Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 32

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 32

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 32: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 32. A gefe, Nawal tana karanta Suratul Rahman cikin murya mai laushi,…

4,467 words

A gefe, Nawal tana karanta Suratul Rahman cikin murya mai laushi, “Fabi ayyi alaa’i rabbikuma tukadhiban…”Sai na ji zuciyata ta cika da shauƙi da salama. Da safe bayan mun gama sallar Asuba, muka ci ƙaramin abin kari. Hajja ta ce, “Yau sai muje Rawdah, in Allah ya yarda.” Cikin raina sai na ji kamar wani farin ciki ya motsa. Rawdah! Wuri ne da nake ta mafarkin ziyarta tun muna gida. Nawal ta rungume filo tana turo baki, “Ni kudin papa yayi kadan hajjaji.” Hajja ta ce, “kinga nawal kina godewa Allah ina lefen kudin da yabayar.” Sai ta ce min, small mom kiyiwa dady magana ni inason yasiyamana mota bazanyi masa yanzu ba.” “ Ai yabani kudi karki damu zai ishemu.” Murmushi tayi kawai tana kallona. Bayan mungama muka shirya cikin red egypt jalbab Amina ma ta shirya cikin farin hijabi. Muka fito duka hudu cikin farin ciki. Wato su basa magana sai da dalili bakamar mu ba ayita zance amma tunda nafara zama dasu na fahimci kowacce magana tasu da dalili sukeyi. Hajja, ni, Nawal, da Amina. Kowacce da tasbihi a hannu, fuskoki cike da annuri.

Mun fita daga Al-Qamar Royal Suites da misalin ƙarfe tara na safe. Iskar Madina tana da wani irin daɗi “Bab Al-Salam side, ladies’ Rawdah area.” Na lumshe ido ina jin sunan “Bab Al-Salam” ya tsaya a zuciyata Ko da kalma ce, amma tana da salama a ciki.

Mun isa harabar masallacin Annabi (SAW), wuri mai yalwa da farin dutse da hasken rana mai laushi. Fitilun Ottoman suna walƙiya, tsuntsaye suna shawagi a saman domes masu buɗewa da rufewa. Mun saka takalma a jaka, muka shiga cikin sashin mata.

A ƙofar Bab Al-Rahmah, wasu ‘yan uwata mata daga ƙasashe daban-daban suna jiran lokacin shiga Rawdah. Anan aka rarraba mu kashi-kashi Arabiyyah, Turkiyyah, Africiyyah, da Indonesia. Hajja ta kalle ni ta ce, “Ku bi ni, mu tsaya da ‘Africiyyah.”

Mun zauna a wani ɓangare mai labule fari, ƙasa cike da kafet mai santsi, ƙamshin turaren bakhoor yana fitowa daga wutar mabkhara da ke gefe. Kowa cikin shiru yake, wasu suna karatun Al-Qur’ani, wasu suna addu’a.

Na kalli hasken da yake shiga daga Rawdah Dome, ya faɗa saman kafe Wata mata mai daraja ta zo da murya mai nutsuwa tana cewa “Ladies, now Rawdah is open, please move slowly, no rush, no noise, just du’a.”

Na ji jikina ya amsa kafin zuciyata.

Mun tashi cikin ladabi, muka fara tafiya cikin layi, ƙamshin miski da oudh yana biyowa iska.

Na rika jin kalmar “Subhanallah… Alhamdulillah… Astaghfirullah…” daga ko’ina.

Sai muka shiga waje mai ƙasa mai launin kore mai haske koren kafet ɗin Rawdah! Wannan shine Rawdah Al Jannah. Na tsaya, hawaye suka cika idona. Zuciyata ta ce, “Ni Ramlah, ni wadda na zo daga nesa, yau ina tsaye a cikin Aljanna a duniya.” Na durƙusa a ƙasa, na ɗaga hannuwa cikin natsuwa “Ya Allah, Ka karɓi ibadata, Ka yafemin, Ka gyara rayuwata. Ka shiryar da wanda zuciyata ke so.” Na ji muryar Hajja tana karanta salatin Annabi (SAW) “Allahumma salli ala Muhammadin wa ala ali Muhammadin, kama sallaita ala Ibrahima…” Na furta tare da ita cikin kuka.

