Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 35
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 35: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 35. Ko zakizo yanzu, ki taimaka. Ni ma kaina ke ciwo sosai… bana jin…
4,491 words
Ko zakizo yanzu, ki taimaka. Ni ma kaina ke ciwo sosai… bana jin daɗi.”
“Innalillahi… to gani nan,” ta faɗa cikin damuwa, tana kashe wayar da sauri.
Ya ajiye wayar gefe, yana kallonta.
Hannunsa ya miƙa, ya ɗan dafa gefen gadon inda take kwance, ya ɗan lumshe ido.
“Please… don’t scare me like this,” ya faɗa cikin raɗa.
Bargo ya janyo, ya rufe ta a hankali, kamar yana tsoron ta ɓace idan ya motsa da ƙarfi.
Shi ma ya kwanta gefenta, ba don yana jin daɗi ba, sai don zuciyarsa ta kasa barin jikinta shi kaɗai. Ciwon kai ya ƙara ƙaruwa, yana ratsa kunnuwansa zuwa cikin ƙirjinsa.
Nana hadiza
09030569336
[19/11, 7:45 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA CASA'IN DA UKU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Yana jin zuciyarsa na bugawa da sauti, amma dakin gaba ɗaya yayi shiru. Wani irin yanayi mai nauyi ya lullube su shiru mai magana.
Cikin mintuna da bazasu gaza ashirin ba, sai aka ji karar takun ƙafafun Hajja a ƙofar dakin.
“Asad?” muryarta ta kira cikin sanyi.
Ya ƙi amsawa, saboda muryarsa ta kasa fita.
Sai kawai ya miƙa hannu ya buɗe ƙofar da ƙyar.
Ta shiga, da fuskar damuwa.
“Subhanallah… me ke faruwa haka?”
Asad ya sunkuyar da kai, yana rike kansa, ya nuna da hannu inda Ramlah take.
“Bata motsi tun dazun… ban san me ke damunta ba.”
Hajja ta ƙarasa kusa, ta zauna a gefen gadon, ta rike hannun Ramlah.
Hannun ya yi sanyi kamar ruwa.
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Menene wannan nake gani?
Asad! Me ka yi?!”
Muryar Hajja ta cika dakin, tana rawar jiki, hannunta ta rike da gefen ƙofa.
Ta zuba masa ido, idanunta suka cika da hawaye.
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil! Asad, anya kuwa da girmanka?
Kai da mutane ke kallo a matsayin jagora, kai kake haka?!”
Asad ya kasa magana, jikinsa yana rawa kamar wanda ya kamu da sanyi.
Ya zauna a gefen gadon yana riƙe kansa, numfashinsa yana fita da sauri.
“Hajja… please… I didn’t mean to… wallahi…”
Amma kalmomin sun kasa fita yadda yake so.
Hajja ta ƙarasa gadon da Ramlah take, zuciyarta na bugawa da ƙarfi.
Ta dafa jikinta zafi!
“Innalillahi, jikinta kamar wuta!
Kuma kamar bata numfashi…”
Ta ɗan ja da baya, muryarta na rawa.
“Yau na shiga uku! Wane irin abu ne wannan, Asad?!
Ni wacece zan kira yanzu, gidan nan ba kowa!”
Ta fara lalubar wayarta cikin gaggawa, hannunta na rawa sosai.
“Subhanallah! Zara’u… Zara’u tana gidan nan.”
Ta shiga kiran lambar yayar Asad, Dr. Zara’u likitar gida kuma yayarsa ta jini.
Kira ɗaya… biyu… ta amsa cikin kasalalliyar murya, “Ranki ya daɗe, barka da asuba, Hajja.”
“Zara’u, dan Allah, kawo kanki sashen Asad yanzu!Ba lafiya, Ramlah ta kwanta bata motsi, jikinta zafi kamar wuta, Asad ma yana kwance Ki zo yanzu kin ji, dan Allah!”
Cikin firgici, Zara’u ta amsa, “Na ji Hajja, gani nan tafe.”
Hajja ta kashe wayar, ta durƙusa kusa da gadon tana karanto istigfari, idanunta cike da hawaye.
Asad yana gefe, yana girgiza kai kamar wanda ya rasa komai.
“Hajja… I didn’t want to hurt her, wallahi… I swear… I love her.
