Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 17
Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 17: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 17. Sosai yayi wata kiba ya kara haske kyanshi ya…
3,357 words
Sosai yayi wata kiba ya kara haske kyanshi ya kara bayyana ,
Suna zaune afalo khadeeja tayi [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: Matashi da cinyarsa , Shikuma yana taje mata gashinta.
"Khadeejana ina sonki" Ya fada yana shafa gashin kanta,
Murmushi khadeeja tayi tare da sumbatar hannunsa ,batace komai ba sai murmushi datayi ,dan wannan kalmar ta riga ta zame mata jiki ,arana saiya fade ta dau dari.
Dagata yayi daga kan cinyarsa ,ya koma dayar kujerar ya zauna tare da rungume hannu yana turo baki,
Kallonsa tayi na dan lokaci ,wato waishi adole fushi yayi ,toh kuma ni menayi masa?
"menene kuma yaya fushi kayi ? Konayi maka wani abune? Dan Allah kayi hakuri kaji.ta fada cikin shagwaba .
Kara turo baki yayi harda dan bubbuga kafa akasa,
"ni wllh ban yarda ba Allah " Ya fada yana murza kafa ,irin yadda yara keyi idan sun so rigimar banza.
Murmushi Khadeeja tayi cikin kulawa tace"toh kayi shiru fada min menene? Waya taba min yayana?
Turo baki yayi ,kafin yace "toh ni kullum fa nike cewa ina sonki! Amma ke baki taba cemin ko sau daya kina sona ba. Please deejana kice kina sona dan Allah koda sau daya ne nima naji kalmar nan daga bakinki kinji!!" Ya karasa yana wani marairaicewa kamar maraya.
Murmushi khadeeja tayi cikin kunya ,take kallon gemu fuskarshi zuwa sajensa,da yayi buzu buzu ,dan har yanzu bai gyara ba.
Tashi tayi ta matso kusa dashi ta zauna ,fuskarshi ta rike da hannayenta ,cikin kayataccen murmushinta tace"yaya kameel ko da bance ina sonka ba kaima kasan dole na soke ,kasancewarka dan uwa agareni ma ya wadatar ,dan haka kadaina damun kanka akan saina furta maka da bakina. Ta karasa tana shafa sajen fuskarshi.
" Ni wllh banyarda ba wayo zakiyimin kawai,ni ba son yan uwantaka nake sonji daga gareki ba ,so nake ki soni so irin na masoya ,sonake mu gina soyayya mai dunbin tarihin da yan bayama zasu ji labarinta,
Wllh khadeeja ina sonki ,ina miki son da ni kaina banyiwa kaina irinsa,ki yarda dani ki manta da komai ki karbeni mugina kyakykyawar soyayya, irin ta gaskiya da amana . Sauka yayi ya durkusa agabanta tare da rike hannayenta , " Khadeeja ina mai nemanbalfarma agareki,baijira jin ta bakinta ba yaci gaba , Dan Allah ki yafemin dukkan abinda nayi miki abaya ,kisani ina yinsune ,badan son raina ba ,wllh khadeeja ban tabajin dadin abinda nake miki ba , Duk lokacin dana musguna miki ,sainaji ciwo sosai aciin raina .
Ina takura mikine dan kawai in nesantaki da zuciyata ,domin koda yaushe kina yawan fadomin araina ,sai inji na tsaneki bana son ganinki ko kadan.
Atunanina hakan shizai nesanta zuciyata daga barin tunaninki.
Khadeeja na fara sonki tun ranar da idona ya sauka akanki,na tsinci kai cikin mayen giyar sonki, Ko me nakeyi kina cikin zuciyata .
Amma saboda tunanin cewar ni ba ajinki bane ,kuma ina ganin kamar na fadi kasa ace na rasa waddda zan so sai yar aikin gidan mu ? Wannan shine dalilin dayasa nake kokarin dakura rayuwarki ,dan sosai nakejin haushinki araina . Gani nake da gangan kike sanyawa nake tunaninki.
Shiru yayi tare da ajiyar zuciya ,
Kamo hannunt ya karayi ya mikarda ita tsaye , Janta yayi zuwa cikin kitchen ,wata kofa ya bude saigasu cikin wani falo mai kyau sosai.
abin mamaki gaba daya falin hotone nazane ,kuma khadeeja ce ajikim zanen .
Hotuna sunfi hamsin wasu manya wasu kanana,harda wanda tana barci aka zana ta.
Kallonta kameel yayi ganin yadda ta bude baki cike da mamaki tana bin hotunan da kallo.
Murmushi yayi ya jata zuwa gaban wani hoto tana sanye da hijabi har kasa ,tadan zaro ido alamar dai tana cikin tsoro ,
"kin tuna wannan lokacin ? Kameel ya fada yana murmushi kafin yaci gaba ,wannan ranar dana fara ganinkine acikin gidan nan ,ranar da kika shigo cikin rayuwata .
Bayan kin fita daga dakin nan banmasan lokacin da hannunaya zana kib.ya fada yana murmushi .
Haka yayai ta nuna mata zanen yana fada mata lokacin dayayi shi.
Sosai jikin khadeeja yayi mugun sanyi wani irin son kameel ne yake kara shiga cikin sako da lunhu na zuciya da gangar jikinta .
Vikin kuka ta rungumeshi ajikinta sosai kafin ta bude baki cikin muryar kuka ta fara magana.
"meyasa kayimin haka ? Meyasa ka boyemin Sonda kakemin? Kasan irin halin damuwa da soyayyarka ta jefani? Kasan tsawon lokacin dake dauka ina kuka akanka?
Bansan adadin kwanakin da soyayarka ta hanani barci ba ,
Duk lokacin dana ganka inaji kamar in hadiyeka ne dan so. Amma kullum fargaba nake akan wane irin hukunci zan fuskanta daga gareka ,nayi iyakar kokarina wajen boye soyayyarka azuciyata ,ina ta adduar Allah ya ciremin kai daga raina ,amma kullum kara shiga zuciyata kake ,
Duk lokacin dana ke tare da kai inajin kwanciyar haakali dakuma jina cikin kyakykyawan yanayi koda zakayi ta muzguna min ,nakanso inkanni atare dakai.
Tun bansan meke damuna har nagano soyayyarkace tayi min babban kamu .
Shin bakayi mamakin yadda naki barin gidannan ba ? Duk da irin halin kinci da takurar danake fuskanta ga ahalain gidan ?
Kaine sila soyayyarkace ta hanani matsawa daga inda kake .
Nayanke barin gidan nan da kuma soyyarka ne lokacin daka budemin sirrin jikina .
Nayi kuka marar adaddi awannan ranar naji na tsaneka bana son ganinka ko kadan .
Kameel ina sonka !! Ina maka son da bansan adadinsa ba kaine burin rayuwata kaine zabina .
Khadeeja ta karasa cikin kuka sosai tana kara rukunkume kameel ajikinta.
Kameel kam gaba daya ya zama spechless,yanzu dama duk wanann abunda ke faruwa suna cike da son junansu batare da sun sani ba?
Wayyo meyasa ban gano tana sona ba? Da mundade da zama abu guda dana dade da nuna mata soyayya yar gaske ,amma yanzuma lokaci bai kure ba.
Rungumeta kameel yayi shima yana ajiyar zuciya kamar wanda yaci kuka yakoshi.
Bayyana irin farin cikin da kameel ke ciki awanna lokacin ma bata bakine .
Ashe deejensa ma nasonshi?
"ina sonki deejena ,ina fatan in mutu da sonki Ya fada yana hadw bakinsu guri daya .
Cikin sauri khadeejama ta kamo harshensa tana tsots cikin salon da bata taba yi masa irinsaba ,
Sosai take bashi wata irin zazzafar kiss ,duk ya rude ya susuce ,
"Ana ahubbuki ya habibatee kateer kateer"
Kameel ya fada yana shinshina wuyamta yana bata kiss ta ko ina ,,
"wa'ana ya habeebee" Khadeejabta fada tana rukun kumeshi .
Neman faduwa suke suna kokarin cinye juna da soyayya ,
Daukanta yayi cilak ya nufi dakinsu da ita Kwantar da ita yayi tare dacire kayansa ya kashe wuta ya jamusu bargo.
Tsuka nayi dan bana iya ganin komai ,dan bukulu nace ina harararsa ,yaki barina in dauko muku rahoto ,
Bakajin komai sai nishinsi d surutan kameel .
Mommy fa damuwa tayi mata yawa tana zuwa gidansu aisha ta nemi guri ta zauna cike da damuwa ,ta rabka uban tagumi.
Mommyn aishace ta fito ta ganta cikin mamaki tace , Aa hajiya ya haka ba yanzu muka rabuba kika koma gida?
Hmmm kedai hajiya ki barni bakin cikine aran nan nawa kamar ya kasheni,
Wllh bokan nan yaci amanarmu yayi mana karya,
Yarinyar dayace ko hanyar kano ta daina kallo yoh yanzu haka tana gidana ,kuma abin tashin hankalinma tana nan ta dawo da katon ciki ajikinta.
Mommy ta karasa cikin tashin hankali harda kwalla a idonta.
Cikin tashin hankali itama mommyn aishan take kallon mommy hajiya kina nufin yarinyar cikine da ita ? Kuma tana gidanki yanzu haka?
Kwarai kuwa hajiya wllh ina komawa da ita nayi tozali.
Wani karin bakincikin yarinyar wai ashe yar gidan kanwarlhajice maryam ,ta fada tana jin wani kunci azuciyarta.
Hmmm dama duk wanda yaso ganin wani cikin kunci karshenya shine zai kare cikin kuncin da baida magani,Allah kasa mufi karfin zuciyarmu ameen.
Hajiya karki rainamin hankali mana! Dan tsabar rainin wayo nizakizo kicewa wai kin koma gida kintarar da yarinya? Toh dama can kinsan tana gidan shiyasa kika hanani zuwa gidanki ,ko aisha kika hanata zuwa.
Toh wllh baki isa ki rainamin hankaliba ,kekinsani nafi karfinki nafiki hau da bala'i nina koya miki zuwa girin boka ,kuma sirrrinki kaf bawanda ban sani ba .ta karasa cikin huci da bacin ran abinda mommyn ta kawo mata ,wanda take gani kamar rainin hankaline.
Cikin bacin rai mommy ma yo kanta da masifa ,dama kuma akule take . Karki fadamin maganar banza mana,idan kinsan sirrin nawa me zakiyi muguwa azzaluma ,kun hada baki da boka kin cuceni kamar ba yar uwarki ba ,wllh ki sani bazan bata kudina abanza saina dau mataki akanki ,
Au ni kike gaya wa haka ? Lallai kinyi abainda akeso toh ki saurari abinda zai biyo baya . Zamu gani idan mijinki yasan abinda kika kulla masa akan yan uwansa da kuma kanwarsa data mutu .......
Toh fa ana wata ga wata masu karatu meke shirin faruwane ?
Kubiyoni sannu ahankali, Taku anty mammy🙏
mrs babi💘💘
Share and comment please
More comment More typing. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
GIDAN AIKINA🍒🍒
Na mammy kabeer (anty mammy)
ELEGANT ONLINE WRITER'S
Page 61 / 62
Kallon mommy aisha mommy take cike da dana sanin hada kai da ita da tayi ,kuma tasan halin hajiya mari muddin tace zata aikata abu ba mutuncine da ita ba .
Amma duk da haka dole ta nuna mata bafa tsoronta takeji ba dan haka cikin masifa itama mommy tace,
"ke hajiya talatu kisani duk wani borin kunya dazakiyi ,wllh abanza baki isa ki bani tsoro ba ,maha'inciya kawai butulu,inace akan wanna aikin million biyu na bayar amma abanza .
Shine zakizo kina min barazana ? Toh kije ki tonamin asirin mana saime ? Kuma kisani aurene tsakanin dana da yarki ko? Toh na fasa hadawa kiyi duk abinda zakiyi. Mommy ta fada tana huci .
Dariyar yan duniya hajiya talayu tayi ,sannan tace Zakisan kuwa kinyi da yar halak aini nan d kike gani wllh kowa yaci tuwo dani miya yasha ,shegiya karamar yar duniya ,wllh saina ga bayanki .
Yata bazatayi jiran danki abanza . Ta fada tana hararar mommy.
Tashi mommy tayi ta bar gidan cikin bacin rai .
Zama hajiya talatu tayi tana kada kafa, Hmmmn zakisan kinyi dani wllh shegiyar mata kawai mai son abin duniya .
Aishace ta shigo gidan ta tarar mahaifiyarta tana ta masifa ita kadai.
Zama tayi tana kallon mahaifiyar tata .
Mommy lafiya kike ta fada ke kadai kamar wata zararriya? Ta fada tana dariya.
Kallonta uwar tayi hmmmm kedai ki barni da wanan matsiyaciyar matar ,ni zata nunawa tashanci ?
Mommy wace kuma ?
Wacece banda wannan shegiyar hajiyar kameel , Yanzu ta bar gidan nan wai tana komawa gida ta tarrar da wannan yarinyar ta dawo harda ciki.
Zaro ido aisha tayi mommy kina nufin yar aikin nan ce ta dawo ?nashiga ukuna ni aisha ,ta fada tana dafe kirji.
Hmmm ki bari kawai aisha wllh saina yiwa matar nan tsiyar da saita raina kanta .
Wllh mommy nidai ina son yaya kameel gaskiya kisan yadda zakiyi ,haba mommy yama zaace nasha zaman jira banza ,
Ta fada tana ji kamar tayi kuka ,wllh na tsani khadeejan nan mommy wai meyasa bazaki boka ya kashe ta ba muhuta gaba daya?
Ki bar komai ahannuna zanyi abinda nagaya dace Zata gane kurenta wllh.
Bangaren su kameel kuwa bayan hankalinsu ya dawo jikinsu ,suna kwance yana rungume da abarshi barci ne yayi awon gaba da ita ,dan ba karya ta wahala sosai .
Kameel jarumin namijine inya damketa baya mata ta wasa ,wai ahakama yana tausaya mata ganin cikin dake jikinta.
Murmushi kameel yayi ya sumbaci kumatunta ,sannan ya tashi ya shiga toilet .
Wanka yayi ya tsarkake jikinsa jinsa yake kamar wani dan jarari saboda rashin damuwa ,yana farin cikin samun khadeeja amatsayin matarsa ,domin tana isar masa sosai yake samun nutsuwa agurinta ,ji yake shikam ya gama samun farin ciki arayuwarsa .
Koda ya fito kitchen ya shiga yayi musu girki ya ajiye afalo.
Dakin ya dawo ya zauna abakin gadon yana shafa fuskar khadeeja ahankali yana murmushi,kasancewar bata da nauyi barci yasa ta bude idonta ahankali tana karanta adduar tashi daga barci.
murmuahi tayi masa lokacin da suka hada ido,
"shine kasani barci ko" Ta fada ashagwabe ,
Murmushi kameel yayi yace "aa ba ruwana saidai ki tuhumi kameelata itace ta sanya ki barci baniba, Ya fada yana dan dariya kasa kasa ,ganin yadda ta wani hade rai tana kallonsa.
"wacece kameela kuma" Ta fada tana hararar gafenta .
Dariya kameel yayi ahankali ,ganin yadda khadeeja ta kasa boye kishinta,
"Kina son sanin kameelata ? Toh ai kin dade da saninta tunda har ajiyarta kika karba .ya karasa yana dariya ,
Turo baki khadeeja tayi "Allah ya kyauta wllh ni bawata ajiyar wata kameela dana karba ,"
Ta fada tana kokarin tashi ta bar gurin ,cikin fushi.
Sosai ta bawa kameel dariya yana jinjina kuruciya irin ta khadeeja wai har yanzu bata gane kameelar tashiba.
"Aikuwa bakiga yadda take sonki ba ko ganinki tayi saita jijjiga ,ke ko muryarki yaji sai ta motsa.ya fada yana dariya,
Harara ta khadeeja ta galla masa ,kafin tace "wllh tun wuri ma ka fada mata ta daina sona danni bana sonta " Ta karasa tana murguda baki
Bude baki kameel yayi ,wai da gaske kike baki sonta ? Wllh idan kika kita zata shiga wani halin .
Ya fada yana karyar da wuya.
".ni gaskiya kadaina min maganar wata kameela anan gurin ,dama nasan ba damuwa kayi dani ba ko tausayina ma bakayi kake min zancen wata kameela ,kenan aure zakayi ko? Shikenan kaje kayi tayin auren nasan ba sona kake ba dama abakine,ta fada sai hawaye sharrrrr,
Da sauri kameel ya tashi ya rungumeta "ayya habeebatina ,wasa nake miki fa kinga kameelar fa takice ma batawa ba "ya fada yana kamo hannunta ya dora akan kameelar tashi.
Kunya ce sosai ta kama khadeeja ,wayyo Allah kishi baiyi ba jibi yadda ta wani bada kanta dan Allah ? Ashema kameelar ba budurwa yake nufi ba,
"kai nima akwai banza wllh ta fada ahankalitana mai jin kunya.
"Ki kwanar da hankalinki deejena ke kadaice zabin raina banda kamarki azuciyata ,kuma ba wacce zata sami guri araina .zuciyata takice ke kadai. Ya fada yana dan shafa bayanta.
Tueo baki khadeeja tayi tana dan bubbuga kafa "ni wllh bazan yarda ba tunda ka sa nayi kuka saika goyani . Ta fada tana turo baki da buga kafa irin na tabarar nan.
Dariya kameel yayi sosai kafin ya kalleta yace " yanzu ke idan nace zan goyeki saiki yarda ? Ki duba fa kiga yadda kika zama yar lukuta dake kalli katon cikinki fa ai idan na goyeki saiki ballani haka kawai kiyiwa kameelata asara .
ya fada cikin tsokana,
Kukan shagwaba khadeeja ta sanya masa harda zama tana turje kafa ,
"wllh niba yar lukuta bace kaine dan lukuti ,kuma ai kaine kasa nazama hakan ba kaine kayimin cikinba shine yanzubzakacemin na zama yar lukuta mai katon ciki. Ta karasa tana turje kafa.
zama yayi shima ya kamota ya dora akan cinyarsa ,
"yi hakuri wasa nake miki fa ,keba yar lukuta bace nine nan dan lukuti baban doya kalli cikina fa katoto dashi . Ya fada yana hura cikinsa wai dan taga cikin nashi ya zama kato ,amma yana nan flat dashi .
Dariyace ta kama khadeeja wai dan lukuti baban doya ,dariya ta sanya tana kallon flat cikin nashi daya bude yana nuna mata.
"kalli fa kaga cikin naka kamar ma babu ciki agurin shine katoton ahaka?ta fada tana dariya .
Shima dariya yayi dama burinsa yasanyata dariyar ,
"nima wllh bazan yarda ba ,saikin bani cikin na ajiye mikishi tunda hakane .
Ya fada shima cikin shagwaba ,
Dariya khadeeja tayi tare da rungumeshi
"wllh yaya inkayi shagwaba ko? Kyau kakeyi sosai ,sai inji kamar inyi ta kallonka,ta fada cikin yarinta.
Dariya yayi shima yana riketa ajikinsa sosai ,kema inkikayi shagwaba ko ,zuciyata narkewa takeyi sosai tana miki kyau ,ke fa komai ma kyau yake miki kinga wannan cikin ma ko? toh kyau yayi miki ina sonki deejena . Ya fada da iyakar gaskiyarsa."
"Nima ina sonka mijina "ta bashi amsa.
Ajiayr zuciya kameel yayi yana mai jin farin ciki ,wai shine haka yake zama yayi ta shiririta dan kawai ya farantawa khadeeja rai ? Kai soyayya tayi arayuwa ,ya fada azuciyarsa yana murmushi.
Dagowa khadeeja taui tana kallon fuskarshi , Gaskiya yau dole agyara wannan fuskar ,kar naje anacewa mijina tsohone mai gemu ,. Ta fada tana kyalkyalewa da dariya.
Shafa gemunsa zuwa sajensa kameel yayi yana dariya shima ,
Kallonta yayi yace "nine tsohonko? Shikenan aikuwa kema saina mayar dake tsohuwar .ya fada yana dariya ,
Hannunsa ta kama zuwa toilet ta zaunar dashi inda kayan kyaran fuskarshi yake .
Sosai ta gyara masa fuskarsa ya dawo asalin kameel dinshi ,harma yafi da kyau .
Kallonta yayi yana murmushi mai cike da so yace "ashe matana ta iya gyaran fuska haka?
dariya tayi itama tace "ainasan yadda kake gyara fuskarka shiyasa nima nayi maka irinsa.
Wanka yayi mata suka fito ,bayan sun shiryane sukaci abinci ,kwalliya sukayi ,dan yau gidan doctor zainab suke son kai ziyara ,
Sunje gidan doctor zaina sunjima suna hira ,sosai taji dadin ziyarar da suka kaimata islam ma tayi murnar ganin aminiyar tata sosai ,sai la'asar sakaliya suka bar gidan ,
Waya kameel ya siyowa khadeeja mai bala'in kyau da tsada yayi mata siyayya sossi da sosai .
Bai barta ta shiga store din ba shiya shiga shibkadai .
Haka ya dawo da kaya niki niki.
Sannnu tayi masa shikuma ya shiga motar ,kiss yayi mata kafin yajabmotar suka nufi gida,
Tun kafin su karasa cikin babban falon suka fahimci akwai matsala ,saboda hayaniyar dake tashi afalon.
Da sauri suka karasa cikin falon .
hajiya talatuce ita da aisha sai mommy da kuma maryam .
Wllh dama na fada miki ni ma shegiyar kainace ,kuma wllh yau saina tona miki asiri duk abinda kikayiwa mijinki saina fada tunda kika karya min alkawari.
Hajiya talatu ke fadin haka cikin masifa.
Kinyi kadan kizo har gidana kice zaki tona min asiri wllh ,duk wani munafurci da kikeji dasi saidai ya kare akanki azzaluma marar mutunci butulu. Mommy ta fada cikin tarin dana sanin biyewa wannan matar mai tonon silili.
Bazakisan ni butulu bace saina fadawa mijinki asirin da kikayi masa kika rabashi da yan uwansa kikayi masa asiri ya manta dakowa.
sannan kika yiwa kanwarsa asiri itama tayi ta fama da jinya harta mutu, Ko bamune mukaje gurin boka aka sa mata dutse acikinta ba dan ta mutu idan tao haihuwa ? Hajiya talatu ta fada tana nuna mommy da dan yatsa .
turus su khadeeja suka tsaya cike da mamaki da al'ajabin abinda matar nan ke fada .
Kallon inda suke tsaye mommy tayi da duk wadanda ke dakin .
Atsorace mommy ta bude baki cikin rawar jiki tana kallon khadeeja .
Wacce ta kure mommy da ido cikin rashin saninn abinyi......
Toh masu karatu muje zuwa ,
Taku anty mammy 🙏
Mrs babi💘
share and comment please
more comment More typing. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
GIDAN AIKINA 🍒🍒
Na mammy kabeer (anty mammy)
ELEGANT ONLINE WRITER'S
Page 63/64
Wannan page din nakine baby na mallaka mikishi kiyi yadda kikaso dashi 🥰🥰
Cikin rawar jiki mommy ke kallon khadeeja ,dan bata taba tsammanin ganinsu yanzu ba .
Khadeeja kuwa cikin wata irin kasala da mutuwar jiki ,tareda dauke tsammani take kallon mommy jikinta na karkarwa.
"yanzu mommy itace silar da na rasa mahaifiyata? Yanzu dama lamarin mommy yayi nisan da zata iya raba mutum da rayuwarsa?
Wannan wane irin rashin imani ne haka? Mommy is behind all kuncin rayuwar danake ciki,domin ita ta rabani da mahaifiyata tun ina karama , Ya rabb kabani kwarin gwuiwa da juriya.
Cigaba hajiya latatu tayi kuma ellh kisani kamar yadda kika sa yara tayi ta zaman jiran danki wllh bazai tafi abanza ba saina dau mataki.
Cikin sauri mommy ta matsa kusa da hajiya talatu tana cewa" Haba hajiya dan Allah kiyi shiru mana karki batamin suna gaban yayana ,koma menene kijirani idan nazo gidanki saimuyi "ta karasa tana kallon khadeeja jikinta duk yayi sanyi .