Kenza eBookz

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 19

Complete book: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy)Chapter 19 of 21FantasyBy Mamy Kabir (aunty Maamy)

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) - Chapter 19

Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 19: Gidan aikina by mamy kabir (aunty maamy) Chapter 19. Tana shiga dakin cikin farin ciki ta kwanta…

3,363 words

Tana shiga dakin cikin farin ciki ta kwanta akanshi tana juyi , Bude ido kameel yayi yana kallonta ,dadi yaji sosai aranshi ganin yadda take farin ciki.

Juyowa yayi yana daga kwancen ya rungumeta yana murmushi ,

"da alama yau kinsamo mana wani labari mai dadi naga kina ta farin ciki bani nasha"kameel ya fada yana shafa cikinta.

"ina cikin farin ciki mijina Abba ya yafewa mommy da kansa yace ya yafe mata alhamdulillah ,"ta fada hawaye na cika mata ido.

"Allah sarki Khadeeja yar albarka ji yadda take ta farin ciki dan abba ya yafewa mommy . "Shine kike ta wannan murnar kamar anmiki albishir da gidan aljanna? Ya fada yan dan hararata.

"yaya dole nayi farin ciki,bana fatan mommy tayi ta jin kunvi kanar yadda naji ,ina son kowa ya kasance cikin farin ciki yaya,ta fada tana sunbatar bakinsa.

"Allah yayi miki albarka deejena ya baki farin ciki har karshen rayuwarki ,kamar yadda kike son ganin farin cikin wasu "

Ameen yayana dan Allah yaya ka yafewa mommy kaima ka zame mata da nagari mai sanyata farin ciki ,aljannanrka na kasan kafarta kaji yayana ,ta fada tana karkata kanta .

Kameel rasa me zaiyi yayi kawai ya hade bakinsu yana mata wani zazzafan kiss ,tuni ta rikice ta susuce dan wata irin kalar soyayya mai zafi yake nuna mata gaba daya sun rikicewa juna dan itama khadeejan ba'a barta abayaba sosai take maida martani. Sun farantawa juna sosai sai sumbatu suke ta fama zubawa kowa yana yabon dan uwansa .

Anyi bikin islam ,inda akasha shagali sosai ,haka aka gama biki lpy aka kaita gidan mijinta dake zoo road saidai muce Allah ya bada zaman lpy.

Doctor zainab ta dawo gidan abba da zama inda aka gyara mata part dinta itama,murna gurin khadeeja kamar me mommynta ta dawo kusa da ita.

Sosai mommy ke kulawa da khadeeja ,dan fur taki batun komawarsu sabon gidansu.

Wata rana suna zaune afalon mommy na guda ta kama khadeeja ,lokaci daya nagudar ta taso mata gadan gadan ,

Nan da nan mommy ta sanyata adan clinic din dake cikin gidan tana bata kulawa. Kameel sai safa da marwa yake yana ganin yadda khadeejansa ke faman shan wahala kamar zata mutu .

Sai salati take tana maimatawa.

Gabadaya kameel ya rude ya rasa ina zai sanya kanshi ,mommynsace ta karaso gurin da yake tsaye yana ta karkarwa yana kallon khadeeja dan yana cikin dakin sam yaki fita daga dakin hannun khadeeja na cikin nashi ,sai sannu yake mata.ji yake kanar ya karba mata nakudar tausayinta yakeji sosai aransa ,wannan aikin kameelar tasa fitarsa akwai wuya dole yaja mata kunne.

Juyiwa yayi yana kallon mommynsa cikin mutuwar jiki ya rungumeta ya sanya kuka. "mommy khadeeja bana sonna rasata mommy wanan wahalar tayi yawa please mommy do something ,ya fada yanakara rungume mommyn nashi Itama rungumeshi tayi tana mai jinwani sanyi aranta ,yaushe rabonta da dan nata harta manta ,amma yau sanadin nakudar da khadeejan keyi ya sakko ya dawo gareta ,Alhamdulillh Allah shine abin godiya.

Hawayena ya zubowamommy cikin nadama mai tarin yawa ,take shafa kan dan nata ,kayi hakuri son insha Allah zata sauka lpy karka damu kaji? Kaidai kayim........

Shiru mommy tayi saka makon wani uban nishi mai hade da kara da khadeejan ta saki,saiga gkaton danta ya fado yana dirowa wani ya biyo bayansa,cikin minti daya saiga wata yar ta fado,

Gwalalo ido kameel yayi yana kallon ikon Allah makar amafarki yake ganin abin khadeeja ta haihu yara har uku .......

Toh aimun hadu next page danjin irin murnar da kameel zaiyi da samun yan ukunsa. .taku anty mammy🙏

mrs babi💘💘

share and comment please.

More comment more typing. [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

GIDAN AIKINA 🍒🍒

Na mammy kabeer (anty mammy)

ELEGANT ONLINE WRITER'S

Page 67/ 68

Gareku masoyana wannan page din yake

Fayum Ummu ja'afar Hurairah Antyn ummi Cry cry member Da sauran masoya masu bibiyar novel dina.

Kwalalo ido kameel yayi yana kallon ikon Allah kamar amafarki yake ganin abun ,khadeejan sa ta haihu yara har uku.

Juyawa yayi yana kallon mommy wacce itama ido bude take kallon yaran ,manya dasu sai wutsil wutsil suke ,doctor na ta kokarin kyarasu.

"mommy kinga yara uku ta haifa duka nawane "? Ya fada yana nuna yaran idonsa abude ,tsabar farin ciki yama rasa ne zaiyi,

Ido tab da hawaye mommy ta dafa kafadar kameel tana jijjiga masa kai,tabbas kameel yarankane da Allah ya azurtaka dasu ,naka ne duka,ta fada hawayena zubowa daga idonta , Cikin wani irin farin ciki marar misaltuwa kameel ya rungume mommy yana kuka, Allah mai yadda yaso alokacin dayaso ,wai yau shi kameel shine aka haifa masa yara har uku duk nashine ! Wane irin farin ciki zaiyi shikuwa ?me zai yiwa khadeeja dan ya nuna mata tsantsar farin cikinsa? Durgusawa yayi agurin yayi sujjada ,yana mai godewa Allah .

Karasawa yayi jikin gadon da khadeeja ke kwance cikinn hawaye itama tana jinjina da baiwa da buwaya irin ta uban giji,yau itace ta haifi yara har uku kigis duk na tane ! Allah shine abin godiya.

Zama yayi saitin kanta ta ruko hannunta yana shafa kanta ,yama kasa magana sai hawaye yana murmushi. Share masa hawayen khadweja tayi tana girgiza kai,alamu ya daina zubar da hawaye dukda itama hawayen takeyi.

Sumbatar hanunta yayi cikin zallar farin ciki da so Yace"meri janiman,meri dunya ,bohaat bohaat shukriya meri rani, Nagode nagode bani da abinda zan saka miki dashi ,kingama min komai arayuwata kinkasance mahadin rayuwata ina sonki sosai ,kinbani farin ciki kin haifa min yara masu kyau kamarki Allah ya kasheni da sonki matata" Ya fada hawayensa na zuba kan fuskarta.

Murmushi tayi tana jan dogon hancinsa ,sannan ta turo baki cikin shagwaba ,bayan yaranka sun wahalar dani nakusan mutuwa fa ,ta karasa tana turo baki.

Kissing din bakin nata yayi yana jin wani sabon nishadi na shigarsa, Sorry my wife zanyi musu fada sun wahalar min dake .

Toh rasai idan kungama rashin kunyar taku saiku bamu guri dan ingyarata ko,doctor ta fada dan musu hararan wasa.dan ganin sun manta dasu agurin ma.

Kunya ce ta kama khadeeja ,ta rufe idonta dan harga Allah ta manta su mommy agurin , Tashi kameel yayi yana kallon yaran nashi yace"kai mommy ni wllh na manta daku agurin nan ma kawai ta matata nake ina tauyamata yadda tasha wahala ,gaskiya nan gaba ni zanyi nakudar nan Ya fada yana daukan baby girl din. Fara sol da ita kamarsu daya da uwarta kyakykyawar gaske kamar yar indiyawa ga gashi sosai akant, Rungumeta yayi cikin wani tsantsan farin ciki yana hamdala ,wata zazzafar kaunar yarinyarce ke ratsa dukkan sassan jikinsa.

Ohh hajiya babba kijimin yaro da wani batu fa ? Daga haihuwar yarinya ya fara batun wata haihuwar ,toh kaji da kyau allura zanyi mata saita huta sosai kafin ta sake haihuwa.

"haba mommy wace allura kuma ana zaune kalau? Dan Allah kiyi hakuri ni wllh yara nake so da yawa ,ni banki nan da wata shekarar ta kara haifo min kamar wadan nan bama.ya fada yana daukan namijin bayan ya ajiye macen,kallon yaron yayi cike da da kauna wannan kam ko ba'afada maka ba kasan yaron kameel ne dan kamar antsaga kara ,sunbatar yaron yayai tare da yi masa kiran sallah akunne kamar yadda yayiwa macen ,haka shima dayan yayi masa ,sake daukar macen yayi ya runhumeta ajikinsa .wata kalar kauna yakewa yarinyar sosai yake kallonta kamar Khadeejanshi,

Har aka gama gyara khadeejan akayi mata dinki dan ta karu kamerl yana zaune yana rungume da babynsa ,ajikinsa jinsa Yake kamar bashiba ,wai shine yake da yara har uku ?

Nan da nan labarin haihuwar ya bazu cikin dangi da abokan arziki ,murna agurin su maryam ba 'a magana , Kullum gidan cike yake da yan barka ,yau kwana uku da haihuwar yan uwa na malam madori duk sunzo ,su inna lami ma ba'abarta abaya ba. Lokacin daga irin daular da khadeeja ke ciki, gaba daya jikinta yayi sanyi ,lallai ikon Allah sai kallo yanzu yar da suka turo aikatau dan ta lalace itace Allah ya sanyata cikin wannan daular ga yarta can na fama da goyon shegen da,Duniya ba tabbas Allah mun tuba.haka tayi ta neman yafiya agurin khadeeja tana kuka ,khadeeja kuwa kwantar mata da hankali tayi tace ta jima da yafe mata dama bata kullaceta araiba.

Gaba daya yanzu mommy ta koma ga Allah ya shiga taitayinta ,taji tsoron Allah ikon Allah ya wuce tunanin mai tunani,yanzu yar da take gudun hada zuria da ita itace ta haifa maya jikoki masu kyau da daukar hanakali har uku,Allah na tuba ta fada tana share hawayenta. Duk adarare take komai jikinta yayi sanyi sosai ,sai nan nan take da mutane tayi sanyi akan halayenta. Ga wata irin kaunar yaran dake cike da zuciyarta ,amma tsoron daukarsu take saboda tana gudun karsu hanata daukan yaran . Yauma suna zaune dayake khadeejan apart din doctor take, Shima kameel nan ya taro da zama .

Mommy ta shigo dakim suna zaune khadeeja na cin farfesun kayan ciki kameel na gefenta shima tana bashi abaki,yana rungume da babynsa ajikinsa, Islam kuma tana sanyawa dayan yaron kaya ,doctor na shirya dayan shima.

Mommy tashig da sallamarta,ta zauna agefe gaisheta khadeeja tayi sannan islam na ta gaisheta , Kameel dai yana zaune yana cin namanshi da khadeeja ke bashi abaki ,yana rungume da babynsa. Shiru mommy na zaune idonta na kan yaran da ake shiryawar ,sosai take son daukan yaran ta rungumesu amma batasan ta yaya zata faraba. doctor ce ta gama shirya na hannunta ,dan haka ta mikowa mommy shi tana cewa Hajiya karbi wannan maihidan naki ,naga alama yafi sauran rigima,shikenan kullum shan nono.ta fada tana mikawa mommyn shi [12/7, 10:31 AM] Saratu Kabir: Hannu na rawa mommy ta karbi yaron tana mai zuba masa ido ,hawayene ya cika mata idonta cikin nadama da danasani mai tarin yawa aranta,yanzu da tayi wasa rabon wadan nan yaran sai ya kasheta,tayiwa Allah godiya dayasa ta fahimci gaskiya tun kafin ta bar duniyar,da yazatayi da tarin hakin mutane data dauka ?dole ta nemi yafiyar kowa da kowa,

Kallonta kameel yayi ta gefen idonsa ,sosai yakejin mugun tausayin mommyn nashi dan yasan ta nuna musu so da kauna,abu guda dayi musu shine tarbiyya da basu samu agurinta ba. Ajiyar zuciya yayi tare da lumshe idonsa yana jingina da jikin gadon dasuke kai yana kara rungumar yarsa,

Doctor kuwa ficewa tayi dan ta basu guri ko akwai abinda zasu tattauna,dan tana fatan ace sun sami kusanci tsakaninsu.

