Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 31

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 31

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 31: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 31. Na kasa kallonsa. Wata irin rawar jiki ta mamaye ni, zuciyata ta…

4,496 words

Na kasa kallonsa. Wata irin rawar jiki ta mamaye ni, zuciyata ta karye, jikina ya yi sanyi, amma wani ɓangare na zuciyata na so in tsaya. Sai naji yadda yake ƙoƙarin lasar bakina Na rufe ido, wani irin nauyi ya sauka daga ƙafata zuwa kai. Na buɗe baki cikin rawar murya“Ka… ka bari dan Allah… Kada wani yashigo.” Amma bai saurareni ba sai yashiga lasar leɓena yana wani jan numfashin dale dagamun hankali ga wani yanayi da nake kokarin shiga yana kokarin aza hannunsa kan kirjina…Kamar da gayya, aka buga ƙofa.

Na tura shi a hankali na janye jikina. Ya ɗan ja numfashi mai zafi, sannan ya juyo ya ce,

“Come in.”

Dr ne ya shigo. Sun yi magana kaɗan kafin yayi masa allura ya fita. Kafin nayi numfashi sosai, Hajja ta shigo da su nawal sun dawo daga siyayya.

Tacemun “Natashi mu tafi, flight ɗinmu ƙarfe tara ne,” ta faɗa.

Na rasa abin cewa. Shi kuwa yana satar kallona yana murmushi kamar ba shi ne ya rungumeni minti kaɗan da suka wuce ba. Natsaya ina kallonsa ina zazzare idanuwa.hajja ta kalleni ta kallesa.

“Badai hanata kayi ba, Asad?” Hajja ta tambaya da sigar wasa. Ya yi murmushi kawai, ba tare da ya ce uffan ba.

Nawal ta ce, “Small Mom, ga phone ɗinki.”

Na karɓa, na ce “Thank you,” cikin jin nauyi. Gani nakeyi kowa yasan menene mukeyi

Ina kallo yadda suka matsa kusa da mahaifinsu, suka yi masa sallama da addu’a.

Hajja ma ta yi masa nasiha sannan tace, “Zamu tafi.” Ya ce zai tura musu kuɗi ta account ɗin Umar. Sukayi godiya suka fita.

Da zarar suka fita, sai na ji muryarsa

“Ke ba za ki yi min sallama ba?”

Na tsaya na kalle shi fuska da ta sha wahala, amma idanu masu cike da wani abu mai nauyi. Na ce a hankali, “Allah ya baka lafiya,” amma cikin zuciyata ina masifa

‘Ya gama tattabeni, sai ya wani narke idan yaga sun shigo…’ “Bring your phone to me,” ya ce. Na amsa, “Okay,” na kai masa. Ya yi dialing wasu lambobi sannan ya miko min.

Bayan haka sai na ga ya zaro wani rafin dollar daga aljihunsa, ya miko min.Na kalle shi cikin mamaki. “Ki karba mana. Buy whatever you want. Kin ji?” Na girgiza kai “Is too much.”

Ya yi murmushi wanda ya sa zuciyata ta ɗan tsaya.

“Ko kin raina?” Na ɗan shagwabe murya, “Wallahi is too much.”

Ya ɗaga gira cikin wasa

“To ko ki karba, ko kuma nayi kissing ɗinki yanzu har su shigo!” Nayi dariya cikin tsoro, “A’a! Zan ɗau 100 dollar kawai.”

Ya yi dariya sosai. “Da Nawal tas, zaku cinye ta kuma ku nema kari. Bakisan Nawal ba, ko? Zakisanta.”

A raina nace, ‘Ai nasan ta shugabar masu son alatu.’ Amma ban furta ba, sai na ce kawai“Na gode. Allah ya saka maka da alkhairi.” Ya ɗan tsuke fuska.

“Come here. Ban son godiya, give me a light kiss, kin ji?” Na riƙe kafadata, ina dariya cikin nauyi “Aa… na fita.” Na juya cikin sauri na bar ɗakin, zuciyata tana bugawa kamar na yi gudu.

A mota na tarar da su suna jirana.