A gefe, Nawal ta rufe fuska da hijab, hawayenta na zuba. Amina kuma tana karatun Suratul Yasin, Wani lokacin ana barin mutum da addu’ar da zuciyarsa ta fi so.

Ni kuma kalmomi ɗaya ne kawai suke maimaituwa a raina “Ya Allah, Ka bani damar da zan gyara son da ke tsakanin mu, Ka bari ya zama halal, Ka kare mu daga makiya.”

Wata mata daga Indonesia ta kama hannuna, ta ce cikin murya mai rauni,

“Pray for me, sister…”

Na ce mata, “And you, pray for me too.”

Suka murmusa, muka haɗa hannuwa muka ce, “Ameen.”

A lokacin da nake fita daga Rawdah, na ji wani sanyi mai zurfi ya mamaye ni.

Kamar zuciyata ta bari wani nauyi a can ƙasa.

Na kalli saman rufin masallaci, na ga hasken fitilu masu launin gold. Da muka fita daga sashen mata, iska mai laushi ta bugi fuskata.

Hajja ta kalle mu tana murmushi.

“Ku ga yadda Allah yake kawo salama a zuciya idan an ziyarci Annabi?” Na gyaɗa kai cikin hawaye.”

Haka muka wuni a masallacin Annabi (SAW), cikin nutsuwa da ibada. Na ji kamar rana ta yi gajiyar haske, amma zuciyata bata gaji da ambaton Allah ba. Muna zaune a cikin sashen mata, kowacce cikin karatun Qur’ani, sai iska mai ɗauke da ƙamshin bakhoor ke shigowa ta cikin window ɗin masallaci tana lullube mu da salama. Da magariba ta gabato, muka fito cikin nutsuwa.mukayi alwalah sannan muka koma mukayi sallah bayan sallar isha’i muka fito. Fitilun masallaci suna haskawa. Mun koma Al-Qamar Royal Suites, muka shige sashen cin abinci. Abincin dare chicken mandi, dates pudding, da fresh laban sai salad sai tea sai fruits. Muka zauna a teburi, kowa da kofin shayi a gabansa.

Hajja ta ɗan gyara zama, ta dubeni da murmushi. “Ramlah,” ta faɗa cikin muryar kulawa, “ Gobe zamu shiga makkah ?” Na ɗago kai, “Naam, Hajja” Ta ce cikin natsuwa, “Abbanki da Momy suna Makkah. Insha Allah, zamu taddasu can kafin mu koma gida.” Na ɗan ware ido cikin mamaki, “Hajja, da gaske?” Ta yi dariya. “Eh munyi waya dasu yau da safe.”

Na ji zuciyata tayi sanyi Amma momy bata gayamun ba ko danayi mata sallama. A karo na farko tun tafiyarmu, na ji wani irin farin ciki ya cika ni. Sai kawai Nawal ta juyo tana murmushi da mugun salo. “To Small Mom, to yanzu kirashi mana. Ku gaisa naga ke bakisan hakkin miji ba kina kallo my love har video call muka gama ke kuwa kin barmun dady haka..” Na ɗan ƙura mata ido, “Yaya nawal menene haka kike faɗa..” Ta harare ni cikin wasa, “Haba! Ni dai ban san soyayya irin taki ba. Daddy dai ba mutum bane da zai gaji da jin muryarki bayan naga tsananin soyayyarki acikin idonsa.” Na yi dariya a hankali, amma ban kira ba. A zahiri, na so, amma wani abu a zuciyata yana hanani wata kunya ce, ko tsoron da kalmarsa ke jawo min.

Sai dai ban san cewa Nawal tana da “shirin ta” ba. Bayan munsaka armless gown zamu kwanta yaya aminatu tanata waya da yaranta a palour hajja ma tana cikin nasu dakin naji kamar da mai martaba suke waya na dan zauna bakin bed Ko motsi na danyi, ko na ɗan gyara rigata, sai na ji tana ɗan murmushi tana danna wayarta Ashe tana turawa Asad hotona da motsina, kamar wata yar jarida. Na saki jiki a gado cikin gajiya. Nawal tana gefe tana danna waya tana murmushi. Na dubeta, “Me kike dariya haka?” Ta ce, “Nothing, Small Mom, kawai dariya.” Kafin ta ba ni amsa, wayata ta fara ringing. Idona ya sauka a screen ɗin Zee’ameerah calling…

Na ji zuciyata ta tsaya na ɗan lokaci.

