
Post
KIDA A RUWA BOOK 4 PAGE 19
..... not even the General has been looking for his position as NSA for a long time but he didn't get it. Dabo is also a member of this secret line, which is the same for UNIT ZERO, why he found him. Nimrah was looking at Dadah as if she was going to cry. In her mind, she was surprised to find him like this. After yesterday, they parted until bedtime, Dagger's conversation came back to her (Go to your husband today, let him reduce your rivalry and destroy him with nuts...). What does that mean? Why would Nabeeha do that? I don't believe you. But why is he willing? She had no one to answer, so she wiped away the tears that were about to fall from the woman's side as she sat down. When she found herself holding his left hand on his stomach, the drip was put on him. Her stomach was swollen, even though it was bigger than hers. There is a kind of soft head in the hand of a man, the man is also a veteran like their father. For the first time in her life, she laid her eyes on him. She looked at him more like a curmudgeon than ever. Don't let her lie, I swear, Dadah is the most beautiful person in the house. Especially now one keeps the hair on the face. And the hair is mixed with white s
*_Typing📲_*
*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*
*_GENERAL FICTION_*
_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._
*_BOOK 4_* _Chapter 19_
__________________ __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.........Koda ta shige shi ficewa yay dan Dabo ne ke kiransa akan wani babban al'amari daya taso. An kama wata mota da bomb a kusa da fadar shugaban ƙasa. Bama Dabo ɗin kaɗai ba har Janar tun ɗazu yake neman layinsa matsayinsa na NSA amma bai samu ba. Shima Dabo dan wannan layin na sirrin su ne daya shafi UNIT ZERO shiyyasa ya samesa. Sosai Nimrah ke kallon Dadah kamar zatai kuka. A ranta kam tana mamakin miya same shi haka bayan jiya lafiya lau suka rabu har lokacin barci, zancen Dagger ya shiga dawo mata (Kije ga mijinki dan yau kaɗan ya rage kishiyar ki ta halaka shi da ƙwaya....). Mi hakan ke nufi? Mi zai sa Nabeeha ɗin ta aikata haka to?. Kai ina bata yarda ba. To amma mizai sa taƙi yardar? Bata da mai bata amsa dan haka ta share hawayen dake neman zubo matan tana kaiwa zaune. Samun kanta tai da riƙo hannunsa na haggu dake a saman cikinsa, dan ana damar ne aka saka masa drip ɗin. Cikin nata ta rumtse, duk da yafi natan girma. Ga wani irin taushi kai bakace hannun namiji bane, namijin ma tsohon soja kamar Dadansu. Karo na farko a rayuwarta data zuba masa idanunta. Kallo sosai take masa irin na ƙurulla fiye da ko yaushe. Badan kar ace tayi ƙarya ba data rantse Dadah yafi kowa ƙyau a gidan. Musamman a yanzu daya ajiye gashin saje a fuska. Gashin kuma ya gauraya da tsilli-tsillin farin gashi da yay matuƙar ƙara masa kamala da cikar haiba masu irin shekarunsa da nutsuwa ta gama ratsawa da kwarjini na musamman. Tabbas kalmar Dattijo kalma ce mai daraja da malam bahaushe kan faɗa ga mutanen da shekaru suka fara matsawa a sahun ƙuruciya. Bata taɓa ƙara jin girma da darajar wannan kalmarba irin yanzu data gama sanin ai nahin HAYSAM ABDUL-RASHEED SHEHU. Domin kuwa duk namiji daya fara shiga shekarun dattijan taka da suka fara ne daga 45 zakaga al'amuransa sun dai-daita nutsuwarsa da kamewa sun yalwata. Sai dai in har asharari ne a shekarun samartakar sa.. Dadan su kuma kamili ne mai addini kowa ya sani.... Motsin da yay da hannunsa ya saka tunaninta yankewa. Tai saurin ƙoƙarin sake matsawa tana kallonsa. Sai kuma akai sa'a ma bai ko buɗe idanunsa ba ya cigaba da barcin. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi, sannan ta zuba tagumi tunaninta ya koma kan wayarta da Dagger....