Sai muka koma hotel. Na yi wanka, na ji jikina ya saki kadan. Daman na yi brush can asibitin, don haka na fara gyaran kai.

Ni dai ba kwarewa nayi da skincare ba. Ina ganin su suna shafawa, ni kuma sai kallon su nake. Nawal ta shirya ni cikin abaya baki iri ɗaya da tawa, komai ɗin mu iri ɗaya.

Tace zata ɗaukeni ta tura wa Daddy hoton “Amaryarsa.” Na yi dariya, zuciyata na cike da mamaki wai su ba sa jin kishi ne?

Bilkisu fa mahaifin mu daya , ba ta sona saboda mahaifiyarta bata sona. Amma nikuma kishiyar mahaifiyarsu sun maida ni kamar ‘yar uwarsu. Na ce a raina, “Wato mu talakawa ne muke kishi, su masu hali ba sa kishi kome?” Na kalli madubi a karon farko na ji wani abu ya motsa a cikin zuciyata.

Ba wai soyayya ba rudani ne.

Bayan mun huce filin jirgi, muka nufi wajen shiga ciki. Nawal ce ta ja hannuna, tana dariya kamar kullum. “Small Mom, kinkira Daddy kuwa?” ta tambaya tana ɗan kallo na da ido ɗaya mai ɓoye nishadi.

Na girgiza kai a hankali. “No.”

Ta tura baki, “Why?”

Na ɗan yi shiru, sannan na ce, “Na kira shi kuma. Me zan ce masa yanzu?”

Ta ɗan juyo gare ni gaba ɗaya, idonta ya ɗan faɗa. “Small Mom, what are you saying haka? Your baby ne fa mijinki ne fa yanzu bakiga yadda muke kula da mazajen mu baniba? Shiyasa rashin kulawar nan ke sanya hankalin su a waje..”

Na kauda fuska cikin jin nauyi, “Ke bakyajin kunya wallahi. Sis please, stop it.”

Ta yi dariya da sigar raini, ta matsa kusa da kunnena tana cewa, “To gaskiya you have to change tabbijan. Kin san kuwa Daddy na lover boy ne? Wallahi you better change kafin wasu mata su nannade miki shi.”

Na dubeta da mamaki, “Keh, ke kina magana kamar kina magana nifa kunyar kalaman nan nakeji.”

Ta yi dariya sosai tana girgiza kai, “To bari in gaya miki sirri. Kinsan me yasa Mamah ta mallakesa? Mahaufiyar mu?Saboda kulawa da yake samu a hannunta. To bakiga yadda take kula da shi ba? A lokacin da suke tare Yana son a bashi mahimmanci, a girmamashi.”

Ta ɗan taɓe baki tana ƙare min kallo. “Small Mom, please call him kice we are about to board kin ji?”

Na yi shiru kamar wadda aka tsare da tambaya. Zuciyata na tsalle-tsalle, ban san me yasa nake jin nauyin kiransa ba.

“Okay,” kawai na faɗa a hankali.

Tana dariya tana saka min lambar a wayata, amma sai na tsaya da mamaki.

Na ga sunan da ya fito a sama “Zee’ameerah ”

Na ɗago kaina a hankali, “Nawal, ni fa ban saka sunan nan ba.”

Ta yi murmushi ta jingina da kujerar jirgin da muke tsaye a gaban layin shiga. “Ai Daddy ne yayi saving haka. Na gaya miki wallahi ki iya soyayya. Kin ga kuwa, ya saka miki sunan da babu wata a duniya da yake da shi Zee’ameerah!”

Ta matsa kusa kinsan me sunan yake nufi? Nakada mata kai nace a’a.

“ma’anarsa daga harshen Larabci ‘tauraruwar zuciya, wato “star of the soul. Ƙin gane ko? “Oya call him.”

Na ɗan jinkirta, zuciyata na bugawa kamar ana kada ganguna. Na latsa kiran, amma bai ɗaga ba. Sai kawai daga baya na ga ya kira ni. “Ki ce masa hello my soul..,” Nawal ta raɗa cikin kunne na.

