Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 36
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 36: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 36. Wani lokaci kaɗan bayan haka, sai Doctor Idris ya shigo. Shi ne…
4,458 words
Wani lokaci kaɗan bayan haka, sai Doctor Idris ya shigo. Shi ne babban likita na bangaren ƙashi mutum ne mai nutsuwa da kwarjini, sanye da farar rigar da ta yi masa kyau.
Assalamu alaikum, ranki ya daɗe,” ya gaishe da Hajja.
“Na ji Zara’u ta ce akwai matsala.”
“Eh, likita,” Hajja ta ce tana nuna ni, “ga yarinya nan, kafarta ta kumbura sosai sai kuka takeyi tana faɗin zafi zafi sosai..”
Ya kalli ƙafar a hankali, ya saki ajiyar zuciya.
“Tabbas tsagewar ƙashi ce,” ya ce a hankali.
“Zan sa ayi X-ray scan yanzu, amma ina buƙatar a kwantar da ita.”
Aka kira ƴan aiki biyu suka shigo da gadon hannu (mobile stretcher), suka ɗauke da hankali, naji jiki na kamar guga.
Hajja tana binmu da addu’a, tana cewa,
“Allah ya saukaka miki ramlah.”
Aka tafi da ni Royal Infirmary da aka tanadar musamman ƙamshin disinfectant da white jasmine na Zara’u na gauraye cikin iska.
Bayan an gama dubawa, Doctor Idris ya ce a yi min allurar bacci kafin suyi abunda zasuyi.
Na ji kaina yana nauyi, komai ya fara juya min a hankali. A ƙarshe, na ji muryar Zara’u tana faɗi, “Bismillahi, ku riƙe ta a hankali.”
Daga nan kuma, ban sake sanin komai ba.
Da asuba ma ƙarar kiran sallah tana yawo cikin harabar asubutin. Nurse Hauwa ta shigo da tray ɗin allura a hannunta, tana sanye da farin rigar.
“Ranki ya daɗe, likita ta ce a yi mata allura kafin a haɗa ruwan zafi,” ta ce da ladabi, tana gaishe da Hajja.
Hajja, wacce take zaune a gefe tana lazumi, ta ɗaga kai cikin damuwa.
“To, yi, amma ki yi a hankali. Jikinta kamar wuta yake.”
Na ji yadda Nurse ɗin ta shafa min hannu da auduga, sannan ta saka allurar a hankali.
Wani irin zafi ne ya shige ni, har sai da na saki ƙaramar ƙara.
“Wayyo Allah na!”
Dr. Zara’u ta shigo daga ɗaki ɗaya tana ɗauke da tray na tea “Yanzu Ramlah,” ta ce cikin taushi, “za mu haɗa miki ruwan zafi, ki shiga ciki. Wannan zai taimaka wajen rage zafin.”
Nana hadiza
09030569336
[22/11, 9:07 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA CASA'IN DA SHIDA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Lokacin da na ɗan tashi daga kan gadon, sai na yi tunanin ana saka min reza ne a ƙasana saboda irin azabar da nake ji.
Radadin ya yi tsanani sosai, har sai da na fashe da kuka ina ambaton Allah.
“Wayyo Allah na, Hajja!”
Hajja ta zuba min ido cikin tausayawa, sai kuma tafara da magana cikin ɓacin rai.
“Yarinyar bata haihuwa ba, amma an mata ɗinki Ga tsagewar ƙashi, ga azaba kamar ta mace mai nakuda.Wallahi Asad bai kyauta ba ko kaɗan.”
Dr. Zara’u ta ɗan sauke numfashi tana fadin,
“Hajja, hakuri za a yi. Abin da ya faru, ya riga da ya faru.”
Ai basu gama rufe baki ba, sai wayar Hajja ta fara ringing. Ta ɗaga tana faɗin cikin fushi, “Asad ne ko?
To ka saurara! Wallahi baka kyauta ba!
Ga yarinya nan, jiya bata yi bacci ba saboda azaba. Ashe ba buguwa ba ce, tsagewar ƙashi ce!” Muryarta ta cika da ɓacin rai, tana magana tana faɗa
Daga ƙarshe ta kashe wayar tana fadin,
“Allah Ya kyauta!”
