Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 13

Post

KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 13

.....with the situation she is in, she wants to see where she will develop. Then she prevented his heart from thinking long and imagining that he was with his wife. As soon as that came to her mind, she pushed away the dirty thoughts and said (What is my water if this is the case?). When Uncle Ma'aruff was about to pass the mosque, she couldn't help but pick up her phone. She sent him a short message like this. (Everyone goes to the mosque except my Dad. If my Baby misses the Friday prayer, I see Boni). Then she put down the phone and they went to the kitchen with Ruky. You have to prepare a lot of food as usual every Friday like this and Aunty Mimi spends the whole day in the house.. .....★★ Nimrah's message reached Dadah's phone just when he was standing in front of the mirror and spraying his body with perfume. It is very beautiful in the soft white fabric that sits on his body. Here's a hat that looks like a mask of ALLAH. Through the notification, he saw Little Shadow's name as he was saving. He put the perfume down after spraying and picked up the phone and entered the message. His unprepared smile slipped from him. He repeated the message three times and then put the phone i

Standalone post2,002 words

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 4_* _Chapter 13_

__________________ __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

...........Har masu tafiya massalaci suka gama shiryowa suka fito tare da yara da aka ɗakko school babu Dadah babu labarinsa. Nimrah dai nata dannewa, bata yarda kowa ya lura da halin da take ciki kan son ganin ta ina zai ɓullo ba. Sannan ta hana zuciyarsa yin dogon tunanin hasaso mata yana tare da matarsa ne. Da hakan yazo mata a rai sai tai a'uziyya ta ture gurɓataccen tunanin da faɗin (Inama ruwana idan haka ne?). Sai da taga har su Uncle Ma'aruff na shirin wucewa massalaci ta kasa daurewa ta ɗauki wayarta. Gajeren saƙo ta tura masa kamar haka. (Kowa ya tafi massalaci amma banda Dadah na. Idan Babyna ya rasa sallar juma'a naga Boni). Daga haka ta ajiye wayar suka wuce kitchen ita da su Ruky. Dan dole a haɗa abinci mai yawa kamar yanda sauka saba duk irin wannan ranar ta juma'a da dama su Aunty Mimi ke yini gidan..

.....★★

Saƙon Nimrah ya iso wayar Dadah ne a dai-dai lokacin da yake tsaye gaban mirror yana fesa ma jikinsa turare. Yayi matuƙar ƙyau cikin yadi mai laushi fari tas daya zauna masa a jiki ɗas. Ga hula ya mirza masha ALLAH. Ta notification yaga sunan Little Shadow kamar yanda yay saving. Ya ajiye turaren daya gama fesawa ya ɗauka wayar ya shiga saƙon. Murmushin da bai shirya ba ya suɓuce masa. Ya sake maimaita saƙon har sau uku sannan ya saka wayar aljihu yana juyawa ya kalla Nabeeha dake barcin wahala a gadonsa. Komai bai ce ba ya ɗauka takalma ya saka sannan ya fice.

Tun kafin ya gama bayyana mayataccen ƙamshinsa ya gama gauraye sashen. Cikin rawar jiki Rayhana dake a babban falo zaune tana dakon jira numfashinta yay wata kalar fusga kafin ya dawo da ƙyar. Dan sai da ta haɗa da iskar baki wajen jawo shi. Da rawar lips data murya take masa sannu da zuwa. Hannu kawai ya ɗaga mata ya wuce batare da ko kallonta yayi ba. Ita ko kamar mayya haka take binsa da kallo idanunta na cika da ƙwalla. Wani abu mai ɗaci ya ƙara tokare mata ƙirji ganin har ya nufi ƙofar fita ya dawo ya nufi sashen Nimrah. Cikin sauri da son yay mata ko magana ne ta ce, “Dadah bata nan”. Cak ya ɗan tsaya. Sai kuma ya juyo zai wuce batare da yayi maganar da take so ɗin ba. Dan ya san Nimrah bazata wuce sashen Mammah ba. Lips ta cije da ƙarfi, zuciyarta tamkar zata kama da wuta. Komai a duniya bawan ALLAHn nan yayi birgeta yake tun a shekarun baya bama yanzu ba. Ita kaɗai tasan girman darajar abinda take ji game da shi a zuciyarta. Yayinda a yau wani kishi mai tsanani na duka matan nasa ke neman halaka ta. Musamman Nimrah da duk wanda ya kalleta ya kalla Dadahn yasan ba ƙaramar shoshalewa akayi a tafiyar nan ba. Ji take kamar bazata iya cigaba da zaman gidan nan ba. Amma dole ne ta daure kodan samun cikar burinta kamar yanda First Lady ta tsara mata da kuma yima First Lady ɗin aikinta....

•==•===•==•

Kasancewar guri yana gab da ƙurewa, ga Imran na jiransa su wuce massalacin bai shiga sashen Mammah ba. Drivern Daddy Imran ya fito da sauri ya buɗe masa murfin, sai da ya shiga kusa da aminin nasa dake ƙare masa kallo yana murmurshi tunda ya fito sannan. Securitys ɗin dake tare da Imran ɗin ne suka buɗe gate. Dan su Malam Almu sun wuce sallar juma'a tare da su Bilal. Harda Mole kuma da Sanda da basu san Dadah ya dawo ba. “Surukina ba gaisuwa? Anya bazan ƙwace yarinyata daga hannunka ba koda na sati ɗaya ne?”. Daddy Imran ya faɗa cike da tsokana. Batare da Dadah ya kallesa ba ya ce, “Idan ma kayi hakan kunya zata baka”. Cikin dariya Imran ya ce, “Kar dai ka cika baki ta baka mamaki. Dan ita ba irin matarka bace mai tafiya ta dawo da kanta.” Murmurshi kawai Dadah yayi batare da ya sake cewa komai ba. Shima Daddy Imran bai sake magana ba kasancewar sun kusa isa massalacin. Dan Central mosque suka zo...

Bayan an idar da salla basu biya ko ina ba suka dawo nan gidan. So suke su ci abinci anan sannan su tafi gaida Baffah da Uncle Nasiru. Shigowar su Ja'afar kenan suma. Suna fitowa a motoci sai gasu Dadahn. Cikin kiciɓus akai haɗuwar ragabza tsaƙanin Dadah da Mole. Ga kuma Sanda daya gama daburcewa.. Idan akace muku Dadah to kawai kuyi ruff da bakin ku. Dan kuwa zaku sha mamaki idan nace muku kallo ɗaya yayma Mole ya ɗauke kansa. Sanda kam yi yay kamar bai ganshi ba. Hasali ma da hannu ya amsa musu gaisuwa. Sai kuma ƙannesa suka zagaye su. Daga haka suka shige ciki akabar Mole da zufa Sanda da jin fitsari na neman kufce masa... Dadah baiyi mamakin ganin ƙannen nasa ba. Sai ma Biebah ce ke ɓoye-ɓoye dan tasan tayi saurin zuwa gida. Ilai kuwa da Dadah ya kafeta da ido sai duƙar da kanta tayi tana addu'a. Bai ce mata komai ba ya ƙarasa inda Mammah take shi da Daddy Imran. Su Aheel dake riƙe da hannun Dadah ƙafa da ƙafa duk suka jingina a jikinsu. Gwaggo Khadijah da Mammah suka gaida. Gwaggo Khadijah na jera ma Dadah sannu da dawowa. Su Aunty Mommy ma duk suka zo suna gaishe su. Harda Biebah da ke fatan kar Dadah yay mata faɗa. Alhamdullahi kuma baiyi ɗin ba. Ruƙayya da Nimrah ne kawai babu. Sai da suka miƙe domin zuwa dining da aka cika da kanyan abinci kala-kala sannan. Dai-dai lokacin Nimrah da su Mimi suka saka ta sake sabon kwalliya ke fitowa daga kitchen ɗauke da jug na glass da aka zuba ruwan tataccen tuffa da strawberry, dariyar hirar da suke yi da Ruky take yi a hankali. A kan Dadah idanunta suka fara sauka. Dan ya kai zaune kenan a kujerar da Bilal ya gyara masa ne. Kawar wa yay cike da basarwa ganin yanda ta tsaya cak kamar wadda akama tsawa. Sai da Daddy Imran dake murmushi ya furta, “Daughter ƙaraso mana.” Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta ɗanyi. Ta ɗaga ƙafafunta da ƙyar ta iso tana ajiye jug ɗin. A karo na biyu suka sake haɗa ido da Dadahn dake mata kallon ƙasan ido. Ita ta fara kawar da nata yanzu. Fuskarta da murmushi ta zagaya inda Daddy Imran yake tana gyara galenta ta duƙa tana gaishe shi. Da kulawa ya amsa mata da tambayarta fatan dawowa lafiya?. Kasa amsawa tayi. Sai ma ta koma tambayarsa ya su Ammie da Lolo da Yaya Khalifa?. Yace mata suna lafiya maybe ma ta gansu sun zo anjima. Tayi fatan ALLAH yasa su zo ɗin kafin ta maida akalar gaisuwar tata kan Dadah. Dan cike da dakiya tamkar yanda suke gaishe shi a da ta ce. “Dadah ina wuni?”. “Kina lafiya?”. Ya amsa mata shima da normal voice batare daya kalleta ba. Ma'aruff da Ja'afar suka mintsini juna ta ƙasan table. Yayi da Ammar da Bilal sukai sigina da ido. Hakama su Aunty Ummi abin sai ya basu dariya. Sannan mamakin Nimrah na kashe su. Yarinyar akwai shegen wayo da iya taku. Su Shariffa dai babu damar magana saboda suna matuƙar jin nauyin Dadah. Garama Asma'u da Ruky kallon uba suke masa. Dan su basa jin Dadah nada banbanci da Daddyn su. Dan cike da farin ciki Ruƙayya ma dake fitowa a kitchen yanzu ta ƙaraso inda yake tana masa sannu da zuwa. Dadah dake kallon ta da ɗan murmurshi ya amsa. Da ƴar tsokana ya ce, “Ina, ina Baby ta taddo Asma'u Mammah?”. Dariya Ruky ta sanya da kowa dake wajen tana rufe fuska. Hakama Mammah dake bashi amsa da “Maybe yau da daddare ne”. Sabuwar dariya suka sanya. Banda shi dake ɗan mitsilin murmurshi kawai idonsa akan Nimrah dake zubama Gwaggo Khadijah tuwo. Dan ita da Mammah shi akai musu. Saboda kawai yana son tazo kusa da shi ya ce, “Zoki bani tuwon nan nasu Gwaggo”. Yanda yay maganar da dakewa itama haka ta amsa masa da girmamawa. Bayan ta kammala da Gwaggon ta zagaya inda yake dan Asma'u ke zubama Mammah. Ata kusa da shi inda ta tsaya Adeel ne zaune. Ta ɗayan gefen kuma Daddy Imran. Dan haka ta tsaya ata wajen Adeel ɗin. Wani irin shige masa hanci da mayataccen ƙamshinta yayi sai da ya ja numfashi da ƙyar. Itama nashi ƙamshin ba ƙaranin tasiri yay mata ba a gangar jiki da ruhi. Ta dai danne kamar yanda shima ya basar Ta saka tuwo ta ɗauka spoon zata saka masa a kan plate ɗin kafin ta zuba miya ya faki idon kowa ya mintsine ta a cinya ba arziƙi ta saki spoon ɗin ya faɗi ƙasa. Kaf wajen nan babu wanda zai ce ga yanda akai, dan haka suka shiga mata sorry. Shi ko fishaa yama kalleta ya ɗauke kansa bai ce komai ba. Dole ta kai duƙe ƙasan table ɗin zata ɗakko spoon ɗin. Dama can hannayensa a saman jikinsa suke. Dan haka yay amfani da damar ya cafke ɗayan hannun Nimrah cikin nashi. Dan ta riga ta kai duƙe babu mai ganinsu. Sannan ya take cokalin da ƙafa.........✍️

In ban tonawa Dadah asiri ba ku ce ni ba Jikan Man Musa bace🤣🤣🤣🤣🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️.

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*

_(2k)_

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_ *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*