Na runtse ido cikin kunya, sannan cikin muryar da ba ni da ƙarfin fita, nace“Yanzu zamu tashi.” Shiru. Sai kuma na ji muryarsa ta fito cikin sautin waya, mai sanyi amma da wani nauyi da natsuwa

“Okay…” Sai kuma ya ɗan yi shiru na sakanni, kamar yana nazari.

Daga ƙarshe yace cikin wata murya da ta tsaya a zuciyata “Then clean that thing you put on your lip.” Na ɗan ji gabana ya faɗi. “Is just lipgloss fa…” Ya ɗan yi ajiyar zuciya, sannan yace “Yes. Ki goge. Ibada zaki, ba kwalliya ba. You hear me right?” Na yi shiru. “Yes,” kawai na ce da murya ƙasa.

Sai kawai na ji wayar ta katse.

Nawal ta juya tana hararata, “Small Mom, what is this now? Kawai haka? Ba love you, ba bye gaskiya shikenan tunda ni baki daukeni a matsayin sister ba bazan ma zauna nan ba.?” Na yi shiru, ba don ban da magana ba, sai don ban san me zan ce ba.

Hankalina ya tashi.. Ta fara kumbure fuska kamar yarinya da aka ɗauke wa abinci.

“Wato ta tura masa hotona kenan,” na faɗa a raina ina jin haushi.

Ban sake ce mata komai ba har muka sami kujerunmu muka zauna.

A cikin jirgin Na jingina da kujerar window, na kalli fitilun waje suna haskawa. Wani irin sanyi ya lullube ni. Muryar Asad tana sake dawo min a cikin kai “Then clean that thing you put on your lip…”

Nana hadiza

09030569336

[09/11, 8:11 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA TAMANIN DA UKU

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Sai na ɗan taba lebena, har yanzu yana ɗan ɗauke da ɗan ɗanɗanon lipgloss ɗin. Na ɗan murmusa cikin kaina. Wani lokacin, daƙilewa daga miji ko saurayi ba ƙiyayya bace kulawa ce. Na juyo, Nawal ta ɗan duƙar da kai tana murza wayarta. Ta saka earpiece tana ta murmushi. Na kalle ta, “Kin turamasa hotonmu ne?” Ta ɗago kai, tana dariya ta ce, “Of course! Ai ya kamata yaga yadda muka gyara masa amaryarsa.” Na ɗan girgiza kai, “Wato bakyajin kunya ke kuwa?.”

Ta ɗan murmusa , “Eh mana, kinsan shaquwar mu da dady kuwa? .” Sai ta ɗan leƙo ta ce cikin raha, “To ai ke kika fiye jin nauyin soyayya. Daddy ba zai ci zarafinki ba. Sai dai ya ɗan fasa zuciyarki da kalma.”

Na ɗan murmusa cikin gajiya.

Sai na ce, “Kin san me? Soyayya ba wasa bace Nawal.” Ta ɗan daga gira. “Toh, amma so kuma ba nadama bace.” Na yi shiru. A zuciyata kalamanta suna yawo, suna haɗuwa da tunanin Asad.Jirgin ya fara motsi,Na jingina da kujerar, ina kallon sama. A zuciyata tambaya ɗaya ce “Shin me yasa nake jin wani iri a cikin raina?”

Na buɗe ido ina kallon Nawal.

Ba kowace ƙasa bace take da iskar da ke sanyaya zuciya, amma Madina tana da irin wadda idan ta shafi ranki, sai zuciyarka ta natsu.”

Babban filin jirgin sama na Madina Al-Munawwarah ya cika da haske da kyan tsari. Fitilun ƙasa suna haskakawa kamar taurari, iska tana ɗauke da ɗan ƙamshin itatuwan mint da turaren da ake sakawa a cikin injinan sanyaya iska. Jirgin mu ya tsaya cikin nutsuwa, na lumshe ido na ji wata nutsuwa ta ratsa ni irin wadda ba ta zuwa da hutawa, sai da imanin cewa kin isa ƙasar Annabi (SAW). Da muka fito daga jirgi, na ji kamar duniya ta sauya. Kowa cikin sutura mai tsafta da farin kaya, wasu suna tafe da tasbihi, wasu kuma cikin murmushi da hawaye na godiya. Mun tsaya aka mana checking a cikin filin jirgin komai tsari, komai shiru.Wani yaro mai kyau da uniform mai rubutun “Al-Najm Concierge Service” ya zo da trolley, yana taimaka mana da kayanmu.

Ina juyawa, sai na hango wata luxury car ta tsaya a gabanmu. Black Lexus LX600, sabuwa, Wani direba mai tsayi, sanye da farin “thobe” da rawani mai tsabta, ya fito cikin ladabi yana cewa “Welcome to Madina, Ya Sayyidati Ramlah.”

Na yi mamaki har sun san sunana? Nakalli hajja ya Sister Amina Nawal ta kalle ni tana dariya, “Daddy kenan, ai ya kira hotel ɗin ya ce su kula da mu kamar sarauniyoyi.”

Na ɗan murmusa, zuciyata tana ɗan dokawa da jin wannan kalmar “sarauniya.” Sai muka shiga motar. Cikin motar kamarfita ta aljanna

ƙamshi, sanyi, da karatun kur’ani mai laushi yana fita a hankali daga speaker. Nawal ta ɗora kanta a jikin gilashin motar, tana murmushi, “Amaryar dady ko missing din dady kikeyi yanzu?” Na juyo ina kalleta hajja ma ina gani tayi murmushi nikam kunya tacika ni ta ko’ina. Gidaje da hasken fitilu suna tafe kamar taurari. Madina… waje ne da yake da salo na daban. Ko iska dabantake.

Mun isa gaban wani babban gini mai tsayi Al-Qamar Royal Suites hotel mai yawan haske da ƙamshin turaren oudh. An rubuta sunansa a bakin kofar “Al-Qamar Royal Suites Madina Al-Munawwarah.”Kamar aljanna a duniya. An buɗe ƙofa aka tarbe mu da murmushi da girmamawa “Assalamu Alaikum, welcome to Al-Qamar Royal Suites. Your rooms are ready.” Nawal ta kalle ni da murmushi, “Kin ga kuwa, daman nace wannan hotel din mukeso gamu ga masallaci.”

Mun shiga cikin lobby, bene ne mai launin silver. A gefe na ga masu aiki suna rarraba Arabic coffee da dates cikin kofi na gilashi.

Na karɓa a ladabce, na ɗan sha, sai na ji wani sanyi ya ratsa har cikin ƙirjina.

Kamar ana wanke damuwa da su.

Mun ɗaga zuwa “Royal Floor”, bene na 15, inda executive suites suke. Dakinmu ya buɗe cikin haske farin labule, gadon guda 4 sai palour, madubi mai tsayi, da window da ke kallon Haramin Madina.Na tsaya a gaban window, na kalli fitilun masallacin Annabi (SAW) suna haskawa cikin dare. Na ɗan ji zuciyata ta motsa, na furta a hankali “Ya Allah, ka karɓi tafiyarmu, ka tsaremu daga dukkan fitina.” Nawal ta fito daga ɗaki tana riƙe da wayarta.

“Small Mom, Please text him.”Na ɗan yi murmushi. Amma a zuciyata akwai wani irin abu nakeji sai nake gani kamar yana kallon na kamar yadda yayi jiya.’ Na juya daga window, na shige cikin dakin. Na zauna a gefen gado, na ɗauki wayata. Na buɗe contact list, na duba sunan nan da yake lumshewa da emoji Zee’ameerah Sai zuciyata ta buga.

Na ɗan murmusa cikin jin nauyi ko da yake ba tare muke ba, amma kalmarsa a yau, har yanzu tana cikin kunnena“Clean that thing you put on your lip…” Na dafe ƙirjina, na lumshe ido, na ji sanyi mai kama da natsuwa da rauni ya ratsa ni. Hajja ta kalli agogon bango sannan ta kalle mu. “Ku tashi ku yi wanka, mu ci abinci, mu shiga masallaci. Ko da yake da saura, yanzu ƙarfe takwas na safe.”

Muryarta da ta cika da kulawa tmamaye ɗakin. Nawal ta juya a kan gado tana cewa cikin kasala, “Hajja ni bari kawai nayi bacci tunda da sauran lokaci maje anjima ko?.”

Na kalle ta ina murmushi. Ni kuwa, ko da jikina bai gama hutawa ba, amma zuciyata kawai so takeyi ta ganta a masallacin Annabi (SAW).

Amina ma ta rufe idanuwa, tana cewa da dariya, “Small mom kema ki kwanta ki huta please, zuwa 1 sai muje ko.” Hajja ta saki numfashi tana dariya, “To,Nima dai da alama baccin nakeji.” Na shige banɗaki, ruwa mai dumi yafara sauka a jikina. Na lumshe ido ina jin yadda ruwan yake ratsa ƙasusuwa. Wi yau nice cikin waƴannan attajiran da djniya takeji dasu Yaa Allah ka tabbatar mun da farin ciki acikinsu karkasa su juyamun baya daga baya kamar yadda momy tayimun.

Bayan na gama, na saka light gown sai ƙamshin turaren oudh ya lullube ni.

Nawal har yanzu kwance take, ta ninke filo ta rungume. Na kalle ta, na yi murmushi, “Ita da duniya kamar abokan wasa suke rayuwar su babu damuwa ko kuncin wani ko tunanin wani nutsuwarsu har mamaki take bani.”

Na fita zuwa falo. Hajja ta kwanta a kujera, hannunta na riƙe da tasbihi. Idanuwanta na lumshe, amma leɓenta na motsi da ambaton Allah. Sai zuciyata ta ji natsuwa irin natsuwar da koda kin yi shiru, tana ratsa ranki baiwar Allahn nan akwai ibada yadda takeyi rayuwa dasu nawal daban da yadda takeyi agidan sarki abun da mamaki ko da yake nima uwar amarya ta sanar dani hajja batason mulki ko kadan.

Na ɗauki wayata a gefe, sai na ji tana ringing.

Idona ya kai ga sunan da ke haskawa a screen ɗin Zee’ameerah Na kalla ko kafin numfashi ya fito daidai, na danna “Answer.”

“Assalamu alaikum,” na furta cikin kasalalliyar murya. Muryarsa ta fito daga dayan ɓangaren, mai sanyi, amma cike da mamaki da kulawa.

“Zee’ameerah, bazaki kwanta ki huta ba?” Na yi shiru kadan, sai na ce cikin natsuwa, “Ai na huta. Nayi wanka yanzu.” Sai ya yi dariya a hankali, irin wacce ta fito daga ƙasan zuciya.

“To, tunda ke bakya missing dina to ni inayi , then have a sleep, kin ji? Ki huta,. Kin gaji sosai, kuma ina son ranki ya samu natsuwa.” Na yi shiru na ɗan lumshe ido, muryarsa tana yi min kamar iska mai taushi. Na ce da murya ƙasa kasa, “Bazab iya bacci yanzu ba. Zuciyata tana so ta fita inje masallacin Annabi.” Shiru ya biyo bayan kalmar. Sai na ji kamar yana murmushi daga can.

“ mashaa Allah naji dadin kalmar nan kuma ni As’ad nayi miki alkawari duk shekara zakije aduk sanda kikeso har ki kai wasu. Yanzu ki kwanta dai kisamu nutsuwa kinji

Amma ki tuna… idan kika shiga, kada ki manta da ni a cikin addu’arki.” Na ɗan saki numfashi, “Ba zan manta ba, insha Allah.”

“Good girl,” ya faɗa cikin natsuwa.

Sai ya ƙara da cewa, “Zee’ameerah… kina jin daɗin Madina?” Na amsa a hankali, “Ina jin daɗi fiye da yadda zan iya faɗi.” Ya yi shiru, sannan ya ce cikin murya mai raɗaɗi, “Madina tana da nutsuwa” Na lumshe ido, na ji zuciyata ta buga. “Ka huta,” kawai na faɗa cikin jin kunya. “Ki kula da kanki,” ya ce kafin ya katse wayar. Na ajiye wayar a gefe, zuciyata tana rawa da wani abu mai laushi. Bayan mun farka...

Na ji ana buga ƙofa a hankali. Nawal ta miƙe tana goge idonta. “Small Mom, kin ji? Mu tashi mu shirya.” Na tashi cikin natsuwa, muka yi brush, muka shirya cikin fararen abayoyi iri ɗaya. Hajja ta shirya tana sanye da abaya mai launin toka, fuskarta cike da annuri.

Sai ta ce, “Ku tashi, mu tafi, kafin rana ta yi yawa.”

Nana hadiza

09030569336

[10/11, 10:31 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA TAMANIN DA HUDU

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Mun fito daga hotel ɗin Al-Qamar Royal Suites, iska mai daɗin sanyi tana kadawa.

Madina cikin safe kamar aljanna ce iska mai ɗauke da ƙamshin itacen miski, fitilun titi suna ta kyalli, kuma mutane suna tafiya cikin ladabi. Mun isa kofar Masallacin Annabi (SAW). Wani sauti mai laushi na adhan yana fita daga masallacin, yana haɗuwa da kukan tsuntsaye da suke shawagi a saman rufin Harami. Nawal ta ɗan kama hannuna.

“Small Mom, kin ji daɗin iskar nan?”

Na murmusa, “sosai.” Mun shiga cikin masallacin cikin nutsuwa. Na tuna kalmar Asad “Kada ki manta da ni a cikin addu’arki.”

Na ce cikin raina, “Ya Allah, ka shiryar da shi, ka bashi natsuwa kamar yadda nake ji yau ka kuma karemun shi daga dukkan sharri.”

A gefe, Nawal tana karanta Suratul Rahman cikin murya mai laushi, “Fabi ayyi alaa’i rabbikuma tukadhiban…”Sai na ji zuciyata ta cika da shauƙi da salama. Da safe bayan mun gama sallar Asuba, muka ci ƙaramin abin kari. Hajja ta ce, “Yau sai muje Rawdah, in Allah ya yarda.” Cikin raina sai na ji kamar wani farin ciki ya motsa. Rawdah! Wuri ne da nake ta mafarkin ziyarta tun muna gida. Nawal ta rungume filo tana turo baki, “Ni kudin papa yayi kadan hajjaji.” Hajja ta ce, “kinga nawal kina godewa Allah ina lefen kudin da yabayar.” Sai ta ce min, small mom kiyiwa dady magana ni inason yasiyamana mota bazanyi masa yanzu ba.” “ Ai yabani kudi karki damu zai ishemu.” Murmushi tayi kawai tana kallona. Bayan mungama muka shirya cikin red egypt jalbab Amina ma ta shirya cikin farin hijabi. Muka fito duka hudu cikin farin ciki. Wato su basa magana sai da dalili bakamar mu ba ayita zance amma tunda nafara zama dasu na fahimci kowacce magana tasu da dalili sukeyi. Hajja, ni, Nawal, da Amina. Kowacce da tasbihi a hannu, fuskoki cike da annuri.

Mun fita daga Al-Qamar Royal Suites da misalin ƙarfe tara na safe. Iskar Madina tana da wani irin daɗi “Bab Al-Salam side, ladies’ Rawdah area.” Na lumshe ido ina jin sunan “Bab Al-Salam” ya tsaya a zuciyata Ko da kalma ce, amma tana da salama a ciki.

Mun isa harabar masallacin Annabi (SAW), wuri mai yalwa da farin dutse da hasken rana mai laushi. Fitilun Ottoman suna walƙiya, tsuntsaye suna shawagi a saman domes masu buɗewa da rufewa. Mun saka takalma a jaka, muka shiga cikin sashin mata.

A ƙofar Bab Al-Rahmah, wasu ‘yan uwata mata daga ƙasashe daban-daban suna jiran lokacin shiga Rawdah. Anan aka rarraba mu kashi-kashi Arabiyyah, Turkiyyah, Africiyyah, da Indonesia. Hajja ta kalle ni ta ce, “Ku bi ni, mu tsaya da ‘Africiyyah.”

Mun zauna a wani ɓangare mai labule fari, ƙasa cike da kafet mai santsi, ƙamshin turaren bakhoor yana fitowa daga wutar mabkhara da ke gefe. Kowa cikin shiru yake, wasu suna karatun Al-Qur’ani, wasu suna addu’a.

Na kalli hasken da yake shiga daga Rawdah Dome, ya faɗa saman kafe Wata mata mai daraja ta zo da murya mai nutsuwa tana cewa “Ladies, now Rawdah is open, please move slowly, no rush, no noise, just du’a.”

Na ji jikina ya amsa kafin zuciyata.

Mun tashi cikin ladabi, muka fara tafiya cikin layi, ƙamshin miski da oudh yana biyowa iska.

Na rika jin kalmar “Subhanallah… Alhamdulillah… Astaghfirullah…” daga ko’ina.

Sai muka shiga waje mai ƙasa mai launin kore mai haske koren kafet ɗin Rawdah! Wannan shine Rawdah Al Jannah. Na tsaya, hawaye suka cika idona. Zuciyata ta ce, “Ni Ramlah, ni wadda na zo daga nesa, yau ina tsaye a cikin Aljanna a duniya.” Na durƙusa a ƙasa, na ɗaga hannuwa cikin natsuwa “Ya Allah, Ka karɓi ibadata, Ka yafemin, Ka gyara rayuwata. Ka shiryar da wanda zuciyata ke so.” Na ji muryar Hajja tana karanta salatin Annabi (SAW) “Allahumma salli ala Muhammadin wa ala ali Muhammadin, kama sallaita ala Ibrahima…” Na furta tare da ita cikin kuka.

A gefe, Nawal ta rufe fuska da hijab, hawayenta na zuba. Amina kuma tana karatun Suratul Yasin, Wani lokacin ana barin mutum da addu’ar da zuciyarsa ta fi so.

Ni kuma kalmomi ɗaya ne kawai suke maimaituwa a raina “Ya Allah, Ka bani damar da zan gyara son da ke tsakanin mu, Ka bari ya zama halal, Ka kare mu daga makiya.”

Wata mata daga Indonesia ta kama hannuna, ta ce cikin murya mai rauni,

“Pray for me, sister…”

Na ce mata, “And you, pray for me too.”

Suka murmusa, muka haɗa hannuwa muka ce, “Ameen.”

A lokacin da nake fita daga Rawdah, na ji wani sanyi mai zurfi ya mamaye ni.

Kamar zuciyata ta bari wani nauyi a can ƙasa.

Na kalli saman rufin masallaci, na ga hasken fitilu masu launin gold. Da muka fita daga sashen mata, iska mai laushi ta bugi fuskata.

Hajja ta kalle mu tana murmushi.

“Ku ga yadda Allah yake kawo salama a zuciya idan an ziyarci Annabi?” Na gyaɗa kai cikin hawaye.”

Haka muka wuni a masallacin Annabi (SAW), cikin nutsuwa da ibada. Na ji kamar rana ta yi gajiyar haske, amma zuciyata bata gaji da ambaton Allah ba. Muna zaune a cikin sashen mata, kowacce cikin karatun Qur’ani, sai iska mai ɗauke da ƙamshin bakhoor ke shigowa ta cikin window ɗin masallaci tana lullube mu da salama. Da magariba ta gabato, muka fito cikin nutsuwa.mukayi alwalah sannan muka koma mukayi sallah bayan sallar isha’i muka fito. Fitilun masallaci suna haskawa. Mun koma Al-Qamar Royal Suites, muka shige sashen cin abinci. Abincin dare chicken mandi, dates pudding, da fresh laban sai salad sai tea sai fruits. Muka zauna a teburi, kowa da kofin shayi a gabansa.

Hajja ta ɗan gyara zama, ta dubeni da murmushi. “Ramlah,” ta faɗa cikin muryar kulawa, “ Gobe zamu shiga makkah ?” Na ɗago kai, “Naam, Hajja” Ta ce cikin natsuwa, “Abbanki da Momy suna Makkah. Insha Allah, zamu taddasu can kafin mu koma gida.” Na ɗan ware ido cikin mamaki, “Hajja, da gaske?” Ta yi dariya. “Eh munyi waya dasu yau da safe.”