A hankali na ɗaga, “Assalamu alaikum.”

Muryarsa ta fito daga wayar cikin sanyi “Wa alaikumus salam, Zee’ameerah. Me yasa baki kirani ba tun safe?” Na yi shiru kadan, “Na gaji ne. Mun fito daga Rawdah muka dawo da yamma.” Sai na ji yana dariya a hankali.

“Mhm, to me yasa bakiyimun text ba? Kinyi kyau sosaii rigar tayi miki kyau sai naji dama kina kusa dani..?” Na yi mamaki, zuciyata ta buga. “Wace riga?” Muryarsa ta sauya zuwa ta lallausha “Wacce Nawal ta turamin hotonta… armless, launin ruwan hoda.”

Na rufe baki da tafin hannu, na kalli Nawal da ido Ta rufe fuska tana dariya. “Sorry Small Mom, wallahi so kawai nake ya ganki.”

Na ji Asad yana murmushi daga dayan ɓangaren. “Karki ɗaure fuska haka, Zee’ameerah. Kema kin san wannan rigar... tayi miki kyau.”

Nana hadiza

09030569336

[11/11, 11:44 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA TAMANIN DA BIYAR

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Na kasa magana. Zuciyata ta tsaya tsakanin kunya da jin daɗi. Sai kawai na ce cikin murya ƙasa kasa, “Dan Allah ka daina irin wannan magana. Yaya jikinka kuwa?” Ya yi shiru. Sai na ji kamar yana murmushi cikin natsuwa.

“Na ji saukj, amma kin san menene maganina yanzu?” Na yi shiru. Ya ce, “Ke nakeso Ni yanzu.” kunya takama daman manya suna waƴannan abubuwan? Na juya gefe, zuciyata na rawa. “Don Allah ka huta. Ka sha magani, ka kwanta.” Sai na ji muryarsa ta lafa sosai, kamar yana magana da zuciyata kai tsaye

“Idan har zan samu ki cikin mafarki yau, to wallahi zan fi samun lafiya da duk wani magani.” Na kasa cewa komai. Sai kawai na ji idanuna suna cike da hawaye marasa suna.

“Ka huta, don Allah,” na furta cikin murya mai rauni. “Korata kikeyi?” ya faɗa cikin sanyi.

Na yi murmushi da hawaye, “ Aa .”

Sai kawai na ji yana cewa, “Good girl, my lah lah…”Muryarsa ta faɗi a hankali kamar iska mai taushi, sannan wayar ta katse.

Na jingina da filo, ina tunanin wannan wani suna ne lah -lah wato last name dina ya dauka yayi amfani dashi zuciyata tana bugawa kamar ana kirga lokuta. Tsigar jikina na amsawa sosai Nawal ta leƙo ta ce, “Small Mom, kin ji dadi ko ai bama ki fara soyayya ba wallahi nasan akwai drama gaba..?”

Na jefa mata filo, “Ke kin cika ɓata min rai.” Tayi dariya sosai, “To amma ai yanzu kima kinji dadi small mom soyayya akwai dadi sosai da sosai uhmm bari dai kiga.. Na kalli gilashin taga inda fitilun Madina suke haskawa kamar taurari.

Washegari tun da asuba muka shirya.

Iskar Madina ta yi sanyi, ta lullube birnin cikin natsuwa. Hajja ce ta fara fitowa daga ɗaki tana cewa, “Ku shirya, yau zamuyi niyyar Umrah, mu bar Madina inshaa Allahu.”

Ni da Nawal muka rufe jakunkunanmu, muka fito cikin farin kaya hijabi mai launin fari yayi mana kyau sosai sai hotuna sukeyi nima dai naga idan ina baya zasu daukeni yar kauye sai nadinga yimana hotunan, sai karamar jaka a gefe. Amina ma ta shirya, fuskarta cike da annuri. Daman ita akwai fara’a Muka zauna a falo, muna jiran motar da zata kai mu filin jirgin ƙasa na Haramain High-Speed Train Station. Cikin mintuna kaɗan wata mota mai launin baki, Toyota Alphard Executive Lounge, ta tsaya a ƙofar Al-Qamar Royal Suites.

Direban ya fito da murmushi, yana cewa, “To Makkah, insha Allah.” Mun shiga cikin motar cikin natsuwa. Kamar yadda muka saba, Nawal tana ta hira, Hajja tana karatun Suratul Kahf, Amina tana jan tasbihi, ni kuma zuciyata tana tsakanin farin ciki da wani irin yanayi na tunani. Da muka fita daga cikin Madina, sai iska ta sauya ta koma busasshiya amma mai ɗan ɗumi. Titin Madina Makkah yana da kyau, gefensa cike da duwatsu masu launin ruwan kasa, wasu kamar an nika su da gawayi.

Rana na haskawa a sararin sama, haskenta ya ɗauki duwatsun. Na jingina da kujerar mota, na lumshe ido. A cikin zuciyata, addu’a ɗaya ce “Ya Allah, Ka karɓi tafiyarmu, Ka sa mu isa lafiya, Ka karɓi Umrah ɗinmu.”

Lokaci zuwa lokaci, Hajja tana faɗin muci aabunda ake kawo mana tabbas akwaita xa kulawa shiyasa su nawal suke sonta.

Nawal ta ce, “Hajja, kin san Daddy ya ce yanzu suna marocco ?.”

Hajja ta murmusa, “Umar yagayamun ai wai an duba cctv ankama wanda yazuba masa poison Amma mai martaba yace abar komai a hannunsa.” Nawal tace “To grandpa in banda rashin hankali shi yazata babu cctv a asubutin ne?.” “ Ai da dr khalid ashe suka haɗa baki.” Da hanzari na jiyo ina fadin innalilahi. Dr. Khalid?” Nan.hajja tashiga bamu labari wai ashe kudi yabashi sosai yanzu duk suna rufe a prison. Yaya amina tace “ Amma Waziri bai kyauta ba. Duk mukayi shiru dai da jimami.

Ni kuma na kalli window, na hango wani rubutu da ya wuce “Welcome to Makkah Al-Mukarramah.” Sai zuciyata ta tsaya da bugawa na ɗan lokaci. Wannan ce ƙasar da kowane musulmi yake mafarki ƙasar da Annabi Ibrahim ya tsarkake domin Allah.

Mun tsaya a wani ƙaramin masallaci a bakin titi, Masjid As-Sayl Al-Kabeer wato wurin da ake yin miqat ga masu niyyar Umrah daga Madina. Anan muka tsaya muka fito cikin ladabi.

Wurin cike yake da mutane daga ƙasashe daban-daban wasu daga Asia, wasu daga Africa, wasu kuma Turawa.

Dukkansu cikin farin kaya, da fuskoki masu annuri da natsuwa.

Iskar masallacin tana ɗauke da ƙamshin turare.

Mun shiga masallacin cikin shiru.

Hajja ta ce, “Ku daura niyyar ku, ku yi wanka da sabuwar niyya. Wannan ce farkon tafiyar ibada.” Na shiga bandaki na yi wanka, na fito cikin farin hijabi. A can cikin zuciyata, na ce“Labbayka Allahumma Umrah.” Sai na ji zuciyata ta amsa da wani irin sanyi.

Hawaye suka cika idona ba tare da sanina ba.

Bayan nan babu wani abu da ya rage sai Ka’aba wuri mafi tsarki a doron ƙasa.

Na fito na same su suna jira addu’a.

Hajja ta kalle ni, ta murmusa “kinyi kyau sosai Ramlahtu.” Na ce cikin jin kunya, “Nagode.”Nawal ta ce da dariya, “Dole aturawa masoyi hotonki.” Na jefa mata kallo, “Kin fara ko.” Sai ta yi dariya, tayi gaba.