Amma jikina bai saurare ni ba. I lost myself.”
Hajja ta kalle shi da idanu masu cike da bacin rai da tausayawa lokaci guda.
“Asad… soyayya bata hana hankali.
Ya sunkuyar da kai cikin nadama, muryarsa ta dushe.
“Na san na bata, Hajja… amma wallahi ban yi da niyya ba..”
karar ƙofar da aka buɗe da hanzari.
“Hajja! Ina Ramlah? Ina Asad?”
Muryar Dr. Zara’u ta cika sararin dakin.
Hajja ta nuna da hannu gadon, hawaye na gangarowa daga idanunta.
“Gani nan, Zara’u… ba mu san me ya same ta ba.”
.Cikin mintuna kaɗan, Dr. Zara’u ta iso.
Ko da ta shiga dakin, ta tsaya cak ganin halin da ake ciki Ramlah kwance a kan gadon, Hajja tana kuka, Asad kuma yana gefe yana rike kansa kamar wanda ya rasa komai.
“Subhanallah… me ke faruwa a nan?”
Dr. Zara’u ta kalli Hajja cikin gaggawa ta ce,
“Hajja, a saka mata kaya da sauri mu tafi Asibiti.Wannan ba abin jira ba ne.”
Hajja ta taso da hanzari, tana taimaka wa.
Asad kuwa ya kasa motsi, yana kallo kawai.
Dr. Zara’u ta kalle shi, tana fadin cikin bacin rai,“Kai ma ba ka da lafiya, Asad.
Jikinka ya nuna ciwon kai ne ya kama ka sosai.Zan baka allura domin ka samu natsuwa.”
Ya girgiza kai a hankali, muryarsa na rawa
“Dr… ta… ta suma, ko?”
Zara’u ta ɗan harare shi, idonta ya nuna mamaki da takaici.
“Asad, da girmanka da iliminka, shin ka ga abin da ka jawo?
Wannan karamar yarinya ce!
Aure ba wasa ba ne, kuma ba zai zama azaba ba.”
Ya kasa ɗaga ido ya kalle ta.
Sai kawai ya furta cikin raɗaɗi,
“I lost control… gaba ɗaya… I didn’t mean to, wallahi… but”
Ta daga hannu cikin gaggawa, ta katse shi,
“Kada ka ce komai yanzu.
Wani lokaci shiru yafi magana.
Ka tashi ka zauna gefe.
Bari mu ga yadda za mu taimaka mata.”
Suka fita da Ramlah bayan an rufe ta da kaya. Hajja tana biye da su cikin tashin hankali, tana karanto istigfari.
Da suka isa babban asibitin birnin, aka kai Ramlah kai tsaye ɗakin gwaje-gwaje.
Zara’u ta tsaya kanta, tana bincike da kwarewar likita amma zuciyar uwa.
Bayan wasu mintuna ta fitar da numfashi mai nauyi, ta ce cikin tausayawa,
“Zan yi mata allurai biyu ɗaya don rage zafi, ɗaya don ta samu natsuwa. Sannan Nurse ta shirya kayan ɗinki, dole mu gyara gabanta a ciki da waje. Hajja, jikinta ya ji rauni sosai, kuma kafarta ta kumbura daga gwiwa zuwa ƙasa.”
Hajja ta rike kirjinta da tashin hankali, ta ce cikin murya mai rawa, “Dinki, Zara’u? Kin ce dinki?”
Zara’u ta gyada kai cikin tausayi.
“Eh, Hajja. Dole ne ya yagata sosai cike da waje zamuyi mata.
Jikinta yayi zafi fiye da tunanin mu.
Sannan kafarta ta dama ta kumbura Allah Ya taimake ta, amma ina fatan ba karaya bace ba. Sai mun yi hoton ƙashi yanzu nan.”
Kai, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Wannan yaro bai kyauta ba,” cewar Hajja cikin tashin hankali, tana kallon yadda likitoci ke ci gaba da aiki.
Ana tsaka da dinkin ne Ramlah ke matse idonta sosai, tana ƙoƙarin jure radadi duk lokacin da zare ya shigo.
Zara’u tana kula da ita da tausayi, zuciyarta na ƙuna.
Bayan sun kammala aikin, aka ɗauki hoton ƙafarta domin tabbatar da ko ta karaya.
Alhamdulillah, ba karaya bace amma ta ji buguwa mai tsanani.
Zara’u ta nemi likitan da ke karkashin sashen ƙafa. A hankali ta fita daga ɗakin, tana maimaita “Allah ya taimake ta.”
A gefe guda kuma, gidan sarauta ya dauki hayaniya. Labarin abin da ya faru ya bazu cikin sauri fiye da wutar daji.
Gabaki ɗaya aka shiga tashin hankali.
Yanzu kowa yana magana, ana zagin Haneefah da Ayshatu su da suka dinga faɗin Asad bashida lafiya yanzu gashinan dai shine har da karya kafar amarya da kuma ɗinki magana sai bazuwa takeyi. Gimbiya maryam kuwa ciwo takeyi sosau musamman bayan an ce amaryar Asad tana asibiti da rauni.
Mai Martaba ya girgiza kai cikin bacin rai.
“Anya kuwa wannan Asad ɗinane mai tausayi da hakuri yarima ba haka yake ba, wanda muka raina, shine wannan da ake magana akai? Gaskiya wannan abin kunya ne. Allah ya kyauta.”
Asad ya durƙusa a gaban babansa, jikinsa yana rawa.
“Rankaka ya daɗe… kayi hakuri. Na yi kuskure. Ban san abin da ya shige ni ba.
Wallahi, ban nufa cutar da ita ba.”
Mai Martaba ya ɗan ja numfashi, idanunsa sun nuna takaici.
“Asad, soyayya ba hauka bace.
Kunya ta ishe mu.
Yarinyar nan amanace gareka.”
“Na gode, ranka ya daɗe…” Asad ya furta cikin murya mai rauni, sannan ya sunkuyar da kai.
Bayan ya bar sashen Mai Martaba, ya kira Zara’u a waya.
Cikin ɗan ɗaci, ta ɗaga.
“Menene kuma, Asad?”
Ya ɗan yi shiru kafin yace da karyewar murya
“Ban isa nakiraki ba kenan?”
Ta yi masa dariya “Ai kai daman ka rainani wallahi gani kakeyi nice kanwar taka, matarka ka kira kaji ko? To gashinan sai da Mun yi mata ɗinki a ciki da waje. Ka kuma bugi ƙafarta har sai da aka daure ta.
Kunyar ku ta ishe mu.”
Ya rufe idanunsa cikin nadama, muryarsa ta kasa fita. “Thank you… bari nazo.”
Ya katse wayar, ya zauna na ɗan lokaci cikin shiru. Zuciyarsa na bugawa da sauti.
Ya tashi, ya nufi bandaki yayi wanka, yana jin nauyin duniya a kan kafadarsa.
Bayan ya gama shiryawa cikin rigar jalabiyya mai duhu, ya fito da fuska mai ɗauke da damuwa. Ya umarci P.A cikin murya mai sanyi “Ka sanar… zan fita yanzu.” ya gyada kai, ya buɗe masa ƙofa.” Duk inda yake kallo fuskar Ramlah yake gani idonta mai natsuwa, muryarta mai sanyi, da halinta mai taushi.“Yaa Allah,” ya furta a zuciyarsa.
Radadin zafin da na ji yana yawo a jikina, kamar ana hura min wuta a ƙirji.
Na yi ƙoƙarin buɗe idona, amma hasken dakin yana dishi-dishi, yana haɗuwa da wani irin jiri.
Nana hadiza
09030569336
[19/11, 8:56 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA CASA'IN DA HUDU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Cikin rauni, muryata ta fito ƙasa-ƙasa
“Wayyo Abbana…”
Na furta kalmar cikin hawaye, zuciyata na bugawa da tsoro da rikicewa.
A hankali idona suka gama buɗewa, sai naga shi tsaye a gaban gadona Asad, fuskar sa cike da kuka da nadama.
Sai na saki kuka mai ƙarfi, wanda ya sanya Hajja ta fito da hanzari daga bandaki,
tana fadin cikin ɓacin rai
“Wai, Asad! Ban ce maka ka bar ta ta huta ba?! Za ka sake illata mata jiki ne?!”
Muryarta ta cika dakin, tana nuna masa da hannu, idanunta cike da hawaye.
“Hajja…” ya kira cikin muryar da ke rawa,
amma kafin ya karasa, ta katse shi:
“Ka fita gefe! Wannan yarinya bata buƙatar ganin ka yanzu.”
Na ji jikina yana rawa, na ƙoƙarin miƙewa, amma sai wani zafi mai tsanani ya shige ni daga ƙasa zuwa ƙirji. Na riƙe bargona, hawaye suna bin kuncina.
“Wayyo Allah…” na faɗa cikin rauni,
“wayyo Hajja… jikina yana min ciwo.”
Hajja ta matsa kusa da ni, ta zauna a gefen gadon, tana rike hannuna.
“Sannu, ɗiyata… ki kwantar da hankali, zafin zai lafa da yardar Allah.”
Na ji muryarta cike da tausayi da ƙauna.
Na kalli ƙafata, sai na ga an nannaɗe ta da bandeji, sai hawaye suka sake zuba daga idona.
“Hajja…” na kira cikin muryar yarinya mai rauni,“akaini gurin Momy.”
Ta yi murmushi mai cike da tausayawa, ta shafi kuncina. “Allah sarki, ni ce Momynki yanzu. Ki kwantar da hankalinki, kin ji, Ramlah?”
Kuka ya sake kufce min, na furta cikin hawaye “To Hajja… to amma dan Allah, kada kimaidani can gida.”
Hajja ta rungume ni, tana raɗa a kunnena,
“Babu wanda zai maida ki can. Ki huta, kin ji? Allah yana tare da ke.”
A gefe, Asad ya tsaya yana kallo cikin shiru.
Idanunsa sun kumbura saboda gajiya.. bakinsa yana motsawa da kalmar “sannu.”
Hajja ta juyo gare shi da tsawa a cikin idanuwanta.
“Ka fita, Asad. Ka Bari ta huta.
Wannan yarinyar bata buƙatar kalamanka yanzu bayana azabar dinkin dakaja mata ita ba haihuwa ba ga kuma buguwa.”
Bayan wasu mintuna, Dr. Zara’u ta shigo.
Ta dubeni da murmushi mai taushi, ta ce da Hajja, “Abita a hankali sosai, amma zata samu sauƙi. Bazata iya tashi yau ba dole sai gobe.”
Hajja ta gyada kai. “To, to, Allah ya saka da alkhairi, Zara’u.”
Dr. Zara’u ta murmusa.
“Ni zan kula da ita, Hajja.
Amma kar a bari bayin gidan su shigo.
Ki sani, wannan magana idan ta fita, zai zama gulma.”
Hajja ta yi dariya mai ɗan sanyi, ta ce,
“Ai sun turo wasu, amma na maida su.
Na san bakin mutane, ban son gulmar su amma nasan yanzu ma suna can an yaɗa maganar..”
Dakin ya koma shiru.
Sai karar numfashina, da kukan da ke barazanar komawa sabo.
Hajja ta ɗora hannunta a kan fuskata, tana karanto addu’a.“Allah Ya sa wannan ciwon ya zama kaffara. Ki huta, kin ji, Ramlah?”
Na gyada kai cikin hawaye, zuciyata na jin kamar ta fashe.
A gefe kuma, Asad ya ja numfashi mai nauyi,
ya juyo da fuska mai cike da damuwa, sannan ya fita daga dakin a hankali kamar wanda zuciyarsa ta ɓalle gida biyu.
*******
Kwana biyu kenan da Ayshatu ta kasa gane kanta. Tun bayan rikicin da ta yi da Alhaji Muqaddam, zuciyarta ta rikice. Sai dai abin mamaki, shima ya sauya ɗabi’a ya zama shiru, baya fita sosai, yana zaune cikin tunani.
Gidan da da can yake cike da hayaniya, yanzu shiru yake a ko yaushe cike da nauyi.
Sauran matan nasa ma, babu wadda ke farin ciki.Daga gefe kake jinsu suna kuka, suna guntun maganar da ba a iya fahimta.
Da asuba Ayshatu ta fito daga ɗakinta cikin sanyin jiki, ta shiga sashensu tana tambaya,
“Yaya jiki?” Amma kowa na kau da kai kamar suna boye wani abu.
Washegari da safe, sai ta farka tana jin jikinta a mace, tamkar wuta ta ziyarci fatarta.
Kuraje sun bazu daga wuyanta har zuwa bayanta. Zazzabi ya rufe ta, jikinta ya yi nauyi kamar ta ɗauki dutse.
A daddafe ta tashi ta shirya, ta nufi Asibiti, tana tuka mota da kyar saboda jiri da ciwo.
Da ta isa Asibitin, likita ya amshi bayananta, ya yi mata gwaje-gwaje. Daga baya aka bata gado saboda zafin jikinta da rashin ƙarfi.
Bayan an mata allurai biyu, ta dan ji sauƙi, ta jingina da filo tana maida numfashi.
Ɗan lokaci da ta dan huta, likitan ya dawo da sakamakon gwaje-gwaje a hannunsa.
Fuskar sa ta nuna damuwa, amma yana ƙoƙarin boyewa.
“Barka da war haka, Hajiya Ayshatu,” ya faɗa a hankali.
“Barka,” ta amsa, tana ɗan ɗaga kai.
“Kin daɗe kina wannan rashin lafiyar ne?”
“Aa, kwanan nan ne kawai.
Da farko sai na ji jikina yana canzawa, sannan kuraje suka fara.”
Likitan ya gyada kai, yana duba takardar a hannunsa.
“To, me yasa kika ɗauki lokaci kafin ki zo asibiti?”
Ta lumshe ido, muryarta na rawa.
“Mun yi rikici da mijina… mu biyu ba mu haɗu ba tsawon lokaci.Sai kwanan nan ne muka daidaita.”
Ya ɗago ido ya kalleta.
“Ke ce amaryar Alhaji Muqaddam, ko?”
Ta ɗan jinjina kai, tana murmushi mai nauyi.
“Eh, ni ce. Lafiya dai, Doctor?”
Likitan ya sauke numfashi.
“To, Hajiya, gaskiya ne mai nauyi zan fada.
A farko banso na gaya miki kai tsaye ba, amma kin cancanci sanin gaskiya.”
Ta zuba masa ido cikin tsoro.
“Wannan cutar da kika gani waɗannan kurajen da suka fito a jikinki ba kurajen yau da kullum ba ne.
Su ne alamun infection mai tsanani.
Amma abin da ya fi damuwa shi ne…”
Ya dakata, yana kallon takardar gwaje-gwajen da yake rike da ita.
“…A cikin sakamakon gwajin mijinki, da sauran matansa, duk an tabbatar suna ɗauke da cutar HIV.”
Kamar an jefa mata wuta a jiki.
Idanunta suka firfito, numfashinta ya tsaya cak.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” ta furta da murya mai girgiza dakin.
“Doctor, me kake cewa? Cutar me?”
Ya miƙa mata takardar a hankali.
“Ki karanta da kanki.
Sakamakon ya fito jiya.
Basu dade da sanin hakan ba ma.”
Ta karɓa, tana kallon rubutun da idanunta suka kasa rufe shi.
Numfashinta ya yi nauyi, hawaye suka fara gangarowa.
“Ni fa, Doctor… ni fa?”
“Kin yi sa’a, Hajiya.
Mun yi miki gwaji, kuma baki da ita.
Amma dole ne ki kula sosai daga yanzu.
Abin da kika tsira daga shi, wasu basu samu damar ba.”
Ayshatu ta fashe da kuka mai tsanani, tana girgiza kai.
“Ya Rabbi!
Wannan mutum, wannan tsinanne wai shi ne zai kaini ‘honeymoon’? Ashe cuta yake shirinyi?!”
Ta rufe fuska da hannu, tana kuka da ciwon zuciya.
“Doctor, nagode.
Dan Allah sallameni.
Zan sayi magunguna a waje.”
Likitan ya yi mata addu’a a hankali.
“Ki kula da kanki, Hajiya.
Ki yawaita istigfari.”
Bayan ta fita daga Asibiti, ta tsaya a bakin mota tana kallon sararin sama.
Hasken rana yana fitowa a hankali, amma a idanunta, duniya ta zama duhu.
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil,” ta maimaita sau da dama.
“Allah ka shirye ni, ka yafemin zunubaina.”
Duk yadda ta so ta shiga mota, ƙafafunta sun kasa ɗaukar nauyin jikinta.
Ta jingina da bango tana hawaye, zuciyarta na tambayar kanta:
“Shin wannan ce sakamakon son duniya da kishi? Shin haka rayuwa tayimun?”
Sannan ta juya, ta shiga mota, tana jin kamar kowace kalmar “Astaghfirullah” da ta furta na saukar mata da salama.
Da ta koma gida daga asibiti, zuciyar Ayshatu kamar ana tsaga ta da wuƙa.
Komai a cikin gidan ya fara bata haushi bango, labule, kujera, ko ƙamshin turaren da da ta fi so.Duk sun zama mata tamkar masu tuna mata da abin da ta tsira daga ciki.
Bata tsaya ko ina ba.
Cikin sauri ta kira ƴan aikinta uku, muryarta cike da ƙarfin hali amma a zahiri numfashinta yana rawa.
“Ku haɗa min duk kayana,” ta faɗa.
“Duk abin da na mallaka a nan, ku sanya a jakunkuna.
Kowane abu da kuka gani nawa, ku cika mota da shi.
Ba zan zauna a gidan nan ba.”
Sun kalle ta cikin mamaki, amma ba wanda ya iya cewa uffan.
“Ku yi sauri,” ta ƙara faɗi. “Ina so in bar wannan gidan kafin rana ta fito.”
A cikin sa’o’i kaɗan, ɗakin da ya saba cike da ƙamshi da kyalli ya koma fanko.
Jakunkuna da ledoji suka cika motarta gaba ɗaya.
Ta tsaya a tsakiyar falo tana kallon gidan da da can take alfahari da shi.
“Gidan arziki…” ta furta a hankali, hawaye na bin kuncinta.
“Amma babu albarka.”
ƴar aikinta mai suna Falmata ta matso kusa cikin tausayawa.
“Hajiya, ina za ki tafi?”
Ta goge hawayen idonta, ta ɗan murmusa da ƙarfin hali.
“Ina zuwa wurin wanda nake da tabbacin ba zai jefar da ni ba
Mai Martaba.
Shi ne kawai mutum ɗaya da nake ganin zai fahimce ni yanzu.”
Da wannan kalma, ta juya, ta fitar da motarta daga gidan da ya zama tamkar kabari a idonta.
Tana tuka mota, iska ke kadawa ta cikin window, tana dukan fuskarta da sanyi mai cike da raɗaɗin tunani.
A idonta, titin da take bi ya yi nisa kamar tafiyar rayuwa mai cike da nadama da tambayoyi.
“Allah…” ta faɗa a hankali, “idan wannan ce kaffarar kuskurena, na yarda.
Tafiyar bata da sauƙi.
Gari daga gari take wucewa, rana na huda, iska na tashi.Amma babu abin da ya hana ta ci gaba zuciyarta ta gama yanke shawara.
Duk inda ta tsaya ta ɗan huta, sai ta kalli kanta cikin madubi ta ga mace daban ba Ayshatu mai kyau da ƙasaita ta da ba.
Wannan Ayshatu sabuwa ce mace mai raunana, mai nadama, mai neman gafara.
Wataƙila wannan ce karo na farko da ta ji zuciyarta tana da sanyi, tana da buƙatar samun natsuwa ba tare da duniya ba.
Nana hadiza
09030569336
[20/11, 8:33 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA CASA'IN DA BIYAR
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Sai wajen yamma lilis Ayshatu ta iso masarautar. Saninta a gidan yasa bata sha wahalar shiga ba, domin ko mai gadin ƙofar babban ɓangaren ya gaishe da ita da girmamawa. Ta amsa cikin nutsuwa, muryarta cike da rauni da gajiya.
Ta yi sa’a, domin Mai Martaba yana gari a wannan rana. Bayan ta nemi izinin shiga, aka ce ta jira domin yana da baki.
Ta zauna a falon jiran baki, zuciyarta na bugawa cike da tsoro da tashin hankali Kowace dakika kamar shekara ce a idonta. Bayan awa kusan biyu, sai aka fito daga ciki aka ce, “Mai Martaba yana son ganinki yanzu.” Tayi addu’a a ranta “Yaa Allah, ka sanya ya saurareni kasa na samu mafita na tuba yaa hayyu yaa qayyum.”
Cikin nutsuwa ta tura ƙofar, ta shiga babban falon da ta saba gani tun tana yarinya.
Haske mai sanyi ya cika dakin, turaren oud yana yawo cikin palon kuma Mai Martaba na zaune a kujerarsa ta fata, uwargidansa kuma a gefensa tana masa bayani cikin ladabi.
Da ta gan su, Ayshatu ta durƙusa cikin girmamawa, ta ce,
“Barka da yamma, ya Mai Martaba, Allah ya ƙara lafiya.”
Ya ɗaga hannu alamar amsa, yana kallonta da ido mai zurfi idon wanda yake ganin fiye da abin da ake faɗa.
Uwargida kuwa ta kalleta da wani irin yanayi kamar tsana da mamaki sun haɗu wuri ɗaya.
Ta rafka mata harara, sannan ta ce cikin murya mai ɗaci “Mai kuma yakawoki bayan ƙin gama wulakanta mana masarauta??
To, me ya kawo ki yanzu? Kin gaji da rayuwar da kika zaɓa kenan?”
Mai Martaba ya ɗaga hannu da natsuwa, yana fadin.“Ya’isa, ki bari ta yi magana.”
Uwargida ta yi shiru, ta maida kai gefe.
Ayshatu ta kasa magana na ɗan lokaci, sai kawai ta fashe da kuka mai ƙarfi, tana share hawaye da hannunta.
“Ranka ya daɗe,” ta ce cikin murya mai karyewa, “na zo gareka ne saboda na rasa kowa. Na shiga cikin masifa da matsala da ban taɓa zato ba. Mijin da na aura… shi ne aka tabbatar yana ɗauke da cutar HIV.”
Uwargida ta juya da hanzari, muryarta cike da zafi sosai “Tunanin nan kika fito da shi?
Kin dawo nan saboda neman a tausaya miki kenan? Ayshatu, ki ji tsoron Allah.”
Ta ɗago kai, tana kallo cikin hawaye, ta ce,
“Wallahi da gaske nake, Hajiya.
Ba don neman tausayi ba, don neman mafita nake. Ga takardar sakamakon gwaji nan.”
Ta miƙa takardar cikin girmamawa.
Aka karɓa, aka miƙa wa Mai Martaba.
Ya karɓa cikin natsuwa, ya ɗauki lokaci yana karantawa. Bayan ya gama, ya ɗaga kai yana kallonta.
“Yanzu Ayshatu,” ya ce cikin murya mai nutsuwa, “yaya kike so mu yi?”
Ta sunkuyar da kanta ƙasa, hawayenta na zuba.
“Ranka ya daɗe, don Allah ka rabani da shi gaba ɗaya. Ba wai don tsana ba, amma rayuwa ta ta ƙare da shi. Ban jin daɗin aure, ban jin kwanciyar hankali.”
Dakin ya yi shiru.
Kowa na jiran abin da Mai Martaba zai faɗa.
Sai daga baya ya sauke numfashi a hankali, ya ce,
“Rabuwar aure dai dole ce idan har lamarin haka yake.
Gaskiya ta bayyana a rubuce, babu yadda za a yi a rufe ta.”
Uwargida ta yi saurin ɗagowa da mamaki.
“Ranka ya daɗe! Ka biye mata kenan?
Waye ya tabbatar da wannan takardar gaskiya ce?
Wataƙila ma ta ƙirƙira tai!”
Ta juya tana fadin, “Ki tafi can dangin mahaifinki mana duk rashin arzukin da kikayi har karfine dake nakara tunkarar wannan masarautar. ko ki saya gida ki zauna ba sai ƙin dawo mana ba.”
Amma Mai Martaba ya tsayar da ita da murya mai ƙarfi, amma mai natsuwa.
“ki bar wannan magana.
Ayshatu kamar diyata take, kuma amana ce a hannuna. Koda kuwa bata kasance cikin gidan sarauta ba yanzu,
to ni zan tsaya mata.”
Ya juya ya kalli Ayshatu cikin tausayawa.
“Ki kwantar da hankalinki.
Zamu yi abinda ya dace.
Akwai shashen Zara’u likitar gidanmu.
Zaki iya zama a can zan saka ayi miki gyara.
Za mu kula da lafiyarki, sannan mu shirya yadda za a raba auren cikin mutunci.”
Ayshatu ta ɗago kai cikin hawaye, ta ce da rawar murya “Nagode, ranka ya daɗe.
Allah ya saka da alkhairi.” Sai kuma ta danyi jinkiri tace “Nasan nayi kuskure ranka yadade danAllah ayimun afuwa babana Ka yafemun nagane sharrin shaidan ne.”
Mai Martaba ya ɗan murmusa cikin tausayi.
“Anmiki afuwa, Ayshatu.Kuma Allah yana tare da masu hakuri. Ki huta yanzu. Ki bar komai a hannunmu.”
Haka ta miƙe a hankali, ta gaishe da uwargida cikin ladabi, duk da har yanzu uwargida ta kasa boye ɓacin ranta.
Bayan ta fita daga falon, Mai Martaba ya ɗan juyo ga uwargidansa ya ce,
“Koda me kike gani, bai kamata mu zargi wadda ke cikin rauni ba. Rayuwa ba ta cika da nasara, amma Allah yana da hikima a kowanne lamari.”
Uwargida ta lumshe ido, ta yi shiru.
A waje kuma, Ayshatu ta jingina da jikin bango, ta sauke numfashi mai nauyi.
Hasken yamma na faɗuwa, iska tana kadawa cikin sassauta.
“Allah ka yafemun kayimun afuwa,” ta faɗa cikin zuciyarta,
********
Daren ranar, bacci ya gujeni gaba ɗaya.
Radadin ciwo da zafin da nake ji a jiki ya fi ƙarfin da zan iya jurewa. Kowace numfashi kamar ana sare min jijiya ne da wuka mai kaifi. Gabadaya jikina kamar ba nawa ba ne tamkar na mutu amma ina numfashi.
Hajja tana zaune kusa dani tana tambayata, “Ramlah, jiķinne?Kin sha maganin da Zara’u ta baki kuwa?”
Nayi ƙoƙarin yin murmushi amma hawayen da suka zubo min sun bayyana gaskiya.
“Hajja, kafata ce... kamar ana ta da wuta a cikinta.”
Ta zauna a gefen gadon, ta ɗora hannunta a gwiwata. Zafin ya kara tashi sosai har sai da na saki ƙaramar ƙara.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,” Hajja ta furta cikin firgici. Ta kalli amintacciyar baiwarta, Halima, wacce ke tsaye gefe cikin tsoron magana.
“Halima, je ki kira Zara’u yanzu nan!
Ba zan bari wannan yarinyar ta wahala haka ba.”
Bayan mintuna kaɗan, Zara’u likitar ta shigo cikin sauri,tana sanye da farin labcoat, tana riƙe da waya a hannunta Kamshinta na turaren oud rose ya cika dakin.
“Ranki ya daɗe,” ta ce tana durƙusawa ga Hajja, “me ke faruwa?”
Hajja ta nuna ni da hannu, “Ki duba kafarta Zara’u, zafin ya kai mata kai.
Na fara tsoro, wannan ba buguwar ƙafa ba ce kawai.”
Zara’u ta matsa kusa, ta ɗan buɗe bandage ɗin da ke kafe ƙafar.
Numfashinta ya ja a hankali, idanunta suka cika da damuwa.
“Anya, Hajja,” ta ce a hankali, “ba tsagewar ƙashi bace ba kuwa?
Ga kumburi, ga zafin da ya kai jiki.
Bari in kira Doctor Idris shi yanzu .”
Ina jinsu suna magana amma hankalina yana can wani wuri. Kafata kamar ana watsa mata gishiri cikin rauni ne. Na runtse ido, na rufe baki ina jin hawayen ciwo na fita da sautin numfashi.
Da Zara’u ta ga halin da nake ciki, ta sake min allurar rage zafi,
tana shafa bayan hannuna cikin taushi.
“Ki daure, Ramlah,” ta faɗa cikin taushi, “za mu taimaka miki yanzu.
Amma wannan ciwon... akwai alamar tsagewa a ciki.
Ba zan ɓoye miki ba.”
Hajja ta juya ta tsaya daga gefe, tana ambaton Hasbunallahu wa ni’imal wakil.
“Wannan yaro bai kyauta ba wallahi bai jyauta mana ba,” ta ce da damuwa. “Ai ba ƙaramin ciwo bane wannan.”