Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 20

Post

KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 20

.....refuse the bed. Then he showed her next to him. When she sat down, he just turned his eyes and blinked saying, "That's enough crying". She had to stop crying and go in to clear her mind. No one is knocking on the door. Looking at the door, he didn't move, let alone open his closed eyes. She directly said to come in without thinking about anything. Daddy Imran Doctor followed him. Nimrah stood up and greeted them. Both answered and focused on Dadah. He didn't know what to do since he came out for a long time and he felt his heart pounding. And since he left, he was calling his phone to hear if he had reached home, but he was still fighting. Even Ogansu called him and he was not picked up. Yay a small part with the pouring of mud. "Is Mr. Almu okay? Is Sanda still worried?" It was Mole who was asking him with his eyes closed. Malam Almu took a heavy breath and said, "Whly my mind is awake, Malam Buba. Sanda doesn't know where he is in this town. I made sure that even if he went to the bus station, he wouldn't find our village car. Then one of my friends at the station went and I called him...

Standalone post1,993 words

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 4_* _Chapter 20_

__________________ __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Kukan Nimrah ƙasa-ƙasa ya sashi buɗe idanunsa dake jazur kamar garwashi, ya ɗan ja numfashi da miƙa mata hannu alamar tazo. Takowa tai a hankali ta inda yake a baki-bakin gadon. Sai ya nuna mata kusa da shi. A ɗofane ta zauna, sai kawai ya maida idanun nasa ya lumshe yana faɗin, “Kukan ya isa haka”. Dole ta shanye kukan ta shiga share wayen nata. Babu wani jimawa akai knocking ƙofar. Kallon ƙofar tayi, shi ko bai motsa ba balle buɗe idonsa dake rufe. Kai tsaye tace a shigo batare da tunanin komai ba. Sai ko ga Daddy Imran Doctor biye da shi. Miƙewa Nimrah tayi tana gaishe su. Dukansu amsawa sukai hankalinsu akan Dadah....

∆~~~~∆~~~~∆

Zuwa yanzu hankalin Malam Almu ya fara tashi da rashin samun wayar Sanda. Bai san miyasa ba tun fitar daya dage sai yayi jiyan nan yake jin zuciyarsa na rawa. Ga shi kuma tunda ya tafi ɗin yake kiran wayar tasa yaji ko ya isa gida amma yaƙi shiga. Har Ogansu ya kira shi kuma ba'a ɗaga ba. Yay ƙaramin tsaki tare da zuba tagumi. “Wai lafiya kuwa Malam Almu?. Ko har yanzu damuwar Sanda ɗin ce da?”. Mole ne ke tambayarsa cikin tsaresa da idanu. Malam Almu yaja numfashi mai nauyi ya fesar, tare da faɗin, “Wlhy hankalina a tashe yake Malam Buba. Sanda bai san ko'ina ba fa a garin nan. Na tabbatar kuma a sanda ya tafi ko yaje tasha bazai samu motar ƙauyenmu ba. Sannan abokina ɗaya dake tashar yayi tafiya dan na kira shi ko Sanda ɗin yazo yace min ai shi yaje gida matarsa ta haihu”. “Eh lallai dole hankalinka ya tashi. Amma nake ganin ai Sanda ba yaro bane ƙarami. Ka ƙara masa lokaci mu gani, idan bai dawo ba ko baije gidan ba saika nema alfarmar masu gidan kabi bayansa. Ni sai na riƙe maka gate ɗin idan sun yarda. Tunda kaga yanzu basu wani damu da fita da driver ba zaman banza kawai nake yi”. “Aiko na gode malam Buba. Indai haka ne bari ma na kimtsa. Zuwa anjima sai na samu Hajiya da maganar, da safe kawai na kama hanya”. “Shike nan, ALLAH yasa a dace”. “Amin”. Malam Almu ya faɗa yana miƙewa ya shiga cikin ɗaki. Shima Mole miƙewa yay da waya a hannu ya fita wajen gate ɗin yana neman layin Dagger.....

(((((((@)))))))))

Yanzu ma dukkan abinda ya dace doctor ya masa. Ya ƙara masa allura guda ɗaya sai magunguna da yazo masa da su yace sai yaci abinci ya sha. Sai ruwan sanyi da yace a ɗan saka masa a jikin dan saukar zazzaɓin. Daga haka ya miƙe. Dai-dai da isowar su Mammah sashen. Dan wayar Nimrah da Imran ya ɗauke a jikin Dadahn ya miƙa mata tana fita falo dan basu damar duba shi kawai tai kiran Mammah tahau yi mata kukan wai Dadah bashi da lafiya. Shine fa hankalinsu ya tashi suka nufo sashen. A falo suka iske Nimrah tana kai-kawo. Suna gama hawowa ta gudu wajen Mammah ta rungumeta. Tashi hankalin Mammah ya sake yi, itama ta rungumeta cikin sigar lallashi amma batace komai ba. Sai su Gwaggo Khadijah ne ke tambayar miya same shi??. Bata samu basu amsa ba Daddy Imran da Doctor suke fitowa a ɗakin. Cikin mamaki yake tambayar su, Gwaggo Khadijah tace Nimrah ce ta kira Mammah. Bai ce komai ba face girgiza kansa, sai kuma yace su shiga to shi bari ya raka likita. Basu shigan ba kai tsaye, sai sukace Nimrah taje ta sanar masa. Koda ta shiga ta isar da saƙon su yaja sakanni bai buɗe idanunsa dake lumshe ba. Sai zuwa can ya buɗesu ya zuba su a kanta. Ƙasa tai da nata tana wasa da yatsun hannunta. “Waye ya faɗa musu?”. Yay tambayar a dake. Baya ta ɗan matsa na jin tsoro. Cikin in-ina ta ce, “Dadah kayi haƙuri naji tsoron ganin yanda kake yi ne”. Kansa kawai ya girgiza da faɗin, “Zoki gyara min filon nan”. A ɗarare ta ƙarasa inda yake, shi kuma ya yinƙura da ƙyar ya tashi zaune. Filon da ya tashi a kai ta ɗauka ta saka jikin fuskar gadon ata bayansa, shi kuma yaja bargon dake gefen ƙafafunsa ya rufa. Sai dai iya ƙugunsa yake. Sannan yace taje ta shigo da su...

★Babu wanda tausayinsa bai kamasu ba a cikinsu. Dan kallo ɗaya zaka fahimci baya jin daɗi, duk da kuwa shi mutum ne mai tsananin shanye abu da kame kansa. Amma yanda launin idonsa da jijiyoyin kansa ke miƙe raɗa-raɗa sai kamewar tasa ta gagara shanye komai. Addu'a sosai sukai masa, tare da fatan samun lafiya mai ɗorewa. Sannan Gwaggo Khadijah ta fara faɗan miyasa tun daren basu kirasu ba. Ƙaramin murmushi kawai yayi amma bai ce komai ba. Ita dai Mammah batama yi magana ba tun addu'ar da tai masa, tunaninta nakan ina Nabeeha? Dan ita ya dace su gani tare da shi ba Nimrah ba, kar dai Muhammad ɗinta ya zama mai fifita sashe akan sashe a tsakanin matan nasa. Yaje da Nimrah tafiya ya dawo sannan ya cigaba da kwana da ita alhalin Nabeeha ya dace ta amshe shi. Sun ɗan ja mintuna a ɗakin dan har Imran ya dawo abu dai na sukar Mammah a rai, shima sun gaisa sukai masa ya mai jiki, ya amsa musu da cewar da sauƙi ciwon kai ne kawai yay masa tsanani. In sha ALLAHU doctor kuma yace zuwa anjima kaɗan komai zai yi dai-dai, yanzu ma yace a sama masa abinci mai sauƙi yaci ya sha magani ya sake kwanciya. Sai a lokacin Mammah tai maganar ina breakfast da aka kawo tana kallon Nimrah dake lafe a jikinta. Nimrah ta ce, “Ga shi nan”. Tai maganar tana miƙewa inda yake.....

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Tunda Amimah tazo ta sake sanar mata Dadah ne fa baida lafiya shiyyasa ashe Imran yazo hankalinta ya tashi. A rikice take tambayar miya same shi. Amimah tace, “Ban sani ba Aunty, kece ya kamata kije ki jiyo mana. Dan su Mammah ma har sun zo sun fita, kuma yarinyar nan tun ɗazun tana tare da shi. Kinga sai suma ɗauka ke abin bai dameki ba ko.” Nabeeha dake jin kamar zuciyarta zata fito ta nufi sashen Dada, sai dai zuciyarta na'a cikin matsanancin tsoro musamman akan abinda ya faru tsakaninsu asubahin yau. A falo ta samu Imran yana waya, bata tsaya bi takansa ba dan wani jin tsanarsa take a ranta ta wuce bedroom ɗin da suka kwana jiya. Ƙofar kawai ta tura ta shiga batare da neman izini ba balle yin sallama. A dai-dai wannan lokacin Nimrah data gama haɗama Dadah tea ɗin da yace kaɗai zai sha ta isa gaban gadon inda yake. Yanda aka turo ƙofar ya saka zuciyarta bugawa, ta jiyo da sauri tana kallon ƙofar kamar yanda Dadah ya ɗago shima ya kalla wajen. Cikin ido Dadah da Nabeeha suka kalla juna, sai ta tsaya cak gabanta na faɗuwa. Nimrah kuwa kanta ta kawar kamar bataga komai ba. Cike da rashin ji da son ɓatama Nabeeha rai ta canja shawara, maimakon bama Dadah tea ɗin tabar wajen kamar yanda tai niyyasa sai kawai ta kai zaune a bakin gadon kusa da shi, duk da wajen baida yawa saboda yana zaune ne a baki-baki ƙafafunsa a miƙe a yanda su Mammah suka barshi. Nimrah ɗin ya kalla, sai ya ga fara'ar fuskanta ta ɓace ɓat, baice komai ba ya ɗan matsa mata danta zauna da ƙyau, dai-dai Nabeeha na ƙarasowa gaban gadon itama ranta a ɓace da ganin zaman da Nimrah tayin, sannan itace da mijin mizai sa ita ta zo, wannan munafunci ne kuma tasan Imran ne ya ƙullashi, zako tayi maganinsa wlhy. Sai dai cikin danne zafin da take ji ta furta, “Subahannallahi My D. Miya faru ne? Yanzu nake ji baka da lafiya, dama ciwon kan bai sauka ba har yanzu?”. Tai maganar tana hawowa gadon sosai ta ɗayan ɓangaren, ta kai hannunta a goshinsa, idanun kawai ya ɗan lumshe da ƙoƙarin jinjina mata kan nasa, bata damu ba ta sake sakko da hannun saman wuyansa. Wani irin abu yazo ya tokare maƙoshin Nimrah, sai dai ko kallon inda Nabeeha take bata sake yi ba. Sai ma kofin tea ɗin data miƙama Dadan. Nabeeha ta saki ɗan murmurshin ƙeta, dan a safiyar yau ta zauna tama kanta huɗubar shirya abubuwa masu yawa akan Nimrah. Ta saka a ranta zata ajiye shawarar kowa ta gina ra'ayin kanta tunda itama dai ai mace ce, sannan mutum ce ba robot ba balle ta zama abar control ɗin kowa. Tafi kowa sanin wanene Haysam, sannan tace ta zaɓi abinta matsayin miji, duk tsanani kuma ta yarda zata zauna da shi da halinsa. Mizai sa ta cigaba da zaman yin rayuwa a gidan aurenta tare da wata banzar yarinya. Dole ne ta kawar da ita. Dan akan Haysam wlhy sai inda ƙarfinta ya ƙare, ko Mammah data haifeshi dole ta bar mata shi balle wannan shashar yarinyar ƴar cikinta. Badai ita ta aiko Haysam da shatin kiss ba dana turare a jiya. Ta jira nata aiken dan ita a zahiri zata yi.........✍️

Ke wlhy ƙawata matsalar ki kenan🥱. Mi kuma ya kawo a zahiri zakiyi🥺? Ai ya hakan ne zaki sa a cimu da yakin🥲🚶.

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*

_(2k)_

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_ *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*