Yayin da direban ya kunna injin, sai na lumshe ido ina jin zuciyata tana cewa“Labbayka Allahumma Labbayk…”

Bayan sa’o’i da dama a hanya, alamar rana na kusa da faduwa. Da muka karasa cikin birnin Makkah, sai na ji zuciyata ta tsaya na ɗan lokaci. Gidaje masu tsayi suna zagaye da harami, fitilu suna haskawa kamar taurari.

Direban da yake sanye da farar thobe da rawani ya juya yana murmushi.

Ya ce cikin murya mai taushi “الحمد لله، وصلنا مكة المكرمة. إن شاء الله، عمرة مقبولة.”

(Alhamdulillah, wasalna Makkah Al-Mukarramah. In shaa Allah, Umrah maqboolah.) Alhamdulillah, mun isa Makkah. In shaa Allah, Allah Ya karɓi Umrah ɗinku.

Hajja ta murmusa, ta ɗaga hannunta cikin girmamawa ta amsa da harshen Larabci cikin kyakkyawar lafazi “آمين، جزاك الله خيراً يا ولدي.”

(Ameen, Jazakallahu khayran, ya waladi.)

Ameen, Allah ya saka da alheri, ɗana.

Direban ya gyaɗa kai cikin ladabi, yana murmushi. Na ji hawaye suka tsaya a gefen idona na kasa magana, sai murmushi kawai.

Wannan farin ciki ne da baya da kalma.

Mun fara shirin Umrah. Mun tsaya a ɗaki, muka sake gyara sutura cikin farin ihram Hajja da Amina suna tafiya da nutsuwa, Nawal tana ɗaukar hotuna tana dariya. Mun fita cikin nutsuwa, iska mai ɗan ɗumi tana kadawa.

Na ji zuciyata na maimaita Labbayka Allahumma Labbayk, Labbayka la sharika laka Labbayk… Harabar Harami ta cika da mutane daga duk duniya. Kowanne cikin farin kaya, fuskoki suna walƙiya da addu’a.

Mun rika tafiya har muka hango Ka’abah daga nesa baki. Sai na ji gwiwoyina sun yi rauni, zuciyata ta cika da wani irin farin ciki da tsoro lokaci guda. Na ɗago ido, hasken fitilun harami ya bugi bangon Ka’abah, yana haskawa.Hajja ta ce da murya mai sanyi,kuyi addua sosai kada kutsaya hotunan nan kunji

Na ɗaga hannuwana, na furta cikin hawaye “Ya Allah, Ka karɓi ibadata. Ka tsarkake zuciyata daga dukkan son duniya. Ka bani ƙarfin da zan yi soyayya da halal, in guji haram.”

Sai muka fara tawafi, muna zagaye Ka’abah sau bakwai. Iskar harami tana ɗauke da ƙamshin Zam-zam da turaren oudh.

Kowace zagaye kamar ana share wani ɓangare na zunubi daga zuciya.

Nawal ta riƙe hannuna, tana cewa, “Small Mom, kin san kuwa wannan shine wurin da addu’a baya dawowa babu amsa?”

Na murmusa, “Na sani.” na faɗi addu’a da nake so fiye da komai.” Ta tambaye ni da wasa, “Anya kuwa ba soyayyar Daddy kika roka ba?” Na yi dariya cikin kunya, “Ke dai Allah ya shirye ki.” Mun kammala tawafi, muka nufi Maqaam Ibrahim, muka yi raka’a biyu. Sai muka sha Zam-zam, muka yi addu’a da hawaye da murmushi. Daga nan muka fita zuwa Sa’i tsakanin Safa da Marwah. Na kalli titin Sa’i mai sheƙi, fitilun sama suna haskawa. Kowane zagaye kamar tafiyar zuciya ne daga damuwa zuwa natsuwa.

A karshe, lokacin da muka isa Marwah, Hajja ta ɗaga hannu da murmushi,“Alhamdulillah, Umrah ɗinku ta kammala.”Na ji kamar a wannan lokacin zuciyata ta zama sabuwa kamar an share duk wani nauyi a cikinta.

Mun koma cikin Al-Qamar Al-Haram Suites, hotel mai kallon harami daga window ɗin bene na 12. Hajja ta ce, “Ku huta, ku ci abinci.”

