
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 69
.....in. Therefore, I want to stop the work of their house and build them here in the house since there is a space at the back. If it is possible, change the whole structure of the house so that Bilal and Ammar can have their own and everyone can live in it. Start living with them, Jaafar, the bottom of what we have on the ground, I want to do that right, but I know the time is running out..." Imran interrupted him by saying, "Why are you saying that. I told you to stop playing with me." "Hmm! Imran, I'm not kidding." "Well, you know that wherever you are, we are together." "It's impossible. My son, I want you to keep working while I hide. I left a message for you in my room.." Just then they arrived at the door of Imran's house where Ojo was kept. The soldiers who were with them had already driven from their cars, so Zak-Shadow ignored Imran's look at him and opened the car and left. When he saw that Imran had no intention of coming out, he looked and said, "Ma'am, come out and give us the key". When Imran came out, he knew who Haysam was, he knew what was going on.
.....Motar shiru Zak-Shadow na murza siyarin a hankali tamkar baya so, a gefensa Imran ne zaune cikin alamu na tunani mai zurfi. A gabansu motar sojoji ce haka ma bayansu. Sai dai sukai tafiyar fin mintuna goma tsakaninsu da inda suka baro a karo na farko Zak-Shadow yay magana idanunsa akan titi. “Ina son su Ma'aruff su dawo kusa da Mammah”. Kallonsa Imran yayi na sakanni, kafin cikin damuwa ya ce, “Saboda mi?”. “Saboda bazai yiwu mu duka muyi nesa da ita ba.” “Wace irin magana ce wannan? Kai ina zaka da har zakai mata nisa?”. Murmushi mai yalwa Zak-Shadow yayi yana sake juya sitiyarin cike da ƙwarewa, sai kuma ya ɗan kalla Imran fisha ya maida idanunsa kan titin. Kamar bazai ce komai ba dan har Imran ya fidda rai da samun amsa, kafin ya ɗan furzar da iska. Cikin komawa serious ya ce, “Imran nasan ka san abinda nake hange, kuma bana jin akwai abinda zai hanashi faruwa sai wani ikon ALLAH. Mutanen nan sun gama shirya komai kafin su tunkaremu, kuma zaka tabbatar da hakan yanzu babu jimawa. Dan haka ina son a tsaida aikin gidansu ai musu gini anan cikin gidan tunda akwai fili ta baya. Idan zai yiwu kuma a canja tsarin gidan gaba ɗaya ma har Bilal da Ammar su samu nasu kowa ya zauna a ciki. Ka fara zama da su Ja'afar ɗin kasan abinda muke da shi a ƙasa, dan naso yin hakan dama sai dai nasan lokaci ya ƙure......” Cikin ɓacin rai Imran ya katseshi da faɗin, “Wai miye kake faɗa haka. Na gaya maka ka daina min irin wannan wasan.” “Humm! Imran ba wasa nake ba”. “To ka sani kuwa duk inda kake muna tare”. “Bazai yiwu ba. Dan ina son a lokaci dana ɓuya kai ka cigaba da aiki. Na ajiye maka saƙo a ɗaki na..” Dai-dai nan suke isowa ƙofar gidan Imran inda aka ajiye Ojo. Tuni sojojin da suke tare duk sun dirga daga motocin da suke, dan haka Zak-Shadow bai kula kallon da Imran ke masa ba ya buɗe motar shima ya fita. Sai da ya ga Imran bashi da niyyar fitowa sannan ya leƙasa da faɗin, “Malam fito ka bada key mana”. Shiru Imran ya kasa motsawa, dole Zak-Shadow ya zagaya ta inda yaken ya buɗe masa da kansa. Tamkar wanda juwa ke neman zubarwa haka Imran ya fito, yasan wanene Haysam, sani irin na ciki dabai ɗin nan. Tunda har ya ambata batun zai ɓuya akwai abinda ya gama shiryawa, wanda shi Imran yake gudu da son yaƙa. Ganin duk sojojin sunyi tsaye alamar shi suke jira da ƙyar ya iya ciro waya a aljihunsa ya shiga ƙoƙarin kiran mai kula da gidan, sai dai har kiran ya tsinke ba'a ɗaga ba. Ya sake na biyu ma haka, zai sake na uku Zak-Shadow yay ɗan murmurshi. Sai kawai ya dubi sojojin yace su ɓalle ƙofar. Hakan kuwa akai, sun tafi da nufin ɓalle ƙofa suka sameta a buɗe. Tun a anan aka tsaya kallon kallo, sai dai basu ce komai ba suka tura gate ɗin suka shiga. A tsakar gida suka tadda mai kula da gidan a yashe, ga wayarsa da Imran ke faman kira a gefe. Tattaɓashi ɗaya daga cikin sojojin yayi, cikin sauri ya ɗago ya ce, “Baya numfashi”. Cikin tashin hankali Imran ya iso wajen, shima ya tattaɓashi amma da gaske baya numfashi. Suna ɗagoshi sukaga alamar an dakeshi ne ta ƙeya da wani abun. A take shugaban tawagar ya basu umarnin shiga gidan, shiko Imran sai jijjiga yaron yake yana ambaton sunansa amma babu alamar rai tare da shi. Zak-Shadow na gefe tsaye kawai ya zubama Imran ido...
Cikin abinda bai fi mintuna goma ba su Zak-Shadow suka fahimci babu Ojo a gidan an fita da shi. Dan a cikin gidan a ɗakin da Imran ya tabbatar ya ajiye Ojo duk ya aɓaci da jini har ta kan stairscase da falon. Dama gidan babu komai a cikinsa. Amma duk da haka sai da sojoji suka bincike ko wane lungu da saƙo nashi. Iyakar tashin hankali Imran ya shiga, amma abin mamaki Zak-Shadow ya dake a zahiri, koda akwai wata damuwa a tare da shi ya barma ransa. Tuni sojojin dake tare da su har sun isar da saƙo zuwa Headquarter. Ba'ai wani dogon lokaci ba aka zagaye anguwar da sojoji. Maƙwaftan dake jikin gidan duk an sakasu sun fito duk da ma sabuwar anguwa ce. Su akai taima tambayoyi suna bada amsar komai dalla-dalla. Sun tabbatar da wasu mutane ne suka zo gidan, hakan na nufin sune suka ɗauke Ojo kusan awani uku da suka shuɗe kenan, dan wasu sunga motar data shigo anguwar har cikin gidan, sannan duk sunji sanda mai kula da gidan keta ihun neman ɗauki amma tsoro ya hana su fita kasancewar su mata, ga shi kuma sunyi harbin bindiga har sau biyu. Cikin sa'a wani saurayin yaro ya bada siffar motar kaf da lambar jikinta, daga haka suka baro gidan shi kuma yaron Zak-Shadow da Imran ɗin suka wuce da shi asibiti. Sai dai me, suna isa asibitin sai ga sojoji an saka sun biyo bayansu wai kulawar yaron zata koma ƙarƙashin ikonsu. Tun daga nan Zak-Shadow ya fahimci anzo dai-dai wajen.....
<<%>><<%>><<%>>
Ɓatan Ojo ya sake hargitsa komai ta kowane ɓangare, dan hatta a cikin su jami'an sojin dake jin Zak-Shadow bazai iya aikata abinda ake zarginsa a kai ba zukatansu sun fara rawa da wasi-wasi. Sai dai a gefen zukatan nasu basa fata hakan ta kasance. Sai dai mizai faru kuma, ana kukan targaɗe kan batun Ojo sai kuma ga na karaya ya faru, dan kuwa misalin ƙarfe biyar na yammar wani mummunan labarin ya sake isowa hukumar sojoji. Wai an harbi jirgi mai saukar angulu na sojoji dake ɗauke da su Dagger a hanyar kawosu nan Abuja. Sabon zance kenan. Cikin gaggawa aka aika jami'ai inda abin ya faru. Kuma a cikin wani ƙauye abin ya faru, har an samu mutuwar fararen hula shida wasu sun jikata. Hakama sojojin dake tare da jirgin mutum biyu a cikinsu sun rasu, sauran sun raunana. Su Dagger su goma sha uku ne, an samu gawar biyar a cikinsu, sauran takwas ba'aga ko mutum ɗaya ba, hakan na nufin an ɗaukesu kenan. Duk da zancen bai gama bayyana ko a Headquarter ɗin ba, a yanayin nan duk wani masoyin Zak-Shadow dole ya kasance cikin jimami da fargabar abinda zai iya biyo baya, domin kuwa case ɗin su Dagger shine tushen case ɗin Ojo da ayanzu kai tsaye ake tuhumar Zak-Shadow akai.
_____________★
A Defence Headquarters kuwa, batun ɓacewar Ojo da batun su Dagger ya kai ga har gidan gwamnati. Abin mamaki, cikin ƙanƙanin lokaci aka kira taron gaggawa. (Emergency Security Council Meeting). Ba a ɓata lokaci ba, tuni manyan jami’an tsaro suka hallara cikin ɗakin taron, kowanne da fuska mai ɗauke da damuwa da jimamami, dan rashin su Dagger da Ojo kai tsaye na nuna tabbacin zargin da akema Zak-Shadow ne, duk masu bashi kariya basu da wani sauran abin faɗa. Bayan ƴan mintuna kaɗan da tattaunawa, an fito da hukunci mai nauyi. COAS ya samu umarni daga sama kai tsaye na kama Zak-Shadow. An kuma tabbatar masa a daren yau dan ba'a buƙatar wata hayaniya. Wannan shine saƙon umarni da COAS ya samu a dai-dai wannan lokaci da agogo ke neman buga ƙarfe shida na yammaci a ofishin ministan tsaro bayan fitowarsu daga meeting room. Shiru General Yusuf yana kallon ministan tsaro dake bada umarnin bai iya cewa komai ba na ƴan dakiku. Ya kasa ma kallon sauran takardar da ke gabansa. Sai da Ministan ya sake maimaita umarnin da baki cikin ɓacin rai, yana jaddada cewa umarnin daga shugaban ƙasa ne, sannan Janar ya furta, “Yes, sir”. Ya faɗa yana sauke numfashi mai nauyi tare da miƙewa ya fito. Da sauri aka buɗe masa mota ya shiga, tunda suka baro ofishin minista ya faɗa duniyar tunani. A zuciyarsa kalmomin Minista ne kawai ke maimaituwa a kwalwarsa kamar amsawa kuwwa ne a cikin kunensa. Haysam Abdul-rasheed... to be apprehended. Hankalinsa a tashe yake matuƙa, zuciyarsa na masa zafi. Duk da cewa aikin soja ya koya masa ya bi umarni ba tare da tambaya ba, wannan karon zuciyarsa ta ƙi yarda. Amma ba shi da zaɓi. Suna isowa office shima yay kiran Director of Military Intelligence dake ƙoƙarin barin office. Amma dole shima ya yanke nasa hanzarin ya amsa kira. Tunda ya shigo office ɗin ya fahimci akwai matsala sosai, dan fuskar COAS ta nuna kai tsaye. Yayi gaisuwa cikin girmamawa. Amma COAS bai iya ya amsa da baki ba hannu kawai ya ɗaga masa. Kafin bayan sakanni biyu ya fara magana muryarsa cike da raɗaɗi, “Issue the arrest directive Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu quietly. No noise.” Shima ba ƙaramin faɗuwa gabanshi yayi ba, ya ɗan zaro idanu waje zuciyarsa na girgiza. Sai dai kafin ma yace komai COAS ya miƙe abinsa alamar baya buƙatar wani zance. Rai a dagule ya fice daga ofis ɗin ba tare da ya tsaya da kowa ba ya bar Headquarters ɗin gaba ɗaya zuwa gidansa, kamar wanda yake guje wa wani abu da zuciyarsa ta kasa jurewa.
Bayan mintuna talatin, takardar Arrest Directive ta fita da cikakken sa hannun doka. An tura ƙungiyar jami’ai shida daga Military police da zasu kama Zak-Shadow bisa umarni, tare da amsar dukan abinda ya shafi matsayinsa.
(((*)))(((*)))
A ɓangaren Zak-Shadow da Imran sam basu sam mike faruwa ba, dan yanzu ma suke isowa gida daga asibiti bayan jam'an sojan nan sun tabbatar musu da komawar kulawar yaron a ƙarƙashinsu bisa umarni daga Headquarter kai tsaye gida suka nufa.. Sun yi ƙoƙarin kauda hankalinsu daga tashin hankali, kowa da tunanin da yake ƙoƙarin ɓoyewa, duk da shi Imran yaso su cigaba da tattauna maganar da suka fara ɗazun da Zak-Shadow ɗin, amma shi kuma yanata kaucewa sai kawai ya haƙura yay shiru shima har suka iso anguwarsu. Zak-Shadow sai da ya kai Imran har gida sannan shima ya shiga. Bilal ne ya buɗe masa gate, dan ya fito zai je massalaci sallar Magriba da aketa kira. Shima sai yana ajiye motar bai shiga ba ya fito domin gabatar da sallar kamar yadda ya saba. Bayan idar da sallar magriba ya fito Bilal tare da shi. Labarin rigimar Nimrah Bilal ke bashi har suka iso ƙofar gate ɗinsu, hakan kuma yay dai-dai da isowar motar data saka Zak-Shadow tsayawa. Shima sai Bilal ya tsaya yana kallon motar kawai........✍️
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 70_
__________________
https://chat.whatsapp.com/J92XqvWDRch1EJPdGDBa41?mode=wwt
https://vm.tiktok.com/ZSHWHk4ULWbMN-geqJz/ This post is shared via TikTok Lite. Download TikTok Lite to enjoy more posts: https://www.tiktok.com/tiktoklite
https://chat.whatsapp.com/KfkKd9vD8MrAst8i8CQDsj?mode=wwt Assalamu alaikum, Mutanen arziki Ina musu capacity😍🥰 kuna Neman Inda zaku Samu ingantattun Kaya masu kyau da quality sosai 💝 Kamar Kayan Yara Zannuwan Gado Kayan kitchen Shoes and bags Jewellery Laces, atamfa,shadda Dadai sauransu. To nesa tazo kusa, Maza Danna wannan link din domin Samun Kaya masu inganci da ƙayatarwa da idan kika saka ko ina kika shiga sai an kalleki an ƙara kallo.
Ko ku nememu ta wannan number 08165751018 ❤️❤️❤️😘 __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________