Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 66

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 66

.....the strength of blood like those of those who are bound was in front of Zak-Shadow who was about to enter his department. He and Imran stared at each other. In anger, Zak-Shadow said, "Give me a way". "What are you planning to do?". "I will follow you and pass". "It's okay to hit me, but if I push you to pass, you won't be able to enter this department. And I'm asking you to be more patient about what you did yesterday. I know you've been treated unfairly, Haysam, but look at Uncle Nasiru or his good son and let this girl and her behavior go." "Is it under the meter again?". "Please be patient, she will not hurt anyone again. Haysam Please, I am begging you not to follow her and become one. Leave her alone, she will know the other day". "I can't continue living with her". "Dear son of GOD, don't say that, that's what I fear more than anything. You are the leader of this house, what you have done will be easy to learn from Ja'afar. Sometimes when women do wrong to us, the solution is not to divorce them, the solution is to train them in the house. Don't forget that you are the one giving me this lecture. Why are you going to close your eyes now? She is not old enough to let go

Standalone post1,838 words

......Yanda hankalin su Janar ya tashi a wannan gaɓar har ba'a magana. Dan gaba ɗaya komai ya juye a yanda basa fata kuma basa zato da tsammani. Ga takurawa da suke samu daga gidan gwamnatin. Dole a karo na farko kwamitin bincike ya aikama Imran takardar gayyata. Wannan takarda kuma ta riskeshi a dai-dai lokacin da yake fitowa zai zo gidan su Zak-Shadow domin dubashi da duba jikin Nimrah. Harda matarsa, sai Ruƙayya da bataje makaranta ba jiya ta kwana da zazzaɓin mura. Ai ko tanata murna zata ga sabuwar ƙawar da Dada yace ya kawo mata. Komai Imran bai kawo ba game da wannan takarda ta gayyata, dan tunaninsa ma ai ana kan bincike ne game da su Dagger, yasan kuma za'a iya nemansu akan hakan. Suna shigowa gidan Zak-Shadow na fitowa daga sashen Mammah a zuciye, kallo ɗaya yay ma motar Imran ya ɗauke kai zai wuce. Imran ya san Zak-Shadow sani bana wasa ba, dan haka shima a kallo ɗaya da yay masa ya fahimci akwai matsala, ko gama kashe motar baiyi ba ya ɓalle murfin ya fito, cikin hanzari da ƙarfin jini irin na masu ɗammara ya sha gaban Zak-Shadow dake gab da shiga sashensa. Kallon kallo suka zubama juna shi da Imran ɗin. Cikin fushi Zak-Shadow ya ce, “Bani hanya”. “Mi kake shirin yi?”. “Zan bigeka na wuce”. “Sai dai ka bugeni ɗin, amma in dai sai na matsa ka wuce bazaka shiga sashen nan ba. Sannan ina roƙonka ka ƙara haƙuri akan wanda kayi jiya. Nasan an maka ba dai-dai ba Haysam, amma ka dubi Uncle Nasiru ko dan nagartarsa ka ƙyale yarinyar nan da halinta.” “Kasan mita sake min ne?”. “Kayi haƙuri indai ba wani raunin ta sake jima wani ba. Haysam Please ina ƙara roƙonka kada ka biye mata ku zama ɗaya. Ka barta ita da kanta zatai dana sani wataran”. “Bazan iya cigaba da zama da ita ba”. “Dan girman ALLAH kar kace haka, dan dama abinda nafi tsoro kenan fiye da komai. Kai jigo ne ga wannan gida, abinda kayi zai zama mai sauƙi wajen koyi gasu Ja'afar. A wasu lokutan idan mata suka kuskure mana, ba rabuwa da su bane mafita horasu a cikin gidan ne mafita. Karka manta kaine kake min wannan huɗubar fa. Miyasa yanzu idanunka zai rufe? Ita dai bata isa sakaka sakin Nimrah ba, ta dinga kallon yarinyar kawai a matsayin matarka duk da ƙarancin shekarunta ya isheta hukunci mai zafi da zai fi kowanne. Amma dan ka rabu da ita ai tamaci nasara kenan”. Kallonsa kawai Zak-Shadow yake yi, amma ya gagara sake cewa komai. Sai dai har yanzu zuciyar na'a maƙoshi, bai kuma gama tantance amsar kalaman Imran ɗin ba ko ƙin amsar. Dai-dai nan Ruƙayya da basu san da zuwanta ba ta kama hannunsa cike da farin ciki tana faɗin, “Dadana nazo”. Idanu ya lumshe a hankali, sai kuma ya juyo yana kallonta, yanda yarinyar ke masa murmushi cike da farin ciki sai shima bai san ya mata murmushi kaɗan ba, sai kuma ya ɗauketa gaba ɗaya yana sauke ajiyar zuciya. Batare daya sake kallon Imran ba ya juya sashen Mammah. Imran ya girgiza kai yana murmurshin shima. Dan ya tabbatar badan zuwan Ruƙayyan ba da wahala ya fasa shigar. Shima bayansu yabi, dama matarsa harta shige. Ba ƙaramin farin ciki Mammah tayi da ganin Zak-Shadow ya dawo ba, ta sauke ajiyar zuciya idonta akan Imran. Dan ta tabbatar badan zuwan nashi ba za'ayi mara daɗi ne yau a gidan. Murmurshi Imran yayi shima, cikin girmamawa yay mata nunin ta kwantar da hankalinta. Cikin jinjina kai tace, “ALLAH yay muku albarka”. Da Amin ya amsa yana hararar su Ma'aruff da suka tuttura baki alamar basu so ba, sun so yau Dadansu yaci ƙaniyar Nabeeha ne wlhy, amma Yaya Imran ya hana. Gargaɗi ya shiga musu da ido, dan haka suka haɗe hannaye alamar ban haƙuri. Daga nan suka maida hankali akan Aunty Hafsat matarsa dan ƴan gidanta ne sosai. Hasalima shi Ja'afar ƙanwarta zai aura mai suna Shariffa. Ma'aruff kuma ƙanwar su Imran ce sunanta Lailah. Dada kam tunda ya shigo bai kula kowa ba dama, kai tsaye inda Nimrah take ya nufa, itama hankalinta nakan Ruƙayya tunda suka shigo. Itama Ruƙayyan hankalinta akan Nimrah yake. Dada na ajiyeta kuwa ta koma kusa da ita ta zauna, cike da farin ciki ta ce, “Dada itace wannan?”. Kansa ya ɗaga mata yana kallonsu su duka, dan daga gani hali zai zo ɗaya. Sai Ruƙayya ta rungume Nimrah, cikin raɗa ta ce, “Daga yau ke ƙawata ce inji Dada”. Cike da farin ciki Nimrah tace. Eh. Ruƙayya ta ƙara rungumeta, sai kuma ta kalla ƙafarta ta ce, “Kinji ciwo ne?”. “Ƴar daba ce a gidan nan ta yankani da wuƙa ni da Dada”. Furucin Nimrah ya shiga kunnen kowa a ɗakin, hakan yasa Aunty Hafsat da Imran da Mammah da sai yanzu sukaji sunan da Nimrah ke kiran Nabeeha da shi duk suka kalleta. Su Bilal kam kwashewa sukai da dariya. Imran ya ce, “Nimrah ƴar daba kuma?”. “Eh Yaya” tace da Imran kasancewar haka taji su Ja'afar na kiransa. Caraf Ruƙayya ta ce, “K ba yaya ba Dady”. Kallonta Nimrah tayi itama, ta ce, “Ai su Uncle Ammar Yaya suke cewa”. Mammah tai murmurshi a karo na farko, cikin katse taƙaddamar tasu ta ce, “Nimrah su Yayansu ne, ke kuma Daddy zakice keda ƙawarki Ruƙayya ko?”. Kanta ta jinjinama Mammah tana murmushi, sai kuma ta kalla Ruƙayya ta ce, “Shike nan nace Daddy”. Ruƙayya tai dariya itama. Sai shirmen nasu ya burge kowa, ciki harda Dada dake sauke ajiyar zuciya kawai. Ƙarshe ma ya fice a ɗakin, Imran ya tashi ya bishi.....

(())★(())★(())★(())

Bayan sallar Azhar Imran ya amsa kiran kwamiti dan dama ƙarfe biyu suka buƙaci ganinsa. Bai gayama Zak-Shadow ba ya baro gidan akan zai je wani waje ya dawo. Shima Zak-Shadow bai tambayesa ina zai je ba ya wuce cikin gida dan akwai aikin da yake so ya kammala. Zuwa gobe da safe yake so ya zauna da Ojo.

★★★

Sojoji huɗu ne a matsakaicin ɗakin binciken da aka shiga da Major Imran Abbas, duk da kuwa yasan ɗakin ba baƙonsa bane. Cikin nutsuwarsa ya kai zaune bayan ya miƙa gaisuwar girmamawa a garesu, sai dai a zuciyarsa ya fara wasi-wasi amma ya danne.. Brigadier General Abraham Yohana ne ya fara magana. “Major Imran Abbas ka sani wannan zamane na sirri. We expect full honesty from you”. Ya ɗan ja numfashi yana jujjuya biro a yatsansa, kafin ya ɗan matsa kusa da teburin da takardun ke kai. “Before we proceed Major,” ya sake faɗa cikin murya mai sanyi sai dai cike da iko, “this is an official military inquiry. Anything you say here will be part of the record. Are you willing to cooperate fully with this Board?” Cikin girmamawa Imran ya ce, “Yes, sir! I’ll cooperate fully”. Takardar gabansa ya ɗan duba, sai kuma ya ɗago yana sake kallon sauran jami’an da ke gefe, kafin ya dawo da idanunsa kan Imran. “Good. Let’s start simple. A ranar 17 ga watan jiya May a ina Zak-Shadow ya kwana?”. Ba ƙaramin dukan zuciyar Imran wannan tambaya ta bazata tai ba. Sai kawai ya samu kansa da zubama Brigadier General idanu na sakanni. A zuciyarsa hasashen miya kawo wannan tambayar yake? Brigadier General ya sake katse masa tunani da maimaita tambayar. Ajiyar zuciya Imran ya sauke. Kai tsaye ya ce, “Sir yana sansani tare damu”. “Washe gari 18 fa?”. Gaba ɗaya Imran ji yake kamar zai rikice, amma ya ce “Itama haka....” “Ka tabbatar?”. Shiru yay ya kasa cewa komai. Brigadier General ya cigaba da faɗin, “To amma miyasa kuma anan bayanansa ya saɓa da abinda ka faɗa yanzu?”. Yay maganar yana yin nuni da projector daya bada umarnin a kunna. Ana kunnawa kuwa videon ranar da Zak-Shadow ya koma jejin bayan an kai hari na biyu garin Marke da Gangare ya bayyana. Tun daga isowarsa sansani a mashin da shigarsa mota shi da karnukansa har isowarsu Gangare da bayanin da yayi cikin ɓacin rai kan abinda ya faru, inda yace baya nan cikin kwana biyu kacal sun bari an musu irin wannan illar ya maimaita kansa yafi sau huɗu dan a sake tabbatar da ƙaryata abinda Imran ɗin ya faɗa ma. “Har yanzu kana akan bakan ka na cewar yana nan ɗin komai ya fara faruwa?”. Lt. Col. Peter Okon ya faɗa yana tsatstsare Imran da idanu. Shiru Imran yayi zuciyarsa na wani irin dokawa, zuwa yanzu ya fara hasaso al'amari mai girma, dan kuwa ba rami miya kawo rami. Babu dalili miya kawo ɗaukar video sirri akan su a lokacin da suke kan aiki. Imran nada haƙuri da sanyin hali, amma akan Zak-Shadow bashi da haƙuri da kawaici. Dan haka cikin tsaurara harshe a karo na farko ya ce, “Sir! Akwai makirci a wannan al'amarin kwarai da gaske. Eh naji kai tsaye zance Haysam baya cikin sansani tun daga ranar farko da aka kaima sojojinmu hari. Domin kuwa yazo ziyartar gida akan abinda ya shafesa, hakan kuma bawani abu bane a hukunce mun sani, musamman da idan mukai dubi da dalili mai ƙarfi ne ke iya saka Haysam motsawa daga sansani, sai kuma ya tabbatar babu wata matsa sannan baya iya wuce kwana biyu duk tsanani”. “Eh muma bamuce laifi yayi ba na zuwa gidan, sai dai miyasa ba'a kai harin ba sai bayan ya tafi? Kuma yanayin harin yay dai-dai da abinda ya faru shekaru uku da suka wuce.” Aka sake kunna wani video da aka ɗauka daga rikicin shekara uku da ta wuce, lokacin da Special Recon Unit ta jagoranci farmaki a yankin Gulmadu. Hoton ya nuna Zak-Shadow yana magana da sojoji, sai kuma a nan gaba aka ga wuta ta tashi, kamar umarnin harin daga gare shi ne. Wani kalar rinewa idanun Imran sukayi, sai dai kafin yay magana Colonel Galadima ya ce,........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 67_

__________________

https://chat.whatsapp.com/DMVSa4G3a9sDd8Jjgm0mzs?mode=ems_copy_t

Kin Dade kina Neman group din dazaki tallata kayanki kyauta Baki samuba to ki hanzarta shiga free advert group na EASHAS BITES AND BEAUTY domin tallata Kayanki kuyi saving number dinta domin samun shiga group dinnan akwai members Sama da 500+ aciki💃💃💃💃👇👇👇👇

wa.me/ +2348064705686

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________