Kenza eBookz

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 18

Complete book: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy)Chapter 18 of 21FantasyBy Mamy Kabir (aunty Maamy)

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 18

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 18: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 18. Aishace ta mazo kusada mommyn cikin rashin kunya…

3,372 words

Aishace ta mazo kusada mommyn cikin rashin kunya da fitsara ,tace mommy meye kuma abin damuwar ? Ai yadda kika ci amanarmu kika je kika dawo da yarinyar nan gidan nan batare da kinsanar damu ba ,toh dole yau abaude komai dan kowa yasan abinda ke faruwa.

Haba mommy kece kika kawo shawarar mu batar da khadeja daga rayuwar danki ,kuma shine zakije kindawo da ita ? Wato ni kin mayar dani wata shashasha kin barni ina zaman jiran danki,

Hmmm ni dama na jima da sanin bawai so kike na auri dan nakiba ,kinason ki rabashine da wannan yar matsiyatan da baki son ta haifa miki jikoki ,kuma gashinan taje ta kwaso cikin shegenta ta kawo muku cikin gida kum.......

Tasssss!!! Kakeji kameel ya dauke aisha da wasu tagwayen maruka har uku saida ta fadi kasa ,bai tsaya ba ya rufeta da duka ta ko ina kamar jaka ,dukanta yake kamar an aikoshi saida yayi mata laga laga.

Uwarta na ta ihun. Azo ataimakesu zai kashe mata ya,

Da gyar Abba da duk abinda suke fada akan kunnensa ya shigo cikin falon ya kwace aisha daga hannun kameel .

Ai aguje mommy ta ja yarta suka bar gidan tana zage zage.

Mommy kuwa kuka take sosai ,dan bata taba tsammanin zuwan wanan ranar ba arayuwarta ,ranar tonon asiri ,agaban alhaji ,agaban yayanta uwa uba agaban yarinyar data tsana fiye da komai arayuwarta .

Gaskiya hajiya talatu ta cutar da ita ta ci manarta.

Alhaji kuwa cikin fushi matsananci ya shige dakinsa ,yana Allah wadai da matar rasa yayi nadama da danasanin aurenta. Banda albarkaci yayan da suka haifa wllh ba abinda zai hanashi yin shari'a da ita .amma dole ya dauki mataki mai karfi akanta.

Kameel ma cikin wani irin kunci da jin dama bata tsatson mommy ya fito ba yake kallon mahaifiyar tasa ,

"mommy kin cutar da zukata da yawa Allah shine kadai yasan hukuncin dazaiyi akanki ,mommy badan ba kasance da agareki ba danayi miki bakar addu'a, Amma duk da haka rayuwace ta isheki kuma Allah ba azzalumin sarki bane ,zai sakawa wadanda kika cutar." Yana gama fadin hakan ya kamo khadeeja ,dake tsaye kamar wata status .

mamaki da al'ajabine cinkushe cikin ranta .

Haka tabi kameel suka shige dakinsu ,ita batama san me yakamata tayi ba ,kuka zatayi kome?

Ruwa mai sanyi kameel ya tsiyayo akofi ya bata abaki ,ba musu ta karba tasha dan tana neman abinda zai sanyaya mata zuciya sosai.

Zama yayi akusa da ita ya dora kanta akan kirjinsa yana shafa bayanta ahankali .

Wani marayan kuka khadeeja ta sake tana kankameshi lamar zata koma cikinsa. Dan sai yanzu ta samu zarafin yin kukan .

Bai hanata ba shima kawai shafa kanta yake yanajin radadi sosai b acikin zuciyarsa .

Gaskiya uwa irin mommy idan Allah ya baka ita to baar jarraawace agareka,ta raba Abba da ahalinsa ,tayi silar rasa ran kanwarsa saboda son zuciya irin nata, Ya rabb ya shiryar da mommy idan tana da rabon shiriya.

Khadeeja ta jima tana kukanta kamar zata shide ,

"me ummata tayiwa mommy ? Meyasa ta rabani da mahaifiyata? Yaya kameel me nayiwa mommy ta zama silar kuncin rayuwata? Yaya da gaske mommy ita tayi silar dana rasa ummana?"

Ta karasa cikin sigar tambaya tana kuka.