Na ji zuciyata tayi sanyi Amma momy bata gayamun ba ko danayi mata sallama. A karo na farko tun tafiyarmu, na ji wani irin farin ciki ya cika ni. Sai kawai Nawal ta juyo tana murmushi da mugun salo. “To Small Mom, to yanzu kirashi mana. Ku gaisa naga ke bakisan hakkin miji ba kina kallo my love har video call muka gama ke kuwa kin barmun dady haka..” Na ɗan ƙura mata ido, “Yaya nawal menene haka kike faɗa..” Ta harare ni cikin wasa, “Haba! Ni dai ban san soyayya irin taki ba. Daddy dai ba mutum bane da zai gaji da jin muryarki bayan naga tsananin soyayyarki acikin idonsa.” Na yi dariya a hankali, amma ban kira ba. A zahiri, na so, amma wani abu a zuciyata yana hanani wata kunya ce, ko tsoron da kalmarsa ke jawo min.

Sai dai ban san cewa Nawal tana da “shirin ta” ba. Bayan munsaka armless gown zamu kwanta yaya aminatu tanata waya da yaranta a palour hajja ma tana cikin nasu dakin naji kamar da mai martaba suke waya na dan zauna bakin bed Ko motsi na danyi, ko na ɗan gyara rigata, sai na ji tana ɗan murmushi tana danna wayarta Ashe tana turawa Asad hotona da motsina, kamar wata yar jarida. Na saki jiki a gado cikin gajiya. Nawal tana gefe tana danna waya tana murmushi. Na dubeta, “Me kike dariya haka?” Ta ce, “Nothing, Small Mom, kawai dariya.” Kafin ta ba ni amsa, wayata ta fara ringing. Idona ya sauka a screen ɗin Zee’ameerah calling…

Na ji zuciyata ta tsaya na ɗan lokaci.

A hankali na ɗaga, “Assalamu alaikum.”

Muryarsa ta fito daga wayar cikin sanyi “Wa alaikumus salam, Zee’ameerah. Me yasa baki kirani ba tun safe?” Na yi shiru kadan, “Na gaji ne. Mun fito daga Rawdah muka dawo da yamma.” Sai na ji yana dariya a hankali.

“Mhm, to me yasa bakiyimun text ba? Kinyi kyau sosaii rigar tayi miki kyau sai naji dama kina kusa dani..?” Na yi mamaki, zuciyata ta buga. “Wace riga?” Muryarsa ta sauya zuwa ta lallausha “Wacce Nawal ta turamin hotonta… armless, launin ruwan hoda.”

Na rufe baki da tafin hannu, na kalli Nawal da ido Ta rufe fuska tana dariya. “Sorry Small Mom, wallahi so kawai nake ya ganki.”

Na ji Asad yana murmushi daga dayan ɓangaren. “Karki ɗaure fuska haka, Zee’ameerah. Kema kin san wannan rigar... tayi miki kyau.”

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA TAMANIN DA HUDU

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Mun fito daga hotel ɗin Al-Qamar Royal Suites, iska mai daɗin sanyi tana kadawa.

Madina cikin safe kamar aljanna ce iska mai ɗauke da ƙamshin itacen miski, fitilun titi suna ta kyalli, kuma mutane suna tafiya cikin ladabi. Mun isa kofar Masallacin Annabi (SAW). Wani sauti mai laushi na adhan yana fita daga masallacin, yana haɗuwa da kukan tsuntsaye da suke shawagi a saman rufin Harami. Nawal ta ɗan kama hannuna.

“Small Mom, kin ji daɗin iskar nan?”

Na murmusa, “sosai.” Mun shiga cikin masallacin cikin nutsuwa. Na tuna kalmar Asad “Kada ki manta da ni a cikin addu’arki.”

Na ce cikin raina, “Ya Allah, ka shiryar da shi, ka bashi natsuwa kamar yadda nake ji yau ka kuma karemun shi daga dukkan sharri.”

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull