Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 39

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 39

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 39: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 39. “My Lah-Lah… kar ki sake cewa haka.

4,497 words

“My Lah-Lah… kar ki sake cewa haka.

Zuciyarki ita ce gidana. Idan ta yi rauni, ni zan durƙusa.Kin san ba zan iya huta in kina cikin damuwa ba, ko?”

Na share hawayena, amma murmushi ya fito ta tsakanin su. “Ranka ya daɗe…”

Ya ce cikin dariya

“Don’t worry about anything.

In less than one hour, zan tura miki kuɗi zuwa account ɗinki kibashi dakanki. Ki turo min bayanin lambar Abbanki. Kinji, my Queen? I will do something kinji.”

Na ce cikin jin kunya,

“DanAllah, ba haka nake nufi ba…”

Ya katse ni cikin murya mai sanyi amma mai ƙarfi “Ramlah… this is not help.

This is love. It’s my duty to make your heart calm, no matter the storm.

And wallahi, I’ll do it mahaifinki is my friend also.”

Shiru nayi. Na kasa magana, saboda kalamansa sun shiga cikin raina kamar ruwan sanyi. Sai na ji muryarsa ta sake yin rauni.

“Ki share hawayenki, kin ji?

Ki ci abinci, ki sha ruwa. Ba zan bar komai ya taɓa mutanenki ba. Ni da ke mun zama ɗaya, ko kin manta?”

Na lumshe ido, murmushi mai sanyi ya bayyana a fuskata. “Ban manta ba…” na ce a hankali.“Allah Ya saka da alkhairi, habibie..

Na gode da komai.”

Sai ya yi dariya mai natsuwa, yana cewa,

“Ba godiya a tsakaninmu, My Lah-Lah.

Ki daina damuwa.Just smile for me, please.”

Na ce,“Toh…” cikin sanyi, na ɗan murmusa.

“Good.Now, that’s the Ramlah I fell in love with,”ya ce cikin dariyar da ta narkar da zuciyata.

Sai muka yi shiru na daƙiƙa goma

wanda shiru ne mai cike da magana.

Numfashinsa yana yawo cikin kunnena, nawa kuma yana gudu da sauri kamar raina ya yi ta bugawa dan farin ciki.

Kafin ya kashe wayar, sai ya ce cikin raɗa mai daɗin gaske“Ramlah…Ki sani, kafin wannan dare ya ƙare,zan tabbatar da cewa Abbanki ya samu mafita. Allah ne shaida, ni da ke ba soyayya ce kawai ke tsakaninmu ba ita ce zuciyata gaba ɗaya.”

Nana hadiza

09030569336

[28/11, 10:20 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ƊARI DA HUDU

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Wayar ta kashe, amma kalmomin sun rage suna yi min yawo a rai kamar sautukan zuciya.

Na jingina da jikin gadona, zuciyata tana rawa, idona suna cike da hawaye.

Sai na ce a hankali“Ya Allah, ka tsare mini shi.

Ka kare min wannan soyayya da amana.”

Da daddare, bayan na yi sallah, na tura masa bayanin kasuwancin Abba. Ban san ko ya gani ba, domin bai ce komai ba. Sai bayan kusan a wanni uku har nafara bacci ma wayata tashiga vibration.

Voice note ne kawai “My Lah-Lah, ki saurari wannan. Ba na son ki tayar da hankali.”

Na kunna whatsapp dina nashiga a hankali. Muryarsa ta fito mai nutsuwa “Na tura wa Abbanki saƙo. Ba kuɗi kawai zan tura ba. Bana son a jingina komai da ni ina so gidan ya ɗaga kansa da kansa.”

Zuciyata ta buga. Na mamaki. Ya ci gaba“Abbanki mutum ne mai hankali da mutunci. Yana kokari sosai a kasuwanci, sai dai rashin damar da zai fitar da kayansa zuwa kasashen waje.”

Sai ya yi shiru kadan sannan ya ce “Na haɗa shi da Humaira Global Logistics kamfanin da ke sarrafa kaya zuwa Dubai, Doha da Istanbul.Na masa fully sponsored export slot for one year.Kayansa za a dauka daga gida, a yi clearing, a fesa, a nannade, a fitar waje ba tare da ya biya kobo ba.”

Na dafe kirjina, zuciyata na rawa.sai na fashe da kuka nacigaba da saurara “Na kuma haɗa shi da kamfanin dillalan kayan gida a Dubai Za a rika siya masa kaya da farashin da zai ba shi riba mai yawa. Duk wata zai iya tura bales dina biyu zuwa uku. In shaa Allahu, kafin shekara ta zagayo, zai zama daga manyan masu fitar da kaya.” Hawayena suka fara zuba. Muryarsa ta sake yin laushi“My Queen… Ina so ki san cewa bana taimaka shi saboda ni…Ina taimaka shi ne saboda Allah.

Ina ganin irin tarbiyyar da ya baki. Ina ganin irin nutsuwarki. Ina ganin yadda kike jin damuwarsa fiye da kanki hakan yakara tabbatarmun da tarbiyar da yabaki da tausayin iyayenki dakikeyi wanda hakan yakara sanya naji dadi sosai.”

Na rufe baki da hannuna. “Ni ba zan iya ganin masoyiyata tana kuka saboda damuwar iyayenta ba. Gidanku shi ne gidana.

Farfadowarsa shine farin cikina.”

Sai voicenote ɗin ya ƙare da maganar da ta sa zuciyata ta narke Ki gaya masa kada ya ji tsoro.Wannan dama ce ta gida ce, ba ta siyasa ba.Ni na ba shi ne saboda Allah ba saboda komai ba.”

Hawayena suka gangaro sosai, na zauna a kasan gadon ina hawaye ina murmushi.mikewa nayi nashiga bandaki nayi alwala nayi sallah nashiga yimasa addua kala kala ina fadin ilove you asad Allah katsaremun mijina kakaremun shi…

Washegari..

Da safe, bayan na gama nassin Al-Kahf, kasancewa juma’a ce wayata ta yi ƙarar kira nayi sauri na amsa ganin abba ne

“Auta, kina ina? Inata kiranki tun asubahi” muryar abba takarasa da karyewa..

Nace masa ina wayar tana dakine. Yace DanAllah “Ki zo gida yanzu-yanzu idan kina iya.”

Hankalina yadan tashi jin kamar yana kuka na yi tunanin wata matsala ce . Na sanar da uwar amarya xanyi fitar sirri ta ce

“Allah yakara miki lafiya driver yana tsaye yana jiranki..”

Driver ya fitar da ni, har zuciyata sai bugawa take. na shiga falonmu, na tarar da Abba zaune shi da yaya abbas sai momy sai uncle hamza. Fuskarsa kamar wanda ya sha kuka.

Na durƙusa cikin ladabi nace “Abba…ina kwana?” nahaɗa gabadaya na gaishesu.

Ya ɗago a hankali.

Hawaye suka zubo masa ba tare da ya iya riƙe su ba. Na firgita.

“Abba don Allah menene?!”

Ya kamo hannuna, ya riƙe gam, muryarsa na rawa “Auta… Auta… Yau mijinki yayimun abunda baa taɓa yimana ba nida yan uwana ya farfado damu daga masifar da muke kokarin shiga munyi asarar miliyoyi harda kawunki?” Na yi shiru, zuciyata ta tsaya cak. Ya cigaba, hawaye suna kwaranya “Wanda ke cikin duniya, amma zuciyarsa ta wuce kowa…

Wanda ya ga damuwata, bai tambayi komai ba… Bai tofa min magana ba…Sai ya yi abinda da can ya kamata ɗana ya yi… Amma shi ya yi min…” Na rike kirjina, hawayena suka cika. Sai ya miƙo min takardar email mai fassarar Turanci daga kamfanin Humaira Global Logistics, da signature ɗin Asad a ƙarƙashinta.

"Fully sponsored export clearance for Mr. Abubakar Musa

— Dubai

— Doha

— Istanbul

— One year."

Jikina ya yi sanyi.

Abba ya fashe da kuka, ya durƙusa ƙasa gaba ɗaya. Ni ma na durƙusa tare da shi.uncle hamza shima kuka yakeyi sosai gabadaya hankalinsu atashe yake

“Ya Allah… Ka saka masa da alkhairi.

Ya Allah ka albarkaci wannan yaro…

Ka ƙara masa daraja fiye da wacce yake ciki.

Ka bashi dukkan alkhairin da mutum zai iya samu…”

Hawayensa na zuba kamar ruwan sama.

Ya ce “Na so inje har cikin gidansa amma baya kasar mun kirashi munyi masa godiya.”

Na share idona, nace“Abba kadaina kuka.” Abba ya girgiza kai. “Ke ki kira shi. Kiyi masa godiya kinji.”

Na tashi a hankali na karasa gefe na ɗauki wayata. Hannu na yana rawa.

Na danna video call.

Ya ɗauka nan take.

Fuskarsa ta bayyana sanye da farar jalabiya, yana cikin office, glass wall a bayansa yana kallon ginin Emirates Tower.

Yayi murmushi “My Lah-Lah…”

Sai ya hangi hawayen da ke fuskata, ya ɗaga gira yana firgita. “Baby what happened?? Are you okay??”

Abba ya matso a hankali ya tsugunna kusa da ni, yana goge idonsa.

Asad ya ganshi, sai murmushinsa ya tsaya…

Yayi shiru kamar wanda aka danna mute.

Sai Abba ya ɗago kai a hankali ya ce cikin murya mai karyewa:

“Ranka yadade… Na gode.

Da dukkan dawainiyarka gareni nagode da dukkan farantamana Allah ya saka maka da alkhairi fiye da abinda kake tunani.”

Hannun Asad ya tafi gefen fuskarsa, kamar yana shirin danne hawayensa. Ya ce cikin girmamawa “Alhaji…

Don Allah ka daina wannan magana.

Wannan ƙaramin abu ne. Abinda na yi ba komai bane saboda Allah nayi..”

Na kama fuskata saboda hawaye.

Abba ya sake cewa“ Banyi kuka ba saboda damuwa , Amma nayi kuka yau. saboda jin girman abinda ka yi.”

Sai Asad ya yi murmushin da bangeji, ya ce: “Abba… duk inda nake a duniya, zan tsaya muku. Ba don komai ba…Chromosome guda a jikinta ya fito daga jikinka.”

Abba ya rufe fuska da tafukansa.

Ni kuwa hawaye suka balle. Asad ya ƙare da“Abba, wannan ba taimako bane.

Hanya ce. Ina son ka dogara da kanka fiye da kowa.Na kuma yi hakan ne da girmamawa, ba da izinin Ramlah kawai ba har da izininka.”

Sai ya juya murya ta yi laushi sosai“My Lah-Lah… Ki daina kukan nan ƙinji..”

Call ɗin ya ƙare.

Abba ya zagayo ya rungume ni cikin ƙarfi.

“Allah ya albarkaci aurinki, Auta.

Allah ya saka miki da alkhairi tabbas yau haihuwa tayimun rana Allah ya raya muku zumuncinku.” haka su momy ma suka dinga yimun addua

Na fashe da kuka cikin muryar sanyi“Ameen Abba…sai anjima.”

******

Ranar Lahadi ce rana mai sanyi da iska yau garin yayi kamar zaayi fuwa turare ke yawo cikin harabar masarauta. Gabadaya ginin da yake kewaye da shukokin fure masu haske.

Ni kuma a wannan safiyar, na zauna a falona na musamman na fi kowa sanin yadda shiru ke natsar da rai. Kamar kullum, na yi video call da mumt, ta yi min nasiha ta ce,

“Ramlah, ki kula da al’amuranki, ki ci gaba da zama da kowa lafiya, Ki san aure a gidan sarauta, kallo yake da yawa.”

Na ce mata “To, mumy.”

Na ajiye wayar, na ɗauki littafin Al-Mahabba fi Zaman Az-Zawaj da Dr Zara’u ta bani. Ina karantawa a hankali, amma zuciyata tana yawo wajen Asad. Kwanaki uku kenan rabona da jin muryarsa bai kira ba, bai aiko saƙo ba. Na fara jin kamar zuciyata tana zafi naduba whatsapp din still bai hawa ma kwata kwata dan saƙon nina basu nuna alamar zuwa ba.

Firdausi ce ta shigo falon da dariya tana ɗauke da tray. “My Lah-lah, ga smoothie ɗin ki, ban sani ba ko zaki iya ci. Amma wallahi kin rame sosai, ranki ya dade.”

Na ɗaga kai na yi murmushi.

“Na gode, Anty Firdausi. Ina jin sanyi kawai ne.”

Kafin mu ƙara magana, sai wayata ta yi vibration. Na ɗauka da sauri “My Heartbeat ❤️ calling…”

Na ji bugun zuciyata ya ƙaru, na danna amsa.

“My Lah-lah…”

Muryarsa mai taushi, mai nutsuwa, wacce ke sa zuciya ta narke, ta karade kunnuwana.

“Kin yi shiru sosai. Ina missing dinki.”

Na yi shiru na ɗan lokaci, sannan na ce cikin sanyi, “Kai ne fa baka kira ba. Na fara tunanin ko ka manta da ni.” Ya yi dariya a hankali.

“Forget you? You’re the peace I breathe, Ramlah.I was only working on something important.”

Na ce da jin kunya, “Toh, Allah ya taimake ka. Ina nan lafiya.”

Nana hadiza

09030569336

[28/11, 10:20 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ƊARI DA BIYAR

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Sai ya ce cikin dariya mai sanyi, “I know. Amma kin canza muryarki — kamar mai ɓoyon damuwa.zan dawo very soon.”

Ban yi zaton very soon ɗin da ya faɗa yana nufin yau ba sai dai a cikin sa’o’i kaɗan, masarautar ta ɗauki hayaniya da motsin mutane….

Wani motar royal convoy ya shigo cikin ginin da ƙarar siren ɗinsa ta tashe duk ma’aikata.

Babu wanda ya san me ke faruwa.

Sai kawai aka hango Mai Martaba yana fitowa daga wani taro, a tare da manyan hakimai da fursunoni, ana cece-kuce.

“Yarima Asad ne ya dawo daga tafiya ba tare da sanarwa ba!”

Wani abu ya tsaya a wuyana na kasa motsi.

Na ji ƙafafuna kamar sun tsaya cak.

Firdausi ta zaro ido tana faɗin,

“My Lah-lah! Wato yau ne…?” na kalleta nace “ Antyna kema tsokanata kikeyi ko?.”

Ɗan lokaci bayan haka, sai aka fara motsin royal guards, ana gyara hanya.

Sai na ji ƙarar bude kofar..

Yana shigowa kamar sarki daga almara.

Sanye yake da royal white thobe da golden embroidery a gefen wuyansa, rigarsa tana sheƙi Ƙamshin turaren Louis Vuitton Ombre Nomade ya cika falon.

Idanunsa suka tsaya a kaina na kasa daga kaina saboda kunya da bugun zuciya.

“My Lah-lah…”

Ya kira cikin sanyi, Na kasa magana.

Sai ya ƙaraso a hankali har gabana.

Ya ɗaga hannunsa, ya kama hannuna cikin natsuwa. “You didn’t even smile…”

Na ƙara sunkuyar da kai. Sai kawai ya ɗan murmusa, ya ce da taushi, “Kin fi ko wace mace da na gani. Duk inda na je, na tuna murmushinki. Amma yau da ganinki… na gane ban taɓa yin kewar mace haka ba.”

Na ɗan ɗago kai, idanuna cike da hawaye. “Ranka ya dade, me yasa baka sanar dani za ka dawo ba?”

Ya yi dariya. “Ina so na gani ko za ki nuna damuwarki. Amma yanzu da na ganki ba sai an ce min komai ba. I knew you missed me.”

Na yi shiru, sai kawai na ji hannunsa yana shafa fuskata “You’re glowing, Ramlah. Menene sirrin ne.”

Sai kawai Hajja ta shigo daga ƙofar gefe, tana murmushi. “Yarima, soyayyar ce agaban iyaye kuma? Bakaga ana jiranka a waje ba.”

Ya durƙusa kadan cikin ladabi ya gaidata Na ji zuciyata ta tsaya. Uwargida tace “ ohh ashe akwai ranar da zan ganka kana soyayya haka Duk suka yi dariya a falon. Hajja ta juya tana dariya ta bar mana waje.

Yana matsowa kusa, ya ce a hankali cikin turanci “Can I have a hug now, or I still have to beg my queen?”

Na yi murmushi , na ce a hankali,

“You don’t need to beg, Amma akwai mutane ababban palour inajin kunya.”

Ya ƙara zuwa kusa, ya rungume ni cikin natsuwa, yana fadin, “Welcome home, my peace i will be back anjima akwai inda zanje.”.

Ayshatu kuwa tunda ta ji labarin dawowarsa, zuciyarta ta shiga tsalle-tsalle.Ta tsaya gaban madubi, tana gyara lipstick ɗinta mai launin wine red, tana taɗa gashinta da hannaye biyu.

Ta ɗaura veil ɗin Turkish lace mai sheƙi, wanda yake bayyana girman kirjinta da laushin fatar fuskarta.

“Ai dole ya kalleni yaa tuna irin soyayyar da mukayi,” ta furta cikin zuciya.

“Bazan bari wannan yarinyar ramlah ta ƙwace min Asad ba. Mijina mai hankali, mai kuɗi, mai daraja…”

Ta ɗauki turaren Amouage Reflection Woman, ta feshe kanta sosai har turaren ya cika ɗakin.

Sai ta ɗauki data, ta fesa Oud Muattar, tana murmushi mai cike da dabaru.

“Zan tsaya a gaban fadar Mai Martaba,” ta ce.

“Ina tabbas zai kalla ni… ko ya tuna da ni.”

Ta yi tsaki kafin ta fita.

“Ina ta haɗa soyayya amma yanzu zan yi amfani da duk abin da mace ke yi domin ta jawo hankalin namiji.”

A hankali ta taka cikin babban harabar masarauta, tana yatsine motsi kamar balerina.

Duk ma’aikatan suka tsaya suna gaishe ta amma ita ba kowa take gani ba, sai shi.

Asad ne ya fito daga motarsa.

Sanye cikin royal white embroidered thobe, fuskar nan tasa mai haɗa tsananin ƙwazo da salo.Bodyguard ɗin sa suna biye dashi a tsari.

Ayshatu ta tsaya dabas a gabansa, ta ɗan jingina da pillar, tana ɗauke fuskarta da murmushin da ta san yana kashe maza.

“Asad… barka da dawowa.”

Muryarta mai raɗa da ta saba yi masa abaya.

Ta ɗan gyara veil ɗinta, tana nuna wuyanta kaɗan, dan taja hankalinsa Amma Asad…

Bai tsaya ba. Bai juyo ba. Bai ma gane wacece ba. Ya wuce ta kamar iska, kamar babu wanda yake tsaye a wajen.

Ayshatu ta zaro ido.

Tayi saurin matsawa fili kadan ta sake gwadawa, tana fadin “Asad! Ka dawo lafiya… ina so in… in taya ka murna.” Har yanzu bai tsaya ba. Sai kawai ya ce da direbansa da ƙaramin tsawa mai natsuwa “Ka buɗe ƙofar sashen Mai Martaba.” Wani ƙayataccen dogon Royal Guard ya bi ta gefe ya ce da ita cikin mutunci “Hajiya Ayshatu, Yarima yana cikin gaggawa ne. Ana jiran sa a fada.” Maganar ta ƙara mata zafi.

Ayshatu kai tsaye? tsaya, zuciyarta na tafasa.

Ta kalli bayansa yana tafe da girmansa, dogarawa, kwanciyar hankali… Duk alamar mace bata da matsayi a zuciyarsa.

“Ni Ayshatu… ni da ya taɓa damuwa da ni… yanzu haka yake wulakamtani agaban bayi agaban mutane?”Sai hawaye suka cika idanunta. Da zarar Asad ya wuce, dogarawa suka rufe ƙofar. Ayshatu ta tsaya tana kallo kamar wacce aka datse numfashinta.Zuciyarta ta ce “To shikenan. Ramlah ta mallake shi.

Amma wallahi sai na tarwatsa.

Sai na bata mata zaman aure.

Sai naga ko ita zata iya riƙe wannan wuta…”

Ta juya cikin fushi ta fice daga harabar masarauta kamar wacce ƙakin mamaki ya cika mata ƙirji.

***

Da zarar Asad ya isa ƙofar babban shashen Mai Martaba, dogarai biyu suka buɗe ƙofar da ladabi. “Ranki ya daɗe, Yarima Asad ya iso,” ɗaya daga cikinsu ya sanar.

Asad ya shigo da girmansa, kai tsaye ya tsugunna a gaban uban gidansa cikin ladabi na sarauta.Mai Martaba ya ɗago kai, idonsa ya yi zurfi da damuwa. “Asad… ka dawo lafiya?. Zancen Waziri ya girmi duk tunaninmu.”

Asad ya miƙe a hankali, ya tsaya da mutuncinsa na namiji mai ƙima.

Yana kama hannun kujera ya zauna a gefen Mai Martaba.

Wani babban hafesan masarauta ya miƙa masa takardar rahoto. Asad ya buɗe ya karanta, idanunsa suka sauya launi. “Ya sake yunƙurin guduwa daga kurkuku?”

Mai Martaba ya girgiza kai. “Kuma har da yunƙurin kitsa rikici.Yana taron wasu tsofaffin masu neman kujerar fada.

Duk bayanan suna nan.”

Asad ya rufe takardar a hankali, numfashinsa ya yi nauyi. “Waziri ba zai taɓa daina cutar da masarauta ba. Na yi masa alheri fiye da duk wanda ya taɓa yi masa… amma ya dawomun da sharri.”

Mai Martaba ya ce “Na san halinka, Asad. Idan kai ka yanke hukunci, ba zan tsoma baki ba.” Shiru ya ratsa dakin, Asad ya ja numfashi. “Waziri ya shiga hannun hukuma gaba ɗaya.Kar a sake masa wata dama.

Masarauta ba wajen wasa bace.”

Mai Martaba ya yi murmushi mai ɗauke da alfahari. “Na gane cewa zuciyar ka ta girma, Asad.Ka san yadda ake riƙe masarauta da mutunci.”Amma sai Mai Martaba ya juyo ya kalli shi da wani irin sirrin kallo. Martaba ya yi dariya mai taushi.“Allah ya albarkace ku.” Asad ya gyada kai da ladabi, ya juya cikin girmamawa.

A wannan lokacin Ramlah tana zaune a sashen Hajja, tana shan tshayi mai ƙamshin ginger da lemongrass.

Idonta na kan wayarta tun safe.

Sautin hirar Hajja da Firdausi na tashi a falon, amma ita zuciyarta tana can wurin mutum guda.Ta bude WhatsApp Last seen 10 minutes ago.Zuciyarta ta buga.Ta latsa Call.

Sunan sa ya bayyana “My Heartbeat 💛”

Ringing…

Ringing…

Ringing… No answer.Ta sake kira.

Hawaye suka cika idonta ba don komai ba sai kewar da take shaƙa tamkar iska. “Ko dai…”

“Ko yana yayi fushi dani?“Ko yana gurin meeting har yanzu? Yanzun nan fa yadawo amma har yakara fita.”

Ta riƙe shawl ɗinta ta matse kirjinta. Hajja ta kalleta. “Lafiya, Ramlah?”Ta girgiza kai, tana ƙoƙarin murmushi. “Ba komai, Hajja.”Ta sake duba wayar Babu kira, babu saƙo.Sai dai numfashinta ya rikice.Zuciyarta ta shiga rawa.

A lokacin kuwa…Asad yana fada.Yana gaban Mai Martaba suna tattaunawa

Wayarsa a kan silent take Lokacin da ya fita daga fadar, sai ya duba wayar 8 MISSED CALLS My lah lah💛 Zuciyarsa ta tsaya cak. “Ya salam… Me ya same ta?”Ya kira.

Kawai sai Ramlah ta ɗaga cikin kuka mara ƙarfi. “… ka tafi kabarni…”Muryar sa ta canza gaba ɗaya, kamar zaiyi kuka shima batasan yafi missimg dinta ba akanshi?. “ My lah lah! No no no kin ji? Ki daina kuka… ki gaya min menene?”Ta share hawaye. “Na kiraka… baka ɗaga ba… sai jiranka nakeyi”

09030569336

NANA HADIZA

[28/11, 10:20 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ƊARI DA SHIDA

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Ya dafe gashin sumar kansa yana murmushi mai cike da damuwa da ƙauna. “Sweetheart… wallahi ina fada da Mai Martaba ne.

Nima zuciyata ta kasa zama.

Shine na kira da zarar na ga missed calls ɗin ki.” Ta yi shiru tana jin muryarsa tana shigowa jikinta kamar magani. Asad ya furta a hankali:

“Ramlah… please kar ki sake kuka saboda ni. Ki tsaya ki saurare ni fa…Ina sonki sosai.”

Zuciyar Ramlah ta narke.. “habibie…”

Ya murmusa. “I will come to you soon.

Very soon, My Lah-Lah.”

******

Ganin fita zaiyi nashiga dakin firdausi mukayita hira har wajejen yamma sannan naji fadawa sunayi yi masa kirari alamar yashigo bangaren hajja. Asad na gama gaisawa da Hajja da ladabi kamar yadda ya saba, ya zauna kaɗan yana tattaunawa da ita.

Idanunsa duk suna yawo cikin dakin, yana neman mutuniyar tasa...

Hajja ta murmusa ta ce, “Matar taka ta na cikin kitchen tun dazu. Allah Ya sanya muku alkhairi naga sai cin tuwo.takeyi kwana biyu yanzu haka ciki ne daita...”

A nan ne zuciyarsa ta yi wani irin bugawa mai sauti.Ya miƙe da sanyi, ya rusuna ya ce,

“Hajja, zan dawo Yanzu... Ina son na ganta kafin in tafi meeting.” Hajja ta yi murmushi mai ma’anoni sosai. Ta kallesa tana mamakin yadda baya boye sonta agaban kowa..

Ya yi gaba, ya tura ƙofar kitchen ɗin a hankali… Sai wani sanyi mai daɗi ya buge masa hanci..Ramlah ce… ita kaɗai…

Tana tsaye a gaban counter ɗin marble, sanye da doguwar riga mai launin sky-blue, kanta ɗan lanƙwasa yana kokarin buɗe yogurt.

Fitilar sama tana saukar da haske akanta.

Gashinta da ya zubo gefen fuskarta ya soma motsi kaɗan saboda AC. Sai ta ɗaga kai… Idonsu ya haɗu. Kamar a cikin fim. Kamar lokaci ya tsaya. Sai dai wani murmushi mai launin ƙauna ya bayyana a fuskarta.

“Ranka ya daɗe…” ta yi magana da murya mai sanyi, wacce ta doke shi har cikin ransa.

Ya matso cikin nutsuwa irin nutsuwar mutum mai ƙima da iko, amma zuciyar sa ta narkar da shi idan ta zo gareta.. Kafin ta san me yake shirin yi, Sai ya janyota hannu biyu — ya rungumeta. Ba da ƙarfi ba.Ba da zafi ba.Da irin rungumar da take gaya maka“Na rasa numfashina tun da ban ganki ba.”

Yashiga cikin wuyarta sosai, numfashinsa yana bugawa da nata.ya dan lashi wuyan nata Kamshin turarensa Oud Royal Blend ya gauraya da na jikinta. Kitchen ɗin ya cika da daɗin ƙamshi da dumin soyayya.

Ta sauke ajiyar zuciya. “Ka tsoratar da ni…” ta furta a hankali. Ya ɗan ware ta kaɗan, ya zuba mata ido. Idanun nasa sun yi duhu, sun cika da soyayyar da ba a iya ɓoyewa ba.“Na tsorataki?” Yafada yana shafa saman breast dina. Wani nishi nayi sai ya sauke hannunsa kuma. Ya ɗaga min haɓa da yatsarsa ɗaya. “Ko ni na tsorata da yadda nake kewarki i really i want to do again..”

Na sunkuyar da kai cikin jin kunya.

Ya murmusa, irin murmushin da yake fitowa ne idan ya ga abin da yake so fiye da komai.“Ramlah…” Na ɗaga kai a hankali.“Ki dawo sashinki.” Ta blink ɗin ido sau biyu tana kallonsa. “Yanzu?” Ya matso kaɗan, ya kusanto kunnen ta sosai, har numfashinsa mai ɗumi ya jiƙa fatar wuyanta. “Na gyaramaki dakin gaba ɗaya. Na canza komai saboda ke.

I want you there… babu inda ki dace sama da niƙanki.” Zuciyarta ta buga sau uku lokaci ɗaya. Na ce cikin taushi, “Insha Allah. Sai na gama abinda nake yi…”

Ya ɗan riƙe kumatuna biyu yana kallona kamar yana nazarin zuciyata. “Ni kuma zan je wajen meeting. Ba zan dade ba.”

Suka yi shiru na seconds kaɗan, shiru mai cike da zafi da nishadin soyayya. Sai ya yi mata wani murmushi mai narkar da gaba ɗaya jikinta. “My Lah-Lah… ki jira dawowata bari nadanyi kissing dinki kadan baƙinki na galabaitar dani...” Ta juya gefe ina murmushi na ce, “ ranka ya daɗe Allah yadawo dakai lafiya..”

Ya ɗan ja numfashi, kamar yana ƙoƙarin danne sha’awar sa. Ya juyo zai fita.

A ƙofar kitchen ɗin ya tsaya, ya waiwaya ya ƙara cewa cikin taushi “ina sonki….”

Ya fita. Kitchen ɗin ya yi shiru, amma zuciya ta cika da wani irin zaƙin soyayya da ban taba ji ba. Wato abunda na fahimta game da masu kudi basu da cikkken lokaci tunda nazo banga ya zauna gabadaya agida ba dazu yadawo daga tafiya amma yatafi meeting..yea kowanne aure da kalar nashi zaman..

Na gama abinda nake yi a kitchen, na yi sallah, na sauya kaya zuwa doguwar riga mai launin champagne gold rigar da ke zamar dani kamar ƙaramar balarabiya.

Sai na nufi sashenna cikin nutsuwar mace da take son mijinta Sashen ya yi shiru, ƙamshin white oud yana yawo koina. Ma’aikatan dake gefen ƙofa suka durƙusa suna gaishe ni da “Ranki ya daɗe, Allah ya raya miki mijinki.”

Na amsa da ladabi, n shiga ciki. A take ma tsaya cak. Numfashinta ya rikice.. Kamar ba sashensa ba ne.Kamar ba a duniya ba ne.

Dakin ya zama royalty fantasyCurtains masu launin soft mauve & gold suna yin launin sarauta. Floor ɗin ya koma Italian marble mai haske kamar ruwa. Sofa set ɗin an maye gurbinsa da velvet royal purple.A saman center table akwai flowers ba na gida ba, fresh imported lilies masu ƙamshi.A jikin gado kuwa, an shimfiɗa premium satin bedspread mai sheƙi. Sai idonna ya sauka… A kan gadon, akwai ƙaramin akwatin gift, an ɗaura ribbon. Sai kuma wani farfajiyar bango da aka rubuta da gold marker“For My Lah-Lah…

The Queen of My Peace.”

Na rufe baki da hannuna, hawayen farin ciki suna taruwa. Wato shima yayi gyara kenan? Dan koina ya canza acikin sashen nasa..Jikina ya yi sanyi..

Na zauna a gefen gado a hankali na buɗe akwatin…Cikinsa akwaiƘaramar zoben love-knot small necklace mai rubutun “My Heart” ƙaramin katin rubutu da muryar Asad “Ina kaunarki , domin zuciyata tana huta idan na san kina cikin natsuwa. Ki huta, ki murmusa… ki jira dawowata. Your home is with me.” Ta lumshe idona, na rungume katin a kirjina. Zuciyata ta buga… na murmusa… sannan na ce a hankali “Allah ya dawo min da kai lafiya.”

Ayshatu kuwa ganin yakara fitowa tayi sauri ta shafa turaren Oud Al-Malaki, wanda ta san Asad yana son ƙamshinsa. Ta sanya riga mai matse jiki sosai, ta zauna a corridor dantasan Asad zai bi ta wajen. Zuciyarta cike da zafi da kishin Ramlah. Ta yi tsaye, ta ɗaura murmushin da ta saba yi idan tana son ta kama hankalinsa Sai ga Asad ya shigo daga kofa mai babbar tsaro, bai tsaya ga kowa ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull