Kamar da wasa complete novel - Chapter 9
Kamar da wasa complete novel Chapter 9: Kamar da wasa complete novel Chapter 9. Batare da tace komai ba ta dauka tafita, rufe dakin yayi sannan suka nufi…
3,317 words
Batare da tace komai ba ta dauka tafita, rufe dakin yayi sannan suka nufi cikin gidan ai tana jiyo hayaniyar mutane tayi azamar sake lullube fuskarta saura kadan tayi karo da itacen da aka girke domin dafa sanwa, hannunta yayi saurin rikowa dama tun adaren jiya yake da wannan burin sakamakon tafiya da hankalinshi da kunshinta yayi, babu damar yin musu domin bata ganin gabanta sosai kanta akasa yake sannan mayafin mai duhune sosai, har dakin ayiyah ya shigar da ita ya zaunar da ita nan fa aka shiga zuba guda ana shewa, shidai ficewa yayi yabar dakin duk kuma sai taji wani iri wato wurima da wanda kasani dadi gareshi amma idan akace baka san kowaba to baka iya sakewa, tana jiyoshi atsakar gida suna yarawa da kakanninsa wato abokan wasanshi yana cemusu,
"Ni duk kunyi min tsufa, ga matata can duk tafiku kyau kuje ku ganta gyalenta kadai ya isa ya siyeku gaba daya...."
Daga haka yagudu bata sake juyo maganarshi ba, duk kuma sai tashiga kadaici danma anata zuwa gaisheta kamar wata sarauniya, tana zaune shiru shiru sa'arta daya Maryam da Mariya na kewaye da ita nan tayi masa text massage tana daga tukunkune cikin mayafi,
_Wai kana inane?_
Babu jimawa saiga reply yadawo mata dashi,
_Ina zuwa nan bada jimawa ba._
Zaman shiru taci gaba dayi sai dai idan ankirata awaya ta daga amma tana jiyo hirar mutane awaje group group. Wurin sha daya da wani abu tafara jiyo guda sosai da karfi aifa nan mata aka kifa kwarya ana kida mai dadi wasu kuma na rera wakar aure,
Wasa wasa gudar nan har cikin dakin da take ta cikin mayafin ta samu nasarar hangoshi sanye da babbar riga da hula, har inda take yatako yazo ya dagata, tsakar gida suka fita inda ake yin wannan kidan, daya bayan daya ake zuwa ana zuba musu kudi shi sai asaka masa acikin aljihunshi ita kuma cikin jakarta, sunfi minti talatin tsaye ana zuwa zuba musu kudin nan ita har tagama kosawa da wannan tsaiwar danma jingine take jikinsa amma babu wanda zai gane, saida kaf dangi na uwa da na uba suka gama zuba musu kudin sannan aka maida ita daki, shi kam ficewa yayi bata kara jin alamunshi ba har azahar lokacin ne kuma aka maida ita dakinshi dake can soro wai tayi salla taci abinci, kamar kuwa sun san tana da bukatar komawa dakin domin amatse take da ta canja pad din jikinta dan ita atabar pad tadade ajikinta to tayi awa uku,neat tasamu dakin anshare angyarashi an fitar da kwanukan abincin daren jiya ankunna turaren wuta na tsinke.
Bayan su anty juwairiyya da suka rakota sun fita wanka tashiga tayishi sauri sauri tafito dan kar wani yashigo ai kuwa tana fitowa tana kokarin manna pad jikin pant dinta yashigo, danma lullube take da mayafi, bai kalleta ba yawuce gaban akwatinshi sannan ya janyo kayanshi dake rataye jikin kofa yasaka cikin akwatin, kasa saka pant din tayi agabanshi sai bathroom tawuce tasaka sannan tafito lokacin yana rufe akwatin,
"Ranki yadade kiyi sauri ki shirya yanzu za akawo miki abinci...."
Bai karasa rufe bakinsa ba yaji knocking abakin kofa, tashi yayi daga gaban akwatin,
"Inajin ma gashi nan ankawo... Bari mugani"
Kofar yabude yafita ai kuwa su mariyane dauke da kwanukan abinci, karbowa yayi yashigo dashi lokacin tana saka bangles, ajiye mata yayi yajuya ya dauko wasu kayanshi dake kan drewar din dakin,
"To hajjaju nabarki lafiya, sai mun hadu a sabon gida..."
Zama tayi tana kallonshi,
"Ban ganeba, wai kana nufin ni kadai zan zauna adakin nan shiru har lokacin da za araka ni gidanka?"
Murmushi yayi,
"Ehh mana, kodai kinfi son nazauna mu zauna tare? Kibari zan turo miki su Mariya suzo su tayaki zama"
Daga haka yadauki kayanshi har katuwar akwatin yafice, bai jima da fita ba sai gasu mariya sunzo ai kuwa tasha hira domin yaran sunada surutu shiyasa taji dadin zama dasu inbanda labarin gidan da na makaranta ba abinda suke bata. Har la'asar tana tare da yaran amma mutane na dan shigowa musamman baki masu tafiya suna yimata sallama da fatan alkhairi shiyasa zuwa karfe biyar na yamma gidan tsit sai mutane kadan na kusa amma bakin nesa kam duk sun tafi, bayan sallar magrib su anty Fauzy suka zo suka shigar da ita cikin gida lokacin ma baba yadawo har turakarsa suka kaita ta gaidashi sannan aka maida ita dakin ayiyah, ayiyah kam sai nan nan take da suruka matar auta guda komai tagani ta tura mata gabanta da haka har motar daukarta tazo, anty Fauzy da anty Kubra ne zasu rakata, daki daki aka bi da ita tayiwa kowa sallama sannan aka fita da ita bayan anfitar da kayanta,Baffa ne yayan salim a motarshi shi yadaukesu yakaisu wanda tafiyar bata da wani tazara sosai can, koda sukaje su basu wani jimaba suka yimata sallama suka fita, hamdala tayi acikin zuciyarta ta bude fuskarta tana bin dakinta da kallo wanda yasha kayan alatu domin gadonta kadai abin kallone gashi dakin babu laifi da girmanshi saboda ya cinye komai dan iya mirror dinta kadai duniyane wurin da ya lashe ba dan kadan bane cire mayafin tayi ta fita falo wanda shima ba laifi ga dining area taciki ga kitchen nan ga store cikeda kayan abinci domin komai biyar biyar abba yayi mata kama tun daga kan shinkafa, taliya, macaroni, indomie, crate din kwai,semovita manja, man gyada komai biyar,
Ba karya gidan fahad yayi domin yarone mai zuciya shi dai barshi da kwalisa da iyayi amma yanada zuciyar neman na kanshi duk da baiyi karatu mai zurfi ba domin iyakacinshi diploma kawai sai sana'ar dinki da yasaka agaba kuma yayi sa'a sana'ar ta karbeshi, iyakar gata tasan iyayenta sun nuna mata domin komai mai kyau da tsada aka yimata ita kanta gidan ya burgeta dan dagwas dashi shi ba kato can ba kuma shi ba karami can ba abinta dai dai misali, tsakar gidan dan madaidaicine yasha interlocks harda flowers shuke sai pop shikenan sai kofar falo ma'ana dai safe content ne komai aciki, abu dayane yabata takaici bedroom guda daya zasuyi shearing tunda ga dayannan ba agama ba asalima data buda ko fulasta ba ayiba sai uban tarkacen kayan aikin gidan da aka zuba aciki aka rufe, alhalin gado guda biyu abba yasai mata kamar sauran yan uwanta gashi karshenta sai dai komawa akayi dashi gida......
*kamar da wasa na kudine idan har kin san baki biyaba dan girman Allah karki karanta.*
*_Ummi Shatu_*👌🏻 [11/28, 08:17] Hafsat Rano: © *HASKE WRITERS ASSO.*
*KAMAR DA WASA....!*💖
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
*17*
*Kamar da wasa na saidawa ne yar uwa idan kinada bukata kisiya sai ki karanta.*
***Ba karamin kyau tayi masa ba, yau sai yaga tafi koyaushe kyau kamar zaka saceta ka gudu ko kuma ko dan bai taba ganinta cikin kwalliya kamar haka bane shiyasa yau yaga kamar canjata akayi? Kunshin dake hannunta yaketa zooming yana kallo sannan yakoma kan fuskarta itama yarinka zooming dinta yana gani,dariyar shakiyanci yayi lokacin da ya kurawa kirjinta ido bayan yayi zooming,
"Aita boye abu ayita boye abu to yau dai gashi ina kallo..."
Saida yagama ganin komai sannan yatashi yafita sallar magrib bayan ya kullewa salim dakinshi, daga can gidansu yawuce alla alla yake yi gobe tayi adaura aurensu da bilkisu shiyasa a wannan daren baccinshi rabi da rabine yayinda ita kuma amaryar ma gaba daya daren ranar kasa bacci tayi kwata kwata bare gashi bata salla balle tatashi tayi sallar nafila ko tarage damuwa shiyasa abun yayi mata yawa, juyi kawai tai tayi danma da alama agidan ba ita kadaici bata yi baccin ba domin tana jiyo kannen ammah sunata shan hira da yan garko awannan tsohon daren, sai daf da asubah tasamu bacci ya dauketa,wurin 6 da wani abu tatashi tayi wanka tashirya cikin daya daga cikin dinkin da fahad yayi mata,yake kawai takeyi amma zuciyarta cike take da damuwa da bacin rai, gashi ta kasa cin komai sai ruwan lipton kadai da tasha. Fahad kuwa tun asussubah yatashi dama bacci sama sama yayi shi, karfe tara zasu tafi garin garko inda acanne za adaura auren, kamar bilkisu shima kasa cin komai yayi dakyar ayiyah ta tirsasashi yasha ruwan koko daga nan wanka yayi, tun yana cikin toilet din yasoma jiyo hayaniyar mutane yan zuwa daurin aure domin kofar gidansu ne m point din, yana fitowa babu bata lokaci yazuba sabuwar farar shaddarsa harda babbar riga yasha turare, kai wannan ango yasha kyau gaskiya domin ba karamin fitowa yayiba fess, koda yafito kansa har wani sara masa yayi saboda al'ummar da yagani, abokanshi ne, yan shagonsu, abokan yayyenshi, yan uwa da yan unguwa ga uban tarin motoci jere reras, salim ne yakama hannunshi sukaje har gaban motar da zai shiga suka shiga nan kowa yashiga dama su baba sunyi gaba nan suma suka dauki hanya, haka kawai garin yayiwa fahad kyau bama shi kadai ba kusan kowa da wannan shine zuwansa nafarko garin ya burgeshi, babban masallacin garin acanne za adaura auren bayan an idar da sallar juma'a,
Bilkisu tana can gabanta sai faduwa yake wanda bata san dalili ba sai dai tana danganta hakan da wannan auren da za adaura mata shi yau gashi kuma ayau din za akaita gidansu fahad domin yau ammah ke gudanar da yininta shiyasa su maama sun kammala kintsa mata kayanta gaba daya hatta wanda zata tafi dasu gidansu fahad an shirya mata cikin daya daga akwatinta na lefe. Ana idar da sallar juma'a aka daura auren fahad da bilkisu akan sadaki naira dubu talatin,bayan an gama daurin auren sun daddauki hotuna suka dawo, direct gidansu bilkisu suka wuce lokacin tasake wanka tashirya cikin leshi riga da skirt,tun kafin tafito su meenah suka rigata sukaje sunata hotuna da ango da abokansa,ita kam adole tafita itada khulsum bayan angama yimata kwalliya,
Kasa kasa take kallonshi tana son taga koda gaskene yayi kyau din kamar yadda taji su hindu nata zuzutawa, babu laifi kam yafito sosai,shima anasa bangaren tunda ya hangota hankalinsa yayi kaura daga gareshi yakoma kanta saboda ta hadu iya haduwa shiyasa har dana sanin kwaso abokansa suzo ganinta yayi, wani kishine ke lullube zuciyarsa sama sama duk abinda yakeyi idonshi na kanta, saida suka gama yin hotuna da mutane sannan yamatso wurinta nan fa kowa yarude da daukarsu awaya, ita haushima abin yake bata,
"Barka da yau Hajjaju...,ya fama da jama'a?"
"Alhamdulillah"
Shine abinda tafada kawai suka cigaba da hotuna, ana gamawa bilkisu takoma gida, angwaye dai daga can wurin walima suka wuce wadda zasu gabatar afilin makaranta. Bayan su Abba sun dawo kiran bilkisu yayi domin abata sadakinta sannan yakara yimata Nasiha shida waliyyinta, duk saida tabi ta bata kwalliyar fuskarta da hawaye da kuka shiyasa tun daga lokacin ba akara samun kanta ba har dare lokacin da za arakata domin fada ne na iyaye daga wannan yagama sai wannan yazo yayi nasa, ya mudan shima harda zuwa yayi mata nasihar azauna lafiya sannan yabawa maama dubu goma yace abata Allah yasanya alkhairi, tun bayan magriba su khulsum ke binta tatashi tashirya amma taki tashi saida aka fadowa ammah ai iyallo naji tazo tahau fada babu shiri tatashi tashiga bathroom tayi wanka tafito, abinci kam rabonta dashi tun jiya da rana, kayan da zata saka sai faman jikeshi da turare su meenah keyi kamshin har hawa mata kai taji yanayi, hatta pant din da zata saka gani tayi maama na shafeshi da almiski, tabe baki tayi tazauna gefen gado ta bude drewar din gadonta ta dauko pad ta warce pant din a hannun maama azuciyarta tana cewa,
"Yara kwayi kwa gama"
Bra din da zata saka ma itama saida suka tsuma ta da turare daga nan kuma suka dawo kanta itama zasu shafeta da madarar turare, tana ki tana komai saida suka shafa mata sannan tasaka kayanta tanemi wuri ta zauna duk da tanaji ana cewa tafito amma taki koda motsi saida su hajjaye suka zo suka fito da ita, saida aka kaita wurin ammah da abba tayi musu sallama sannan aka fita da ita inda motoci ke jira, kawarta khulsum ce agaba sai su iyallo da suka sakata atsakiya ba awuce dasu ko inaba sai gidansu fahad inda dangi sukayi dafifi suna jiran zuwansu, dakin ayiyah aka kaita tana lullube cikin babban mayafi, saida aka gama yan gaishe gaishe da taya juna murna sannan aka damka amanarta a hannun su ayiyah daga nan yan kawo amarya suka tafi bayan su maama sun shigo mata da akwatinta.
Duk dauriyarta saida tayi hawaye lokacin da taga kowa yatafi anbarta acikin mutanen da bata saniba,mutane sai zuwa ganinta akeyi amma babu Wanda yasamu nasarar ganin fuskarta saboda a lullube take. Har wurin karfe goma saura mutane basu daina shigowa ba sai gajiya su anty Fauziyya sukayi sukace arakata masaukinta ta kwanta ta huta, yaya asabe ce takama hannunta suka fita tarakata dakin dake soro wato dakinsu fahad su maryama kuma suka biyosu da akwatin kayanta da food flasks din abinci guda biyu, zame mayafin kanta tayi bayan sun gaggama ficewa tafara bin dakin da kallo, babu wani tarkace dayawa aciki sannan dakin baida girma caan dan madaidaicine mai dauke da babbar katifa anshifideta da sabod bed sheet sai akwati babba guda daya amma dakin fes yake yasha sabon fenti da jan carpet malale aciki ga kofar toilet nan komai dai neat, bata ko taba Food flasks din da aka kawoba taci gaba da zamanta shiru har goma da wani abu sai lokacin taji gidan ya danyi shiru alamar mutane sun ragu, sha daya saura yan mintuna taji alamun bude kofa gyara mayafinta tayi ta lullube jikinta,fahad ne yashigo rikeda leda,yana sanye da danyen boyel kalar ruwan siminti kanshi babu hula, sallamar da yayi kawai ta amsa daga nan ta guntse bakinta, agefen katifar ya zauna yana zaro wayarshi daga aljihu,
"Hajjaju yagajiya?"
"Alhamdulillah"
Bai kara magana ba yamaida hankalinsa kan wayar hannunshi, ita dai tana zaune ta jingina da pillow sai karkada kafa take kamar wata sarauniya, sunfi minti biyar ahaka babu wanda yasake cewa uffan sai karar fanka da ta cika dakin, ledar da yashigo da ita yamika mata gabanta ya ajiye,
"Ki ci abinci gashi nan..."
Batayi magana ba ta dauke kai,
"Kinji...."
"Naji..."
Tabaya ya kwanta rigingine yana kallon sama yana danna wayarshi zuwa can yadago ya kalleta,
"Bazaki ci abincin ba ne? To kitashi kiyi wanka ki kwanta"
Shiru tayi batayi magana ba yayinda shikuma yatashi zaune ya buda ledar dake ajiye agabanta yadauko malt guda daya ya balle ya dan sha sannan ya ajiye, Flaks din da ke ajiye ya bubbude, sakwara ce da miyar ganye tasha kaji gashi ta soyu, dama yunwa yakeji dan shima rabonshi da abinci tun yaushe mikewa yayi yashiga bathroom ya daurayo hannunshi yadawo yaja abincin gabanshi yafara ci tana zaune tana kallonshi dama guda ukuce sakwarar babu bata lokaci yatashi da guda biyu, kallonshi tayi adage,
"Malam jimana...."
Dagowa yayi ya kalleta,
"Ai abincin nawane ba naka ba so zaifi kyau idan kabar min kayana haka"
Tsame hannunshi yayi daga cikin miyar yamayar da murfin ya rurrufe sannan yajanyo ledar gabanta yabude, gasasshiyar kaza ce mai romo sai kayan sanyaya makoshi malt guda biyu da fresh milk zindimemiyar roba, kazar yabude yasoma yaga yana ci yana korawa da malt,
Harararshi tayi ta janyo flask din gabanshi tana turo baki budewa tayi itama tafara ci tana kallonshi yanata cin kazarshi,
"Gaskiya wannan yaron akwai mugun ci....tab"
Sai da yaci rabin kazar sannan yamike yashiga bathroom, wanka yazarce dayi shiyasa yajima aciki, tana cin abincin tana sake jinjina kuruciyarsa to inbanda kuruciya menene na zama yacinye kazar da ita yasiyowa?
Itama da kazar ta dora bayan ta cinye sakwarar amma bata ci da yawaba domin cinya kadai taci da dan abinda ba arasa ba saboda tarihi ko nan gaba zata tuna da taci kazar aurenta. Tana kammalawa yana fitowa daga wankan da kayanshi ajikinshi gaban akwatin kayanshi yatsaya yabude yaciro riga da wando roba kamar sport wear yakoma bathroom din yasaka sannan yafito tana zaune inda take yazo ya kwanta saitin kafafunta bayan yaja pillow daya, babu jimawa yayi baccinshi,saida taga yayi bacci sannan ta mike tashiga bathroom ita a ka'idarta idan tana period indai zatayi fitsari to saita canja pad, shiyasa saida ta dauki pad acikin handbag dinta sannan tashiga toilet, jikinta kawai tagyara amma batayi wanka ba ta canja pad tafito, akwatin kayanta tabude wai kozata samu kayan da zata saka tayi bacci dasu amma abin haushi duk night wears din bazata iya sakawa ba domin duk marassa nauyine kuma asha shagarai tasan da biyu su meenah suka yimata haka gashi ita bata iya kwana da kaya ajikinta ba, daga karshe dai sai hakura tayi tamaida akwatin tarufe, juyawa tayi ta kalleshi yawani baje yana baccinsa cikin kwanciyar hankali ga sanyin fanka yana fifitashi, bra din jikinta ta cire tabar kayan dake jikinta taje gefen katifar ta zauna ta kishingida, wayarta taciro ta duba misalin karfe daya nadare agogon wayar ya nuna mata, kashe wayar tayi tai addu'a ta shafa sannan tamaida kanta kan pillow dayake itama amutukar gajiye take bata wani jimaba bacci yace muje zuwa......
*_Ummi Shatu_*👌🏻 [11/28, 08:17] Hafsat Rano: © *HASKE WRITERS ASSO*
*KAMAR DA WASA...!*💖
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
*19*
Cikin bedroom dinta takoma ta zage tashiga toilet tayi wanka tafito ta zauna tayi shirin bacci cikin wani night wear milk colour riga da wando,wandon iyakarshi cinya sai rigar da bata wuce cinyaba itama, handbag dinta ta janyo ta debo wayoyinta gaba daya ta kashe sannan ta rufe jakar da kamar ta zauna zaman kirga kudaden dake ciki wadanda aka zuzzuba mata tabari sai zuwa gobe ta kirga domin bacci kawai take ji, kashe wutar dakin tayi tai kwanciyarta bayan ta lulluba domin bata iya kwanciya da kaya ba ajikinta tasan babu mamaki cikin dare idan zafi ya dameta ta fige rigar ma gaba daya. Misalin karfe 10 saura fahad yashigo gidan tareda tawagar abokanshi wadanda suka iyo masa rakiya, key dinshi yadauko yabude gidan yashiga yana jin wani farin ciki na ratsashi, har falo suka shiga danma baiyi garajen kaisu dakiba kamar yasani yace kawai su tafi yasan yanzu tayi bacci amma sukace karyane kawai dai yana yimusu kora da haline, bedroom yawuce yana shiga ya kunna fitila awayarshi ya haska ya kunna wuta, bude ido daya tayi ta kalleshi jikinta lullube da duvet hular kanta ta cire saboda santsi,kitson ya zubawa ido kamar yasamu tv
"Yadai....?" Ta fada tana yamutsa fuska domin ba kadanba sosai tafara jin dadin baccin da ya katse mata ta hanyar kunna wuta itafa duk dadin barci da nisan da yayi matsawar zaka kunna wuta to sai ta tashi,
"Ah babu komai..."
Daga haka yakashe wutar yafita,
"Ai nafada muku dama tayi bacci, yanzu gashinan haka kawai kunsa na tashi baiwar Allah..."
"Dakyau mijin yar gata... Wato ma idan tana bacci ba atashinta" inji hamza na shagonsu, shi dai alla alla yake su tafi domin shima yana son ya kwanta ya huta, ai kuwa sun wahalar dashi kafin su tafi daga karshe daya bayan daya yarinka turasu sannan yamaida kofar gidan yarufe yadawo ciki itama kofar falon yarufe yashiga dakin, wannan karon bai kunna wuta ba kawai da fitilar wayarshi yayi amfani yashiga bathroom bayan yadauki kayan baccinshi, wanka yayi,yana cikin wankan yalura da pad din data jefar cikin dustbin duk da haka bai hakuraba saida ya dauki dustbin din yayi masa kallon kurulla daga karshe dai yagane menene, baki yatabe yasaka rigar baccinshi armless da wandonta duk jajaye, yana rike da kayan da yacire, drewar yabude ya watsa kayan sannan yafita falo dan bazai iya bacciba sai yaci wani abu, balangun da yazo dashi yabude kulli daya yaci yakoshi sannan yasha yoghurt guda daya sauran yasa cikin fridge, dakin yakoma yaje kan gadon yana shirin kwanciya yaji tace,
"Malam yadai?"
"Kamar ya? Kwanciya zanyi mana"
"Bana skwatin, ban iya kwana mutum biyu agado daya ba..."
Da mamaki yake kallonta duk da ba ganinta yakeba tunda dakin akwai duhu,
"Amma dai ai kema kin san gadon nan yayi miki girma ke kadai...."