Dr. Zara’u ta matsa kusa da ni ta taimaka min na zauna. “Ramlah, bari mu tafi bandaki. Ruwan nan mai zafi zai taimaka wajen wanke rauni.”
Ta kira ƴar aikin asubutin, mai suna Maryam, ta kawo wheelchair ɗin da aka yi da leather upholstery. Aka taimaka min na zauna a kai, na ji kamar an cire min rai saboda zafin.
Lokacin da muka shiga bandakin, naji ƙamshin rose-scented steam ya buge ni.
Tiles ɗin kasa suna sheƙi kamar madubi, ƙasan ruwa na zuba daga golden tap cikin porcelain bowl mai ɗauke da gishiri.
“Bismillahi,” Zara’u ta ce, tana zuba ruwan ɗumi cikin bowl, sannan ta haɗa da gishiri.
“Ramlah, ki daure kin ji? Wannan shi ne zai taimaka wajen hana infection.”
Da suka taimaka min na shiga sai wani irin ƙara ta kuɓce daga bakina.
“Wayyo Allah! Ruwan nan kamar wuta!”
Na riƙe bango da hannu ina kuka, hawayena suna haɗuwa da zufa.
Zara’u ta rike ni tana rarrashina kamar yaro.
“Ki daure, Ramlah. Ba za mu jima ba.”
Bayan sun gama, Zara’u ta taimaka min na koma wheelchair, ta kaini gadon asibitin.
“Hajja,” ta ce cikin natsuwa, “na gama. Amma dole a kula sosai.Yanzu zan bata maganin zazzabi, sannan in yi mata allura ta bacci domin ta huta.”
Na ji jikina yana rawa saboda zafi da gajiya.
Hajja ta zauna gefena tana share min zufa da white towel.“Sannu Ramlah. Allah Ya baki lafiya. Na yi ƙoƙarin yin magana, amma muryata ta makale.
Zara’u ta ɗauko injection tray ta haɗa allura cikin nutsuwa. “Ramlah, wannan zai sa ki huta. Ba tada zafi sosai.”
Da ta saka allurar, wani irin sanyi ya lullube ni.
Numfashina ya fara laushi, hasken fitila ya fara birgima a idona, sai na fara jin komai na nisa.
Hajja ta yi addu’a a hankali tana fadin,
“Allah Ka kawo mata lafiya. Ka sauƙaƙa mata, Ya Rahman, Ya Rahim.”
A hankali na lumshe ido, zuciyata na rawar jiki,sai na ji kamar ana ɗauke ni daga duniya zuwa wata duniyar daban duniyar da babu zafi, babu kukan ciwo, babu radadin da nake ji yanzu.
Cikin baccin da ya yi nauyi, na fara jin kamar ana shafawa a wuyana kamar ana kokarin zura hannu aciƙin rigata hannaye masu dumi, masu taushi, suna bin fatar jikina a hankali kamar ana ƙoƙarin tabamun breast dina.
Na buɗe idona a hankali, hasken fitar ɗin dake dakinya faɗa a idanuna, sai na hango Asad tsaye a gabana, yana kallona da fuskar da ta nuna gajiya da tashin hankali.
Hajja kuma bata ciƙin dakin ma gaba daya
Kafin in fahimci komai, sai kawai na ga Asad ya juya ya sa key a ƙofar,
sannan ya dawo kusa da gadona, numfashinsa yana fita cikin sauri.
“My Lah-Lah…” ya furta da muryar da ke sanyi amma cike da girgiza zuciya.
“Please mana, kidaina kuka.
Wallahi jiya ma ban iya bacci ba saboda tunaninki.”
Ya durƙusa a gefen gadon, hannunsa na neman hannuna a hankali.
Jiƙinsa yana dumi, ƙamshin turaren Oud Amber Blend ɗinsa ya cika dakin,
yana gauraye da ƙamshin magungunan da ke kusa da gadona.
“My Ramie…” ya ce yana kallona cikin ido,
“Stop crying, please.
