Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 38
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 38: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 38. Hawayen farin ciki suka cika idanuna, sai na ce cikin murya mai rauni,
4,494 words
Hawayen farin ciki suka cika idanuna, sai na ce cikin murya mai rauni,
“Ni dai ka dawo kawai, ranka ya daɗe.”
Ya murmusa yana kallona kamar zai taɓa ni daga nesa.
“In shaa Allah, My Lah-Lah.
Just few days left.”
Screen ɗin ya yi sanyi da karshe, amma zuciyata ta ƙone da zafin kewarsa.
Na ajiye wayar a kaina, na rungume ta kamar shi ne a ciki.
Nana hadiza
09030569336
[27/11, 5:22 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA ƊARI DA DAYA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Ayshatu tana ta sintiri a cikin dakinta, tafiya tana dawowa kamar mai neman hanyar fita daga tunani. Damuwa ta cika mata zuciya, ta kasa samun nutsuwa. Duk sanda ta rufe idonta, sai hoton Ramlah ya sake bayyana a zuciyarta , nutsuwa, kyakkyawa, mace mai halin da ta san Asad keso don yanason kunya sosai tasan wannan kuma yanason girmamawa ma dan taga yarinyar ita kamta ta girmamata.
Tasan halinsa, tasan son da yake yi wa mata masu kamanni irin na Ramlah kirar jiki mai kyau,ko’ina na jiƙinta ya cika yayi taf ga hips ga cikar kirji daya daga ciƙin abunda ke rikitasa,ga murya mai taushin da ke nutsar da zuciya.
Ta dafe kirjinta cikin ɓacin rai. “Ya Allah, daga ina zan faro?” ta furta cikin ɓacin rai.
“Ko wannan yarinyar bata fita daga gidan nan ba,. Ina zan saka kai? Ina zan fara komawa cikin wannan masarauta?”
Wayarta ce ta fara ringing.
Sai ta ji gabanta ya buga Muqaddam.
Ta tsuke fuska, ta ɗaga wayar tana mayar da murya ta cikin ɓacin rai “Muqaddam, Menene kakira kacemun duk soyayyar da kake furtawa na karyar ne? Ka bar ni cikin danasani ka kashemun aure kasani naci amanar mijina Ka tunzura ni cikin bala’i?...”
“Haba Ayshatuna… haba habibie…” muryarsa ta fito sanyi kamar na wanda ke neman salama. “Me yasa zaki min wannan zargin? Ina son ki, kin san haka. Ban da kowanne ciwo fa, kuma takardun karya ne kawai aka…”
“Karya!” ta katse shi da huci.
“Karya ka ke! Ko me ka ce, ya isa! Mai Martaba ya bani takardar sakina. A ranar da ka bari na zama abin dariya, abinda na sani shi ne ka munafuki ne azzalumi kuma i ka ci amanata!”
Ta ji ya yi shiru a can ɓangaren. Sai daga baya ya ce da rauni “Aysha… kinga dai. Ki bani dama. Karki rabu dani. Zan…”
Ta ji jikinta ya dauki zafi. Hawaye suka taru a idanunta, amma ba na rauni ba na zafi, na baƙin ciki, na jin an yi mata wayon da ya zarce tunani.
“Muqaddam,” ta ce da murya mai kaifi, “tabbas kai mutum ne da bai san darajar mace ba. Ka yi abinda kake so amma ka sani Allah ya isa. Kuma daga yau, kada ka sake kirana, ko da ni ce mace guda daya ce a duniya.”
Ta katse wayar da karfi, ta jefa ta saman gado, tana huci kamar wacce ake rufewa da hayaki.
Ta dafa bango ta zauna a ƙasa tana haki.
Zuciyarta cike da takaici.
Komai ya yi mata nauyi komai ya rikice
amma abu daya ta tabbata da shi Ramlah ce ta tsare mata hanyar dawowa cikin gidan asad Kuma hakan ya ƙara mata tsanar yarinyar da bata da laifi a zahiri amma ta zama sheƙaƙƙiyar barazana.
