Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 70

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 70

..... he shouted, and extended his hand to them, as a sign that they did not allow him to do what they came to do. One of the officers approached to put a restraint band on him but he failed. He said in a trembling voice, "I'm sorry Sir! Why can't I". Murmurshi Zak-Shadow was here as well, the idiot who said nothing did not answer himself and put.... ★★★★ Ja'afar's car arrived just as the MP officers were leaving the door of the house. They followed the two cars and looked at them, they were not even aware that Ma'aruff got out and opened the gate for them and they got inside. When they come home, they go to greet Mammah first before going to their rooms to take a bath. Today, as always, they went there. From the moment they came in, they heard the voices of Nimrah, Mu'azz and Ruqayya who had not returned home. As they said goodbye, Mu'azz and Ruky came to each other and shouted at each other. Nimrah has no chance to fly because of her feet. Bilal greeted them, they responded with care and asked him to work, his son is a worker. Biebah came out from the kitchen and greeted them, and then they went to Mammah's room. As soon as she entered the evening prayer, she did not come out aga

Standalone post2,106 words

.......Cikin nutsuwa jami'an Military Police suka fito a tsare. Babban cikinsu ya matsa kusa da Zak-Shadow cikin girmamawa da risinar da kai yayi gaisuwa. Amsa masa Zak-Shadow yayi cikin jinjina kai batare da yace komai ba. Sai kuma ya juya yana kallon Bilal yay masa alamar ya shiga gida. Bilal da bai fahimci komai ba face abokan aikin Dadan ne sukazo maybe zasuyi magana ne akan aiki sai ya shige gida abinsa kawai. Sai a lokacin Zak-Shadow daya sake binsu da kallo a taƙaice ya furta, “Akwai matsala ne?”. Cikin sake risinar da kai ogan nasu ya ce, “I'm sorry Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed... by the order of the Defence Headquarters, you are under arrest. You’re to come with us quietly.” Zak-Shadow yay shiru kawai yana kallonsa na tsawon daƙiƙu, amma bai ce komai ba. Sai kuma a nutse ya koma kallon fuskokin sauran suma da duk suka risinar da kai alamar suna matuƙar jin nauyin kallonsa ma. Sai kawai yay wani ɗan murmushi yana sauke ajiyar zuciya. “Understood” ya furta cikin dakakkiyar murya, tare da miƙa musu hannunsa, alamar basu damar yi masa abin da suka zo yi. Wani daga cikin jami’an ya matso domin ɗora masa restraint band amma sai ya kasa. Sai ma cikin rawar murya ya ce, “I'm sorry Sir! wlhy bazan iya ba”. Murmurshi Zak-Shadow yayi anan ma, batare da yace komai ba ya amsa da kansa ya saka....

★★★★

Motar su Ja'afar ta iso dai-dai Jami'an MP na barin ƙofar gidan. Sukabi motocin biyu da kallo, batare da sun kawo komai a ransu ba su ma Ma'aruff ya fita ya buɗe musu gate suka shiga ciki. Idan har suka shigo gida sukan fara zuwa su gaida Mammah ne kafin su wuce nasu ɗakunan yin wanka. Yau ma kamar kullum can ɗin suka nufa. Tun a farkon shigowa suke jin surutun Nimrah da Mu'azz da Ruƙayya da bata koma gida ba. Sunayin sallama Mu'azz da Ruky sukayo kansu suna musu oyoyo. Nimrah dai babu damar tashi saboda ƙafa. Gaishe su Bilal yayi, su ka amsa da kulawa suna tambayarsa ya aiki dan shi kam ma'aikaci ne. Fitowa Biebah dake kitchen itama tayi ta gaishesu, daga haka suka nufi ɗakin Mammah, dan in ta shiga sallar magriba bata sake fitowa sai tayi har isha'i. Har sun je ƙofa Ma'aruff ya juyo yana tambayar, “Dada fa? Ko yana sashensa?”. Biebah ta ce, “Yaya tun ɗazun ya fita har yanzu bai dawo ba”. Bilal ya ce, “A'a ya dawo Auta, tare ma mukayi sallar magriba. Zamu shigo gida yayi baƙi baku gansu a ƙofar gida ba?”. Yanzu kam Ja'afar ne ya ce, “Eh muna isowa wata motar sojoji na barin ƙofar gidan, amma mu bamu ga Dada ba”. “Maybe ya riga ya shigo ne”. Duk sun gamsu da abinda Bilal ɗin ya faɗa, dan haka suka ƙarasa shiga wajen Mammah....

★Bayan idar da sallar isha'i su Ja'afar sun ta baza idon san ganin Dada ya fito a masallaci shima amma shiru. Kuma sun tabbatar idan yana gida jam'i baya wucesa. Sai da kowa ya shashshare suka tabbatar dai babu shi sannan suka koma gida. Kai tsaye sashensa suka nufa, tunda sun san shi kaɗai ne yanzu Nabeeha anyi yaji. Da knocking suka fara kafin su shiga. Sai dai ko ina shiru fitilu ma duk a rufe. Ma'aruff ya kunna fitilar falon haske ya gauraye ko ina. Sallama suka ƙara yi amma shiru babu alamar mutum. Sai kawai suka zauna a falon. Abin kamar wasa fin mintuna talatin babu motsin Dada, Bilal yaje yay masa knocking ƙofa amma shiru, dai-dai nan kiran Biebah ke shigowa wayar Bilal ɗin. Ma'aruff ya ɗaga. “Yaya Bilal Mammah tace wai ina kuka tsaya?”. Miƙewa Ma'aruff yayi da wayar a kunne yana amsa mata da, “Gamu nan zuwa, muna sashen Dada ne kuma da alama baya gidan”. Bai jira amsarta ba ya yanke kiran suka fito suka koma sashen Mammah. Duk sun sakankance Dada yaje wani waje ne har sunyi dinner sun dawo falo suna hira. Sai dai ganin Mammah tayi sukuku da yawa suka zagayeta da tambaya. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke, batare data amsa musu ba tace, “Biebah kwashe yaran nan su koma ɗaki kinga sun fara barci anan”. Biebah ta ce, “To Mammah” tana miƙewa. Sai da ta tada Mu'azz ya wuce ɗakinsa sannan tazo ta ɗauki Nimrah takai ɗakin Mammahn ta ɗauki Ruky ma. Sai a lokacin Mammah ke amsa su Ja'afar. “Tun ɗazun nake jin zuciyata na rawa, sannan ina jina tamkar cikin tsoro-tsoro”. Duk kallonta suke cikin tashin hankali suma a karo na farko. Jikin Bilal a sanyaye ya ce, “Mammah wani abu ya faru ne kuma?”. “Babu abinda ya faru Bilal, kawai dai na fahimci bayan abinda ke faruwa a gidan nan na shirmen Nabeeha kamar Muhammad nada damuwa, sai dai yana ɓoyewa. Yau kuma gashi tunda ya fita har yanzu bai dawo gida ba, bai kira kowa a waya ba, kalla agogo ƙarfe goma saura. Sannan jiya na fahimci kamar Imran bai kwana a gidansa ba shima”. “Tabbas Mammah maganarki na kan hanya, dan kinga ɗazun da safe wasu jami'an soja sun kawo ma Dada takarda, amma sai yaƙi ya buɗe a gabanmu yace muzo muyi shirin tafiya kasuwa”. “Nima kuma yanzu kaga da yay baƙin nan Yaya Ma'aruff cayay fa na shigo gida, bai bari sunce komai a gabana ba.” Shiru falon yay tunanin kowa ya fara dawowa jikinsa. Kamar an saita sai ga kiran Imran na shigowa a wayar Ja'afar. Ɗagawa yay cike da zumuɗi yana gaisheshi, Imran ya amsa da kulawa yana tambayarsa lafiyar kowa, sannan ya ɗora da tambayar Zak-Shadow. Ɗan jimm Ja'afar yayi, sai kuma cikin damuwa ya ce, “Dada baya gida, muma bamu sameshi ba.” Da mamaki Imran yace, “Baya gida kuma?”. “Eh wlhy Yaya. Mun zata ma kuna tare ai a wajen aiki. Dan Bilal yace bayan fitowarsu a massalaci sallar magriba yayi baƙi kuma kamar jami'anku ne”. Imran ya ɗauki sakan biyu shiru kafin yace, “Ina Bilal ɗin?”. Wayar Ja'afar ya miƙama Bilal. Koda ya amsa sai da ya fara gaisheshi, Imran ya amsa a taƙaice ya cigaba da jeho masa tambayoyi. Ba ƙaramin rikita Imran amsar Bilal tayi ba, dan yana faɗar motar da suka zo da ita ya gane jami'an MP ne. A dai-dai kuma lokacin yake canja channel daga tv da nufin kallon labarai aka nuna jirgin sojoji ya samu haɗari da yamma a wani ƙauye, kuma jirgin na ɗauke da wasu masu laifi ne da aka kama kwanan nan a rikicin daya auku na yammacin ƙasar. Ai cikin tashin hankali Imran ya yanke kiran batare da cigaba da tambayar Bilal ba, dan kai tsaye ya samu amsar tambayarsa ne.....

<<•>><<•>><<•>>

Duk da rufa-rufar da ake ta kama Zak-Shadow zuwa safiya dai zance ya gama fita cewar an kama shi ɗin. Abin mamaki kuma wata ɓoyayyar gidan jarida ta fara fidda bayanan kamashi a shafinta na X, tare da hoton lokacin da jami'an MP ke tare da shi, harda hoton dake da handcuffs a hannunsa. Kafin awa guda mutane miliyoyi sun zuba sharhi akan batun, manyan kafafen yaɗa labarai sun bazama binciken gaskiya. A gidan soji kuwa wasu hankalinsu a tashe matuƙa. Wasu ko na dariyar ALLAH ya ƙara da farin ciki mara misali. Nan fa wasu sabbin zantuka ma suka fara fita iri-iri masu ban mamaki. Kafin ƙarfe biyun rana ƙasa gaba ɗaya ta gama ɗauka. Babu wani labari dake trending sai batun kama Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu. A ɓangaren al'ummar ƙasa da yawa basu yarda zarge-zargen da akema Zak-Shadow ɗin ba, sun fi gaskata al'amarin da batun siyasa ce kawai ko wani abu daban. Su ko maƙiya na hura hanci da hanƙoron bada tabbacin zai iya fiye da haka....

★Ga su Mammah kuwa fassara halin da suke ciki ita da iyalanta ma ɓata lokaci ne. Dan tuni sun taru ƙwansu da kwarkwata a gidan sunata kuka. Sai dai Mammah baiwar ALLAH tana cikin nutsuwarta a zahiri, babu abinda take sai ambaton ALLAH. Imran, mahaifinsa, Uncle Nasiru, Ja'afar, Ma'aruff tunda safe da zancen ya fito suka bazama inda akace an ajiye Zak-Shadow, amma anƙi basu damar ganinsa. Dan wani mugun tsaro aka bama wajen ma da duk mai hankali ya gani yasan lallai akwai magana, sannan al'amarin bamai sauƙi bane ba. ALLAH sarki COAS da kansa ya gana da su yana mai kwantar musu da hankali akan suyi addu'a in sha ALLAHU babu abinda zai faru, gaskiya zata fito dan yanzu haka shima ya baza jami'ai ana kan binciken number motar da akace wanda sukaje ɗaukar Ojo sun tafi da ita. Sannan a yanzu haka ana kan bincike a ƙauyen da aka samu haɗarin wancan jirgin dan kai tsaye an samu tabbacin an harbo jirgin ne gangan ba haɗarin kai da kai ya samu ba.....

<<•>>

A can kuwa ƙungiyar duhu na cikin matsanancin farin ciki ne su da duk wasu munafukai dake ƙin Zak-Shadow. Dan kuwa babu wani kace nace aikinsu ya faɗa fiye da yanda suke so da fata batare da sun sami kowace irin tangarɗa ba. Sun sha bikin cin nasara a daren jiya, sun kumayi rabon dukiya ga duk wanda ya taimaka musu aikin ya tafi dai-dai. Ƙungiya kuma ta ɗauki sabbin members da za'a tada sabon jadawalin aiki da yafi na baya muni da zubar da jini. Dan sunyi alwashin duk wanda yace zai tare musu gaba kamar Zak-Shadow sai sun masa kisa irin na wulaƙanci. Shi kansa Zak-Shadow ɗin sunfi buƙatarsa a raye ne dan ya dinga kallon nasarrasu a gaɓar da bazai iya komai ba. Tunda yace shi mai kishin ƙasa ne da baƙin ciki zasu kashe shi. Dan sunyi alƙawarin dasa masa ciwon zuciya. A yanzu haka Ojo na hannunsu, dan sune suka saka aka ɗakko musu shi. Haka ma su Dagger na hannunsu, sune suka saka aka harbo jirgin nan, saboda suna buƙatar su Dagger a tafiyarsu, babu wanda zai musu kamar yanda Dagger ke musu su sami natsuwa, dan sun gwada yaransa amma basu sami biyan buƙata ba. Shiyyasa suka sake sabon shirin dawo da shi ta hanyar jifan tsuntsu biyu da dutse ɗaya, kuma sun sami nasara, dan haka yanzu lokaci ne na sake SABON WASA........✍️

Alhamdullahi 🙏.

Tabbas yanzu shine lokacin sake SABON WASA kam masu karatu. Dan anan book 1 ɗinmu zai ƙare. Ku muje zuwa book 2 inda ainahin baje kolin cakwakiyar take.

Idan nace daku cakwakiya kawai kaɗan ma kenan, dan book 2 ɗin nan ba'a magana. In sha ALLAHU zai zo muku da fiye da abinda kuke tunanin gani. Dan book 1 tamkar shinfiɗa muka baza, yanzu zamu tsunduma ainahin labarin KIƊA A RUWA MAI TADA HANKALIN DODO...

★Ya zata kasance da Zak-Shadow?.

★Abin zai tsaya kansa ko zai haɗa da Imran?.

★Zasu sake shi da wuri ko kuwa zasu turashi kurkuku?.

★Ina batun Nabeeha da ƴan uwansa da uwarta?.

★Mi uwarta ke shiryawa?

★Nimrah ƴar Amana, yaya girman wannan tsuntsuwa zai kasance a gidan su Zak-Shadow? Ina batun aurenta da Zakinmu? Wane wasa za'a buga ita da Nabeeha ne?.

★Ina mahaifin Nimrah ne? Ya rasu a cikin wanda suka rasu ko kuwa an ɗaukesu tare da su Dagger?.

★Ƴan uwanta da gaske duk sun rasu babu ko ɗaya daga dangin uwa dana uba?.

Kai jama'a kada na cika ku da zance, Amma fa KIƊA A RUWAN kiɗa a ruwan ne fa, dan za'a buga wasa iya wasa, soyayya iya soyayya, cakwakiya iya cakwakiya. Rikita rikita iya rikita-rikita, gumurzu iya gumurzu. Dan ni kaina Bilynku na saka sulken yaƙi😎🏃🏼‍♀️.

Ku muje zuwa book 2 kawai mutanensa❤️❤️❤️💃🏼.

Bilyn Abdull ce. ((C--2025))

_________________

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JuUwr2QU7XMEYXZ7L7 Mmn surayya me kayan kamshi Ina amaran da uwayan gidan tou kumatso kusa Mmn surayya ta gwangwaje ku da kayan kamshi munada Turaran wuta na danal banat Kajiji Turaran kaya watau abbasiyya Kabbasa spray Humra Kwallacca Uwa uba Ina kuyarda yadda xaki hadasu Zaku iya samuna ta wannan number wayar kamar haka👇 08103143517 Ina katsina Ina aika kaya ko ina

__________________

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*