I can’t stand to see you like this.
Kin sani ai… you are my peace.”
Na kasa magana, hawaye kawai suka cigaba da sauka daga idona. Na juyo gefe, amma sai kawai na ji hannunsa ya rungumeni a hankali daga gefe,yana shafa kaina kamar yana rarrashin yaro.
“Please,” ya ce cikin rauni,
“ki yarda dani.
Na san na cutar da ke, amma wallahi…
zuciyata bata taɓa dukan haka ba akan wata mace sai ke.”
Jiƙinsa yana radamun jikina saboda dumin zafin jiki da gajiyarsa. Na tureshi da rauni ina fadin cikin kuka,
“Just go… please… am scared.”
Ya tsaya yana kallona da idanunsa masu duhu,
idanun da suke da saurin bayyana abin da zuciyarsa ke faɗi fiye da harshensa.
“Ramlah…” ya faɗa cikin sanyi.
“Ba zan taɓa cutar dake ba.
I swear to God, I love you.
Ki daina tsorata da ni.”
Knocking ɗin ƙofar ne ya katse shiru.
Sai ya miƙe, ya nufi ƙofar ya buɗe, hasken waje ya faɗo cikin dakin.
Hajja ta tsaya a ƙofar da idanunta masu cike da fushi da damuwa.
“Asad,” ta ce cikin murya mai ɗaci amma natsattsiya,
“zo ka fita kafin ranka ya baci.
Me kake ƙoƙarin yi haka?
Bakaga halin da ka jefa yarinya nan ba?
Kalli idonta tun jiya kuka takeyi!”
Muryarta ta cika dakin, tana haɗuwa da ƙamshin turare da sanyin iska daga AC.
“Bansan sanda ka zama haka ba wallahi,” ta ƙara, tana girgiza kai.
Asad ya juyo, yana duban kasa cikin kunya.
“Ki yi hakuri, Hajja,” ya ce da murya mai rauni.
“Zan tafi yanzu.”
Sai ya karaso gefen gadona ya sunkuya,
yana kallona da idanun da suka cika da hawaye da ƙauna.
“My Lah-Lah…” ya faɗa cikin sanyi,
“I’m travelling today.
Ga wayarki nan na kawo miki.
I will be calling you everyday.
Please ki kula da kanki.”
Ya ɗan tsaya, yana dafa hannuna a hankali.
“Ina sonki, Ramlah.
Ina sonki sosai.
Allah Ya yi miki albarka, Ya kula da ke.
Ki daina kuka… kin ji?”
Murya ta makale, hawaye suka ci gaba da zuba.Na iya jin ƙamshin turarensa yana cika numfashina, yana barin wani irin dumi mai sanyaya zuciya amma mai zafi a lokaci guda.
Hajja ta juyo gefe tana share hawayenta, ta kasa cewa komai.
Asad ya ɗora wayar a gefen gadona, ya ɗan matsa ya dafa gashina da taushi.
“Ki kula da ranki, kin ji?
I’ll miss you… My peace.”
Ya miƙe, ya ɗauki mukullensa, sannan ya nufi ƙofar. Kafin ya fita, ya juyo ya kalle ni na ƙarshe. Haske ya bugi fuskar sa, idanunsa suna nuna ƙauna da nadama lokaci guda.
“Take care, My Lah-Lah…”
Ya fita cikin natsuwa, ƙamshin turarensa ya cika dakin gaba ɗaya har bayan fitarsa.
Na kifa kaina a kan pillow mai launin cream gold, hawaye suna bin kuncina.
Hajja ta dawo ta zauna a gefena, tana shafa kaina cikin taushi.
Da rana ta fara haske, dakin Royal Infirmary ɗin ya cika da ƙamshin turaren white jasmine da Zara’u ta shafa. Fitilun golden chandelier na sama suna ɗaukar hasken rana ta cikin gilashin taga, suna dinga yawo a bango.
Ni kuma ina kwance, jikina yana ɗan sauƙi, amma har yanzu nauyin ciwo da gajiya suna lullube ni.
