Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 41
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 41: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 41. Shi kuma bai bata lokaci ba ya rungume ni da hannayensa biyu tamkar…
4,490 words
Shi kuma bai bata lokaci ba ya rungume ni da hannayensa biyu tamkar zai kare ni daga duniya. Rungumar ba ta da ƙarfi ba Yana shafa bayana a hankali, yana sauke numfashi wanda yake cike da soyayya marar iyaka.
A cikin wannan rungumar, muryarsa ta sake rikicewa, tana fita kamar ta wanda zuciyarsa ta yi nauyi sosai “Kada kiyi kuka, Ramie… don Allah kada ki saba min da hawaye. Kin san hawaye naki suna karya zuciyata.”
Na kara fashewa da kuka saboda yadda kalamansa suka shige ni fiye da komai. Ga wani tsananin xafin da kafata ma.tsoron Ya ɗagani kadan daga kirjinshi, ya riƙe fuskata da hannayensa, yana share hawayen da yake ƙoƙarin ɓoyewa amma ya kasa.
“Yar aljannata… kina ji na?”
Na lumshe ido saboda rawar da jikina ke yi, amma na iya cewa cikin sanyi “ ina ji…”
Ya girgiza kai a hankali, murya ta sake rikicewa “Ni ma ban san me ke samuna ba… sai dai nasan abu daya ba zan taɓa bari kiyi kuka ni ina raye ba.”
Na sake jingina kaina a kirjinshi wannan karon ba don tsoro ba, sai don zuciyata ta sami natsuwa a wurin da ya fi dacewa da ita.
Yana shafa bayana cikin sanyi, yana sauke kalmomi masu taushi da nauyin soyayya:
“Kada ki gudu min… kada ki jin tsoro wannan shine favourite abunda nakeso. Ni dake nake… daga yau har zuwa duk ranar da Allah Ya rubuta min numfashi.”
Da muka shiga bandakin, hasken toilet ya laushi sosai...
Ya tsaya a gabana na ƴan dakiku biyu yana kallona kamar yadda jarumin Indiya ke kallon masoyiyarsa kafin su yi magana.
Ruwan zafi yana ta huci a gefe, yana bada ƙamshi da sautin da ya cika gurin da nutsuwa.
Ya matsa kusa da ni sosai, amma ba da sauri bada laushi, kamar wanda ke tsoron kada ya katse natsuwar da take tsakaninmu.
A hankali ya ɗaga hannunsa ya kama gashin kaina, yana shafawa Ya ce cikin murya mai laushi, ta zuciya “Ramie… idan kina gajiya, ki bari in miki wankan da kaina”
Yadda ya furta hakan ya sa idona lumshewa ba tare da niyya ba.
Ya ɗauko robar ruwan zafi, ya gwada da hannunsa, sannan ya matsa kusa da ni a hankali.
A bakin wuyana ya zuba ruwan sannan ya shafa gefen wuyana da tawul ɗin kamar yadda ake gani idan jarumi yake kula da matar da yake so fiye da numfashinsa.
Ruwan ya zubo yana tafiya a hankali a jikina, amma ba ruwan bane ya sa na ji kamar na narke ina jin kulawarshi ce.
Ya ɗan durkusa kadan ya zo da fuskarsa kusa da wuyana, murya ta fita kamar raɗa
“Kada kiyi kuka. Ki dubeni, Ramie.”
Na ɗago ido a hankali, idanuwana cike da hawaye amma ba na ciwo ba na natsuwa da soyayya.
Ya yi murmushi mai taushi, irin murmushin Indiya da ya kan sauƙaƙa zuciya tun kafin kalmomi su fito.
Sannan ya ɗora hannunsa a gefen fuska ta, ya share gefen idona yana cewa
“You are my peace… my little blessing.”
Ya jawoni a jikinsa da natsuwa ba karfi ba a slow-motion style, irin yadda ake ganin hugg a Indian movies.
Ruwan zafi yana ci gaba da tururi a gefe, ƙamshin sabulun bandaki yana tashi, jikina yana jin kwanciyar hankali kamar ruwa mai taushi ya lullube ni gaba ɗaya.
Ya rungume ni yana jingina kansa a saman gashin kaina, yana sauke numfashi..
kukan shagwaba,
na jin daɗin kulawa,
kukan da mace ke yi idan ta sami wurin da zuciyarta takan samu hutu.
Na manna fuskata a ƙirjinsa, hawaye suna shatata cikin ruwan zafi da tururi.
“Ka sauƙaƙa min… don Allah… ka tsaya nan ka riƙe ni…”
na ce a hankali, muryata tana rawa tamkar amaryar da ta tsinci kanta cikin soyayya mai yawa.
Shima ya tsare bayana da hannuwansa biyu, ya ƙarasa jinginowa da ni cikin ruwan,
kamar jarumin Indiya da yake rarrashin masoyiyarsa a cikin ruwan rain scene.
“Shhh… Ramie… I'm here.”
Muryarsa mai laushi ta shiga kunne na.
Ya ɗaga haɓata da yatsunsa, ya share hawayena yana dubana da idanuwansa masu cike da tausayi da soyayya.
“Kada kiyi kuka… kin ji?
Kukan ki yana karya min zuciya fiye da komai.”
Na sake rirrike shi, jikina yana rawa da shagwaba da natsuwa.
“Ramie… I promise… you are safe with me.
I will hold you… as long as you need.”
Ya shafa bayana a hankali,
yana lumshe ido kamar wanda ke jin daɗin kasancewa kusa da ni fiye da numfashinsa.
Tururin ruwan ya lullube mu biyu,
jikinsa ya kafe ni da zafin kulawarsa,
ni kuma ina zuba kukan shagwaba a ƙirjinsa
amma wannan kukan ba na damuwa ba ne…
Kukan mace ce wacce ta samu masoyin da ya iya rarra
(KUYI HAKURI DA WASU KALAMAN MASU TSAURI INAYIN WASU DAN AIKA SAKO NE👌👌Ku saurara da kyau, domin wannan magana ba ta buƙatar laushi.
Hakkin miji ba abin wasa ba ne. A matsayin mace, ba girki da kwalliya kaɗai zasu rike miji ba. Idan kika kasa kula da shi a gadon aure, kina tozarta hakkin da Allah ya ɗora miki mata dayawa basu iya sarrafa maza ba sai dai su kwanta su bar miji da aikin sarrafasu to tayaya zai dinga marmarinki yana shaawarki?? Yawancin matan aure na yin babban kuskure
su bar miji cikin buƙata bakisan me yafison taɓawa jikinsa ba bakisan komai ba, su ki kulawa da shi, su yi kamar saduwa ibada ce da ba ta da muhimmanci… to wallahi ku gyara gadonku ki iya mitsitsike mijinki wai ku bakusan lada kuke samu ba??
Me mazan suke.boyewa kullum cikin wayoyin nasu? Har basu so matan su gani? Kalmomin batsar ne da kalamai na romancing wanda kika kasa yimasa.. Me kike tsammani zai faru idan kika bar mijinki da kishinsa, da sha’awarsa, da damuwarsa, ba tare da kin kula ba? Idan ya sami wata wacce ta iya lallashi, nutsuwa, magana mai sanyi, kyakkyawar kulawa, wacce ta san Yadda zata suɗe miji da lasheshi ta sarrafashi akan gado.. sai ku fara cewa an tayi masa sihiri.
Wallahi ba sihiri ba ne! Aikin da kika ki yi ne wata ta yi. Allah ya ɗora wa mace ta kasance abin kwanciyar hankali, abin rarrashi, wacce ta iya sassauta zuciyar mijinta, ta taimaka masa wajen cifano soyayya da nishaɗin aure.