Islam ma mikowa mommy dayan yaron tayi tace zata je ta duba girkin da mommynta ta sanyata ta fice,rungume yaran mommy tayi ajikinta ,duk yadda taso boye kukanta saida kukan ya kwace mata ,tana rungume da yaran ajikinta ,tana kuka jikinsu gaba daya sai yayi sanyi,shikansa kameel din wani irin tausayin mommyne ya kamashi ance da da mahaifi sai Allah ,dan haka kallon mommyn yake cikin tausayawa duk ta rame tayi duhu wananan izzar duk babu ta sauketa ,kai yannzu wannan gwalagwalan dake sanyawa ma duk ta ciresu,kallon khadeeja kameel yayi cikin damuwa.

Girgiza masa kai tayi alamu ya rarrashi mommyn nashi,aikuwa da saurinsa ya sauko daga kan gadon ya zo ya tsugunna agaban mommyn yana rike da babynsa ajikinsa,da alama dai yana matukar son yarinyar,dagowa mommy tayi tana kallon kameel cikin kuka take cewa,

"ka yafemin dana. Ka yafemin dan Allah na cutar daku na shiga hakkinku,na zama muguwar uwa banyi mukh adalciba ban baku tarbiyya ba ,na rabaka da matarka na cutar daku duk akokarina na ganin bata haifamin jikokiba dan gudun hada jini da talakawa ,bansan cewa itace zata zama silar farin cikin gidan nan ba ?bansan cewa itace zata tsamomin yarana daga mugun halin da suke cikiba ,bansan cewa itace zata zama silar shiriyata ba ni kaina ,bansa da wane ido zan kallekuba . Khadeeja ina mai neman yafiyarki akan kuskuren dana aikata miki dan Allah ki yafemin kameel ka nemamin yafiyarta ,inba hakaba hakkinta kadai ya isheni . Ta karasa cikin kuka wanda yagi wand takeyi.

"mommy ki daina kuka haka ya isa please mun yafemiki tun da jimawa ,ke mahaifiyarmuce ,bazamu so ganinki cikin damuwa ba dan Allah ki kwantar da hankalinki mommy fast is fast"kameel ya fada yana jin dadin yadda mommyn tashi ta gane gaskiya.

Kallon khadeeja mommy tayi "ki yafemin khadeeja dan Allah ki yafeni,wllh hajiya talatu itace silar komai ita ta jefani cikin mummunar rayuwar nan na tuba ku yafeni,

Cikin kuka Khadeeja tace "mommy dan Allah kiyi shiru wllh na jima da yafe miki ,ban kullaceki araina ba nasan watarana zaki gane ni ba sharri bace agareku,dan Allah mommy kiyi shiru na yafe miki.ta fada cikin kuka .

Nagode muku Allah ya shi muku albarka ,Allah ya raya muku yaranku ya hade kanku . Cewar mommy cikin jin dadin yafiyar data da suka karba.

Sosai khadeeja ke farin ciki yau taji dadin wanann ranar ta kasance mai muhimmanci agareta . Mommy ce tace "son ka bani kishiyar tawa na ganta mana ,tana murmushi.

Cikin dannshagwaba kameel yace "mommy ni gaskiya bana son rabuwa da itane wllh ina sonta sosai araina ira da yan uwanta ,amma ita wannan inajinta sosai acan cikin raina.ya fada yana sunbatar yarinyar ,

Murmushi mommy tayi Allah ya raya mana ita son tana karbarta lokacin daya miko mata ita .

Kallon yaran take cike da so da kauna ,kamarsu daya mazan sak bazaka banbancesuba ,farare sol dasu masu tsananin kamada son dinta ,kallonta takai kan macen masha Allah yarinyar kyanta har yayi yawa kamarta daya da mamanta sosai saidai yanayin idonta na babantane, Allah ya raya minku.ta fada cikin murmushi.

Kallon juna kameel da khadeeja sukayi cike da jin dadi da murna aransu ,dan langabowa jikin khadeeja kameel yayi yana son kissing din bakinta , Zaro masa ido tayi tana nuna masa mommy dake zaune kan wata kujera rike da yaran ahannunta.

Turo baki yayi yace"mommy kinganta ko?wai bazan ...da sauri khadeeja ta rufe masa baki tana zare ido jin yanason fadawa mommy abinda zaiyi ta hanashi.

Kallonsu mommy tayi tana dariya cikin farin ciki tace ,barshi khadeeja nasan kome zai fada ba haka bane kuma bazan yarda da zancensa ba.

Cire hannun khadeejan kameel yayi daga bakinsa yace"wllh mommy dan bakisan me zance miki bane shiyasa ,ai tasan bata da gaskiya shiyasa ta rufemin baki,ya fada yana turo baki ,

Dariya mommy da khadeeja sukayi,mommy tace ato yanzu dai sondina ya girma shima babanedan haka rigimada shagwaba ba nashi bane ni yanzu wadannan sune nawa ,ta fada tana gyara musu kwanciya ajikinta.

"au mommy haka zakice ko?dan kin sami wasu yaran shine zakice ni yanzu banaki bane ko?shikenan bari nima in yafi gurin mommyna tunda anan ana nunamin wariyar launin fata.ya fada yana kokarin sauka daga kan gadon yana turo baki,

Kallon khadeeja yayi yace "na tafi tunda kin biyewa mommy ta korar miki miji kuma kameelama tayi fushi ya fada yana ficewa daga dakin.

Dariya khadeeja tayi cikin farin ciki jinta take kamar wata yar shekara ukutsabar rashin dumuwa, Jingina tayi tana kallon yadda mommy ta kasa dauke idonta daga kan yaran ,Allah shine mai komai mai kowa sannan mai juya al'amuransa yadda yaso ,kamar dai yadda ya juya kiyayarta daga zuciyar mommy zuwa so ,Allah ya dawwamar wannan soyayyar. Dagowa mommy tayi itama suka hada ido da khadeejan murmushi sukayi dukansu khadeeja ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta.

" kisaki jikinki dani khadeeja ki daukeni tamkar mahaifiyarki ,yanzu duk daya kuke agurina keda su kameel dan haka ki kwantar da hankalinki dani kinji?mommy ta fada cikin sanyin murya.

"ba komai mommy na yarda dake kuma dama tunda can matsayin uwa na daukeki.ta fada tana murmushi.

Yau ta kama ranar litinin kuma yaune sunan yaran khadeeja an rada musu sunan mazan sunci sunan abban kameel wato kassim ana ce masa aman,dayan kuma sunan baban khadeeja wato musa ana ce masa aiman , sai kuma macen sunan umma khadeja maryam ana ce mata mama.masu karatu kuzo kuga yadda khadeeja tayi wani irin zazzafan kyau mai daukan hankali ,dan mai kyalliya aka dauko ta musamman ta gyara maijego kai kace amarya ce.

Koda kameel ya shigo dakin tsayawa yayi saroro yana kallon khadeeja ,masha Allah ,watabarakallahu fi ahsanil khalikin,shine abinda kameel ke maimaitawa abakinsa, Lafin ya taho ahankali ya rungumeta ajikinsa ,ga wani irin kamshi dake tashi ajikinta dan gyara akayi mata in and out dama tuni dinkinta ya warke da kanshi.

"kinyi kyau matata kinfi ko wace mace aduniyar nana cikin idona ,ina sonki matata.ya fada yana shinshina wuyanta yana kokarin sauya salon zancen.

"Yaya kameel zaka batamin kwalliya ta fa ta fada tana cireshi daga jikinta.

Kallonta kameel yayi da idonsa dasuka kankance sukayi ja ,"please deejena ki barni nadan ji dumin jikinki ,ke ko tausayina ma bakiyi ko yaushe rabona dake Allah kameelarki fa tana cikin damuwa kullum kukan nemanki take kalli fa kigani" ya fada yana nuna mata yadda kameelarshi ke harbin iska . Yana kara rungumeta ajikinsa .

Buga kafa khadeeja takeyi tana kukan shagwaba " ni wllh yaya kasakeni zaka batamin kwalliya ta fa ta fada tana lumshe ido dan ya fara sauke mata network.

Laaaaa!!! kai kameel zo kaficemin daga dakin nan, yau naga marar kunyar yaro ,yanzu ko tausayin yarinyar nan bakayi zakazo ka dameta da shegen fitina ,ohh ni yasu wannan zamani Allah ka shirya mana yara sam basu da hakuri.cewar mommy tana shigowa dakin dan daukar yaran zuwa dakinta.

Girgigit khadeeja ta banbare daga jikin kameel cikin wata mashahuriyar kunya ,tana mai sunkuyar da kanta ,yanzu shikenan kameel ya kunyatata a idon mommy ,ace tana jego amma tana makalewa miji.

Kameel kuwa wani hade rai yayi yana kokarin kara kamo khadeejan ,ita kuwa tana matsawa,"haba mommy kema irin haka sai annemi izini ake shigowa daki idan ma'aurata suna ciki ,yanzu kawai mommy kin katse mana jin dadi.ya fada yana turo baki dan harga Allah abaiso mommy ta shigo yanzuba.

Kaci gidanku kameel marar kunyar yaro ,fice ka bani guri tun kafin in fitar dakai ,mommy ta fada tana nuna masa kofa .

Sumsum yayi hanyar waje yana turo baki ,haka kawai anzo anhana mutun hutawa da matarsa ,wllh ana gama sunannan zamu bar gidan ma sai inga ta yadda za'a hana mutum kebewa da matarsa.

Rike baki mommy tayi, Allah ya shiryeka son wllh zama cikin indiyawannan ya koya maka rashin kunya. Ke kuma wllh idan baki kiyayeshiba wllh zaiyi miki wayo ya sake dirka miki wani cikin da yaranki kanana baruwana ,mommy ta fada tana daukar yaran ,ta jeresu cikin wani hadadden gado mai shegen kyau.

Yaran sunci kwalliya cikin wasj kaya masu kyau ,kala daya saidai banbancin na mata dana maza.

Khadeeja dai tayi tsuru tsuru cike da kunya har mommy ta bar dakin ,turo baki tayi haka kawai dan kana jego kuma bazaka dan kula da mijinka ba ka dan dauke masa kewa ba.ta zauna tana ta turo baki.

Islam ce ta shigo taci kwalliya itama ,sister ya naga kinta turo baki haka? Ta fada tana zaunawa kusa da ita. "Mommyce mana ko tausayin yaya bataji tawani koreshi daga dakin nan. Dariya islam tayi tana kallon khadeeja ,wllh kema khadeeja akwai jarababba,yanzu kina jegon kike makalewa miji ?har dan ankoreshi kike fushi?wllh ba ruwan wani idan ya kara dirka miki wani cikin da yara kanana.ta fada tana dariya.

"waiku cemuku akayi ciki yace zaiyimin wllh kawai baku tausayinsa ne kawai ta fada tana turo baki.

Mommy kuwa dakinta ta kai yaran ta kwantar dasu dan ba'a bukatar mutane suyi ta daukarsu saboda baki dan yaran kyansu yayi yawa .

Komawa dakin da baki suke mommy tayi tana tambayarsu ko da abinda suke bukata , Sosai yan uwan Abba sukejin dadin yadda mommy ke kula dasu ita da doctor.

Ana can ana ta hira da raha adakin maijego ,gidan ya cika da yan uwa da abokan arziki,

Mommy anata hidima da baki ,duba agogo tayi ynzu kusan awa uku da dauko yaran ,ya kamata akaisu sudan sha nono,dan haka ta nufi dakinta dan dauko yaran ,saidaime tana zuwa babu yaran babu alamarsu akan gadon nasu.

Zaro ido maommy tayi cikin tashin hankali ta fito aguje tayi part din doctor karo sukaci da doctor zata fito ,hajiya babba lpy kuwa.doctor ta tambaya, Inafa lafiya kin dauko yaran nan ne doctor bangansu ba basa cikin dakina,

Readers Also Read