Hajja tana zaune a gefe tana karatun Alƙur’ani cikin nutsuwa, Zara’u kuma tana duba medical file ɗina tana rubuce-rubuce cikin note pad ɗinta.
lokaci kaɗan sai muka ji ƙarar takalman mata a gefen ƙofar. A hankali aka turo ƙofar, sai matan sarki suka shigo cikin shashensu na alfarma sanye da abaya masu launin royal blue da gold trimmings, ƙamshin turarensu yana ɗaukar iska gaba ɗaya.
Hajja ta tashi ta amsa musu da girmamawa, ta nuna musu su zauna.
“Sannu da zuwa, ‘yan uwa,” ta faɗa da murmushi. “Allah ya sa alkhairi.”
Uwargida ta fara magana cikin natsuwa,
“Mun ji labarin rashin lafiyar amaryar Asad, muka ce sai mun zo mu gaishe ta.”
Zara’u ta ɗan gyara hijabinta cikin ladabi, ta amsa musu,
“To, Allah ya saka da alkhairi. Alhamdulillah tana samun sauƙi yanzu.”
Uwargida ta ɗan matsa kusa da ita, tana kallona daga nesa cikin murmushi.
“Ai kam ta yi kyau sosai, duk da bata da lafiya wayasani ma ko mun samu baƙo.”
“Toh,” wata daga cikin su ta ce da muryar dake nuna ta saba da fada,
“amma naji ana cewa wannan yarinyar ai an taɓa aurenta, ko Zara’u?”
Ni da Hajja muka yi shiru, muna jin su, amma babu wanda ya motsa.
Kunya ta lullube ni daga ƙafa har kai.
Zara’u ta ɗago idanunta daga takarda ta kalli mahaifiyarta wacce itace ke tsakiyar su,
ta ce cikin natsuwa “gaskiya yarinyar nan budurwa ce. Mun tabbatar da hakan da gwajin da muka yi. ba’a taɓa saduwa da ita ba.”
Dakin ya yi shiru na ɗan lokaci. Kowa yana kunyar yadda zara’u tafadi maganar kai tsaye
Sai daga baya uwargida ta ce cikin mamaki,
“To, amma kin san dai yarinya ce da ta taɓa zama a gidan aure, ko?”
Zara’u ta gyada kai cikin ladabi.
“Wannan yarinyar dai virgin ce sosai.”
Sauran matan suka fara yin maganganu cikin ƙasa-ƙasa,wasu kuma suna ta murmushi kamar da mamaki.
Hajja da ke gefena ta lumshe ido, tana murmushi cikin zuciyarta.Ni kuma kunya ta gama lullube ni. Idanuna suka cika da hawaye ba na ciwo ba, ba na tsoro ba,
sai dai saboda jin yadda ake magana a kaina.
Zara’u ta kalli su cikin ladabi amma da murya mai nuni da ƙarfin mata masu ilimi.
“Don Allah, ku bar wannan magana, ku bar wannan yarinya ta samu natsuwa.
Ba lokaci bane na maganganu.
Lafiyarta ce kawai muke nema yanzu.”
Uwargida ta gyada kai da murmushi.
“To, haka ne, haka ne, likita.
Muna mata fatan alkhairi.”
Suka miƙe cikin natsuwa, suna fita ɗaya bayan ɗaya, ƙamshin turarensu yana bin su.
Bayan fitarsu, Dr zara’u tace “ƙinji ko hajja suna can anata gulma kala kala saboda rashin aikin yi ko me ruwansu.” Hajja da ranta yagama ɓaci tace “ Ai haka sarautar take babu sirri komai a banƙade.
Nana hadiza
09030569336
[24/11, 10:41 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA CASA'IN DA BAKWAI
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Hajja ta fita zuwa masarauta, bayan ta tabbatar da na sha magunguna.
Dakin ya yi shiru, sai ƙamshin Oud Amber da Dr Zara’u ta shafa kafin ta fita.
Lokacin da ta dawo, ta miƙo min waya tana murmushi mai natsuwa.
