Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 37

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 37

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 37: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 37. Na ɗan yi murmushi na ce, “Ni fa yanzu duk abinda aka dafa zanci.…

4,499 words

Na ɗan yi murmushi na ce, “Ni fa yanzu duk abinda aka dafa zanci. Banda zabi ranki yadade.” Hajja ta ce da natsuwa, “Toh,shikenan kiduba dinning din sai kiga me zaki iya ci ko. Yaya jiƙin naki?”. Nace mata naji sauki sai tace “ Alhamdulillah kenan. Da sauƙi ke nan.”

Sai ga Firdausi ta fito daga cikin ɗaki tana riƙe da shopping bag.

Ta tsaya a gabana tana kallona da fara’a, tana ta kamshi da turarenta mai ƙanshi.

“Matar yaya,” ta ce tana dariya, “wallahi kayan nan da kika sa basuyi kyau ba.

Ke fa matar yarima ce, amma kina irin wannan shigar ai sai a ce bamu da mata masu salo acikin masarauta.”

Hajja ta ɗan kalleta tana murmushi, ta ce,

“Firdausi, ke da wannan surutun naki. Duk wannan adon da tayi, kina cewa batayi kyau ba?”

Firdausi ta fashe da dariya. “Hajja ai ba wai batayi kyau bane,

sai dai ina so in ga ta fi haka. Matar mutum mai daraja ai ta dace ta zama abin kallo.”

Hajja ta girgiza kai. “To, amma ki bar maganar.” “Babu komai hajja ki barni please,” Firdausi ta ce tana kallona da murmushi.

“Na yi order na kaya tare da naki, yau za su kawo. Na tabbata zasu miki kyau sosai, domin ina so ki koma cikakkiyar mace, wacce babu wanda zai kawo mata raini a cikin masarauta.”

Na ɗan murmusa cikin kunya. “To, Anty Fidy, nagode sosai. Zan gyara.”

Ta yi dariya. “Babu komai, yarinyar kirki.

Ki sani Ramlah, mace tana buƙatar kula da kanta ba don kowa ba, don kanta.

Koda kina da kyau, ki ƙara salon gayu sosai da ado kinji kisan shigar da zakiyi kayan da yayana yakeso. Sannan ki riƙa saka kaya masu tsafta, masu kyau masu tsada wannan najikinki sun danyi sauki. Kin san mijinki mutum ne mai kima,kuma babban mutum da mutane sukeso suke ji dashi kuma acikin masarautar nan ma mata da yawa suna sonsa sosai.”

Hajja ta dubeta da murya mai taushi. “To Firdausi,bazakiyi shiru ba haka? Ya isa mana banason fitsara fa.”

Firdausi ta ce cikin nutsuwa, “Haba ranki yadade Hajja, nifa ina jinta kamar yaruwata wallahi dole na gayamata gaskiya.”

Na ji kalamansu suna shiga raina.

Na murmusa na ce, “To, na fahimta. Zan kula zan gyara yayata.” Babu komai, ni fa ina so ki koma cikakkiyae macce wacce babu wanda zai kawo miki raini aciƙin masarautar nan kwata kwata,gaki da kyau da sura ai wallahi ki dinga cakarewa wannan dinkin baiyiba zan bawa baiwar dake kaimiki dinki numbar tailor dina shi zai dinga yimiki mai kyau.” Hajja ce tace wai bazakiyi shiru ba?” Murmushi firdausi tayi tace “ DanAllah hajja kibarni nagayamata gaskiya mijinta babbar mutum ne acikin masarautar nan ma wallahi mata harinsa sukeyi ga ayshatu nan ta kaso aurenta duk yadda xatayi ya maidata nasan sai tayi dan haka wallahi Allah ki canza shiga shigarki tazamana wacce idan yayata yaganki zai rikici ba kidinga shigar tsofaffi ba da danyan shekarunki ko janbaki ko kwalli bakya sawa suma fa sunada sirrin jan hankalin namiji ballanta shigar data bayyana ko’ina cif cif ajikinki. In kinji haushi kiyi hakuri ni na daukeki kamar yar’uwata wallahi. Lokacin da ayshatu na auren yayana wallahi Allah ko wucewa tayi sai kin yabeta kada ma akai da magana salo.”