Ta share hawaye tana fadin “Ga dukkan alamu… da gaske zan iya rasa Asad saboda ita. Amma wallahi sai nasan me zanyi.”
Daren nan Ayshatu bata runtsa ba. Tana ta zirga-zirga a cikin dakinta, ta rasa inda zata sa kanta. Kyakkyawar fuskar nan tata ta kumbura da kuka, gashin kanta duk ya tuje, lipstick ɗinta ya goge. Ta tsaya gaban madubi, ta kalli kanta sosai fuskar mace da ta saba mallakar komai a gidan Asad kulawa, kudi, murmushi, wasa, zance komai…
Sai yanzu take kallon kanta tare da tambayar da ta ke jin zafinsu “Ni Ayshatu, ta ina zan bar wannan yarinyar ta kwace min Asad?”
Ta buga hannunta a kan madubi.
Sai ta jingina kanta da bango, tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
Wayarta ta sake ringing.
Sunan da ya bayyana ya sa ranta yakara ɓaci MUQADDAM CALLING…
Ta kalli wayar da raini.
Ta ɗaga a fusace, tana faɗin “uban menene kakirani kayimun ba nagayamaka karka kara kira na ba?”
Shi kuma a can yana faɗi cikin rawar murya “Ayshatuna haba, haba Habibie, kar ki ce haka wallahi bani HIV fa! Karyar mutane ne! Ki bani damaki dawo gare ni… Mai martaba ya bani umarni danAllah!”
Ta yi tsaki tana hura hanci. “Muqaddam, kai ba namiji bane. Kuma kasani wallahi Allah na gama zama dakai har abada. Allah Ya isa tsakanina da kai.”
Ta kashe wayar kaf, ta jefa ta gefe.
Sai ta zauna a gado, ta ɗora hannayenta biyu a kai.
TO ME YA FI ZAFI?
Ba wai HIV ɗin Muqaddam bane.
Ba wai rashin auren ke damunta ba yadda zata koma gidan Asad takeso tasamu mafita..
Abin da ya fi zafi gareta shine Asad,
Yanzu yana tare da wata yarinya… kuma yana santa da alama sosai.
Saboda ganin yadda ya kula da Ramlah lokacin da suke Asubuti, yana mata kallo irin da ba ta taɓa gani ba, zuciyarta ta ƙone.
“Ramlah… wannan kuka kawai kika fara. Ki shirya.”
Ayshatu ta share hawayenta.
Ta daga wayarta, ta fara rubuta lambobin sirri.
Ta kira wata lamba Wata mata ce ta ɗaga cikin muryar manyan masu aiki na gidan sarauta “Assalamu alaikum, Hajiya Ayshatu.”
Ta kwantar da murya, amma cike da mugunta tace “Ina son mutum guda uku daga cikin bayin cikin gidan. Masu sirri. Wadanda zamuyi aiki dasu kamar abaya.
A can aka ce “Za’a samo, Hajiya. Kin ba da umarni ni nawa zartarwa ne.” Ta murmusaamma murmushi irin na macen da tunaninta ya cika da mugunta. Bayan sun karaso bangaren nata ta kalle su tace “Ina so ku bani duk bayanan wannan yarinyar Ramlah.” sai duk suka zuba mata idanuwa da mugun tsoro “Zan san duk motsinta , wanda take magana da shi, lokacin da take barci, yanda take tafiya komai.”Duk sukayi shiru suna tsoron hukunci. “Zai kasance kamar muna karanta zuciyarta.” Ayshatu ta ce cikin sanyi “ Eh hakane sannan kuma ina so ku shiga jikinta ba tare da ta gane ba.”
“Ranki yadade duk yadda kikace haka zamuy.” daya daga ciƙin bayin bangaren ramlah tafada.
Ta ja gashin kanta gefe, ta zauna tana dariya dariya mai raɗaɗi da zafi, irin wacce ke fitowa daga zuciyar mace da kishinta ya fara zama cuta. “Game on, Ramlah. Gidan sarauta ba na marasa dabara bane.”
