Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 33
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 33: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 33. Sai Bilkisu ta ce, babu wanda ya isa ya aura mata shi. Momy kuwa ta…
4,488 words
Sai Bilkisu ta ce, babu wanda ya isa ya aura mata shi. Momy kuwa ta tsaya akan cewa, ‘babu mai yiwa ƴarta wannan auren itama yarta atsaya agani ɗan shugaban kasa ne zaizo yana sonta , Auwalu ba class ɗin mu bane.’sai maganar ta rikice.” Ya ce, “ Zainabu ta ce ina raina ta ne saboda banasonta da ƴarta itama sai dai asamowa diyarta mai kudin gaske. Ni kuma na faɗa mata gaskiya cewa idan mutum mai ibada ne, ba dole sai da kudi ba. Sai kawai ta zazzageni, kafin in sani, tuni ta mare ni.Bilkisu ta shiga tsakanii.”
Ya ɗan yi shiru, yana girgiza kai.
“Daga nan nayi shiru, na bar komai ga Allah. Na sauwake mata saboda Annabi (SAW) ya ce mafi kyau shine wanda yafi gafara. Dan gaskiya bazan iya cigaba da zama daita ba.
Tana ganin ni ne na baki Asad na hana ƴarta.”
Na ɗaga kai cikin mamaki.
Abba ya ce, “Eh, tana ganin ni na sa auren naku ya faru ba Allah ba.
Tana ganin na ci amanar Bilkisu saboda kin auri Asad.”
Na rufe baki da tafin hannu.
Ya shafi kaina, yana murmushi mai taushi.
“kaddara tana tafiya ne da umarnin Allah, ba da ra’ayoyin mutane ba.
Zainabu na cikin fushi, amma lokaci ne zai koya mata hankali.
Na share hawaye, muryata tana rawa.
“Abba, Amma me yasa take ganin na cuci Bilkisu?”
Ya murmusa da ƙorafi. “Ramlah, ba kowa bane yake gane adalcin Allah a lokaci guda.
Kin ga Bilkisu ta amince yanzu, har na karɓi kuɗin aurenta. Kaddara ce kawai babu laifi a gare ki.”
Na jinjina kai, hawaye na zuba.
Zuciyata cike da ciwo da tausayi. Na kasa jurewa. Kukan da nake ta daurewa tun daga lokacin da Abba ya faɗi sun rabu, sai kawai ya fito da ƙarfi. Na kalli Abba cikin hawaye, murya na rawa, “Abba… dan Allah ka taimaka ka dawo da ita. Ba don halinmu ba, dan Allah ka taimaka saboda Allah.” Na share hawayena, zuciyata kamar zata fashe. “Ka dawo da ita, Abba. Uwa ce fa… koda ta yi kuskure, bata daina kasancewa uwa ba.”
Dakin ya yi shiru na wasu sakanni.
Kowa yana kallona, idanu masu cike da tausayi da mamaki.
Momy ta dago kai, ta ce cikin murya mai ɗan ɗaci. “Ai zama ya kare, Ramlah. Har abada. Zainabu ba matar kirki bace.
Allah ya shiryata kawai.” Na juyo ina kallon Momy, hawaye suna ci gaba da zuba.
Abba ya shafe gashin kansa, yana fitar da numfashi mai nauyi. “Ramlah, ai babu ni babu ita har abada. Na so Zainabu tabbas amma yanzu… banjin wannan son a zuciyata, ko ƙadan.”
Na ɗan rufe idona, hawaye suna zuba.
A wannan lokacin na gane soyayya da aure ba wai farin ciki bane, sai akwai jarabawa a cikinsa.
Cikin wannan shirun, sai na ji muryar Bilkisu a gefe tana kuka.
Ta taso a hankali ta zo kusa da ni. “Ramlah…” ta kira ni cikin kuka, tana riƙe da hijab ɗinta. “Dan Allah ki yafe min. Wallahi Momy ce ta zuga ni. Ni ce na kai harin kashe ku a ranar bikin ki.” Na ɗago kai cikin firgici, na ce da muryar da ta kasa fita, “Bilkisu… kina nufin ke?!” Ta rushe da kuka.
