Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 38

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 38

..... he got down in his anger and asked her younger brother to continue living in the house. He also didn't speak again and fixed his body and put on clothes. She was just following him and looking at him. Her heart is filled with his love, and finding a husband like him is not a small pleasure. He came to the front of the bed and stood with his hands in his pockets, looking at her face in the evening, even if she couldn't look into his eyes. They have been married for eleven years, but she still can't look into Zak-Shadow's eyes despite her intelligence and her intense love for him. At the end of civilization, when she was two years old, she was taken to the UK, and she never went to Nigeria until she was an adult and when they got married. She used to feel that he was charming and full of her every time he was in front of her, sometimes she even went to talk to him on the phone rather than face-to-face. She wrapped her arms around his neck and rested her head on his chest. So he took her into the bathroom and went to the jacuzzi. Down to earth in whispers and a style of love like that of adults is wan.....

Standalone post1,986 words

........A wahale ta kalla agogon dake bangon ɗakin, ƙarfe shida saura fa na yamma. Wani irin ciwo ƙasusuwanta ke mata, tun kusan ɗaya da rabi bawan ALLAHn nan bai barta ta huta ba, sallar la'asar ma a ɗakin yayi ta, duk da yanda yaga tayi laushi tun ɗazun bai raga mata ba har sai da ta fara masa kuka da roƙo da magiya, a hankan ma sai da ya mula dan kansa... Fitowarsa a bayi ya katse mata tunani, ɗaure yake da towel yana tsane jiki da wani, suna haɗa ido ta tura masa baki. Nashi bakin ya ɗan taɓe yana ɗauke ido a kanta shima. Sai da yaje gaban mirror cikin muryarsa data koma can ƙasa ya furta, “Ki tashi ki gyara jikin ki raguwa kawai. Ki damu mutum yazo-yazo sai yazo kuma kiyita raki”. Cikin sake tura baki ta ce, “Kai dama ai baka da tausayi wani lokacin, amma idan bani ɗinba ma wazai iya da kai. Kuma ni ALLAH bazan iya tashi ba, bakaji ƙasusuwana ba kamar ana sassarawa fa”. “Da sauƙi ma tunda sarawa ce ba niƙawa ake ba”. Ya bata amsa cike da gatse. Bata sake cewa komai ba, dan so take ya sauka a fushin nasa yabar ƙannenta su cigaba da zama a gidan. Shima bai sake magana ba ya gyara jikinsa tare da saka kaya. Ita dai tana binshi da kallo harya kammala. Zuciyarta kuwa wani ƙara cika take da soyayyar sa, tasan samun miji irinsa ba ƙaramin morewa bace. Gaban gadon yazo ya tsaya hannayensa a cikin aljihu yana kallon fuskarta dake a marairaice, ita ko ta kasa kallon cikin idonsa. Shekara ta goma sha suke da aure, amma har yanzu bata iya kallon tsakkiyar idon Zak-Shadow duk da wayewarta da matsanancin soyayyar da take masa, to ƙarshen wayewa ma tun tana shekara biyu a duniya aka tafi da ita UK, ba kuma ta taɓa zuwa Nigeria ba sai a shekarun girma kuma a lokacin sukai aure. Takan ji ya mata kwarjini da cika mata waje a duk sanda yake a gabanta, wani lokacin ma tafi sakewa da shi a waya fiye da kasancewa a face-to-face.... Ɗagatan da yay ne cak ya katse mata tunani, kamar wata babyn wasa duk da kuwa ita ba ramammiya bace jikinta a mulmule yake da ƴar ƙibarta sai dai bamai yawa ba. Hannayenta ta zagayo a wuyansa tana mai kwantar da kanta a ƙirjinsa. A haka ya shiga da ita cikin bayin ya dire cikin jacuzzi. Ƙasa-ƙasa cikin raɗa da wani salon soyayya irin ta manya yana wani kalar shinshinar wuyanta daya sakata lumshe idanunta tsam-tsam ya furta. “Kiyi amfani da ruwa mai zafi sosai zai daina taguwar Zak... Sarkin raki” dai-dai nan ya sakar mata ƴar sumba a cikin kunne data sakata zabura. Yanda ta ƙanƙame jikinta ya sashi sakin wani lallataccen murmushi na ganin dama, cike da takunsa na zarra da jarumta ya bar mata bathroom ɗin gaba ɗaya har lokacin da ƙaramin murmushin a lips ɗinsa, ƙyawawan idanunsa kuwa sun wani shige ciki sosai jan cikinsu yafi yanda suke akoda yaushe. Sai wani luuu yake da su yana buɗewa a gajiye... Gaban mirror ya koma ya saka turare kaɗan ya fice a ɗakin gaba ɗaya dan yana son zuwa gidan su Imran gaida iyayensa.....

<<★>><<★>><<★>>

ƘAUYEN BANKAURA

Rakwacammm!! Ɓarin bazata ya karaɗe kunnen Umma dake tsakar gida tana aiki. Da sauri ta kalla ƙofar ɗakin, tare da ƙwala kiran sunan Nimrah da tasan tana ciki. Shiru taƙi amsawa. Umma tai ƙwafa da faɗin, “Nice nake kiranki kina min shiru ko, shike nan ALLAH ya baki sa'a na shigo ɗakin nan jikinki ne zai gaya miki.” Tsulum ta fito jikinta fututu da garin tuwo ko fulawa. Suna haɗa ido da Umma sai ta fashe da kuka tana ɗaga yatsa sama bayan ta lashesa akan harshe. “Umma na rantse bani nai miki ɓarin nan ba, ɓeran ɗakinki ne......” kuka ya ƙwace mata. Rasama abin cewa Umma tayi, kawai ta cigaba da kallonta. Itako tana ƙara ƙarfin kukanta da rantsuwar ba ita bace ɓera ne yay ɓarin nan. Dai-dai nan Babanta dake bayi ya fito. “Kaiya-kaiya lafiya dai kuwa? Uwa kin san bana son wannan shashancin kukan banzar fa. Mi akai miki?”. Ran Umma a ɓace ta ce, “Sai anyi mata. Ko ita tayi ai ta iya kukan iskanci. Kuma wlhy yau babu mai hanani dukanki a nan gidan. Fulawar mutane kika ɓarar min daga kawowa ai musu mirjin taliya, bayan a sama na sakata saboda sanin halinki”. “Na rantse ɓera ne, Baba kace karta dake ni, ai dai ɓeran yafi ta kamo ta daka”. Nimrah ce ke maganar cikin uhun kuka bayan ta rugo tazo jikin Babanta ta ɓuya. Kansa kawai ya girgiza da faɗin, “ALLAH ya shiryeki Uwa, al'amarinki ya fara bani tsoro, yanzu kiyi laifi amma tsabar shaƙiyanci kice wai ɓera ne? Shekaran jiya fa haka kika ɓarar da mangyaɗa Inna ta hana a taɓaki da Kawunki Tanimu, yanzu kuma kayan mutane, sana'ar kike so uwar ki ta daina?”. “Baba na rantse ɓera n.....” Bummm!!! Abinda Umma ta jeho mata ya daki bakinta. Ai data buga wani tsallen ihu ta zube ƙasa saita fara birgima da faɗin wai Umma ta cire mata bakinta. Haushi ya ƙara turniƙe Umma tazo kanta da tsumagiya ta fara zuba mata a jiki, da ƙyar Baba ya kwaceta. Sai ga Inna ta shigo itama tana sababi, dan a duniya idan kana son ganin tujararta to ka taɓa Nimrah a gidan nan, shiyasa ma take wani iskancin da hujja. Maimakon taima Umma kaɗai faɗa sai ta haɗa harda Baba wai basa son Nimrah. Su dai haƙuri suka koma bata....

Da Nimrah Inna ta tafi sashenta, acan ta lallasheta ta bata nera ashirin wai ta sayo awara da kunu gidan Zinaru. Aiko da farin ciki ta ɗauki kwano ta tafi, gidan Zinaru mai awara da gidansu akwai ƴar tazara kaɗan, dan gidansu Nimrah yana cikin gidajen ƙarshen gari, sune na ƙarshe ma sai jeji babu gidaje a bayansu sai wasu ƙauyukan. Har tabi ta cikin gari ta canja hanya ta koma ta bayan gida tabi wai tafi sauri. Tafe take tana shan majina da doke-doken abubuwa da karan dake hannunta. Wani lokacin ma har yara ƴan uwanta idan ta gamu dasu sai dai kaji ta zuba maka duka, kafin ka rama ta zura da shegen gudu. Gata ƴar sirit babu ƙiba sai tsayi. Taje birtalin da zata fita a bayan gidan ta koma hanyar gari sosai ta hango wasu mutane zaune a ƙasan wata ƙatuwar bishiyar mangwaro dage wajen. Humm Nimrah neman magana ake gaya muku, sannan Nimrah faɗi ba'a tambayeka ba. Fasa tafiyar tai ta koma hanyar inda mutanen nan ke a mangwaro. Babu zato sukaji ƴar muryarta na faɗin, “Suwaye ku?”. Da wani irin sauri duk suka juya suna kallonta, sai mutum ɗaya da bai juya ba sai ma runtse ido da yayi tare da jan hiraminsa dake kan wuya da sauri ya rufe fuskarsa alamar baya son ta ganshi, kuma tabbas ta sanshi ne shiyyasa yayi haka. A hasale wani zai mata magana na kusa da shi ya hanashi ta hanyar riƙe masa hannu ya matse. Murmushi yayi mata tare da faɗin, “Yarinya miya kawoki nan?, mu baƙi ne”. Fuska a ya yamutsa, maimakon kula zancensa na farko sai catai, “Baƙi? A bayan gari”. Sosai mamakin shegen wayonta ya bayyana a kan fuskokinsu. Wanda yay maganar dai ne ya sake mata murmushi. Ya ce, “Eh zamuje ƙauyen Garjalle ne”. Batace komai ba, sai ma ido data zubama jakunkunan gabansu, sai kuma ta koma kallon wanda ya rufe fuskarsa. Ganin yanda ta zuba masa ido yasa wanda yay mata magana ɗazun ɗakko naira hamsin ya miƙa mata. “Kinga ƴar Baba amshi wannan ki wuce gida kada a nemeki”. Kuɗin ta zubama ido, sai kuma ta girgiza kanta tana kamo gefen kallabinta da aka kulle ta nuna masa. “Bana so, nima Inna ta bani zanje sayen awara ne”. “Yauwa to maza kije ki sayo kada ta ƙare”. Harta juya zata wuce sai kuma ta dawo. Ta ce, “Kai Baba to miye a wannan ƙaton jakan da yawa? Wannan kuma miyasa ya rufe fuskarshi ko bashi da lafiya?”. Babu wanda a cikinsu baiji kamar ya hamɓare yarinyar nan ba. Amma dai wanda ke amsata ya daure ya ce, “Eh baida lafiya. Jakun kuna kuwa mangwaro ne muka zuba”. “Ai yanzu ba lokacin mangwaro ba ne”. Ta amsa tana sake matsosu. Tsawa na ɗazun ya daka mata dan ya kasa haƙuri, “Ke wuce ki bar nan komu yanka ki mai shegen surutun tsiya, ƴar firit dake sai sa ido kamar aljana”. Ganin ya ƙare maganar yana jawo wani ɗan icce a kusa da shi da gudu tabar wajen kuwa. Sai da tai nisa daga nesan tana hakki ta juyo ta ce, “Ku! In ALLAH ya yarda sai kura ta cinye ku masu jajayen ido irin na fatalwa”. Daga haka ta sake zurawa a guje. Takaici ya saka wanda yay mata tsawar nan ciro wata ƴar mitsitsiyar bindiga ya saita ta. Cikin sauri wanda ya rufe kansa da hirami ya kaɓar da bindigar yana yaye hiramin da girgiza masa kai alamar karya aikata wannan kuskuren. “Mi kake nufi ko kana da alaƙa da ita ne?”. “Babu ruwanka da koma ya nake da ita, ka duba mana yarinya ce ƙarama dududu bata wuce shekara bakwai da wani abu ba. Sannan a tsarinmu bamuyi haka da ku ba ai. Babu cutar da yara, babu cutar tsoffi”. “Kai baƙauyen banza anƙi abi dokar taka, kodan kaga mun biyo ta hannunka ne kake tunanin bazamu iya aikin da kammu ba. Kada ka manta kuɗi muka biyaka kai mana komai. Sannan da kake kiranta yarinya ai a yarintar tata tasan rashin kunya ma manya ko. To na rantse maka duk inda naga yarinyar nan a garin nan sai na fasa mata kai kuwa”. Da sauri mai hiramin nan ya kalla Ogan tawagar, kafin ma yayi magana ogan ya ce, “Kaga manta da shi, babu abinda zai mata kasan shi dai da zuciyar tsiya. Kamar yanda mukai alƙawari da kai tun farko babu canji, bazamu taɓa yara da tsoffi ba. Kai dai kaje ka fara mana aikin tantance yara mazan da muke so. Zuwa jibi ka tabbatar aikinka ya kammala zuwa dare zamubi gida-gida mu tattaresu waje guda. Ga kayan aikinka nan da kuɗaɗenka zaka iya tafiya”. Kansa kawai ya jinjina, sai kuma ya miƙe. “Bazan tafi da waɗan nan kayan ba yanzu, sai magriba zan dawo ɗauka.” “Baka da case Goga”. Ogan ya faɗa yana bashi hannu. Daga haka ya gyara hiraminsa ya zagaya wata hanyar ɓadda kama ya koma cikin gari..........✍🏼

(Lallai cakwakiya, to wanene wannan 🤔? Yaya batun wanda yace sai ya kashe Nimrah? Kuna ganin zai ƙyaleta kuwa🤔🥲😳. Hummm kudai muje kawai, dan ba'a fara komai ba ma. Cakwakiya ce iya cakwakiya a cikin littafin nan🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️).

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 39_

__________________

*_Kuyi hakuri dani, ni kaina bana gane kai na saboda uzurirrika da suka zagayeni wlhy. Amma ina sha ALLAHU ina gab da kammalawa na dawo da hankalina gaba ɗaya kanku. Ina muku fatan alkairi gaba ɗaya 😘😘😘😘😀🙏_* __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________