“Ga wayarki, ranki ya daɗe,” ta ce, sannan ta juya ta fita don ta duba sauran marasa
Na ɗan dafa wayar a hannuna, zuciyata tana tsinkayar sautin da nake tsammanin zan ji.
A hankali na kara ta.
“Hello, my queen…”
Muryarsa ta fito cikin rauni, cike da ƙauna da damuwa. Da sautin, kamar murya mai sa zuciya ta yi rauni, na amsa a hankali “Na’am…”
Ya sauke numfashi mai nauyi irin wanda ke fito da zafin da zuciya ke ɗauka.
“Na ji muryarki,” ya faɗa cikin taushi.
“Amma kamar baki da ƙarfi… kin sha maganin kuwa?”
Na yi shiru na ɗan lokaci, zuciyata na bugawa cikin rauni.
Sai na ce cikin muryar da ke rawa “Jikina ne kawai Nasha…”
“Subhanallah,” ya ce, murya cike da tausayawa.
“Kin san bana iya son jin haka ko?”
Na amsa da ƙyar, kamar wacce numfashi ya ke neman ƙarewa “Eh… suna dubani.”
Sai na ji shiru a can ɓangaren, sannan muryarsa ta dawo a hankali tana raɗa kamar addu’a “My lah lah, ki sani ina cikin jirgi yanzu, amma wallahi tun da safe zuciyata tana bugawa saboda ke. Ko ina nake, kina cikin zuciyata. Kiyi hakuri ina kara baki hakuri ƙinji banyi haka da gangan ba.”
Ya ɗan yi shiru, kamar yana sauraron numfashina da ke fita a hankali daga ɗayan ɓangaren. Sai ya ce da rauni “Kiyi haƙuri, kin ji, my love? In shaa Allah, za ki warke.
Allah Ya baki lafiya. Da zan iya, da na canza wannan zafin da kike ji in ɗauka a jikina.
Amma ina nan ina addu’a ki warke, kin ji?”
Na kasa magana.
Hawaye suka zubo daga idona, saboda yadda muryarsa ta cika da soyayya da tausayawa.
Sai na ji ya sake magana, muryarsa ta yi rauni sosai.
“Ina sonki fiye da duk wata kalma da zan iya furtawa. Ki rufe idonki, ki huta.
Ki tuna da murmushinki murmushi ɗaya naki yafi min kwanciyar hankali da komai.”
Na ɗan yi shiru, ina sauke ajiyar zuciya, sai numfashi kawai ke fita daga bakina.
Ya sake magana cikin sanyi,
“Kiyi shiru yanzu, ki huta kin ji?
Na fi son jin numfashinki fiye da kalmanki.
Zan kira ki da zarar jirgin ya sauka.
Amma ki sani da dukkan ƙaunar da Allah Ya bani, ina sonki sosai.” Sannan cikin sanyi ya ƙara cewa
“Ki kasance da ƙarfi, masoyiyata.
Ki jira dawowata.
Domin ni da ke soyayya ba ta yankewa.”
Na lumshe ido, hawaye suna sauka a hankali a kuncina. Muryarsa ta tsaya, sai na ji ƙarar da ke nuna ya kashe wayar.
A can gefen duniya, shi kuma ya jingina da kujerar jirgin, ya kalli hotona a wayarsa, yana shafawa kamar yana taɓawa da gaske.
Ya furta cikin muryar da ba kowa ke ji ba,
“Ya Allah, ka bata lafiya Ka kiyaye min masoyiyata, domin ita ce sashin zuciyata.”
Hawayen da bai iya boyewa ba suka zubo,
sai ya ɗaga kansa sama, yana murmushi cikin raɗaɗin ƙauna da addu’a ɗaya “My Lah-Lah… my peace. I will love you till the end.”
****
Ɗinkin nan da aka yi min a asubutin nan, daya ne daga cikin irin azabar da mata ke fuskanta, azabar da kalma bata iya bayyana sai wadda Allah Ya jarraba da ita. Zafin da nake ji a lokacin ya zarce tunani, amma duk da haka, akwai wani irin sanyi da kulawa da na keji daga mutanen da suke kewaye da ni. Da gaske, in ba da ƙaunar da nake gani daga Hajja da ahalin ba, da na kasa ɗaukar wannan yanayin.