Kasa magana kameel yayi kawai kallon khadeeja yake dan shi kansa yana kunyar ace wai mommynsa ce tayi silar da khadeeja ta rasa mahaifiyarta. Kuma sukazo sukayi ta sanya rayuwarta cikin tsanani da ukuba.

Ganin irin kukan da khadeejan keyi ne yayi yawa ,yasa kameel ,

Ruko fuskarta da hannayensa ,cikin tattausan murya yake magana,

"khadeeja kiyi hakuri ,kowane bawa da irin tashi kaddarar, Kekam hakataki kaddarar ta kasance , Khadeeja mun cutar da rayuwarki da yawa ina mai jin kunyar hada ido dake ,khadeeja nayi fatan dama ni ba dan mommy bane .

Hakin mommy yayi muni khadeeja da ana sake uwa dana zamo na farko dazan saketa. Khadeeja ina kaunar mommyna sosai araina amma ina tsoron mugun halinta inaji tsoron wataran kar mugun nufinta ya fara sauka akanmu .

Khadeeja yau nayi fatan dama bani da uwa ,dama na tashi maraya kamar ke ,khadeeja mommyna muguwa ce bata da imani ,ina jin.......

Da sauri khadeeja ta toshe masa baki jin irin kalaman dayake fadi game da mahaifiyarsa .

"ya isa haka yaya kameel ,ka daina fadin mugayen kalamai akan mahaifiyarka , Koba komai itace silar zuwanka duniya ,

Ni bandaukeku matsayin azzalumaiba ,asalima na yafe muku duk abinda kuka aikata akaina .

Kawai inajin ciwon rashin mahaifiyata ne arayuwata, Domin datana da rai na tabbata bazan shiga Irwin kumcin dana shiga abaya ba .

Ta karasa cikin kuka.

Rungumeta kameel yayi yana rarrashinta sun dauki lokaci mai tsayi ahaka kafin barci yayi awon gaba da ita .

Gyara mata kwanciya yayi ya fice zuwa fakin Abbansa.

Azaune ya tarar da Abban nashi yayi shiru cikin tagumi.

zuwa yayi ya zauna kusa dashi ya cire masa tagumin da yayi yana kallonsa cikin tausayawa.

"Abba ka daina sanya damuwa aranka ,karka bari damuwar mommy tayi tasiri akanka har ta haifar maka da wata matsalar .

Abba mataki ya kamata kadauka ,domin ta kiyaye gaba."

Kameel yafada yana kallon Abban nashi cike da tausayawa.

Ajiyar zuciya Abba yayi yana kallon kameel, Kameel yanzu wane mataki zan dauka akan mahaifiyarku? Ta riga ta gama cutar da rayuwata , Koma me zanyi mata ahalin yanzu kaina zan tonawa asiri domin duk wanda zaiyi kwatancenta dole za ace matatace uwar yayana.

Abba ya fada cike da damuwa.

Shikru kameel yayi nadan lokaci lafin ya kalli Abban yace"abba meai hana ka kara aure?

Kallon kameel abba yayi kafin yace 'kameel aure kuma wannan ma ba mafita bace domin wacce zan auro din ma ba sanin halinta nayi ba.

"Abba wannan itace mafita akan wannan lamarin domin idan kayi aure dole mommy zata gane amfaninka zata san cewa ashirye kake da daukan ko wane mataki agareta ,infact ma zaka iya rabuwa da ita.

Sannan abba idan kayi aure karka zauan da matarka anan gidan ka bar mommy ita kadai har saita gane kuskurenta

Nima nan da sati zan bar gidannan zan koma gidana ,

Abba munesanta da mommy mu barta ita kadai dan ta dandana zafin kafaici.

Hakan ne kadai zaisa ta gane kuskurenta ta koma ga Allah.

Shiru Aba yayi yana nazarin maganar kameel ,maganarsa akan hanya take toh amma wazai aura yanzu da girmansa ?

Kameel banki ta taka ba amma yanzu wa kake ganin zan aura,nidai kasan ba wata bazawara gareniba danni bani da tsarin mata biyu .

Murmushi kameel yayi ,yace"Abba ainajima dayi maka mata ,

Toh masha Allah kace da yayiwa ubansa mata? Toh wacece?

