Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 53

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 53

.....it was his son who drowned. What he did also increased his doubts in the hearts of the government officials who are always reminding the governor himself. After their servant Zak-Shadow, the government house had to gossip about Zak-Shadow's pride. They say that he is only a Lieutenant Colonel and that he is going to become a General one day. They say that this will be able to establish a coup on the ground. Oho, he doesn't know my name, he just left the government house at the airport and will go to Abuja. Their flight is about to take off too. There he found Ojo waiting for him, he bought tickets for him as well. He didn't plan on taking Ojon, but he was determined to pull him back in his body more than before for some reason of his own. Less than ten minutes after arriving at the airport, their plane took off. They landed in the federal city after less than an hour's journey. At the airport they parted ways with Ojo, he went to his barracks and found them Ma'aruff came to pick him up. They embraced him with joy. Ojo, who was following them with a grumpy look, handed Jaafar the Zak-Shadow briefcase in his hand. Before he was caught and chopped. He just raised his hand to him

Standalone post2,090 words

.......Duk da yanda yake maganar kai tsaye ta sosa zuciyar gwamna haka ya danne, dan harga ALLAH wani irin kwarjini da cika waje Zak-Shadow ɗin yay masa. Ya jima yana jin labarinsa da jarumtarsa a wajen yaransa musamman kwamishinan tsaro a tsakanin wannan rikicin, amma bai taɓa tunanin mutumin fa ya wuce yanda ake labarin nasa ba. Cikin danne abinda ke ransa da nuna aminta da zancen Zak-Shadow ɗin ya tabbatar masa zai yi ƙoƙarin yin abinda ya dace in sha ALLAHU daga yau zuwa gobe ma. Dan ya fahimci hukumar sojin ma wani girma na musamman take bashi. Sun ƙara tattaunawa akan batun ƙara sojoji a cikin jejin kafin meeting ɗin ya tashi. A gidan Gwamnatin sukai sallar azhar, daga nan sukai zaman cin abinci da gwamna wanda Zak-Shadow yaƙi cin komai a wajen. Wannan ba sabon abu bane, dan duk wanda ya sanshi yasan ba'a ko'ina ake bashi abu yaci ba. Dan komai nashi da tsari. Kai da yawansu zasu iya ratsuwar basu taɓa ganin ya zauna cin abinci a gaban kowa ba. Idan zai ci abinci yakan killace kansa ne yaci a nutse. Hakan da yayi ma ya ƙara saka jin shakkarsa a zukatan jami'an gwamnatin da akai zaman hadda gwamnan kansa. Dan bayan barowar su Zak-Shadow gidan gwamnatin sai da sukai ƴar gulma akan girman kan Zak-Shadow yayi yawa. Acewarsu yana Lieutenant Colonel kawai yana wannan isar da izza inaga ya zama General watarana, ai kowama ya shiga uku. Acewarsu wannan tsaf zai iya assasa juyin mulki a ƙasa.

Oho shi baima san sunayi ba, dan daga gidan gwamnatin airport ya wuce zai wuce Abuja. Jirginsu yana gab da tashi ma. Acan ya samu Ojo na jiranshi, shi ya saka ya saya masa tickets harda shi. Bai tsara matakin ɗauka akan Ojon ba, amma ya ƙudira sake jansa a jikinsa fiye da da saboda wani dalili nashi. Mintina baifi goma da zuwansa airport ɗin ba jirginsu ya ɗaga. Tafiyar da bata gaza awa ɗaya ba suka sauka birnin tarayya. Anan airport suka rabu da Ojo, shi ya wuce barrak shi kuma ya samu su Ma'aruff sun zo ɗaukarshi. Cike da farin ciki suka rungumeshi kuwa. Ojo dake binsu da kallon ƙurilla ya miƙama Ja'afar ƴar briefcase ɗin Zak-Shadow ɗin dake hannunsa. Kafin ya ƙame tare da sara masa. Hannu kawai ya ɗaga masa batare daya kallesa ba, amma yana lure da kallon ƙurillar da yake ma su Ja'afar ɗin. Kaɗan ya cije lips ɗinsa, a ransa yana raya (Yaro tsaya matsayinka kada zancen ƴan duniya ya ruɗe ka. Dan in kace zaka tsalla gonar zuri'ata zan yanka maka kazar wahala ne kuma sai ka figeta da sili-silin gashi). A zahiri kam bayan mota da Ma'aruff ya buɗe masa ya shiga ya zauna. Suma duk gaba suka shiga Ja'afar yaja motar suka kama hanyar gida. Gaba ɗaya sun cika masa kunne da surutu kamar wasu ƙananun yara, shi dai yana jinsu da kunne kawai, wani lokacin kuma yakan yi murmurshi ko girgiza kai da faɗin, “ALLAH ya shiryeku” a taƙaice. A haka suka ƙaraso gidan....

(((★)))★(((★)))

Zantukan Ojo kaf sunje kunnen oga Jush shugaban ƙungiyar duhu. Dan haka ya tara meeting na gaggawa ga members ɗin ƙungiyar. Dama dukkan motsinsu a tsakanin nan a cikin meeting ɗin suke kala-kala. A duk sanda ya bada umarni babu mai wasa wajen amsa kiransa. Dan haka a yanzun ma cikin gaggawa suka gama hallara. Kowa da kowa yazo idan ka cire Dagger da dama ba akowane zama suke zama da shi ɗin ba sai suna buƙatar hakan saboda a wajensu sunan karen farauta kawai yake amsawa. Saɓanin kowanne zama yau oga ne ya fara magana kafin ma su tambayi dalilin zaman. Sai da ya fara kunna musu recording ɗin muryar Ojo da aka tura masa duk suka saurara. Batare da jiran cewar wani a cikinsu ba ya cigaba da faɗin, “Zamu rushe wasu ɓangarori na plan c”. Gaba ɗayansu kallon kallo suka shiga yi a tsakaninsu, cikin alamar tambayar juna a yanayin kurame suke ɗan jujjuya hannayensu. Wasu ko na ɗan ɗage kafaɗa da taɓe baki irin na suma basu gane ba. Oga Jush dake binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya yay ƙaramar gyaran murya daya dakatar da gungunan nasu dake tashi a ɗakin. Tsitt sukayi gaba ɗaya, tare da maida hankali kansa. Sai da yaja sakanni cike da shan ƙamshi sannan ya cigaba da magana. “Kamar yanda na faɗa bama buƙatar wasu ɓangarori na plan c kwata-kwata saboda na fahimci wani abu a yanzu”. “Kamar mi kenan oga?”. “Muna buƙatar su Dagger a raye. Dan haka Viper ka dakatar da plan ɗinmu na tura masu kashesu”. “Yanda kace haka za'ai Sir. Amma miyasa kace hakan? Bayan kasan zaman mutanen nan a raye hannun sojojin nan komai zai iya faruwa, ciki kuwa harda sanin mu su wanene. Musamman haɗarin yafi girma akan Dagger da shi ya sammu. Gara ma sauran su Dagger ɗin suka sani”. Tabbas zancenka a kan hanya yake kuma kana kan dai-dai Viper. Amma abinda nake son ku tuna ba ko yaushe ake iya kama tsuntsu ta baki ba, dan wani tsuntsu ba hatsi yake ci wajen ƙoto ba ababen cikin ruwa ne abincinsa. Ba kashe Dagger ne mafita ba, yin amfani da shi wajen kama mutumin nan ta wuya shine ya dace”. Sake kallon kallo suka shiga yi, dan su sam basu wani fahimci komai ba. Cike da izza Mr Specter sarkin ƴan girman kai tamkar ogan nasu ya furta, “Na fahimci abinda kake nufi Oga, kuma nayi na'am da wannan tsarin. Kai tsaye ma ni har wani ƙyaƙyƙyawan tunani yazo min”. Karo na farko Oga Jush ya saki murmurshi idonsa akan Mr Specter, shiyyasa yake matuƙar son shi, dan shima akwai kwanya. Yana wani jinjina kai da lumshe idanu da buɗewa a lokaci guda ya ce, “Yes Mr Specter muna saurarenka, wane tunani kayi?”. Wani ƙarin girman kai Mr Specter yaji, dan haka ya gyara zamansa yana ajiye ƙatuwar sigarin hannunsa a ɗan bowl ɗin da yake tara tokar. “Sir ina ganin wannan sabon shirin zai dace da yin jifa da karan farautarmu a jikin fatsar da zata kamo mana wannan babban kifin. Ina nufin wannan yaron Ojo, dan aikinsa na ƙyau sosai, sai dai gaggawa zata hana masa yin doguwar tafiya dan Zak-Shadow ba sakarai bane”. Murmurshi mai faɗi Oga Jush ya sake saki, sai kuma ya shiga tafama Mr Specter, dole suma sauran suka zama ƴan bin yarima akasha kiɗa kawai. Sai da sukai na fin sakan goma sha biyar sannan suka sarara. Oga Jush ya ce, “Lallai ka gane mi nake nufi a sabon shirin mu na ɓangaren haggu. Na ɓangaren dama kuwa lokaci yayi da tafiyarmu zata gayyato manyan babba da jaka na ƙasar nan, hakan ne kawai zai bamu damar farauto kifin cikin ruwa dake gadarar shi ISHA'U DUTSE NA RIMI ne BAKA FARGABA, to amma a ƙarshe shima ai yace SAI NA RUWA ko”. A karo na farko saura ma suka fahimci darasin Ogan nasu, dan a tare suka kece da dariyar mugunta da na hango nasara. Sun sake tattauna abinda ya dace musamman akan fara horar da sabbin yara da maye gurbin Dagger a cikin yaransa da su Zak-Shadow basu kama ba da gaggawa, sai al'amarin Ojo da shima dole su gaggauta, daga haka taron ya watse zukatansu fes.....

<><><><><><><>

Tun shigowarsu harabar gidan Zak-Shadow ya zubama baƙuwar motar dake fake a dai-dai ƙofar sashensu idanu. Koda Ja'afar ya kammala parking a inda ya dace har Ma'aruff ya fita ya buɗe masa sashen da yake hankalinsa nakan motar dai, a karo na farko shima Ma'aruff ɗin ya juya ya kalla motar, sai kuma ya juyo batare da jiran tambaya ba ya ce, “Dada motar Momyn su Ismat ce, jiya tazo da yamma itama”. Kauda idanun nasa yay daga kan motar, batare da yace komai ba ya miƙama Ma'aruff ɗin wayoyinsa biyu. Ja'afar ma daya riga ya fito can gefen ya buɗe ya ɗauki briefcase ɗinsa. A tare suka rufe motar, sai kuma suka kalli juna suna murmushi ganin ya nufi sashen Mammah. Da sauri sukabi bayansa sun ɗan tafa kowa ya janye hannunsa yana yarfarwa da ƙoƙarin danne dariya duk a lokaci guda, sai kuma akai sa'a Dadan ya juyo zai kallesu ganin basu biyo shi ba. Da sauri suka gimtse fuskoki tare da zabura inda yake. Shaƙiyancin Ja'afar da Ma'aruff babu wanda bai sani ba, dan haka ma ya juya abinsa ya cigaba da tafiya suna take masa baya. Sallamar su ta saka Mu'azz dirowa a kujera da gudu yayo ƙofa, cike da farin ciki yake faɗin, “Oyoyo Dada na”. Guntun murmushi Zak-Shadow yayi, tare da tsayawa cak har Mu'azz ɗin ya ƙaraso inda yake ya rungumeshi. Kan yaron ya shafa, dai-dai shima Ja'afar na kai masa rankwashi da faɗin, “Ɗan iya kenan, wato Dadanka ma kai kaɗai, ai mu riƙo aka kawomu gidan naga”. “Ai rankwashin da yafi wannan ya kamata kai masa”. Cewar Ma'aruff yana harar Mu'azz shima. Baki Mu'azz ya tura yana sake maƙale Zak-Shadow, dan in dai muguntar Uncle ɗin nasa biyu ne ya saba da ita a gidan. (Mu'azz ɗan Aunty Ummi ne, mahaifinsa ya rasu tun yana a ciki, dan watan Aunty Ummi ɗin bakwai da aure mijin nata ya rasu, ba kowa bane face yayan Imran, rasuwar ta gigitata dama ahalinsa da su su Zak-Shadow ɗin, har takai ta shiga wani yanayi na ciwo dole aka dawo da ita gida, a haka ta ƙarasa rainon cikin ta haifeshi. Ko bayan haihuwar tasa ma ansha fama da ita kafin ALLAH yasa ta koma dai-dai ta cigaba da shayar da shi, sai dai rainonsa gaba ɗaya Mammah da Mimi ne sukayi shi, har ya kai yaye. Ta jima a gida bata sake wani auren ba kusan shekara biyar dan tama koma karatu, sai da Zak-Shadow yay mata jan ido sannan. Ƴan gidan su Imran basu taɓa nuna kwace Mu'azz ba a hannunsu, sun san yana samun dukkan gata anan gidan, sai dai kuma suma hakan baya hana suyi masa nasu gatan. Dan haka Mu'azz shine jika na farko a gidan tunda har yanzu matar Dada Nabeeha bata haihu ba duk da kuwa tare akai bikinsu da Ummi ɗin a lokacin. Gashi a gidan sabon aurenta har ta sake yara biyu). “Dada! Nima kaga Mammah ta kawo min sabuwar ƙanwa. Sunanta Nimrah”. Mu'azz yay maganar yana raba jikinsa dana Dada. Bai jira amsarsa ba ya bar wajen da ɗan gudu. Inda Nimrah take maƙure a tsakanin kujera tunda sukai sallama ta tashi ta buƴa a wajen dan har yanzu bayan Mammah da Mu'azz ɗin taƙi sakin jiki da kowa a gidan. Hannunta ya kamo cike da farin ciki ya ce, “Nina taso ga Dadana da nake baki labari yazo”. Kafaɗa Nimrah ta maƙe alamar bazataje ba. Da damuwa a fuskar Mu'azz ya juya inda su Dada suke tsaye har yanzu yana kallon su. “Dada kaji wai bazata zo ba”. Maimakon Zak-Shadow ya basu amsa sai ya shiga takawa a nutse har inda suke..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 54

__________________

https://vm.tiktok.com/ZSHcfQFhUuBVU-MpLRV/https://www.instagram.com/dijas_delicacy_?igsh=MWp3MThqcXlsZXB2eg==Wa.me/+2348140002981

Instagram

https://www.instagram.com/dijas_delicacy_?igsh=MWp3MThqcXlsZXB2eg==

Assalamu alaykum mutanen Sokoto Da kewaye Shin Ko kunsan cewa DIJAS DELICACY ashirye take Domin faranta ranku a bukukuna Da kowani irin even? Kama Daga samosa, doghnut, spring rolls meat pie, birthday cakes Da sauransu Bata tsaya anan ba tana amsar orders koda yaushe. Inda samosa kike nema frozen Ko fried duka tana dasu akan 3k 10pcs and she bakes daily🥰 Bata tsaya anan ba GA masu son gyaran jikinsu wata skin care tana siyarda best skin care products Kama Daga face wash, face cream,body butter, shower gel dadae sauransu tana aeka Kaya a kowani gari cikin aminci Da yardar allah GA no. Dinta kiyi saving Domin samun naki was.me/+2348140002981 __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________