Hajja ta ce tana murmushi, “Allah Ya albarkaceku, ku duka. Na jingina da kujera, ina ta wasa da ring ɗin hannuna, zuciyata cike da kewarsa ta wani bangaren kuma ina jujjuya maganganun firdausi. Duk da yake kullum muna waya, yau ina jin wani yanayi daban. Wani lokaci idan ka saba da mutum sosai, da zarar bai bayyana ba, sai ka ji duniya ta yi shiru.Tashi nayi na hau sama ina shiga daki na danna lambar momy maganganun firdausi suke yawo acikin raina gaba daya cike da damuwa babu yadda tafadi babarsu nawal.to ai ko jiya dana ganta ta haɗu matar ba kadan ba. ina zaune a ɗakin Hajja, sai na ɗauki waya na kira Momy don in gaisheta.

Da ta ɗaga, muryarta ta fito da nutsuwa irin ta uwa mai cike da ƙauna.

“Ramlah ɗiyata, ya jiki? Na ji daɗin jin muryarki wallahi.”

Na murmusa cikin farin ciki. “Lafiya lau Momy. Ina gida, Hajja na kula da ni sosai. Amma kinji abinda Firdausi ta ce min yau?”

Ta yi dariya a ɗayan ɓangaren. “Wai me kuma wannan yarinyar ta sake faɗa miki?”

Na ce da dariya, “Ta ce wai in dinga yin ado….” Nakwashi maganar gaba daya na gayawa momy. Na ɗan yi shiru Momy ta yi dariya sosai har sai da ta ce, “To ai, ɗiyata, da gaske Firdausi take. Ki saurare ni da kyau, Ramlah.”

Muryarta ta koma cikin natsuwa, irin wacce take cike da hikima.

“Ki sani, mace ce ake kira ginshiƙin gida.

Aure fa ba soyayya kaɗai bace, akwai sirruka da ƙawatawa da gyaran jiki.

Ke mace ce, kuma masarauta kike ciki. Namiji idan ya ganki kullum cikin tsari, cikin tsafta da kamshi, sai zuciyarsa ta ƙara natsuwa gare ki.”

Na kasa magana, na saurareta sosai.

Ta ci gaba da faɗi cikin natsuwa

“Dama tun da Zara’u ta gaya min cewa kin warke, nasan lokaci yayi da zaki fara kula da kanki sosai.

Ki dinga saka kaya masu kyau sosai ba wai ado ba su agurin masu kudi kaya masu tsada kenan haka zaki daure kina saka luxury kinji, wadanda suka dace da darajarki, waɗanda ke fidda kwarjini sannan in mijinki na nan adinga saka masa masu bayyana jiki yadda zaiji dadin kallonki.”

Na murmusa a hankali. “Momy, ai yanzu na fara ganin yadda rayuwar sarauta take.”

Ta ce, “Eh ɗiyata, ki sani masarauta na da dokarta. A can babu wanda yake so mace ta zama kamar mara natsuwa ko kuma mara ƙawatawa.Aure a gidan mai martaba tamkar tafiya ce a kan layi sai mace ta riƙa kamewa da kula da kanta.”

Na gyada kai, na ce, “To Momy, zan kiyaye.”

Ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta ce da wata irin murya mai sanyi da tsari“Ramlah, ina son ki fahimci abu guda. Miji yana son mace da ke tsafta, mai kamshi, mai nutsuwa, amma wacce ta san yadda zata ɗauke hankalinsa cikin daki tafiyarki salonki shagwaba duk kikara kinji. Wannan shine sirrin zaman aure ba ta hanyar hayaniya ba, ba ta hanyar nuna ƙarfi ba, sai ta hanyar ladabi da hankali.”

Na ji kalamanta suna shiga raina

“Kin ji ko?” ta tambaye ni.

Na ce da murmushi, “Na ji, Momy. Zan kula, in sha Allah.”

Ta ce, “Toh, Allah Ya sa albarka.

Kuma ki sani, kamar yadda Firdausi ke gaya miki, masarauta tana kallon ku.

Idan kika kiyaye kanki, kika kasance cikin tsafta da natsuwa, zaki mallaki zuciyar mijinki da karramawar gidan gaba ɗaya.”

Na murmusa, ina jin sanyi a zuciyata.

“Na gode sosai.”

Na ce cikin farin ciki, “To, Momy. Nagode. Ina sonki.”

Ta ce, “Nima ina sonki, ɗiyata. Allah Ya tabbatar da alheri a cikin aurenki.”

Na kashe wayar ina murmushi.

Na tashi na duba madubi, na kalli kaina da rigar bubu mai launin turquoise da Firdausi tagama gayamun magana akanta sai nima yanzu naganni kamar su hajja nasaka dariya . Na ɗan juyar da kaina gefe, na ga hasken fuskata yana haskawa.

Da yamma bayan na yi sallar la’asar, na shirya cikin hijabi mai launin cream na tafi masarauta na gaida Mai Martaba.

An karɓe ni da girmamawa kamar kullum, na shiga falonsa da nutsuwa. Ya kalle ni da murmushi yana cewa, “Ramlah, kin ƙara lafiya sosai. Allah Ya ƙara miki lafiya.”

Na durƙusa cikin ladabi, na amsa da, “Ameen, ranka ya daɗe.”

Mai Martaba ya saka mini albarka, ya ce, “Ki koma ki huta. Kin cancanci kulawa.”

Na gode, na fita daga falon cikin natsuwa.

Da na koma bangaren Hajja, ta ce cikin annuri, “Ramlah, yau na yanke shawara, ki koma shashinki. Ai yanzu kin samu lafiya.”

Nana hadiza

09030569336

[24/11, 10:41 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA CASA'IN DA TARA

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Na ji sanyi a zuciyata, amma sai na ce da murmushi, “To Hajja, idan kina ganin lokaci yayi, zan koma.”

Ta ce, “Ai lokaci yayi. Gidanki fa yana jiranki, kiji kiyi shirye shiryen mijinki yana nan dawowa.”

A wannan lokacin, iska mai sanyi ta fara kadawa daga wajen masarauta. Rana ta fara dusashewa, kuma iska tana ɗauke da ƙamshin incense da ake kunna wa a ƙofar fadar.

Sai dai kuma a daidai lokacin, wani labari mai nauyi ya bayyana cikin masarauta. A rana ɗaya kacal, labari ya bazu kamar wuta cikin ciyawa.

Cikin yamma, mutane suna ta kai-komo, hayaniya ta cika cikin fadar sarki. Muryoyin masu gadi suna yawo, wasu matan gida suna ta fadin “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”

Na kalli Hajja cikin mamaki. “Hajja, me ke faruwa haka?”

Ta tashi a hankali, ta ɗan dubi kofa, sannan ta ce da mamaki, “Ba kin ji ba? Waziri... an ce an kama shi.”

Na buɗe ido. “An kama shi?”

Ta sauke numfashi, ta ce, “Ai ashe ma, akwai munanan ayyuka da yake aikatawa a bayan masarauta. Ana bincike ne, aka gano yana haɗa baki da wasu ‘yan siyasa wajen fitar da bayanai na sirri.”

Na kasa magana, zuciyata ta buga da sauri.

Waziri dai mutum ne da ake girmamawa sosai a fadar, yana kusa da Mai Martaba. Ban taɓa tunanin haka ba amma tunawa danayi dashine fa yasanyawa asad magani sai nayi shiru.

Cikin daƙiƙa kaɗan, hayaniyar kuka da ihu ta fara tashi daga bakin fadar.

Ni da Firdausi muna zaune a falon Hajja, ina duba Instagram, ita kuma tana cin abinci cikin natsuwa. Sai muka ji hayaniya daga ƙofar waje muryoyi na mata suna kuka, sai kuma ƙaran takalma da murya mai rauni tana roƙo.

Hajja tana sama, amma cikin ƴan mintuna ta sakko da abayarta mai launin shudi, fuska ɗauke da natsuwar mace mai daraja.