"doctor zainab wadda ta rike mana khadeeja likacin data bace."

Shiru Abba yayi yana nazari ,shin kana ganin zata amince kuwa ? Bazatace nayi mata tsufaba? Abba ya fada yana kallom kameel da murmushi.

"haba Abba na tabbata bazata kika ba domin bakayi tsufan da zatace aa ba ,idan har ka yarda toh kabar komai ahannuna kawai."

Shikenan kameel Allah yayi muku albarka ya kareminku,sannan ya kara shiryar daku baki daya.

ameen Abba "kameel ya fada.

Ko kwana uku ba'ayi da yin maganar ba komai ya kankama domin kameel da kanshi yaje wa da doctor zainab maganar abbansa bai sha wahalaba kuwa ta amince amma sai dai tace zata zauna gidanta har sai ta aurar da islam. Cikin kankanin lokaci akayi komai da komai aka gama ,ranar juma'ah za adaura auren.

khadeeja ta manta da komai ta mika lamarinta gurin ubangiji,kullum tana adduar Allah yajikan iyayenta da rahama .

Sannan tana kula da mijinta kamar yadda yake kula da ita ,cikinta sai kara girma yake kamar me tayi kiba sosai tayi fari kwanin sha'awa ,yanzu idan kameel ya fice suna tareda maryam suna hira ,

Sam maryam bata zama da mommy yanzu dan abin yayi mata ciwo itama wace irin uwa Allah ya basu haka?

Abin duniya ya taru yayiwa momy yawa kullum cikin kuka take,babban tashi hankalinta har yanzu alhaji baice mata komai ba gashi kuma yaji duk irin tuggun da ta hada masa .

Kullum ciki fargaba takena wanehukuncin abba zai zrtar akanta?

Tayi baki ta rame ta lalace abin har yayi mata yawa ko abinci bata iyaci , Yaya duk sun gujeta sosai tayi nadamar biyewa hajiya talatu . Yanzu fatan ta daya Allah ya hutar da zuciyar iyalin nata su dawo gareta ,abin ya isheta ,saidaitayi ta kuka adaki.

Yau juma'a kuma yau aka daukara auren abba da doctor zainab .

Sai lokacin kameel ke fadawa khadeeja ,tayi murna sosai dan tasan koba komai Abba yayi dacen mace tagari mi nagarta.

Abba ne ya shigo baban falon da babar rigarsa ,dawowarsa keam daga guri daurin auren .

Mommy nazaune afalo ita kadai tayi shiru tana ta tunani,batama san abban ya shigo ba.

Goro ya ajiyema farare tas masu yawa agabanta.

Dagowa tayi tana kallonsa , Alhaji wannan goronfa? ta fada gabanta na faduwa.

Alhamdulillah goron daurin aure nane yau aka daura auren . Ya fada yana nufar dakinsa.

Mikewa tsaye mommy tayi cikin tashin hankali,

Aure kuma?.......

Toh masu karatu sai mun hade next page .

Manage please. Anty mammynku ce🙏

mrs babi💘💘

share and comment please.

More comment more typing. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

GIDAN AIKINA🍒🍒

Na mammy kabeer (anty mammy)

ELEGANT ONLINE WRITER'S

Page 65/66

Wannan paging nakune masoyana ,naji dadin comment dinku sosai🥰

Sadiya gambo sani @fatima zara Makiyya Ummu nasreen Umu ja'afar Ummubnat Amina lawal Sweetyn baba Maman layla.

Mokewa tsaye mommy tayi cikin tashin hankali ,jikinta na rawa.

"aure kuma alhaji ? Bangane ba dan Allah kayi min bayani waye yayi auren ? Kodai kameel ne yayi aure? Momy ta fada cI'min tashin hankali sosai da sosai.

Tsayawa abba yayi ya juyo yana kallon mommy cikin murmushi ,yace "nine nan nayi aure yanzu haka daga gurin daurin auren nake ,ba kameel bane yayi aure ,danme kameel zaiyi aure shida yake da mace nagartacciya mai dorashi akan hanyar kwarai.

Ai aure namune muda muke neman mata na gari ,wadanda zasu iya taimaka mana mu gyara rayuwarmu ba su jefamu cikin halaka ba. Abba ya fada yana murmushi ,kai bakace magana yake fadawa mommy ba .

"Alhaji dan Allah karkayi min haka haba alhaji wane aure kuma yanzu ? Bakayi aure tun muna da jajayen sawun mu ba alhaji sai yanzu? Dan Allah kayi hakuri akan abinda ya faru sharrin shedanne. Mommy ta fada cikin mugun tashin hankali hawaye tuni ya wanke mata fuska.

Murmushi Abba yayi cikin kallon kin rainamin hankali,yace Ai bakin alkalami yariga ya bushe hajiya ,aure kam nayishi kuma ina cikin farin ciki sosai dn haka karki batamin mood dina ,ya fada yana shigewa dakinsa.

Zaman yan bori mommy tayi ahurin tana sanya kuka sosai ,shikenan tawa ta kare,alhaji ya kara aure nashiga ukuna ,ni yar yarbawa menajawowa kaina haka? Ina zama na da mijina da yarana ,wannan shegiyar talatun tazo ta tona min asiri ,yanzu kiduba ni alhaji keyiwa wanann walakancin haka? Ta fada cikin kuka sosai,

Kuka take agurin kamar wata yarinya nadama da dana sani suncika mata zuciya da rai sosai abin yayi mata ciwo yanzu shikenan anyi mata kishiya?

Kameel ne suka fito shida khadeeja kwana biyun nan yan yawan fita saboda shirye shiryen bude kamfaninsa da akeyi akwannan,

Dan tsayawa sukayi suna kallon mommy dake kuka sosai har abin tausayi ma,

Runtse ido kameel yayi tabbas yana jin zafin halin da mahaifiyar tashi ke ciki ,amma ko ma menene ita ce ta jawa kanta ,kuma yana son taji ajikinta sosai hakan zaisa ta nutsu ta gane gaskiya.

dan haka kallon khadeeja yayi yadda tawani shagwabe fuska ciki da tausayin mommyn , Dan hade rai yayi yace ki koma ciki kawai zan wuce bazan jima ba kinji? Ya fada yana wucewarsa ko waigowa baiyiba .

Kallo mommy tabushi dashi cikin jin wani irin ba dadi aranta ,ta cuci kanta ta bata rayuwar yayanta da kanta ,bata bari mahaifinsu ya basu tarbiyya ba sannan itama bata basu tarbiyya mai kyau ba ,yau gashi dan cikinta ya ganta tana kuka amma ya fice ko ajikinsa bai damu da halin da take cikiba.

Khadeeja kuwa cike da wai irin tausayin mommy ta karaso gurin da mommy ke durkushe tana ta kuka ,da gayr take taka kafarta dan sosai cikinta yayi firma,

Zama tayi ahankali cikin dan tsoro tana kallon mommy da fuskar tausayi. Kafin ahankali ta bude bakinta tace ,

"mommy rayuwa bata da tabbas agaremu ,dan adam baya taba dawwama cikin farin ciki,yau da gobe na Allahne, Sannan shike da iko akan al'amuranmu , Mommy kin aikata abubuwa da yawa arayuwarki wanda sakamakon hakan kike gani yanzu, shin mommy kin manta da cewar karamin kuskure kan jefamu cikin danasani na har abada?

Mommy bansan me nayi mikiba kin tsaneni kin tsani farin cikina mommy kin salwantar da rayuwar mahaifiyata ,kin jefa tawa rayuwar agarari ,sannan mommy cutar warki ba akain kadai ta tsayaba har yayan cikinki mommy gaba daya ahalin yanzu basa jin tausayinki.

Mommy kinsan menene dalili? Ta fada tana share hawayen dake zuba daga idonta kafin taci gaba, Kin raini rayuwarsu da rashin tausayin wani ,kin koyar dasu son kansu da kuma kin talaka , Mommy yanzu mai gari ya waya ?

Ina mai baki shawara akan ki tuba ga Allah akan laifukan da kika aikata , Mommy zuwa gurin dan duba ko boka shirkane ga Allah ,mommy duk wanda yaje gurin dan duba ,baza'a karbi sallarsa ba har ta tsawon kwana arba'in ,

Shin mommy kisan adadin sallolin da kikayi asara?