[=][=][=][=][=]
Rayhana na gama zayyane ma First Lady abinda ke faruwa a gidan dake nuna sakamakon aikin data sakata ta saki wata dariya. Wayar ta ajiye tare da miƙewa ta fara kai-kawo a katafaren ɗakin nata. “Lokaci yayi da Adeel zai dawo shima”. Ta faɗa a zahiri tana sake kwashewa da dariya. Sai kuma ta sake komawa bakin gado tai zaman ƙafa ɗaya kan ɗaya. Waya ta ɗauka tai kira. Ana ɗagawa cikin gaisuwar girmamawa ta ce, “Ranka ya daɗe na cika aikin ku. Shegen ya kai ƙasa tun a daren jiya. Sai muje next”. Ban san mi akace mata daga can ba tai dariya da faɗin, “An gama, sai na jika”. Daga haka ta yanke tana dariyar dai. Kamar wadda ke magana da wani ta furta, “Wannan shine lokacin, lokacin da nake jira Hasiba. Nayi alƙawarin sai na mallaki abinda kikace yafi ƙarfina. Zan tabbatar miki ni ba kanwar lasarki bace, tun farko a bariki aka haifeni ba hayenta nayi ba kamar ke. Muje zuwa farkon wasa. Ni dake ɗan halak ka fasa.” Ta sake kwashewa da dariya. Tare da ware hannaye ta ce, “Barka da zuwa DUNIYATA NABEEHA. Barka da zuwa DUNIYAR HASIBA ADEEL. BARKA DA ZUWA DUNIYAR SU OGANA, HAYSAM”....
Tofa munga Boni. Dole na kaima ƙawata gulmar nan yau. Gata ga uwataresa ga miji kuma duk a komar First Lady 🏃🏼♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️🥱😂.
ππππππππππ
Sam Nimrah ta kasa cin abincin da aka kawo daga sashen Mammah. Tadai cirema Dada ruwan lokacin da taga ya ƙare har ya fara ja masa jini. Tun tana zaman kallonsa da tune-tune iri-iri akansa musamman akan zantukan Dagger dana mutanen da sukai kidnapping ɗinta kwanaki har barci ya ɗauketa a bazata. Ƙasa take zaune saman carpet a gaban gadon, sai dai ta saka ƙaramin fillo na kujera yanda yay mata ɗan tudun da har take iya ganin Dadah da ƙyau. Hannunsa na dama data cire masa ruwa ta saka ƙaramar plaster yatsun riƙe a cikin nata. Kanta kwance akan katifar tana fuskantar shi. Daga yanda yake kwance ya buɗe idanunsa da sukai matuƙar nauyi a hankali. Cikin sa'a kuwa suka sauka akan fuskarta datai yanayi kamar mai shagwaɓa. Hakan na nuna kodai mafarki take, ko kuma ta kwanta da wani tunanin a ranta. Idanun ya runtse da ƙarfi, saboda wani irin kartawa da cikinsa yayi na ciwo, ga zafi da yake jin jikinsa na ƙara ɗauka. Sake jin matsar cikin ya sashi damƙe hannunta sosai cikin nashi. A zabure ta farka da faɗin, “Wayyo hannuna Ruky miye hak.....” Maganar ta maƙale ganin saɓanin Ruky data ambata dan mafarkinta take. Cikin ƙarfin hali da jarumta Dadah ya buɗe idanunsa yana sassauta mata riƙon. Idanunta data ɗan zuba masa ta kawar dan har wani yarrr take ji a jikinta sakamakon kallon da yake mata ga idanunsa jazur. Muryarta da sanyi da kuma rawa-rawa ta ce, “Sannu Dadah ya jikin?”. Kansa ya ɗan jinjina mata alamar da sauƙi, a ransa yana mamakin yaushe tazo ɗakin? Rashin mai bashi amsar ya sashi buɗe baki da ƙyar ya furta, “Bani ruwa”. Kamar abinda take jira kenan ta miƙe zaram tana cire hannunta dake cikin nashi har yanzu. Hannun nasa ya kalla shima. Cikin lumshe ido da cizar lips ya yunƙura ya tashi zaune. Sai dai gaba ɗaya cikinsa a takure yake a ɗaɗɗaure, har takai ya kasa zama da ƙyau, ya kuma kai hannunsa na haggu ya riƙe shi tare da ɗan duƙewa daga yanda take zaunen. A haka Nimrah data fita ta ɗakko ruwa a falonsa ta dawo ta sameshi, dan hankalinta ma bai kai a ƙaramin fright ɗin bedroom ɗin ba. Cikin ɗari-ɗari ta iso gabansa, sai dai a kallo ɗaya ta fahimci halin da yake ciki. Da sauri ta kai durƙushe a gabansa tana mai ɗora hannunta ɗaya a cinyarsa tare da leƙa fuskarsa da yanayin damuwa. “Dada har yanzu baka da lafiya?”