Amina ta kwanta, Nawal ta kunna TV, ni kuma na fita zuwa balcony.

Iskar hotel din tana da ɗan ɗumi amma tana cike da ƙamshin turaruka kala kala a hotel dn

Na tsaya ina kallon hasken Ka’abah daga nesa. Idona ya cika da wani shauƙi mai sanyi irin wanda ba a bayyana da kalma.

Nana hadiza

09030569336

[13/11, 7:15 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA TAMANIN DA SHIDA

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Wayata ta fara ringing.Sunan da ya fito a screen ɗin… Zee’ameerah .

Na tsaya na ɗan numfasa, kafin na danna “Answer.” Muryarsa ta fito da sautin da nake jin yana cikin ƙirjina “Hello my Zee’ameerah…”

Na yi shiru, sai murmushi ya subuce daga bakina.

“Assalamu alaikum.”

“Wa alaikumus salam,” ya ce cikin natsuwa.

Sai kuma ya ce, “Yaushe zaku dawo ne? Na rasa kaina wallahi. I miss you, terribly.”

Na lumshe ido, “Ka ce an sallame ka ne?”

Ya yi dariya mai taushi, “Yes baby, just yesterday. Amma yanzu… I’m in Morocco for a short business trip.”

Sai ya ɗan yi shiru, muryarsa ta koma mai rauni, “Kewarki ke addabani, Ramlah. Even my body feels your absence. Every breath reminds me of you.”

Zuciyata ta buga da sauri.

Na ɗan furta da murya mai rauni, “Asad, please stop… you need to rest, ka huta.”

Sai ya ce cikin lallashi, “Rest? How can I rest when you’re away? You know, your silence is louder than any voice I’ve heard.”

Na ji jikina ya yi sanyi. Kalmar ta shiga har cikin raina.

Na ce da murya ƙasa, “Ka huta, don Allah. Zan kira ka gobe idan mun dawo daga harami.”

Sai ya ce cikin murmushi mai sauti, “I’ll be waiting, Zee’ameerah. And don’t you dare make me wait too long.”

Na ɗan yi dariya a hankali, “Allah ya kara maka lafiya.”

“Ameen,” ya ce, sannan muryarsa ta yi rauni sosai, “Good night, my peace.”

Na kashe wayar a hankali, zuciyata na bugawa. Na jingina da bango, hasken Ka’abah na haskawa a window ɗin dakin.

Na furta cikin raina “Ya Allah, ka sanya soyayya ta zama mai albarka, ba jarabawa ba.”

****

Muna zaune a masallaci bayan sallar la’asar, hasken rana yana fadowa ta cikin window mai gilashi.

Iskar Masjid Al-Haram tana da ɗan ɗumi, tana ɗauke da ƙamshin turare.

Lokacin ya kusa ƙarfe biyu na rana.

Wayar Nawal ce ta fara ringing a gefe.

Ta kalli screen ɗin, sai ta ɗan turo baki, ta ce, “Uhm, Mamaa ce.”

Na kalle ta, “To ki ɗauka mana.”

Ta ɗaga wayar ta kara a kunnenta.

Cikin jin haushi ta ce, “Mama, bake kikace kar in kara kiranki ba? To ni kiran menene kikemun yanzu? Kindame ni wallahi.”

Na ji muryarta ta ɗan yi tsami.

Sai ta ɗan yi shiru, ta ce, “Kudi kuma? Mama, yaushe na baki million goma? Yaushe na baki, Mama?”

Ta ɗan sake numfashi, “Haba Mama, menene haka?”

Kafin in yi magana, sai kawai naga ta katse wayar, ta jefa ta gefe tana tsaki.

“Uff!” ta furta tana girgiza kai, “Wallahi zan iya haukacewa da wannan matar.”

Na tsaya kawai ina kallonta, amma ban ce komai ba. A cikin zuciyata, na ji tausayinta.

Mun ci gaba da zama har muka yi sallar magariba da isha’i.

Da muka fito daga masallaci, iska mai ɗan sanyi tana kadawa daga bangaren harami.

Na kalle ta a hankali, na ce, “ Yaya Nawal, dan Allah, zamuyi magana.”

Ta juyo, ta ɗan ce, “Small Mom, lafiya dai ko?”

Na ce cikin murya mai nutsuwa, “Wace ce ta kiraki dazu?”

Ta ɗan share gumin da bai ma fito ba, ta ce, “Mom dita ce.”

Na ɗan girgiza kai. “Yanzu Mom kike yiwa haka, kina mata tsawa kamar yarinyar ki?”

Ta ɗan tura baki. “Small Mom, ni wallahi ba zan iya jurewa ba. Uwata haihuwata kawai tayi, amma bata san komai a kaina ba! Sai yawon duniya Dubai yau, London gobe. Kin san me? Wallahi papa yarikemu kamar yaransa tun muna yara fa wannan matar sai aikin neman kudi babu abunda dadyna bai mata ba indai ana zancen matan masu kudi sai kinsa momy ga kawaye bazaki gane ba wallahi ko zancenta banaso dady sai da yazame mana uwa uba fa komai yana tsaye akanmu ita kuwa babu abunda yayimata zafi damu sai dai kudi kudi…Da auren Daddy ma, ta dinga bin maza, yanzu kuma mijinta ne ke wahalar daita fa shine takirani inajin ya cinye mata dukiyar shine tacemun wai asara tayi kuma nasan fada kawai tayi..Wallahi kwanan nan na bata kuɗi acikin wanda dady yabani nayi siyayyar kayan baby ne kuma Sis Amina ma fa nasan tana bata, amma yanzu wai tambaya take, kamar.. inajin zafin abunda tayiwa dady, cuz dadyna is a nice person ya cancanci amana ba cin amana ba wallahi yagyaramata rayuwa but..!” Ta faɗi haka da hawayenta na shawagi a idonta. Na tsaya ina kallonta cikin nutsuwa, na ce a hankali,

“Nawal… uwa ba ta da maye gurbin ta.”

Ta ɗan kalle ni, tana ɗan girgiza kai kamar ba ta yarda ba. Na ci gaba cikin taushi,

“Uwata ta rasu tun ina ƙaramar yarinya. Bansanta ba bantaba ganinta ba wacce natashi tagani amatsayin uwa sai ta dinga sukata tana illata nr Kin san menene hakan yake nufi? Yana nufin babu wanda yake kula da jikinki idan kinyi kuskure, babu wanda zai tsaya ya yi miki addu’a kafin ki fita daga gida kokuma akan wani abun, babu wanda zai zuba ido yana kallonki da soyayyar da bata da sharadi.”

Na ɗan tsaya, numfashina ya dushe, sannan na furta cikin murya mai rauni,

“Ki ji ni Yaya Nawal, koda uwa ta yi kuskure, ita ce uwarki. Ba laifin ta kika gani ba kaddararki kika gani. Koda ta barmu a duniya, tana da daraja.”

Hawayena suka fara zubo, na share su da sauri amma muryata ta dushe.

“Kin san me yasa? Domin Allah ya ce, ‘wa bil waalidaini ihsana’ ki kyautata wa iyayenki, ko suna masu cutar da ke. Domin idan kika kyautata musu, Allah zai kyautata miki.

Ko da ba ta nuna soyayya ba, ke ki nuna mata. Saboda wata rana… wata rana Nawal… za ki so ki ji muryarta, amma babu ita.”

Sai ta tsaya tana kallona da idanu masu cike da hawaye, kamar yarinya.

“Small Mom… kina nufin… in daina fushi da ita?”

Na ɗan riƙe hannunta, na ce cikin sanyi,

“Daina fushi da ita. Ki ji tsoron asarar albarka. Ki roƙi Allah ya shiryar da ita, ki dinga yi mata addu’a. Mahaifiyarki ce, Nawal. Ko ta barmu, ba ta daina kasancewa uwa ba kikirata kibata hakuri karki kara yimata masifa ko tsawa kinji.”

Sai ta fashe da kuka mai sauti, ta jingina kanta a kafaɗata.

“Ni ban san me yasa nake jin haushi ta haka ba,” ta ce cikin kuka.