“Idan kika iya tsallake wannan wuta, sai na girmama ki Amma kafin nan… sai kin dandani ƙura.”
Suƙan bayin na barin shashin nawa sai suka saka dariya dayar tace kiji zafa jazamana masifa matar da babu ruwanta da kowa kuma ina mu ina kula matar yarima nidai kunga babu ruwa a wannan lamarin. Dayar itama tasaka dariya tace “ Ni wallahi kallon mara hankali nake mata ita ahaka so takeyi ya maidata ai.” Suka saka dariya kowanne yana kudurce babu ruwansa a wannan aikin.
***?
Mikewa nayi a hankali na sauko daga bene, ƙafata a hankali kan marbled tiles ɗin da ke sheƙi kamar madubi. Duk inda na taka sai iska mai ɗauke da ƙamshin white oud ke biyoni koina a cikin sashen ya canza, ya sabunta, ya yi kyau fiye da yadda na barshi.
Bayan na wuce falo na farko, na nufi babban main kitchen na masarautar da ke a gefen shashena. Ina shiga sai na tsaya cak saboda mamaki. Komai ya sabunta cabinets fari, marble countertop mai sheƙin milky cream, sabbin kayan girki na zamani guda-guda a ko’ina.. Mashaa Allah nafaɗa ina murmushi.
Ma’aikatan kitchen suka ganni, sai suka tsaya cak suka duƙa tare da gaisuwa. “Ranki ya daɗe, Allah ya ƙara lafiya.” Na amsa cikin ladabi, ina murmushin da na saba yi.Kafin in ƙara ce musu wani abu, Uwar Amarya ta karaso da sauri tana riƙe da tray.
“Ranki ya daɗe,” ta ce da rawar murya.
“Me kike bukata da baki aiko mu kawo? Me ya kawoki har ki zo da kanki?”
Na yi murmushi a hankali, na jingina tafin hannuna kan counter.
“Uwar Amarya, aikin gida ne. Ina son yin wani abu da kaina.”
Ta zaro ido cikin mamaki.
“Haba ranki ya daɗe! Wannan aikinmu ne. Mu ne za mu yi miki komai. Ki hutawa kawai.”
Na girgiza kai cikin ladabi.
“A’a… wannan maganar ta baki ce.
Wannan girkin, ni zanyi amfani da shi.
Dan Allah ki bar ni nayi.
Inaso su bani waje mutym daya ta tsaya, ku bamu waje.”
Ta tsaya tana kallona na daƙiƙu biyu, tana nazari. Daga ƙarshe ta ɗago kai ta ce “To ranki ya daɗe. Idan kika ce zakiyi dole mu bi umarnin ki.”
Ta juya ta umarci sauran ma’aikata da su barni. “Uwar Amarya… akwai kazar Hausa a freezer?” Ta murmusa. “Akwai duk abinda kike so, ranki ya daɗe.”
Na bita zuwa babban royal store.
Na ɗauko rubutun kayan da nake so, koina ya cika makil da kayan abinci freezer biyu ce manya sai fridge masu kofa biyun nan suma manya biyu..
Wani abu ya tuna min da kalmar momy“Abincin mace, shi ne sirrin lafiyarta. Ki kula da jikinki, Ramlah.”
Wannan ya bani ƙwarin guiwa.
Na miƙa mata rubutun kayan haɗin girkin.
Ta karɓa cikin girmamawa.
“To ranki ya daɗe, yanzu zan dawo.”
Na koma kitchen ɗin.
Wata daga cikin baiwa ta riga ta kawo min kankana, kwakwa da cucumba a saman counter.
Ta yi saurin karɓar kayan daga hannuna “Ranki ya daɗe, bari in taimaka miki.”
Na yi murmushi.
“To ki matse min su a juicer. Ina buƙata su.”
Ta yi aikin cikin tsafta da nutsuwa.
Saida ruwan kayan ya cika jug mai kauri, mai launin crystal. Ta saka a cikin fridge ɗin sanyi, sannan ta dawo tana durƙusawa.
Nana hadiza
09030569336
[27/11, 5:22 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA ƊARI DA BIYU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
“Nagama ranki ya daɗe.
Umarninki nake jira.”
Na yi mata murmushi mai sanyi.
“Allah ya saka da alkhairi.”
Ta miƙe cikin ladabi, ta barni cikin kitchen da iska mai sanyi da ƙamshi.
Na jingina da counter ɗin a hankali, na lumshe ido. A hankali na ɗauki wayata, zuciyata na harbawa kamar rawar soso. Na duba call log har yanzu shiru. Sai kawai wayar tashiga vibrating.
“My Heartbeat ❤️ Calling…”
Numfashina ya tsaya na ɗan lokaci. Na lumshe ido cikin nutsuwa, sannan na ɗaga wayar a hankali.
“My Lah-Lah…”
Muryarsa ta fito kamar daga cikin kunnenamai rauni, mai sanyi, mai nauyin ƙauna da gajiya.
Na runtse ido, murya ta na rawa ta amsa
“Na’am…”
Sai ya yi ajiyar zuciya mai zurfi, mai nauyi, mai kama da wanda ya sha aiki.
“Kin tafi da hankalina yau.”
Ya faɗa da wata murya wacce ta tsaya kai tsaye a zuciyata.
Na ɗan gyara tsayuwata na ce da sanyi
“Me kake nufi?”
Ya ɗan yi dariya mai laushi.
“Tun safe nake son kallon ki… ko voice ɗinki.
But you didn’t call me.”
Na dan rufe fuska da tafin hannuna, zuciyata tana rawa.
“Nayi niyyar kiran ka… amma na ga baka kira tun safe ba, sai nace ko kana busy.”
Ya yi shiru na daƙiƙa biyu.
Sai muryarsa ta yi sanyi sosai “Even if I’m in the middle of a meeting, I want your call, Ramlah.”
Na yi shiru.
Ban saba jin irin wannan kalaman ba, musamman daga shi.
Duk sanda yake yi, sai gabana ya buga.
Na ce cikin kaushin murya
“Ni… kawai naji kamar… zan dameka shiyasa...”
Sai ya katse ni cikin son kai na manyan maza
“Damu na. Ina so ki dameni.
Ki kira ni, ki tura min saƙo, ki tambaye ni me nake yi. Ni aure nayi da ke, Ramlah not distance Nasha gayamiki ina son soyayya inason kulawa ko?.”
Gabadaya jikina ya yi sanyi.
Na jingina da mable din, na kalli gilashin taga inda rana ke faɗuwa..
Ya sake magana cikin muryarsa mai narkewa “Tell me… what are you wearing today?”
Na dan yi ajiyar zuciya ina murmushi.
“Rigata ce… atamfa bubu.”
“Color?”
Muryarsa tayi kama da wanda yake tunanin ni a gabansa.
“Blue… da gold embroidery.”
Ya yi wani irin shiru da ban saba ji ba.
Sai yace cikin kasala mai sweet “I wish I could see you right now.I miss your face.I miss your voice.I miss your presence around me.”
Na ji hawaye sun taru saboda daɗin soyayyar da nake ji.
Ya tambaya cikin murya mai taushi “Me kika ci? Kin sha magani?” Na amsa “Na ci. Na sha magani kan nawa yadaina ciwo ma.”
“Good girl…”
Ya ce a hankali irin yadda ya saba yi idan yana so ya kwantar da hankali na.
Sai zuciyata ta yi wani irin lumshewa. Ya tambaye ni Yanzu me kike so na yi miki?”
Na bata murya cikin tsantsar soyayya “Ka tsaya min. Ka yi magana dani.”
Ya yi dariya mai natsuwa. “To… come closer to your phone.”
Na dan matsa wayar kusa da fuskata.
Zuciyata na bugawa da ƙarfi.
Sai ya yi magana da muryar da nake jin kamar yana raɗa a kunnena “Ramlah…” “Na’am…” “I love you zuwa wani mataki da ban san zan iya ba. Ki kula da kanki har sai na dawo. Ki ci. Ki sha magani.
Ki yi dariya. Ki kwanta idan kina jin bacci.
Ki daina tunanin komai sai ni acikin ziciyarki.”
Shirun da ya biyo bayan wannan kalmomin ya tabbatar min da abu guda Yarima Asad ba wai kawai yana sona ba… yana rasa natsuwa idan nayi hira dashi ko idan ina daga gefensa.
Sai ya ce da sanyi “Kiyi min alƙawari…” Na ce“Me zan ce?” “Ki daina saka hijabi mara kauri idan zaki fita gurin hajja.” Na saka dariya cikin kunya “Ranka yadade”
Ya murmusa ya katse ni “I don’t care.
You’re mine. And when I come back…
I want to see my Lah-Lah shining for me alone.”
Na yi shiru saboda kunya ta rufe ni gaba ɗaya. Ya ce a hankali“Are you blushing?”
Na ce cikin rauni“Am not…”
Ya yi dariya “You are. Even without seeing you… I know.”
Duk jikina ya yi wani irin laushi, kamar na karya a tafin hannunsa.
Sai ya ce “Goodgirl inada meeting hanzu Na ce a hankali “Tohm Allah yabada saa…”
Ya ce “Ki yi min kiss tukunna.”
Na yi dariya ina fadin “Ni kunya nakeji…”
“Hmm?” Muryarsa tayi laushi da taushi.
Na lumshe idona… sannan na yi ƙaramar murya “Mwah…”
Sai ya yi murmushi mai cike da jin dadi “That’s my wife.”
Ya kashe wayar cikin salo na manyan maza.
Na kira mai aikin tawa Nace mata ta yi min grating na kayan miya ta yanka albasa da kyau. Ta amsa cikin ladabi
“To, ranki ya daɗe.”
Ina tsaye ina duba recipe book ɗina na girke-girke, wanda na rubuta da kaina, sai ga Uwar Amarya ta dawo da ledoji. Ta ajiye su a kasa cikin ladabi ta ce “Ranki ya daɗe, ga su nan… duk an samo.”
Na murmusa na ce,
“Toh, Allah ya saka da alkhairi.”
Sai na fara hada kayan hadin sassaken ɓaure, kaza,ganyen idon zakara,minannas, kayan miya, maggie da man zaitun, sannan kimba, kaninfari, citta, tafarnuwa, sai kuma ruwan kwakwa mai kauri.
Na juyo na ce cikin natsuwa,
“Kawo min tukunya nan . Bayan ta kawo na hada dukka kayan hadin aciki sannan na kalleta nace Idan ta tafasa, ta dahu ku rufe ku kawo min ɗakina.”
Uwar Amarya ta sunkuya da biyayya ta ce,
“To, ranki ya daɗe.”
Komawa ɗakina nayi. Wanka nayi da warm lavender water, na shafa Oud Blossom lotion, na saka rigar gida mai launin peach gold. Bayan sallah na fara azkar, sai kawai aka sanar da ni “Ranki ya daɗe, kina da baƙi.”
Na sauko ƙasa da sauri cikin nutsuwa.
Sannan na hangi Yaya Billy tsaye tana murmushi . Na ce cikin farin ciki,
“AA, kece tafe haka? Yaya Billy!”
Ta yi dariya har dimples dinta suka bayyana.
“Ni ce mana, yar baturiya! Kinga yadda kika yi kyau kamar balarabiya? Haba Ramlah, ni fa sai na tsaya kallonki ranki yadade”
Na lumshe ido cikin jin kunya.
“Wallahi, Yaya Billy, bana son wannan sunan.”
Ta kwashe da dariya tana shafar hannuna.
“Ai dole ne. Ki kalli kanki, ki ga yadda kika dawo kamar Princess Amirah!”
Mun zauna kusa da juna, muna gaisawa sai aka kawo mata kayayyaki a gabanta abjnc, snacks fruits, da farfesun kifi..
Na ce cikin murmushi,
“Yaya Billy, baki gaya min za ki zo ba. Da an shirya miki abinci na musamman.”
Ta tura hanci ta yi tsaki cikin dariyar ta.
“Kinga dai… dakyar Abba ya bar ni. Sai da Momy da Yaya Aliya suka saka baki. Kinsan har yanzu ina can, biki saura three weeks ragas!”
Na ce,
“Masha Allah, Allah ya kaimu sannan ya tabbatar mana da alkhairi.”
Ta ce tana dariya,
“Ameen, matar yarima. Gaskiya ni ina ta kallonki. Kin canza sosai. Wai masarautar nan da zarar an shigo, sai a fara yin kyau kamar an goge mutum da zinariya!”
Firdausi daga can gefe ta ce,
“Wallahi kuwa, Yaya Billy, na ce mata tun da safe. Ku ga yadda take glowing kamar wacce aka yiwa royal spa treatment.”
Na ɗan dube su da murmushi cikin kunya, zuciyata na cike da godiya ga Allah.
Na kuma ji wani irin kwanciyar hankali da nake ji a gidan sarauta…
Duk da ƙalubalen da nake ciki.
Bayan mun gama hira da Yaya Billy sai na tashi zan koma ɗakina, zuciyata na cike da wani irin kwanciya da natsuwa saboda ganin dangi. Firdausi tana kallo ina hawa benen, tana murmushinta ta kalleni tace matar yaya zan koma sai kuma da safe. “ Tohm Antyna nagode ayiwa hajja godiya kamin na karaso ta amsamun ta huce.
Nakarasa Da zarar na shiga ɗakina, Na ajiye mayafina, na cire takalmi a hankali, na zauna kan kujerar velvet cream. Nacewa google set the room a nan ne ta saita mun ac sannan ta yayemun labule na bayan na danna remote Sai kawai na ji knocking.
“Ranki ya daɗe…”
Muryar Uwar Amarya ta “An kawo abincin da kika umarta.”
Na ce,
“a ajiyemun a kasa.”
Natashi nayi alwala sannan nayi sallah bayan nayi ne yaya billy nasan tagama cin abincin yanzu ina kokarin mikewa kenan sai naga wayata tana kara alamun ringing
My Heartbeat Calling…
Zuciyata ta buga.
Na ɗaga a hankali.
“Assalamu alaikum…”
Na furta da ƙanƙanin murya kamar yarinya
Sai kawai na ji numfashinsa ya ɗan sauya kayan muryarsa tayi sanyi
“My Lah-Lah… kiyi hakuri wallahi banida nutsuwa ne kwatakwata nafison nayita jin muryarki har mungama meeting din.?”
Na runtse ido, gabana ya doka.
Yana jin komai.
“ Allah yabada sa’!” nace cikin jin kunya.
Ya yi murmushi mai sa muryarsa ta yi laushi, wanda nakan ji kawai idan yana cikin nishadi.
“Ameen my lah lah kinga da hajja tabani ke da ba haka ba Ko kina so ki kashe ni da tunani ne? Wallahi tun safe bana iya aiki saboda ke.”
Na dafe kaina cikin kunya.
“Ranka ya daɗe, kada ka yi maganar da za ta sa zuciyata ta buga haka…”
Ya yi dariya.
Wacce ta fi kowace dariya dadi a kunnena.
Nana hadiza
09030569336
[28/11, 10:20 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA ƊARI DA UKU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
“Ba zan daina ba.Na tafi aiki? Na dawo?
Na hau jirgi?Na sauka?
Zuciyata tana tare da ke kawai.”
Na ƙarasa kwanciya a jikin cinyoyina ina wasa da labulen gado.
Na ce cikin taushi
“Me ka ci yau?”
Ya ce,
“Ba komai.
Na fi so ki gaya min naki.”
Na yi murmushi.
“Farfesun kaza ne…
Da ruwan kwakwa”.
Na ji shiru, sai kuma numfashinsa ya ɗan yi nauyi.
“My Lah-Lah…
Don Allah…karki soma shiga kichen?”
Na makale.
Zuciyata ta kulle.
Kai na ya tsinke da wani irin nauyi.
“Ni? Me nayi?” Nace cikin rikicewa.