. Bai iya bata amsa ba tsahon sakanni, sai ma sake runtse idanunsa da yake yi. Hankalinta ya sake tashi. Sai ta miƙe tana faɗin, “Na shiga uku Dadah bari na kira Daddy, dama yace idan ka farka na kira shi ya daw....” Bata kai ƙarshen zancen ba da barin wajen ya riƙota da ɗayan hannunsa. Kusa da shi ya zaunar da ita. Sai dai baiyi magana ba saboda halin da yake ciki. Hankalin Nimrah ya ƙara tashi, ganin yanda ya dafe ciki kawai takai hannunta saman cikin itama. Kamar jira yake sai ya kama hannun nata ya ɗora saman cikin nashi sannan ya maida nashi akan natan ya danne. Karan farko ta saki kuka tana ƙara matsowa jikinsa sosai. Cikin rufewar ido ta ɗora ɗayan hannun ta saman fuskarsa tana ƙoƙarin ɗagowa. Ita a dole sai taga yanayinsa. Jikinsa kawai ya ƙara jawota ya ɗora kan nasa a kafaɗarta. Kuka ta ƙara saki da ɗora hannunta akan bayansa tana faɗin, “Dadah dan ALLAH ka bari na kira Daddynmu ko Mammah. Wlhy jikinka zafi sosai. Na shiga uku Dadah mike damunka?”. Yanda sautin kukanta ke shiga har tsakkiyar ɓargon jikinsa da tsokar jini ya sashi sassauta mata riƙon yana aro jarumtar dole ya yafama kansa. Cikin dauriya ya ce, “Bani ruwan na sha..” Da sauri ta matsa daga jikinsa ta yakito ruwan ta ɓalle murfin. Dama bata ɗakko kofi ba, dan haka ta miƙa masa gorar. Shiru yay yana kallon ruwan kamar mai nazari. Sai kuma ya basar. Maimakon amsa sai ya buɗe mata baki alamar ta bashi. Babu musu ta saka masa akan baki. Cikin ƙanƙanin lokaci ya gama zuƙeshi tas yana sakin ajiyar zuciya. Itama ajiyar zuciyar take saki tamkar ita tasha ruwan. Sai kuma ta koma jera masa sannu. Fuskarta ya ɗan tsare da idanunsa yana sakar mata ƙaramin murmushi, sai kuma ya kai hannu ya share mata hawayen.. “Kiddo bana son kuka. Kimin addu'a kawai na samu sauƙi”. Kanta ta jinjina masa. Sai kuma ta ce, “Dadah a kira Mammah?”. Kansa ya girgiza mata. “Karki kira kowa”. “Amma Dadah baka da lafiya fa. Jikinka kuma zafi sosai.” “Zai bari kimin addu'a kawai”. Yay maganar yana zamewa ya sake kwanciya. Dai-dai nan wayar Nimrah ta hau tsuwwa alamar shigowar kira. Jiki a saɓule ta miƙe ɗaukar wayar. Shi kuma ya bita da kallon ƙasan ido. Yanda tai sallama da ambatar “Daddy....” ya sashi fahimtar Imran ne. Sai kuma ya ɗan kallo shi. Kamar zatai kuka ta ce, “Daddy jikinsa kawai zafi sosai. Kuma yana riƙe cikinsa ban sani ba ko yana masa c....” Alama yay mata akan ta bashi wayar. Babu musu ta tako inda yaken ta miƙa masa. Dai-dai Imran na faɗin, “Nimrah baƙya jina ne?..” Gyaran murya Dadah yayi, hakan ya sashi fahimtar shine ya amshi wayar. Dan haka yace, “Zakina ka tashi kenan? ya jikin?”. “Alhamdullah”. Dadah ya bashi amsa a hankali. “Kayi haƙuri gamu nan zuwa da Doctor. Dama yace zaka tashi da zazzaɓi mai yiwuwa ma da ciwon ciki. Nima na ɗan fita kan wani case ne.” “Basai ka wani zo da Doctor ba, shrmenta ne kawai. Nasan da nayi wanka zan ware”. “Ba zancen shirme Haysam. Duk wanda ya sanka yaji muryarka yasan baka da lafiya. Kai dai gamu nan”. Bai jira amsarsa ba ya yanke kiran kawai. Wayar Dadah ya kifa akan cikinsa yay shiru. Dan tabbas baida lafiya, sosai kuma yake jin jikinsa..........✍️
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*
*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*
*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*
*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*
*_Akwai VIP Telegram 💃_*
*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*
*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*
_(2k)_
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (2k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.
_(1,500 CFA)_ *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_AREWAPEN (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*