Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 68

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 68

...the two government monitors from the other side. He saluted with respect as per the law even though there is someone who is better than you. "Good morning, sirs." There is no one among them who does not feel something in his heart, the voice of Zak-Shadow is the clear voice of enough men who come out straight and straight. And his voice is heart touching even though he is speaking in a low voice. "Morning, Lt. Col. Haysam. Please, have your seat". Brig. Gen. Abraham said in silence that Zak-Shadow's charismatic son completely filled his eyes like the others, his face was full of no sign of playfulness as everyone knows him with a lack of cheerfulness and a lack of speech. Calmly and calmly, he sat where he was shown, the room was silent for a while before the Brigadier turned his attention to reading the contents of the paper in front of him. Lt. Col. Haysam, we have invited you here to help this committee with some information on some of the activities that you have led in the past few days. We expect full cooperation from you". He closed his eyes a little, then opened them again, without any sign of fear or worry on his face, he said, "Yes, sir. I'm ready to answer your questi

Standalone post2,037 words

.......1:pm.

Duk taurin kan Zak-Shadow baya raina na gaba da shi a wajen aiki ko a shekaru na girma. Mutum ne mai tsantseni da taka tsantsan na kiyaye duk abinda baya so a masa bai yarda yayma wani ba. Zamu iya cewa kusan wannan ɗabi'ar tasa na ƙara masa nagarta da martaba a idon manyansu. Duk da suna sama da shi suma basu yarda su wulaƙanta shi ba. Dan yana musu kwarjini da cikar kamala. Kai ko haushin Zak-Shadow kake ji sai dai ka cika bakin zaginsa a bayan idonsa da ɗaukar alwashi, amma da kun haɗu ido da ido sai kaji gaba ɗaya zafin kan naka ya gudu ka koma jin shakkarsa. Kamar yadda aka tsara, ƙarfe ɗaya da rabi na rana motarsa ta shigo Defence Headquarters cikin nutsuwa. Bayan an tabbatar da shaidarsa, aka raka shi zuwa babban zauren taron kwamitin binciken. A cikin ɗakin, akwai manyan jami’an soja shida da suka haɗa da, Brig. Gen. Abraham Yohana (Shugaban kwamiti). Col. Osama Galadima (Memba). Lt. Col. Peter Okon (Memba). Major Lami Barde (Recorder). Col. Haydar (Memba). Sai jami'an gwamnati biyu masu sa ido dake daga can gefe. Yayi gaisuwa irinta mutuntawa kamar yanda doka ta tanada duk da kuwa akwai wanda yafi rank a wajen da wanda suke dai-dai. “Good morning, sirs.” A cikinsu babu wanda bai ji wani iri a zuciyarsa ba, dan muryar Zak-Shadow irin dakakkiyar muryar nan ce ta isassun maza dake fita kai tsaye kuma a dake. Sannan amonta na kama zuciya koda yana magana ne a ƙaramin sauti. “Morning, Lt. Col. Haysam. Please, have your seat”. Brig. Gen. Abraham ya faɗa cikin dakewar dole dan kwarjinin Zak-Shadow gaba ɗaya ya cika masa ido kamar sauran, ga fuska ya tamke babu alamar wasa kamar yanda kowa ya sanshi da ƙarancin fara'a da rashin yawan magana. Cike da nutsuwa da ƙasaitarsa ya kai zaune inda aka nuna masa, ɗakin ya ɗan yi shiru kafin Brigadier ɗin ya maida hankalinsa ga karanta abinda ke a takardar gabansa. Lt. Col. Haysam, mun gayyace ka nan ne domin taimaka ma wannan kwamiti da wasu bayanai kan wasu ayyukan da kai ne ka jagoranta kwanakin da suka gabata. Muna sa ran cikakken haɗin kai daga gare ka”. Lumshe idanu ya ɗanyi kaɗan, sannan ya sake buɗesu, babu alamar wani fargaba ko damuwa a fuskar tasa ya ce, “Yes, sir. I’m ready to answer your questions.” Kai Brig. Gen. Abraham ya ɗan jinjina yana juya takardar gabansa, sannan ya cigaba da da faɗin, “Kafin mu ci gaba, Lt. Col, muna son tabbatarwa ko kana da masaniya game da ɓacewar wani Lieutenant mai suna Ojo, wanda ya kasance cikin rundunar da ka jagoranta a aikin karshen nan daya gabata?”. Shiru na ɗan lokaci kamar bashi da niyyar bada amsar, sai kuma yay wani ɗan malalacin murmurshi, “Yes sir! Na sani, sannan ba ɓata yay ba yana hannuna, kuma yarona ne na kusa da kowa ya sani. Wasu dalilai ne kuma yasa na riƙesa, nasan kuma yin hakan ba laifi bane a ɓangaren bincike”. Hall ɗin ya yi shiru tamkar babu mai rai a ciki, kowanne da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa game da amsar daya fara badawa kai tsaye da babu gargada ko shakka, sun san wanene Haysam, bashi da tsoro, bai yarda ya ajiye gaskiya ba koda zata ƙwaɓe. Suko manyan jami’an da ke zaune a teburin gefe masu saka ido a madadin gwamnati kowannensu cikin matsanancin mamaki suke kallon Zak-Shadow ɗin, dan sun fahimci ya ma wuce yanda ake labarinsa ashe. Ji yanda yake bada amsa kai tsaye fuskarsa a haɗe, babu wani shakka ko tankaɗe abinda zai faɗa ɗin. Ba ruwansa da yay musu daɗi ko kar yay musu. Brigadier General Abraham Yohana ne ya katse shirun da ɗan murmushi. Cikin son gyara tambayarsa ya ce, “Hakane, sai dai a wannan yanayin kasancewar Ojo a hannunka ya canja labarin daga bincike zuwa son kare kanka a dalilin wata gaskiya da akace ka fahimci shi Ojo ɗin zai fitar data shafeka. Shiyyasa report ya nuna inda da gaske akan tuhuma kake son kama Ojo office zaka kawo shi ba wani waje daban ba da baida alaƙa da wajen aiki. Domin kuwa an samu wasu videos a kayan Ojo da bincike ke ganin saboda shi ne ka killaceshi”. Zak-Shadow yay wani sakaran murmurshi a karo na biyu yana ɗan kauda kansa gefe, sai kuma ya maida dubansa ga Brig. G. “Sir! I'm sorry, mizai hana muje kai tsaye ga abinda kuke buƙatar ji kawai. A lokuta da dama ana min kallon bahagon mutum, sai dai a zahiri mutane ne basa fahimtata, a komai nafi son abu kai tsaye, maida gaba baya a zance nakan kallesa kamar aikin mata ne. Dan ALLAH cikin girmamawa kawai muyi abinda ya dace”. Cikin taushi yayi magana, amma ga mai tsatsar zuciya zasu kalli kalamansa a masu zafi. Kamar jami'an gwamnatin dake wajen da wasu a membobin zaman. Sai dai shi Brigadier General yasan Haysam sani na amana da gaskiya, shiyyasa ko kaɗan bai ɗauki kalaman nasa a komai ba face na mazan fama. Sai kawai ya murmusa idanunsa akan Zak-Shadow ɗin. Shi ko Lt. Col Peter Okon cikin jin zafin kalaman Zak-Shadow ɗin ya ce, “Lt. Col Haysam Abdul-rasheed Shehu. An samu wasu video clips daga ayyukanka da suka gabata, musamman wanda ya faru a yankin Bankaura, wannan video clips kuma a cikin kayan Ojo amintacen yaronka aka same su kamar yanda kaji tun farko. Gasu za'a kunna maka ka gani”. Ko kallon inda yake Zak-Shadow baiyi ba, bai kuma amsa masa ba. Koda aka kunna tvn ma yaja wasu sakanni kafin ya kai idonsa kansa. Zuciyar sa ta ɗan buga musamman a wajen harbin Umman Nimrah da mahaifinta, amma bai nuna ba. Sai dai har videon ya kai ƙarshe bai ɗauke idonsa akan tvn ba, sai da ma Brig. G. Ya ɗan buga table ɗin sannan. Su duka ya kalla cikin idanu ɗaya bayan ɗaya, sai kuma ya ɗan yi murmurshin da su kuma ya daki zukatansu. Kai tsaye ya ce cikin murya mai ƙarfi, “Sir! Ai ban san a aikin namu harda masu ɗaukar aikin videos ba ma sai yanzu, ba zan tsaya ina kare kaina da magana kawai ba, sannan ban damu da sanin dalilin daya saka a ɗaukemu videos ɗin ba. Sai dai ko bayan na ɓata kamar yanda masu ɗaukar ko ogannin da suka saka a ɗauka ɗin ke buƙata ina so a bincika comm log ɗin mu da footage ɗin asali dan wannan edited video ne. Sannan akan Ojo ban yarda da fallasa abokin aiki ba tare da hujja ba. Mun fi son tabbatar da gaskiya kafin mu kai rahoto.” Tabbas buɗaɗɗun kalaman Zak-Shadow ba ƙaramin tasiri sukai a zukatan su Brig. G. Ba, dan haka hall ɗin yay shiru na wani lokaci, kafin Col. Haydar ya nisa cikin jimami da nauyin furuci ya ce, “Lt. Col. Haysam ka fahimci cewa wannan kwamiti ba yana tuhumar ka da laifi bane bisa son kai ko wata manufa, amma muna bukatar gaskiya. Wannan al’amari ya wuce duk abinda muke tunani. Musamman daya kasance mun samu tabbacin Ojo na hannunka kai da Major Imran”. “Sir, na san aikin soja, kuma na san kima ta fi darajar rayuwata......” “Kana nufin an shirya maka ƙarya kenan Lt. Col?”. Lt Col. Peter Akon yay maganar cikin katse Zak-Shadow yana tsatstsare shi da ƙananun idanunsa. Shima cikin ido ɗin Zak-Shadow ke kallonsa dole sai Lt. Col. Akon ɗin ya fara janye nashi, dan wani abu mai zafi ya gani a cikin idanun Zak ɗin. Amma sai ya wayance da faɗin, “Muna saurarenka Lt. Col. Haysam.” Wani shegen murmushi Zak-Shadow ya ɗan saki kaɗan, tare da janye idanun nasa ya maida kan Brig. G. Maimakon wanda yay tambayar dan tsabar yarfi. “Sir idan hakan ba shiri bane, to miye ake son ni Haysam na kira shi? Mun san akwai leak tun lokacin da muka gano Ojo yana aiki da wasu a waje. Mun tabbatar yana aika bayanai ga wani bangare a ɓoye. Mun fara bincike a kansa tare da Major Imran a yanda ya dace, gashi kuma abin na neman canja salo mai ban mamaki. Ko akwai kuskure akan abinda muka yi?”. Bring. G. Ya nisa yana gyara zama, “Tabbas kuna kan dai-dai Lt Col. Haysam, sai dai miya sa baku kai rahoto kai tsaye ba? Sannan office ya kamata Ku ajiye shi ba wani waje ba.” “Sir hakan ta faru ne because muna so mu tabbatar da gaskiya kafin mu gurfanar da shi, muna son mu kama shi da hujja mai tabbatar da gaskiya, kuma laifina ne ni kaɗai babu Major Imran a ciki”. Shiru ne ya ratsa ɗakin. Sai Brigadier General ya ɗan jingina kai ya ce cikin sanyi, Lt. Colonel Haysam, gaskiyarka zata bayyana. Amma dole ka san wannan al’amari ya kai matakin da ya wuce mu. Za a tura tattaunawar mu kai tsaye ga Chief of Defence Staff da kuma Office of the Minister of Defence. Muna so ka tsaya kan gaskiyarka, but until further notice, you are under administrative watch”. Ya ɗan yi shiru, sannan cikin murya mai nauyi ya ƙara da cewa, “Har zuwa lokacin da za mu kammala bincike, an dakatar da kai daga duk wani aiki na soja. Za ka zauna nan Abuja, kuma ba za ka iya fita daga FCT ba tare da izini daga ofishin Defence ba.” Ko kaɗan babu wani alamar damuwa a fuskar Zak-Shadow ya miƙe, ya yi salute cike da girmamawa, tare da faɗin, Yes, sir. I have nothing to hide. Na amsa. Na sadaukar da raina ga wannan ƙasa, ba zan fara gujewa gaskiya yanzu ba saboda hana maƙiya nasara, zan basu ƙafa fiye da yanda suke tunanin samu, amma a sanar da su koda ace zan ɓuya, wata rana gaskiya zata dawo dani ko ta kawo wani wanda ya fini”. Daga haka ya juya abinsa ya fita. Yana fitowa idonsa ya sauka kan Major Imran dake tsaye jikin motarsa alamar shi yake jira. Idanu suka zubama juna na wasu sakanni, kafin Zak-Shadow ɗin ya cigaba da takowa a hankali har inda Imran yake. Murmushi Imran yayi shi kuma Zak-Shadow ɗin ya hararesa. Sake murmusawa yay, cike da rashin damuwa ya furta, “Gaskiya zata fito, amma sai lokaci ya kai da yarjewar UBANGIJI”.....

((★))

A ɓangaren su Brig. G. Ƙofar na gama rufewa bayan fitar Zak-Shadow ɗaya daga cikin mambobin kwamitin Col. Haydar ya juyo yana kallon Chairman ɗin Kwamiti Brig. G. “Sir, idan har ya kasance gaskiya ne wannan makirci ne to mun shiga cikin irin abin da ba a taɓa ganin irinsa ba. Kuma hakan na nuna akwai wani bigger hand a cikin wannan abun, kuma gaskiyarka ba Lt. Col. Haysam kawai aka hara ba gidan soja ne gaba ɗaya”. Kasa ma bama Col. Haydar amsa Brig G yayi, dan shi kansa ya ɗauki zafi musamman da kalaman Haysam na ƙarshe a yanzu. Miƙewa yay cikin bada umarni yace a ɗakko masa Ojo daga inda Major Imran yace sun ɓoyeshi, daga haka ya fice, dole kowama ya miƙe har jami'an gwamnatin dake tare da su.........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 69_

__________________

https://chat.whatsapp.com/DMVSa4G3a9sDd8Jjgm0mzs?mode=ems_copy_t

Kin Dade kina Neman group din dazaki tallata kayanki kyauta Baki samuba to ki hanzarta shiga free advert group na EASHAS BITES AND BEAUTY domin tallata Kayanki kuyi saving number dinta domin samun shiga group dinnan akwai members Sama da 500+ aciki💃💃💃💃👇👇👇👇

wa.me/ 2348064705686

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________