji .

Amma tana dawowa gida saita ga khadeejan kuma,tayaya hakan ta faru?

Kallon juna su ummi sukayi tare da tabe baki ,

Alhaji me wannan shegiyar ta dawo yimin agida ?ta fada tana kallon Abba kamar zata rufeshi da duka.

"Mommy !!! Ya isheki karki kara kiran matata da sunan karuwa ,kuma ba kowane ya dawo da itaba nine nan dan haka ni zaki tuhuma ba Abba ba " Ya karasa yana huci dan yaji zafin kiran khadeeja datayi da sunan karuwa.

Kameel yanzu da kanka kaje ka dawo da wanann karuwar gidan nan ? Bakaga abinda ke jikinta bane ,taje tayo cikin shege zata kawo makashi kuma ka karba? Tonikam bazan yarda ba dan ubanki zoki ficemin daga gida.mommy ta fada cikin wani irin yanayi mai kamada da zare.

Nufo khadeeja tayi gadan gadan ,zata fizgota ,

Da sauri kameel ya tareta ,tare da rike hannunta yana watsa mata wano irin kallo mai cike da fassara kala kala,

"mommy koda wasa kada ki bari hannunki ya sauka akan matata,domin ba baiwarki bace ,

Sannan kada ki kara shegantamin da ,wannan cikin da kike gani to nawane,kuma kema kin sani ,dan haka koda ciwon kai matata tayi kisani bazan taba ayrda ba sai inda karfina ya kare.

Ya fada yana sakin hannunta ,tare da jan khadeeja dake kuka sosai suyi dakinsu.

Abbane ya taso yazo gaban mommy yana murmushi, Kinga tayuwa ko hajiya ? Kinga irin tarbiyyar da kika dora danki akai ? Kinga yadda Allah ke al'aarinsa akan bawansa ?

Kisani khadeejan da kike ikirarin ta bar miki gida toh ,itama nan gidansune ,domin khadeeja yar kanwatace maryam ,wadanda kika rabani dasu , Kin cuceni hajiya ,sakayya tana gurin Allah kije duniyace ta ishi kowa riga da wando.

Abba yana fadin haka yayi shigewarsa dakinsa ya barta nan tsaye .

Tashi ummi tayi tace mommy na tafi sai anjima dama nazo ganin yar uwatane ,

Tayi ficewarta ,dan harga Allah bata wani jin tausayin mommy domin ita ta jawa kanta komai .

Maryam kuwa wayarta ta dauko ta hau online abinta .

Mommy kuwa tana tsaye kamar an shukata agurin , Komai ya tsaya mata cak. Ta rasa meke mata dadi,

Yanzu duk uban kudin data narkaakan aikin nan ya tashi abanza kenan? Boka ya cuceta yayi mata karya,harda cewa ko hanyar kano khadeeja bazata kara waiwaitaba , Saigashi tazo ta tarar da ita acikin gidanta? Kai dole ta sake sabon shiri bazai yiwuba .

Haka ta sake bazama ta fice daga gidan .

Kameel kuw ayana rike da khadeeja dake kuka sosai har cikin dakinsu.

Zaunar da ita yayi akan kujera ya dauko ruwa mai dan sanyi ya tsiyaya mata akofi yabata tasha.

Zama yayi akusa da ita tare da kamo hannunta ya rike cikin nashi,

Cikin sigar rararashi ya fara magana"kiyi hakuri deejena ,nasan abinda mommy ke miki sam bata kyautawa , Amma kiyi hakuri zanci gaba da kare miki hakkinki ta kowace siga ,bazan bari ta cutar dake ba .

Ina sonki khadeeja wannan kadai ya ishemu rayuwa ,ba ruwanki da ita dani take kiyayyar ba dake ba ,domin nina kawoki gidannan duk wanda ya kiki to ni yaki,

Zanci gaba da yakarta akanki bazan bata damar koda yi miki kallin banza bane ki yarda dani kinji"?

Ya fada yana share mata hawayen dakezuba a idonta.

Ji yake kamar ya hadiye zuciya dan bacin rai ,bayason abinda zai taba masa khadeejan sa ,abubuwa sunyi mata yawa tana bulatar kula da samun gata ahalin yanzu.

kallonsa khadeeja tayi tana share hawayenta ,kafin ahankali cikin nutsuwa ta fara magana " yaya mommy mahaifiyar kace,bai kamata kana magana da ita haka ba ,kasani kome zatayi itadin dai uwace ,kuma ni bantaba kullatarta azuciyata ba . Dan Allah kadaina yi mata haka domin hakan ba abinda zai gyara saidai ya kara batawa.

Uwa uwace koda ta karace ,watarana zata gane gaskiya ta daina nuna kiyayyarta akaina.

Ina son kasami rahamar ubangiji dan Allah kadaina maida mata magana ,hakan na min ciwo ,please ka rinka kai zuciyarka mesa ,koba komai iata ta haifeka."

Ta karasa tana kallon kyakykyawar fuskarshi.

Wata ajiyar zuciya mai cike da nishadi kameel ya sauke ,lallai samun mace ta gari yafi komai dadi arayuwa ,yanzu duk abinda mommy kemata ita kokarinta ayiwa mommyn biyayya!

Wani irin son tane ya kara shiga can cikin zuciyarsa .

rungumeta yayi ajikinsa yana sauke ajiyar zuciya . "ina sonki matata ke alherice agareni,Allah ya faranta miki kamar yadda kike faranta min.

Dago kanshi khadeeja tayi ta hade bakinsu guri daya ,yaudai khadeeja da aknta ta fara nuna masa wani salo na soyayya mai wuyar fassaruwa.

Shikuwa mutumin tuni ya birkice mata,sai nishi yake yana lumshe ido ,

sosai khadeeja ke bawa kameel wata zazzafar soyayyar data kusan zautar dashi, i love u baby kawai shine abinda kameel ke iya fadi cikin sarkewar murya ,

Daga karshema daukarta yayi kamar yar baby yayi daki da ita,

Akan gado ya ajiyeta auka dora daga inda suka tsaya.

Hammmm da alama fa masoyan nan sabon amarci suke son kara budewa ,dan sun jima suna farantawa juna rai ,albaeka dai kam yau khadeeja ta shata gurin kameel ,yanayi yana hawaye .

hakika ya tabbatar bazai iya cikakkiyar rayuwa batare da khadeeja ba ,itace macen data dace da halittarsa ,yana matukar kaunarta sosai aranshi .

Bayan sun sami nutsuwa ne,suna kwance ya rungumeta yana shafa cikinta ahankali ,

"khadeeja ke dta dam ce acikin mata ,zumarki mai wuyar samuce aduniya baki daya, Dan Allah ki soni ki rikeni har abada ,karkk juyamin baya .

Zan zame miki mijin tace arayuwata ,ki taimakeni karki gujemin aduk lokacin dana zo gareki.ya fada yana kissing kafadarta.

Kara rike hannunsa khadeeja tayi sosai cikin nata, bata ce komai ba amma kana kallon fuskarta kasan tana cikin nishadi sosai.

Yau kwanan khadeeja uku da dawowa gidan mijinta ,

Wata irin shakuwa ce da soyayya ta sarke sosai atsakaninsu ,kullum suna tare da juna ,basa rabuwa komai tare sukayi ,ko babban falo idan ba masallaci kameel zaijeba bazaka ganshi ya fitoba ,

Readers Also Read