Mutane dayawa sun zo suka duba ni. Ko momy ma tazo tare da su Yaya Aliya, tana kallona da idanun mamaki da tausayawa. Abba kuwa, bai iya zuwa ba, amma ya kira ni a waya da muryarsa mai taushi yana faɗin, “Auta, ki kasance mai haƙuri. Allah yana tare da mai jurewa. Zafin nan da kike ji, da sannu zai zama tarihin ƙarfi, ba ciwo ba.” Na kasa magana, sai hawaye suka gangaro min a hankali saboda irin yadda kalamansa suka shafi zuciyata.
Su Yaya Usman ma suna kira daga nesa, suna bani kwarin gwiwa. Uncle Hamza da matarsa ma sun zo, suka zauna kusa da Hajja suna ta bani labarin gida da dariya, suna ƙoƙarin sauya yanayin zuciyata. Da gaske kulawar da nake samu daga masarauta ta sanya na fara jin sauƙi, saboda soyayya tana warkar da ciwon da magani baya iya warkarwa.
Amma su Yaya Aliya kam, sai tsokana. Tun bayan da suka zauna, sai ta kalle ni da dariya ta ce, “To, Ramlah, kin ga garin soyayya an karyo kafa. Ashe, ƙauna ba ta zuwa da furen turare kaɗai ba, har da dinki.” Hajja ta yi dariya tana girgiza kai. “Ke Aliya, baki da dama wallahi. Ki bari, yarinya bata da lafiya fa.” Amma Yaya Aliya sai dariya take, ta ɗora da cewa, “Hajja, ai soyayya bata cika ba sai da ƙanƙance kafa.”
Ni kuwa kunya ta lullube ni gaba ɗaya, sai na ce cikin dariya mai rauni, “Hajja, ki ji fa Yaya Aliya.” Ta ce, “kyaleta kinji.” Dakin gaba ɗaya ya cika da dariya.
Bayan sun tafi, na kwanta a kan gadona ina kallon rufin ɗakin. Fitilar da ke saman dakin ta yi haske mai laushi, tana haskaka bango da ƙamshin turaren oud wood da ke yawo a iska. Hajja tana zaune a kusa dani, tana karatun Yasin da muryarta mai sanyi wacce ke kwantar da hankali. Na ji hawaye suna gangarowa a kuncina, amma wannan karon ba na ciwo bane na jin ƙauna, na jin rahamar Allah da kulawar da ke kewaye da ni.
*********
Bayan sati guda da sallamowa daga Asubuti, jikina ya soma samun sauƙi sosai.
Zafin da nake ji a ƙafata ya ragu, sai ɗan kaikayi na warkewa. Numfashina ya koma daidai, amma har yanzu jikina yana da rauni kamar wanda aka sake ƙera shi da sabuwar ƙarfi.
Ina kwance a ɗakin Hajja, wanda ƙamshin turaren Oud Al Qamar yake yawo a cikinsa, yana gauraye da ƙanshin magani. Labulen suna kadawa a hankali da iska mai sanyi daga AC. Wurin yana da kyau sosai, fitilun crystal na sama suna haskawa.
Hajja ce ke kula da ni tamkar jaririya.
Duk lokacin da na ce bana jin yunwa, sai ta ɗauki faranti ta matsa kusa dani. “Ramlah, ki ci abincinki, kin ji? Ki sha magani. Dole ki ƙara ƙarfi kafin Asad ya dawo, kada ya ganki haka.” Sai ta saka murmushi mai cike da ƙauna, ta gyara min bargo, sannan ta dafa min kafata da man shafawa mai ƙamshin mint balm. Kullum ina kallon Hajja da mamaki irin kulawarta da tausayinta sun zarce bayani sai iyaye. Da rana kuwa, Firdausi ce ke ɗebemun kewa. “Aunty Ramlah, yau na kawo miki fruit salad! Wallahi, hajja tace sai kin ci domin kiyi kyau sosai kamin mijinki yadawo. Sai ta ɗora min kwano a gefe, tana zaune ta fara labari.
Na murmusa cikin natsuwa, na ce “ Antyna nifa wannan kazar banajin dadinta.” Ta fashe da dariya tana cewa “Haba My Lah-Lah ɗin yaya ki daure kici mana uhmm….bari dai nayi shiru” Dukkan maganarta ta saka ni dariya, ta ɗan ɗauke min hankali daga tunanin da nakeyi. Mutanen masarauta kuma suna yawan zuwa dubani. Suna gaishe da Hajja da ni da girmamawa. Wasu na yin addu’a da gaske, wasu kuma sai murmushi mai zurfi wanda ke nuna magana a bayan murya.
Wata daga cikinsu, mai suna Hajiya Saffiya, ta shigo da kyautar ƙaton turare ta ce“Allah ya baki lafiya, amaryar ɗan sarki.
Munzo muganki, tunda yanzu kin murmure, sai haihuwa kawai!” Na yi murmushi da ladabi, na ce “Allab yasaka da alkhairi.”
Dr. Zara’u kuma bata barni ba.
Kullum da safe tana zuwa da takardarta da stethoscope ɗinta tace mun “Ramlah, yau kin fi jiya kyau sosai. Kawai ki ci abinci sosai, ki huta. Ki daina jin tsoro ko damuwa, domin jiki yana jin dukkanin damuwa da take a rai.”
Tana gayamun haka sai ta rike hannuna da laushi, tana fadin,“Kin san me? Asad ya kan kirani kullum yana tambayarki.Na gaya masa jikinki yana kyau sosai.Sai ya ce in gaya miki, ‘My peace should not cry again.’”
Na ji idona ya cika da hawaye, amma na dan murmusa. “Nagode, Likita. Ki gaya masa naji sakonsa.”
Da yamma kuwa, bayan kowa ya fita, sai direban Asad ya kawo wata ƙaramar gift box mai ɗauke da furen white roses. A ciki akwai ƙaramin katin rubutu mai ɗauke da ƙamshin turarensa“My Lah-Lah, ina fatan kin murmushi yau. Don murmushinki yana bani natsuwa. I’m counting the days to see you again.”
Na karanta sakon sau biyu, zuciyata na rawa kamar akwai murya a ciki. Sai na ɗaura hannuna a ƙirjina, na lumshe ido cikin natsuwa. Na ce cikin raina “Ya Allah, ka dawo min da shi lafiya.”
Da dare, bayan na yi sallah, Hajja ta dawo da warm milk a kofi mai launin fari “Ki sha ki kwanta, Ramlah,” ta ce cikin tausayi. “Kin yi kyau sosai yanzu gashi har jiƙinki yadawo.”
Na ɗauki kofin na sha a hankali, sai na lumshe ido. Zuciyata ta cika da godiya.
“Alhamdulillah,” na furta a raina.
*****
Washegari Ina zaune a babban palour na Hajja, ina sanye da doguwar riga mai launin emerald green, ƙamshin Jasmine Mist yana fita a jikina. Hajja tana gefena tana ba ni labari cikin natsuwa, Firdausi kuma na waya tana dariya tana cewa, “Aunty, Mamy tace in tambayeki, kin fara cin cake ɗin da aka aiko daga palace kuwa?” Na murmusa kadan, na ce, “Ba tukuna ba, amma zan ci. Allah ya saka da alkhairi.”
Daidai lokacin muka ji ana kwankwasar ƙofa. Ɗaya daga cikin baiwan Hajja ta shigo cikin ladabi tana fadin “Ranki ya daɗe, akwai wata mata a ƙofa ta ce ta zo gaisheki.”
Hajja ta gyara zama, ta ce,
“To, shigo da ita mana.”
Na ɗan miƙe zaune, ina sanye da shawl na lulluɓe fuskata saboda nagaji da kwanciyar.
Ba a dade ba sai ga wata kyakkyawar mace ta shigo ko baa gayamun ba nagani.itace ayshatu dan naga kamar nawal a tattare daita kamshin oud rose na bin ta.Ta durƙusa ta gaishe da Hajja cikin ladabi. “Lafiya lau, Hajja, dama nazo gaisuwa.” Hajja ta kalleta da murmushi, sannan ta ce “ Ayshatu ashe ƙinzo to madallah sannunki.” ayshatu ta murmusa tana fadin, “Wallahi Hajja.”
Na ɗan gyara zama cikin ladabi na gaishe ta, “Sannu da zuwa.” Ta amsa da fara’a tana cewa, “Allah ya ƙara lafiya, ya sauƙaƙa miki.”
Hajja ta ƙara da cewa “Eh, bata jin daɗi ne, shi yasa nake rike da ita a nan.
Amma yanzu, Alhamdulillah tana ƙara samun sauƙi.”
Ayshatu ta ce dakyar, “Allah ya baki cikakkiyar lafiya.” “Ameen,” Hajja ta amsa, tana murmushi. Sai dai tun da ta shigo, take kallona kamar tana son tuno wani abu da ta manta. Ni kuma zuciyata na bugawa, saboda kamanninta sun tuna min da Nawal.
Bayan ta fita, na koma ɗakina.
Da zarar na zauna a gado, wayata ta fara ringing. Na duba My Heartbeat ne a rubuce.
Sai zuciyata ta doka da sauri, hannuna na rawa na ɗaga wayar. “My Lah-Lah…”
Muryarsa mai sanyi ta jiƙa kunnena, kamar yana kusa da ni.
“Menene? Kin yi shiru?”
Na ɗan yi shiru, na kasa magana.
“Please, answer me mana. Kada zuciyata ta tarwatse.” Cikin jin kunya da motsin rai nace a hankali, “Ni... kabarni ni kadai. Ka dawo kawai.” Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan muryarsa ta sake narkewa “Ƙinsan yadda nake kewarki kuwa? I can’t even sleep, Ramlah. Amma ki yi haƙuri, just one week more... zan dawo.” Na ɗan tura hanci cikin bargo, na ce da murya ƙasa,
“One week? For real?”
Sai kawai na ji dariyarsa mai nutsuwa daga can. “Yarinya ashe kina sona sosai.
Am on my way, in shaa Allah, My lah lah…”
Na murmusa ina jin zuciyata tana rawa.
“Yaya, ni dai bansan ko na warke ba.”
Ya yi dariya ya ce, “Toh, ni zan tabbatar da hakan da zarar na dawo. Allah Ya kiyaye ki, My Lah-Lah.” Ya kashe wayar, amma kalamansa sun ci gaba da yawo cikin kunnena kamar sauti mai daɗin kiɗa.
Na kwanta a kan gadona, na rungume pillowna, hawaye masu daɗin soyayya suna zuba a hankali. “Allah… ka dawo min da shi lafiya.”
Nana hadiza
09030569336
[24/11, 10:41 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA CASA'IN DA TAKWAS
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Washegari bayan na idar da sallar asuba, sai na koma baccina cikin nutsuwa. Na yi bacci mai daɗi har sai ƙarfe ɗaya na rana kafin na farka. Rana ta riga ta haske sosai, hasken da ke shigowa ta taga yana bugawa a bango, yana bayyana ɗigon haske a cikin ɗaki.
Na miƙe a hankali, jikina yana yin sanyi. Na shiga bandaki nayi wanka da ruwan dumi, na fito na shafa man argan oil da Hajja ta kawo min daga wajen Dr. Zara’u. Sai na ɗauki atamfa bubu mai launin turquoise, na daure kai da gyale mai ɗan haske.
Gabana ya warke sosai, har mamaki yake bani. Zafin da nake ji kwanan nan kamar bai taɓa wanzuwa ba. Wani irin sauƙi nake ji, kamar baniba. Wataƙila saboda magungunan da likitoci suka bani ne, domin gaskiya ban taɓa ganin irin su ba. Duk da haka, a zuciyata ina godiya ga Allah da irin kulawar da nake samu daga Hajja da Asad.
Bayan na fito daga ɗaki, muka zauna da Hajja muka gaisa. Ta kalle ni da murmushi tana tambayata, “To, Ramlah, me kike sha’awa yau a dafa miki?”