Na rungumeta a hankali, “Kukan nan da kike ki daina kiyi mafa kyakyawan zato tunda tayi aure yanzu.”

Mun zauna haka na ɗan lokaci, tana kuka cikin ƙirjina, ni kuma zuciyata na cike da wani irin taushi. Iskar Makkah tana kadawa daga window, tana shiga cikin masallacin da muke zaune a ƙofar sa. Na ɗaga kai sama, na furta a raina “Ya Allah, ka shiryar da ‘ya’ya da iyaye, ka sanya soyayya ta gaskiya tsakanin su.”

Bayan muka gama hira da Nawal a masallaci, sai naje hotel ɗin Jabal Omar, inda iyayena suke sauka. Na kira Momy, cikin muryarta mai taushi ta ce “Ramlah, mu a bene na uku muke. Ki hau lifta, ɗakin 312.” Na gyara abaya, na ɗaura mayafi, na shiga lifta cikin natsuwa. Zuciyata cike da murna da dokin ganin su. Kamar mafarki ne, bayan watanni, zan sake ganin fuskokin da suka zame min uwa da uba.

Da na fito daga lifta, ƙamshin turaren mabkhara da sandalwood ya doki hancina.

Na buga ƙofa a hankali, kafin in maida hannuna, sai naga Momy ta buɗe ƙofar da kanta.

“Subhanallah!” ta faɗa cikin farin ciki, “Ramlah ɗiyata!”

Na rungume ta, hawaye suka fara fita kamar ruwa.

“Na yi missing ɗinku sosai,” na ce cikin rawar murya.

Bilkisu ta fito daga ciki, tana murmushi, “Ramlah! Ke kam kin canza fa. Kin ƙara kyau, kin ƙara kiba!”

Sai Yaya Aliya ta biyo, tana dariya, “Ni ma fa nayi mamaki wallahi kin zama kamar baby!”

Muka yi dariya gaba ɗaya, cikin nishaɗi.

A wannan lokacin ban ma san meye tsakaninmu ba, sai farin ciki.

Na ji dadin ganin su fiye da komai.

Da mintuna suka wuce, sai kawai Abba ya buɗe ƙofa ya shigo. Fuskarsa cike da annuri da girmamawa, sanye da farar jallabiya, yana riƙe da tasbihi. Na miƙe cikin girmamawa, na rungume shi da hawaye.

“Abba, na yi missing ɗinka sosai,” na ce da muryar da ta kasa fitowa.

Ya shafa kaina da hannunsa, “Ramlah ɗiyata, Allah ya albarkace ki.”

Momy ta ce tana dariya, “Kin ga mijinki ne fa ya bamu kujeru guda biyar.”

Na yi murmushi cikin kunya. “Mijina?”

Nana hadiza

09030569336

[13/11, 7:15 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA TAMANIN DA BAKWAI

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Abba ya gyara zama, ya kalleni da idanu masu zurfi irin kallon uba da yake cike da tausayi da tsoro lokaci guda.muka gaisa sosai anan ne nake cewa Abba “ Ina mom?”

Ya ɗan numfasa, ya jingina da kujera.

“Ramlah, mun rabu.”

Na ji kamar wani abu ya tsaya a cikin zuciyata. “kun rabu?” na maimaita, kamar ban ji daidai ba.

“Eh,” ya ce. “Sun meabu ne saboda wani abin da bai kamata ba.”

Na ɗaga kai, hawaye suka cika ido. “Abba, saboda me? Me ya faru?”

Ya share gumi a goshinsa, ya kalli ƙasa.

“Ranar da abin ya faru, ni ma ban taɓa tsammani ba. Wai Momynki ta mare ni.”

Na buɗe ido cikin firgici, “Mareka, Abba?”

Ya ɗaga kai a hankali. “Eh… saboda Bilkisu.”

Na kasa magana.

Ya ɗan yi shiru, sai ya ci gaba da magana cikin sanyi “Ranar da Auwalu almajirin gidanmu ya ce yana son Bilkisu, sai na ɗauki maganarsa da gaske. Na kai shi kasuwa, na ba shi tallafi, sannan na ce masa, ‘Ka shirya, zan baka Bilkisu idan lokaci yayi.’

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull