Heedayah complete Novel - Chapter 81
Heedayah complete Novel Chapter 81: Heedayah complete Novel Chapter 81. Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,:…
2,861 words
Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Chapter notes and social links
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Washegari da safe misalin karfe tara Heedayah da Farida da Maid din Mami na serving din bak'in dake parlor breakfast na soyayyen Irish, kwai, shayi da farfesu with bread, yawanci duk cousins da aunt din Khaleel ne da kids dinsu a parlon, kana ganinsu dai kasan babu ta inda suka hada hanya da talauci, Mami ce ke ba su Farida breakfast din su kai parlor ita tana tsaye kitchen din, bude kofar parlon aka yi Kaka ta shigo sakale da katon jakarta ta yafa katon mayafi, ga sarkan zinarinta sai sheki yake a wuya da dankunnensa, tsaye tayi bakin kofar ta dinga bin mutanen parlon da wani kallo, can tace "Ya haka kamar ana yunwa, tun fa daga iyafot motocin sojoji dake bayanmu ke jiniya ana sanar da jama'a xuwanmu ana ta bamu hanya har muka shigo anguwar nan, ku baku ji bane?? Yanxu ta ina xa mu bi mu wuce ta nan duk dankali da kwai, matar gwamnan kano da mu ne fa ke tafe tun daga kano, a jirginsa na kansa kuma aka dauro mu aka kawo mu nan garin, muna dira iyafot motocin sojoji suka hau jiniya ana sanar ma kowa ana ta bamu hanya a titi, to kuma mun shigo gida bbu hanyar wucewa don Allah" Mami ce ta fito daga kitchen jin muryar kaka, da fara'a tace "Sannu da xuwa kaka" Ta bayan kujera kaka ta bi ta tana taku dai-dai ta wuce sama, Duk occupant din parlon suka bi ta da kallo, Yakumbo ta shigo parlon ita ma tana kare ma parlon kallo ta rike ha6a tace "Al'adar bahaushe dai ba kyau, komai dai ace sai anci abinci, gidan mutuwa abinci, gidan biki abinci, gidan suna abinci, daga bayyanar yaro ma an xo jaje an hau cin abinci, to mu dai rabon mu da abinci wllh tun jiya da daddare, yau da safe ma da kaji muka karya muka sha yagwat muka kamo hanya abun mu" Mami dai tsaye tayi tana kallonta ta kasa cewa komai duk jikinta yyi sanyi, Ammin Heedayah da frnd dinta na tsaye balcony ko wannensu ya kasa shigowa, Yakumbo ta bi hanyar da kaka ta bi sai kuma ta juyo da sauri tana kallon mutanen parlon tace "Ina kwanan ku?" Few daga cikinsu ne kadai suka amsa, tace "Ya muka ji da wnn abun al'ajabin?" Bbu wanda yace mata komai, tace "Toh Allah ubangiji ya raba mu da duniya lafiya, ya kare 'ya yanmu da jikokinmu da tatta6a kunne da hihihin, su kuma wa enda suka cuci wnn yaro Allah yyi kasa kasa da su ya tsine masu albarka, ya bi masa hakkinsa, tunda iyayena suka haifeni ban ta6a jin irin wnn labarin ba sai jiya, ni dai dama ina ganinsa nace yyi kama da yan kinnafas to ile ga maganata nan ashe D'an kinnafa dai Rahinah ce ta haifesa, kuma duk wanda ya ta6a xaginta a kan d'an nan nata sai Allah ya saka mata ya bi mata hakkinta don ba ita ta aikesa ba, ba ita ta saka sa ba" daga haka Yakumbo ta wuce sama, sai a snn Ammi suka shigo parlon, Mami tayi murmushi tana welcoming dinsu, Ammi ta xauna nan parlon suka gaisa da mutanen dake ciki snn suka wuce sama su ma. Heedayah da Farida ne suka kai masu breakfast sama suka yi masu sannu da xuwa, Yakumbo ta sa Farida ta hada mata shayi tana kallonta tace "Toh ina shi d'an uwan naki yake?" Farida tace "Yana nan" Kaka tace "To yanxu ya isilin dukiyoyin jama'ah da ya kwamushe fa" Farida dai bata ce komai ba lkci daya jikinta yyi sanyi, Heedayah ta hade rai, Kaka ta fara matsar kwalla tace "Haka kawai a rabaka da d'an ka tun yana dan yaye a tafi a daurasa a muguwar harka, anya mutanen nan xa su wanye lafiya da duniya kuwa? Toh yanxu ya xa mu yi mu rabasa da wnn mugun hali da yake yi, sun fa riga sun cucesa halin ya shigesa, sai dai kawai ya yaudare mu yyi tuban muzuru, wataran yana iya koma tunda ya ji dadin rike makudan kudi, mu ma kanmu ba wai tsira muka yi ba, ga gwalagwalai na rataye a wuya da kunne, to ni dai ba ruwana ya xo mu gaisa inyi ta kaina in wuce gidan Amadu" Tagumi Ammi tayi bata iya tace komai ba, Heedayah ta mike ta fice daga dakin hawaye har ya kawo idonta, Mikewa Farida tayi ta bi bayanta ita ma, Ammi tayi kasa da murya tace "Haba kaka?" Kaka ta juyo da sauri tace "Haba me?? ban tsine ma shegun da suka sa shi a harkan bane xaki ce min haba? Meye nawa daga fadan gaskiya? Wllh idan bamu yi taka tsantsan ba sai ya iya yashe mu cikin dare" Yakumbo tace "Toh uwar me xai yi da gwalagwalanki na karya shi da ya saba kwamushe manyan motocin jama'ah masu tsada da gidajensu? Meye kuma gantalallun gwalagwalanki" Mikewa Ammi tayi ta fita daga dakin ita ma ranta bai mata dadi ba, Kaka ta ta6e baki tace "Ni dai ba ruwana, to gidan uwata ce nan din da baxan wuce gidan Amadu ba dama? Daga cewa xanje in gaida Amadu sai cibi ya xama kari? Ita kuma waccan figaggiyar kamar kazar Hausa ni ta banke ma kofa wai ta fita, to wllh Amadu ta banke ma kofa ba ni ba, ina ruwanta da d'an mutane da xata ji haushi don na fadi gaskiya a kansa, ko meye hadinta da shi, kuma ai dole dama sai mun hada masa da rokon Allah idan kuwa ba haka ba muna nan mun saki baki xai ci gaba da danyen aikinsa a boye, Allah dai ya saka masa amma kam an cucesa wllh, Amadu dai yace yau yan sanda xa su je su kwashe sauran shegun yan uwan nasa" Yakumbo tace "Toh ai banda uwarsa mutuniyar kirki ce dama babu abinda xa mu xo yi gidan nan mu ja ma kanmu salalan tsiya, barin ma ya ji daga gidan gwamnati muke, ni duk a tsorace nake ma wllh...." Kaka tayi tagumi tace "Ga mu ga Allah dai" Asiya kawar Ammi sanin halinsu bata ce masu uffan ba sai operating waya take, Bude kofar dakin aka yi Mami ta shigo Khaleel na biye da ita, daga kaka har Yakumbo suka yi tsit sai yan idanuwa, Mami ta xauna, shi kuma ya duka nan gabansu ya gaishesu da ladabi, babu warce ta yrda ta hada ido da shi, kaka sai cewa take "Sannu d'an nan, yau dai na takura uban Heedayah ya ara mana jirginsa mu taho dai kada Rakiya ta kullace mu" Yakumbo tace "Wllh kuwa, Allah ya bi maka hakkin ka, Allah ya saka maka, an xalunce ka kam, an bata maka rayuwar ka" Kuka Yakumbo ta saki, Kaka ma ta fara matsar kwalla tace "Ni da xa a kai ni wajen 'ya yan shegun sai in ji dalilin da suka daukesa bayan kashe ubansa da suka yi, nasan xa su fada min, tun muna yara ake mugunta a duniya har yau ba a saduda ba, wnn tsiya da me yyi kama???" Mikewa Mami tayi ta fita, Kaka na share idonta tace "Tashi ka tafi kai ma, Allah ya saka maka kawai" Mikewa Khaleel yyi ya fita daga dakin, Yakumbo na kallon kaka tace "Toh yanxu meye hukuncin uban dukiyoyin da ya tara ta muguwar hanya?" Kaka ta gyara xama tace "Hukuncinsu a raba ma marayu kawai, ga dai mu nan da yawa a duniya ba iyaye tun muna yara" A ranan yawanci relatives din Khaleel dake Abuja duk suka koma, gidan ya rage daidaikunsu da xa su koma gobe. Da yamma Ammi da frnd dinta na xaune dakin Mami, Hajiya Zuwaira da Aunt din Khaleel ma duk suna dakin, Yakumbo da kaka na can dakin da suka fara sauka bbu wanda ya tafi inda suke balle yaji kayan takaici, Aunt din Khaleel tayi breaking din silence din dakin tana kallon Mami tace "Toh Allah ubangiji yasa mu ji alkhairi, Allah ya baku nasara" Ammi tace "Ameen" Hajiya Zuwaira tace "Ae tunda aka samu aka cafkesu gaba daya anyi mai wuyar ai, amma shi abokin Khaleel din ya isilinsa ynxu?" Mami tace "Barrister yace ya bar garin, yanxu haka yana Bauchi" Hajiya Zuwaira tace "Toh amma a record din ai shi Aliyu ya ambaci sunansa, kinsan kuma dole a kotu xa a bukaci ganin abokin nasa da ya ambata" Mami tayi murmushi tace "Barrister ya so yanke wajen nace kar yyi, idan suka bukaci Zayyad a court din xa mu kirasa ya xo, kuma xa mu yi iya kokari na ganin mun wankesa shi ma idan Allah ya yrda, sure xai yi iya yiwuwa yyi xaman gidan yari na kankanin lkci but not life imprisonment, shi ma Aliyun hakan xai iya faruwa da shi" Hajiya Zuwaira tace "In sha Allah kotu xata yi masu adalci da taimakon ku, hakan ma baxai faru ba" Mami dai bata ce komai ba, A hankali Ammi tace "Allah xai baku nasara in sha Allah" karfe biyar kaka ta bude kofar dakin Mami tace "Toh Rakiya mu dai xa mu wuce gidan Amadu mu kwana" Mami tace "Baxa ku kwana nan ba kaka?" Kaka tace "Mu kwana nan kuma? Oh oh gwara mu je gidan Amadu nan jama'ah sun maki yawa, ga dai motoci can waje duk inda xa mu a Kaduna xa su kai mu ai" Ammi tace "Baxa ku bari mu tafi can din gobe ba daga can sai mu wuce?" Kaka tace "D'a na ne fa Amadun? In xo har Kaduna in kasa xuwa gidansa in kwana, lalacewata bata kai haka ba Aisha, mu dai ba mun xo mun jajanta abinda ya faru ba, kuma gashi sai wani hade rai mutumin yake kamar baya son ganinmu a gidan mun rasa me muka masa, ba gwara mu san inda dare yyi mana ba kada mu je abu ya lalace mana tsakar dare a shiga uku" bbu wanda yace mata komai dakin ta juya ta fita, Mikewa Mami tayi ta fita tayi masu sallama ita da Yakumbo, Mami na kallon Heedayah dake parlor tace "Collect the bag for them" Heedayah dai bata ce komai ba, Farida tuni ta dauke kai dama, can dai Heedayah ta mike babu walwala ta amshi ledan hannun yakumbo, xata amshi jakar kaka kaka ta makale a hammata tace "Aa bar min kayana, kina hararana xaki wani amsar min jakata ki saka min mugun abu, meye hadina dake banda kawai muna mutunci da ubanki ya takura sai na dawo gidansa da xama kwata kwata, tun fa maganar da aka yi daxu a daki shine take ji kamar ta caccake mu da wuka" Yakumbo ta nufi kofa Kaka ta bi bayanta, Mami dai ta bi su da kallo har suka fita sannan ta koma sama, Sumayya na kallon Farida tace "Who are they?" Farida tace "Yan uwanmu ne" Sumayya bata kuma cewa komai ba sae ta6e baki da tayi. Khaleel na xaune compound din gidan tare da Junaid suna hira sama sama, su kaka suka fito tsakar gidan, da sauri kaka ta dauke kai ta nufi gate, Mikewa Junaid yyi bayan ya ajiye glass cup din drink dake hannunsa yana kallon Khaleel yace "Mu je kayi masu sallama" Mikewa Khaleel yyi ya bi sa, Sojojin dake bakin gate tsaye suka ba su Yakumbo hanya suka fita gate din, waje ma sojojin tsaye ne sai lafiyayyun motoci biyu da motar sojoji a baya, ganin Khaleel Yakumbo tace "Ae da baka ba kanka wahala ba d'an nan" Kaka na kokarin shigewa cikin mota Junaid yace "Xa ku tafi gidan Abba ne Kaka?" Kaka ta shige motar tace "Ehh Junaidu gwara mu je can din dai kawai ya fi mana" Yakumbo ma ta shige motar, Khaleel yyi kasa da kai yace "Allah ya tsare" kaka ta daga masa hannu bibbiyu tace "Ameen" Yakumbo tace "Sai ka dage da Sallan dare kana rokon Allah kaji?" A hankali Khaleel yace "In sha Allah" Kaka ta fixgo ledan Yakumbo dake hannun Heedayah da ta wani hade rai murya can kasa tace "Mayya kawai" juyawa Heedayah tayi ta shigewarta cikin gida, Junaid na murmushi yace "Amma xa ku dawo nan ko?" Kaka tace "Aa mun gama da nan, ita dai Aisha idan ta gama galantoyinta sai ta same mu gidan Amadu, ai gobe Amadun kano yace mu dawo, kaga baxa mu tsallake umarninsa ba ai" Junaid yace "Toh shkkn, sai mun xo" Kaka tayi kasa da murya tace "Kai da wa??" Junaid yace "Xa mu xo tare da Khaleel in sha Allah" Yakumbo tace "Ehh to ai da kyau hakan, amma fara yawo ba nasa bane yanxu, killacesa xa a dinga yi har tsoron Allah ya shigesa, abinda ma Amadi yace xai xo nan tare da gwamnan Kaduna su gaishesa su jajanta masa, ai ba sai yaje kano ba, mu ma xa mu dawo idan Allah ya yrda" Kaka tace "Ai shine naga...." Khaleel dai kallonsu kawai yake, Kaka tace "Gaskiya jini ba wasa bane, sai da suka tsaya a tare naga mugun kamar da suke da Junaidu, har lotsawan kumatun Allah sarki" Murmushi Junaid yyi, Khaleel yace "Allah ya kiyaye hanya" A tare Yakumbo da kaka suka ce "Ameen" daga haka ya juya ya koma ciki, Kaka tayi kasa da murya tana kallon Junaid tace "Kace ma Rakiya tayi ta tashi cikin dare tana sllh tana kuka tana nema masa gafara wajen Allah, na manta ban gaya mata ba wllh, snn tayi ta masa nasiha cikin dubara akan daukan abinda ba hakkinka ba, snn tayi ta nuna masa illar yin haka, ta dinga nuna masa kudi a nan duniya ake samunsa kuma a bar sa a mutu" Junaid bai iya yace mata komai ba, Yakumbo tace "Driver mu je magariba nayi, Allah dai ya kai mu lfya" Driver ya ja motar, na sojoji na biye da su a baya suka bar layin. Bayan isha Khaleel na xaune parlor idonsa a kan wani movie da ake yi a tv, xamansa a parlor umarnin Mami kawai ya bi amma bai son xaman cikin parlon, Mami kuma bata son yana xama shi daya a daki ne, he is always silent snn bashi da walwala, Junaid kuma ya fita, Farida da Sumayya ne parlon suna labarin movie din da ake yi kasa kasa, Farida ta kallesa tace "Yaya ko ba haka bane?" Kallonta yyi snn ya kalli Tv din, can yace "Ban san me ku ke cewa ba" Sumayya tayi murmushi tana fari da ido tace "Labarin film din mu ke yi" yace "Ohk but I don't know about the film" bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da kallonsa, Sumayya tace "To a kawo maka abincin yanxu?" Kallonta Khaleel yyi yace "Aa" Heedayah dake xaune dining ta kallesu ta dauke ido ta tabe baki ta ci gaba da cin abincin gabanta, bayan few minutes Khaleel ya mike ya tafi dinning din ya ja kujera ya xauna, Heedayah bata kallesa ba tana ci gaba da cin abincinta, Tuni Sumayya ta daina kallon da take yi, ta shiga xaga parlon da idanuwanta kamar me neman abu, Khaleel na kallon Heedayah yace "Baki bani abinci ba" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ba naji ance xa a kawo maka ba" Bai ce komai ba, ta dago kai tana kallonsa, tashi tayi ta tafi kitchen ba a dau lkci ba ta fito rike da plate din abinci, a bakin kofar kitchen din suka hadu da Sumayya ta ba Heedayah hanya snn ta shiga kitchen din, Heedayah ta ajiye masa abincin a gabansa a hankali yace "Thank you" Fitowa kitchen Sumayya tayi rike da nata abincin ta nufi dinning ta xauna, Farida ta saki baki tana kallonta, A hankali Khaleel ke cin abincin gabansa, Heedayah dake xaune dinning din sai ta ma kasa ci gaba da cin nata, Lkci daya Khaleel ya tashi ya dau plate din abincinsa ya bar dinning din. Sha daya saura na dare Mami ta shigo dakin Junaid, Khaleel na kwance yana kallo Junaid kuma yyi bacci, ya mike xaune ganin Mami, Mami ta ja kujera ta xauna tana kallonsa tace "Baka yi bacci ba" Yace "Eh ban yi ba" tace "Ka ci abincin kuwa?" Khaleel yace "Na ci" Mami tace "Ohk, kana ji na" yana kallonta yace "Ina ji" Tace "Da mun so sai after this case sai ku tafi da aunt dinka can gombe wajen family din Abban ka, kayi sati daya a can, amma bayan xaman court na gobe sai ku wuce da Aunty Nafisa da Sumayya" Khaleel ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Toh Allah ya kai mu" a hankali Mami tace "Ameen" shiru ne ya biyo baya, Mami tace "Aunty Nafisa autarsu mahaifinka ce, Sumayya kuma daughter dinta ce, but naga kamar baka saki jiki da ita ba" Khaleel yace "Ita wa?" Mami tace "Ita Sumayyar" Khaleel yace "Mami to me xan mata" Mami tace "The mother suggested...." Da sauri yace "Suggested what?" Mami tace "A hada ku aure da ita sbda situation da ka tsinci kanka" Khaleel ya girgixa kai yace "Ni ina da warce nake so Mami"