A bakin ƙofar, na hango mata uku masu kamanni da juna, kyawawa amma fuskar su cike da hawaye.

Matar da ke gaba babba ce a cikinsu, tana riƙe da ƙaramin veil a hannu.

Hajja ta tsaya tana kallonsu, tana fadin cikin mamaki

“Au, Laila ce? Ke kika kwaso yara kuna kuka haka? Da girmanki?”

Matar babba ta share hawayenta, ta durƙusa da girmamawa.

“Hajja, don girman Allah, kuyi hakuri da abinda Waziri yayi muku.

Wallahi nasan bai kyauta ba. Amma ki dubi yaransa suna cikin damuwa.

Ku gafarta musu saboda Annabi (SAW), amarya dan Allah ku duba yarana.”

Na kalle ta cikin tausayi, amma ban ce komai ba. Ƴar cikinta ɗaya ta juyo ta kalle ni da harara, ta kafe ni da ido kamar zata hadiye ni.

Sai na mayar da kallona wayata, ban tanka ba na cigaba da kallon hotuna a Instagram, kamar babu wanda ke cikin ɗakin.

Firdausi kuwa, kamar ma bata ji komai ba.

Ta ɗora fork ɗinta ta cigaba da cin dankali da salad cikin natsuwa, har ƙamshin Oud Intense ɗinta ya cika dakin. Ko ɗaya daga cikin matan bai kuskura ya yi mata magana ba sun san halinta, mai ƙyamar rigima.

Hajja ta tsaya tsayin minti ɗaya tana kallonsu, sai ta sauke numfashi, muryarta ta cika da zafi da ƙarfin iko.

“Laila, yanzu baki ji kunyar shigomun fada ba?

Duk abinda Waziri yayi mana, banda nawa ma tunda nazo wannan gidan, bai taɓa kyaunata ba, bai nuna kauna ba.

Bayan Asad ɗina, wanda yafi kowa masa hidima, shine yafi kowa tsananta masa!”

Ta ɗan tsaya, ta kalli su ɗaya bayan ɗaya.

“Ki tuna Laila, sau uku fa yana saka masa guba! Sau uku!

Bayan yasan Asad bai kaunar sarauta, bai sha’awar kujerar iko amma sai ya mayar da shi abokin gaba.

To wallahi, duk hakuri ba bazan bayar ba, saboda nima uwa ce wadda ta san zafin yaranta.”

Kalmarta ta ƙarshe ta fita da murya mai nauyi, ta sa kowacce daga cikin matan Waziri ta durƙusa da kuka.

Wata daga cikinsu ta ce, “Hajja, wallahi mu ba mu da hannu. Don Allah ki tausaya mana.”

Sai Hajja ta juya gefe, ta ɗaga hannu cikin natsuwa.

“Allah Ya kyauta, ku tafi. Amma duk inda Waziri yake, ya sani hukuncin Allah ba ya fasa masu zalunci.”

Matan suka fita da sauri, suna share hawaye, suna rera addu’a da roƙo.

Da suka fita, Firdausi ta juya ta kalli Hajja cikin jin haushi.

“Hajja, ai ke kika saurare su. Ni wallahi ko kallo basu isheni ba, munafukan banza da wofi. Duk cikin gidan nan sai yanzu suka tuna da a tausaya musu saura gimbiya maryam itama?”

Hajja ta kalle ta cikin natsuwa, ta ce da murya mai taushi amma da ma’ana,

“Firdausi, kowacce uwa tanajin zafin yaranta. Amma akwai wasu abubuwa da basu da magani dole a bar su hannun Allah.”

Firdausi ta ɗan yi shiru, ta juya ta ɗauki juice ɗinta tana sha, tana guntse fuska.

Ni kuwa, ban ce komai ba.

Sai na ji zuciyata cike da nauyi, amma kuma wani sanyi yana ratsa ni saboda irin yadda Hajja take magana cikin nutsuwa.

Bayan ɗan lokaci sai aka kira Hajja daga sashen mai martaba.

Ta kalle ni, ta ce da murmushi, “Ramlah, karki damu da irin su. Ki tsaya da natsuwarki. Zaki koma masarauta yanzu, An aiko mota ki tafi shashinki, kin ji?”

Na gyada kai. “To, Hajja.”

Bayan na shirya cikin doguwar riga ta royal blue velvet mai ɗauke da ɗan ado a wuyanta, na saka ƙaramar hijabi mai santsi, na fito.

Sai direban masarauta ya zo cikin nutsuwa ya tsaya a ƙofar falon.

Ya durƙusa da girmamawa.

“Ranki ya daɗe, motarki tana jira.”

Na gyada kai cikin natsuwa, na ɗauki handbag ɗina mai launin cream, na fito.

Ko da muka fito harabar gidan, iska mai sanyi ta bugu da ƙamshin Oud Suhail da ke yawo a cikin falon masarauta.

Motar dake tsaye a gaban farfajiyar, wata daga cikin hadaddun motocin gidan sarauta ce Range Rover SV Autobiography, mai launin milk white, gilashinta a tint, ƙafafunta masu kyalli kamar madubi.

Ɗaya daga cikin masu tsaron masarauta ya buɗe min ƙofa da hannunsa da sauri.

Ya durƙusa da girmamawa.

“Bismillah, ranki ya daɗe.”

Na amsa cikin ladabi, “Na gode.”

Na shiga cikin motar, kujerar leather ta rungume ni da sanyi, ƙamshin air freshener ɗin da ke ciki mai ƙanshin oud & jasmine ya lullube ni gaba ɗaya.

Motar ta fara tafiya a hankali ta cikin harabar masarautar, tana bi ta manyan tituna masu shimfiɗa da ciyayi da furanni masu launin gold da white.

A kowanne wuri da muka wuce, sai jami’an tsaro da bayin gidan ke tsayawa suna gaishewa da ladabi.

“Ranki ya daɗe!”

“Allah ya ƙara lafiya, Uwargida!”

Wasu na durƙusawa, wasu kuma na sunkuyar da kai cikin girmamawa.

Kamar yadda na ga Hajja keyi kullum, sai nake tsayawa in amsa kowanne da murmushi da kalmomin albarka

“Ameen, Allah ya saka da alkhairi.”

“Allah Ya kiyaye ku.”

Wani irin nutsuwa nake ji a raina cike da ƙaunar ganin irin yadda ake girmama gidanmu da mutanen da ke cikinsa.

Ko da yake duk wannan sabo ne a gare ni, amma tunanin yadda Hajja take da ladabi da kame kai yasa nake ƙoƙarin yin koyi da ita.

Da muka isa ƙofar babban sashen da aka ware min, wata ƴar budurwa mai sanye da uniform ɗin palace service ta buɗe min ƙofa cikin natsuwa.

“Maraba da dawowar ki, ranki ya daɗe.”

Na murmusa, na fito cikin natsuwa.

Gaba ɗaya ma’aikatan sashen suka tsaya cikin layi, kowanne yana tsaye cikin ladabi.

Wasu na rike da tray, wasu na tsaye da files na aiki.

Daga bakin ƙofa har cikin babban falon, ana maimaita kalmomi ɗaya:

“Ranki ya daɗe, Allah ya ƙara miki lafiya!”

Na tsaya a tsakiyarsu, na ɗan gyara gyalena, na kalle su da murmushi.

“Na gode, Allah ya saka da alkhairi.

Ina fatan kowa yana lafiya?”

“Alhamdulillah, ranki ya daɗe,” suka amsa cikin murya ɗaya, mai kama da amsa ta masarauta.

Babban palour ɗin na shiga, sai na tsaya cak!

Gaban ido na, komai ya sauya.

Falon da na bar da launin cream da brown yanzu ya koma royal gold and white, haske yana dokar bangon Italian wallpaper mai ɗauke da adon lu’ulu’u masu kyau

Ƙamshin oud Al-Rahman da white musk suka gauraye a iskar ac, suna basu ɗakin kamshin tsarki da alfarma.

Uwar amarya tana tsaye a tsakiyar falon, tana tare ni da murmushi mai cike da ladabi.

Da ta ganni, sai ta tsugunna cikin girmamawa, hannuwanta a kirji.

“Ranki ya daɗe,” ta faɗa cikin murya mai rauni.

Na ɗan yi murmushi cikin kunya, na ce da taushi,

“Dan Allah, ki daina durƙusamun haka. Ai mu duka mutane ne.”

Sai dai ta ɗaga kai ta ce cikin ladabi,

“Ba haka tsarin masarauta yake ba, ranki ya daɗe.

Amarya ko tsohuwa, duk muna kula da ita da girmamawa.”

Sauran ma’aikata suka durƙusa suna gaishe ni cikin tsari, kowanne na faɗin “Ranki ya daɗe, Allah ya ƙara lafiya.”

Na amsa da murmushi ina faɗin “Ameen, Allah ya saka da alkhairi.”

Na cigaba da tafiya a hankali cikin falon, idona na zagaye cikin mamaki.

Sabbin furnitures masu launin gold da white suna kyalli tamkar an shafa musu haske.

A gefen falon, akwai grand piano mai launin milk pearl, a saman shi kuma an ɗora furanni masu launin lavender & white roses.

Fitilun chandelier guda uku masu kyalli suna lumshewa kamar taurari a sama.

Na juyo na kalli Uwar Amarya.

“Uwar amarya,” na faɗa cikin mamaki da dariya mai taushi, “naga guri ya sauya fa.

Ko dai na shiga gidan wata ne?”

Nana hadiza

09030569336

[27/11, 5:22 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ƊARI

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Ta yi murmushi tana fadin,

“Ranki ya daɗe, umarnin Yarima ne.

Ya ce a canza miki komai sabo –daga kayan daki har zuwa interior decoration.

Ya ce ba ya so ki dawo ki ga tsohuwan falon, ya kamata ki fara sabon page.”

Kalmar “umarnin Yarima” ta daki zuciyata da wani irin sanyi mai daɗi.

Sai na zauna a jikin kujera mai santsi, nayi ajiyar zuciya ina murmushi cikin raina.

“Subhanallah,” na furta a hankali. “To saboda Allah, me kayan dakina sukayi?

Duk irin kuɗin da Abbana ya kashe, ace an canza komai?”

Uwar Amarya ta yi dariya cikin ladabi.

“Ranki ya daɗe, tsofaffin kayan suna a waccen sashen, ana jiran umarninki ko a fitar da su gida.”

Na gyada kai, “To, a aikamun su gida kawai.”

Ta sunkuyar da kai cikin ladabi. “To, ranki ya daɗe.”

Na hau sama a hankali zuwa ɗakina, takalmina masu laushi na yin ƙaramar ƙara a kan marble floor.Ƙamshin jasmine & vanilla na fitowa daga gefe.

Da na buɗe ƙofar ɗaki, sai numfashina ya tsaya. Na tsaya a bakin ƙofa na zaro ido, hannuna a ƙirji.

“Yaa Subhanallah!” na furta cikin mamaki da daɗi lokaci guda.

Gaba ɗaya ɗakin ya zama kamar ɗakin sarauniya. Bangon ɗakin an lulluɓe shi da Italian textured silk wallcovering mai launin cream da gold pattern. A gefen dama akwai mirror wall, a gefen hagu kuma akwai bed canopy mai labule daga organza silk mai launin champagne.Kujerun gefen bed ɗin suna kyalli da zane na royal embroidery, a saman side table kuma an ajiye crystal vase ɗin da furannin white lilies.

Na cigaba da tafiya a hankali har zuwa wardrobe area.

Da na matsa kusa, sai taga ta buɗe da kanta automated touch sensor!

Na ce cikin mamaki, “Allahu Akbar!”

Na shiga ciki, sai hasken LED ya kunna da kansa, ya haskaka wardrobe ɗin da ke cike da kayan da ban taɓa gani ba

Dresses masu launin pastel, abaya masu adon stonework, da heels.

A gefe kuma akwai perfume shelf ɗin da aka jera Maison Francis Kurkdjian, Amouage, Tom Ford, Roja Dove, da Baccarat Rouge 540.

Na kasa rike kaina, sai na fashe da dariya ina rufe baki.

“Na shiga duniya ta masu kuɗi kenan! Na zama kamar yar kauye da aka jefa cikin birni!”

Na taɓa rigar dake kusa da ni, tana laushi kamar ruwa. Na zuba ido ga madubi mai cikakken tsayi da aka tsara da gold frame mai ɗauke da rubutun “My Lah-Lah” da gold cursive letters.

Sai na zauna a gaban vanity table ɗin da ke cike da kayan kwalliya.

Na kalli kaina a madubi, murmushi ya subuce daga bakina.

Zuciyata ta cika da farin ciki da tsoron Allah lokaci guda.

Na ɗago kai sama, na furta cikin sanyi“Ya Allah,Ka bani ikon yin godiya da riƙe wannan ni’ima .”

Na lumshe ido, na shafi madubi da yatsana cikin sanyi. Na ce a raina da murmushi mai laushi “Da gaske, soyayyar Yarima ta fi duk wata kyauta da kudi.”

Bayan na gama kallon sabon ɗakina, zuciyata cike da mamaki da farin ciki, sai na ɗauki wayata. Na buɗe WhatsApp, na shiga saƙonninsa “Last seen just now.”

Zuciyata ta buga. Na danna kira cikin tsoro da farin ciki lokaci guda.

Kiran ya shiga, amma bai ɗaga ba.

Na sauke ajiyar zuciya ina murmushi a raina.

“Ko yana meeting ne?”

Kafin na aje wayar, sai ga shi ya biyo kiran.

Na ɗan tsaya na gyara gyalena, sai na ɗaga cikin rawar hannuwa.

“Assalamu alaikum, ranka ya daɗe.

Allah ya ƙara maka lafiya da tsawon rai mai albarka,

Ubangiji ya ƙara girma da arzuki.”

Na faɗa cikin murya mai laushi, cike da ladabi da ƙauna.

Sai na ji muryarsa a hankali, cikin natsuwa da farin ciki, “kin sakani Murmushi my lah lah… amma wallahi raina abace yake.

Yanzu jin kalamanki daga bakinki ne ya sanyaya min rai. Allah ya yi miki albarka bansan ko addu’ar me kika min ba,

amma ina jin kamar zuciyata ta sami nutsuwa.”

Na dan saki ajiyar zuciya, murmushi a gefen bakina. Cikin sanyin murya na ce,

“Ranka ya daɗe, duk wanda ya bata maka rai… kayi masa hakuri don Allah.

Zuciya da haƙuri su ne ginshiƙan mulki.”

Ya yi shiru na ɗan lokaci, sai kuma na ji muryarsa ta dawo, mai sanyi kamar iska mai ɗauke da ƙamshin turarensa.

“Nakiya sai munyi video call tukunna.

Ina so in ga fuskarki, in tabbatar kina lafiya

kin san kwana biyu ban ganki ba, hankalina baya kwanciya.”

Na yi murmushi cikin kunya, kafin in tanka sai na ji kiran ya sauya zuwa video call.

Na ɗaga a hankali. Screen ɗin ya buɗe, sai haskenshi ya cika dakin.

“Subhanallah,” na furta a zuciyata.

Ya fito cikin ash color suit mai laushi, tie ɗin da pocket square dinsa suna matching tone.

Sai naji Ƙamshinsa ma kamar yana fitowa ta cikin screen ɗin. Fuskarsa cike da annuri, idanunsa sun ƙankance.

“My Lah-Lah…” ya furta cikin sanyi.

“Kin ƙara kyau ne ko camera ce ke ɓoye min haskanki? Please, dagomun kanki, kinji?”

Na saki murmushi cikin kunya, na saukar da idona ƙasa. Zuciyata ta buga kamar ana kaɗa gangar zuciya a hankali. Na ɗaga kaina a hankali, idonmu suka haɗu ta cikin screen ɗin.

Sai ya yi ɗan kiftin ido ɗaya gare ni kamar wanda ke raɗa sirri cikin ido.

Gabana ya faɗi.

Na rufe idona da hannuna cikin dariyar kunya.

“Remove your hand, please,” ya faɗa yana dariya, muryarsa mai daɗi ta gauraye da nutsuwa.