“Wallahi ban san me yasa nayi ba.
Mijinki ya gane gaskiya, ya tsawata min, ya yi min fada sosai. Ya ce min, ‘Ramlah bata cancanci mugunta ba.’
Na ji kunya, Ramlah. Na kasa bacci tun ranar.” Sai ta kama hannuna, tana kuka sosai. “Dan Allah ki yafe min.
Yanzu ni ina hannun Momy ta Yaya Aliya.
Momyta waccan… Allah ya shirye ta, saboda ni na gane gaskiya yanzu.” Na daure murya, na ce cikin tausayi, “Bilkisu, idan Allah yana yafe mana kullum, me yasa ni ba zan yafe miki ba? Na yafe, dan Allah. Amma ki tuba daga zuciyarki, ki guji sake shiga cikin muguwar shawarar zuciya.”
Ta rushe da kuka, ta durƙusa ƙasa tana cewa “Na gode, Ramlah. Wallahi Allah ya san ina nadama.” Na miƙa hannu na ɗago ta a hankali.Na rungumeta cikin kaina, hawayena suna zuba a kanta. “Kuka ya isa, yaya Bilkisu. Kowa yana da kuskure. Abin da Allah yake so shine tuba. Mu tuba, mu yafe, mu roƙi rahama.”
Abba ya kalli dukanmu, idonsa cike da hawaye. “Allah ya saka muku da alheri, ku duka. Ku ji, kaddara bata da son rai.
Idan lokaci ya zo, komai sai ya bayyana.” Momy ta lumshe ido, ta share gumi a goshinta. Sai ta ce cikin murya mai rauni, “Allah ya shiryata, Abba. Ka gafarta mata idan ba dan komai ba, dan yaranki.”
Abba ya ce da natsuwa, “Na yafe mata.
Ba don ita ba, don Allah.”
Abba ya kalli ni cikin murmushi, muryarsa cike da taushi da annuri. “Ramlah,” ya faɗa, “kiyiwa maigidan naki godiya, ya bamu kujera guda biyar har da Guzuri. Kinji?”Na ɗaga kai, murmushi a fuskata, zuciyata cike da daɗi “Na ji, Abba,” na ce cikin ladabi, “insha Allah.”
A gefe Momy ta miƙe, ta kama hannuna cikin wasa. “Auta,” ta ce da dariya, “ince dai bakije kina wannan gidadancin ba?”Na ɗan murmusa, na lumshe ido. “Momy, rayuwar gidan sarauta tanada wahala wallahi.
Danma wata mata na gyaramun yadda zan zauna dasu.” “ Ai gwara yabarki anan kikar wayewa auta. Yaya jiƙin nasa? Yanzu ma yana Morocco, yaji sauƙi sosai.”Momy ta ware ido cikin mamaki, ta ce, “To mashaa Allah, auta. Dan Allah kibi mijinki, kizama yar soyayya. Nasanki, kina da gayu sosai, amma ki dage sosai kinji? Tunda abinda muke fargaba ma, Allah ya sanya suna sonki yaransa.Ki zauna da kowa lafiya. Nasani,kinada tsoron Allah sosai amma kudi suna canza mutum. Ramlah, kin shiga gidan mai dukiya sosai. Ki ji tsoron Allah, kinji?
Ki kyautatawa duk wanda ya kamata.”Na jinjina kai a hankali, na ce, “Insha Allah, Momy. Zan kiyaye. Na san da addu’arku komai zai daidaita.” Ta murmusa, ta taɓa kafadata. “Haka nake so, auta.
Yanzu tashi mu je mu gaida hajiyar tasa.
Ko mu yau da daddare zamu huce, yau satinmu biyu kenan.” Na ɗaga kai cikin farin ciki. “To Momy.” Mun fito tare da Momy da Bilkisu da Yaya Aliya muka nufi Mall ɗin Jabal Omar, inda fitilun kasuwa suke haskawa kamar taurari. Kowane wuri cike yake da ƙamshin turaren oudh da amber, mutane suna yawo cikin nutsuwa da fara’a. Na ɗauki abaya kala biyar masu launin toka, baki, da ruwan kasa, sannan muka zaɓi turaruka masu ƙamshi Bakhoor Al-Haram, Raghba, da Shams Al-Madina. Momy ta ce tana dariya,
“Wallahi, Ramlah, sai kin koya min yadda ake gane turare mai tsada.” Na ce, “Momy, ai wayannan basu kai wanda naga su nawal suna saya ba momy kinga luxury kuwa. Tayi dariya tace ai yanzu kema daga kallonki zaa gane kinshiga luxury din.