Baki saniba mommy kuma mutuwa na iya zuwa wa bawa ako wane lokaci,dan haka kiyi ta istigfari Allah maji rokon bayinsane ,zai yafe miki duk laifukanki ,sannan kiyi kokarin janyo yaranki jikinki dan gyara barakar dake tsakaninki dasu.

Nidai na yafe miki mommy duk abinda kikayimin .

Ta fada taa share hawayen idonta ,tare da yunkurawa da kyar ta tashi ta ufi dakinta.

Kuka kam yau mommy har ta rasa wane kala zatayi ,wannan shine karin maganar da bahaushe kecewa da da dukiya ba'a muguntarsu dan bakasan wanda zaka moraba . [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: Yau gashi mommy ta ga hakan da idonta ,yayanta basu damu da halin da take cikiba yarda ta mayar kamar kashi take kokarin ganin bayanta ,itace ta nuna damu da halin da take ciki.

Allah na tuba ka yafemin nayi kuskure arayuwata Allah ina son gyarawa ka bani iko,

Mommy ta fada cikin kuka mai tsanani,

Tashi tayi ta shige dakinta ta kwanta dan wani zazzafan zazzabine ya rufeta ruff.

Ba abinda take tunanowa sai irin asirin datayiwa Abba ta rabashi da kowa nashi ,

Yanzu ga karshen abin inda ta kare tonon asiri da kumabacin rai sune suke kokarin kasheta.

Khadeeja kuwa tana komawa dakin kuka tasha sosai ,yanzu meye amfanin irin wanna rayuwar ta mommy ka wulakanta dan adam bakasan darajar da Allah yayi masaba . Karshe kaikuma kazama abin tausayi ,

Harga Allah tana tausayawa mommy sosai ,dan abinda akwai zafi kowa naka ya gujeka ya juya maka baya,tasan irin wannan yanayin ,dan haka bata fatan wani ya shiga irin halin data shiga abaya.

Haka kameel ya dawo ya tarar da ita cikin wannan yanayin tana ta kuka,

Da sauri ya karaso cikin dakin ,Ya zauna kusa da ita yana shafa fuskarta cikin damuwa yake tambayarta"me yasameki deejena ?waya Tabaminke? keda wa ?" Kameel ya jero mata wadannan tambayoyin .

Share hawayen fuskarta tayi tana kallonshi cikin shagwaba ,"yaya ina tausayin mommy ne bana son ganinta cikin wannan yanayin ,please yaya kayi wani abu" Ta karasa tana kamo hannayensa.

Kallonta yayi cike da mamakin hali iriin nata ,wai tausayin mommy take gaskiya khadeeja yar halak ce kuma mutumce wacce take da kyakykyawar zuciya mai tsafta,

"khadeeja ke yar albarkace kece ake kira da mar'atussaliha,ina alfahari dake matsayi mata agreni,

Kinzama haske arayuwata ,kicireni daga hanyar bata kin saita rayuwata,jinake dama ina da abinda zan sakamiki dashi,nagode khadeeja Allah ya sakamiki da alkhairinsa. Ya fada yana rungumeta ajikinsa ,

Fuskarshi ta rike tana kallonsa"yaya dan Allah ka san abinda zakayi akan batun mommy ,itadin uwace agaremu please,ta fada cikin shagwaba .

Kamo bakinta yayi ya hade da nashi yana tsotsa cikin shaukin soda kauna ,

Zare bakinta khadeeja tayi taan turo baki , "yaya bakace komi bafa"

"shikenan zanyiwa Abba magana dan musn abinyi nidai yanzu ataimakawa kameelata tana jin kishi,y fada yana kamota zuwa jiinsa"

Yau kusan kwanan abba uku agidan amarya can ya tare ya bar mommy ita da halinta ,maryam kam ta koma school dan tace karatu zatayi acan exam ta matso ,khadeeja kuwa kullum suna cikin dakinsu ko garden ,sam kameel baya barinta ta fito falo dan bayason ta hadu da mommy ,yana tsoron abinda zata aikatawa khadeejan .

Mommy kuwa yanzu gaba daya rayuwar tayi mata zafi kullum cikin kuka da rokon Allah ya yafe mata take ,saidai har yanzu bazata ce ga abinda takeji game da khadeejan ba . Amma dai tasan tayi nadama akan abinda ta aikata arayuwarta.

Yanzu burinta mijinta ya dawo gareta dan tana jin zafin yadda ya nuna halin ko inkula akanta ,yau kwan uku ko sashi batayi a idonta ba,abin yaa damunta .

Ita kadai ke azurinta agidan ba mai kulata ,sai yar aiki itama data gama abinda take take tafiya gidansu.

Yauma tana zaune afalo ,duk wannan gayun babu shi ,tayi duhu sosai ta rame sai hanci da idanu dan da alama kameel idonta ya dauko.

Tayi tagumi tana zaune gurum saikace almajira,gaba daya ji take inama tana da damar dawo da baya ,da ta gyara kurakuranta ko zata sami salama arayuwa.

Abbane ya shigo cikin falon ,kwana uku amma har yayi dan kiba ,da alama fa abba zagewa yayi yaci amarcinsa,lol Shigowa yayi da sallamarsa . Neman guri yayi ya zauna yana kallon mommy gaba daya ta sauya kamar ba itaba ,

Kiran sunanta yayi ,amma bata jishiba tayi nisa cikin tunani, "hajiya"ya kara kiran sunanta da karfi. Firgigit ta dawo cikin hayyacinta ,kallon Abba tayi cikin jin dadin ganinshi tace "alhaji barka da zuwa' Mamaki fal ran abba ,wai yau shi akewa sańnu da zuwa ? Lallai rayuwa juyi juyi.

Zamowa mommy tayi daga kan kujera ta durkusa gaban abba, "dan allah alhaji kayi hakuri ka yafemin laifukan danayi maka,nayi nadama na tuba ka gafarceni wllh sharrin shedanne.

Mommy ta fada tana hawaye sosai. Hmmm hajiya kenan ni nace kinyi min laifine? Ai keda duniya itace zata koya miki darasin rayuwa,dan haka ki kwantar da hankalinki ni bance kinyimin komaiba,abba ya fada cikin ko inkula.

Kuka sosai mommy keyi,"alhaji nayi nadama nayi kaico da rayuwata nasan. Ni azzalumace amma dan Allah ka yafemin wllh bazan karaba .

Shiru Abba yayi baice mata komai ba dan yaji ta fara bashi tausayi , Kuka mommy taci gaba dayi tana bawa Abba hakuri ,amma yayi mata banza.

Khadeejace ta shigo cikin falon dan kameel yayi barci dan haka cikin dubara ta zare jikinta ta fito zuwa falon ,shine taga mommy na ta bawa abba hakuri amma yayi mata banza.

"Abba dan Allah kayi hakuri ka yafewa mommy kuskurenta,abba Allah ma munayi masa laifi kuma yana yafe mana ,dan Allah abba na rokeka ina hadaka da mahaliccinka ka yafewa mommy tayi nadama kuma ta tuba abba kayi hakuri please. Khaderja ce ke fadin haka lokacin data durguka gaban abban itama.

"Khadeeja ki daina damun kanki akan wacce bata san darajar dan adam ba ,yanzu har kina nema mata yafiya da kanki? Abba ya fada yana kallon khadeejan .

Cikin kuka khadeeja tace Abba tayi nadama ka yafe mata dan Allah badan niba,ta karasa tana dora kanta akafar abban cikin kuka.

Shikenan khadeeja ya isa daina kukan na yafe mata Allah ya yafe mn baki daya.cewr abba yana dafa kan khadeejan.

"Nagode abba Allah ya kara girma,ta fada cikin farin ciki tana kallon mommy,mommy kiyi shiru dan Allah abba ya yafe miki ki daina kuka ta fada tana share mata hawayen idonta .

Kallonta kawai mommy keyi wannan yarinyar idan har kaci gaba da rayuwa da ita kana cutar da ita ,tabbas saita kai mutum wuta ,dan halinta na daban ne yanzu dubi yadda ta tsaya tsayin daka tana nema mata farin ciki, Wanann abin kunya har ina?

Haka khadeeja ta tashi ta koma dakinsu cikin fatin ciki ,tasan ta kameel mai saukice shimazai sauko in sha Allah.

Readers Also Read