Ki kula da mijinki a gado kamar yadda kike kula da shi a girki da motsa jikinki.Ki nuna masa soyayya, ki sassauta masa, ki rarrasheshi a lokacin da yake buƙata, ki zama mata mai fahimta ba mai hujja a kowane lokaci ba.Aure fa ba wai zama kusa da juna bane kawai aure hutun zuciya ne, kuma mace ce ginshikin hakan.Idan kika dushe, gidan zai dushe. Idan kika yi sakaci, ƙofa ta buɗu ga fitina.Idan kika bar hakkin mijinki, rami kika tona da hannunki.Ku gyara tun kafin lokaci, ku kula da gidajenku, ku rike mazajenku da hikima, soyayya, da kyakkyawan kusanci.)
09030569336
NANA HADIZA
[29/11, 1:18 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA ƊARI DA GOMA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Safiyar ta waye cikin natsuwa. Hasken rana mai laushi ya fara shiga ɗakin ta bayan labule.
Na fara farkawa cikin jin zafin jikinsa a gefena, hannunsa har yanzu ya riƙe hannuna kamar wanda ya kwana yana tsare min zuciya.
Lokacin da na motsa ƙasa kadan, sai ya buɗe ido a hankali, yana murmushin da ya cika ɗakin da wata nutsuwa mai kama da salo na msoyaaa
“Good morning… my Ramie,” ya ce da muryar barci, mai sanyi, mai laushi, mai tsinke zuciya.
Ya kai hannunsa ya shafi gefen fuskata kamar yadda jarumi ke shafa fuskar masoyiyarsa a film ɗin soyayya kafin su tashi daga gado.
Na lumshe ido saboda yadda taushin hannunsa ya shige ni.
“Ka tashi lafiya?” na tambaye shi cikin wata murya da ta fito da sakaini.
Ya murmusa yana matso da ni kusa da ƙirjinsa da natsuwa “Lafiya… saboda kina kusa da ni.”
Kamshi sosai ke fitowa daga gefen gadonsa wani abar turare ce da bantaɓa ganin irinta ba, yana tuna min da yadda daren ya kasance cike da kulawa da rarrashi.
Ya ɗaga kaina daga ƙirjinsa, ya kalle ni sosai cikin hasken rana, ya ce “Kin san yau?
Wannan itace safiya mafi natsuwa da na taɓa yi… saboda na farka ina ganin fuskarki.”
Sannan ya ɗora goshinsa a saman nawa a hankali, tamkar wanda yake yi min addu’a da shagwaɓar soyayya lokaci guda.
Na saki ƙanƙanin dariya cikin kunya, na ɓoye fuska a ƙirjinsa.
Shi kuma ya jawoni ya rungume ni.
“Karki tashi yanzu… ki tsaya min.
Safiya ta fi kyau idan kina jikina.”
Ya kai hannunsa ya gyara gashin kaina da wata irin kulawa wadda tafi magana tasiri, sannan ya rike gefen kumatuna da yatsunsa biyu, yana kallona.
“Do you know…,” ya fara, muryarsa tana girgiza kadan,
“…ayyukan nan na last night da kukanki da rungumar ki… sun sauya min komai.”
Na kasa magana.
Kallon da yake min ya zama kamar yana karanta zuciyata.
Ya ce a hankali, kamar raɗa
“Kin bude wani bangare a zuciyata da ban taba bari kowa ya shiga ba.”
Ya sauke hannunsa zuwa wuyana a hankali, yana shafawa kamar baya son in yi karo da wata wahala.
“Your tears, your shyness, the way you held me… Ramie,
sun bani wani abu da ban taba ji ba
a need to protect you with everything I am.”
Na ji numfashina ya tsaya na ɗan lokaci.
Na ce cikin murya mai sanyi, kamar yar baby
“Am I really that important to you?”
Ya yi murmushin da ya sa zuciyata ta yi wani irin tsuntsuwa.
Ya jawo hannuna, ya sa a saman kirjinshi, inda bugun zuciyarsa ke tsalle da karfi.
“Ki ji…
Every heartbeat is saying your name.”
Hawaye masu sanyi suka sauko min saboda irin zurfin soyayyar da kalamansa suka tsaya da ita cikin zuciyata.
Ya share hawayen da yatsunsa sosai a hankali, yana ce min “Don’t cry, my Ramie…
I'm here,I’m staying…In this life,in every life God gives me you are the one I want.”
Sannan ya jawoni cikin runguma mai zurfi, irin wacce bata da tsari sai emotional peace,
ya lullube ni da jikinsa Na lumshe ido ina jin numfashinshi a fuskata, sannan na furta cikin shagwaba“Don’t leave me…” Ya ce cikin murya mai nauyi, yana dan daga hancina saman nasa .“
Kiran wayar da aka yi masa ya katse tattaunawar da muke yi, ya miƙe cikin nutsuwar mutumin da duniya ke jiran kalamansa. Wannan irin mikewar ce ta maza masu iko ba a garajen tashi, amma a kallo ɗaya ka san akwai al’amuran da suka fi komai muhimmanci a dakon sa.
Ya fita da sauri, ba tare da ya rufe ƙofar ba. Wannan ma ba sabon abu bane rayuwar CEO da yake jagorantar kamfanoni a lokaci guda ba ta bashi sukuni.
Bai jima da fita ba sai ga shi ya dawo, ya cire wristwatch ɗinsa mai daraja, ya wuce kai tsaye wanka. Wankan sa ko da yaushe yana da tsari ruwa mai dumi, steam, da ƙamshin cedarwood da yake manta gajiya.
Bayan ya fito, ya kunna tab dinsa, ya ɗora green tea ɗinsa a gefe. A idanuwansa akwai jan gajiya amma muryara? Har yanzu tana ɗauke da iko da nutsuwar shugaba.
“Zan fita na minti biyar kacal,” ya ce min, ba tare da ya kalle ni sosai ba ya riga ya saba gani nacikin nutsuwa ta alfarma, hakan ma yana bashi kwanciyar hankali.
Sai ya durƙusa kaɗan, ya yi min light kiss, sannan ya fita. Na san zai iya komawa bayan minti biyar… saboda wani emergency meeting saboda haka ban taɓa damuwa da lokacinsa ba. Yana da daraja fiye da lokacin da yake samu.
Na zauna na lumshe ido na dan lokaci. A gidan da na taso ma, akwai dukiya, akwai jin daɗi. Amma gidan nan da na aure wani daban ne Alfarma ce ta duniya ba tare da iyaka ba.
Na miƙe cikin salo, slippers dina na designers suna yin soft sounds a kan marble floor ɗin ɗakin. A nan babu gyaran da zan yi da kaina ma’aikatan floor biyu ne suke kula da wani sashen na ɗaki ɗaya.
Na buɗe wardrobe dina, wacce take budewa ta atomatik, sai haske ya gauraye kayan designers dina da ake jera su . Na tsaya na yi murmushi kayannan su ne na tsohon rayuwata, amma a gidan mijina, komai zuƙuɗe yake, komai high-end ne.
Na tuna lokacin da ya ce min “You grew up wealthy… but I want you to live untouched luxury. Baki da part. Baki da boundary. This is your home.”
Na shiga wanka. Ba wankan gajiya ba, wankan mace da taso cikin jin daɗi wanda ta sake aure ta shiga wani level daban.
Warm water. Laushin towels masu fluffy.
Turaren mai calming effect.
Na fito na saka farar abaya simple, elegant, amma mai daraja. Tunda ina so simplicity ɗina ta bayyana, ba wai saboda tsoro ba amma saboda class doesn’t shout.
Ina tafiya ina tunanin shi. Yana da kuɗi fiye da tunani… amma babu lokacin da zai iya ba ni yadda nake so.
Shi ne kalubalen auren manya.
Kudi suna bayar da komai amma ba lokaci.
Cikin nutsuwar mace da ta saba alfarma na zauna a babban falona, ina jira. Na san shi idan ya fita minti biyar, zai iya zama goma idan ya ce yana nan zuwa, zai iya zuwan ne ko bayan nan a wanni.. Wannan shi ne kalubalen rayuwar auren multibillionaire ba ka auren mutum ɗaya ne kawai ba, ka auri lokaci, ka auri world commitments nasa.
Ban jima da zama ba na ji ƙarar budewar ƙofar da irin murya mai nauyin authority.
Ya shigo cikin nutsuwa, kamar yadda yake kullum ba da sauri ba, ba da ƙoƙarin jawo hankali ba, amma dukkan wuri yana sanin ya dawo.
Yana sanye da riga mai launin navy blue, fresh daga steam cabinet. Ya dube ni kaɗan, ya yi murmushin da nake ji har cikin zuciyata.
“Breakfast?” ya tambaya, murya mai cike da iko amma mai sanyi idan ya zo kaina.
Na mike a hankali. “Yes,” na ce masa cikin ladabi mai alfarma.
Mun zauna kan dining table ɗinmu na tinted-glass, wanda ke kallon swimming pool. An jera breakfast cikin salon manya fresh croissants,scrambled eggs, avocado slices,strawberries,lemon tea da wani ɗan ƙaramin bowl na honey.
Ma’aikatan kitchen suka ja gefe, suka bar mu mu kaɗai ba ya son cin abinci tare da ni a gaban jama’a. Muryar sa tana da kuzari kadan fiye da yadda ta kasance da safe, alamar ya shawo kan wani important call.
Ya zuba min tea, kamar wanda yake ganin aikin ma’aikata ne, amma bai yarda su karɓi wannan damar daga hannunsa ba.
“Kin yi bacci lafiya?” ya tambaya.
Na ɗan murmusa. “Eh. Kai fa?”
“Na saba,” ya ce. “Sleep is a privilege I don’t always get.”
Sai ya ɗan dube ni sosai, kamar wanda yake son tuna wani abu da ya jira ya furta tun safe.
Ya ajiye spoon ɗin da yake riƙe da shi, ya shaƙe hancinsa da ƙamshin turaren jikina, sannan ya ce “By the way…”
Ya ɗan jingina a kujerarsa, yana kallona da idanu masu nannade da sirrin ƙauna da iko
“…private jet ɗina zai tashi karfe 12:00. Zamu je Bora Bora.”
Na tsaya cak. Ba don ban saba da surprise trips ba, amma Bora Bora ba normal luxury bace ita ce luxury ta daya da ke zuwa honey moon.
Ya ƙara cewa cikin salo “Tayar da kanki. Na aika stylist ɗinki. Ki zaɓi komai da kanki.
Muna buƙatar breathing space you and me. Away from meetings, away from noise.”
Ya ɗan dafa hannuna da tips na yatsunshi, yana motsa su a hankali “Ki shirya, princess.”
Zuciyata ta buga da natsuwar farin ciki. Na san idan ya yi plan, ba abu bane da ake wasa da shi. Bora Bora da ni da shi kaɗai wannan wani sabon page ne da nake tsammanin zuciyata za ta jima tana ji.
09030569336
NANA HADIZA
[30/11, 10:59 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA ƊARI DA SHA DAYA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Uwar amarya ta turo ƙofar a hankali, tana riƙe da wani akwati mai sheƙi. Sailub tana bayanta, hannunta ɗauke da wasu ƙananan boxes masu logo ɗin designers.
Sun shiga ɗakin kamar mata masu kawo albishir. Ba kaya bane kawai
sabon page ne na alfarma Valentino White Resort Collection,Dior Cruise Exclusives,Dolce & Gabbana 100% Italian Silk,Jacquemus Island Goddess Gowns. Uwar amarya ta matsa kusa, ta ɗaga kayan kamar tana miƙa zinari “Yarima ya ce… ki zaɓi komai da kikeso. Sauran kuma… ki ɗauka. Naki ne gaba ɗaya.”
Nayi kasa da kai cikin ladabi, amma zuciyata tana bugawa da wani irin tsantseni na farin ciki da nutsuwa “Na gode sosai.” Na zaɓi white satin two-piece mai taushi kamar hazo.
Na sa veil mai silik wanda idan iska ta buga shi sai ya yi rawa kamar fure. Na shafa Jasmine. Ina tsaye gaban mirror dina mai tsayin bango, hasken ɗakin yana haska satin ɗin jikina. Na ɗaga kai… sai na hango shi.
Asad ya tsaya a ƙofar. Cikin nutsuwar da ta fi komai rikitar da mace. Idanunsa sun sauka kaina a hankalidaga ƙafata zuwa saman veil ɗina kamar yana kallon wani abu da yake jin tsoro ya kusanto saboda yawan kyawunsa.
Ya tsaya. Ya kasa magana na mintuna biyu.
Shi da murya irin ta shugabanni… yau ta tsaya masa a maƙoshi. A hankali ya furta “Ya Allah…” “Look at you.” Ya matso… ba da sauri ba… ba da gaugawa ba…
ba kamar namiji ba kamar wani ikon da ya saba samun komai amma bai saba ganin mace ta rikita shi ba. Ya tsaya a bayana, ya dora hannayensa biyu a kan kafaɗuna hannu masu sanyi, masu nutsuwa ya kalli reflection dina a mirror. “Wannan… matar tawa ce?” Yadda ya ce tawa ya zame min sanyi a maraina. Ban iya magana ba. Veil ɗina yana zamewa.
Ya lankwaso ya sa hancinsa kusa da wuyana, yana shakar ƙamshin Jasmine Musk ɗin dake tashi. Ya yi nishi mai zafi, mai laushi, mai romantic weight “Ki kula da kanki, baby.
Domin idan mun je Bora Bora soyayyata zan zuba …” Ya dan ja hancinsa a gefen wuyana cikin sassauci. “…kar ki gudu daga jikina.” Na juyo kadan, idanuna a buɗe. “Ni nace zan gudu?” Ya yi murmushin da yake narkar da zuciya. Murmushin da yake min kyan gaske.Ya ɗaga gira yana wasa da ni. “Asad!” na ce kamar ina yin kuka da dariya. Ya yi dariya cikin muryar da nake jin kamar waƙa Ya jawoni jikin sa, ya manna ni sosai kamar yana mayar da wata sashi ta jikinsa da ya rasa. Ya kwantar da kansa a saman gashin kaina, yana bubbuga bayana da laushi kamar jaririya “Let’s go, My Peace. Jet ɗin zai tashi da mu karfe 12. Today… you’re mine alone.”
---
Mun fito daga shashen hannun juna cikin tafiyar da take bayyana komai game da matsayi iko, alfarma, da soyayyar da take ɓoye a cikin nutsuwa. Gabanmu, royal guards sun yi layi, kowannensu cikin uniform, suna durƙusawa a hankali “Ranka ya daɗe… Ranki ya daɗe…” Muryarsu tana echo Vike da girmammawa Hannun Asad a nawa ya kama shi ba da ƙarfi ba, ba da rauni ba ciken salon soyayya.
Ina jin kamshin turarensa Oud & Amber blend wani irin kamshi da yake da nauyi da daraja. Idan Asad ya wuce, kamshin na nan, kamar saƙon da ya bari a iska.
Na ɗaga kaina zan karasa ciki sai na ji muryar mace ta taso daga gefe muryar da ta yi kama da kuka amma tana kuma ɗauke da soyayyar da ta mutu. “Yarima…!!” Na juya. Ayshatu. Ta tsaya kamar iska ta buga ta. Abaya ce jikinta amma ta matse ta sosai, ba salon masarauta ba. Wannan irin abayar da ake sawa domin a jawo hankali, ba domin a nuna ladabi ba.
Idonta yana dauke da hawaye, amma ba hawaye na ciwo ba hawaye na asara.
Ta yi saurin matsowa, kamar zata riƙe Asad, amma royal guards suka matsa gefe suka tareta da ido. “Yarima… DanAllah ka tsaya ka saurare ni!” Amma Asad bai tsaya.Ko kai ba ya juyawa. Sai ya matso kusa dani. Ya ɗaga hannunsa a hankali ya gyara min veil, yana kama gefen fuskar veil ɗin.
Ya furta da muryar da ta yi laushi amma mafi ƙarfin da zuciya zata iya ɗauka“Don’t let the sun touch your face.” Na tsaya kamar an daka min tsawa. Ayshatu ta yi wani irin numfashi, idonta ya ƙara yin ja. “Asad…! Kana wuce ni haka?? Na gaisheka kayimun banza?? Ka wuce ni tamkar ba ni bace nice masoyiyarka fa??” Nan ne Asad ya juyo da kansa.Ba da tsoro ba.Ba da damuwa ba.Ba da fushi ba.
Cikin authority ɗin da yake shiga zuciyar mace kamar ruwa mai sanyi. “A girmama matar masarauta. Ba a girmama munafuka ba.”
Kamar ana harbin kalma a zuciya.
Ayshatu ta ja baya tana girgiza kai, hawaye suka zubo. Na ji jikina ya yi sanyiba saboda Ayshatu ba, amma saboda ban taɓa tunanin kalmar “matar masarauta” ba zata taɓa fitowa daga bakinsa don ni ba.
Asad ya kama hannuna sosai sosai kamar baya son na bar jikin sa. “Zo.” Mun wuce babu juyawa. Royal guards suka buɗe hanya kamar ana bude wa sarki kofa.
A harabar akwai motocin masarauta guda huɗu Jaguar, Bentley, Mercedes Maybach, da Rolls Royce Phantom.Duk suna jiran mu.
Amma Asad ya bi daya ta tsakiya, ya buɗe min da kansa Rolls Royce Phantom VIII 2024 Royal Edition. Ba sabuwar mota ba ce kawai.
Kyautarsa ta ƙarshe daga Sultan of Oman ce.
Interior cream, gold trimming, soft lighting.
Kamshi? Vanilla, saffron, da sandalwood blend.
Na shiga. Asad ya zagaya ya zauna kusa da ni ba a gaba ba. Ba a nesa ba. Kusa sosai. Ya kama hannuna, ya rufe shi gaba ɗaya da nasa yatsunsa masu zafi suna rufe frozen fear dina. “Kin shirya?” Na ce da ƙasa da murya “Eh.” Ya ɗaga hannuna, ya shafa yatsuna da nasa “Ki daina jin tsoro.
Daga yau… ba ni son ɓoye ki Ina son duniya ta san… ke ce masoyiyata.” Wani abu kamar iska ta tsaya a cikina. Na yi ƙasa da murya “habibie…” Ya kama hannuna, ya sumbaci tips ɗin yatsuna madaidaiciya. Sumbacin da ya fi na soyayya dadi ya fi na alfarma daraja. “Don’t say my name like that…” Ya matsa kusa da kunnena, murya a hankali “…you’ll weaken me.” Na rufe fuska cikin kunya.
Ya yi dariya mai laushi dariya irin wacce idan ya yi, ina jin kamar zuciyata zata faɗi ƙasa. “Let’s go.” Private airstrip ɗin sun tanada mana red carpet. Cikin uniform ɗin Royal Aviation, duka staff sun tsaya a layi suna girmamawa.“Your Highness.”“Your Highness.”
Na kama hannun Asad saboda kunya.
Ya matsa ya juyo zuwa gare ni. “Lah-Lah… ki kalle su. Ke matar Yarima ce.”Na girgiza kai
“Kaina baya so.” Ya matso ya sakar min whisper a kunnena “To, kaina yana so.” Sai ya ɗaga hannuna sama ya sumbaci ni bayan tafin hannuna gaba ɗaya ma’aikatan suka sunkuyar da kai saboda irin soyayyar da bai kamata kowa ya gani ba. Idona ya kaɗa da wani irin jin tsoro Na ce masa cikin shagwaba “Kai…”Ya ce “Yes baby?” Na ce “Kayi shiru…”
Ya yi dariya sosai, ya rungume ni a kirjinsa a gaban kowa.
Bombardier Global 7500 Cikin jirgin kamar hotel ne King size bed,Dining for two,Transparent sky-ceiling,Soft tan leather seats,Silk carpet,Gold-lined bar.
Na tsaya a bakin king-size window ina kallon sararin sama. Asad ya tsaya a bayana ya zagaye kaina da hannunsa ya dafa cikina ya manna kansa a wuyana. “Lah-Lah…”
muryarsa ta yi laushi sosai.“Gobe idan muka isa Bora Bora…zan nuna miki dalilin da yasa nace…you are my peace.”
Na rufe ido don kunya ta ishe ni. Na ce cikin shagwaba mai sanyi “Ni bansan me zaka nuna ba.” Ya yi dariya ya kamo fuskata ya sumbace gefen bakina a hankali…“Zaki gani… kuma ba zaki manta ba.” Na rikice.
Tafiya ta yi nisa. A Private Jet ɗinsa, sai karar AC take, sauran komai shiru kamar ana jin bugun zuciya na kawai.Na lumshe ido ina kallon window, ruwa a ƙasa yake kamar gilashi mai sulbi, rana na haska saman tekun.
Na ji hannunsa ya kama yatsuna a hankali.
Na juya, kamar ba da gangan ba. Nan na tarar da idanuwan Asadsiraran idanun nan na yarima, amma yau… su cika da wani abu daban. Soft. Lukewarm. Boyayyen radadi. Boyayyen so.Ya haɗiye yawu. Ya kasa boye komai.
“R…Ramlah,” muryarsa ta fita da sanyi, kamar ya sha wahalar fadi. “Kin gaji? Ki kwanta hannuna zan rikeki.”Na yi dariya cikin natsuwa.“Ina lafiya, ranka ya daɗe.”
Ya ɗan juya kansa gefe, yana murmushin da ba kowa ke ganin shi ba murmushin Asad na gaske, wanda yake fitowa idan zuciyarsa ta nutse sosai. Ya kalle ni sosai, har na ji zuciyata ta buga da karfi.
[30/11, 10:59 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA ƊARI DA SHA BIYU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
“Wallahi, Ramlah… bana jin daɗin ganin kina
Zaune ke daya.” Sai ya ɗan saki numfashi da rauni. “Ina so in kulle ki ki huta a kirji na… amma sai na ji kamar zan rikice.” Na kasa motsi. Kafin in amsa…
Pilot ya sanar “We’re landing in Bora Bora in five minutes.” Asad ya kama waist ɗina kamar zai rikeni in kada na tashi da jirgin. Idanuwansa a kaina kawai suke.
“Ramlah…” ya kira sunana da murya mai kauri amma mai laushi. “Ina fatan zaki iya jure min yau.” Ya yi shiru. “Saboda gani nayi… ba zan iya boye komai ba a wannan wuri.” Jirgin ya sauka a hankali.
An buɗe mana ƙofa, iska mai ɗumi amma mai laushi ta buga min fuska kamar ta fito daga Arabian perfumed breeze. Hasken rana ya tsaya a kan Asad, yana haskaka fatarsa tamkar zinari mai ɗaukar ido.
Su royal guards sun tsaya a layi, kowanne a sunkuyar da kai da ladabi “Welcome, Your Highness.” “Welcome, My Lady.”
Asad ya ɗan matsa kusa dani,
ya kama yatsuna cikin nasa da salo mai nutsuwa,kamar king ɗin da yake tabbatar da cewa masoyiyarsa bata ɓace masa ba.
Muka taka red carpet kamar masu wucewa zuwa wani private royal event. Sai ya ja ni gefe kadan, ya tsaya yana kallona irin kallon da ba dukkan maza suke yi ba kallo mai sanyi, mai zurfi, mai halartar zuciya.
“Ramlah…” ya kira sunana kamar waka.
“Why are you shining like this today?”
Idanunsa suka tsaya a lebena.
Ya kasa ɗaga kai sama.