Ya ce ƙasa-ƙasa “ kawai banaso shiyasa na cika miki sashen da masu yimiki hidima.” “ Cikin sanyi nace “To kayi hakuri baxan kuma ba.” Murmushi naji yayi yace “ Ni bakiyimun laifi ba kin manta cewa ina kewarki kamar mahaukaci?” Na rufe fuska da pillow, ina jin jikina yayi sanyi. “Don Allah ka daina…” Na furta sosai ƙasa. “Ba zan daina ba, My Queen.” Muryarsa ta yi dadi da soyayya mai nauyi. “bana son ganin ko rauni ɗaya.
Ba zan iya jure hakan ba.” Na yi shiru, zuciyata na tafasa. Sai kawai ya ce “Ki ci abinci, ki huta. I’ll call you before I sleep.
And, Ramlah…” “Na’am…” “Thank you for making my palace smell like home.”
Nasaka murmushi ina daka tsalle daman haka soyayya take haka daɗinga yake.. Ya kashe wayar.
Da na koma palon, zuciyata duk cike da wani nauyin jin kunya saboda hirar da nayi da Asad, amma sai nayi ƙoƙarin gyara fuska saboda Yaya Billy tana zaune tana jirana.
Da zarar ta gan ni, sai ta miƙe ta nufo ni da sauri “Sister…” ta furta muryarta cike da rawa da tausayin kanta. “DanAllah nazo gurinki ki yafemun, kinji? Nasani nayi kuskure… amma wallahi bana samun nutsuwa cikin raina ko kaɗan.” Ta tsaya a gabana, idonta sun cika da hawaye, jikinta har rawa yake yi. Na matso a hankali, na kama hannunta na goge mata hawaye.
“Yaya Billy… komai ya huce. DanAllah ki daina kuka.” Ta ɗan yi murmushi mai rauni, ta jingina kanta a kafadata. “Banda yaruwar data fi Ramlah… wallahi kina da kirki. Hudubar Momy ce ta rinjaye ni a baya amma ba tsabar zuciyata ba.” Na murmusa cikin taushi, zuciyata. “Babu komai, Yaya Billy. Kin sani ai mu biyu ne. Komai ya wuce.” A nan ne ta fara bani labaran gida wasu na sani, wasu kuwa sai da jikina ya ɗauki dumi da mamaki. Mun yi dariya, mun yi hira, zuciyata ta sake gaba ɗaya. Daga ƙarshe Nace “Mu hau sama dan in baki abubuwan da kikace.” Sai ta tsaya cak ta ce cikin wasa “Amma ba zan shiga dakin mijinki ba o!” Na yi dariya sosai “Yaya Billy wannan ba shashinsa bane, ki daina damuwa abunki.” Dole ta yarda muka hau. Duk kayan da nasan zata so turaruka, mayuka, veil, kaya na haɗa mata kimanin guda ashirin masu tsada sosai. Ta kasa boye farin cikinta. Har kuka ta sake saboda yadda hidimar ta yi mata yawa. Bayan mun gama, na ɗauki wayata na tura mata ₦2,000,000 nan take.
Ta daga kai cikin mamaki kamar zata faɗi.“Ramlah… wannan kuma meye?”Na ce mata cikin natsuwa “Abba ya kashe kuɗi sosai a bikina. Banason jarinsa ko ɗaya ya taɓu.
Duk abinda kike soki gayamin, kada ki gaya musu. Wannan kuɗin ki bar su a hannunki. Ki yi hidima dasu. Ai event ɗinku biyu ne, ko? Kamu da wuni? To ni zan ɗauki nauyin komai. DanAllah ki yarda.”
Ta fashe da kuka kamar wacce aka zare mata wani abu daga zuciya ta rungumeni kamar karmu rabu Sannan ta ce da muryar da ke rawa “Ramlah… Banso na faɗa miki saboda Yaya Abbas yace kar a gaya miki, amma…
Su Abba sun yi asara sosai wannan satin.
Har sun soma maganar siyar da gidanmu dan abiya wasu mutanen kudin kayan da sukayi asara. Su na cikin wahala sosai yanzu.”
Na tsaya cak. Wani abu ya fasa zuciyata tamkar tsinke. “Subhanallah.” Na furta ina dafe ƙirji.“Allah Ya mayar masa da alkhairi, Ya tsayar da wannan jarabawa.” Ta ce “Ameen” tana share hawayenta.Sai muka ci gaba da hira har magariba. Sai da na kira driver ya mayar da ita gida sannan na koma sama jikina yana yi mun nauyi.
Na kwanta a kan gadona, na tattara dukkan tunani na sarkoki guda huɗu, kuɗin hannuna, Na san zan iya siyar da su a matsayin gold investment, su yi dala dubu goma sha biyar.
Wannan zai taimaki Abba, zai basu sauƙi, zai kwato gidansmu Na ce a raina “Ya Allah, duk abin da zan iya yi don iyayena, ka bani ikon yi.” Na lumshe ido, zuciyata ta cike da missing din asad kawai so nakeji nagansa na rungumesa. Na dafa ƙirji, na ce a raina “Ya Allah, kar ka barni in ji daɗi ina sanin iyayena suna cikin damuwa…” Sai kawai na jiyo wayata tana vibrating a gefen gadon.
Na ɗauka cikin gaggawa.“My Heartbeat calling…” Zuciyata ta buga.
Na share hawayen da ban san lokacin da suka sauko ba, na ɗaga cikin murya mai rauni “Assalamu alaikum…” Sai muryarsa ta fito cike da sanyi, mai nutsuwa, amma da zurfin soyayya da yake shiga zuciya kai tsaye.
“Wa alaikum salam…My Lah-Lah…”Shiru ya ɗan biyo. “ yanzu kin kwanta ko? Kayan bacci ne ajikinki ko? I ina nan kusa dake i wish na rumgumeki jikina ima kissing dinki.” Duk d jiƙima ya amsa amma sai nace “ Uhmm .” Sai naji yace “Me yasa muryarki ta sauya? Kin yi kuka ne?” Na yi saurin share kuncina da hannuna, ina ƙoƙarin yin dariya, amma sai ta fito da rauni. “Eh… aa, ban yi kuka ba, kawai gajiya ce, ranka ya daɗe.” Ya yi shiru.
Shiru mai nauyi, wanda kalmomi basa buƙata.
Na ji yana sauke ajiyar zuciya a hankali, sai muryarsa ta yi taushi fiye da da.
“Ramlah… you can’t lie to me.
Even through your breath, I can hear your heart crying.”
Na rufe idona, hawayen da nake riƙewa suka zubo. Na kasa amsawa. Tsoro nakeji baikamata in gayamasa ba tunda yaya billy tatafi nakejin damuwa gabadaya walwalata ta ɗauki ni kadai nasan irin kudin da abba yakshe na biki na ahaka ma wai an bashi gudumawa shiyasa wani lokacin nakanci ba auren masu kudin ba hidimar da zaayi musu ahaka ma ko watanni banyi ba gashi yacanza komai na daƙin kai Allah yayimana arxuki amj albarka.
Katsemun tunanin da nakeyi yayi Ya ce cikin murya mai cike da damuwa,
“Please… tell me. What happened?”
Na yi shiru, amma daga ƙarshe sai kawai kalmomi suka fito a hankali.
“Na samu labari ne daga gida…Su abba sunyi asarar wasu kayansu Sun yi asara sosai, har suna tunanin siyar da gidan mu Kawai… zuciyata ce ta tsaya. Ina son taimakawa amma ban san ta ina ba.”
Sai shiru ya sake biyo. Sai naji yayi numfashj yace “Subhanallah…” ya furta da murya mai sanyi. “Why didn’t you tell me earlier?”
Na yi shiru, sai na ce,
“Ba zan so in dameka ba. Ka san ni ai… bana son komai sai natsuwarka kuma ma ni banso na gayamaka ba.”
Ya yi shiru na dan lokaci, sannan muryarsa ta koma cike da ƙarfi da nutsuwa.