Daga nan muka nufi hotel gurin Hajja, wato mahaifiyar mijina Ko da muka isa, an riga an shirya mana karɓa.Ƙamshin turaren koina Hajja ta tashi tana murmushi da girmamawa, ta rungume Momy. “Ahlan wa sahlan!” ta ce cikin muryar Larabci mai daɗi,
“Marhaban bikum, ya ahl al-baiti.”
( Barkan ku da zuwa, iyalan gida.)
Na kalli yadda ta kalli Momy da Abba da girmamawa, zuciyata ta cika da godiya.
Momy ta ce cikin murmushi, “Hajja, kin yi mana abin alkhairii sosai. Allah ya saka da alheri.”Hajja ta ce, “ Ai tsakanin mu da juna babu godiya Wallahi ku mutane ne masu daraja.”Abba ma ya yi godiya, ya kalli ni da murmushi, “Ga Ramlah nan duk abunda tayi ba daidai ba danAllah a gyara mata.”
Na sunkuyar da kai cikin kunya, na ce, “Na gode, Hajja.” Ta murmusa tana kallona da idanu masu cike da tausayi da annuri. “Ki zauna lafiya da mijinki, ki kula da shi, ki kula da yaransa. Ki zama uwa a gidan.” Na amsa cikin natsuwa, “Insha Allah, Hajja. Zan yi iya ƙoƙarina.”
Nana hadiza
09030569336
[15/11, 6:59 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA TAMANIN DA TAKWAS
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
A gefe, Nawal ta shigo da gudu tana murna.
Ta hango Bilkisu, ta saki ihu cikin farin ciki. Tafara gaidasu abba sanna ta juya gurin yaya billy tace “Billy! Kina nan a gari! Wallahi kin ɓoye min!” Bilkisu ta yi dariya, ta rungumeta.
“Nawal! Ni ma wallahi na yi kewarki sosai.”
Suka tsaya suna hira kamar yara biyu da suka daɗe ba su haɗu ba, suna dariya, suna tuna abubuwan baya. Na tsaya ina kallonsu, zuciyata tana cike da godiya. Na ji natsuwa mai zurfi irin wacce mutum ke ji bayan dogon rikici da damuwa. Momy ta kalle ni daga nesa, ta yi murmushi. “Auta…” ta kira ni a hankali,
“Allah ya baku zaman lafiya har abada.”Na ɗaga kai, hawaye masu sanyi na taruwa a ido,na “Amin, Momy.” Duk suka yi murmushi, suka juyo ga juna, suka ce cikin baki ɗaya “Amin, ya Rabb.”
*******
Asad yana kwance akan farin gadonsa mai kyan gaske a ɗakin otel ɗinsa dake Casablanca, Morocco. Dakin shiru yake, hasken lamp ɗin gefen gado yana fitar da launin ja duhu., amma zuciyarsa tana ci kamar ana kona ta.
Jikinsa sai zufa yake yi, gabansa yana rawa, zuciyarsa kamar zata faso ƙirjinsa.
Wani irin sha’awa mai tsananin gaske ta taso masa, irin wadda rabon da ya ji tun da daɗewa. Ya runtse ido yana maimaita sunanta a hankali “Zee’ameerah…” Sai kuma ya buɗe ido, yana maida numfashi cikin wahala.
Hannunsa yana girgiza, jijiyoyin fuskarsa sun fito fili. Desire and faith sun shiga faɗa a cikinsa zuciyarsa na kiran haram, ruhinsa na kiran Allah. Ya ɗauki wayarsa, ya danna numbar Nawal amma itama bata shiga, saboda tun da Ramlah wayarta bata shiga amma kiran bai shiga ba. Ya sake ƙoƙarin samun sauki, amma zuciyarsa na ƙin natsuwa. Ganin haka, sai wani tunani mara kyau ya fara tasowa a ransa. Ko yayi wasa da gabansa har yakawo? Har ya dasa hannunsa gabansa Sai kuma ya tsaya cak. Ya ɗan tashi daga kwance, yana jin bugun zuciyarsa yana ƙaruwa. Ya dafe kansa da hannayensa biyu, ya ce cikin harshen Larabci mai raunana murya “أعوذ بالله من الشيطان الرجيم…”
(A’udhu billahi minash shaitanir rajim )( Na nemi tsari da Allah daga shaidan da aka jefa a cikin zuciya.) Ya zauna da ƙarfi, yana girgiza kai. “La’a… wannan ba daidai bane. Ba zan cutar da kaina da zunubi ba.” Kalmar ta sake dawo masa kamar ana karantawa a kunnensa. Ya sanya hannayensa a fuska, yana sauke numfashi mai nauyi. “Allahumma ighfir li. Ka tsare ni daga zuciyata. Ka bani natsuwa.” Ya ɗaga hannu sama yana roƙon Allah. Zuciyarsa tana bugawa, amma a hankali sha’awar ta fara raguwa da istigfarin da yake maimaitawa.
Ya tashi daga gado, ya wuce bandaki ya ɗauro wanka ba don sanyaya jiki ba, sai don sanyaya zuciya. Yana gamawa sai ya saka thobe mai sanyi, ya shimfiɗa sajjadah ya tsaya sallar nafila, yana kuka cikin sirri.
“Ya Allah,” ya faɗa cikin murya mai ƙasa, “kada ka bar ni a hannun kaina ko da idon gizo. Ka bani ikon jimrewa, ka haɗa ni da matata cikin halal.” sai ya tuna A addinin Musulunci, istimna’i (biyawa kai bukatar jima’i da hannu) haramun ne idan babu ƙarfafa dalili na magani ko gujewa zina kai tsaye.
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya matasa, wanda zai iya aure to ya yi aure, domin aure yafi kiyaye ido da al’aura wanda bai iya ba, to ya yi azumi, domin azumi yana rage sha’awa.”
(Bukhari da Muslim) yakuma tuna Illar istimna’i ga lafiya kuwayana lalata kwakwalwa da tsarin sha’awa,yana haifar da gajiya da raunin jijiyoyi,yana sa mutum ya rasa kuzarin soyayya ta halal,kuma yana iya kaiwa ga bacin rai (depression). Saboda haka, istigfari, azumi, da nisantar tunani mara kyau sune maganin irin wannan jaraba.
Asad yana kammala sallar sa, ya zauna yana jan tasbihi. Fuskarsa ta koma cike da nutsuwa. Zuciyarsa ta saki numfashi, tana jin kamar wani dutse ne ya sauka daga ƙirjinsa.
“Allah ka tsare min ita,” ya furta cikin natsuwa, “domin ita ce dalilin da yasa zuciyata ke neman halal, ba haram ba.”
Sai ya ɗauki wayarsa, ya rubuta saƙo ga Ramlah “My Zee’ameerah, I prayed for you tonight. May Allah keep our love within His mercy, not within our desires.” Ya ajiye wayar a gefe, ya rufe idanu, ya yi murmushi mai ɗan zafi da natsuwa. Soyayya ta musulmi, ba ta tsayawa a jiki ba tana farawa da zuciya.
******
Ko da Ayshatu ta shigar da Alhaji Muqaddam kotu, gari ya cika da maganar Tace, yana cin zarafinta, yana dukanta, kuma tana son a rabasu ita bata auren wallahi Sai dai Alhaji Muqaddam ya tsaya akan maganarsa “Wallahi ba zan sake ta ba.
Ba wai saboda girman kai ba, sai saboda ina ganin har yanzu inason matata.” Kotun ta dage karar sau uku, tana jiran su daidaita a gida, amma babu canji. Ayshatu ta koma gida tana kuka, zuciyarta cike da ƙiyayya da damuwa. Ta kulle kanta a ɗaki tana zubar da hawaye ba wai don ba ta son zama da shi ba, amma don ta gaji da ciwon da zuciyarta ke ji kullum. Da rana, bayan ta fito daga kotu da niyyar kammala gyaran takardunta, sai kawai ta ji ana buga ƙofa. Tana buɗewa, sai taga Alhaji Muqaddam tsaye, sanye da farin jallabiya, fuskarsa cike da damuwa.
Ya shigo dakin ba tare da izini ba, kamar wanda ya dade yana jiran wannan damar. “Aysha,” ya ce cikin murya mai sanyi amma mai nauyi, “na gaji da wannan rikicin. Ki faɗi komai kike so ki faɗa, amma wallahi, ba zan rabu da ke ba.” Ta juyo tana kallonsa cikin hawaye, “To me yasa kake duka na? Me yasa kake zubar min da mutunci, Muqaddam? Kullum sai ka ce ni ba mace bace, ba matar kirki bace!”Ya ɗan dafe kansa, yana girgiza kai, “Na san nayi kuskure. Ni ma yanzu na fara gane cewa ba da duka ake gyara mace ba. Amma ki taimake ni, Aysha. Idan zaki gyara halinki, mu zauna lafiya. Na gaji da zama a kotu, na gaji da magana, na gaji da r
Rigimar mu kullum kina cemun banida dabi’u Asad zanyi kokari na gyara ko nace nafara gyarawa.” Ta yi shiru, hawaye na ci gaba da zuba. “Muqaddam,” ta ce cikin rawar murya, “ni ma na gaji. Ba wai bana son zama da kai ba, amma ni mace ce mai zuciya, ba dutse ba.Ko mutum yaji ciwo da kalma, balle duka?”
Ya matso kusa, yana kallonta da idanun da suka fara cike da nadama. “Aysha, wallahi ba nake nufin cutar da ke ba. Sai dai na kasa fadin ‘ki yafemin, saboda girman kai.
Amma yau... na yarda, nayi kuskure.”
Ta ɗan juya kanta, tana shessheƙa.
“To me yasa yanzu? Me yasa sai da kake ganin ina neman rabuwa da kai ne ka gane gaskiya?”Ya zauna a kusa da ita, yana dafe ƙirjinsa.“Saboda na fara jin ciwon rashin ki a zuciyata.
Saboda duk lokacin da nake ganin mata, ban ga wata da kamarki ba.”Aysha ta fashe da kuka, ta ce, “Ka bari ni kawai, Muqaddam.
Koda nayi kuskure, me yasa zaka dinga cutata har haka?”Sai ya dafa kafaɗarta a hankali. “Domin na kasa sarrafa zuciyata. Amma yanzu, Allah ya bani hankali.
Wallahi, Aysha, idan zaki yarda, zan gyara. Zan zama mutum na kirki.
Ki daina kuka, ki bani dama guda.” Ta girgiza kai cikin hawaye,“Ban san ko zuciyata zata iya yarda da kai ba.”Ya ce cikin natsuwa, “Ki yarda da Allah, ba dan ni ba.”Sai ta rufe fuskarta da hijab tana kuka.
A cikin kukan nata ta furta,“Na gaji, Muqaddam. Na gaji sosai.”Ya ɗaga hannu sama yana istigfari,“Allahumma ighfir li. Ka bani ikon gyara, kada in sake cutar da wadda ke da hakki a kaina.”
********
Kwanaki biyun nan bayan ziyarar da muka yi, Hajja ta ce yau sai mu fita mu ɗan zagaya kasuwa, mu sayi tsarabe-tsarabe kafin mu koma gida. Mun nufi wani babban mall da ake kira Al-Zahra Royal Mall, yana kusa da Harami, inda fitilu ke haske kamar rana.
Wurin cike yake da manyan mata, yawancinsu cikin abaya masu sheƙi, hannunsu cike da jakunkuna na Louis Vuitton, Dior, da Hermès.Na tsaya ina kallon su cikin mamaki, na ce a raina “Allah kayi mana arziki, dan Ya Rasulillah.” Ban ma san inda zan fara gani ba. Kullum ina jin labarin kasashen larabawa suna kashe kudi, amma yau ido na ya gani. Wata mata ce ta ɗauko sarka guda ɗaya ta zinariya, aka ce mata SAR 45,000 na kusa faduwa. Sai ta ce da kasaita, “Wrap it please.”Hajja ta juya ta kalle ni tana murmushi. “Ramlah, wannan ai ke kika dace da ita,” ta ce, tana nuna wata sarka mai siffar crescent moon da lu’ulu’u a tsakiyarta.
Na girgiza kai cikin kunya, “Hajja, a’a fa, wannan fa mai tsada ce sosai.”
Ta yi dariya ta ce, “Ni nayi niyyar siye miki, ki karɓa mana. Tsarabar Hajja ce.”Na kasa magana, hawaye sun tsaya a ido. “Na gode sosai Hajja,” na furta da muryar da ta yi sanyi.
Nana hadiza
09030569336
[15/11, 6:59 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA TAMANIN DA TARA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Na ji kunya da farin ciki lokaci guda.
Na juyo ina kallon Nawal, tana dariya, “Small Mom, yanzu dai ke ma kema gaskiya kidinga sakin jikinki” Na saki murmushi kawai.
Na fitar da dala dubu biyu daga jaka na, na mika mata. “Ga wannan, ki siyo wa mai martaba, ban san me zan siya masa ba.”
Ta kalle ni da dariyar tsiya, “Au! Me martaba? To, kina nufin Daddy bazaki siyawa dadyna ba kenan? Lallai ma, Small Mom!”
Na yi saurin kare kaina, “Wallahi ba haka nake nufi ba, kunyarki nake ji.” Ta kyalkyale da dariya, “To muje to, akwai kudin da papa ya baki na $5000 ai. Muje mu kashe su kafin su Nan ko!” Na kalle ta da mamaki, “To shine baki gaya min ba? Kin san da nayi masa godiya ai !” Ta ce tana dariya, “Yanzu hajja tabani tace tasan ke bazaki karba ba.
Mun shiga wani babban shago a cikin mall ɗin, ana kiransa Al-Qasr Boutique shagonsa kamar fadar sarki ne, ƙamshin turaren oudh, sannan labulen shago yana haskawa Anan ne muka fara siyayya da gaske.
Na ga jallabiya manya guda uku, kowacce tamkar kayan sarki.
Mai siyarwa ya ce, “Hadhihi min ‘Dar al-Jamal’. Thalathah alaf riyal liwahida.”
(Wannan daga Dar al-Jamal ne, kowacce riyal dubu uku) kusan million da yan kai fa.Na kasa magana.Nawal ta kalle ni, “kin ji? Amma gaskiya wayanna basuyi ba ko?Na ce, “Wallahi da ban gani da ido ba, da na yi zaton karya ne jallabiya fa ashe har da ta masu kudi jallabiyar.” Ta zabarwa Asad kala biyu launin toka mai haske da ruwan dorawa.
Sai ta ɗaukarwa mai martaba jallabiya launin ruwan kasa mai kyau.
Bayan haka, sai ta ce, “To yanzu turaruka!”
Mun je sashen turaruka wani wuri mai kyau kowanne turare yana cikin kwalba kamar lMai siyarwa ya kawo mana Fanar al-Mahabba, Malikat al-Qamar, da Sirr al-Oudh.
Na taɓa kwalbar Malikat al-Qamar ƙamshinta ya lullube ni.Na furta a hankali, “Wallahi, ban taɓa jin irin wannan ƙamshi ba a wajenmu mu talakawa.” Nawal ta yi dariya, “Haba Small Mom, ke ba talaka bace!” Na ce a hankali, Gaskiya ce.”
Ta ce tana dariya, “Daddy ai baya sa ƙasa dana haka, Small Mom.”
Na juyo na kalleta, “To Allah ya ƙara masa arziki, ni dai wannan ƙamshi ya isa a ce Alhamdulillah.”
Na ji wata nutsuwa mai taushi a zuciyata.
Na lura da yadda Hajja ke kashe kudi ba tare da wani tunani ba, amma a cikin dukkan alatu ɗinta akwai natsuwa bata yi da girman kai.
Da muka fita daga mall ɗin, iska mai ƙamshi tana kadawa daga Makkah. Na ɗaga kai sama, na furta a raina“Ya Allah, ka bani arziki da albarka, ba arzikin da zai dauke min imani ba.”
Kwanaki biyu suka shude, babu kira daga Asad. Na ji kamar zuciyata tana kullewa da damuwa. Na so in tambayi Nawal, amma kunya ta hana ni. Ina ta duban wayata lokaci zuwa lokaci, amma shiru. Sai kawai na riƙa daure fuska a gaban kowa, kamar babu abin da ke damuna. Dan text dinma kwana biyu baiyi ba haka nadinga jina wani iri wannan ce soyayyar na tamabaye kaina? Yaa Allah ka datar damu.
Da aka ce gobe zamu tafi gida, sai na ji kamar wani dutse ne ya sauka daga ƙirjina. Na fara jin sauƙi, kamar an ɗan buɗe mini wani sabon numfashi. Da rana muka fita zuwa wani babban mall, Nawal tana son sayen kayan baby. Wurin yana cike da mutane suna yawo. Ni dai na tsaya a gefe ina kallon ikon Allah yadda arziki ke tafiya a hannun wasu kamar iska. Hajja tana ta sayen abubuwa, ni kuma zuciyata tana maimaita addu’a ɗaya “Allah ka ba mu arziki mai albarka, dan wallahu mai kudi suna shagalinsu.”
Da muka dawo, muka shirya kayanmu da komai. Gobe da sassafe za mu wuce, don haka a daren na ce musu “Zan je in yi dawafin bankwana.”
Na fita cikin farin hijabi, zuciyata cike da nutsuwa da ɗan kunci. Ina shiga harami, iska mai sanyi ta daki fuskata, ƙamshin mabkhara yana gauraye da ƙamshin Zamzam. Na samu wuri a gefen Ka’abah, na zauna na lumshe ido, na ɗaga wayata na kira Abba. Muryarsa ta fito cike da farin ciki. “Auta, kina lafiya?”
Na amsa cikin taushi, “Lafiya lau Abba, Alhamdulillah. Abba, ya bani kuɗi bundle na dollar, sai kuma Umar ya bani $500. Wallahi ban san abin da zan yi dasu ba. Ina so idan na dawo ka aiko wani ya karɓi kudin, ka ƙara a kasuwancinka, dan Allah. Sannan a yiwa Yaya Billy kayan daki da su.” Abba ya yi dariya, kamar mai jin daɗin yadda nake magana. “Auta, ki daina damuwa da kuɗi haka. Ai Allah ne mai azurtawa nima yayimun alkhairi ban faɗamiki baniba ta dalilinsa ma na kara buɗe wasu shagunan guda biyu ina harkar zobo da nakeyi to yayimun hanya zuwa waje alkhairin dana samu a satin nan bantaba samu a rayuwata ba naga kina firgita da yanayin kudinsu da kuma kashewa ko? Ahakan akwai wanda suka fisu arzuki auta da abunda wayannan sukeyi su agurinsu bazasuyi ba haka Allah yake ikonsa.” Na ɗan yi dariya cikin jin kunya. “Abba, ba tsoro nake ba… kawai ikon Allah nake gani. Komai design ne, komai luxury, hatta silifas, Abba!
Gaskiya ban taɓa ganin irin wannan ba.”Ya sake dariya, yana cewa, “Ai kuɗi kenan, Auta.
Kin shiga cikin masu kuɗi sosai, ki yi addu’a. Nikaina dalar dana gani satin nan Allah sai danayi mamaki. Kuma maganar kuɗin nan, ki barshi a wurinki. Ni yanzu ina da abin hannuna, idan na buƙata sai na sanar dake.
Amma, Auta…” Ya ɗan tsaya, muryarsa ta yi sanyi. “Ki daina nuna musu kauyencinki, kinji?
Kada su rainaki. Ki zama mai kamun kai,Nasan zakiyita ganin wasu abubuwan kamar almabazzaranci kuma ba haka bani ba kowannen mu da wadatar da Allah yabamu.” Na murmusa cikin jin daɗin kalmarsa.“To, Abba. Allah ya ƙara lafiya.”Ya ce, “Amin, Auta.
Dan Allah, ki zauna lafiya da kowa, ki kula da mutuncinki da addininki. Arziki yana zuwa ne don a gwada mutum, ba don a ɓata shi ba.”
Hawayena suka cika ido.Na ce cikin muryar da ta kasa fita, “Insha Allah, Abba. Zan kiyaye.” Mun yi sallama. Na kashe wayar, na ɗora hannuna a kirji.Na kalli Ka’abah. Na janye hijab dina a hankali, na fara tafiya cikin harami, ƙafafuna suna taka ƙasa mai sanyi,
zuciyata tana bugawa cikin farin ciki da tsoro lokaci guda haka nagama dawafina nayi addu’oi na yanzu bana manta mamana a addua tunda yayimun text ya tunasar dani.
Washegari da sassafe muka tashi muka nufi filin jirgi. Iskar safiya tana da sanyi, Na zauna a bayan motar, zuciyata na duka Kamar yadda nake jin farin cikin tafiya gida, haka kuma ina jin wani zafi mai nauyi rabuwa da su Nawal. Da muka isa King Abdulaziz International Airport, ana ta hayaniya, mutane suna shiga da fice da jakunkuna. Kallo ɗaya na yi wa Nawal, sai naga tana turo baki, idonta cike da hawaye. Ta ce, “Small Mom, Dubai zamu wuce, ba gida ba.” Na ce cikin mamaki, “Dubai kuma? Ni kuma fa?”
Ta ɗan yi dariya cikin hawaye, “Wallahi dady yaki. “ Sai naji hajja tace min “ Kina ji, Small Mom, karki yi kuka kinji? Indai Asad ne, sai kin gaji da ganinsa.” Na murmusa. Cikin dariya Hajja ta ce, “Ni dai nace ki yi hakuri, Auta. Indai Asad ne, sai ki gaji da ganinsu.
Amma ke Nawal, wallahi idan kika sakata kuka ranki xai baci.” Amma da lokaci ya yi, hawayen ban kwana suka fara. Na rungume Nawal sosai, tana kuka a kafadata, tana fadin “Grandma, wallahi bana son gidan sarauta nan, da binku zamuyi muntsani gidan Small Mom, Allah kada ki sake ki zauna lafiya ki dinga yimasa rigima, kinji?” Na ɗan yi dariya da hawaye a fuska,Ta yi dariya cikin kuka, ta goge idonta. “To ai idan kika zauna shiru, zaki rasa darajarki, Small Mom.
Kada ki yarda ki zama kamar wacce batasan ƙanta ba wallahi gidan nan sai su sanya ki samu ciwon zuciya, ki zama mace mai kaifi da so.” Hajja ta ɗan shiga yimata fada “Nawal, ke dai baki canzawa ko? To kuje ana jiranku mana.” Na juyo na rungume Yaya Amina.
Na ce cikin murya mai sanyi, “Ki gaida yara, kinji? Ki gaya musu ina missing dinsu sosai.”
Ta amsa cikin murmushi, “Zan gaya musu, Auta.” wai suma autaa suke tsokanata dashi.
An fara kiran flight ɗin su.Na tsaya ina kallonsu suna nufar hanyar shiga jirgi, suna dagamin hannuwansu na ɗaga musu Nima. Hawayena suka cika, amma na ƙi bari su zubo. Na ce a raina“Allah ya tsare ku, Allah ya haɗa mu da alheri.”
Flight ɗinsu ya fara tashi, na bi jirgin da kallo har sai ya ɓace cikin sararin sama.
Wani sanyi ya lullube ni, amma zuciyata na cike da natsuwa. Bayan mintuna kaɗan, sai kuma aka fara kiran jirginmu. Sai na kama hanya cikin natsuwa, da sarkar Hajja a wuyana, hawaye a ido, Nasaba da nawal jinta nakeyi kamar yar uwata komai ni komai nagyara komai karki kaza komai dady yafison haka wannan sune cikakkon masoyana.
haka muka tashi zuwa kasar mu ina missing makkah da madina.
Nana hadiza
09030569336
[16/11, 9:49 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA CASA'IN
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********