
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 67
.....I'm worried, nothing will happen". He hung up the call and waited for her answer. Mammah who was looking at him said, "Are you alright?" He called a number. He was greeted briefly. Before he said, "Did Imran come to the Headquarters today?" I went out to pray with Faruk and I saw his car coming in, but I didn't see him out, I went back to the office to do some work." "Check me, what time did he come out, and did he go to the office?". "Okay sir!". The phone hung up and he fixed it, not even four minutes later he called him again. But he picked it up and started explaining to him one of the reasons to check. "Sir! I checked that his car is still there. And now I can hear the whispers that it is special to be with him, and now he is in the research room". Zak-Shadow didn't say anything for a few seconds, then he cut off the call with a sigh. Now he understood everything. So he called Col Faro, son of y.....
........10:30pm
Aunty Hafsat ta kira wayar Biebah tana tambayarta ko Imran ya dawo nan gidan. Biebah ta ce, “A'a gaskiya Aunty, ni dai banga Yaya Imran ba, dan sanda na dawo islamiyya ma Dada kawai na tarar a compound zaune. Kuma Mammah tace baku jima da wucewa ba lokacin.” “Har yanzu Dada na gidan?”. “Eh yana nan, gashi ma tare da Mammah na bashi?”. Kafin ma Aunty Hafsat tayi magana Dada yay ma Biebah alamar ta bashi wayar. Cikin girmamawa ta kawo masa. Sallamar da yayi ta saka Aunty Hafsat saurin gaisheshi. Ya amsa a taƙaice da tambayarta “Har yanzu bai dawo ba?”. “Eh wlhy Yaya har yanzu, ni tsoro ma ya fara kamani. Dan sanda muke fitowa gida zamu taho nan gidan dama wasu mutane kamar jami'anku sunzo sun bashi wata takarda. Sai dai ban san ta micece ba amma naji yana ce musu zuwa 2 ɗin zai je. Daga haka ya shigo mota kuma bai sake min zancen komai ba”. Cike da mamaki Zak-Shadow ya ce, “Takarda? kuma jami'an mu?”. “Eh, dan ɗaya akwai wandon sojoji a jikinsa”. “Okay ina zuwa to. Kada ki damu babu abinda zai faru”. Yanke kiran yayi batare da ya jira amsarta ba. Mammah da ke kallonsa ta ce, “Lafiya kuwa?”. “Babu komai Mammah ina zuwa”. Yay maganar yana miƙewa ya fita. Duk da kallo suka bishi har su Bilal. Dan suna zaune ne dama ana hira.
A waje Zak-Shadow yay ɗan tsai cikin nazari. Zancen Col Faro ne ya shiga dawo masa na jiya. Dan haka ya zaro waya a aljihu yana jinjina kai da cije lips yay kiran wata number. Ana ɗagawa daga can aka gaishe shi, a taƙaice ya amsa. Kafin ya ɗora da gaɗin, “Kaga Imran ya shigo Headquarter yau?”. “Eh tabbas Sir! Na fito salla ni da Faruk naga motarsa ta shigo, sai dai banga fitarsa ba dan na koma office ina wani aiki”. “Bincika min ƙarfe nawa ya fito, sannan office ya shiga ko mi?”. “Okay sir!”. Wayar ya katse ya gyara tsaiwa, ko mintuna huɗu ba'ai ba wancan ya sake kiransa. Koda ya ɗaga sai ya fara masa bayanin daya sakashi yin cak. “Sir! Na duba har yanzu motarsa na nan. Yanzu kuma nake jin ƙus-ƙus ɗin wai zama akai da shi na musamman, a yanzu haka ma yana a ɗakin bincike”. Shiru Zak-Shadow bai ce komai ba tsahon sakanni, sai kuma ya katse kiran yana mai furzar da huci. Yanzu kam ya fahimci komai. Dan haka yay kiran Col Faro, dan ya tabbatar a wajensa ne kawai zai ji abinda yake so. Sai da ta kusan tsinkewa ya ɗaga. Baima jira ko gaisuwa sunyi ba kai tsaye ya ce, “Imran na tare da ku?”. Sai da Col Faro yay ɗan jim sannan cikin tsantseni ya ce, “Kada ka tada hankalinka. Na tabbatar zuwa safiya zasu barshi ya fita”. “Bazai yiwu ba, gani nan zuwa”. “Kayi haƙuri dan ALLAH kar kazo, dan zuwanka haɗari ne babba ga Major Imran. Ka bari muga abinda safiya zatayi. Ni kaina yanzu ina ƙoƙarin son sanin mi suka tattauna da shi ne dama zan kiraka na gaya maka. Amma zuwanka yanzu zai iya sake ɓata komai”. Da wani irin zafin rai Zak-Shadow ya kaima motar da yake jingine a jiki naushi, batare da yace komai ba ya yanke kiran. Ya jima zuciyarsa na hanƙoro a cikin ƙirji, kafin daga ƙarshe ya danne komai ya koma wajensu Mammah. Wayar Biebah ya amsa yay kiran Aunty Hafsat. Ya ce ta kwantar da hankalinta akwai aikin da Imran keyi amma zuwa safiya in sha ALLAHU zai dawo gida. Bai jira amsarta ba kuma ya yanke. Koda Mammah ta sake masa tambaya amsar daya sake bata kenan itama. Daga nan ya musu sallama ya wuce. Tun daga nan ta sake fahimtar akwai matsala, sai dai tasan bazai faɗa ba...
Sam Zak-Shadow baiyi wani barci ba a wannan daren. Ya kwana ne akan ƙafafunsa yana salla da kuma zaman lissafe-lissafen abubuwa a taƙaice. Dan ya gama auna komai ya kuma fahimta gwargwadon hangensa. Ya auna hanyoyin kuɓuta da tsaida gaskiya yaga duk wadda yabi zai iya saka Imran a haɗari, sai kawai yay murmushi yana mai tabbatar ma kansa amsar hanyar ƙarshe kawai. Duk da ya san zai saka Mammah da ƴan uwansa a tashin hankali. Amma zai samu abinda yake so a ƙarshe koda kuwa sunci nasara a kansa shi Imran zai ƙarasa abinda yake fata kuma shi zai ci nasarar sannan zai kuɓuta. Sai kawai ya sake yarda zai sadaukar, dan ransa fansa ne ga Imran balle ma wannan harin kai tsaye nashi ne. Da wannan hukuncin ya kwana a ransa, dan haka duk wani abinsa mai muhimmanci ya killacesa waje guda a ɗakin ya kuma ajiye wasu domin Imran........
<<%>><<%>><<%>>
WASHE GARI.... 7/6/2013.
8:30am
Kamar yanda Zak-Shadow yay tsammani a wannan safiya ya samu baƙuncin ɗan aike daga kwamiti. Ya jima yana kallon takardar gayyatar mai tambarin Defence Headquarters a jiki. Sai kuma ya ɗan saki murmurshin ƙasaita. Gefe ya ajiyeta kawai ya cigaba da shan coffee ɗinsa, su Ja'afar dake kallon takardar cikin son sanin mike a ciki dan suna tare da shi ne a tsakar gida tunda suka dawo daga motsa jiki da suka bishi bayan sallar asuba. Basu koma ciki ba anan Biebah ta kawo musu coffee shine suke zaman sha har aka kawo takardar. Ƙasa-ƙasa Ma'aruff ya ce, “Dada badai aiki zaka koma ba tun yanzu? Wlhy bamu gaji da ganinka ba, dan ALLAH ka yi kamar wata uku”. Cikin marairaicewa Ja'afar ma ya ce, “Eh dan ALLAH Dada. Kaga ma ko warkewa fa baka gama yi ba yankan hannunka.” Rasama mizai ce musu yayi, suko sai sake shagwaɓe masa suke kamar wasu yara ƙanana. Sai kawai ya ce, “Tom naji, ku tashi kuyi shirin kasuwa nima zan fita ne”. Badan sun so hakan ba suka amsa da to, dan su fa idan yana gida ko fita kasuwar basa son yi, tunda duk shagunan akwai yara, su matsayin oganni ne ko sunje zaman office ne. Sai da ya tabbatar sun shige ciki sannan ya ɗauki takardar ya duba. (Directive from the Board of Inquiry. Defence Headquarters, Abuja. Ana gayyatarka domin bayyana a gaban kwamitin bincike a yau 1:pm. Subject: Preliminary Inquiry concerning recent allegations on classified operations. Brig. Gen. Abraham Yohana, Secretary Board of Inquiry).
Ƙasaitaccen murmushi ya sake saki mai cike da ma'anoni, sai kuma ya maida takardar ya ninke ya ajiye. Daga ƙarshe ma ya miƙe ya nufi sashen Mammah. Kusan awarsa ɗaya a sashen Mammah ya koma nashi sashen, tun faruwar rikicin Nimrah bai kuma saka Nabeeha a idonsa ba, bai kuma nemeta ba sai dai yana ganin gilmawar ƙanenta da Mamansu da bai san mitake a gidan ba har yanzu. Shi kuma bashi da lokacin tambaya ko neman ba'asi, idan taso ta dawo gidan ma da zama matsalarsu ce wannan. Yana buɗe ƙofar ɗakin nasa akan Nabeeha ya fara sauke idanunsa, tana zaune a kujerar dake kallon kofar. Kwanaki kaɗan har ta rame, ga idanu a kumbure jajur alamar cikin kuka take har yanzu. Ɗauke idanunsa yay tamkar bai ganta ba, sai ma ya hau ƙoƙarin cire kayan jikinsa hankali kwance. Ai ko ta sake ƙuluwa, zuciyarta na ƙuna da rawar murya ta ce, “Saboda kayi sabon aure kake wulaƙanta ni?”. Babu alamar ya jita ma, dan hanyar bayi ya nufa, da sauri ta tashi tasha gabansa, ya tsaya cak yana kallonta da birkitattun idanunsa, kasa jure kallonsa tayi ita kam, dole ta risinar da idannunta tana ƙara ƙarfafa kanta ta ce, “Haysam idan kana son zama dani ka ɗauki yarinyar can ka maidata inda ka ɗakkota, ka warware tatsuniyar gizo-gizon daka ƙulla kuma”. Ƙirjinta dake sama da ƙasa alamar da ƙyar take tattaro maganar tana gaya masa ya zubama ido, yanda takai ƙarshen zancen nata da rumtse ido sai tama bashi dariya. Amma sai ya dake abinsa kai tsaye ya ce, “To Mama Nabeeha idan naƙi fa?”. Kamar zatai kuka dan takaicin Mama daya kirata ta ce, “Zan koyi abinda bazai mana daɗi ba ni da kai”. Maimakon amsata zagayeta kawai yay ya wuce bayi a binsa. Wayyo jitai kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu. Zuciyarta na bata shawarar ta jirashi wata na ingizata ta tafi kawai. Harta wuce fuuu zuwa kofa sai kuma ya dawo jikin ƙofar bayin, cikin fashewa da kuka da masifa ta ce, “Wlhy idan har baka yi abinda nake so ba nabarka har abada, mugu kawai azzalumi ALLAH ya isa ban yafe ba. Ga gidan nan na bar muku macuta”. Daga haka ta fice fuuu. Duk abinda ya faɗa yaji, amma yay kamar bai jin ba ya cigaba da wankansa. Itako tana fita ɗakinta ta wuce, kai tsaye tace ma Momyn, “Momy muje kawai”. Murmurshi Momy ta saki a karo na farko na cin nasara, kafin ta ce, “Yaƙi yarda kenan?”.. Bata tanka zancen ba ta ce, “Momy ni dai muje”. Ba ƙaramin tashi hankalin Ismat yayi ba jin gidan zasu bari, ita kam ai ita za'a shukama tsiyar sakata yin nisa da masoyinta Ja'afar. Sai kawai ta sanya musu kuka da magiyar ita dai kada su tafi. Abi komai a hankali. Ai wani mari mai lasisi Momy ta bata, daga haka bata sake iya magana ba suka tattara kayansu da dama sun haɗa tun jiya Hinde ta dinga fita da su wajen mota. Tana son zuwa ta sanar ma Mammah tana tsoro, dole ta haƙura a gaban idonta Momyn Nabeeha taja mota ita da Nabeeha a gaba su Amima a baya suka wuce. Sai a lokacin ta falla zuwa sashen Mammah ta sanar mata. Mammah zata tada hankalinta ƴaƴanta suka zagayeta da daɗin baki. Koda Zak-Shadow ya dawo sashen yin breakfast da tai masa maganar shima cikin rashin damuwa ya ce, “Mammah ba ita ta zaɓi haka ba. Ki saka musu ido kiga iya gudun ruwansu kawai yafi sauƙi. Yanda ta tafi da ƙafarta da ƙafartata zata dawo”. Ba yanda zatai dole tai shiru.........✍🏼
Mu gayama ƴar Daba gaskiya ko muyi shiru duniya ta gaya mata 😂🏃🏼♀️🏃🏼♀️?.
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 68_
__________________
https://chat.whatsapp.com/J92XqvWDRch1EJPdGDBa41?mode=wwt
https://vm.tiktok.com/ZSHWHk4ULWbMN-geqJz/ This post is shared via TikTok Lite. Download TikTok Lite to enjoy more posts: https://www.tiktok.com/tiktoklite
https://chat.whatsapp.com/KfkKd9vD8MrAst8i8CQDsj?mode=wwt Assalamu alaikum, Mutanen arziki Ina musu capacity😍🥰 kuna Neman Inda zaku Samu ingantattun Kaya masu kyau da quality sosai 💝 Kamar Kayan Yara Zannuwan Gado Kayan kitchen Shoes and bags Jewellery Laces, atamfa,shadda Dadai sauransu. To nesa tazo kusa, Maza Danna wannan link din domin Samun Kaya masu inganci da ƙayatarwa da idan kika saka ko ina kika shiga sai an kalleki an ƙara kallo.
Ko ku nememu ta wannan number 08165751018 ❤️❤️❤️😘
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________