“Kin san irin kewarki danake ji kuwa?

I just need you near, but you’re hiding your face…”

“Why are you looking at me like that?” na tambaye shi cikin sanyi.

Ya ce, “Because... I still can’t believe you are mine.”

Muryarsa ta canza, ta yi nauyi, ta yi sanyi kamar muryar zuciya da take fadin gaskiya.

Na ji hawaye suna taruwa a idona, amma na yi murmushi. Na ce, “ you always say things that melt my heart.”

Ya murmusa.

“Then let it melt, my love... so I can live inside it forever.”

“Ranka ya daɗe, ban san da wane harshe zan mika godiyata ba.

Na ga sashen, na ga daki…

wallahi har yanzu nake mamakin yadda kake tunani a kaina har nesa haka.

Na kasa gane ko ni ce, ko wata daban.”

Sai ya yi dariya cikin natsuwa, yana girgiza kai, “My Lah-Lah, kina da kyau, kina da daraja da kin san yadda nake son ki, da kin san cewa komai da nake yi,

ina so ne in ga murmushi a fuskarki.”

Na ɗan sunkuyar da kai cikin murmushi, na ce “Allah ya saka maka da alkhairi, ya albarkace ka fiye da yadda nake roƙa.

A duk addu’ar da nake yi, sai na roƙi Allah Ya baka natsuwa, saboda kai ka bani tawa.”

Sai na ji ya yi shiru na ɗan lokaci, idanunsa suka sauka a kaina ta cikin screen ɗin.

“Ramlah…” ya faɗa da muryar da ke sanyi sosai,

“kalaman ki suna fiye da duk wani kyautar da za a iya ba ni.

Just hearing that, my heart is at peace.”

Na ɗan murmusa, na ce cikin natsuwa

“Na gode, ranka ya daɗe, da kulawa

duk wani abu da nake gani yau, na san daga zuciyarka ne. Ubangiji ya ƙara maka daraja, kuma ya bani ikon kula da kai kamar yadda kake kula da ni.”

Na lumshe ido, ina jin sautin zuciyata tana bugawa da sautin muryarsa.

Na ce masa, “You know what,? Sometimes I feel like even the light in my room gets jealous of you.”

Ya yi dariya, muryarsa ta narke cikin speaker kamar zuma.

“Toh me yasa?”

“Because...” na ce a hankali, “whenever you appear, everything else stops shining.”

Shiru ya biyo baya.

Ya daga hannunsa a cikin wayar kamar yana son ya taɓa fuskata.

“Ramlah... I wish I could touch you right now.”

Na dan ja numfashi.

“You don’t have to,I can feel you... here.” Na dora hannuna a kirjina.

“My heart never forgets your voice.”

Ya ce cikin muryar da ta yi sanyi sosai

“And my heart... never forgets your name.”

Na ɗan buɗe yatsuna a hankali, na kalle shi cikin wasa, sai murmushinsa ya ƙara faɗa min rai. Idanunsa suna kallona kamar yana tare da ni a dakin, muryarsa tana fita da salo irin wanda yake shiga cikin zuciya ba tare da izini ba.

“Kin sani,” ya ƙara faɗa, yana juyar da ring ɗin yatsansa,

“duk da nesa, koda jin muryarki ne, kamar ina rike da hannunki.

Kin koya min soyayya ta gaskiya ba ta salo ba, ta zuciya.”

Na ɗan lumshe ido, murmushi mai sanyi ya suɓuce daga bakina.

Sai muka yi shiru na ƴan dakikoki, muryar zuciyarmu tana magana fiye da kalmominmu.

Iskar AC ta kadawa fuska, amma wani irin zafi na soyayya ne ya ratsa jikina.

Na ce cikin ƙasa da murya,

“Yaya, ka gaji da nesa?

Ni fa har na fara jin gidan kamar babu iska idan baka nan.”

Ya yi murmushi mai cike da laushi, yana kallo kai tsaye cikin kamara.

“Kin san me nake so?

Na dawo gida in ji ƙamshinki saboda a duk inda nake,

numfashin duniya baya daɗi idan ba na jin naki.”

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull